You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taimakawa kwarai ko"

"Rukayyah ba ta dawo cikin tunanin ta ba, ta koyi abubuwa ta ci gaba da gudanar da al amuran rayuwarta tamkar kowa."

"Rabi ta dauko robar ruwan (Eva) mara sanyi sosai ta mikawa Saifuddeen, ya karba ya bude murfin ya"

"kafa kai yana sha. Tun bai mika mata ba ta kama robar ta rike gudun kada ya shanye ita ba ta sha ba. Ya sakar mata suka yi mata dariya shi da Rabi, ta kama robar ta soma sha kamar yadda ta ga yana yi."

Alhaji ya aiko Asi ta zo ta kira Saifuddeen su ci abinci ya tafi gida dare ya yi. Ya mike a salube daga gadon

Rukayyah kamar wanda aka zarewa laka. Hajiya na tambayarsa ko zai samu zuwa Jalingo goben daurin auren Rukayyah?

"Gaba daya yanayin fuskarsa ya sauya, fararen idanunsa suka canza launi daga farare zuwa jajaye kamar"

"an watsa masu barkono ya ce,  Da kyar ne! Daga haka ya juya zai fita."

"Ai kuwa Rukayyah ta duro daga gado da gudunta ta bi shi ta tokare hanyar wucewa, ta hanyar wara"

"hannuwanta biyu hagu da dama a bakin kofar, ta kuma kankaneta, wato ba zai fita ba."

"Daga shi har Hajiya matsanancin mamaki ya kama su. Rukayyah da ba ta san ya ake kuka ba, amma sai"

"ga ta tana yi. Tamkar jaririn da uwar shi na ba shi nono, bai koshi ba, ta tsige shi ta ajiye shi za ta fita."

"Daga shi har Rabi da Hajiya sun yi sororo, ganin Rukayyah ba ta da ranar daina kukanta, ya juya ga Hajiya"

yanayin fuskar shi ya nuna neman shawarar abin yi. Ta ce  kama hannunta mu je dining din .

"Har ya kai hannu zai kama hannun nata, sai kuma ya fasa da sauri ya maida hannuwanshi ya sarke a baya,"

ya yi dummm! Kalamun Hajiya na dazu suka dawo masa.

 & ..ba mamaki fyade ka yi mata.

"Ya runtse ido ya ce,  Hajiya kin yi izini, in kama hannun nata? "

"Ita kanta Hajiyar matsanancinyar kunya ce ta kama ta, domin ta fahimci abin da ya tuno, wanda ta san"

ba ta kyauta ba. Domin an ce  Ka kyautata zato ga dan uwanka Musulmi balle dan ka na cikinka. Duk abin da ka furta a kan shi na ALHERI ko sharri shi zai bi shi.

"Ta yi murmushi ta ce,  Ba komai, kama ta mu je ai lalura ce, ko Musulunci ya yarda da hakan. "

"Ya kama hannun ta suka jera suka fito falon inda su Alhaji suke, Hajiya da Rabi na bin su a baya."

"Ba Alhaji Dambatta mahaifin Saifuddeen ba, ba Mama Amina mahaifiyar Rukayyah ba. Haka ba Hajiya"

"Umaimah mahaifiyar Saifuddeen ba, babu wanda cikin su zuciyarsa ba ta gaya mai abu guda ba, a lokacin da Saifuddeen da Rukayyah suka doso su, rike da hannun juna. Fuskar Rukayyah cike da annurin"

"ganin cewa& ., Mamanta ya fasa tafiya ya bar ta& & !"

"Toamma cikin su babu wanda ya furta tunanin nasa a fili, kowa ya hadiye abinsa cikin cikinsa. Saifuddeen"

"ya ja kujerar kusa da Alhaji ya zauna yana cewa,  Sorry Alhaji& mun barku kuna ta jiran mu, rigimar"

Rukayyah ce wallahi.

"Rukayyah ma ta ja ta kusa da Saifuddeen ta zauna tana cewa,  Sorry Alhaji. Alhaji da Mama Amina ba su"

san san da suka sa dariya ba.

