You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ke bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali, gami da kulawar iyalinsa, ba wai shi ya wanzar da muhimmin lokacin shi wurin kula da su ba."

Sannan yana da iyali. Ba kowacce mace ce za ta yarda ta zauna da Rukayyah ba a wannan suna dai da

"aka kira ta da shi na MAHAUKACIYA. Ina ya samu lokacin kansa ma balle na mata biyu, har da maras lafiya, wadda ku ka ce min ko sallah sai an koya mata?"""

Alh. Aliyu a nutse yake sauraronsa yana murmushi yana kuma mamakin hali irin na Usman kullum ayana

abu kamar bai taba zuwa makarantar boko ba. A raunane cikin sagewar gwiwa Saifuddeen ya dago ya dubi kanin mahaifiyarsa ido cikin ido ya ce.

"""Wallahi-wallahi Baba ni ba tausayin Rukayyah nake ji ba, don ban ga abin tausayin a tare da ita ba."

"Mutumin da ke da cikakkiyar lafiya, ji da gani, babu abin da ba zai iya ba."

"In gaya maka gaskiya, na samu kaina cikin wani hali na matsanancin so da kaunar Rukayyah, tun lokacin"

da al amarin nan ya same ta. Ni kadai na san halin da zuciyata ke ciki.

Kuma ko da na zo nan ba daurin auren Rukayyah na zo ba. Na zo ne da tunanin watakila akwai wani

ALHERI da Allah ke nufin zuwan nawa da shi.

"Don haka ka taimake ni, kada ka raba ni da wannan alherin da ke cikin auren Rukayyah. Tana da lafiya,"

"ko ba ta da lafiya, ba abin da ya dame ni ba ne."

"Abin da na sani shi ne ita Rukayyah kanta nake so, ba wani abu nata ba. Ina mai yi maka alkawarin cewa"

"zan zauna da Rukayyah muddin rayuwata, ta samu lafiyar ta ko ba ta samu ba."

"Zan yi kokarin in raba nawa tunanin biyu, in ba ta rabi, in har akwai halin yin hakan. Rokon ka nake kada"

ka raba ni da ALHERIN da ke tare da Rukayyah. Ni na ce naji-na-gani a kan me za ka damu kanka?

"Alhaji Usman cikin sarkewar murya domin Saifuddeen ya bi ya daddaure shi da jijiyoyin jikinsa ya ce,"

 amma& .amm& .amma fa Saifuddeen ko shekara ba ka yi da yin aure ba& .

"Alhaji Aliyu ya soma harzuka, (abin ki da dama ina lafiyar kura& ) Ya ce,  Ka ga Usman dukkaninmu nan"

"muna da abin yi. Don haka in za ka ba shi auren Rukayyah, ka yanka sadakin ta yanzu in biya."

Ina ruwanka da yadda zai yi ya zauna da ita? Mai daki ba shi ya san inda yake mai yoyo ba? In kuma

"Aliyun naka za ka yi ta jira to Bismillah, ni nan jirgin karfe shida zan hau in koma don haka kai muke sauraro. "

"Alhaji Lawal wani abokin Alhajin ya ce,  Kwarai kuwa, wannan zance naka Alhaji haka yake. Kuma"

Saiffuddeen ba dan uwanta ba ne?

Shi ya fi kowa cancanta da ya aure ta cikin halin da take don ya san ciwon ta ya san mutuncin iyayenta ba

kamar bare ba.

Sannan wannan share hawayen da ya yi maka godiya ya kamata ka yi masa ba wai ka tsaya kana zakule-

zakule ba. Ba kowadanne maza ne masu zuciya irin ta Saifuddeen a wannan zamanin ba.

"Alhaji Usman ya rasa ta cewa, domin falon ya kacame da zantuttuka na masu hankali. Cikin nuna goyon"

bayansu dari bisa dari ga al amarin.

Ba shi da zabi ban da ya bude baki ya ce ya yanke sadakin Rukayyah da Saifuddeen naira dubu goma.

Alhaji Aliyu ya sanya hannu cikin aljihu ya kirgo naira dubu goma cif babu dadi babu ragie ya mikawa

Alhaji Lawal wanda Alhaji Usman ya wakiltawa waliccin Rukayyah.

