You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin a yanzu ku ne kawai jin"

"dadinta kuma sanyin idaniyar ta. Allah ya raya ku, yasa masu albarka ne."

Ni zan yi kokari duk san da na samu dama in zo in ganku. Baban ki kuma ki daina cewa baban

"Jummai ne Babanki ne, idan kin yi sallah ki dinga yi masa addu a kina cewa Allah ya raba shi da KAIDIN MACE, kina jina ko? "

Rukayyah ta gyada kai cikin jin dadi. Tun daga lokacin ta kullaci kalmar kaidinkishiya a zuciyarta.

"Kullum addu arta kada Allah ya hada ta da kishiya, ko a lahira ne."

"Bayan sallar La asar Hajiyar ta yi haramar tafiya. Dukkansu suka yo mata rakiya bakin mota, tasa"

"direbanta ya sauke akwatin tsarabar da ta yo masu na kayan sawa  yan waje masu tsada da kayan wasan yara su jirage da motoci na Hafiz suka yi ta murna, ta kirgo kudi masu yawa ta ba Amina har sai da ta yi"

hawaye don ta rasa da bakin da za ta yi mata godiya.

"Rannan Rukayya take tambayar Mamanta, ""Wato Mama ita mace kaidi ne da ita? Dariya ta kama"

"Amina ta ce ba kowacce ba. Ta ce ana gane mace mai kaidi a fuska ne? Ta ce a a, sai ta yi ne za a gani."

"Rukayyah ta yi shiru cikin dan tunani, can anjima ta ce,  To Mama su maza ba su da kaidi? "

"Ta ce,  Ba su da shi, sai dai macen tafi karfinsu. "

"Ta ce,  Uyo! Shi yasa Anty Jummai ta fi karfin Babanmu, ya kore mu, saboda ita tana da kaidi? "

"Amina ta yi dariya sosai, surutun Rukayyah har tsoro yake ba ta kamar wadda ake kitsawa abubuwa"

"a tsakar ka, ta ce,  Ban sani ba, ki shirya ki je can Jalingo ki tambaye su. "

"Ta ce,  Wallahi ba za ni ba, kada kaidin ta ya shafe ni. "

(Mafarin kiyayyar Rukayyah kenan da kishiya).

"[12/17/2019, 19:14] Takori: W"

"ani makocinsu Alh. Labaran Mai Bargo ya fito neman auren Mama Amina, yana da mace daya da"

" ya ya takwas. Ba da jimawa ba ta yi aurenta bayan da ta yaye Hafiz ta bar su a hannun Goggo Salmai, wadda ita ma a yanzu ba ta sana ar komai."

"Suna ci suna sha ne daga cikin kudin da Hajiyar Legas take aikowa, Rukayyah ba ta wani damu da"

"auren da Mamanta ta yi ta tafi ta bar su ba, don gidaje uku ne kacal tsakaninsu da gidan Alh. Labaran."

"Kusan Rukayyah ita ta kashewa Mamanta aure, domin da sanyin safiya take sa Hafiz a gaba ko"

"karyawa ba su yi ba, su tafi kofar gidan su yi ta buga musu kofa, dole maigidan ya katse barcinsa ya fito ya bude masu in yana son kansa da kwanciyar hankali."

"Idan girkin Amina ne dole ya bar dakin da sanyin safiyar ya koma na uwar gidansa, don kuwa"

"Rukayyah zama take ta sa su a gaba ta yi ta zuba hira ta duk abin da ya faru jiya wanda Maman ba ta sani ba, komai Alhajin ya yi sai ta tambayi dalilin yinsa tun yana amsa mata har ya gaji."

Rannan ya fito wanka yana so ya canja kaya ba yadda zai yi don dakin falle daya ne ga Rukayyah ta

kasa ta tsare dole haka ya juya masu baya yana sanjawa.

"Rukayyah ta daga ido ta dube shi, yau ne rana ta farko da ta taba ganin shi ba riga ba hula, sai cewa"

"ta yi,"

"""Mama me yasa ki ka aure shi kan shi duk furfura? Ba gara baban Hafiz ba fari sol, bashi da furfura"

dubi bayan shi bakikkirin da shi.

