You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara bi ta kanta ba."

"Can kuma ta ji kamar cikin dusasshiyar murya kankanuwa Saifuddeen na cewa,  haba Salima& ki"

bari& ki bari& don & . Allah.

Daga baya kuma ya mike da sassarfa ya yi saman bene ta rufa masa baya ita ma da gudu tana fadin

"da ka tsaya mana, idan ba tsoro ba&  Daga haka ba ta kara jin duriyarsu ba, har karfe sha dayan dare."

"Wayarta da ke gefe ta yi kabbara alamar shigowar kiran wayarta kenan, sunan Hajiyata ya bayyana"

"a fuskar wayar, ta mika hannu ta amsa da hanzari ta ce,"

 Hajiyata ba ki yi barci ba?

"Ta ce,  Na kasa barci Rukayyah, tunaninki nake, sai yanzu nake cewa da na sani da ban takura ki kin"

"bi su ba, da na bi shawararki, na tura Rabin tunda ba sabawa kukai ba na san ba za ki ji dadin zama ba, ba za ki sake ba. "

"Ta ce,  Ba komai Hajiya, kada wannan ya dame ki, in ba da hakan ba ai ba za a taba sabawar ba. "

"Ta ce,  Haka ne, in ce ko dai dakin kwanan da suka baki mai kyau ne, kuma ya wadace ki?"""

"Rukayyah ta yi dan jim, ta daga fararen idanunta tana walainiya da su cikin kallon tafkeken"

"kayataccen falon da aka yasar da ita, aka mance da ita kamar shara, ta ce a ranta « yeah& it s indeed a beutiful room!  Don haka a fili sai ta ce"

" eh, ba abin da babu Hajiya, toilet din dakin ma wallahi (Jacuzzi), wanda nake ce da ke ina so din"

"nan?"""

Hajiya ta yi dariya ta ce a ranta Rukayyah ba za ta taba daina wautar ta ba. A fili kuma ta ce  to ai shi

"kenan mu kwana lafiya, baki da sako gun Aminan? "

"Ta ce ki gaishe ta dai, amma Hafiz ya baki kilishi ki kawo min, ki ce masa ya duba dakina cikin lokar"

"mudubi na akwai akwatun (kayan zane) na, duk ya baki ki taho min da su, da zan taho na sha afa ban taho da su ba. "

Cikin mamaki Hajiya ta ce  kayan zane? Wane irin kayan zane? Ta ce lah! Hajiya baki san ni

"Archititect ba ce? Ta ce  ina na sani, babu damuwa zan karbo miki . Suka yi sallama cike da kaunar juna."

"Da shirun ya ishe ta don dai ita ba gwanar kallon talbijin ba ce sai ta kira Nafisa, sai da wayar ta yi ta"

"burari ta gaji ba a amsa ba, ta sake kira, wannan karon ma sai da tayi kamar ta tsike kafin Nafisa ta dauka. Tun kan su gaisa ta katse ta da cewa."

 Wai ke kin dauka kowa ma gwauro ne irin ki? Da za ki dinga kiran masu aure during bed time?

(Lokacin kwanciya barci).

"Rukayyah ta kama baki, kafin ta samu abin fadi Nafisa ta ci gaba da cewa,  zan kira ki da safe, yanzu"

lokacin cherie na ne. Ta kashe ba tare da ta saurari amsarta ba.

Haushin da Nafisa ta bata ba kadan ba ne. Ta zuba uban tagumi da hannuwa bibbiyu tana zancen

zuci.

"Wato dai ita diya mace duk kyawunta duk isarta duk kudinta duk mulkinta, haka duk iliminta."

Gatanta da martabarta shi ne dakin aurenta.

"Yanzu da a ce tana da aurenta ita ma, wa zai ce ta zo aikin kuku gidan mutane har a dinga"

wulakanta ta irin haka?

Ta yi filo da jakar hannunta ta mike kafa sosai a kan doguwar kujera ta kwanta. Ba jimawa barci mai

nauyi ya dauke ta.

