You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke"

kara sakin juyi cikin jin dadin barcinta.

Shiru-shiru Alhaji ya ga ba su da niyyar fitowa. Ya dubi agogonsa ya mike tsaye yana cewa da Usman.

" Anya mutanen nan na da niyyar fitowa? Me suke yi ne?"""

"Shi ma ya mike ya ce,  Bari in dubo su in gani. "

"Ya shiga cikin gida. Tun daga tsakar gida yake cewa,  Yaya ki fito mana, kun bar Alhaji yana ta jira kin"

biyewa Amina za ta koya miki kailula& .

"Yana shigowa ya tadda su duka sun yi jugum-jugum a gabanta, a can gefe kuma Rukayyah ce ke barci, ita"

"kuma Hajiyar ta harde kafa sai shan kamshi take yi ya ce,  Lafiya? A a kai Saifuddeen daga aikesai ka share gindi ka yi zamanka, ka bar Alhaji yana ta jiran ku? "

"Ya juya ga Hajiya ya ce,  Alhaji ya ce ki fito ku tafi nan da karfe shida da rabi jirgi zai tashi, yaushe har ku"

ka je Yola?

Shi sam bai ma lura da wata Rukayyah da ke barci ba. Da ganin Yahanasu (Umaimah) ya san yau

"rigimarta ce ta motsa, ko dai da Alhaji ko da Saifuddini. Ta juyar da kai wani gefen daban, tana taunar goro, gurus-gurus, gururus rus-rus, ta ce,  Rukayyah ce ke barci, sai ta tashi za mu tafi. "

"Haushi ya kama shi, kafin ta ankara ya takarkare ya zubawa Rukayyah duka a baya. Ba shiri ta tashi a"

firgice tana zazzare ido. Sannan ta bi Baban da kallo cikin tsoro don wannan abu ne da ba wanda ya taba yi mata. Ya daga gira ya ce.

 Yauwa! To tashi ku tafi. Yanzu wannan yarinyar ta isa Alhaji ya zauna yana zaman jiranta ta tashi daga

barci?

"Hajiya kamar ta yi kuka ta rungumo Rukayyah ta ce,  Amma wallahi Usman ban san ba ka da imani ba sai"

"yau. Ana bukatar yarinya ta samu nutsuwa da hutu, ko tunanin nata ya dawo, shi ne za ka kara lalata al amarin? "

"Dariya ta ba shi sosai ya dara ya sake darawa ya fita yana cewa,  Kada ya dawo din, wannan fitinanniyar"

"yarinyar  yar kankanba da za ta yi zamanta a hakan ai da an huta, da lau take kya ji gidan nan cikin lumanar da ki ka ji shi? Ni kan ku fito ku tafi, bana son abin da zai bata ran Alhaji. "

"Saifuddeen ya karkace kai ya kwantar da murya ya ce,  Hajiya tunda barci za ta yi, a barta mana mu tafi."

In Allah ya kai mu (next week) sai in zo in taho da ita& .

"Ai kamar dama jira take ya tanka. Wata uwar harara data zuba masa, ta sa shi sanyawa bakinsa linzami"

gabanin karasa babatunsa. Ta fiddo ido da murya duka ta ce.

"""Ai ba gidan ka zan kai ta ba, balle matar ka ta karasa hallaka ta. Ko ka ce min ba ka shirya ba, ko sai ka yi"

"shawara da matarka. Nawa gidan zan kai ta, in ci gaba da kula da ita da lafiyarta, tare da nema mata magani har Allah ya ba ta lafiya."

Sannan ne zan ba ta zabi na zama da kai ko a a? Wannan auren da aka yi wa Rukayyah ba da yawu na ba

ban yarda da shi ba.

In ma akwai wata kulla-kulla a cikinsa za ka kunce ta sarai. Ban da gulma da nunkufurci yarinyar cikin

"hankalin kanta ma ba ka so ta ba, ba ka ce za ka aure ta ba sai cikin rashin TUNANINTA?"

"Don haka in za ka wuce ka dauko matarka to ka wuce, amma Rukayyah ba matar zuwa gidanka ba ce."

"Rayuwa kam an riga an nakasta mata ita, cikin gidan. Don haka ba za ta koma ba a yi sanadiyyar"

"ajalinta& .."""