"Amina ta mike ta rufe ta da duka kamar Allah ya aiko ta da kyar Alhaji Labaran ya kwace ta, ya ce,"

 Rabu da ita babanta take tayawa kishi.

"Ta kore su duka suka fita suna ta kuka, amma ba su koma gidan Goggo Salmai ba, sai suka je bayan"

kyauren gidan suka labe suna ta kuka kamar wasu marayu.

"Karfe goma ya fito zai tafi kasuwa, anan ya tadda su abin tausayi, ya kamo hannunsu ya dawo da su"

"dakin. Har zuwa lokacin ba ta huce daga kunyar da Rukayyah ta ba ta a wurin mijinta ba. Ta ce,"

" Don me ka dawo da su? Gobe goben nan in Allah ya kai mu zan maida su gidan ubansu, in ba haka"

ba Rukayyah ba za ta bar ni in yi zaman aure ba.

"Ya ce,  Yanzu dai ki yi hakuri ki ba su abinci, kina gani da alama ko karyawa ba su yi ba."

"Da ya fita ya dade yana tunanin hanyar da zai bi ya taimaki rayuwarsu Rukayyah, alhalin yana jin"

dadin zama da uwarsu amma ya sadaukar.

Yana dawowa ya ba ta takardar saki ya kuma rubuta a ciki cewa ba abin da ta yi masa shi da kansa

ya ga hakan ya fiye mai kwanciyar hankali.

"Amina ta yi ta kuka, ta ce idan ya yi haka ne don ta koma gidan su Rukayyah, ya yi kuskure, har"

abada ba za ta koma ba.

Ta tattara  yan komatsanta ta dawo gidan su dakinta na da. Rukayyah murna kamar me an samu

"abin dai ake so, ta ce,"

 To ba shi kenan ba mun huta zuwa bugun kofa da sassafe.

Ta kama ta da duka da kyar Goggo Salmai ta kwace ta.

"Ta dauki Rukkayyah ta maida ta makaranta, aka maida ita baya, wato ajihudu na firamare, da a"

Jalingo ne da tuni ta gama aji shida.

"Shi kuma Hafiz aji biyu, kullum tare suke tafiya, in ya gaji ta goya shi, in ta raka shi nasu ajin sai ta"

"tafi nata ajin, bayan ta gargade shi da cewa in sun tashi ya zo kofar ajinsu ya zauna ya jira ta kada ya sake ya yi wani wurin."

"Da yake ana riga tashin kananan yaran in sun tashi sai su taho gida tare har ta kare firamare, shi"

kuma lokacin ya yi wayo sosai.

"A lokacin Amina tana sana ar dinki da keken dinkin da Hajiyar Legas ta aiko mata, tana kuma samun"

"kwastomomi sosai saboda iya dinkinta. Shekaru goma da rabuwar ta da babansu Rukayyah kuma rabon su Rukayyah da garin Jalingo, amma sun tsaya sun gina rayuwarsu ba abin da suka nema suka rasa Allah ya rufa musu asiri ta kowanne fanni har Rukayyah ta gama ji uku na karamar sakandire."

A wani zuwa da Hajiyar ta yi ta shiga lallaba Aminar da ta amince a mayar masu da aure da Baban

"Rukayyah, domin hakika yana bukatar taimako, an kore shi daga aiki saboda wasa da aikin, ga masifar Jummai duk ta kadar da shi, ba ta bar shi da komai ba sai gidan da suke ciki."

Shi ma daga baya da taimakon addu o in da Hajiyar tasa ake yi masa wuyan shi ya yi dan kauri suka

"shiga fafatawa a kan rashin haihuwa, inda ya ce ta san ita ba haihuwa take yi ba ta kore mai mata da"

 ya ya.

Aminar da Hajiya ke bai wa labarin ta ce wannan kuma lalurarsu ce. Amma babu ni ba kuma zama

da Jummai har abada.

"Tun da Hajiya ta kyankyasa mai labarin mutuwar auren Aminah, ya susuce, ba shi a Gombe ba shi a"

"Jalingo. Yana rokonta ta yafe masa su koma da aurensu, ta ce atabau kuma haihata-haihata, ita da kara"

"zama da Jummai. Rukayyah na kara zuga ta da cewa wallahi kuwa ba za mu koma ba, Jummai tasa a sake koro mu da kaidinta."

