You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da karatu in samu nutsuwa,"

mazan nan duk makarya ta ne Nafisah ki rabu da su yadda ki ka gansu.

Dadin bakin su da rawar jikinsu akan mace ya daina rudarki. Goben nan insha Allah zan sayo JAMB

in cike da sakamako ya fito in fara karatu a ATBU.

"Nafisa ta yi murmushi ta ce,  Karatu ai baya hana aure, kuma ai ba duk mazanne suka taru suka"

"zama daya ba, abin dace ne kawai RAK!"

"Don haka ki nemi zabin Allah, ba wai zabin ran ki ba. "

Gaban Rukayyah sai da ya fadi da jin kalmar da Nafisa ta ambata. Babu wanda ke kiranta da wannan

"suna a duniya, sai mutum daya."

"Ta bata shiru na dan lokaci, ta dade ba ta yi magana ba har Nafisa ta yi tsammanin ko ta ajiye ne,"

can ta daure a hakali ta ce.

" Nafisa, a ina ki ka ji wannan sunan? "

"Ta kyalkyale da dariyata ce,  A bakin da ki ka san kina jinsa. NI da Allah bani Hajiya, idan mutum ya"

"biye wa surutunki sai ki cinye mai credit, alhalin kuma ba biyan shi za ki yi ba. "

"Rukayyah ta hadiye mamakinta ta ce,  Ke ni fa ba a gidan Hajiya nake ba. "

 A ina ki ke?

Ta sake yin jim. Ta rasa me yasa duk wani al amari da ya shafe shi yake da nauyi a harshe da

"zuciyarta. Can dai ta daure, a hankali kamar mai ciwon baki ta ce,"

" A gidan Yayanki, Alhaji ya turo ni girkau, saboda matar gidan na fama da laulayin ciki. "

"Nafisa ta mrumusa ta sake murmusawa, ita ma a hankalin ta ce,"

" Yayana, baya da suna?"""

"""Ni sunan ne wallahi yake bace mini, wata ran in ce Shamsuddini, wata rana in ce Kamaluddini. Da"

na ga ba zan iya bambancewa ba sai na hakura da fadi kwata-kwata.

"Nafisa dai dariya take sosai ta ce,  Ashe kina nan kina shan haushi. Ai ni zuwa gidan  yan gayun nan"

ya fi karfina.

"Ta ce,  Nima ya fi karfin nawa, to amma ya zan yi tunda Alhaji ne ya sani?"" Cikin dariyaNafisa ta ce."

" Dadi na da Alhaji kenan, akwai son kulla ALHERI, don Allah kar ki sake ki fito gidan nan ba a kulla"

ALHERIN nan ba& ..

"Cikin rashin fahimta ta ce,  Nafisaah& ban gane ba&  "

"Ta ce,  Ai dama ba za ki gane ba, to tunda ba ki gane ba, je kitambaya min Yaya Saifuddini."

" Wane ALHERI ne Alhaji ke son kullawa a tsakaninku? Wane ALHERI ne, ke tattare da tarayyarku? "

"Ta kashe wayarta ba tare da ta sake sauraron Rukayyah ba, ta bar ta da buhun tunani. Sake da baki."

Ta samu kanta da maimaita tambayar Nafisah

" & .wane ALHERI ne, Alhaji ke son kullawa a tsakaninmu????"""

"[12/17/2019, 19:15] Takori: Wannan turaren mai kashe mata jiki da laka, ya bakunci hancinta. Ko"

dayake ta dade tana sunsunar tashin kamshin sa cikin dakin amma hirar Nafisah ta dauke mata hankali bai sa ta juyo ba.

Sai yanzu ne ta waiwaya bayan ta a hankali suka yi ido hudu da wanda ake gulmarsa. Ya hade cikin

"shigar da ba ta taba ganin ya yi ba, wato Kaftan na shadda mai laushi (Excellencior) ruwan siminti yana rike da hular shi a hannun dama bai sanya ba."