"[12/17/2019, 19:15] Takori: C"

an cikin barcinta a tsakar kanta ta dinga jiyo gunjin kukan Salima. A firgice ta tashi ta zauna daram

"da duwawunta, tana ware idanu kamar masaki."

"Iska ta dauko mata rikicin da ake tafkawa tsakanin mata da mijin, abin ki da dare, ko ina ya yi tsit."

"Sai dai duk kaifin jinta, ta kasa jiyo mai Saifuddeen ke fadi, wanda ke magana cikin lallashi da kwanciyar murya, sai hargagin Salima."

" & akan me za ka ce in bata daki, sai ka ce wata kishiyata& . Yaya zance ka je ka dauko min kanwata"

"sai ka dauko min  yar uwarka? An yi ne da biyu, tunda ba tun yau ba na san ana bakin cikin kwanciyar"

hankalin da nake da shi a cikin gidana& .

"Da alama wannan karon Saifuddeen din ne ke magana, har ta yi nasarar jiyo kalmarsa ta karshe"

"wadda ya fadi cikin kosawa,"

" To ni ya zan yi, ya ki ke so na yi for Allah s sake Salima& .? "

"A fusace ta katse shi da cewa,  Ba wani Alhaji, wannan duk munafuncin Hajiya ne& . "

"Ya yi magana cikin babbar murya wannan karon da ta kada  ya yan hanjin Rukayyah, fitsari ya kulle"

mata mara har ya soma diga.

" It s enough! Enough Salima, ki shiga hankalinki ki san abin da ki ke gaya mini!! Hajiyar tawa ce"

MUNAFUKA? Kada ki kara fadin abin da zai sa in wulakanta ki.

"Na fada miki tsakani na da Allah, ba ni na ce Rukayyah ta zo ba, Alhaji ne& "

"Idan kuma ba ki yarda ba, ki yi duk abin da za ki yi, amma Rukayyah ba zan maida ita ba sai ranar da"

"suka ce ta dawo don kansu, ki iya furucinki, kada nan gaba ko da wasa ki maimaita irin furucin da ki ka yi mini."

"Zan jure komai amma BAN DA A TABA MUTUNCIN HAJIYA. Kuma wallahi zargin ki da rashin yarda,"

shi yake janyo miki rashin kwanciyar hankali a kullum.

"Tun kan in san ki, na san Rukayyah, tun tana shekaru goma take zuwa gidanmu, wallahi da son ta"

nake da ke din nan ban aure ki ba.

"Kuma da Hajiya so take in aure ta, wallahi ba sai ta turo ta gidanki ba. Umarni ne kawai za tayi, ba"

ni kuma da yadda zan yi in tsallake.

"To Hajiyata, ba haka take ba. Ba ta taba budar baki ta fadi wani abu na muzantawa a kanki ba."

"Amma ke kullum cikin zarginta ki ke, da rashin kaunarki."

"Ke din nan wallahi ba ki isa tasa miki ido ba. Ke din banza! Ko me za ki fada ki tsaya a kaina, amma"

wallahi duk son da nake miki zan iya hakura da ke& ..

"Jikin Rukayyah sai rawa yake, saboda razana, daga baya kuma ya yi sanyi kalau. Ta juya ta kwanta a"

"barin kafadunta na dama, ta runtse ido tana mamakin Salima."

 Wai Hajiya ta turo ta don Saifudden ya aure ta& . Wai Hajiya ta kulla munafunci& . Ta ce a ranta

 wai me yasa wasu matan suke irin haka ne?

"Ita wallahi ba ta taba tunanin haka ba, ba ta taba kawo hakan a ranta ba. Ba ta taba tunanin ta so"

Saifuddeen ba daidai da rana daya.

"Kwata-kwata baya a layin irin mazan da take da burin hada rayuwar ta da su, kuma bai taba burge"

ta ba.

"Baya ga igiyar rakumi da ta yi nesa da kasa a tsakaninsu, ba ta taba sha awar yin auren zumunci ba,"

"domin tana ganin auren mugunta ne, auren tauye hakki, wanda za a dinga kwarar daya daga cikin ma auratan."