"Shekaru goma sha biyu da rabuwar su lokacin Rukayyah har ta fara babbar sakandire, Hafiz kuma aji"

"daya, Allah ya nunawa Jummai iyakarta."

"Ta dawo daga aiki za ta tsallaka titi kenan wata DAF, ta taho da gudu Jummai ba ta lura ba tana ta"

"zuba sauri motar ta murkushe ta kanta ya fashe jini kamar an yanka rago, aka tattara kasusuwanta da tsokokin da suka makale kan titi aka yayyafa ruwa aka yi mata sallah aka binne."

Bayan sadakar arba in din Jummai da kyar da jibin goshi Hajiya Umaimah ta shawo kan Amina ta

yarda aka maida aurensu da Baban su Rukayyah suka tattara suka dawo Jalingo.

"Alh. Aliyu Dambatta ya so ya dauke shi ya koma aiki a daya daga cikin kamfanoninsa, ya ce shi kam"

"ba zai iya zama Legas ba, don haka Alhajin yasa hannu ya samar masa aiki a gidan talbijin na Jihar Taraba."

A

binda Usman ya fara yi da ya dauki albashinsa na farko domin ya yi (repenting) kurakuransa

"dagazuciyar iyalansa, shi ne daukar Rukayyah ya kai ta sabuwar makaranta ta Gwammatin Tarayya mai tsada wato (FGGC Bajoga, Gombe)."

Rukayyah na daga cikin (first set) wato daliban farko da makarantar ta dauka. Inda a nan ne su

Rukayyah aka yi kilin har da kilina. Ta san mutane sosai daga jihohi daban-daban.

"Surutun Rukayyah har girmanta ba abin da ya canza, sai dai da girman ya soma hawanta ta san a"

inda take yinsa. Ba ta da daukar raini ko kankani sai dai ko ka ki Allah dole ka kaunace ta domin kyawunta da ban dariyarta.

"Sannan tsiwarta kan burge mutane da dama, idan ta soma hura hancin nan har tsatstsafar da gumi"

yake.

"To amma fa Rukayyah na da rauni, abu kadan sai ya sata kuka. Sai dai lallashi kadan sai ya wanke"

"bacin ranta. Ba ta da hakuri, amma tana da afuwa. Ma abociyar tsaftar jiki da ta wuri. Don haka jikinta yake lukui-lukui, kamar na jarirai."

Sai kuma Hajiya Umaimah ta fiddo shi sarari da tsadaddun sitturu kala-kala ta yadda in ta yi

(dressing) sai ka dauka diyar wani hamshakin ce.

Duk kasar da ta je tsarabar Rukayyah daban ce kuma ta fi ta Nafisah. Nafisah ita ce autar Hajiya a

"wurin haihuwarta ne Hajiyar ta samu matsala da ta haihu aka juyar mata da mahaifa. Tsiranta da Saifuddeen shekaru bakwai, ta girmi Rukayyah sosai, amma in suna shawara sai ka ce wasu sa anni ne."

"Nafisah ba ta da aminiyar da ta wuce Rukayyah, haka ma Rukayyah ba ta da  yar uwar da ta wuce"

Nafisah. An yi mata aure tun tuni tana zaune a Jos tare da mijinta da danta dan shekaru biyu Abdulsamad.

Tun dawowar su Rukayyah Jalingo ne ta soma zuwa hutu gidan Hajiyar Legas. Duk hutu tana can

"suna tare da Nafisah, kafin a yi mata aure."

Abin da kowa na gidan ya sani shi ne babu jituwa kuma babu shakuwa ko kankani tsakanin

"Rukayyah da Saifuddeen, domin yawanci sanda take zuwa hutun shi yana can Walesdin Birtaniya."

"Rukayyah ta ki jinin miskilin mutum mai fadin rai da dagawa, magana wannan wurin Saifuddeen aiki"

"ce ja, kuma tsada gare ta. Ko ya ka ke da shi kuwa sai dai kai ka fara yi masa magana."