Hajiya tana ba su labarin cin abincin Rukayyah da rigimar ta lokacin fitar Saifuddeen. To magana in mai

tsayi ce Rukayyah ba ta iya kwaikwayonta sai ta yi shiru.

"Sai dai fa duk abin da ta ga an yi ita ma sai ta yi, komai Saifuddeen ya bude ya zuba a filet din shi ita ma"

"sai ta zuba a nata filet din, to amma fa ba control afkawa kawai take. Filet din ya cika ya yi tsiri har yana zuba a kasa babu wanda ya yi yunkurin hana ta."

"Ya sanya cokali yana ci ita ma ta soma ci duk da a koshe take, in ka ganta kamar ba abin da ya same ta."

"Ya dube ta ya girgiza kai ya ce,  Yanzu wannan uban abincin duk a cikin ki za ki zuba shi?"""

"Ta dube shi ita ma ta ce,  Duk a cikin ki za ki zuba shi. "

"Saifuddeen ya yi dariya ya ce,  Rukayyah in aka saba da lalurar ta ba za a sha wahalar communicatingda"

ita ba.

"Da yake ta cika bakinta taf da abinci ba ta samu damar cewa komai ba, Alhaji ya ce,  Nima haka na gani. "

"Shiru ta ratsa na a kalla mintuna uku. Baka jin komai sai karakainar cokula cikin tangaran. Alhaji ya ce,"

 To yaaa? In ce ko goben za ka samu zuwa Jalingon tare da mu daurin auren RUKAYYAHH& & ???

"[12/17/2019, 19:16] Takori: Ko tantama baya yi (Dambatta Shipping -Dambatta Motors) ne yau a"

"gabansa. Wadanda ya yi tattaki har Kwatano ya sayo dankareriyar motarsa da yake fantamawa da  yanmata a cikin garin Gombe da ita a katafaren kamfanin su, domin an hado mai da wata magazine mai dauke da tallan duk wasu abubuwa da kamfanin ke yi wanda a kowanne shafi hoton Saifuddeen ne. Ya"

"dade yana mamakin kamanninsa da Rukayyah, ya sha tambayar kansa to ta ina?"

"A hanzarce ya mika mai hannu, Saifuddeen kamar ba zai mika ba, can dai ya daure ganin su Alhaji na"

"kallonsa, ya mika masa ya kuma mikawa abokin su kai musabiha, daga nan ya maida hannuwansa, sai"

"kauce-kauce yake da kai, don shi kam yadda ya tsani ya bude ido ya ga mutuwarsa haka ya tsani kallon fuskar fiance din Rukayya ko a kan me?"

"Aliyu dai ya lura bai samu shiga ba wajen Yayan Rukayyah, don haka ya tattara kafatanin hankalinsa ya"

mikawa Alhaji Aliyu Dambatta wanda ya ce ya saurare shi da kunnen basira.

"Ya fiddo takardun asibitin Rukayyah ya warware, ya soma yi wa Aliyu bayani dalla-dallah, gumi ya soma"

"wanke shi tun daga kai har yatsan kafarsa, Alhaji ya kammala bayaninsa ya linke takardar ya mikawa Saifuddeen ya karba ya sanya cikin brief case din Alhajin, ya kare bayanin da cewa."

" To ka ji, mu ma nan da muke zaune da ita, har da uwar da ta haife ta kuwa, Rukayyah ta manta mu, ko"

"yadda ake alwala ba ta sani ba, amma komai ka koya mata a hankali za ta iya."

"Don haka idan kana ganin ba matsala, ta fannin kai kanka, iyayenka da iyalinka, to karfe hudu na cika"

"kamar yadda aka sa insha Allah ba za a gota ba. Za a daura muku aure ka dauki matarka ku tafi, don yarinyar da ba ta san inda rayuwarta tasa gaba ba, ba amfani a tsaya yi mata biki. Don haka muna"

sauraron amsarka.

Daga Aliyu har abokinsa kamar ruwa ya cinye su. Zuciyar Saifuddeen ta ci gaba da zabalbala kamar ana

luguden sakwara a turmi.

Sai dai shi kansa bai san dalili ba. To tsoro yake kada Aliyu ya ce baya yi ko kada ya ce yana yi? Allah

masani.

