You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mukulli. Shi kansa bai san dalilin wannan

"sammakon nasa ba. Amma da ya yi tsam da ransa ya fahimci Hajiya yake so ya riga tashi don kawai ya samu damar ganin Rukayyah, da yadda ta kwana."

To sai kuma ga shi sammakon nasa ya zama na banza masu gidan basu bude kofa ba. Yan kuma

jin tsoron ya buga ya lalata al'amarin.

"Allah mai jinkan bayi, sai ga Rabi ta bullo daga sashenta rike da makullai zata shiga don daura"

abin Karin-kumallo kafin masu gidan su fito.

"Mamakin ganin Saifuddeen a wannan farar safiya ya kamata, don bata taba ganinsa ya yi wannan"

"sammakon ba. Koda yake ba abin mamaki ba ne, tunda kurwarsa tana gidan. Rabi ta ce a ranta,"

"""Amarya ko ta buzuzu ce ana sonta, balle Rukayyah sarauniyar kyawawa (kamar yadda ta rada mata)."

"Suka gaisa, sannan tasa mukulli ta bude kofar. Kai tsaye dakin su Rukayyah ya nufa, ya murda"

kofar.

"Munaya barci ta ke sosai akan sallaya, Rukayyah kuwa zaune dungurgur a tsakiyar gado ta hada"

kai da gwiwa kamar wadda ta rasa Uwa da Uba. Ita kanta bata san abin da ke damunta ba.

"Yana shigowa ta sauko da gudun gaske ta yi masa abin da ya fi so, wato (jin Rukayyah a cikin"

"jikinsa). Da rawar jiki ya soma sauya akalar tata manufar wadda tayi ne a dalilin  kewa da wasu bakin abubuwa daban da bata sani ba cikin dan kankanin tunaninta, har ta kai ga zubewa akan carpet. Gluedin nata ya bita ya cigaba da abin da yake ganin shi ne kadai kwanciyar hankalin dukkaninsu."

"Gaba daya ta zama tamkar wata rakuma, shi ke da akalar rayuwarta. Yana cikin jan linzamin"

"rayuwar tata yadda ya ke so, gab da cikamin al amarin sai ji ya yi can cikin kwakwalwarsa Munaya na tambayarsa cikin muryar magagin barci,"

"""Yaya Rukayyah fadowa ta yi daga gadon ne?"""

"Cikin matsananciyar faduwar gaba da katsewar gudun jini a cikin jikinsa, domin gaba daya ya"

"manta da Munaya. Bai juyo ba ya tattara duk wani sauti da ya saura a makoshinsa, ya ce, ""Eh"". Yana kokarin gyarawa Rukayyah botirin suwaitar ta da ya balle."

"Ya ciccibeta ya aza bisa gadon ya ja da baya ya jingina da garu yana maida lumfashi a wahale,"

idanuwansa jawur kamar na mai ciwon 'apolo'. Sun kuma kankance ko Munayar baya gani sosai.

" Security din Hajiyar ta ci gaba da zubo masa tambaya,"

"""To ko mu sauke katifar kan kafet mu dinga kwana a kasa?"""

"Bai amsa mata ba, ta koma kusa da Rukayyah, wadda har zuwa lokacin idanunta a rufe suke,"

"numfashinta bai dawo dai-dai ba, ta ce"

"""Ki tashi ga Yaya Saifuddeen ya zo""."

"Zuwa lokacin shi a zaune yake dirshan a kasa, cikin matsanancin ciwon mara, ya juya masu baya."

"Rukayyah ta mike zaune ta ce,"

"""Saifuddeen""."

Da sauri ta isa gareshi ta juyoshi tana girgizawa. Munaya ma ta karaso ta ce

"""Yaya Saifuddeen, baka da lafiya ne?"""

"Ya yi banza da ita, ta ce"

"""Ko a kira Hajiya ne?"""

Da sauri ya kada mata hannu. Ganin ya rike cikin shi da dukkan hannuwan shi ta ce

"""To in kawo maka kanwa?"" Ya daga mata kai da sauri."