"Da alama ya dade tsaye a bakin kofar ta, ba mamaki duk hirarrakin da suke yi ita da Nafisa ya ji"

"su.Kuma wani kuskure da ta yi shi ne hands-free da ta saka a wayar, yayin da suke hirar. Kwarjininsa da"

"cikar zatinsa ya soma kidima ta, musamman da ya kasance ba su taba kadaicewa tare na lokaci mai tsawo haka ba. Ta samu kanta cikin gigicewa ba ta san san da ta yi cilli da wayar hannunta ba."

Wani irin asirtaccen kallo yake mata mai tada tsigogin jikin duk wata lafiyayyar mace. To hakan ce

ta faru da Rukayyah.

"Ba ta san san da ta zame daga bakin gadon da take zaune ba, ta yi zaune dirshan a kan carpet bisa"

"kafafunta ba, ta sunkuyar da kai ta manne ido tana murza yatsun hannunta kamar mai laifi, ko kuwa makaryacin da ya nannaga karya aka kure shi."

"Ya karasa shigowa cikin dakin, ya jingina da bango ya harde dogayen hannuwansa a kirji, yana"

"murmushi ya ce,"

" RAK, kenan! I just come to thank for the delicious break fast (Na zo domin in gode da kyakkyawan"

"karin kumallo). Amma ke kin ga ya dace mu cinye abincin, wadda ta sha wahalarsa ta samu sudi? "

"Cikin daburcewa da sarkewar murya ta ce,  & ba& ba komai ai. Bana cin abinci mai nauyi da safe,"

Yana haifar min da indigestion (bacin ciki).

Ya jima yana kallonta da sauraron yadda take furta lafuzzanta a tausashe. Kai ba ka ce ita ce mai

kankanbar nan da giringidishi da soyayyen ido ba. Bai yi zaton fitsararriyar yarinyar akwai namijin da zai iya razana ta ba.

"Ashe dai duk mata daya suke, wurin rauni, da saurin karaya? Ji-ji da kan nata, karambani da fitsarar"

"tata, ta san a inda take yin su (a gaban Hajiyarta)."

"Shi kadai ya yi murmushi  Duk da haka ki zo mu je, ko tea ne sai ki sha, saboda amanarki Hajiya ta"

ba ni dole in kula da cin abincinki.

"Ba musu ta mike saboda rudewa kodankwalin ta manta ba ta dauka ba, suka jera suka fito suna"

sauka daga step cikin nutsuwa.

"Salimah na bisa tebir ko cokali ba ta taba ba, hannun ta na dama dafe da goshinta, gashin kanta a"

harbatse idanun ta kozai-kozai. Sai faman fyace majina take da tissue. Alamu ne na rashin wadatar barci a tsayin daren baki dayansa. Ko miyau ta kasa hadiya.

"Dalili shi ne tunda ya mike ya ce zai je ya kira Rukayyah su karya tare, kimanin mintuna talatin"

"kenan, babu shi babu Rukayyan, babukuma alamunsu."

A sannan ne ta jiyo takun su suna son saukowa daga benen mai doguwar matattakala mikakkiya har

"goma sha biyu. Ta daga jajayen idanunta a hankali ta dube su. Kai ka ce tare aka tsugunna aka haife su saboda tsabar kamannin su, sun kuma yi bala in dacewa da juna. Ba ta taba ganin ganin macen da ta"

dace da Saifuddeen a duniya irin Rukayyah ba& .

Ba ta san san da zuciya tattare da matsanancin kishi suka kwashe ta ta mike da karfin gaske da

kuma mugun gudu ta yi kan Rukayyah ba.

"Daga Saifuddeen din har Rukayyah, sun dauka wani mugun abun ne mai ban tsoro da cutarwa ya"

biyo ta kamar maciji ko kadangare. Shi Saifuddeen hannuwa ya bude domin ya rungume abarsa amma ina!

Hannuwanta biyu ta sa iyakar karfinta ta tankado Rukayyah tun daga matattakala ta uku ta kuwa

"dinga sulmiyowa daga benen (Step-by-step), har matattakala ta goma sha biyu har ta dangana da kofar falon a sume."

Kanta ya yi mugun bugawa da karfen kofar sannan dan kunnenta wanda yake na silber siriri ya fice

"ya karto tun daga kasan kunnenta har kusa da bakinta, jini ya soma bubbulowa."