"Dakikai suka wuce suka zama mintuna, amma ba wanda ya yi tari a cikinsu. Can dai abokin Aliyu ne ya yi"

"karfin halin cewa,  Ko za mu iya ganin ita Rukayyan? "

"Alhaji ya ce,  Why not?Kai Saifuddeen tashi maza ka je ka zo musu da Rukayyah. "

"Yana zaune bai tashi ba, kamar wanda aka sa kusa aka kafe shi a wurin. Gaba daya tunaninsa baya a"

"duniyarsu Alhaji, yana can a duniyar tunanin makomar rayuwar Rukayyah Usman Jalingo, a Gombe gidan Aliyu Dukku."

"Sai da Alhaji ya sake maimaitawa, har yanzu Saifuddeen bai ji ba. Alh. Usman ya kai hannu ya girgiza"

kafadunsa a firgice ya dago yana bin kowa da kallo daidaya.

"Alhaji ya lura da kidimewar da ya yi, yana tsammanin Aliyu ya bada amsa ne bai ji ba yana can a duniyar"

tunani.

"Ya ce,  Tunanin me ka ke ta yi ne haka ana ta magana ka yi banza da mutane? Cewa na yi ka je ka zo da"

Rukayyah.

Ya mike kamar wanda kwai ya fashewa a ciki a salube ya nufi cikin gidansu Rukayyah.

Dakin Maman cike yake da taron mata makotansu da aminan arzikinta wadanda sun zo tayata urnar

"daurin auren Rukayyah ne, inda taya murna ya koma jaje da koke-koken wadanda suka saba da Rukayyah."

"A lokacin ita Rukayyah zaune take kawai tana bin kowa da kallo daidai, in ta ga dama ta kwaikwayi"

maganr su in ta ga dama ta yi shiru ta kyale su. Amma da ganin fuskar ta ka san cikin damuwa take.

"Munaya ya hango a bakin famfo tana zukar ruwa, ya ce  Zo nan Munaya. Da gudu ta zo gabansa tana"

dariya. Ya soma watso mata tambayoyi.

 Dazu da ku ka shiga Rukayyah ta yi kuka?

"Munaya ta gyada kai,  Ta yi kuka sosai ma, amma da ta ga Anti Asi da Hajiyar Legas sai ta yi shiru. "

"Ya ce,  To je ki maza kamo hannunta ki kawo min ita nan. Ki fadawa Hajiya su Alhaji ne suka ce a zo da"

ita.

Ta yi ciki da gudu shi kuma ya koma soron ya jingina da bango.

Ba komai ya hana shi shiga cikin gidan ba sai tsoron irin rungumar da Rukayyah za ta kawo masa a cikin

"mutane, wanda kuma ke sanya shi cikin wani hali na bala in da bai san irinsa ba bai taba ji ba akan mace, a kafatanin rayuwarsa."

"Sai ga ta sun fito tare da Munaya, ta riko ta kam-kam tana ta murnar Rukayya ta biyo ta ba tare da ta sha"

"wahala ba. Tana shigowa soron suka yi ido hudu ta kuwa tafi da gudu za ta kankame shi, ya daka mata tsawa tun kan ta karaso ya ce,  Stop it Rukayyah  Tare da fiddo dukkan idanunsa waje."

"Ba karamin razana ta yi ba, tuni ta ja birki a inda take tare da kankame jikin ta wuri daya cike da tsoro ta"

"runtse ido kamar mai jiran saukar duka. Sai duk ta ba shi tausayi ya dan saki ya ce,"

 Shige mu je. Ya yi gaba Munaya ta kama hannunta suka bi shi a baya.

"Aliyu ya dago ido a hanzarce yana kallon Rukayyah da ke shigowa, wadda ke tafe kanta tsaye abin ta. Ba"

"ta daddara ba dai kusa da Saifudden (Mamanta) ta nufa saura kadan ta zauna a cinyarsa ya yi wuf ya matsa ta yi mugun zama, irin wanda ba ka zata ba din nan damma! Akan kafet."