"Duka wannan magana tana yinta ne kasa-kasa a tsakaninsu su biyu, ko Mama Amina da ke uwar daka ta"

"kunna rediyo tana sauraron karatun Alkur ani mai tsarki, ba ta san suna yi ba. Munaya kuwa dama tunda babansu ya fita ta bi shi a baya ta je ta zauna a cikin mota."

"Bai ankara ba sai ganin Hajiya ya yi ta mike ta kama hannun Rukayyah, ita ma ta mike tana gyara mata"

"mayafin abayarta suka yi waje ba tare da an sake bi ta kansa ba. Rukayyah kuwa har suka bar dakin ba ta bar waiwayonsa ba. Tana so ne ta ce ya taso su tafi, ba ta san ya za ta yi ta fada ba."

"Zufa (gumi) yake tun daga tsakar kansa har yatsan kafarsa, ya jike kashirban da gumi, kamar babu fanka"

"mai gudun gaske da ke wulwulawa a falon. Gaba daya kansa ya daure, ya kasa fahimtar me Hajiya take nufi ne?"

" Ba za ta ba ka Rukayyah ba, saboda ba ta yarda da soyayyar da ka ke yi mata ba& .. "

"Zuciyar shi ta fahimtar da shi abin da kwakwalwarsa ta gaza fahimta, baya son ta zai ce a aura masa?"

"& & . A gidan ta Rukayyah za ta zauna, ta kula da ita da lafiyarta. Cabdi! Ashe kuwa za ta yi jinyar mutum"

"biyu, daya mai ciwon SO, daya mai ciwon KWAKWALWA. Don shi kam a yadda yake jin Rukayyah a yanzu, ma ana son ta da kaunarta cikin zuciyarsa, in da za a auna tabbas za a samu sakamakon cewa ; ya fi"

sonta a kan kansa.

"Ya fi son ta da komai na duniyar, tana da lafiya, ko ba ta da lafiya. Shi ma ba shi da lafiyar, yana fama da"

sebere ciwon soyayyah!

"Bai auri Rukayyah don ya yi jinyar ta gidan Hajiya ba, sai don ya yi jinyar ta cikin nashi gidan, da irin salon"

"kauna da soyayyar da yake son ta budi idanu da su. Ya koya mata kaunarsa, shi kadai ransa, yadda ko ta"

dawo tunaninta ba za ta iya rabuwa da shi ba& & .

"Bai auri Rukayyah don ya yi jinyarta kadai ba, har ma da maganin matsalarsa."

An kuma gaya masa mata irin su Rukayyah su ne kadai maganin matsalarsa. In ba haka ba zai ci gaba

"dabin mata, kala-kala, kamar bunsuru, wanda shi a kan kansa baya so."

"Wata irin matsala ce Allah ya dora masa, wadda daga shi sai Shi Ubangijinsa suka sani. Yaya zai yi ya"

fahimtar da Hajiya ne? Mai wani irin bahagon tunani? Mai nuna nata ba nata bane? Mai nuna farin cikin na wani ya fi na nata?

"Yaya zai yi ya fahimtar da ita ba auren jinya ya yi ba, AUREN BIYAN BUKATAR RAI ya yi? Rukayyah ita ce"

"irin mance da ya dade yana kwadayin samu, amma yake yaudarar kansa da gangan."

"Yau ga shi ya samu dare daya, farat daya rana daya ba tare da iyawar shi ko dabarar shi ba. Bayan ya"

"fidda rai. Amma ya samu cikin wani hukunci da irada na Ubangiji. Yana mai cike da doki da farin ciki, yaya Hajiya za ta juya masa farin cikinsa saboda son ranta da wasu hujjojinta marasa madafa na rashin"

fahimta?

Ba ta yi la akar da cewa soyayya ba lallai ta faru a sanda aka so faruwarta ba. Ita wata irin aba ce da ba

"ruwanta da LOKACI ko LAFIYA da dangoginsu. Abu ce wadda ke faruwa a duk san da ta so, ta gudanar da TUNANI ta sarrafa GANGAR JIKI. In haka ne kenan ba shi da laifi don ya so Rukayyah a rashin TUNANIN"

TA.

"Lallai kuwa idan da gaske take, tana shirin ganin bambancin dan jiya da na yau. Wannan rage idon da ake"

"mata, za a daina. Rukayyah is his wife. Kuma kowa ya shaida. Don haka ba zai bari a yi masa sakiyar da ba ruwa ba!!!"