"Mutum daya ta ga Saifudddeen na fara gaisarwa wato Hajiya, amma ko mahaifinsa shi yake fara"

kula shi. Rukayyah kan ce a ranta ;

" Albasa ba ta yi halin ruwa ba, domin dai Hajiya mutum ce mai karfafa zumunci da inganta shi, mai"

saukin kai da rashin daukar duniya da fadi.

"To haka ma Nafisah, amma Saifuddeen da kyar a shekara ya je Jalingo sau daya, domin gaida Alh."

"Usman, abubuwan gaban shi sun fiye masa komai muhimmanci."

"Don haka ita sam-sam ba ta shiga shirginsa, daga gaisuwa shi kenan za ta tashi ta bar inda yake, ko"

"kwayar idanunsa ba ta taba kallo ido cikin ido ba, domin a ganinta hatta kallon da yake yi wa kowa na raini da wulakanci ne."

Ko ko ita kadai yake wa hakan? Allahu a alam.

"Haka lokacin aurensa ba ta wani zakalkale ba, wai ita kanwar ango, a dakin Hajiya ta yi ta boyewa,"

"ko an sata abu sai ta zame tasa Nafisha, don a ganinta ba irin su Saifuddeen akewa karar  yan uwantaka ba."

"Sau daya Hajiya ta taba aiken ta gidansa, da ke a unguwar Lekki, don ta kai wa amarya wasu sakonni."

"Ba irin dabarar da ba ta yi ba domin ta zillewa aiken hakan ya faskara, dole ta daure ta shirya direba ya kai ta."

"Irin tarbar da aka yi mata kadai da irin matar da ta gano, ta jinjina kai, ta tabbatarwa kanta mai"

"girman kai ya auro daidai da shi, ko kuma wadda ta fi shi."

"Ko wurin zama ba a ba ta ba, balle common ruwa wannan abin saukar bako. Babu tambayar wace"

"ce ke, ko daga ina ki ke? Ta ce sako ne daga Hajiyar Saifuddeen. Ta ce  to , shima da kyar."

"Shi kenan, iyakar maganar kenan ta mike za ta tafi, aka ce  ki gaida ita ."

Tun daga wannan lokacin Rukayyah ba kara marmarin zuwa gidan Yayan ba. Ta tattara su shi da

"matar tasa ta zuba a kwandon shara, sannan ta soma kame kanta a gaban Saifuddeen, wannan surutun nata, kankanba da raha, karambani da giringidishi ba ta yin su a gabansa, kada ya raina ta."

"In banda darajar zumunci da wallahi ko gaida shi ba za ta yi ba, to ya ci darajar mai daraja a"

"idanunta, ya ci darajar fitowa daga jikin Haj. Umaimah, ya ci darajar kasancewa da ga Alhaji Dambatta, da darajar shekarun shi. Shi yasa a duk inda ta gan shi cikin gidan kalmar  ina kwana ko ina wuni ke hada su. Shi ma a gare shi amsar guda daya ce a kullum, wato lafiya lau, ba tare da ya dubi inda take ba, in kuma a tsaye yake dama wucewa zai yi yana wucewar zai ce lafiya, ba tare da ya juyo ba kamar ba da"

dan adam yake magana ba.

"Idan ya yi mata hakan wani kulubi, kululu da takaici ke tasowa ya tokare ta a kahon zuci, ta ji kamar"

ta yi kuka ko ta amayo zuciyarta.

"Ko ta kudire ba za ta kara gaishe shin ba, in suna gaban Hajiya, ba ta bada goyon bayan wannan"

gabar ta babu-gaira babu dalili dole tasa su gaisa da juna ko sun ki ko sun so.

"Abin da Rukayyah ba ta sani ba shi ne, irin wannan kallon da take yi wa yayan nata, shi ma irinsa"

yake yi mata.

"Ya rasa wacce irin yarinya ce ita, mai tsananin jin kai da fadin rai, hadi da wuce gona da iri. A"

"ganinsa Rukayyah ba ta aje kanta anan kusa ba. Ko Nafisah diyar Aliyu Dambatta, ba ta gadara da dagawar da Rukayyah ke yi."

"Bai taba haduwa da yarinyar da ba ta taba yi masa kallo biyu ba, sai RUKAYYAH USMAN JALINGO,"

" yar sakandire ma kenan, wannan in ta shiga jami a yana tsammanin tafiya ma sai an yi mata."