Balle kuma auren MAI MATA. Allah ya tsare ta! Har kullum kaidin Jummai ga uwarta fresh ne cikin

tunaninta. (Allah sarki rashin sani!).

Da Salima ta san yadda take da mijinta da watakila ba ta bata zuciyarta ta bata ta mijinta ta kuma

tsaya tana tada hakarkarinta haka a banza ba.

"A ganinta wannan hauka ne muraran, domin ya wuce a kira sa kishi. Kuma abin da Salima ta yi"

kanta ta zubar.

"Ko Saifuddeen bai yi niyyar kula ta ba, yanzu dole ya kula ta. Tunda ga shi ya gani a zahiri, ba ta son"

"nasa, ba ta mutunta nasa. Har uwarsa ma, ba ta ganin girmanta, wannan rashin wayo ko rashin hankali har ina?"

"Ai kuwa tunaninta daidai ta yi shi. Jin sa ta yi yana saukowa daga benen cikin zazzafan taku, dam-"

dam-dam kamar ya fasa tayal.

"Ta gintse idonta da karfi, cikin tsananin tsoro da razana. Ta dauka ya hango ta ne a zaune tana"

sauraron rigimar su shi da matar shi ya zo ya yi mata barin makauniya.

"Ta bi ta kankame jiki a wuri daya, ta kamo jakarta ta rungume, yadda ba za ta sha wahalar samun"

kudin achaban da zai danga nata da gidan Hajiya ba.

"Ji ta yi yana jan gefen rigarta da karfi,  Ke RAK, ke Rukayyah& Rukayyah, ya za ki kwanta a falo?"""

Ta saki wata irin kakkarfar ajiyar zuciyar samun tsira. Ta bude (blue)din idanuwanta a hankali tana

"dubansa. Sanye yake da (Pyjamas) farare sol samfurin (Mark & Spencer), ya kama tsakiyar su ya rike da hannunshi na hagu, amma hakan bai boye bakin lallausan gashin da ke kwance luf a kirjinsa ba, sai sheki yake cikin hasken lantarki."

Ashe dai kallon tsoro ko ko kallon kiyayya take yi wa SAIFUDDEEN ALIYU DAMBATTA. Yau ne ta ga

"zahirin Saifuddeen sak, dole Salima ta haukace da kishin abinta."

"A kamanni kam Usman Jalingo ne sak, amma a launin murjewar fata da gargasar kuruciya shi ne za"

"ka bambance su. Fari ne sol, in ba ta yi kuskure ba ta ce har ya fita. To a zahirance ba fin ta ya yi ba, jin dadi da hutu ya fita."

"Idan a ce za ta dauko mudubi ta kara, to da fuskarta ce za ta gani a fuskar Saifuddeen, sai dai"

wannan ta maza ce da suka amsa sunan MANYAN MAZA.

Ita dai ta san ita kyakkyawa ce mai alfahari da kyawun nata a ko ina. To amma ko ita da jininta bai

"son dan Aliyu Dambatta, ta san ya fita kyau, ya dara mata nesa ba kusa ba."

"Iyakar kushewar mai kushe, ba zai ce ga abin da bai da kyau a jikinsa ba, sai dai ko a halayya."

"Wannan din ma sai mutane kalilan na kut-da-kut, kamar uwa, uba da matar da so bai rufewa ido ba, kamar Salima Modu."

"Duk wadannan nazarai ta yi su ne cikin  yan dakikai, shi ma tunanin da ya yi a kanta cikin  yan"

dakikan Allah ya yi yawa da su.

Mafi rinjaye shi ne Rukayyah is a sleeping beauty. Wato irin mutanan nan da ba ka ganin hakikanin

kyawunsu sai in suna barci.

"Da kuma ta bude idon, ya ga wasu irin idanuwa blue kamar dawisu. Irin idanun nan da kuka ko barci,"

bacin rai ko farin ciki baya canza musu launi. Ya kuma gano dalilin Salima na tada musu hankalinta a kan

sai ya maida Rukayyah inda ya dauko ta cikin daren nan. (Rukayyah ba irin matan da namiji zai kalla ya

"iya kawar da kai ba ne, komai walittakarsa)."