Ta koma gefe ta tsaya tana huci kamar macijiyar da ta so yin sara ta kuskure. Shi kuma sai ya bi

"Rukayyah da gudu, ya ciccibe ta ya kwantar a doguwar kujera gaba daya ya kidime miyau ya kafe a bakinsa. Daga bisani ya yi kan Salimah yana cewa."

 Ba ita ki ka kashe ba auren mu ki ka kashe kuma wallahi Alhaji ba zai kyale ki ba& .

Ganin in ta tsaya ba shakka ita ma tankado ta zai yi wato ya ramawa Rukayyah ba shiri ta karasa

"dakinta da gudu ta banko kofa ta murza key, ta jingina da kofar tana maida numfashi."

Ya dinga buga kofar da kafa da hannu kamar wani sabon mahaukaci yana fadin.

"""Fitowa za ki yi ki fuskanci shari ah, ki fuskanci wanda ya turo miki ita da kanki, amma ni ba ni da"

kwarin gwiwar da zan kalle shi.....

"Ki gaya masu da bakin ki ke  yar ta adda ce,  yan uwansu su kiyayi gidanki. Ban taba son Rukayyah a"

"rayuwata ba, amma yanzu kinsa dole na aure ta. In ya so sai ki hada mu mu duka ki kona da fetur."

"Ta zame min dole, dole ta zo gidana, amma ke ba dole na ba ce& fitowa za ki ki tafi gidan ubanki,"

wannan gidan na uban Rukayyah ne& .

"Ya ga cewa wannan duk shirme yake, don kuwa ba ta da alamar budewar. Ga wadda ke can rai a"

"hannun Allah ita ke bukatar taimakonsa, in ta mutu cikin gidansa me zai ce da Hajiya Umaimah ya fidda kansa?"

Da gudu ya sauko daga benen ya kinkimo Rukayyah ya yo waje. Masu gadi da yaran da ke kula da

"gidan duka suma suka biyo shi a guje, suna tambayar shi abin da ya faru da Madam, don su sun dauka Salima ce."

Ya cillawa wani yaronsa Don mai kula da shukokin gidan makullin motarsa ya fiddo ta daga

mazauninta ya bude masu.

"Don ne ke tukin motar ba tare da ya tambayi inda za a ba, shi kuma yana baya rungume da"

Rukayyah wadda jinin da ke bulbula na gefen kunnenta shi ya fi komai gigita shi.

"Wani asibiti mai zaman kansa Don ya kai su, ba da bata lokaci ba suka karbi Rukayyah suka soma ba"

"ta taimakon gaggawa, wadda har zuwa lokacin ba ta san inda kanta yake ba."

"Don suman da ta yi kam ta farfado, amma she is still unconscious wato bata cikin hayyacinta."

Suka fara dinke bayan kunnenta wanda ke ta zubar jini. Likitocin na tsammanin wannan matsalar ita

kenan da ta huta an yi mata allura za ta warware. Sun tabbatar babu gocewar kowanne kashi balle karaya.

"Don haka Saifuddeen ya dan samu nutsuwa, da tunanin da ta warware ya dauke ta daga nan"

"asibitin ya zarce kai tsaye ya maida ita inda ya dauko ta, ya hakura da cin abincin gara kullum ya biya can gidan ya ci, ko ko ya yi ta bin gidanjen abinci (Restaurants) ya fiye mai kwanciyar rai, kada ya je Salimah"

kan shegen kishinta na banza ta janyo mai tashin hankalin da ya fi karfinsa.

" Amma fa lallai za ta dandana kudarta. YA ce a ransa. Babu duka babu zagi, babu je ki gidanku,"

amma sai ya yi watanni uku uffan bai ce mata ba.

Ya kuma yanke shawarar rokar Rukayyah alfarmar ta rufa masu asiri ta ce zamowa ta yi daga bene.

Don haka bai ma yi tunanin kiran Hajiya ba. Ya ja bakinsa ya yi gum. Wajejen sh abiyun rana Alhaji

"ya kira shi. A sanyaye ya amsa. Alhaji ya ce,"

 Wai kuwa Saifuddeen wane irin mashiririncin mutum ka ke son ka zama ne? Ina takardun da muka

yi da kai za ka turo min kafin sha day ana rana na kayan da suka iso daga Barbados jiya da daddare?