Saura suka ce sun shida. Don haka aka ci gaba da gabatar da daurin auren kamar yadda shari ah ta tsara.

Dumbin jama ar da ke waje suka shaida daurin auren Rukayyah Usman Jalingo da Saifuddeen Aliyu Dambatta.

Nan da nan abokan aikin Alhaji Usman suka shiga yada al amarin cikin kafafen yada labarai. Mai shela ya

dauki bututun magana yana fada cikin annashuwa.

"""An daura auren Alhaji Saifuddini da Hajiya Rukayyatu, akan sadaki naira dubu goma lakadan ba ajalan"

ba. Allah Ubangiji yasa an yi a sa a ya tabbatar da ALHERIN da ke cikin auren.

"Hajiya Umaimah, wadda ke tsaye jikin famfo tana gabatar da alwalar sallar La asar, wannan bakon"

"al amari ya isa kunnuwanta. Ba karamin kidimewa ta yi ba. Sauri-sauri, gudu gudu ta yi sai dakin Aminah."

Ta yafa mayafinta ta nemi wuri mai tsabta ba tare da ta ce da kowa uffan ba wadanda su ma jama ar

"dakin sun kacame da hayaniyar farin ciki da tu ajjibi na al amarin Ubangiji mai ban mamaki, ta dungura goshinta cikin sujjadah."

"Sai da ta gabatar da sallar nafilah raka a biyu kwarara, ta daga hannayenta ta yi addu o i na musamman,"

"wadanda daga ita sai zuciyarta sai Ubangijinta suka san me ta rokawa Rukayyah da Saifuddeen. Sannan ta shafa. Ta je ta rungume Rukayyah, hawayen matsanancin farin ciki na zubo mata."

Mama Aminah mahaifiyar Rukayyah kam uwar dakinta ta shige ta boye. Lallai wani farin cikin gaba yake

"da a yi masa kuka, ko a yi masa dariya."

Rukayyah kam bin kowa take da kallo daidai. Sai dai kallo daya za ka yi mata ka tabbatar jikinta ya yi

sanyi irin na kowacce diya mace a yayin da aka daura mata igiyar aure.

"Ko kuma don ganin Hajiya na kuka ne, Allah masani. Wani kwaikwayo-kwaikwayon magana da take duk"

sai ta bari ta daina ta yi shiru da ita. Munaya ta matso gaban Hajiya cike da fara a take tambayarta.

" Hajiyar Legas, da gaske ne da Yaya Saifuddeen aka daura? "

Hajiya ba ta kula ta ba. Mikewa ta yi tana tattara komatsan ta cikin jakarta.

Ta bi Amina har uwar daki wadda ke kwance a gado kamar an yi mata duka saboda kaduwa da al amarin

"Ubangiji mai ban mamaki. Ta ce,"

 Ya za ki zo nan ki kwanta? Tashi ki tattaro min duk wani abu da ki ka san mallakin Rukayyah ne cikin

gidan nan. Jirgin karfe shida za mu bi mu koma.

"Amina ta yunkura ta mike zaune, cikin nauyin murya ta ce,  Tun yanzu Hajiya kamar ana korar ku?"""

"Ta ce, ""Yo me za mu zauna mu yi miki? Ba ki ji ni ba ne yau jin kaina nake kamar a gajimare, kamar an yi"

mun bushara da Aljannah.

"Wallahi Amina burina kenan na shekaru goma sha tara, ban taba furtawa kowa ba."

Tun ranar da aka haifi Rukayyah nake da wannan burin cikin raina. Sai dai na riga na yi wa kaina

"alkawarin ba zan taba yi wa Rukayyah auren hadi ba, auren da namiji zai wulakanta ta, sai auren da ake son ta."

"Ina ta jiran wata rana Saifuddeen ya furta min da bakinsa yana son Rukayyah, amma ina! Daga baya ma"

"na gane kin junansu suke. Ya je ya jajibo aure a Maiduguri, tun daga okacin na fidda raina a al amarin, na ci gaba da yi wa Rukayyah addu ar samun mijin kwarai wanda zai so ta ya rike ta tsakanin da Allah."