"Sannan ko uwar da ta haife shi ma ba ta yarda da shi ba a kan Rukayyah, shi ma kansa bai yarda da"

kansa ba. To (why MATARSA)?

"To amma ya dace su yi mai uzurin ko shi ne bunsuru wurin neman matan, ba zai taba neman"

"Rukayyah ba, bai kuma taba jin birbishin son ta ba a zuciyarsa, sai haushi da take ba shi. Rukayyah ai Nafisa ce, idan har zai iya taba Rukayyah ashe kuwa zai iya taba Nafisa."

"Duka ba ma wannan ba, Rukayyah ba ta daga cikin classiques din da har yake jin zai iya hada jiki da"

"su, bar ta dai a sister n, irin wadanda suka zame maka dole."

Hakan nan sai yau ne ya ga abin da Hajiya ta dade tana fada masa watau shi da Rukayyah kamar an

tsaga kara ne. Nafisa ita ce mai kama da  yan Dambatta.

Ya yi tsaki cikin jin haushin kansa da abin da ya tsaida shi ga kallon Rukayyah ya ce

" kin wani tsaya kina kallon mutane, kamar yau ki ka fara ganinsu, taso mu je in nuna miki daki. "

"Ba musu ta mike ta dauki jakarta ta rataya, tana shirin kama akwatin ya dakatar da ita ta hanyar"

"daga mata hannunsa na dama,  no, bar min kawai ."

"Ga mamakinta sai ya sa hannu ya dauki akwatin ya yi gaba, ta bi shi a baya kamar mai ciwon kafa."

"A saman benen dakuna ne a rurrufe har guda biyar, kofar daya a bude take, ga kuma hasken fitila"

"nan tana iya gani da ya ratso ta karkashin kofar, ranta ya ba ta dakin uwargida Salima ne kenan."

Ya aje jakar Rukayyah a kofar daki na farko ya shiga dakin da ke buden ya jawo (drower) jikin

mudubi ya fito da makullaye ya dawo ya soma gwargwadawa.

"Ita dai tana tsaye jikin karfen bene, tana mamakin fasihin maginin da ya kwalmada karfe da rodi,"

"siminti da katako ya gina gidan Saifuddeen Aliyu Dambatta, (Arch. ABDULHAKIM KHALIL RIBADU)"

"(Zuciyar Mutum). Domin hatta rufin gidan abin kallo ne, wanda aka yi shi da wani irin gogaggen katako mai sulbi kamar tile."

"In ba ta yi kuskure ba hakika gidan ya fi na Aliyu Dambatta, a fasali, tsari, hikima da gwanintar da"

"aka yi amfani da su wurin ginin, sai dai karami ne wato daidai mace daya da  ya yanta."

"Abinda ta lura shi ne kwata-kwata babu daki a (main) falon da ke kasa, sai a wajen gidan, wadanda"

aka tanda domin ma aikata masu share-share da goge-goge.

"Kenan gidan kwata-kwata ba a gina shi da zummar amsar bakin kwana ba, sai su da suka zamewa"

"masu gidan dole, kuma babu yadda za a yi da su. Sun zama duwawu dole a zauna da su, in har ana son zama lafiya da iyaye."

Da kyar ya samu mukullin da ya bude dakin. Don haka ya soma kokarin zare shi daga jikin  yan

"uwansa ya mika mata. Dakin duhu-dudum, ya kunna makunnin lantarki haske mai ni ima ya wadaci dakin."

"Ya shiga ya ajiye akwatin ita ma ta shigo. (Salima da ke leken su ta taga, sai ta fashe da kuka)."

"Ya kalli ko ina fes yake, ba tare da ya dube ta ba ya ce  duk abin da ki ke bukata da safe sai ki gaya"

mini .

"Ta tura baki cikin gajiya, amma shi a gare shi duk tsabar wulakancin ne da samun wuri. Ta yarfar da"

hannu gefe.

