You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan fahimce shi, kuma wai ba gida daya zai ajiye mu ba."

"Ya kare da cewa da ita ni na kawo mai Aliyu ba wani ba, balle in ce an yi min auren dole. Shi ba"

"karamin mutum ba ne da zai zauna yana daukar gutsiri tsomar yara, don haka ta tashi ta ba shi wuri tun ranta bai baci ba."

"Mama ta danne bacin ranta ta ce sai karyar da ya yi na cewa shi ma aikacin banki ne, alhalin dan"

"kasuwa ne, ta ce anya Daddy mutumin da zai gina neman auren shi a kan karya da karairayi abin amincewa ne?"

"Daddy ya ce da ita, ""Abin da ake nema a aure abu uku ne, shi ne nasaba, sana a da muhalli. Kuma"

"duk ya binciki Aliyu a kansu, babu wanda ba shi da shi."

"Don haka ta tashi ta ba shi wuri, kuma mu fara shirin mu daga yau, domin tuni ya turawa iyayen"

Aliyu sati mai zuwa su kawo sadaki a daura aure kamar wata wadda ake neman kai da ita.

"Shi ne na roki Mama ta bar ni na taho wajenki, na san ke kadai ce za ki iya tsawatarwa Daddy ya"

"fahimci illar da ke tattare da irin wannan auren tunda ba na so, auren soyayya ma a wannan zamanin kaka ya kare?"

"Wallahi yanzu bana son Aliyu daidai da kwayar zarrah, idan kuma Daddy ya dage a kan"

maganarsa to wallahi duniya zan shiga ba za ku kara jin duriyata ba. Ta ci gaba da kuka sosai.

"Dariya ta bai wa Hajiya don ta san duk barazana ce irin ta Rukayyah, amma babu inda za ta iya zuwa"

"tabar Mamanta, saboda son da take mata."

Rukayyah da ba ta iya kwana a ko ina daga wajenta sai dakin Maman saboda tsananin shakuwar da

"suka yi kai ka ce ba  yarta ce ta fari ba, duk wani Fullancin Amina in dai akan Rukayyah ne ta ajiye shi."

Ta ce  na ji daina kukan haka nan .

Ta dakatar da kukan amma ba ta fasa shashsheka ba.

Hajiya ta rungumo ta barin jikinta na dama tana jijjigawa a hankali kai ka ce  yar goye ce take

"lallashi ba katuwar budurwa ba. Ta ce,  Bar ni da shi, jibi Litinin in Allah ya kai mu zan je da kaina in same shi har Jalingon."

Me ake da makaryacin mutum nima ban goyi baya ba .

Rukayyah ta ji dadi bakinta ya kasa rufuwa ta sunkuya ta kama kafafun Hajiya tana godiya. Hakika

ba tun yau ba ta tabbata a duniya baya ga iyayenta ba ta da kamar Hajiyar Legas (Sunan da ta likawa Hajiyar kenan tun tana kankanuwa). Yadda kuma take jin mahaifiyarta haka take jin Hajiyar cikin ranta.

****

"[12/17/2019, 19:14] Takori: ASALIN SU"

A

"salin kakan su Rukayyah Mal. Abdullahi Jauro, mutumin Jalingo ne iyaye da kakanni. Jauro Abdullahi,"

malamin Addini ne sananne a garin Jalingo.

"Malami ne mai karantarwa, ba shi da komai sai tarin ilimi. Matarsa daya, Ma u, wadda Allah ya"

azurta da haihuwar  ya ya biyu kacal ; Yahanasu (Umaimah) da kaninta Usman da suke kira Shehu.

"Tun sunakanana Jauro da Ma u suka rasu, ba su bar masu komai ba sai gidan da suke ciki da"

karsanoni uku masu shayarwa da shanu biyu.

Umaimah ita ta ci gaba da kula da kaninta Usman ta fannin zuwan shi makarantar boko da ta allo a

"kan lokaci, tsaftar jikinsa da abincin da za su ci."