"Dama an ce gwano bai taba jin warin jikinsa. A kullum tunanin Saifuddeen, shi ne Allah yasa wata"

"rana wata mu amala ta hada shi da Rukayyah, ya nuna mata iyakarta, ya nuna mata ita a cikin mata bera ce."

"Ya tsani Rukayyah saboda girman kanta, amma da ya lura Rukayyan na da matsayi mai girma a"

"wurin Hajiya, shi yasa yake iya takunsa."

"Bai taba nunawa Rukayyah wani abu na ashsha a fuska a gaban Hajiya ba, haka in a gabanta ne"

gaisuwarta kadaran-kadahan yake amsawa.

"Hajiyar ta rasa dalilin irin wannan kin jinin na Saifuddeen da Rukayyah babu gaira babu dalili, kai ka"

ce iyayensu ba nono guda suka tsotsa ba.

"To ita ma Rukayyar kamar ta san irin tunanin da yake yi a kanta, ba ta taba bari sun kebe da shi ba."

Ba ta taba bari wata mu amala ko yaya ta shiga tsakaninsu ba. Ba ta taba bari ta zauna a wuri in

yana nan ba.

"Da ya shigo za ta yi wuf ta mike, ta gaishe shi ta wuce, kai ka ce ajali ya kawo mata."

"Hajiya dai ta san Saifuddeen mutum ne mai ALHERI, da dumbin kyauta, amma ba ta taba ganin ko"

sau daya ya dauki kwandalarsa ya ba Rukayyah ba.

"Ita dai tasan shi mutum ne mai ALHERI ga kowa, amma bata san dalilinsa na zama mara alkhairi ga"

tilon  yar uwarsa ba.

*****

W

"ashe garin zuwan Rukayyah Lagos, duk da rashin kwanciyar hankalin da take ciki, da sassafe ta shiga"

"kicin ita da Rabi suka hadawa Hajiya da Alhaji karin kumallo na kunun gyada, funskason fulawa da miyar tantakwashi wanda Rabi ta kwaba fulawar tun daren jiya."

Suna aikin su suna hira tana bai wa Rabi labarin matsalarta da Aliyu.

Jinin Rabi da Rukayyah Allah ne ya hada shi kamar kawa da kawa.

"Rabi ba wata tsohuwa ba ce ba ta fi shekaru arba in ba, ita ce amintacciyar mai aikin Hajiya, kusan"

shekaru talatin kenan suna tare don tun tana kankanuwa aka kawowa Hajiyar ita daga Mayo-Belwa.

"Hajiya ce ta yi mata aure da direban Alhaji Mal. Audu, Allah ya jikan rai, suka zauna anan baskwata"

"din gidan. Rabi ba ta taba haihuwa ba, macece mai tsaftar gaske, da ta lakanci sirrin girke-girken gargajiya da na zamani daga hannun Hajiya, ga ta da amana."

"Hajiya ta jima tana gwadata ta fannoni da dama, don haka ita ke kula da shiyyar Hajiya gaba daya,"

"babu inda ba ta shiga, kuma ita ke dafawa Hajiya da Alhaji duk abin da za su ci tun lokacin da Hajiyar ta kamu da ciwon kafa, sai ko in Rukayyah ta zo hutu. To wannan aikinta ne."

Hajiya tana son girkin Rukayyah kwarai wanda take cewa ba shi da maraba da na Amina.

"Rabi ta gama jin labarin Aliyu kaf daga bakin Rukayyah sai ta yi murmushi ta ce,"

" Ke ni fa dama tsokanar ki nake, wannan Aliyun tunda na gan shi na san ba ajin aurenki ba ne, don"

kwata-kwata ba ku yi matching ba.

"Rukayyah ta bude baki cikin mamaki ta ce,  Ai kuwa Aliyu kyakkyawa ne har ma ya fi ni kyau, ke dai"

bar shi da karyar shi da ta bata shi a zuciyata.