"Ya dauka kichin zata je kawo kanwar, ashe tana da abarta cikin kofi data kada jiya da daddare ta"

"sha, ruwa kawai ta zuba a ciki ta karkada ta mika masa."

"Don haushi ko karba bai yi ba, ya mike a daddafe zai bar dakin. Rukayyah ta rikeshi tana kuka."

Bai saurareta ba ya kwace jikinsa ya fita.

"Ta biyoshi har falo tana ta yi kamar ranta zai fita, suka yi kicibus da Rabi wadda ke jera abinci a dining."

Cikin tausayin Rukayyah ta ce

"""kai kuwa don Allah don Annabi Babangida ka zauna da ita""."

"Gwiwarshi ta yi sanyi kalau, ya dakata har Rukayyah ta cimmashi ta rikeshi ta baya, ya ce"

"""Mama Rabi asibiti nake so inje in dawo. Ita kuma Rukayyah ba zata gane ba& "". Ta ce"

"""To ku tafi tare mana, idan Hajiyar ta sauko sai inyi mata bayani""."

"Hakika da shawarar Rabi abar dubawa ce, da ita ce kadai maganin ciwonsa. Amma sanin kansa"

ne yin hakan dai-dai yake da fuskantar fushin Hajiya mai tsanani.

"Ya koma cikin kujera ya zauna, shiru, bai ce komi ba."

"Rabi ta fuskanci Saifuddeen cikin damuwa yake. Ita ma rukayyah ta bishi ta zauna, ta kwantar da"

"kanta barin kafadunshi, tana hadiyar zuciya, irin na wanda ya ci kuka kamin ya sami abin da yake so."

"Rabi ta je ta dauko abincin karin kumallo ta kawo leda ta shimfida a gabansu, sannan ta daura"

"tiren, ta daga ido ta dubesu."

"A yadda ta gansu sun mannewa juna kamar suna tsoron a rabasu, sai ta ji su duka sun bata"

tausayi. Ta wuce kichin ta barsu nan tana addu'ar Allah ya ba Rukayyah lafiya.

"Ya dago ya dubeta, ita ma ta dubeshi, suka yi murmushi. Ya zunkuda kafadarshi da ta dora karfi"

"akai, ta goce, suka yi dariya. Ya ce,"

"""Rak, rigima!""."

Ya sauka a kujerar ya zauna ya soma hada tea itama ta hada bayan ta rambada dan banzan

"sukari da gahwah (coffee), ya yi dariya ya ce,"

"""Yau zan gani idan kin san dadin harshenki, ko baki sani ba?"""

"Ita ma dariyar ta ke, ta dauki kofin ta kai bakinta."

"Wani irin bauri mai hade da mugun zaki ya daure mata harshe, ba shiri ta kwararo na bakinta"

"bisa ledar. Ya yi murmushi ya ce,"

"""Good, ashe kin san bazai yi dadi ba, kika yi ta laftawa?"""

"Ta kai hannu kan nasa kofin zata dauke, ya rike abinsa tamau, ta  ja- ya- ja duk shayin ya bare a"

"jikinsu. Ta soma gajiya, ta ce,"

"""Saifuddeen, ba ni""."

"Cikin mamaki ya ce,"

"""Anki a baki, sai kin ce sweety Saifuddeen& .""."

"Ta maimaita cikin sigar tambaya,"

"""Sweety Saifuddeen& & .???"""

"Cikin murmushin kauna, so da matsanancin bege ya ce"

"""Sweety Rukayyahhh "" Ta yi dariya ta saki kofin tana jan hannuwanshi, ta ce"

"""Saifuddeen, shige mu je& ""."

"Irin yadda Hajiya ke ce mata, in tana so ta shiga daki."

"Ya kama baki, yau Rukayyah mamaki ta ke ta bashi, ba dan kadan ba. Tana da saurin fahimtar abu."

"Ya bita kamar wani rakumi yana sunsunarta tamkar ya hadiyeta. Bata sakeshi ba, tana ta janshi"

"har kofar dakinsu. A Hausarta wai wanka zata yi masa, irin wanda Asi ke mata."