Ni kadai na san bakin cikin da nake kwankwada tun ranar da Saifuddeen ya yi aure. Matar da ba ta san

"darajar wadanda suka tsugunna suka haifa mata shi ba, ai ba abar tutiya da ita a matsayin suruka ba ne."

"Kullum na daga ido na dubi nagartacciya Rukayyah a gabana, tana ta haba-haba da ni da Alhaji, sai na yi"

dakacen INA MA A CE matar Saifuddeen ce& ..!

"[12/17/2019, 19:16] Takori: Annurin da ke fuskar shi ya kau, kuzarin da ke tare da shi ya ragu. Ya yi sanyi"

"da cin abincin shi, idanun shi suka kara kadawa suka yi jawur fiye da dazu, shi bai ce eh, ba shi kuma bai ce a a ba. Duka Alhaji da Hajiya na lura da shi, amsar da ya baiwa Hajiya dazun ita din ya maimaitawa"

Alhajin.

 Da kyar ne& .

"Rukayyah ma ta ce,  Alhaji da kyar ne& .. Wato ta gane sunan wannan mutumin da Saifuddeen ke"

"magana da shi, ana yawan kiranshi Alhaji. Ba ta manta ba."

"Jikin Alhaji da Hajiya ma ya yi sanyi, suma suka samu kansu nan take a rashin son zuwa daurin auren"

Rukayyah. Ba su kuma da hujjah. Ko don ga dukkan alamu danlelensu baya so ne? Yanzu shi kenan daga wannan zaman sun rabu da Rukayyah?

Wannan hutun da take zuwa masu? Wannan girkin mai dadi da take yi masu? Wannan surutun nata mai

debewa Hajiya kewa? Wadannan hirarrakin nata masu cike da wauta da sangarta da ke mantar da Hajiya duk irin damuwar da take ciki duka daga yau sun zama TARIHI?

"Za su kai Rukayyah inda cikin tunanin ta da hankalinta ta furta ba ta so. Ta fada ta kara, gara ta bi uwa"

duniya. Lallai fa sai cikin rashin tunanin nata.

"Da lafiyar ta kalau, ta tabbata da yanzu Rukayyah na nan cikin mawuyacin hali, ko kuma watakila ta"

"haure, ta yi wani wurin& .."

"Ta kawar da wannan tunanin daga ranta, tunda kuwa ba abin da zai sa, ba abin da zai hana. Cikin muryar"

"lallashi ta ce,  Ai kuwa gara ka daure ka je. Da Rukayyah lafiyar ta kalau ba za ta ji dadi ba a ce ba ka je"

"daurin aurenta ba. Wannan zai kara tabbatar mata da tunaninta na cewa ba ka son ta& """

"A razane kwarai ya dago ya dubi Hajiya cikin kaasalalliyar murya ya ce,"

" Don Allah, Hajiya in tambaye ki? "

"Ta ce,  To tambaye ni? "

"""Ita Rukayyah ce ta taba ce da ke bana son ta? "

"Ta girgiza kai,  ko daya, ina dai lura da kai. Ko gaisuwar ta ba ka son amsawa, sai don ganin idona. NI dai"

"na san kai mutum ne mai ALHERI, amma ko sau daya ban taba ganin ka yi wa Rukayyah ba. "

"Ya yi ajiyar zuciya mai sanyi kafin ya yi murmushi cikin jin kunyar idanun Mama Amina, wadda zuwa"

"lokacin ta kammala cin abincinta ta mike ta yi wa Hajiya sai da safe ta nufi dakin da aka sauke su. Ya bata fuska ya ce,"

" Haba Hajiya, haba? Me yasa za ki yi wannan maganar a gaban Mama Amina? "

"Ta balla mai harara ta fiddo mai dukkan idanunta ta nuna kanta ta ce,  Ni ni ce uwar Rukayyah ba Amina"

ba.

"Ya ce kamar zai yi kuka,  To don Allah in dai wannan tunanin ne a ranki to ki daina. Ita Rukayyah ce dai"

"na ga kamar ba ta son kula ni, kuma ba ta so in kula ta& amma Hajiya mutum zai ki jininsa? "

"Rukayya ma ta ce,  Hajiya Yaya mutum zai ki jininsa?"" Sai suka bata dariya."