A lokacin ita budurwa ce  yar kimanin shekaru goma sha hudu. Babu irin wahalar rayuwar da ba su

"gani ba, domin ita Umaima sai da ta kai ta da yin wanke-wanke da shara gidan masu kudi, sannan ne za ta yo masu guzurin dan abin da za su ci a leda ita da Usman, ta kuma samo masa kwancen kayan  ya yansu, ita ma tana samun kwancen zannuwa masu tsada daga Hajiyar da take yi wa aiki domin"

mutuniyar kirki ce.

"Su ba  yan Jalingo ba ne,  yan Kano ne. Kasuwanci ne ya kawo su Jalingo. Zaman Umaimah da Hajiya"

"Kubra wadda ta dauke ta kamar diyar cikinta yasa ta soma washewa tun daga cima mai kyau ga sittiru, uwa-uba kwanciyar hankali."

"Babu abin da Hajiyar ba ta sani game da su Umaimah ba, ta kuma fahimci cewa maraici ne ya"

"janyo mata ba wani dalili ba, da burin da take da shi na kaninta Usman, ya samu karatun bokon da ya kallafa rai a kai. Don haka ta ja Umaimar a jiki cikin amana suke taimakon juna."

"Aliyu Dambatta, kani ne ga Hajiya Kubra uwa daya uba daya. A lokacin da ya kammala digirinsa na"

"farko aka turo shi bautar kasa jihar Adamawa nan Jalingon. Ba inda ya yi masauki sai gidan Yayar shi, inda anan ne ya kyalla ido ya ga Umaimah, ya kuwa ce nan duniya babu wadda yake so sai ita."

Babu shakka Umaimah na daga cikin Fulanin uslin Taraba masu bayyanannen kyau irin wanda duk

"wahala, duk talauci kyawun su baya taba boyuwa. Balle Umaimah da ta samu zaman jin dadi tare da Hajiya Kubra, ta yi shar kai ka ce  yar cikinta ce, sai dai ita baka ce ta inda za ka gano bambancin su kenan."

"Hajiya Kubra ita ta shigewa dan uwanta gaba ta aura mai Umaimah, duk wasu abubuwa da ya dace"

"iyaye su yi wa  ya, ita ce ta yi mata."

A lokacin shi ma Aliyun ba shi da komai sai tarin ilimin boko ko gidan kanshi ba shi da shi. Don haka

"sun fara zama a wani daki cikin gidan iyayensa da ke garin Dambatta inda ta baro Usman yana ci gaba da zuwa makaranta a hannun Hajiya Kubra, ya kuma canji ayyukan da Umaimar ke mata."

"Shekarunsu uku cif cikin rayuwar maleji da taimakon iyaye, kafin Allah ya ba su dan su na fari. Kuma"

"a shekarar ne Aliyu ya yi gamon da katar da samun aiki da hukumar shige da ficen jiragen ruwa ta kasa (Nigerian Port Authority) reshen jihar Legas, bayan da ya kammala digirinsa na biyu."

Don haka suka tattara suka koma Lagos inda suka fara zama a gidan gwamnati. Da Usman ya

"kammala karatunshi na sakandire ta dauke shi, suka samar mai gurbi a LASU, inda za ya karanci aikin jarida. Don haka rikon shi ya dawo hannunta suka ci gaba da rayuwa tare."

"Ita ce uwarsa maigidanta ubansa. A lokacin Dambatta ya zama wani babban kusa a (Port Authority),"

ya fara yi masu ginin gidan da suke ciki a halin yanzu. Shekaru biyar ya kwashe yana ginin kafin su koma. Budi da nasara ta kowanne fanni ya rinka shigo masu.

"A yanzu haka Alh. Aliyu Dambatta, shi ke rike da igiyar (Ports Authority) na kasa baki daya. Ya kuma"

"mallaki jiragen ruwa bila adadin nashi na kashin kansa, wadanda ke saukewa al umma kaya, musamman"

"motoci daga Germany, America da Japan, furniture daga China, da duk wasu shige da fice na kasuwanci da ya danganci (overseas) ta hanyar jiragen ruwa."

"DAMBATTA SHIPPING, na daya daga cikin kamfanonin jiragen ruwa da ake tunkaho da su a Africa."

"Ba kayan jama a kadai suke saukewa ba, suna jigilar (passengers) masu sha awar tafiye-tafiye ta"

"jirgin ruwa, suna kuma sauke motocin noma da katafilolin ginin tituna daga Amurka su zuba a kamfaninsu na DAMBATTA MOTORS. Har ila yau suna sauke (containers) da a yanzu suka cika gari daga Ingila, domin sayarwa."