"Mu biyo Haj. Umaimah da  ya yanta Saifuddeen da Rukayyah a hankali, don tantance shin waye mai"

gaskiya a tsakanin su???`

*****

Y

"a mike cikin fushi, da alama ranshi ya yi matukar baci da maganganun Hajiya. Ya taddasu duk cikin mota"

shi kadai kawai ake jira. Ganin Alhaji da Baban Rukayyah sun zuba mai ido cikin tunanin abin da ya bata

"mai rai yanzu-yanzu yana cikin farin cikinsa sai ya dan saki rai, ya bude kofar gaba ya zauna yana kara yiwa Alh. Usman godiya da sallama."

"Motar peageout ce (station wagon), Alhaji na kujerar farko shi da escourtdinsa, Hajiya, Rukayyah da"

"Munaya suna baya. Rukayya na jin muryarsa cikin motar ta shiga waige-waige, sannan ta soma far a, da karfi ta ce, ""Saifuddeen!"""

"Gaba daya suka juyo suka dubeta, babu ya shi da kiran ya tsirga har cikin kwakwalwarsa da jinin jikinsa."

Rukayyah bata taba ambatar sunansa a kunnensa ba.

"Don haka yau da ta kira, cikin wannan tattausan lafazin nata, babu inda bai amsa a gangar jikinsa ba. Ya"

dade bai tattaro hankalinsa ba.

"Shi kuwa Alhaji hamdala ya shiga yiwa Allah, Munaya nata tafi cikin jin dadi."

"Ita dai Rukayyah tun safe ta ji ana ta cewa, Saifuddeen, sannan da ya shigo Asi ta ce, ""Saifuddeen""."

"Yanzu kuma Babanta ya ce, ""Saifuddeen"", don haka ta fahimci Saifuddeen sunansa ne, wanda idan aka kirashi da shi yake yin magana. Don haka sunan ya zauna daram cikin kanta."

"Hajiya kuwa haushin Rukayyah ta ji, ita da ta fi kowa damuwa da ita, bata san sunanta ba har yanzu sai"

Alhaji da Saifuddeen.

Don haka Rukayyah na kokarin tsallaka kujera ta koma gaba wurin Saifuddeen ta duma mata dundu ta

dankafar da ita ta ce

"""Zauna nan 'yar banza, ni har yau baki san sunana ba, ni da na ci kashinki, na ci fitsarinki, sai wadanda"

"kika taras rana tsaka?"""

"Dariya Hajiya ta basu gaba dayansu, Alhaji har tari ya dan sarkeshi. Munaya ma ta ce cikin takaici,"

"""Har ni ma da nake wanke mata undies, nake dafa mata indomie ko  M bata sani ba""."

"Shi dai Saifuddeen murmushi ya ke. Alhaji cikin dariya ya ce ""Kwa ji da bakin cikinku dai, ance daku miji"

"wasa ne?"""

"Rukayyah dai ta koma wurinta tana ta zumbure-zumbure, wato ta ji haushin hantarar da Hajiya ta yi"

"mata. Ta juya tana kallon tsirrai da ke tsere a gefen titi, bata kara magana ba har suka isa airportdin Yola."

"Already jirgi ya kusa gama lodi, kamar ma su kadai ake jira. Don haka suna shiga ana rufe jirgin. Wannan"

shi ne karon Munaya na farko da shiga jirgin sama.

"Don haka tunda ta ji jirgi na kugin tashi ta kankame Hajiya tana salati, hawaye na shatata a idanunta."

Hajiya ta ce me zata yi ba dariya ba?

"Saifuddeen kuwa can bayan Hajiya ya zauna fuskar nan a tamke tsam, ya maka (dark spaces) dinsa,"

amma hakan bai sa cingam din tasa ta ji tsoronsa ba.

"Shi ta bi ta zauna a kusa da shi, amma jikinta ba kuzari. Kanta ne ke ciwo ba tasan ya zatai ta fadi ba,"

amma idanunta sunyi ja ainun.

"Suna zama a kujerun su ta kifa kanta a cinyoyinsa. A nan ne ya ji zafin da kanta ya dauka sosai, ya ce, ""Oh"

"my God!"" Ya kai hannu bisan goshinta, zafi rau, sai ya kara gyara mata kwanciya sosai a jikinsa. Ba ruwansa da mutanen da ke cikin jirgin balle Hajiya da Munaya da ke nesa da su kadan, don Alhaji dama shi kullum dan 'first-class' ne."