"A nan bakin kofa suka ci karo da Munaya. A zahiri a firgice ta ke, ta ce"

"""Yaya Saifuddeen wallahi banga sanda Yaya Rukayyah ta fita ba. "" Sai hawaye sharrrr& & !."

"Ba karamin tausayi da dariya yarinyar ta bashi ba. Tuni ya mance da haushin da ta bashi, wato"

security ce Hajiya ta saka mishi? Amanar da aka bata ne ta ke rikewa.

"Ya yi murmushi, to amma banda abin dariya irin na Hajiya, 'yar wannan Munayar ta isa ta shiga"

"tsakanin, mata da miji, balle ango da amarya?"

"Dama-dama dai da ita da kanta ta hakura da tsohon mijinta, ta zauna gadin Rukayyah da kanta,"

to da wannan kuwa.

"Ya kamo hannunta suka shigo dakin su duka ukun, ya ce"

"""Haba matas, Rukayyah zata bata a cikin gidan nan ne?"""

"Ya sa hannu a aljihu ya fiddo cakulet din galaxy ya bare ya mika mata, ta amshe ta yi ta murna ya"

ce

"""Zan tafi ofis yanzu, me kike so in kawo miki?"" Munaya mayyar fim din Hausa, ta ce"

"""Kaset mai dan Ibro a ciki""."

Ya yi dariya ya ce

"""An gama matas, ban mu kashe& .?"" Ta bashi hannun, ji kake tass!"

"""Amma ko Hajiya zata ce na zo, ko ban zo ba, ki ce na zo ban shigo ba, ina sauri don haka na tafi"". Ta ce"

"""To""."

"Daga nan kai tsaye ofis ya zarce, duk da cewa ranar Asabar ce, to shi bai ga gidan zama ba."

"Nashi gidan baya marmari, ya fice mai a ka. Gidan Hajiya yafi karfinsa, don bazai iya sanyawa"

"Rukayyah ido kamar yadda Hajiyar ke so ba, alhali yana da masaniyar matsayinta na matarsa, mallakin sa."

"Ya san Hajiyarsa kwarai wurin sa ido akan al'amarin 'ya'yanta, babu mamaki ta gano rauninsa, (yana son"

"bare amaryarsa a leda), abin da take tsananin gudu, take sanyawa takunkumi."

"Can nashi gidan kuma bai da ra'ayin zama, bai son ganin fuskar kowacce 'ya mace a halin yanzu"

"sai Rukayyah, bai son kasancewa tare da kowa a duniya, sai Rukayyah."

"Wani sashe na zuciyarshi ya tunatar da shi cewa ""She is now all yours (taka ce kai kadai yanzun)."

Wannan kwarin gwiwar da tabbacin kadai shi ya haifar da sanadiyyar da ya samu kansa da budo

"tsofaffin aiyuka ya soma aiki a kansu cikin nutsuwa, yana gayawa kansa"

"""Ai komai nisan jifa kasa zai fadi, Hajiya ki gama tsumi da tanadinki dole dai wataran ki bani matata""."

"Yana da tafiya Abuja a gobe da safe, don haka daga ofis dole ya jewa Rukayyah sallama."

"A can gidan Hajiya da Alhaji basu fito ba, sai karfe goma sha biyun rana. Wannan ka'idar Alhaji ce,"

duk karshen sati (week-end) shi da Hajiya basa saukowa sai dai-dai wannan lokacin.

Alhaji mutum ne mai matukar kula da lafiyarsa yana da matukar kokari wurin samarwa kansa

"isashshen hutu. Don haka yake garau, har ya fi matar lafiya da kuruciya."

"Tare suka sauko shi ya nufi dining duk da dai a can saman ya sha ruwan lipton da cake, Hajiya"

"kuwa dakinsu Rukayyah ta nufa, Rukayyah na barci sosai kamar matacciya, Munaya na gaban mudubi tana tsantsara kwalliya da jagira da jambaki caba-caba! Da alama daga wanka ta fito."