"Gaba daya ya sake rikicewa, don shi shaf ya mance da wani alkawarin da su kai da Alhajin saboda"

"tashin hankali. Da kyar ya iya cewa,  Am, eh, Alhaji& motar& motar& motar tawa ce ta samu matsala ina"

gab da fitowa.

"Alhaji ya ci gaba da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, fadan nan na Alhaji da ke rikita shi,"

"ya gigita shi, ya gwammace Alhajin ya rufe shi da duka da wannan ruwan bala in. A karshe ya yi kwafa ya ce."

" Ban da sanabe, fi i'li da son nuna iyawa, kamar ka Saifuddeen a ce ka nanikewa mota daya duk"

"miliyoyin motocin da Allah ya mallaka mini, wadanda idan ana shimfida titi da su za ka shimfida ka wuce, amma ka san ka dauka kakyautarwa matan wofi banza a hofi."

"To yanzu kayan da aka debo suka iso (port) ka janyo ban san wadanne ne na wadannan ba, ban san"

wadanne ne na wadancan ba. So ka ke in gwamutsa in ba su ko me?

"Ya ce,  Ka yi hakuri don Allah Alhaji, an kusa gama gyaran yanzu zan je in turo. "

"Ya ce,  Zancen banza, zancen wofi, za ka bata min al amari, an yo min waya ga mutane can a"

"zazzaune suna jira sun je daukar kayansu, babu wani kwakkwaran bayanin da akai masu, har yaushe ka isa ofis din ka turo? "

Da kyar da sidin ludayi ya samu ya lallaba Alhajin da alkawarin idan sakon bai zo ba nan da mitnuna

ashirin ya yi duk hukuncin da ya ga dama.

"Alhaji ya yi tsaki ya aje, shi kuma ya zuki doguwar iska ya fesar. Nan ya bar Rukayyah a hannun"

likitocin bayan sun tabbatar masa babu matsala za su yi iyakar kokarinsu a kanta.

"Ya dauko Don a gaban mota, ya sauke shi a gida. Ya karasa ofis da dan banzan gudu kamar ya tashi"

sama.

Can ya yadda mutane cundum a kofar ofishinsa suna jiran isowar shi. Cikin su kuma babu wanda ya

isa ya zamewa Alhaji bai ji ba.

"Sakatariyar shi Helen ta gabatar masa da (file-file) na masu bukatar ganin nashi, sai da ya tabbatar"

"ya turawa Alhaji sakon ya tafi, ya samu ya zuki kwakkwaran numfashi ya soma attending aiyukan da ke gabansa ta hanyar yin umarnin shigowar mutum na farko."

"Sai kuma ga wayar Hajiya ta shigo, gabansa ya yi mummunan faduwa, da kyar ya iya ya amsa kamar"

maras lafiya.

"Ko gaisuwa ba su yi ba ta ce, Me ya samu wayar Rukayyah ne, tun dazu ina ta kira tana ta ringing ba"

"ta dauka ba?"""

"Ya hadiyi wani busasshen miyau da ya bushe masa a makoshi, gami da jika busassun lebbansa ta"

"hanyar lasar su da siririn halshensa, ya ce,"

" Ni yanzu haka ina ofis, aiyuka sun kacame min, tun safe na baro gidan, watakila ba ta kusa da"

wayar ne.

"Ta ce,  To koma gida maza yanzu ka ce da ita ta kira ni, gani nan a Jalingo abubuwa sun ki dadi."

Usman ya kafe sai ya daura mata aure goben nan sai dai in wannan shi ne abu na karshe da zai yi a rayuwarsa.

Don haka ta hado kayanta komai dare yau za ta shigo Jalingo ta taho Yola akwai jirgi ka yankar mata

"tikiti ka sako ta. Na yi na yi iyakar kokarina amma ban yi nasara ba, karshen ta cewa ya yi idan har ta dage ba za ta auri Aliyu ba, to ta je ya yafe min ita duniya da lahira."