"Suna gab da sauka a filin jirgin saman Legos Hajiya ta dan juya ta kallo Rukayyah, ta kuwa yi kyakkyawan"

"gani. Da sauri ta juya ta ci gaba da hira da Munaya, don ta dauke mata hankali kada ita ma ta juya, gabanta na faduwa, bata son wannan nanikewar da Rukayyah ke wa Saifuddeeni, amma zata yi maganin abin da wurwuri."

"Suna sauka direban Alhaji na jiransu, cikin doguwar motar Alhaji BMW mai kujeru biyar. Rukayyah rike"

da hannun Saifuddeen tam kamar mai tsoron kada ya gudu ya barta.

"Don ma ya zame ne, amma da kanta na barin kafadunsa ne, kanta ke ciwo sosai. Tafiyar ma ba don da"

"taimakonsa ba, da bata iya ta ba."

"Ita Hajiya ta dauka shi Saifuddeen ke riketa don ya nuna mata shi ba shi da ta ido, bayan Rukayyan ce ke"

"manne masa, amma shi lafiyar matarsa ne ya dameshi."

"Jin ciwon Rukayyah ya ke kamar a jikinsa, don haka dukkansu su biyun suke tafe salau-salau."

"Suna shiga falo Rabi ta bullo daga kichin, tana yi musu barka da zuwa, ta karbi jakar hannun Hajiya data"

Munaya ta yi dakin Hajiyar. Hajiya ta ce

"""Jakar Munaya kai ta dakin Rukayyah""."

"Ta ce ""To"". Ba tare da ta dubi Saifuddeen da Rukayyah ba, wadanda suka zauna cikin 3-seater Rukayyah"

"kamar ta shige cikinsa don tsatsuba. Shi kuma sai kokari yake ta zauna nesa da shi, amma ta ki."

"Ta kama hannuwansa duka ta rike tamau kamar zata yi kuka. Ya ce ""Don Allah RAK, ki barni inje in yi"

"sallah..."""

"Ta noke kafada, don ta gane rokonta yake ta barshi ya tafi. Ya marairaice ya ce"

"""To ni yanzu RAK, na yi ta zama kenan banyi sallah ba...?"" Nan ma ta noke kai, ya ce ""Tashi muje mu yi"

"alwalar tare"". Ai kuwa ta mike da saurinta."

"Hajiya ta hade girar sama da ta kasa, ta ce  Munaya kamata kuje daki ko bata so, ki dinga yin alwala a"

"hankali zata kwaikwayeki""."

"Nan da nan Munaya aka cika umarnin Hajiya, aka soma jan Rukayyah, ta fizge hannunta. Hajiya ta yi"

mata tsawa ta ce

"""Ke Rukayyah, wuce ciki ki yi sallah, ina wasa da ke ne?"""

"Ko da can Rukayyah ba ta son fada, balle na Hajiya gigitata ya ke. Don haka ba ta san sanda ta saki"

"hannun Saifuddeen ba, ta bi Munaya tana waiwayonsa. Shi kuma bai kara juyowa ba ya fita."

Yanayin fuskarshi ya nuna bai ji dadin tsawar da Hajiyar ta yiwa Rukayyah ba. Bai kuma isa yayi Magana

ba ya san shine sanadi. Tunda ga dukkan alamu bata son tarayyar su ko yaya ne har kuma ta furta masa.

Ya tadda su Alhaji a masallaci suka yi jam'i.

"Shi da Alhaji suka shigo, lokacin har Rabi ta kare abinci ta jera a dining. Hajiya ta umarceta da ta kaiwa"

"Rukayyah da Munaya nasu daki, ita kuma a damo mata fura mai sanyi."

Don haka Rabi abincin mutum biyu ta aje a dining ta koma wurin su Rukayyah. A nan Munaya ke bata

"labarin an daura auren Yaya Rukayyah. Rabi ta ce ""Da Aliyun?"" Ta girgiza kai ""A'ah da Yaya Saifuddeeni""."

"Nan da nan Rabi ta karkace kai ta yankawa Rukayyah guda ta rungumeta, Hajiya ta yi tsaki daga can falo"

a ranta ta ce

"""Munaya da surutun tsiya ta ke, ko meye abin dorarwa a wannan auren Oho! Mai auren bata san ana yi"

ba.