"Duka wannan yana tafiya ne a saukake da taimakon da daya tamkar da dubu, dan Dambatta"

jikan Dambatta ; SAIFUDDEEN ALIYU DAMBATTA.

"Ba a jima ba Alhjin ya yi (retire) daga gwamnati, ya zauna a babban ofishinsu na DAMBATTA"

"SHIPPING matsayin mamallaki (Proprietor), yayin da Saifuddeen ke matsayin Mai gudanarwa (Managing Director), na dukka kamfunan Dambatta."

"Wannan wani nauyi ne mai girma da  ya ya goma ya kamata su yi shi, amma Saifuddeen kadai ya"

"sharewa Alhaji Dambatta wannan hawayen, na rashin  ya ya."

"Bayan karatu mai suna karatu a kan (MarineLaw), daga jami ar (Wales). A yanzu haka rike yake da"

"igiyoyin dukkanin kamfunan shi kadai ransa daidai da rana daya bai taba gazawa ba. DAMBATTA GROUP OF COMPANIES, shi ne babban reshen su wanda ke a Birnin Tarayya, Abuja. Sauran kamfunan duka na karkashinsa, kuma anan ne Saifuddeen ke gudanar da yawancin harkokinsu, inda Alhajin ke kula da DAMBATTA SHIPPING da ke garin Legas."

"DAMBATTA MOTORS kamfani ne na motocin zamani zallah, wanda ke da reshe a Kwatano,"

"Porthercoat, Abuja da Lagos. Kamfani ne da ke shigo da sababbin motoci (latest) wato kirar jiya-jiya daga shahararren kamfanin nan (General Motors) din America."

"Wato dai daga makerarsu& & . Sai jiragen ruwan DAMBATTA,& & .. sai shagunansu& & .A kamfanin ne"

kadai za ka samu motar nan mai aiki da caji (Chevrolet-Volt) a Nigeria gaba daya. Duka suna karkashin DAMBATTA GROUP OF COMPANIES wanda Saifuddeen ke jagoranta.

Dayawa-yawan mutane kan kalle shi da fuskoki guda biyu; na daya si dan lele ne a wurin ubansa

"(Billionnaire) Alhaji Aliyu Dambatta. Na biyu mugun asharari ne, amma fa ga wasu kalilan mutane"

"(Makusanta da shi), wanda dumbin ALHERIN sa da kirkinsa ya taimaka ainun wurin ba shi siffar mutanen kirki, ya kuma rufe bakin duk wasu kananun zargi da za a iya yi a kansa."

"Haka auren da ya yi ba zato ba tsammani, a lokacin da kowa bai tsammana ba, yana kan gabar"

"murza tashen kuruciyarsa da cin karensa ba babbaka, ya shafe duk wani tabo-tabo da mai kurilla zai iya yi don son binciko hakikanin ashararancin nasa."

"Matashin da akiyasce zai yi shekaru talatin da biyu, kuma wanda ya dama, ya kutsa cikin"

ilmummukan kasuwancin ruwa daban-daban. Ko makiyinsa zai bada shaidar jarumtakarshi da hikimarsa wurin maida kobo ya koma dari.

"A tun tasowarsa, wato lokacin da ya karbo cikakkun takardun kammala karatunsa har zuwa digiri na"

"biyu, ya dora hannu a kan dukiyar mahaifin nasa, kimanin shekaru biyar a baya, tamkar wanda ke yi wa al amarin yayyafin rahmah. Komai ya bunkasa, yakara habaka cikin kudurar Ubangiji."

Har ta kai ga turawan Jamus da na Amuruka sun san da zaman DAMBATTA SHIPPING. Suka soma

"hayar jiragen su domin amfanin kansu, da son hada kai da su don cimma manufa daya duka ta hanayr shige da ficen jiragen ruwa."

"Idan ka dube shi, daga duba na farko, ka ga Hajiya Umaimah, koko ka yi tsammani da ne ga Usman"

Jalingo saboda tsabar kamanninsu.