"Ni kuma na ga me ya yi zafi, kuma ina dalili zan daure mata gindi ta bijirewa mahaifinta? Don haka"

"don Allah ka fara tausarta, ka gaya mata ta cika imanin ta ta hanyar yarda da kaddara. Babu abin da zai faru ga bawa face ya kasanec rubutacce a Lauhul-Mahfuz."

"Allah ya riga ya rubuta Aliyu shi ne mijinta, dukkan mu daga ni har Babanta ba mu isa mu hana ba."

"Ka yanko mata tikitin Yola na ce ta taho a yau din nan zan tura direba ya taho da ita Jalingo, in ta taso sai ka gaya min. "

"In ban da zufa ba abin da yake yi, tun daga tsakar kansa har yatsan kafarsa, kamar wanda aka"

kwararawa ruwa kwanon - sha guda. Tun da haka ne ai maganar boye-boye babu ita.

"Gara ya fadawa Hajiya gaskiyar halin da Rukayyah take ciki in ya so komai ta fanjama-fanjam, amma"

zahirin gaskiya Rukayyah ba za ta iya tahowa Yola ba a wannan halin dai da take ciki.

"Cikin dauriya ya ce,  Hajiya zancen gaskiya Rukayyah ba ta da lafiya& yanzu haka a asibiti na baro ta."

"Na boye miki ne don ina tunanin kafin in tashi ofis ta warware, amma ko wanda ke kanta ba ta sani ba& . "

"Cikin tsawa ta katse shi da cewa,  Me ka yi mata? Daman fa ba ta son tafiyar nan gidan ka na takura"

mata& .

Jikinsa ya soma rawa. Bai taba jin Hajiya ta yi tsawa haka ba. Ya ce cikin sarkewar murya  Wallahi&

"ni& ni ba abin da na yi mata& ki tambaye ta Hajiya, wallahi& . "

"Ta ce,  Rufe min baki. Batun yau ba na san ka tsani Rukayyah, ba ta ci maka ba, ba ta sha maka ba,"

amma ko gaisuwar ta da kyar ka ke amsawa.

"Lafiya lau na dau yarinyar nan na baka, amana. Don ta taimaka maka. Ba mamaki, FYADE ka yi"

mata& . Ta soma kuka.

Hankalinsa duk inda yake in ya yi dubu duk inda yake to ya kai kololuwar tashi. Bai san san da

"hawayen takaici suka zubo masa ba. Makogaronsa ya bushe rayas, babu digon miyau ko kankani a bakinsa."

"Wato shi dan iskan mutum, ko me zai yi na ALHERI ba zai taba wanke shaidar iskancin nasa ba, daga"

"zuciyar wadanda suka yi masa tabbatacciyar shaidar ba (labelling) inji criminologists. Yau ina ranar neman mata, tunda kuwa UWAR da ta haife ka ma ba za ta taba yarda da kai ba, in dai a kan mace ne?"

"Ya tabbatarwa kansa idan ya yi shiru Hajiya ta aminta da zarginta akansa kenan, mutuncinsa ya kau,"

"har abada a idanunta! Bai san san da ya ce,"

" Wallahi, wallahi Hajiya, na rantse da wanda raina yake hannun Sa, ko yatsan  yar ki ban kama ba."

Salimah ce da shegen kishin ta ta ga muna saukowa daga bene tare tsammani take ko son Rukayyah

nake yi shi ne ta tankado ta& .

"Sai ji ya yi Hajiya ta yi cilli da wayar, yadda ba mamaki ta ragargaje, domin ya jiyo karar"

kwankwatsewar tata cikin kunnuwansa.

"Duk namijin kokarinsa da jarumtakarsa, na ganin ya daure ya ci gaba da attending dumbin manyan"

"mutanen da ke gabansa, ya kasa. Dole haka ya tsallake su sai hakuri ya bai wa kowa."

Da sassarfa ya shiga motarsa cikin wani irin tukin ganganci da Allah kadai ya kaddari isowarshi

"asibitin da ya bar Rukayyah lafiya, amma zagi daga fitilun motocin gabansa da bayansa ya sha shi har ya gode Allah."

