You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ka dawo...

Da safe k'ande tanata wanken kayanta..

" uwar dakina lafiya wanke da safe?

" Da banida lafiyar ai bazan wanken ba, goggo ce tace na wanke kayan!

" tooh Ko birni zakije?

" iya habu gidan wa a burni?

" bandai sani ba bari muzuba ido mugani...

" kai habu zanyi tafiya bansani ba ko zan dawo ko zan mutu ko can zan zauna kasani tsoron Allah shine gaba da komai ka dinga sallah ka dinga sallah ka guje wasa da Sallah...

" tohm k'ande..

Wane son k'ande ne yakara shiga zuciyar iya habu nan da nan sai kuka...

" iya kiyi hakuri kidaina kuka duk da bansan mekike yiwa kuka ba!

" wallahi k'ande banson rabuwa dake domin halin ki na daban ne...

" karki damu iya habu kiyimun Addu'a Allah ya shirye ne kawai...

" Tohm..


Birni

Alhaji wai mike faru ne naga sai sauri kikeyi?

" ina sha sha shan yarannan?

" bacci sukeyi ai!

" yabzu ke bazakiyi wa 'yayanki fada ba? Sunfa isa yin komai ace komai sai masu aiki ne zasu dinga yi toh wallahi aure zanyi musu in basu gyara halinsu ba!

" toh Alhaji yakake so nayi? Wallhi kullum inayi musu fada jine basayi...

" ki cewa haruna yadau kaya a mota ya kaimun office ne na huce kauye...

" To Allah ya kiyaye...

" D'akin su farida ta shiga ku tashi malalata har karfe daya kuna barci...

" to mumy yaufa sunday bamu da lecture cewar farida...

" ai that's good for you firdausi tashi kishiga adak'in haruna kice alhaji yace ya kai sako office!!!

" tohm mum mik'ewa tayi kanta ba dankwali ga wane wando duk ya matseta!

" haruna yana kan gado yana waya da mukhtar kawai yaga yarinya ta tsaya a kansa oya dad yace ka dau mota akwai sako!

" Ko daga kai baiyi ya kalleta ba!

" ohh anzo birni shine za anuna mana tak'ama! Kallon sa ta tsaya yi tasa blue din Riga tayi masa kyau..

" kallon ta shima yayi nan yaje wane yar ajikin sa! Ahankali yace will u get out from my room? Karki kara shigo min daki haka! Banson sha shanci...

" ahankali tafita batare da tace komai ba! Tana karasawa palour taga hafsa tazo!!!

" feedy kina hot fa irin wannan kala haka ince anturawa mutumin!

" mtseww ke kyalesa nasamu wane wallahi but da problem fa dan yafeson me addini!

" shi yana sonki ne?

" nop am just playing my game fa!

" Dont mind dear kalamai da tarkon kwauna zaki sakar masa..

" anyway zan gwada but yanada kafiya fa?

" dallah sai kace ba mace ba!!!....

K'auye

" lokacin da Alhaji ya isa kauyen goggo ce tayi masa maraba sannan ya samu guri ya zauna!

" mama farida ce ta bude baki cikin mamaki au Alhaji da gaske birnin zaka tafi da k'ande? Taba baki tayi tace hmm bari dai nayi shiru....

" goggo ce tayi wane iri sannan tace uhm ai k'ande sai hakuri...

" Alhaji ne yace ai nima 'ya tace dan haka zan riketa hannu bibbiyu!!!

" Tohm nagode sosai Allah yabar zumunci ya kara Arzuki...

" babu komai ina k'anden??

" sallamar tace ta katse su ta dur k'usa har k'asa ta gaida shi...

" lpylou Aishatu muje to tinda kin karaso...

" Diris taje tace to ai banyiwa iya habu sallama ba!

" karki damu zan biya ai sai muje!

" to mama farida ayafemu goggo zanyi kewarki..

" k'ande fatana guda daya karki cuci wani karki wulankanta wane ki zauna da kowa lpya kiyi kuma hakuri!!!

" Tohm goggo...