Ta juya tana kallon Alhaji da murmushin sanayya a fuskarta amma ko ubanta ba ta san Allah ya yi ruwan

tsiransa a falon ba.

"Jikin Alhaji Usman ya shiga rawa, cikin matsanancin tashin hankali. Tabbas babu maganar wasa cikin"

"al amarin Rukayyah, fuskar nan tata ma abociyar fushi da zumbure-zumbure a yayin da aka bata mata rai a yau (very innocent) kamar ta yaro karami dan shekaru uku."

"Ya matsa gabanta a hankali ya ce,  Rukayyah. "

"Ta juyo da idanunta daga kallon gudun da fanka ke yi a sama, tana kallonsa, ita ma ta ce ""Rukayyah. "

Cikin wata irin siririyar murya.

"Ya ce,  Rukayyah, nine babanki, ba ki gane ni ba ne?'"

"Ta kuwa maimaita masa sak yadda ya fadi, babu alamar sanayya ko kankani a tare da ita. Abin ki da da"

"da mahaifi, sai ga hawaye jabe-jabe a idanunsa."

"Ita ma sai ta soma hawaye, amma nata babu (emotion), wato dai yinsa kawai take ba tare da ya je har"

karkashin zuciyarta ba.

"Aliyu da abokinsa suka mike tsaye, cike da tsoro suka tasam ma kofa, ba su ce uffan ba. Alhaji Dambatta"

"ya yi karfin hali ya ce da su,  Ya za ku tafi ba ku ce komai ba? Ko mu fita ne ku ganta sosai?"""

"Bakin Aliyu na rawa ya ce,  A a, hakan ma ya yi mun ganta ai Allah ya ba ta lafiya. "

"Suka sa kai za su fita. Ya yi kokarin danne bacin ransa ya ce,  To ai ba mu ji wata kwakkwarar amsa daga"

gare ku ba.

"Abokin yana zura takalmansa cikin rawar jiki da rawar murya ya ce,  Am, eh, nan da rabin awa za mu"

"turo da amsar, don sai mun yi shawara da manyanmu tukunna. "

"Alhaji ya so ya sake tambayar su,  Waya za ku yo ko dan aike za ku turo mu jira ku? "

"Ya ga alama ba sa ko son zancen, kafin ya ankara har sun fice, sai tashin motarsu suka jiyo."

"Ya juyo agogonsa na fatar damisa ya ga karfe biyu da rabi daidai na rana, don haka za su ba su lokacin"

zuwa karfe uku da rabi na yamma kamar yadda suka ce din don jin wadda suke ciki.

Saifuddeen dai takaicin Alhaji ya hana shi magana ga abu kiri-kiri sun nuna masa ita kanta Rukayyah

tsoron ta suke ji amma sai wani lallaba su yake yana kwantar da murya yana bata lokacin sa suna zillewa.

Wato dai masifar Alhaji a kan sa kadai ta tsaya sauran mutane ko za su yaba masa kashi ba zai cira kai ya

dube su ba.

"Ya yi kwafa ya mike don raka Rukayyah cikin gida, don Munaya tun shigowar ta ya ce ta koma. Yana"

mikewa kuwa ita ma ta mike suka fice tare har kofar dakin Mama Amina.

"Nan ya tsaya ya ba ta hanya ya ce,  To wuce ciki ki zauna. Wannan karon ba ta yi musu ba ta wuce don"

"tana tsoron kada ya kuma yi mata tsawar da ya yi mata dazu, ta kuma fahimci ba fita zai yi daga cikin gidan ba."

Wannan karon kai tsaye wajen Munaya ta nufa. Munaya har da tsallen ta Yaya Rukayyah ta gane ta.

Ya koma falon ya ci gaba da taya su Alhaji zaman jiran tsammanin-warabbukan da suke yi. Zuwa lokacin

an samu Alhaji Usman ya yi shiru ya daina kukan da yake yi na tausayin Rukayyah da taimakon nasihohi masu ratsa zuciya kan muhimmancin yarda da kaddara da Alhaji Dambatta da sauran abokansa dake wurin suke ta yi masa wadanda duk tsofaffin ma aikatan gwamnati ne.