"Wannan bai dame shi ba, fatan shi ya tattara Rukayyah ya saka ta a jirgi ko a wane hali take ta tafi,"

"in ya so Hajiya ta daga zaninta ta duba, ta tabbatar bai yi wa  yarta fyade ba."

"Kalaman sun soke shi matuka, har ya iso asibitin bai daina hawayen takaicinsu ba. Ko da yake"

"neman matan ai ya fi karfin ya yi masu fyade, ko da da yakutu aka kera yarinya kuwa wallahi sai dai shi ta yi masa."

"Allah ya tuba in babu Nairar biyan ta akwai surar da sai dai ta taya a siyar mata, don kanta. Balle"

"wata Rukayyah da yake ji, yake kuma gani kamar Nafisah."

Har zuwa lokacin Rukayyah na nan a yadda ya bar ta. Wato idanuwa a bude tangararas suna juyawa

"ko ina, amma jikinta a sake shakaf kamar jikakken tsumma, ba ta umh ba ta umh-uhm."

Ya karasa gaban gadon da take kwance ya dubi dinkin da aka yi a gefen kunnenta an manne da

"plasta. Yasa dan yatsansa a wurin ya shafa a hakali Ya ce,  RAK. "

"Ta juyo tana kallon sa kawai kamar ba ta san shi ba. Ya ce,  Za ki iya takawa ki daure mu je in saki"

jirgin Yola?

"Ita ma ta bude baki ta ce,  Za ki iya takawa mu je in saki a jirgin Yola? "

Ya ji wani sanyi a ransa ta farfado kenan. To amma wannan kallon na rashin sani da Rukayyah ke yi

masa ne bai gane masa ba.

"Ya ce, ""Ko sai na taimaka miki ne za ki iya tashi?"""

"Ita ma ta ce,  Ko sai na taimaka miki ne za ki iya tashi?'"

"Ya gintse fuska, yadda yake mata koyaushe, ya koma Saifuddeen din shi da ta sani, alamun ba wargi,"

"ba sani ba sabo. Cikin muryar umarni ya ce,"

" Ke Rukayyah kin ga ba maganar wasa nake ba& ."""

Daidai lokacin da Dr. Abayomi babban likitan asibitin da wani likita jar fata suka turo kofar suka

"shigo, nurse dauke da tasar magunguna na biye da su. A lokacin Rukayyah na kara maimaita masa abin da ya ce da ita."

" Ke Rukayyah kin ga, ba maganar wasa nake ba& .. "

"Saifuddeen, wanda da alama ya fara kulewa da iskancin Rukayyah, bai kara bi ta kanta ba ya dubi"

"Doctors din a fusace ya ce,  Can we go? "

"Rukayyah daga can kan gadon ta ita ma ta kwaikwaye shi ta ce,  Can we go? "

Likita ya daga mai hannunsa alamar ya fita ya dan ba su wuri minti biyu za su duba Rukayyah.

Ita ma ta kwaikwayi yadda likitan ya yi tana yi masa. Da baya da baya ya juya yana fita cikin gigita

har ya fita daga dakin.

A gigice ya zauna a wani benci da ke fuskantar dakin ya kama kansa da dukkan hanuwansa biyu

yana jujjuyawa. A hankali ya furta

 Na shiga uku ni Saifuddeen! Wacce irin masifa ce wannan?

"Awa daya, biyu har uku likitocin nan na tsananta bincike a kan Rukayyah. Daga bisani ya ga nurse"

din nan ta turo ta a kan wani gado zuwa wani kebantaccen tsakurkurin dakin na urai masu kwakwalwa suka maida kofa da gudu suka rufe.

*****

T

"sananin gigicewar da ya yi ne bai san san da ya kira layin Alhaji ba ya ce,"

" Alhaji ka zo, na shiga uku na lalace& wallahi duk Salima ce ta jawo&  "

"Cikin taushin murya Alhaji ya ce  Ka nutsu, na ce ka nutsu. Ka gaya min abin da ya faru?"""