"Hajiya ta yi murmushi ta ce ""Anya Munaya ba zaki daina zane fuskarki da jagira ba? Yanzu wa"

"yake yayin wannan? Ko ni tsohuwa bazan yi irin wannan cababbiyar kwalliyar taki ba""."

"Ta zumbure baki ba tayi magana ba, don ba abin da ta tsana irin a kushe kwalliyarta. Ta ce"

"""Rukayyah har yanzu bata tashi ba ne?"" Ta ce ""Ta tashi har ta yi break, komawa ta yi"". Ta ce ""To"

"wanka fa, kuma ince ko kin sa-ta ta yi sallah?"" Ta ce"

"""Ni nayi wanka tun dazu, kuma munyi sallah, ita ce dai bata yi ba"". Ta juya ta fita tana cewa"

"""Kyaleta karki tasheta, in ta tashi ta yi, amma daga yau kada ki kara bari ta koma barci ba ta yi"

"wanka ba"". Ta ce ""To""."

Wasa-wasa Rukayyah barci har karfe hudu ba azahar ba la'asar. Hajiya ta soma damuwa. Zuwa

lokacin ta shigo duba tashin Rukayyah fiye da sau biyar.

"Da ta ga bata da niyyar tashi ta hakura ta hau sama gun Alhaji. Ya ce ""Ya ya Rukayyah ne yau tun"

"safe banji duriyarta ba?"""

"Ta zauna cikin rest chair ta ce ""Ni ma abin ya dameni. Wani irin barci ta ke kamar kasa, tun safe""."

"Ya yi murmushi, ya ce ""Allah ya sa tunanin ne ya ke dawowa"". Ta ce ""To amin""."

"Karfe biyar dai-dai Saifuddeen ya yi parking a harabar gidan, bootdin motarsa dankare taf da"

kwalaye.

Ya umarci buzu da Yohan da su kwaso duk kayan da ke bayan motar su shigo da su ciki.

"Hajiya na zaune falo ta ga ana sauke mata kwalayen kayan ciye-ciye da lashe-lashe, lemukan"

"gwangwani da na kwali, cakulet da biskit ba magana, kai har da wadanda ba ta taba gani ba."

Ta saki baki tana kallon ikon Allah kamin ta bara Saifuddeen ya bayyana cikin falon.

"Yana sanye da Caftan na ruwan tokar shadda wagambari, hular da ke kanshi ma kalarta kenan ya"

yi matukar kyau kasancewar ba kasafai ya ke wannan  traditional dressing din ba.

"Ya yi sallama ta amsa, ya nemi wuri a gefenta ya zauna, yana mika gaisuwarshi, ta zuba masa ido"

cikin son fahimtar nishadin da yake ciki. Ta ce

"""Yau dai da alama Madam ta sauko, wannan far'a haka? To wadannan kayan fa? Nawa ne ko na"

"Alhaji?"""

"Ya ji kunya sosai, don ya san ta dago shi, ya sunkuyar da kai yana murmushi, bai ce komi ba."

"Maimakon ma ya bata amsar, sai ya sauya hirar da gaya mata batun tafiyarshi Abuja a gobe. Ta"

ce

"""Allah ya tsare, ya bada sa'a, ya kade fitinar makiya da ta abin hawa"". Ya ce ""Amin""."

"Ta ce ""Zuwa yaushe zamu sa ranka kenan?"" Ya ce ""Sai rana ita yau, in Allah ya kaimu""."

"Munaya ta fito daga daki da filet da cokali a hannunta da ta gama cin abinci, zata kai kicin, duk"

hankalinsa sai ya koma kanta.

"Ta russuna ta gaisheshi yana binta da ido cikin fargaba, ko zata ce wani abu game da Rukayyah,"

amma bata ce din ba.

"Ta wuce su zuwa kicin ta aje ta dawo tana shirin shiga daki, Hajiya ta ce ""Har yanzu Rukayyah"

"bata tashi ba ne?"" Ta ce ""Bata tashi ba""."