Saifuddeen ya koma inda ya tashi ya zauna. Kallo daya za ka yi masa ka fahimci wannan karon hankalinsa

"a kwance yake ba kamar dazu ba (for he has no fear for the outcome), wato baya da fargabar abin da zai biyo baya. An ce labarin zuciya a tambayi fuska."

"Karfe uku ta yi shiru, uku da kwata, nan ma shiru, har uku da rabi babu sakon Aliyu balle wayarsa. Wani"

"daga cikin abokan Alh. Usman ya ce,"

 Da alama yarannan sun maida mu sa anninsu.

Alhaji Usman ya waiga ta wundo ya ga yadda jama ar da ya gayyata daurin aure suka fara taruwa.

Hankalinsa ya yi matukar tashi cike da tunanin da wane bayani zai je yana rokon su su koma inda suka

"fito, yaron ya fasa auren ta? Ko ko bututun magana zai dauka ya yi shela cewa kowa ya tafi an fasa?"

Shi dai Alhaji Dambatta bai ce komai ba. Tunanin asibitin da ya dace ya kai Rukayyah a London yake yi da

auren Aliyu a kanta ko babu.

"Yo wane aure ne ga yarinyar da ba ta san inda kanta yake ba, balle hakkukuwa na aure, na mata a kan"

mijinta?

"Ban da ma rigima irin ta Usman ai shi Rukayyah idan  yarsa ce, ko kuwa a ce yana da iko mai karfi a kanta"

"da ko shekara goma za ta yi babu aure a kanta a wannan halin dai da da take ciki ba abin da zai dame shi da zamanta tunda ba a kanshi za ta zauna ba, illa ya yi ta kokarin nema mata magani a duk inda yake"

cikin duniya.

Shi magani dace ne kawai ba wai babu shi ba na kowacce irin cuta da Allah ya saukar. Abu biyu ya

"amince ba su da magani a duniya, tsufa da mutuwa."

Jama a suka soma cika dankam tun daga farkon layin su Rukayyah har kofar gidansu wasu a motoci wasu

"a babura, wasu a sayyadar su."

Kasancewar Alhaji Usman fitaccen ma aikacin jarida kuma tsohon dan boko a garin Jalingo mai hulda da

jama a daban-daban.

Duk wani mai kallon labaran gidan talibijin na jihar Taraba ya san fuskar Usman Jalingo da zazzakan

turancinsa mai kama da na Obaman Amurka. In ban da gumi ba abin da yake yi abin tausayi shi kuwa Alhaji hankalinsa a kwance yake.

"Ya ce da shi,  To sai me don an bai wa jama a hakuri? Su ba su san kaddara ba? Ake daurawa ma a"

kwance balle ba a daura ba? Ka ga don Allah ka saki ranka ni wallahi in ta nine ma ba za a yi wa Rukayyah aure yanzu ba.

"Usman bai tanka ba, sai yarfe gumi kawai yake yi (Burin kowanne uba na kwarai ya aurar da  ya yansa"

"mata idan sun kai munzalin hakan, domin samun dawwamammen kwanciyar hankali da sauke nauyin da Allah ya dora masa). Wannan ne abin da ke a zuciyar shi a zahiri."

"Karfe hudu saura mintuna goma, wani dan acahaba ya ratso a guje ya yi mugun birki a kofar gidan"

"Usman Jalingo, saura kadan ya murjewa Saifuddeen yatsun kafa wanda ya fito kofar gidan yana magana da Nafisa a waya tana gaya masa cewa tana filin jirgi ne ya zo ya dauke ta."

Ya gaya mata cewa ba zai samu zuwa ba ta dauko shatar tasi kawai tun daga Yolan. Ya juya yana kallon

tsageran dan achaban da ya kusa nakasa masa kafa ba don Allah ya kiyaye shi ba.

Ya kashe machine din ya sauko yana tafiyar su irin ta  yan chaburos ya iso ga Saifuddeen. Ya wani

"karkace kamar ya karye ya daga mai hannu shi bai yarda ba hadadden gaye, ya ce,"

" Hi, sannunka samari. "

"Ya yi murmushi ya ce,  Kai ma sannun ka. Ya zura hannu cikin aljihun ratattakakken jeans dinsa wanda"

ya sha faci a ko ina ya fiddo ambulan fara kal da ita ya mika masa.