"Ya ce,  Rukayya ce& wallahi, Rukayyah ce&  "

"Ya ce,  Me ya samu Rukayyar? "

"""Nima ban sani ba, muna nan asibiti, likitoci suna kanta, da dukkan alamu is a serious case. "

"Ya ce,  Wanne asibiti ne? "

"To anan fa ake yin ta, don in za a kashe shi bai san sunan asibitin da suka zo ba."

Gudu-gudu sauri-sauri ya fita harabar asibitin yana karantowa Alhaji sunan asibitin a (notice board).

Ya koma reception yana trying wayar Hajiya amma aka ce da shi (not available). Dole ya hakura ya

"maida wayar cikin aljihu, ya koma ya zauna fuskarshi cikin tafukan shi kamar ya ce  Wayyo Allah. "

Har zuwa lokacin da Alhaji da masu tsaronsa (Escort) dinsa gami da masu take masa baya wadanda

"yawanci ma aikatan DAMBATTA SHIPPING ne suka iso, bai san sun iso ba."

"Alhajin yasa hannu ya zungure shi, ya yi firgigit ya mike tsaye. Ya ce,  Ina ne ofishin babban likitan? "

"Da hannunsa ya nuna masa ya ce,  To wuce mu je, tunda bakin naka ya mutu. "

Suka rankaya gaba daya a lokacin Dr. Abayomi ya fito daga wannan dan tsakurkurin dakin da aka

shigar da Rukayyah zai shiga ofishinsa.

Ganin Aliyu Dambatta gaba gadi wanda fuskarsa ta zamo sananniya ga kowa cikin kafafen yada

labarai ya yi hanzarin mika mai hannu kana ya yi masu izinin shiga ofishin sa. Shi da Saifuddeen kadai suka shiga ragowar dakatawa suka yi a kofar ofishin.

"Suka sake gaisawa da Doctor, Alhaji ya ce na zo ne a kan case din wannan yarinyar da ku ke aiki a"

kanta.

"Ya ce,  Rukayyah Usman ko? "

"Alhaji ya ce,  Eh. Cikin harshen Turanci."

"Ya ce,  Ku ba mu mintuna ashirin, result din ta bai gama fitowa ba har yanzu. "

"Suka ci gaba da zama shiru, shi likitan yana ta rubuce-rubuce a file din Rukayyah. A lokacin ne Alhaji"

ya samu damar tambayar Saifuddeen abin da ya samu Rukayyah. In ban da zufa ba abin da yake yi don ya lura karamin abu ne ya zama babba.

"Baya son ya tona asirin matarsa balle ga Alhaji, wanda ya fahimci dama yarinyar ta gama sire masa"

tun wulakancin da ta yi wa uwarsa.

Amma sai ya ji tsoron kada Alhaji ma ya yi masa mummunan zargin da Hajiya ta yi masa. Iyakaci

"Alhaji ya ce ya rabu da Salimah, to a shirye yake da ya aikata hakan. Ba don baya son ta ba, illa don yanzu shi ma ta fara ba shi tsoro."

Nafisah ta sha gaya masa cewa matan Bare-bari suna iya kashe kishiya murkus har lahira saboda

"kishi, don haka tun da ya sake ya auri  yar Modu, bai isa ya kara kallon wata diya mace a duniya da sunan so ba, sai ko a bayan ranta. Bai taba yarda ba sai yau."

"Ya nisa ya cije, ya daddage ya shiga gayawa Alhaji komai tiryen-tiryen. Bai rage komai ba bai kara ba"

"har rigimar da suka kwana suna yi a daren jiya na dole sai ya maida Rukayyah. Ya ce,"

" Kuma wallahi Alhaji ni abin da ya daure min kai ba cewa na yi da ita ina son Rukayyah ba, ba cewa"

na yi zan aure ta ba.

"Kawai kiranta na yi a zo mu ci abincin tunda ita ta girka, shi kenan. Ban ankara ba sai gani na yi ta"

hawo benen da gudu ta tankado ta.

"Alhaji ya yi kwafa ya ce,  Ni ba zan ce ka rabu da matarka ba, don ban san irin son da ka ke mata ba,"

"ba kuma mutunci na ba ne na kashe maka

Please Login or Register in order to submit comment