Mikomin ledar kayan nake..

" Aa zan dauka kabarshi!

" banason gaddama...

" Tohm gashi suna shiga ta rungume iya habu tace kiyafeni?

" me kikaye min kidai kiriki mutuncin ki...

" Tohm nasara gida nasara abokan gaba burina na farko ya cika kinsan Allah swt babu yadda bai iyayi da hukuncin sa ba!

" wannan haka yake..

" Toh kasani dai Amanace agurin ka! Addua o saiful muminun k'ande..

" iya habu inshaa Allahu..

Basu isa birni ba sai karfe 6 na yamma tun daga kofar gidan hankalin k'ande ya tashi ana bude musu kofa tace (tamfa tse Aljannar duniya) suna isa Alhaji ya dakko ledar ta...

" Dan Allah kakawo na riki..

" suna shiga bakowa a palour kasan tahil ta samu ta zauna...

" menene haka Aishatu hau kan kujerar mana!

" tohm tace ta zauna tana kallon dak'in...

" bari naje nayi sallah nadawo, ga kwana nan akwai daki na farko sai kishiga...

" Tohm

" farida ce ta sakko tana chwn gum ke ke wacce dirty girl din ce akan kujerar mu?

" k'ande tace nice kazamar kauye ko nasauka ne?..

" To yar matsiyata zaki sauka ko saina karyaki?

" k'ande ce ta miki ta nufi inda Alhaji ya nuna mata..

" ke ballagaza dauke kazaman kayanki kar kikawo mana cuta!.

" wane kallo k'ande tayi mata sannan ta dauka garin sauri sai taje ta bangaje mutum.....

" ke wacece ke zaki bangaje ne?

" kayi hakuri!

" koba k'ande ce ke ba tasss ya wanka mata mari....


*Urs Nana diso*


http//:nanadisoo.mywapblog.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[12/24/2016, 9:08 AM] ('kubrieh cier vervier: _25-27_

*K'ANDE*

Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*




Wane k'allo k'ande tayi mata sannan ta dauk'a garin sauri sai taje ta bangaje mutum.....

" k'e? wacece ke zaki bangaje ne?

" kayi hakuri!

" koba k'ande ce ke ba tasss ya wanka mata mari....

Ma k'wancin ta ta rik'e Amma Dai Nabaka hakuri ko?

" ko zaki rama ne jahila 'yar kauye? Ai sai Dai kiyi aikatau agidan nan yadda kike haka babu mai iya k'allon ki...

" mtswe taja tatafi dak'inta tana shiga wane lalataccen kuka ta saki rabonta da kuka har ta manta wane tsaki tayi tare da fad'in Allah ya'isa mugu kuma sai na rama!

" farida ce ta dan tauna cingam tace sorry uncle yarinyar sai hakuri fa!

" don't mind me dear ne tsoro take bani fa!..

" hmm manta da'ita zan koya mata hank'ali ya mum ya abuja?

" oll fine!...

" k'ada ido farida tayi tace nayi missing naka wallahi...

" same dear!..

" Tsayawa farida tayi tana kallon uncle matashi ne d'an shekara 32 bak'ine Amma yanada hanci kuma yanada ido, akwai shi da girman kai da tak'ama ga kudi agurinsa kamar mi, engineer ne, Yana son mace yar gayu me kuma ilimi, hak'an yasa farida take burgeshi har tayi tunanin sonta yake kullum yazo suna tare hajiya har kara girma ma hamza tak'eyi...

" Gurin 7 kowa yana palour a zaune sunata hira Dady ya shigo!

" firdausi ce tace sannu da zuwa dad..

" yauwa 'yan gidan dad ina kanwar taku?

" hajiya tace wakake nufi Alhaji?

" k'ande mana!

" Au k'ande ka dakko? Kai amma abun yayi kyau tayi wata dariyar mugunta!...

" k'ande dake daki tana zaune ga sanyi ya'isheta fitowa tayi sanyi da bak'in hijjabi tayi sallama tasamu kusa da firdausi ta zauna hajiya ina yini?