" A a na zo da komai na, kuma Hajiyata ta bani kudi, I need nothing. "

Ya juya yana hada hanya ba tare da ya ce komai ba don takaici. Wato ita wannan  yar banzar

yarinyar ba a iya mata.

"Ashe gumu na biyu, na jiransa. Salima ta rufe kofar ta gam da mukulli. Ya tsaya a jikin kofar cikin"

rada yake kiran  pls Salima& ki bude. Ta yi banza da shi.

"Ya sake kwantar da murya kamar marayan da ya rasa uwa,"

" Haba sweety, kin san fa ba mu kadai ba ne a cikin gidan& . Ta daga murya cikin kuka kamar ta kashe"

kanta saboda azabar kishi ta ce.

" Sanin cewa ba ni kadai din ba ce, yasa na kulle tawa kofar, sai ka je ka kwana da ita, kai mai dangi."

Gobe da sassafe insha Allah zan bar muku gidanku. Dadin abun dai nima ba daga sama na fado ba.

"Ya ce a wahalce,  & Salimahhh, kashe ni ki ke so ki yi? "

 Ka mutu din mana ni ina ruwana& ?

"Ya ce,  Na ji babu ruwanki, to miko min makullan dakina. "

"Shiru ba ta amsa ba. Ya ci gaba da magiya kamar wani sabon maye, sannan ta dauko mukullan ta zo"

bakin kofar ta bude kadan ta zuro masa.

Ita da mukullin ya hada ya yi amfani da karfinshi na da namiji ya maida ta dakin ya shige aka banko

kofar ji kake garammmm! Kamar tashin duniya. Sannan ne kunnuwan Rukayyah suka huta.

"Ta muskuta ta gyara kwanciyarta, ta rungume filo a kirjinta, amma barci ko sama ko kasa ya ki zuwa,"

ta neme shi cikin idanunta ta rasa.

Tunani daban-daban suka rika zowa Rukayyah. Wasu abubuwa da dama da take tunani game da

Saifuddeen yanzu ta amince duk ba haka ba ne. Rashin zama tare ne da rashin fahimtar juna ya kawo haka.

Ashe gaskiyar Rabi ne ba duk masu kudin ke da hali iridaya ba. Tabo na farko da ta yi wa irin su

"Saifuddeen na girman kai ya shafe. Ta fahimci mutum ne mai saukin kai matuka, kuma irin mazan nan da duk son da suke yi wa mace, ba za su yarda ta raina masu iyaye ba."

" Saifuddeen ga macen da yake so, bawan ta ne. "

Rukayyah ta ce a ranta. Wato dai abin nan ne da ake cewa wargi ma wuri shi ka samu. Duk irin jan

"ajinsa da kwarjininsa gami da fadin ransa a waje, dubi yadda mace ke tamaula da shi a cikin gida."

"Wannan ita ce MATAR DA YAKE SO. Su da ba su ganin dariyar sa da fuskarsa, don baya son su ne."

"Amma tana da yakinin in ita ce tayi dace da miji mai sonta irin haka, kamar yadda Saifuddeen ke"

son Salimah da ba haka za ta yi wa  yan uwansa ba.

"A ganinta da Salima mace ce mai wayo, sai ta yi amfani da wannan damar ta ja Hajiya da  yan"

"uwanta a jiki, ta karrama kowa nasa ko kare ne kuwa. Hakika da ta yi dacen suruka, irin dacen da ba kowacce mace ke yi ba."

"Domin Hajiya uwar kowa ce, mai nuna nata ba nata ba ne; na wanin ta shi ne nata. Da ko shi"

"Saifuddeen din Hajiya ba za ta bari ya bata mata rai ba, sai dai shi nashi ran ya baci."

"A ganinta in Salima ta ci gaba da wannan halayyar tata, wata rana kwabar ta za tayi ruwa. Abin nufi"

kaunarta za ta raunana a zuciyar mijinta.