Shi da Alhaji suka shigo daga masallaci. yana tafe kamar wanda aka yiwa duka ko kuwa sabon kwai ya

fashe mai a ciki. Nan ya cimma sakon Hajiya na raba masu cin abinci shi da Rukayyah.

Don tana ganin hakan ma duk wani hanya ne da Rukayyah zata rabeshi. Ya yi murmushi ya ce

"""Hajiya, ho!"""

"Yana cin abincin amma hankalinsa duka yana kan kofar dakin Rukayyah, ko zata fito. Shiru kake ji, daga"

ita har Munaya bai ga keyar ko daya ba.

"Suka kare cin abincin Alhaji ya ce ""Sai ka karasa gida ka huta tunda gobe da jibi duk ba ofis. Ka daure ka"

"samu hutu sosai, kuma ka sake tunani kan maganar da na yi maka na ka dawo da matarka. """

Saifuddeen ya dago kyawawan idanuwanshi wadanda a yanzu suka kada suka yi jawur abin tausayi. Wai

me Hajiya da Alhaji ke nufi ne? Kar dai bakinsu daya na ba zasu bashi Rukayyah ba?

"Ya hadiye wani busashshen miyau, mukut! A makoshinsa, wanda ya tokareshi ya ki wucewa sai da kyar."

Cikin kasalalliyar murya ya ce

"""To""."

"[12/17/2019, 19:17] Takori: Alhaji ya ci gaba da kawo mai dalilai da misalan da suka sa ya ke so ya dawo"

da Salima cikin lallashi. Ko zancen Rukayyah baya yi.

"Ya so ya tambayi Alhajin ita kuma Rukayyah fa? Sai ya daure. Ai sun fishi sanin wanzuwar tata, tunda sun"

"nuna hakan suke so, bari ya bi su da yadda suke son."

Alhaji ya tashi ya hau sama ya barshi anan zaune da cunkusashshiyar zuciya.

"Zuwa can dai ya mike ya iske Hajiya tana shan fura, ya russuna, da fara'arta ta ce ""Har zaka tafi ne?"""

"Kansa a kasa ya ce, ""Eh"". Ta ce, ""To, Allah ya bamu ALHERI""."

"Ya cigaba da tsugunnon, bai mike ba. Ta ganoshi tsaf, Rukayyah ya ke son gani, ita kuma ta ki bada"

fuskar a tambayeta.

"Ta samu Rukayyah ta zauna da Munaya, yanzu da ta ganshi zata ce ba tasan zance ba. Ya ce"

"""Dazu Nafisah ta yi min waya cewa gata a Yola, inje filin jirgi in taho da ita. Na fada mata bazan samu"

"dama ba, ta hawo tadi ta taho. To kuma har muka taho ban ganta ba""."

"Hajiya ba ta ce komi ba, ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira wayar Nafisah."

"Nan da nan ta dauka, ta ce ""Hajiya ba dai har kun sauka ba?"" Ta ce ""Zancen yaushe kuma, har mun"

"huta?"" Ta ce"

"""Wallahi wata 'yar banzar mota na shiga sau uku ana sanja taya kan mu iso Jalingo, ban iso ba sai bakwai"

"na maghriba, yanzu haka muna tare da Mama Amina""."

"Ta ce ""Ya yi kyau, kin dai ji duk abin da ya faru da  yar uwarki ko?"""

"Ta share hawayen bakin ciki da farin ciki duka, ta ce ""Na ji abin alhini da abin farin ciki. Allah yasa"

"hakan kaffarar, Rukayyah ne, kuma Allah ya bata lafiya. In Yaya yana gidan hadani da shi""."

"Ta ce, ""Ga ya nan, daman shi ne ya damu da ke, ya dauka ko 'yan tadi sun saida kanki ne"". Ta"

"mikawa Saifuddeen, ya karba ya mike tsaye suna magana irin tasu ta 'yan uwa da suka aminta da juna."

"Ya kammala ya baiwa Hajiya wayarta, ya koma kujerar ya ci gaba da zama, wanda Hajiyar bata ga alamar"

yana da niyyar tashi ba.

"Ta ce a ranta, ""Ka yi ta zama, har duwawunka ya kumbura"". Ta mike da kyar ta bar masa falon."

"Ta shiga dakin su Rukayyah da jugdin furarta ta mikawa Munaya ta ce ""Ungo fura, bata ko zata"

"sha"". Sannan ta samu waje ta zauna, ta ce ""Munaya!""."