"Hajiya ta kama baki, ""Kai ni wannan barci na Rukayyah anya na lafiya ne?"" Ta mike ta ce da shi"

"""Bari dai in dubota sosai, ai bai kamata ka wuce baku yi sallama ba"". Ya ce ""Hajiya barci ga"

"marar lafiya ai hutu ne""."

Ya mike ya bi bayansu duk da ba a gayyaceshi ba. Ya samu Hajiya zaune a gefen gadon da

"Rukayyah ke kwance, ta debi kafafunta wadanda suke sumul-sumul da su, ta aza a cinyarta tana matsamata."

"Ya matsa ga fuskar Rukayyah ya dan leka sosai, barcinta kawai ta ke sadidan cikin kwanciyar"

hankali. Ya ce

"""Hajiya ni ina ganin Rukayyah lafiyarta kalau, ki kwantar da hankalinki""."

"Ta sha kunu tace ""To likita"". Ya yi dariya ya juya ga Munaya wadda ke ta sha'aninta wajen"

"talabijin da C.D, ya ce ""Ya ya dai matas, ki duba cikin kayan can da ke falo akwai kasasuwa na dan Ibro na siyo miki, ragowar kuma ki shigo wa Rukayyah da su""."

"Ta buga tsalle ta yi waje tana yi masa godiya. Ya juya ya russuna yana yiwa Hajiya sallama, ita"

kuwa tana yi masa addu'a.

"Har ya murda kofar zai bude ya sake juyowa ya kalli Rukayyah, kallo mai cike da matsananciyar"

"kauna, tamkar ya saceta su tafi tare, tuni ya hangosu cikin Nicon suna honey mooning."

"Hajiya ta cira kai don ganin abin da ya dakatar da shi, suka hada ido tuni ta ganoshi ta daure"

"fuska sosai, ba shiri ya murda kofar ya fice yana cewa"

"""Mu kwana lafiya Hajiya""."

"Dariya ya bata sosai, ta ce"

"""Oh ni Yahanasu! Allah mai juya al'amura, kamar ba Babangida ba"". Kana ta daga hannuwanta bibbiyu"

sama tana yiwa Allah godiya.

"Kamar jira Rukayyah ta ke ya fita, a hankali ta bude idonta tana kallon Hajiya. Budar bakinta sai"

cewa ta yi

"""Saifuddeen!""."

"Hajiya ta yi murmushi, ta ce"

"""Uwarki nike, ba Saifuddeen ba, tashi muje ki wanke baki ki ci abinci"". Ta kama hannuwanta ta"

yunkura ta mike.

Tsayawar nan da zata yi akan kafafunta jiri ya kwasheta ya maidata inda ta taso kamar kayan

wanki. Hajiya ta kamata ta sake mikewa tana ta mitar

"""Wannan uban barci, ba ci ba sha ba dole juwa ta kamaki ba?"""

"Gaba daya karfin Rukayyah ya na jikin Hajiyar suka shiga toilet Hajiya na ce da Munaya, wadda"

"ke ta jera kayan dadi jikin lokar gado ta rasa inda zata sa kanta don dadi. Choculate iri-iri, biskit kala-kala, har ta rasa da wanne zata fara"

"""Jeki maza ki ce da Rabi ta kawo abincin Rukayyah""."

Ta fita da gudu har tana bugewa da kofa don saurin ta je ta dawo. Kada Hajiya da Rukayyah su

cinye kayan kafin ta dawo.

"Sai da Hajiya ta tabbatar Rukayyah ta dauro alwala, ta yi brushing bakinta, sannan ta kamota"

suka dawo daki. Ta shimfida abin sallah mai girma ta sanyawa Rukayyah hijabin sallarta.

Alhaji ya yi sallama a kofar rike da brief case da alama fita zai yi. Wannan ne karo na farko da ya taba

"shigowa dakin da Rukayyah ta ke, tun zuwanta gidan, domin ya yi kira ta waya, ya yi ta intercom Hajiya ba ta amsa ba, sai ya dauka babu lafiya ne, ko wani abu ne ya faru da Rukayyah."