"Ya mike yana mai duba agogon hanunsa bai kara kallon sashen da Rukayyah take ba. Alhaji ya ce,"

 Hanzarta ka wuce dare ya yi.

Ya yi masu sallama ya juya ya soma tafiya kamar a kan kaya. Ya kasa juyowa ya dubi Rukayyah. Ya

tabbata daga yau ba zai sake yin tsawon awannin lokutan da ya yi yau tare da ita ba.

"Wadanda suka bude wani sabon shafi mai dumbin tarihi a cikin rayuwarshi, suka canza akalar rayuwarsa,"

"suka canza bahaguwar zuciyarsa, suka canza tunaninsa kwata-kwata zuwa wani sabon al amari da bai taba tsintar kansa a ciki ba."

"Rukayyah fa ganin Mamanta ya tafi, a hanzarce ta ture kujerar ta baya ta mike ta bi bayansa da dan"

banzan sauri. Hajiya ta mike da kyar da sassarfa ta cim mata ta rike ta. Rukayyah na fizgewa tana tirjiya.

Ganin za ta kayar masa mata Alhaji ya mike ya kawo agaji. Ya rike ta gam-gam yana lallashi.

" Haba Rukikiks, ta Aliyu mai komai dozen! Gobe in Allah ya kai mu da safe zai dawo& . "

Ganin ba su da niyyar sakinta sai tasa kuka da karfin gaske. Cikin wani zazzakan sauti da ke amo har cikin

kwakwalwarsa yana tafarfasa zuciyarsa.

"Gab da zai karasa fita daga falon ya juyo, ya yi mata kallon da a tunaninsa na karshe ne. Kuka take sosai"

tana miko mai hanunta na dama tunda Alhaji ya rike na hangun da karfin gaske.

"Bai sake juyowa ba, da sassarfa ya isa ga motarsa ya bude ya shiga. Mintuna goma ya share a zaune"

"cikin tunanin da baya da makama. Daga bisani cikin dauriya ya tada motar, masu gadi suka bude masa gate ya fita daga harabar gidan."

"A can cikin gida kuwa Rukayyah ta tara duk jama ar gidan a kanta, kuka take haikan wanda ya tada"

"hankalin Hajiya da Alhaji kwarai. Gefe guda ta samu ta takure tana ta yi, amma Amina ko lekowa ba ta yi ba."

Sai wajen karfe ukun dare ta gaji da kukan barci mai nauyi ya dauke ta. Ta bingire anan falo bisa carpet.

Hajiya ta ce da Asi ta dauko filo tasa mata ta zauna nan su kwana tare. Ita da Alhaji suka nufi sashin Alhaji da ke sama domin ba karamin gajiya su kai ba.

"Asi tasa filo gefen Rukayyah ta kwanta, to amma ta kasa barci. Motsi kadan ta juya ta dubi Rukayyah"

"tana mai tuno kacaniyar ta tun tana kankanuwarta tana kissimawa cikin ranta, wai yau Rukayyah  yar hidima  yar kacaniya  yar komai da ruwanki ce sai yadda aka yi da ita."

Ta yi ta kuka tana sharewa da gefen mayafinta. Ta kara jin tsoron Allah cikin zuciyar ta ta kuma kara

yarda da cewa dan adam ba abakin komai yake ba a wajen Ubangiji. Daga karshe mikewa ta yi ta dauro alwala ta dasa sallah (Kiyamullaili)tana mai rokawa Rukayyah sauki.

*****

D

"aga Alhaji har Hajiya, babu wanda ya zaci Saifuddeen zai je daurin auren Rukayyah, musamman saboda"

"yanayin da ya nuna, jiya. Amma ga mamakin su shine mutum na farko da ya fara doka masu kofa da horn din motarsa a wayewar garin. Sai walkiya yake cikin manyan kaya,  yar ciki da wando da babbar riga ta koriyar shadda (Getzner) babbar, inda duk ya gitta kamshin turaren nan nasa na (Marks& Spencer) mai taushin kamshi ne ke tashi. Hularsa bisa gashinsa, ta sha kari ta tsayar car, ta fiddo zahirin (Billionnaire dan Billionnaire) Saifuddeen Aliyu Dambatta. Kuma babban yayan amarya, tunda dai Rukayyah ba ta da"

wani yayan da ya wuce shi.