"Bai debo komai daga bakaken Dambatta ba, dogo ne kuma mikakke da tsayayyun kafadu masu"

burgewa. Ma abocin faffadan kirji da kakkauran jiki.

"Sai kuma ya dan rankafo kadan, ta yadda zubin halittarsa ya bada kirar wani mutum mai tsararren"

"tsayi mai ban sha awa kai ka ce wani bako ne daga Casablanca (Morocco). Fuskar nan suwal, cikakkiya kuma zagayayya (rounded -face), ma abociyar gargasa ta gashi a kowanne muhallinsa wato gira, saje da gashin bakin da aka saita musamman ya hade da gashin habar (Man s pride) na sassalkan gashin mutanen Jalingo, baki kuma mai sheki, wanda ga dukkan alamu ba a taba gazawa da kulawa da adana"

shi ba.

"Sutturar shi a kullum suit ne, baki da ratsin fari, ko ko baki da ratsin grey wato toka-toka. Da wuya"

ka gan shi da launin wasu kaya daban ba wadannan ba.

"Baya amfani da rufaffen takalmi sai budadde na fata. Agogon hannunsa a kullum (silver) ne(swatch),"

baya amfani da (Golden). Madubin idonsa mai duhu ne (dark glasses) baya amfani da farin gilashi. (Wanda yake amfani da shi kadai a duk lokacin da yake son boye halin da kwayar idanunsa ke ciki).

"Design din shi a na komai daya ne,  yan gidan (Marks & Spencer). Haka motar hawan shi kowa ya"

"tabbatar guda daya ce tal (Opel-Astra), baka sidik. Sautin takun shi daya, baya taba canjawa. Idan ka ji ya canza taku, to tabbata ran shi ne a bace."

A sa ilin ne za ka ji shi yana taku da karfi kuma da sauri kwaf! Kwaf!! Kwaf!!! Kamar ya fasa (marble)

ko ko kamar ya kifa. (Ta hakan ne kadai Hajiyarshi ke gane ran shi ya baci).

"Ta fannin halayya kam kowa ya san yana da ALHERI, abin hannun shi bai taba rufe masa ido ba,"

"(Kullum bayarwa yake, kuma kullum kara samu yake), amman an ce Zuciyar Mutum& & Birninsa. (Sunan"

wani littafin Takori)

Mahaifin Rukayyah Alh. Usman Jalingo ba wani mai kudi ba ne sai rufin asiri. Tsohon dan boko ne

"dan ta-kife mai kifaffen hali da wani irin baudadden ra ayi, abin nufi (Abin duk da mafi yawan al umma suka raja a a kai he opposed it). Kafiya da rashin son wargi ta ko ina, wato ba a sa shi ba a hana shi."

"Ya yi aiki da ma aikatun gwamnati da dama, a yanzu haka dai da gidan talbijin din jihar Taraba yake"

"aiki. Daidadai gwargwado asirinsu a rufe yake, sannan a tsaye yake a kan ilimin  ya yansa biyar ta hanyar kai su makarantu masu kyau ko da zai kwana ya wuni bai ci abinci ba."

"Rukayyah ita ce babba, amma ko kadan babu jituwa a tsakaninsu, haka babu shakuwa ta da da"

mahaifi ko kankani tsakaninta da babanta. Kullum kowannensu kukayake da halin dan uwansa.

"Rukayyah na da wani kullaci a kan Babanta da shi kansa ya sani, don haka ne sau tari duk kafiyarsa"

"da bala insa yana shayinta, ya kan ce macijin sari ka noke ce, mai kaushin hali, fitinanniya, ba ta yi halin uwarta ba. Bayan a zahiri shi kadai take yi wa, amma ba haka ba ne."

"Ba ta yarda ya takura mata, yanzun nan sai ya neme ta ya rasa a gidan, ta yi yaji, gidan danginta na"

"wajen uwa a Gombe (inda nan ta tashi) ko Legas wurin Yayar da baya da kamarta, inda bai isa ya ce don me ba."

"Abu kadan zai yi (sanda tana karama) ta ce  Yanzu ne ya san mu  ya yansa ne?"""

Tun Maman na dukanta tare da bige mata baki a duk san da ta yi wannan furucin har ta gaji ta

"koma lallashi da nasiha, sannan ne Rukayyah ta sauko ta soma gaishe shi, ta kuma daina yi masa wannan gorin. Ta nemi gafararsa."