"Ta juyo ta ce ""Na'am"". Ta ce ""Kada ku dinga fita ko nan da can kinji ko? Tunda ga bandaki nan, ga"

"kayan kallo. Rabi zata dinga shigo muku da abincinku""."

"Fuskar 'yar Munaya ta nuna damuwa tsantsa ta ce ""Amma me yasa Hajiya?"""

"Ta gyara murya ta ce ""Likita ne ya ce ta dinga zama waje daya, hakan zai taimaka kwarai wurin"

dawowar tunaninta.

"Sannan kada ki sake ki barta ita kadai cikin daki, idan ni bana nan. Idan bandaki zaki shiga, to ki"

"sa mukulli ki rufe kofar dakin, sannan ki shiga. Sannan ko waye zai zo a gidannan ya ce zai aikeki wani waje, ko nan da kichin ne ki ce a'ah, Hajiya ta ce kada inje ko ina""."

Munaya ta yi dariya ta gyada kai. Sai kuma ta yi dan tunani da yake yarinya ce mai hangen nesa

"da hankali, ta ce ""Hajiya idan Alhaji ne fa?"""

"Hajiya ta yi dummmm! Can kuma ta ce ""Shi ba abin da zai kawoshi nan ma. Ko me ya ke so ni"

"yake nema"". Ta ce ""to idan kuma Yaya Saifuddeen ne fa& .?"""

"Ta ce ""& ..Ko Saifullahi ne kinji na gaya miki""."

"Ta yi dariya ta buga cinya ta ce ""Anyi an gama Hajiya!""."

"Ta dawo falo ta tadda Saifuddeen har yanzu yana nan a yadda ta barshi, gaba daya ya saki kamar"

"ma a kwance yake, idanunsa a rufe. Wani irin tausayi ya kamata, abinki da da da mahaifi."

Ta tambayi kanta kowanne irin so Saifuddeen ke yi ma Rukayyah???

To amma Rukayyah ma abin a tausayawa ce.

"Ina Rukayyah ina lalurar miji a wannan halin da take ciki? Dole tasan yadda zata yi matarsa ta dawo, in"

ba so take ya koma ruwa ba.

Ita ma tasan matsalar Saifuddeen kwarai ba irin mazan da zasu zauna babu mace ba ne.

"Tsoronta Allah, tsoronta idan Rukayyah ta yi ciki ai sun shiga uku, ana ta neman lafiyarta a koma"

"rainon ciki, da wanne za a ji?"

"Sannan a ka'ida ma masu matsala irinna Rukayyah, ba a son su yi ciki, cikin halin da suke ciki."

"Ta taba ji a talabijin a wani tattaunawa da aka yi da hukumomin kiwon lafiya na kasar Amurka,"

"suke bada fatawa akan genetic, wato gado daga Uwa mahaifiya zuwa dan da ke ciki."

"Da ya kan gado wasu physical characteristic kamar rashin ji, rashin gani, rashin hankali, kuturta,"

"makanta, gurgunta da sauransu."

"A wasu asibitocin ma na America, akan kashewa mata masu tabin hankali kwayayan haihuwa,"

"don kar su haihu cikin halin da suke ciki. Ko 'ya'yan su gado lalurar mahaifansu. Don haka ne ta ke ganin matakin da ta dauka na hana Saifuddeen da Rukayyah mu'amalar aure, taimakonsu ta yi, daga shi har ita."

"To ko shi mijin da ke cike da lafiyarsa da kuruciyarsa, zai dauki wannan hukuncin na Hajiyar idan"

ita mara lafiyar ta ji-ta-gani?

"Ta yi gyaran murya ta ce ""Anya Saifuddeen, ba zaka tafi ka kwanta ba, sai ka ce mai jikin karfe?"""

"Ya yunkura ya mike ya zari makullansa da hularsa ya fice yana cewa ""Na tafi Hajiya, mu kwana"

"lafiya"". Murmushi ta yi, ta ce"

"""Umma ta gaida Asha"". Amma har ga Allah ya bata tausayi daurewa ta yi."

Shi kam tafe yake a mota cikin tukukin zuciya. Yana tunanin da ba Hajiya ce ta haifeshi ba cewa

zai yi bata kaunarsa. !

"What a surprize! Kofar falonshi a bude, sannan ga motar Salima a kofar gida. Yana sanya kai cikin falon"

kamshin gashin kaza na dukan hancinsa.