Ya gicciye yana yi masa wata irin amgana tasu ta  ya yan iska mai ban haushi.

" Wato kana ji ba? Wani gaye ne ya tare ni bakin layin nan ya hada ni da na shan fetur, ya kwatanta min"

nan gidan ya ce in kawowa maigidan.

"Da alama kai dan gidan ne, shi ne nake so ka taimaka ka mikawa Babanka. Ya karba ya yi murmushi ya"

"ce,  Kwarai ni dan gidan ne. "

Daga haka ya sanya hannu a aljihu ya dauko rafar  yan naira dubu-dubu da bai san adadinsu ba ya mika

"masa ya ce,  To ga shi nima na bayar a kara fetur. Ka yi min addu a Allah yasa ALHERIN da na ke tsammani cikin takardar shi ne ka kawo min. "

Warce kudin ya yi da karfin gaske ya fara killace su a kololuwar aljihunsa na bayan wando don yana

zaton kwalele ne zai yi masa ya yi maganin dan banza. Sai da ya hau mashin dinsa ya burga ya tashi ya ba shi wuta sosai ya ce.

 To Allah ya hada ka da ALHERI. Sai kuma ya koma zuba godiya kamar ya zubar da hakoransa. Don yana

"da tabbacin zuwa lokacin kam in ma wasa Saifuddeen yake yi masa, to ko shi ne jirgin sama bai isa ya kamo shi ba."

"Amma akasi ga tunaninsa, Saifuddeen bai ko tsaya sauraron godiya da fatar ALHERIN da yake ta kwarara"

masa ba ya juya da sassarfa ya yi cikin gidan rike da ambulan. Dan achaba dai ya tabbatar yau ALHERI ne ya fito da shi cikin garin Jalingo baki daya. Don haka ya buga babur dinsa a hankali ya tafi.

Ya same su kamar yadda ya bar su wato jigum-jigum ko tari ba mai yi a falon. Ya karasa cikin ladabi ya

russuna ya mikawa Alhaji Usman ya ce.

" Wani yaro ne ya kawo, ina tsammanin daga Aliyu take. "

"Jikin sa na bari ya mika hannu ya karba, yana mai addu ar Allah dai yasa Aliyu ba tozarta shi zai yi ba."

"Gaba daya suka maida hankalinsu ga Alhajin wanda karkarwar da hanunshi ke yi yasa ambulan din subucewa ya fadi, sau biyu yana kokarin farkewa yana subucewa. Ganin haka Alhaji Dambatta ya mika hannu ya dauki takardar ya farke ya warware. Ga abin da ke ciki;"

Z

uwa ga Alhaji Usman.

"Bayan gaisuwa, ina mai baka hakuri ni Aliyu a gaskiya ba zan iya auren Rukayyah da ciwon hauka ba."

"Ni daman na dade ina mamakin dalilin ka na kafewa sai ka aura min ita, alhalin ta ce ba ta sona. Sai"

"yanzu na gane wato ciwon hauka gare ta, shi ne ka so ka yaudare ni ka hada ni da wahala. Iyayena ma na yi shawara da su ba su amince ba."

"Har yanzu ina son Rukayyah ba wai bana sonta ba, don tana da abubuwan da duk namijin da ya san"

"ciwon kansa zai so ta. Don haka ku nema mata magani in ta warke a neme ni a shirye nake ko bayan shekara nawa ne da in aure ta duk da na san ciwon hauka baya warkewa gaba daya, zan daure in lallaba"

in yi maleji a hakan.

Duk wasu abubuwa da na bayar na bar mata duniya da lahira ina taya ku addu a Allah ya ba ta lafiya.

Sa hannun

Aliyu Lamido Dukku.

"Alhaji ya yi murmushi ya mikawa Usman ya ce,  To ka ji abin da nake gaya maka, yanzu ina amfanin da an"

daura ya aiko da wannan takardar ya ce ya sake ta?

"Allah sarki Alhaji Usman hawaye ya soma ya ce,  Karanta min in ji don Allah. "

A fili Alhaji Dambatta ya karanto musu takardar kowa ya ji.