Rukayya na son uwarta fiye da ubanta. Wannan na da nasaba da sakin da ya yi mata da tsohon cikin

Hafiz mai bin Rukayyah bayan zaman ukuba da ta yi na shekaru biyu a hannun Jummai abokiyar aikinsa da ya auro rana tsaka.

"Suka tattara suka koma Gombe gidan iyayenta a lokacin mahaifiyar Mama Amina ta tsufa kwarai,"

"amma a haka take dama koko tana sayarwa don nema masu abin da za su ci, don mijinta baban su"

Aminan ya dade da rasuwa. Tare suke da Asi kanwar Maman a gidan ita kuma tana tallan gasara lokacin ba a yi mata aure ba.

"Don haka dakin Asin suka share suka zauna dukkansu, wannan ne mafarin shakuwar aunty Asi da"

Rukayyah.

A nan aka haifi Hafiz aka kuma yaye shi. Daga baya Asi ta samu miji wani malamin makarantar

firamare aka yi mata aure.

Banda tabarma da filo da kwanuka da buta da Maman ta tattara  yan kudin da ta taho da su daga

"Jalingo ba abin da aka kai wa Asin daki. Wannan bakin cikin da suka gani ne a auren Asi, yasa Amina yin zuciyar neman na kanta kada auren Rukayya ya zo hakan ta kuma samunta."

"Ta soma tuyar masa da kosai a tsahar Dukku, Rukayyah na rike mata Hafiz tare da wanke"

"robobin da kwastomomi suka yi amfani da su. Idan Hafiz ya ishe ta da kuka sai ta duma masa dundu ta ce,"

"""Wai ku maza duka haka ku ke ba ku da tausayi ne? To da kukan ka za ta ji ko da sakin da ubanka ya"

"yi mata ta zama mai tuyar masa?"""

"Rannan karaf kalaman Rukayyah a kunnen Amina. Ta dade tana mamakin furucin yarinayar,  yar"

"shekaru bakwai. Sai da suka dawo gida ta ce,"

 Yaki Rukayyah.

"Rukayyah ta matso gabanta ta zauna. Ta ce,  Me na ji kina fadawa Hafiz dazu?"""

"Rukayyah ta yi shiru ta ce,  To kar in sake ji, ke ma Babanki ne, kuma ni ba sakina ya yi ba, ni na ga"

dama na taho.

"Rukayyah ta zumburi baki kamar za ta yi kuka ta ce,"

"""Ni wallahi ba Babana ba ne, baban Anti Jummai ne. Ina gani yana sayo mata lemo da ayaba da"

"tsire suna ci, in na shiga ya koro ni. Ni wallahi ba Babana ba ne. Sai ta sa kuka."

"Maman ta yi shiru tana kallon ikon Allah, duk dai a kokarinta na wanke kiyayyar mahaifinsu a"

"zuciyarta, da ta lura ta samu muhalli mai girma a zuciyar yarinyar, ta ce, ""Kina makaranta ya aiko muku da naku, ranar Asi ta zo sai ban ajiye miki ba, na ba ta na ce ta kawowa Goggo gaba daya. "

"Rukayyah ta share hawaye cikin rashin yarda ta ce,  Wallahi ba sau daya ba ne, kullum-kullum. "

"Haushi ya suke Maman ta ce,"

" Ke don ubanki idan na sake jin irin wannan a bakinki, sai na yanke miki bakin kowa ya huta, kin ji"

na gaya miki.

Ta kama kunnuwanta ta murde tare da zuba mata rankwashi mai zafin gaske.

"Haj. Umaimah na Lagos ba ta san Usman ya rabu da Amina ba (Damo sarkin hakuri), sunan da ta"

rada mata kenan.

Domin ta je ba sau daya ba ba sau biyu ba ta ganewa a idonta irin cin kashin da Jummai da Usman

"suke mata. Ta yi fadan ta yi nasihar ta ja kunnen duka a banza, kamar kara zuga su take yi. Daga karshe ne ta yi fushi ta ce ta zare hannunta a kan al amarin iyalinsa, ya je ya yi duk abin da yake ganin ya yi"

masa daidai.