Yagana ta fito cikin minis daga kichin tana masa barka da zuwa.

A fusace ya juya yana kallonta kana ya danna kai falon.

"Madam Salima ya yi tozali da ita ta ci ubansu kwalliya, cikin wasu fitsararrun nighties masu"

"laushi kamar jikin mage, wadanda a da yake matukar sonsu, amma yau daga mai kayan har kayan da ke jikinta bakaken kulba ya kallesu."

"Ta sakar mai tsadadden murmushinnan nata, ya gyada kai, ya haye matattakalar bene uku-hudu,"

zuciyarsa na harbawa.

"Ya so ne ya tsaya ya fatattakesu, ya ga idan ma ya tsaya suka ji lafazinsa ai sunyi mukami, don"

haka ya hade fushinsu da na Hajiya ya hadiye.

"Ya murzawa kofarsa key bai kuma zareshi daga jiki ba. Ya tube rigar shadda ya cillar, ya kunna"

A/C ya kunna fanka ya yi dai-dai bisa ni'imtaccen gadonsa amma bai daina zufa ba. Haka zuciyarsa bata bar tafasa ba.

"Yana jin Salima na magiyar ya bude mata kofa, sai ya yago (tissue) ya toshe kunnuwansa. Ta yi"

"har ta gaji, sai ta koma kira a waya."

Da hanzari ya mika hannu ya kashe wayar. Cikin aljihunsa ya jiyo wasu abubuwa ya soma zarosu.

Turarrukan Rukayyah ne da spraydinta 'touch me' mai dadin kamshi dan Dubai. Gami da 'yar kankanuwar wayarta  siemens'.

"Wani matsanancin sanyi ya sauka a zuciyarsa, ya yi murmushi, ya samu kansa da feshe illahirin"

jikinsa da shimfidarsa da (spray) din Rukayyah.

"Ya fada cikin wani hali na bege mai tsanani. In banda sunan Rukayyah ba abin da ke fita bakinsa,"

ya yi ta juyi daga wannan gefe zuwa wancan.

"Ba abin da yake bukata a wannan lokacin illa Rukayyah, ba abin da ya ke so ya bude ido ya gani a"

"wannan lokacin sai Rukayyah, ba abin da yake so a wannan lokacin kamar ya ji Rukayyah a cikin jikinsa, wadda cikin dan lokaci ta mamaye 90% na zuciyarshi. Ta dushe hasken duk wata diya mace mai haske a"

"idanunshi, abun kamar sihiri."

"Mai yasa Hajiya ba zata gane hakan ba? Koko so ta ke ya zauna ya karanto mata zuciyarshi,"

alhalin tana a matsayin wadda yake gani da GIRMA fiye da kowa?

"Sannan akwai wannan nauyin da Allah ya sanya tsakanin da da mahaifi, yaya za a yi ya iya gaya"

mata bazai iya rayuwa ba tare da abin da zuciyarshi da gangar jikinshi ke so ba?

"Shi kansa yasan idan ya ce a yau ya yi barci, to ya yi karya. Rukayyah ta hanashi ko rintsawar ido."

"Matarshi kawai yake so, wadda kuma ba tasan yana yi ba."

"Washe gari karfe shidda ya yi wanka ya bar gidan, ko inuwarsa masu gidan basu gani ba."

Alkawari ne ya riga ya dauka Salima ko ta dawo watanni uku kwarara zai yi bai yi mata magana

ba.

"Wannan ne kadai hukuncin da yake jin zai iya yi mata (babban tashin hankali ga mace kenan,"

kauracewar miji).

"Da ta dawo din kuma sai ya ji duk ya tsaneta, ko ganinta ba ya son yi. Tunani ma ya ke cikin"

"kansa, ya akai ya aureta? Me ya gani a jikinta har ya ja hankalinsa?"

"""Oho kai ka sani malam Saifuddeeni (Takori)."

"Bai kuma san yadda zai yi da ita ba, tunda Alhaji ya ce kada ya fara da ya saketa. To mai zai yi"

"mata banda abin Alhaji banda saki, tunda kuwa duk wani birbishin sonta ya goge a zuciyarsa?"

Ya isa gidan karfe shidda da rabi ko bude gate ba a yi ba. Amma da yake shine mai gadin bai yi

nawa ba wajen bude masa.

Kofar da zata shigar da kai falon Hajiya a kulle ta ke gam

Please Login or Register in order to submit comment