"Ganinsu lafiya ya yi ajiyar zuciya ya ce, ""Na yi zaton har yanzu bata farka ba ne, ince a tasheta,"

"barcin bana lafiya ba ne""."

"Ya dubi yadda Hajiya ta takarkare tana son Rukayyah ta yi sallah, ya yi dariya ya ce"

"""Umaima, sallah ba ta zamo dole akan Rukayyah ba, don haka ku daina takura mata."

"Ubangiji ya yi mata lamunin sallar har zuwa lokacin da ta dawo cikin tunaninta""."

"Ta zare mata hijabin ta ce ""To ai shi kenan, Ubangiji Allah ya nuna min wannan ranar""."

"Ita Rukayyah tuni ta durfafi abincinta, ci ta ke ba ta ko kallonsu sabida yunwar da ta galabaitata."

"Alhaji ya russuna a gabanta, ya ce"

"""Ru-ku-ki Ruki-kis, ta Aliyu mai komai dozen!""."

"Sai ta tsaya da kai lomar bakinta, kamar tana tunanin wani abu, idanunta akansa."

"Ya yi murmushi, ita ma ta yi, ta ce ""Alhaji"". Ya ce ""Rukayyah, Allah ya baki lafiya""."

Ya mike ya doshi kofa da hanzari domin boye hawayen da suka cika idanunshi. Tausayin Rukayyah yake ji

"sosai, har cikin ransa. Hajiya ta bi bayansa."

Don haka yana fita babban likitanshi Dr. Javed ya kira ya ce ya zo da daddare ya sameshi zasu yi shawara

game da patientdinsa da ya gaya mishi.

******

"[12/17/2019, 19:17] Takori: K"

"arfe tara na dare Dr. Javed yana cikin falon saukar bakin Alh. Dambatta, gajere ne baki, kuma Ba'indiye."

"Kwararren likita ne akan cututtukan manya. Lokacin ma Alhajin bai dawo gida ba, don haka ya ci"

"gaba da zaman jira har karfe goma na dare, sannan ne Alhajin ya iso, yana mai neman afuwarshi a bisa zaunar da shi din da ya yi."

"Wannan halayyar Alhajin ce, da duk jama'ar da ke hulda da shi suke yabawa, take kuma kara"

"masa girma da kima a zuciyar kowa, wato saukin kai da girmama kowa ba tare da la'akari da cewa a karkashinsa suke ci ba."

"Dr. Javed ya ce ""Babu komai"". Ya bude brief casedinshi ya fiddo takardun Rukayyah ya mika"

mishi. Ya sanya gilashi kana ya bude yana nazarinsu.

"Alhaji ya ce ""So nake ka bani shawarar asibitin da ya dace in tuntuba ko ya ka gani?"""

Dr. Javed ya yi shiru yana tunani. A yadda Alhajin ya yi amanna da cewa ciwon patientdinsa

"kamar ya warke ya gama, wane bayani zai yi masa ya gane ciwon Rukayyah ba shi da magani?"

"Babu wani likita a duniya da zai ce zai dawo da tunanin da ya riga ya shafe a lokaci daya, sai"

sanda Ubangiji ya so.

Gaba daya jibi ya ke don yasan sababi irin na Alhaji Dambatta. Bari kawai ya yagi rabonsa shi da

"abokanen aikinsa tunda kudinne suke sukarsa, suke gaya mishi karya, suke gaya mishi zai iya samun komi a duk lokacin da ya so."

"Don haka ya karkace kai ya shiga yi mishi bayanin zasu tafi da ita asibitinsu na hadin gwiwa, shi"

"da abokan aikinsa a Delhi, da yardar Allah zasu yi iyakar kokarinsu."

"Amma aikin yana da tsada sosai, kuma ba lallai ne ayi nasara a lokacin ba, sai a hankali."

"Alhaji ya ce ""Babu wani abu"". Ko nawa ne zai iya biya in dai Rukayyah zata samu lafiya."