" lpylou k'ande ya mutun k'auye?

" mutun kauye suna lpya kamar yadda kuke sannu da zuwa Alhaji!....

" yauwa 'yata kinci Abinci? A'a banci ba kuma yunwa nakeji...

" kallonta sukayi su farida da hamza suka saka dariya!...

" shiru tayi bataci musu komai ba!..

" hajiya da Abincin ne?

" A'a Alhaji babu sai dai tasha kwak'i...

" ke farida dak'ko min indomie na dafa mata!

" suka hada bak'i k'anden zaka dafawa!!!

" Ke bazaki dakko bani?

" Aa alhaji kar nasaka wahala zan sha kwak'in..

" firdausi ce ta daka mata tsawa dallah matsa daga kusa dani wannan doyin kauyen naku baza arasa cuta ba!

" k'ande abun yayi mata ciwo tace to menene na yimun tsawa sai kace uwata, kauye kuma kowa yana dashi dadinta ma inda kaza ta fito da kwai anan take kashi!

" useless kawai jahila!!!

" dady ne yace toh daman ku bakusan Asalin ku bani ba? To nema k'afin nazama wane har da fitsari nayi yawo!...

" Hajiya tace shiga can zakiga kitchen ki dauki kwak'i a kofi!

" Toh tace sannan taje ta dakko tajika tadawo tace hajiya sukari...

" budar bakin hajiya tace ubanki ne yakawo sikarin? Dallah jahila sha haka a kauye da ubanki suke sha??

" Alhaji ne yafi to daga toilet k'ande lafiya naganki a tsaya?

" nace subani sukari sun tsaya suna ciwa asalin ka mutunci wai ban isa nasha zaki ba tunda ba yayanka ne ya kawo ba!!!

" Dariya Alhaji yayi yace kawo har madara zan zuba miki ya karba ya hada mata mai dadi...

" haruna yana shigowa yajiyo muryar k'ande yace Alhaji yakawo jaraba har gidan sa!

Babu Wanda ya kalla Sai hamza suka gaisa sannan ya shige dak'in sa!

" k'ande ce ta shige dak'in datake zaune tana ta shan kwakin ta wata dariya ta saki sannan tace dole yan birni su dinga kiba wanga madara da sukari dadi...

" firdausi ce ta kalli hajiyar su tace wallahi ba zai yihuba kowanne kala da dutse sai dad ya kawo dubi yarinyar nan wata dirty da'ita Amma dady yana ji da'ita!

" hamza ne yayi murmushi sannan yace cooldown dear ai ku gaba takaiku kun samu mai aiki....

" mum tace thats true fa ai kuwa kuma ku kwantar da hankalin ku domin sai na azabtar da'ita!...

" yeap mum hakan za'ayi...

" hamza ne ya miki good night farida gobe kiyimin chips da egg kinji?

" oky!!!

" k'ande dake faman zaune ak'asan tahil ga katifa a gefen ta Amma ita tafeson sanyi sanyin kasa bandaki ta shiga taga ta kasa kunna ruwan gidan palour tafita ta ga babu kowa tafiya ta dinga yi har sai da ta'isa kofar gidan sannu baba tsoho dan Allah zo ka kunna min ruwan bandaki Alwala zanyi...

" Alhaji ya hana mu shiga cikin gidan!..

" haba dan tsoho Alwala fa nace zanyi haba!

" To muje..

" suna isa ya nuna mata yadda zatayi tace to nagode yana fita yaga haruna!...

" baba me kazoyi anan kuma?

" yarinyar nan ce tace in kunna mata fanfo bata iya ba!

" toh jika...

" k'ande ce ta murguda baki ko ba zaiyi sallar bani? Sai wane hararata kakeyi!...

" kallon ta yayi hijjabin jikinta baki ne Amma saboda kod'ewa har yazama baki!...

" Dak'in ta sayo tashiga tayi Alwala ta kwanta a kasa ahaka bacci ya kamata!

" Haruna kuwa kulle dakin yayi sannan yace ai bazan kulaki ba ballanta na aji k'anmu!...