"Su Hajiya ba su fito ba tukunna, sai kiciniyar Rabi da Asi a kicin. Rabi ta leko ta yi masa barka da zuwa, ta"

koma bakin aikinta.

Rukayyah ta mike a doguwar kujera da matashi a karkashin kanta. Barcin nan nata take cikin kwanciyar

hankali mai fidda zahirin kyawun fuskarta. Tun Pakistan din nan na jiya ne a jikinta ba ta cire ba sai dai kyakkyawan gyaran da ta yi wa gashinta ya wargaje amma ribbon din bai zame ba.

"Daf da kafafunta ya zauna, ya shagala sosai a kallonta. Rabi ta fito da filas din ruwan zafi a hannunta ta"

wuce ta aje a dining.

Tana fadi cikin ranta wannan ai shi ne irin mijin da ya dace da Rukayyah amma take musu a kai. Kalle su

"don Allah kamar wasu taurari guda biyu, sai haskawa suke."

"Ta zo za ta koma tana kara satar kallonsu da wutsiyar ido ya ce,  Am, Mama Rabi, don Allah zo ga key din"

"mota na ki ba Yohan ya fiddo ma Rak kayanta a bayan mota na. Ta zo ta russuna ta amsa ta ce to, ta fita."

"Da kanta ta dauko jakar Rukayyah wadda ba wani nauyi ne da ita ba, za ta wuce da ita dakin Hajiya ya ce,"

 Kawo nan in duba wani abu. Ba musu ta kawo.

"Ya zage jakar tana tsaye ya cire wayar Rukayyah, hankicinta da turarukanta da (Deo Spray) da wani dan"

karamin zoben ta na zinare mai matukar kyau. Rabi dai na tsaye tana kallon ikon Allah ya zuge jakar ya tura mata. Ta dauka ta wuce a ranta tana cewa

 Shi ko Babangida me zai yi da kayan mata? Zoben ma ai ba zai shiga yatsansa ba. (Tana kiran shi

Babangida ne yadda ta ji Hajiya na kira).

"Hajiya da Alhaji suka sauko daga benen Alhaji, sun yi tsaf cikin shigar GIRMA. Hajiya ta sha leshi dan"

ubansu. Alhaji cikin farar shadda (Wagambari) babbar riga  yar ciki da wando ya kifa hular zanna sai fesa kamshi suke.

Yana kokarin adana kayan Rukayyah da ya diba cikin aljihunsa. Daga Alhajin har Hajiya ba wanda ya lura

amma shi duk sai ya bi ya tsargi kansa na alamun rashin gaskiya. Alhaji ya washe baki cikin fara a ya ce.

"""A a, babban yaya za shi Jalingo kenan. Anya uwargida idanun ta biyu ta barka ka fito da wannan farar"

"safiyar?"""

"Ya dukar da kan shi yana murmushi a ran shi ya ce,  Alhaji kenan, wata rana zuma, wata rana madaci!. "

"A fili kuma sai ya ce,  Ai jiya da na koma ban tadda ita a gidan ba, wai ta yi yaji. "

"Alhaji ya samu wuri ya zauna yana cewa,  Ayya! Abu bai yi dadi ba. Daga Jalingo direct (kai tsaye) sai ka"

"wuce Maiduguri biko, ba sai ka sha wahalar dawowa ba. "

Ya girgiza kai  Ai ni Alhaji na yanke shawarar in rabu da ita kawai& ..

"Alhaji ya fiddo ido ya ce,  Kada ka fara! In ka rabu da ita ka san irin wacce za ka auro? Barta dai tunda an"

san halin ta sai a ci maganin zama da ita.

"Tunda ita ta nuna  yan uwanka ne kawai ba t aso su je in da take ba kai ba, to sai a yi maganin zuwan"

nasu don ku zauna lafiya& ..

"A raunane ya ce,  Ai kamar yadda ka ce din ne Alhaji, duk matar da ba za ta so ka da  yan uwanka ba, to"

kai ma ba kaunarka take ba.