"Rabi ta girgiza kai ta ce,  Ba maganar kyau ake yi ba, magana ce ta ajin rayuwa (Hierarchy of social"

"classes). Ke Rukayyah idan ba ki sani ba bari yau in sanar da ke, ke MATAR MANYA ce. Ba wai kowanne kwashi-kwaraf irin su Aliyu ba. "

"Rukayyah dariya ta yi da ta fiddo siririyar wushiryarta ta ce,  Su waye manya? Idan kina nufin masu"

"kudi, wallahi ba ni da ra ayinsu."

"Yo ni wane mai kudi ne ban gani ba a Jalingo? Amma na zabi Aliyu. NI mijin da nake san aure, ina"

jin har yanzu ba a haife shi ba.

"Rabi ta yi dariya ta ce,  Ba a haife shi ba? To sai yaushe ne? Sai kin tsufa?"""

"Ta ce,  Ba ki gane ba, ina nufin har yanzu Allah bai kawo shi ba."

"Kin ga na farko bana son mutum mai kudi da yawa, amma ina son mai ilmi da yawa, wanda yawan"

iliminsa ya rinjayi abin da ya mallaka.

"Shi mai kudi da yawa illolinsa yawa gare su, na daya kudinsa kan sa ya zamo mai girman kai, ta"

yadda ba zai nuna min irin soyayyar da nake mafarkin samu daga mijina ba. Sai dai ni in nuna masa.

"Na biyu kudinsa kan sa ya zama mai zara, wato mace daya ba za ta taba isar shi ba, tunda yana da"

kudin da zai yi ta neman su ko ya yi ta canza su kamar riga. Kin ga babu maganar na yi daraja da kima a idanunsa.

"Na uku, kudinsa kan sa ya zamo mai sakaci da Addininsa, sabon Allah ba wani abu ba ne a gare shi."

"Don haka ni nake da burin in auri karamin ma aikaci dan albashi mai tarin ilimi, wanda ba zan rasa ci,"

ba zan rasa sha a gidansa ba.

Mu gina rayuwarmu a kan kaunar juna da soyayyah ta Fisabilillahi. Wannan shi ne zaton da na yi

"wa Aliyu, amma ya yi min haka."

"Don haka ki taya ni addu a Rabi, Allah ya cika min burina. "

"Rabi ta nisa ta ce,  To amin, amma ba kowadanne masu kudin ba ne masu irin halayyar da ki ka"

ambata ba.

Babban misali ga shi nan a gabanki; Hajiya Umaimah da Alhaji Dambatta

Rukayyah tace  bari saka irin su Alhaji. Su wadannan mazan jiya ne ba n a yau ba. (They are

extraordinary). A wannan zamanin kam da wuya ake samun irin su biyu cikin dari (2%).

"To kin ga irin soyayyar su nake so, nake fata, nake buri, kullum suna masu farin ciki da juna, ba su"

taba gundurar junansu.

"Wallahi ko yau ki ka zauna a gabansu za ki ga Alhaji yana tarairayar Hajiya a gaban kowa, ni har"

kunya nake ji wallahi. Suka yi dariya.

"Rabi ta ce,  Zance na ya tabbata kenan, ko yaya ne dai akwai su. Ta kada kafada ta juya gira ta ce,"

" of course, kusan haka. Amma kalilan ne. "

Hajiya da ke zaune bisa fararen kujerun robar da ke daura da tagar kicin din tana sauraronsu ba tare

da sun sani ba.

"Ta dade tana tunanin maganganun Rukayyah, wadanda daga ji tana yin su ne heart and soul (wato"

"baka da zuci), tun daga karkashin zuciyarta. Ta ce a ranta ""Ko yaushe ne Allah zai kawowa Rukayyah wannan zabin nata???"""

*****

"[12/17/2019, 19:15] Takori: R"

"ukayyah ta jera komai a kan wani katon tray mai sulbi, Rabi ta biyo ta da butar shayi da kofuna"

"zuwa dinning wanda aka yi shi a kasan falon gidan, abin nufi sai ka taka matattakala uku tukunnan za ka isa tebir, suka ajiye, ta kintsa komai, ta koma dakin da ya zama nata a gidan ta salla wanka."

Ta dade gaban mirrow tana shafe-shafen ta da kakale-kakalen ta na farillah kamar kullum nan da

nan ta fito fes da ita.