"Sannan Hajiya da Alhaji ba sakarkarun iyaye ba ne kamar yadda take tunani, da za su yi saken da"

"mace za ta raba su da dan da suka tsugunna suka haifa mata, suka yi ta wahala da shi har ya girma ya kai munzalin da har ta gani ta aura."

"Hajiya ma abociyar sallah da addu a ce, safe da rana, dare da yamma carbi ne a hannunta tana"

Hailala tana ambaton Allah.

A kan kunnenta rannan ta ji Hajiya ta daga hannu cikin talatainin dare tana yi wa Saifuddeen

addu a a kan Allah ya raba shi da kaidin mace ! Allah ya tsirar da shi daga matar da ba ta nufin shi da ALHERI. Kada Allah ya hada shi da matar da za ta raba ta da shi. Tana rokon Allah yasa ya zama namijin

"duniya, namijin gaske kamar mahaifinsa. Yaya kuwa za a yi Allah ya maido da wannan addu a?"

"Hakan nan wannan wulakanci ko ko dabbanci da Salima ta yi mata, ko kuma ta ce ta yi wa mijinta a"

"kanta, da wannan karramawa da yayi mata, gaba daya ya canza tunanin Rukayyah (from negative to positive), a kan Saifuddeen."

Ta kuduri aniyar nunawa Salima ita din ba ta daga cikin irin dangin mijin da ke bin matan  yan

uwansu suna wulakanta su.

"Hakan nan ita ba daya take da  yan kauyen Dambatta ba, ita cikakkar Bafullatanar Jalingo ce (Kunya"

"ku ka sani ba tsoro ba). To kunyar a ajiye ta gefe, tunda kunyar maras kunya ai asara ce."

"Ta yi aniyar rike amanar da ta daukarwa Hajiya na kula da cikin dan ta da iyakar iyawar ta, tare da yi"

"masa biyayya kamar yadda Hajiyar ta roka daga gare ta, amma ba ruwanta da wadda ba ta san mutunci ba."

"Don haka tunda Asuba ta katse barcin idanunta, tayi sallah ta yi lazumi gwargwadon iko. To daga"

nan fa ta mike ta sauko kasa ta soma neman kicin kusufa-kusufa har Allah ya ba ta ikon samon shi a wata kofa da ke like da falon.

"Kasancewar alfijir bai gama ketowa ba, ta kunna fitilun kicin din. Kicin har kicin, babu na urar da"

"babu, to amma fa babu kintsi ko kadan."

"Ga warin rubabben nama, a gefe dankalin turawa da kayan miya kwando guda duk sun rube, ruwan"

"na tsiyaya kasa ta kasan kwandon, ta ce to amma gida kamar na Saifuddeen a ce babu mai aiki in matar gidan ba ta da lafiya? Oho su suka sani."

Sai a lokacin tatuno zancen da ta ji suna yi da Hajiya jiya na cewa sun tafi biki Maiduguri har tsayin

"sati daya, da suka dawo kuma uwargida ba lafiya, watakila dalili kenan da kicin din ya kazance? Sai ta nade hannun riga ta hau gyara."

"Kauda wannan, wanke wancan, goge nan goge wancan, tuni ko ina ya hau kyalli. Sai da ta gamsu da"

"(neatness) din kicin din, yadda za ta ji dadin aikin ta babu kyama, sannan ta koma tunanin abin da za ta girka."

"Ta bude deep freezer ta ga nama kala-kala, amma duk sun yi mugun kankara ta yadda ba za ta iya"

"fitar da su ba. Hajiya ta gaya mata cewa Saifuddeen abinci sosai yake ci da safe kafin ya fita ba wai soye- soye ba, don in ya ci kuma shi kenan bai kuma cin wani sai ya dawo ofis da yamma."

"Don haka ta dora ruwan zafi ya tafasa, ta yi ta kwarawa wata lubebiyar kaza tana bambaro ta har ta"

samu ta fita da kyar.

"Nan da nan ta yayanka ta hada hadadden chicken cottage da ya ji kayan kamshi, albasa da attaruhu,"

"ta kuma hau kici-kicin kwabin alkubus, da ta kammala ta rufe shi a gefe don ya hau, ta bude ciki lokas ta dauko steamer wadda za ta turara shi."