"Alhaji ya yi murmushin su na manya mai sauti ya ce,  Ni ban ce ba. Ra ayina ne kawai na gaya maka."

Akwai wadanda son da suke wa mazan nasu ne yasa suke kishin  yan uwansa su rabe shi.

"Kamar ya fashe da kuka ya ce,  Don Allah a bar maganar Alhaji, kona min rai take. NI kam ba za ni ba, ko"

"da za ta yi shekara ne ba ta dawo ba, yanzu lafiyar Rukayyah ita ce a gabana& . "

Surutun su ya tada Rukayyah ta yi doguwar mika wadda ta hankada Saifuddeen gaba sosai kasancewar a

daidai kafafunta yake zaune. Ya mike ya koma hannun kujerar ya zauna yadda za ta ji dadin yin mikar ta sosai.

Ta bude idanunta ta kyalla su ta hango Saifuddeen a kujerar ta wanda ta kwana tana mafarkinsa. Ta

kuwa mike da hanzarinta za ta rungume shi duk da ya yi kokarin kaucewa. Tamkar wanda wutar lantarki

"ta ja. Ya nemi jinsa da ganinsa na wucin gadi ya rasa. Kafin ya yi ta maza ya yi kokarin saisaita tunaninsa, ya maida ta kujerarta ta karfin tuwo yana mai fadin."

"""Sorry, sorry, sorry RAK! I m not going anywhere& & am here forever with you&  Cikin wata irin lallausar"

"muryar da daga Hajiya har Alhaji, ba wanda ya yi zaton ta Saifuddeen ce."

Wata matsananciyar kunya ta kama su. Tunanin da ke addabarsu tun jiya suka kuma kwana da shi a

"zuciyarsu, ya kara dawowa ya cukuikuiye kwakwalensu. Shi kam bai ma san suna yi ba, gaba daya hakalinsa da nutsuwarsa ya tafi ga Rukayyah."

Da kyar ya samu ta hakura ta zauna amma ta kama aljihunsa ta rike gam kada ya sake arcewa. Sannan ne

ya maida hankali ga su Alhaji da ganinsa a takure yake. Hajiya ta basar ta hanyar cewa.

 Ni na rasa dalilin da yasa Rukayyah ta makalewa Saifuddeen kadai a gidan nan.

"Alhaji ya gyada kai ya ce,  Ai kamar jariri ne, uwar da ta fara ba shi nono da ita yake budar ido."

Saifuddeen ya ba ta madara a sanda take tsananin jin yunwa.

"To wannan kallon da ta yi masa a yayin da take cin abincin, ya zaunar da surarsa cikin sabon tunaninta"

da ya soma gudana.

"Ya zamanto shi ne mutum na farko da ta budi ido da shi yana mai nuna kulawarsa gare ta, a sabuwar"

rayuwarta. Don haka take jin shi kamar babarta.

"Hajiya ta gyada kai cikin gamsuwa da bayaninsa ta ce,  Haka ne. "

"Rukayyah ma ta ce,  Haka ne. Su duka suka yi dariya."

"Rabi ta shigo, daga can gefen Hajiya ta tsugunna cikin ladabi ta gaishe su, ta ce,  Hajiya ya jikin"

Rukayyah.

"""Alhamdulillahi. "

"Rukayyah ma ta ce,  Alhamdulillahi. "

"Ta ce,  An kammala abin karin kumallo a dining. "

"Hajiya ta ce,  Karfi da yaji dai kun maidani hawa tebur din nan, ko tausayina ba kwa ji. "

"Alhaji ya ce,  Haka za ki daure, tunda an rinjaye ki, cin abinci gaba daya Sunnar Ma aiki kenan. "

"Ta ce da Rabi,  In ce ko a babban tebur ki ka shirya ba a karami ba? "

"Rabi ta amsa da  Eh, ai na san gidan da baki. "

"Alhaji da Hajiya suka mike, Hajiya na cewa,  Dadina da ke kenan, sanin ya kamata. To kira Asi da"

Aminan.

"Saifuddeen ya ce,  Ki bude jakar Rak, na ga brush da maclean ki dauko. Ta amsa da to."