Ta zuba bakin lesi (cotton) mai yarfin kananan furanni ruwan zuma da fararen duwarwatsu. Ba ta

"daura dankwali ba, ta yi parking dogon gashinta a tsakiyar kanta, sai ta zamo wata irin (cute). Dole in ka kalle ta sai ka sake waigowa, da tsammanin ko aljana ce ke son bude ma ido."

"Rukayyah doguwar Bafillatana ce, mai fasali da kira kamar ta kalangu, lebban ta jazur suke, kamar"

"na jaririya ma abociyar tsotso, kuma masu taushi  yan sirara kamar reza aka sa aka yanka mata daidai yadda take so."

"Sirrin kyawun fuskar Rukayyah, yana cikin idanunta da kumatunan ta lukui-lukui, idanun kuwa ba"

"farare ba ne, wasu irin blue-blue ne, tamkar na kyanwa a cikin duhu."

"Sirrin kirarta kuma yana cikin takunta; a duk san da take tafiya, illahirin jikinta rangaji yake, kuma ba"

"ta sauri, wannan halitta ce amma ga yawancin mutane, yanga ce kawai."

"Tana cikin shafa wet lips ta jiyo Hajiya na kwala mata kira, ta ajiye ta fita da dan hanzarinta tana"

"amsawa. Hajiya da Alhaji ne bisa tebir ta karasa gabansu ta durkusa tana gaishe shi, yana kada mata  yan yatsun shi biyu suna bada kara kas-kas-kas!"

"Kamar yadda yake amsa gaisuwar ta a kullum ya ce,  Rukiki-Rukiki, rakakas-rakakas ta Aliyu mai"

komai dozen !.

"Ta yi dariya cikin jin kunya ba tare da ta ce komai ba, sai dai a can cikin ranta ta tsani wannan wakar"

"da Alhaji ke mata, shi kuma kamar ya san ba ta son, duk san da suka hadu sai ya yi mata, ya ce,  Na je gidan mutuniyar ki jiya (Nafisah), Abdulsamad aka yi wa (operation) tana ta cigiyar ki, wai don Allah a tura mata ke ko sati ne ki yi mata tunda kin kare makaranta. "

"Hajiya ta yi farat ta ce,  Ba dai yanzu ba, Rukayyan da ke rikici da ubanta ba a warware ba, ita ce za"

ta tafi wani gari har Plateau?

"Zauna nan ki ci abinci kin je daki kin boye, na fi so in dinga ganinki a kusa-kusa. Cikin jin nauyi ta ja"

"kujerar da ke kusa da Hajiyar ta zauna, ita Hajiya har yau ta kasa gane ita nauyin Alhaji take ji."

"Ya ce,  Hajiya mai Rukayyah, na ga alama ke ki ke daurewa Rukayyah gindi ku ke yi wa Usman fin"

karfi.

"Ta ce,  Ba wani daurin gindi, shi dai rigimarsa da kafiyarsa ta tsiya ke hada shi da kowa, haka kawai"

"zai kafe sai ya aura mata dan karya?"""

"Abin ya bai wa Alhaji dariya, ya ce  Dan karya kamar yaya? "

"Ta kwashe duk labarin da Rukayyah ta ba ta ta gaya masa, ta kare da cewa,  Don haka gobe insha"

Allah ka yi min izini in je in same shimu yi wacce za mu yi. Idan gajiya ya yi da ita ni ina so ya bar mini.

"Allah zai kawo mata miji daidai ita, har nawa Rukayyan take? Bana jin har yanzu ta cika shekaru"

ashirin a duniya.

"Ya ce, ""Aliyu kam bai kyauta ba, ga shi na gan shi nutsatstsen yaro."

"Ban da abun shi ai gadanga basa faduwa a neman aure, ko ni tsofai-tsofai da ni na je neman kamar"

"Rukayyah da gudu za a ba ni saboda darajar mai sunana, ba sai na yi karya ba balle kuma shi (at his thirteith)."""

"Hajiya ta balla masa harara, shi da Rukayyah suka dinga yi mata dariya. Rukayyah ta girgiza kai a"

ranta ta ce wato tsofaffi kenan ma sun san kishi balle mu?

Wani lallausan kamshi da Rukayyah kan ji a cikin gidan lokaci-lokaci na

Please Login or Register in order to submit comment