To zuciyar  yan uwantaka (laushi gare ta). A wannan watan dai ta ce bari ta zo ta ga halin da Amina

"da Rukayyah ke ciki, wadda Allah ya sanya mata matukar kaunarta tun tana jaririya saboda kamanninta da ita."

Ta yi wa Rukayyah tsaraba rankatakaf direba ya kawo ta kofar gidan.

"Ga mamakinta gidan a bude daga waje, amma daga ciki kowanne daki a garkame yake da kwado."

"Ta juya za ta fita, domin ta shiga makota ta tambaya, sai ta jiyo muryar Usman yana cewa."

"""Ga ni nan Yaya. Ba dai har za ki tafi ba?"""

"Ba karamin tsorata tayi ba, kafin ta nutsu ta juyo idanunta zuwa ga inda ta jiyo maganar. Usman ne"

tsaye a bakin tagar dakin Jummai kamar wani dan fursuna. Sai ta karasa har gabansa a hankali ta ce cikin dimuwa.

"""Lafiya? Yau Litinin kana gida ba ka fita aiki ba, kuma ansa kwado a kofar dakin. Ina matan gidan da"

"su Rukayyah?"""

"Yasa hannu yana yarfe gumi, maimakon ya ba ta amsar abin da ta tambaya sai cewa ya yi  Ashe"

Yaya Jummai ba ta da mutunci?

"Wai don ta ce in ba ta dubu biyar za ta je dubo kawarta a asibiti, na gaya mata ba a yi albashi ba"

"kuma ita ma ta sani tunda ofis dinmu daya,  yar dubu biyar din ita ta rage mini kuma da ita za mu ke cin"

"abinci har zuwa karshen wata, amma tasa rigima, ai dole sai na ba ta, don na hana shi ne tasa kwado ta rufe ni wai na daina zuwa aikin tunda ba abin da yake tsinana mata."

Kuma wallahi Yaya idan na dauko albashin nan ko tabawa bana yi bayan dubu goma da nake

"warewa wadda da ita muke cin abinci, ita nake kawowa sauran gaba daya, amma duk ba ta godewa. "

"Umaima ta yi salati ta sanar da Ubangijinta ta ce,  Yanzu ina Amina da yaran?"""

"Duk wani haushinsa da take ji sai ya kau, matukar tausayin shi take ji yanzun. Ba shakka ya fada"

"hannun hatsabibiyar mace wadda babu tsoron Allah a al amarinta, sai addu a."

"Ya ce,  Watanni tara kenan da ta matsa min sai da na sake ta na samu lafiyar bala in Jummai, kuma"

tun daga ranar ban kara ganin su ba.

"Hajiya Umaima don takaici sai ta sa kuka, tana yi tana fyace hanci da habar zaninta ta ce,  Kaicon ka !"

"Ka yi babbar asara da ka rabu da abokiyar rufin asirin ka saboda wannan tambadaddiyar. Yanzu dai gaya min tsakanin ka da Allah saki nawa ka yi mata?"""

"Ya sake yarfe wani ambaliyar gumin daga goshinsa, cikin matsananciyar nadama ya ce,  Wallahi da"

"farko daya na rubuta, amma Jumamai ta ce ba ta yarda ba idan har ban cika she su ba ita za ta fita ta bar min gidan."

"To ni kuma ina sonta sosai sai na rubuta ukun, ga shi yanzu abin ya zo ya dame ni, domin sai yanzu"

"na gane zalunta ta take kiri-kiri, ba ni kuma da yadda zan yi da ita& . "

"Umaima dai don haushi da takaici ba ta kara kallon sa ba, mota ta fada yana ta rokonta tasa"

"direbanta ya yanka kwadon da Jummai ta kulle shi da shi ya yi mata rakiya, ko gani ba ta yi sosai ta ce da direban su tafi Gombe."

"Ya yi parking a kofar gidan su Amina, Hajiyar ta fito, Rukayyah ta fara hangowa goye da Hafiz, kanta"

"dauke da kwanuka rankatakaf da kaskon tuya za ta shiga gidan, tausayi mai tsanani ya kamata, tasa murya ta ce,  Rukayyah !!!. "

"Rukayyah ta juyo lokaci guda ta yi fatalin ala tsine da kayan tuyar Mamanta, ta sheka da gudu ta ce,"

" Hajiyar Legas, Hajiyata !!!. "

"Hajiyar ta rage tsawo, yadda Rukayyah za ta ji dadin rungumarta sosai suka rungume juna."