Ta dauko ta kawo masa har da babbar roba da ruwa cikin butar silba ta Hajiya. Ta russuna ta ajiye robar

"a gabansa ta ce,  Ko in wanke mata ne? "

" A a, kawo, je ki abin ki, an gode, kinashan hidima damu Mama Rabi, Allah ya saka. "

"Ta yi murmushi kawai ta mike ta yi kicin. A ranta tana cewa, ""Akwai iyayen gidan da suka kai ku hidima"

ga na kasa da ku da mutunta dan adam?

"Daga can dining Alhaji da Hajiya, Mama Amina da Asi duka sun juyo suna kallon diramar wanke baki da"

ake tsakanin Saifuddeen da Rukayyah.

Da farko ya matsa maclean din akan brush ya nufo bakinta da shi da niyyar ta bude ya wanke mata. Ta

"kuwa kama hakoranta ta cije gam da karfin gaske, don ta lura wannan dai ba abinci ba ne."

"Sai ya sa a nasa bakin yana cudawa a hakali kusufa-kusufa, ta kuwa yi masa kuri da ido cikin sha awa"

"tana murmushi. Ya fitar ya kuskure bakinsa ya zuba a cikin robar, sannan ya wanke kumfar jikin brush din ya matsa wani ya mika mata."

"Da sauri ta amsa, ya diga mata ruwa a kai ta shiga yin yadda ta ga ya yi cikin dari-dari tana mai kallonsa."

"Ya daga mata gira sai ta ci gaba da yi sosai. Sai da ya rike brush din ya ce,  Ya isa. Sannan ta bari."

"Ya sake zuba ruwa ya kuskure bakinsa ya zubar tana kallo, ta kuwa kawo hannu ita ma ya zuba mata, ta"

kurkure ta wanke brushdin.

"Ya mike ya ce,  To mu je wajen su Alhaji. "

"Ta kuwa juya ta dubi inda Alhaji yake, wato ta gane shi ake nufi, sannan ta mike ya yi gaba ta bi shi a"

"baya, suka zauna a kujerun su na jiya aka fara cin abinci."

"Har aka kare cin abincin babu wanda ya ce komai, kowa da tunaninsa. Tunanin Mama Amina, Alhaji da"

"Hajiya kusan daya ne. Shi ne yanzu in aka yi wa Rukayyah aure a haka, wane mijin ne zai juri wannan wahalar?"

Kuma a yadda Rukayyah ta nuna ba ta son kowa sai Saifuddeen anya raba su abu ne da zai haifarwa da

amaryar kwanciyar hakalin da likita ya ce ana so ta samu?

"Dukkansu ba su da amsar wannan tambayar, don haka shirun shi ne mafi alfanu."

"Da suka kare cin abincin misalin karfe takwas da rabi na safe, Alhaji ya duba agogon hannunsa na danyar"

"Azurfa ya ce,  Karfe goma daidai jirgin da na yi mana (Booking to Yola) zai tashi, don haka in suna da wani abin yi su kammala."

"Suka ce ai ba abin da za mu yi don ba mu zo da komai ba, ko jakar hannu ba mu dauko ba."

"Alhaji ya yi kiran Baban Rukayyah a waya suka gaisa, ya ce,  har da ni za a taho daurin auren Rukayyah,"

don haka sai ka tura mana mota filin jirgin saman Yola nan da karfe sha daya.

"Ya ce,  Ba damuwa zanturo motar ofishinmu. "

"Wato motar gidan talbijin. Ya yi dan jim, kamar yna jin kunyar ya tambaya kana ya ce,  Wai me ya samu"

"Rukayyah ne? Alhaji ba za ku gane ba Rukayyah makirar yarinya ce, annamimiya mai shegiyar kafiyar"

"tsiya. Babu ciwon karyar da ba za ta dorawa kanta ba, saboda ta tozarta ni a idon yaron nan da ya dauke ni kamar mahaifinsa."

Ta san ba ta son sa ta kawo shi? Kawai don ta maida ni karamin mutum a idon duniya.

"Alhaji ya yi murmushi ya ce, ""Usman, Usman kenan! Kafiya ko? Ai ina jin tsotsa ta yi a jinin ubanta, don"

haka  yar na gada ce ba  yar na koya

Please Login or Register in order to submit comment