"A cikin firinji ta samu ganyen alayyahu da kabewa, don haka ta yi kokari ta kara bambaro naman"

"saniya, ta yayyanka ta dora a wuta da albasa da curry wanda za tayi amfani da shi cikin taushen, ba ta sa agushi ba taushe sosai irin ta Mama Amina mai zakin kabewa da daddadan dandano."

"Sannan ta ciri agada ta soya da chips wanda za a ci da kazar. Aikin ya dauke ta awanni uku cur, har"

"karfe tara na safe, sannan ne ta samu ta kammala komai, ta gyara wurin kamar ba ayi komai ba, ta kwashe komai ta kai dining sannan ta yi wanka ta soma sana ar."

"Yau kuma su Rukayyah hadewa a kai cikin Pakistan ruwan goro, turrare(dark orange)mai adon"

"kananun stones bakake, ta tattare sassalkan gashin nan ta kai shi tsakiyar ka kamar kullum. Rukayyah ba ta son ta daura kallabi don haka yau ma ta yafa gyalen a kanta."

"Saikarfe goma daidai ta ji fitowar oga Saifudden da uwargida Salimah, suna sauka kasa."

Tana kallon wayar ta nata tsuwwa idan ta duba ta ga Nafisa ce sai ta dauke kai ta ci gaba da abin da

"take ta kyale ta har ta tsinke. Daga karshe Nafisah (tedt) ta yo ta ce,"

"Ki yi hakuri ki dauki wayar  yan mata ki ji abin da zan ce miki, wani daddadan albishir ne, terribly"

sorry& ..

Ita ma ta maida mata da cewa

" yanzu lokacin hutun gwauraye ne, bana amsa wayar masu aure ba ne. "

"Ta sake turo wani ta ce  don Allah ki yi hakuri ki dauka, kaina bisa wuyana my dear sis, na amshi"

laifina. Sannan ta sake bugowa.

"Sai da ta yi kira sau uku kamar ba za ta dauka ba, sannan dai ta dauka. Jan aji irin na Rukayyah har"

"mamaki yake ba Nafisa, ta ce,"

" Ran ta Aliyu ya dade. Tuba nake, kaina bisa wuyana! "

"Rukayyah ta kwada tsaki ta ce,  Wallahi da na san abin da za ki ce min kenan da ban dauka ba. "

"Da sauri ta ce,  Don Allah da gaske ne kun bata da Aliyun naki? "

"Rukayyah ta ce,  Eh, sai me? "

"Nafisa ta ce,  Thank God, kin san Allah ba ki ji dadin da na ji ba. "

Rukayyah ta kama baki  Saboda dama kina bakin ciki?

" Wallahi ba haka ba ne, ni dai kawai dama bai kwanta mini ba, na dade da wani buri cikin raina a"

"kanki. Amma dai yanzu ba wannan zancen ba ne, zancen Kanal Idris ne aminin Baban Abdul."

Wallahi tunda ya ga hotunan da muka yi a wurin lunching din Bilkisu ya haukace min da lallai sai na

kawo shi Jalingo.

"Kullum wayar safe daban ta dare daban, jiya har sha biyun dare yana gidan nan ya kafa mana kahon"

"zuka ni da Baban Abdul, to da wannan satin za mu zo kuma Alhaji ya fada min kin taho Legas, na fada"

masa ya ce ba damuwa mu zo. Wallahi irin choice din ki ne Rukayyah baya da mata kuma& ..

"Rukayya ta katse ta,  Saurara haka don Allah aku, kina da masaniyar cewa har yanzu ba a warware"

zancen Aliyu ba ko?

"Nima nan ban san matsayina ba, gani nan ne dai kawai amma hankalina ba a kwance yake ba, na"

yo gudun hijira ne saboda haka ki rufa min asiri ki bar ni in fita daga tsaka mai wuyar da nake ciki.

"Wallahi ni yanzu ba ni da ra ayin aure ya fice mini, gara in ci

Please Login or Register in order to submit comment