"Mama Amina ta fito a fusace daga cikin gidan jin karar barnar da Rukayyah ta yi mata, dan ragowar"

"man tuyar duk ya kelaye ya kwaranyo har cikin gidan tana kimanta irin rankwashin da za ta yi wa Rukayyah fitinanniyar yarinya, don inda abin da Rukayyah ta tsana, to a rankwashe ta."

"A bakin kofar shigowa suka yi kacibus da Hajiyar. Ta bude baki tana mamaki ta ce,  Ashe ke ta gano"

ta yi watsi da kwanukan nan? To sannun ku da zuwa Hajiya. Suka karasa ciki ta ce da Rukayyah ta je ta kwaso kayan da ta barar.

"Ba su yi wata kwakkwarar gaisuwa ba Hajiyar ta soma kuka, Aminar ke rarrashinta, ta ce,  Babu"

"komai Hajiya, Allah ya yi iyakar zaman kenan."

"Ta ce,  Ni wallahi ban sani ba, kin san na yi fushi na ce ba zan kara dawowa ba tunda ni din ban isa"

in gaya masa ya ji ba.

"Daga baya na yi tunanin hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar, don haka ne na zo na tadda"

"wannan abin bakin ciki, shi ma yana can tasa ta same shi tun ba a je ko ina ba hakki ya soma dawainiya da shi."

Can na baro shi ta kulle shi da kwado baki gani ba wallahi abin tausayi don haushi ban jira ta dawo

"ba na taho nan, don in na sake muka yi ido hudu ban san abin da zan yi mata ba in huce. Allah ya baki hakuri Amina Allah ya huci zuciyarki. Tunda abin bana gyara ba ne balle a yi tunanin hanyar gyarawa."

"Goggo Salma ta shigo suka gaisa ita ma ta yi ta ba ta hakuri kamar ta tsinke harshenta, su duka suka"

"koma suna lallashin Hajiyar, sai ta ce ni yanzu alfarma daya za ki yi min ki ba ni Rukayyah in tafi da ita ta dinga debe min kewa ke ma ki samu saukin wasu wahalhalun."

"Karaf! A kunnen Rukayyah da ke shigowa ta koma jikin Mamanta ta lafe kamar kyanwa ta ce, ""A a"

"Hajiyata ba zan biki ba, kada ki kai ni gidan Baban Anty Jummai. "

"Ta ce, ""Ba zan kai ki ba Rukayyah wallahi ba zan kai ki ba, wajen Nafisa zan kai ki. "

"Ta yi dan tunani can ta ce,  To Hajiyata, idan na biki wa zai dinga goyawa Mamana Hafiz, idan tana"

"tuyar masa? Wa zai wanke kwanukan da za a zubawa mutane masa?"""

"Maman taso ta doke bakin Rukayyah mai shegen surutun tsiya, amma dai ta bari sai Hajiyar ta tafi."

"Hajiya Umaima ta yi salati ta ce, ""Amina tuyar masa ki ke, ina raye ?'"

"Idanun Amina suka ciko da kwallah, ban da abin Hajiya in ba ta yi tuyar masa ba, me za ta yi? Ita ba"

"miji ba ita ba aiki ba ga  ya ya ga gyatumarta da ta tsufa ainun. Ba ta amsa mata ba, kuma ba ta da niyyar amsawar. Ta ce"

 to don Allah don Annabi daga yau kada a kara tuyar masarar nan. Na dauki nauyin duk wani abu da

za ku kashe daga yau har illa masha Allahu.

Za a bude miki (account) anan duk wata ki je banki ki amso. Sittirun Hafiz da na Rukayyah kuwa duk

na dauka in ce ko shi kenan?

Ta juya ga Rukayyah wadda ke ta murnar jin an ce an daina tuyar masa ta huta da wahalar wanke-

"wanke da kai nika, ta ce"

" Rukayyah na ji uzurin ki. B azan so raba ki da mahaifiyarki ba kam,

Please Login or Register in order to submit comment