"Saifuddeen da ke makure can gefe ya lumshe ido. Wani matsanancin nishadi na binsa, wani sabon farin"

ciki da bai taba tsintar kansa a ciki ba ya baibaye zuciyarsa.

Ya rasa inda zai sa kansa don farin ciki. Wannan na nufin& & ALHERIN da Allah ke son kullawa a

tsakaninsu ???

*****

Y

"a gurgusa da gwiwoyinsa, ya matso gaban Alhaji Usman ya gurfana, bakinsa na motsi, amma ya kasa"

magana.

"Alhaji Usman yasa hankici ya share hawayen idanunsa ya ce,  Yaya ne Saifuddini? Bakin ka akwai magana."

Ba komai haka Allah ya so. Daure ka je ka sallami jama ar nan da ke waje. Ka shaida musu cewa su yihakuri wani uzuri ya sa an fasa daurin auren.

"Ya girgiza kai cikin sanyin murya ya ce,  Alhaji in kun amince mai zai hana ni a DAURA DA NI?"""

"Alhaji Aliyu, wanda ke sunkuye da kai yana danne-danne cikin wayarsa, ya yi hanzarin dagowa kamar"

wanda aka tsikara da allura.

"Ya zubawa Saifuddeen ido kamar bai ji abin da ya ce sosai ba, inda shi kuma ya yi hanzarin sunkuyar da"

kai cikin matsanancinyar fargabar karbar da za su yi wa zancensa.

"Alhaji Usman kuwa bai ji abin da Saifuddeen ya ce sosai ba. Ko kuma ya jin, zuciyarsa ce ba ta amince da"

abin da ya jin ba? Ina Saifuddeen ina Rukayyah? Igiyar rakumi ta yi nesa da kasa! Wai an ce yaro tsaya matsayinka kada zancen  yan duniya ya rude ka.

"Wanda yake daidai ajin Rukayyah ma ya ki ta a halin da ta samu kanta, balle Saifuddeen din da minti"

"daya wannan mai matukar muhimmanci ce a gare sa. Wurin maida kobo ya komadari. Ina ya ga lokacin zama da MAHAUKACIYA, kamar yadda Aliyu ya ce?"

"Alhaji Aliyu ya saki fuska sosai ya dubi Baban Rukayyah da dan guntun murmushi a fatar bakinsa ya ce,"

 To kai ka ji abin da dan naka ya ce. Me ka gani?

"Sauran abokan Alhaji Usman duka suka hada baki suka ce,  Kai abu ya yi kyau. Gaishe ka yaro dan"

albarka! Insha Allah ALHERI ne cikin auren nan domin irin wannan auren Allah kadai ya san iyakar alherin da ke kunshe cikinsa

"Alhaji Usman ya girgiza kai cikin rashin amincewa ya ce,  Ku rabu da Saifuddeen, tausayin  yar uwarsa"

kadai ya debe shi. Amma ina Rukayya ina Saifuddini ?

"Alhaji Aliyu ya tare shi a dan fusace,  Ban gane ba? Wani bambanci ne tsakanin Saifuddin din da"

Rukayyah?

"Alhaji Usman ya jujjuya kai, ya gyara zamansa ta hanyar mike kafafunsa da ya tankwashe ya ce,  Ku dubi"

"wannan al amari da idon basira. A cire tausayin Rukayyah na abin da ya same ta, sannan a cire batun"

 yan uwantaka da ke tsakaninsu.

A yi duba ga mataki na matsayin rayuwar dan adam (Hierarchy of social classes). Saifuddeen ko babu

lalura ba ajin auren Rukayya ba ne.

Ni Usman ba ni da komai in ban da motar da nake hawa da gidan da nake ciki. Idan na dauki Rukayyah

"na aurawa Saifuddeen, na wuce matsayin da Allah ya ajiye ni (na wuce gona da iri)."

Sannan ita ba lafiya ba. Da a ce lafiyarta kalau ne ma to da da sauki. Saifuddeen da yanayin sana ar shi

"mutum ne

Please Login or Register in order to submit comment