"Saifuddeen na Abuja aiyuka sun kacame masa, bai san me ake yi a Lagos ba, don Alhaji kwata-"

kwata bai gaya masa ba.

"Hoton da ya dau Rukayyah ranar daurin aurenta da Aliyu, wadda kuma ta zamo rana mafi"

"dimbin tarihi a gareshi, shi ne ya mayar screendin wayarshi."

"Sai ya dawo gida ne cikin dare abubuwa ke kacamewa, wato tunanin Rukayyah, ko barci yakan"

kasa musamman in ya tuno image na ranar da zai taho.

"Rukayyah ta hana zuciyarshi sukuni, ta wawashe kaso mafi GIRMA na zuciyarshi."

"Da ya ga babu sarki sai Allah, ya soma tattaro inashi-inashi a washe-garin ranar alhamis da niyyar"

"tahowa, shi da ya tafi da niyyar yin sati."

"A kuma ranar ne Rukayyah, Asi da Alhaji suke shirin tafiya kasar India, domin a cewar Jabed sun"

kammala duk wasu shirye-shiryen aikin da zasu yiwa Rukayyah. Zasu yi mata aikin ranar asabar.

Misalin karfe biyar na yamma ya yi parking a harabar gidansu. Ya fito rataye da coatdin

"suitdinshi a kafadunshi na hagu, hannunshi na dama rike da brief casedinshi a masifar gajiye ya tasamma kofar shiga falon gidansu cikin sallama."

"Asi da Hajiya da ke shirya kayan Rukayyah cikin jaka suka amsa. Asi na ta yi mishi barka da zuwa,"

"Hajiya kuwa sai murmushi domin kuwa ba karamin jin dadin zuwansa ta yi ba, don ba ta son ya"

"tafi ba su yi sallama da Rukayyah ba, tasan kuma hakika sun mashi laifi, don basu sanar da shi zancen tafiyar ba."

"Alhaji ne kuma ya hana hakan, ya ce, ta rabu da shi ya je ya maida hankali kan aikin da ya kai shi,"

"yanzu da an fada mishi zai ce sai ya je. Gara dai ya kula da aiyukanshi, Alhajin ya kai Rukayyar."

Nan da nan Rabi ta shiga jere mishi abinci a tebir ya samu wuri gefen Hajiya ya zauna.

Ta zuba lemun shany cikin tambulan ta mika mishi. Ya amsa yana sha suna gaisawa hankalinshi

"akan kofar dakin su Rukayyah, ya ce"

"""Ina Munaya ne, banji duriyarta ba?"" Asi ta yi murmushi ta ce"

"""Kama fadi gaskiya, ce ne ina Rukayyah, ba ina Munaya ba?"" Ya yi murmushi, ya shiga sosa keya"

da 'yan mukallayen motarshi.

"Hajiya ta ce ""Kai da ka ce sati zaka yi, kuma sai na ganka yanzu?"" Ya ci gaba da murmushi, kana"

"ya hau 'yan kame-kame,"

"""Wallahi kuwa, nima na so hakan, to na samu saukin aiyukanne na ce gara dai na taho zuwa"

"sunday sai in koma""."

"Asi ta ce ""Kema dai Hajiya mai sabuwar amarya cikin dankinki, dole ya yi ta bibiyarki, har sai kin"

"gaji kin bashi kayanshi""."

"Hajiya ta yi murmushi, ta ce ""Ba kuma zan bayar ba, sai Allah ya bata lafiya& ..""."

"Ya kulu, ya shaka, ya hau, yayi fam kamar alkubus, dariya ta kama Asi, amma ta hadiye."

"Ya mike bai ce komi ba, ya nufi tebir Asi na yi mishi godiyar motar da ya aika mata ko kallonta"

bai yi ba.

"Har ya zauna sai kuma ya mike ya nufi dakinsu Rukayyah, ita da Hajiya suka yi murmushi. Asi ta"

ce

"""Amma dai da shi zamu tafi ko?"""

"Hajiya ta kama baki,"

"""Rufe bakinki, ko zancen tafiyar bai sani ba. Ai yau akwai daru a gidannan""."

"Ya tura kofar ya shiga da sallama, Rukayyah kwance rub-da-ciki tana ta kallon hotuna a album,"

"sanye da doguwar riga mai santsi kirar Bahrain ruwan zuma, gashin kanta ya sha wanki daga zuwan Asi sai sheki ya ke, an matseshi daga tsakiya da ruwan zumar hair-bound. Kamar a mafarki ta ji muryar"

Saifuddeen wanda ya yi sanda ya kwanta kusa da ita.

"Kamshin turarensa ta ji tun kamin ta juyo, don haka ta yi azamar juyowa suka kurawa juna ido."

"Sannu a hankali kuma ta sauke kai kasa ta soma kuka, ya kama hannunta ta kwace, ta mike zata"

"bar dakin ya yi saurin durowa daga gadon ya sha gabanta, ya kare kofar da hannuwanshi duka biyu, fadin kirjinshi ya hana mata hango kofar. Ya yi narai-narai da ido na wanda yasan ya yi laifi, kana ya kai"

hannuwa ya kama fatar kunnuwansa a hankali ya durkusa akan gwiwoyinsa yana cewa

"""am sorry... sorry sweetie!"". Sai ta yi murmushi."

"Ta zauna dirshan a gabansa, tana share hawayen idonta, ya fiddo hankacinsa cikin aljihu, yana"

"share mata. Tuni ya gane laifinsa, ya tafi kwana da kwanaki, bata ganshi ba."

"Don haka ya koma lallashi cikin launin darussan da ya soma koyar da ita, masu wuyar bari da"

"wuyar mantawa, wadanda Rukayyah ke ma fushi sabida rashinsu data yi kwana da kwanaki. Dukkaninsu"

"dokance suke da juna kamar mayunwatan zakuna, ya hargitsa dan tunaninta, ya gusar da duk wani bacin rai da ke tattare da ita."

In banda tsoron Hajiya ba abinda zai hana shi karbar hakkinsa daga Ruqayyah a wannan lokacin.

"In banda kiran sunan ""Saifuddeen& ."" ba abin da Rukayyah ke yi, shi kuwa na shi al'amarin babbane, ya fi"

karfin biron Takori.

A can falo Hajiya da Asi nata hira a zaton Hajiya Saifuddeen tuni ya fito yana bisa tebir ne. Domin

kujerarta ta baiwa diningdin baya. Asi ce ke fuskantar diningdin.

"Hajiya ta juya tana yiwa Saifuddeen magana, sai ta ga wayam. Kwanukan ma babu wanda aka"

"bude. Ta juya ga Asi,"

"""Wai har yanzu bai fito ba ne Asi?"""

"Asi ta dago kai cike da mamakin tambayar da Hajiya ta yi mata, cikin ranta ta ce"

"""kamar ya ya har yanzu bai fito ba, kin ji min Hajiya da shiga sharo ba shanu, amarya da ango ne fa?"""

"Hajiya bata saurari amsar Asi ba, gaba daya hankalinta ya tafi ga Rukayyah, da halin da zata"

"samu kanta a ciki in tayi ciki cikin wannan halin, sai ga Munaya ta shigo rungume da dan kuikuiyo. Hajiya ta ce"

"""Au, fita kika yi kika bar Rukayyah ita kadai?"" Ta ce"

"""Karyar maigadi ce ta haihu na je in ga 'ya'yan, ga daya ma na dauko miki ki gani""."

"Haushi ya ishi Hajiya, kamar ta kai mata mangara, ta dauke kai akanta ta maida ga Asi, duk a kidime ta ke."

"Ta ce ""Don Allah Asi maza je ki kwankwasa kofar"". Asi dariyar Hajiya ta kamata ganin yadda duk ta rikice kai ka ce sace Rukayyahn zai yi."

A wani bangaren tana mamakin dalilin Hajiya na yin hakan. Tunda dai Hajiyar bata fito fili ta

Please Login or Register in order to submit comment