" Da asuba dady ya shigo dak'inta azaune ya taddata k'an sallaya...

" 'yata kin tashi?

" eh baba me kakeso adafa maka?

" kin iya soya dankali?

" eh na iya kasan muna cinsa muma sai dai ka koyamin yadda zan kunna abin dafawa!....

" To muje na koya miki...

" ya nuna mata komai da komai ta firayi mai yawa ta soya ta wanke wasu flask ta zuba ta dura ruwan shayi duk tajera akan dinning da yake dama tasan abinci ake durawa, ta wanke kwanuka ta shari dak'i ko'ina fafes sannan ta ji nata dakin ta wanke bandaki!..

" sai karfe 9 kowa ya fito duk suna zaune sunfara ci hamza yace chips dinnan yayi dadi fa dubi yadda yaje maggi!...

" kowa yayi shiru farida sai rawar kai takeyi!..

" haruna yana fitowa yasamu guri ya zauna firdausi ita alallai son haruna takeyi domin in ya zauna ta dinga kallon sa kenan!

" k'ande ce ta fito haruna kuma ya taso tace shi kuwa haruna haushin kallon firdausi yakeji!

" ina kwana?

" ko kallonta baiyi ba yace lpya!

" hamza kuwa tun kafin ta karaso yace tsaya anan karki samu muyi amai!...

" Alhaji yace menene haka hamza? Ranka zai bace fa!

" baba ina ne dak'inka in gyara!

" Ai kuwa dakina ya dadi ba agyare ba!

" k'ande ta kalle su firdausi tace sai soyayyar ba'a neman lada!...

" kaikuma uncle kake kowa baruwanka dani tunda ne bana kulaka banson cin zarafi....

" yama kara yimiki ranki sai ya bace!

" farida tace kaje jahila kaje jahila!

" K'ande da ranta yayi dubu ya bace sai cewa tayi jahilai dai tayi ficewarta!

" dady ne yace kuna gab da fuskantar hukunci...

"Tana gama gyara wa ta dawo ita kanta tasan wari takeyi kayanta ta duba ta shafa Alimun...

" fita sukayi da dady ya kaita prime anyi mata komai sukace ss3 zasu sakata ran monday ta fara zuwa,

" tun amota take godiya har aka sauke dady a office farida aka dakko...

" ke mekikeyi a mota dallah malama sauka!

" To ina zanje?

" Hankada ta tayi sannan tace driver yaja mota!

" k'ande ce ta kalli kanta kuka tafarayi da kyar ta'isa gida!...

" shigarta ke da wuya hajiya ta wanka mata mari nan ta dinga duk'anta hakuri k'ande ta dinga bata, dan uwarki zakizo gidana ki dinga yimun iskanci banza jaka kawai hankada ta tayi luuuuu haruna ya riki ta mekikaye mata?

" tana kuka tace wallahi banyi mata komai ba wallhi ni ka maidani gurin iya habu kamaida ni...

" cikin wata sanyar yiyar murya yace daina kuka ina tare dake....

" kallonsa tafarayi sai kuma taje dadin maganar! Da gaske kana tare dani? ....

*Urs Nana diso*


http//:nanadisoo.mywapblog.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[12/27/2016, 5:30 AM] ('kubrieh cier vervier: _27-29_

*K'ANDE*

Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*


Shigarta k'e da wuya hajiya ta wank'a mata mari nan ta dinga duk'anta hakuri k'ande ta dinga bata, dan uwark'i zakizo gidana ki dinga yimun iskanci banza jaka k'awai hank'ada ta tayi luuuuu haruna ya rik'i ta mekikaye mata?

" tana kuka tace wallahi banyi mata komai ba wallhi ni ka maidani gurin iya habu kamaida ni...

" cikin wata sanyar yiyar murya yace daina kuka ina tare dake....

" kallonsa tafarayi sai kuma taje dadin maganar! Da gaske kana tare dani?

Daga Mata Kai yayi alamar "eh"....

Murmushi tayi lokaci daya kuma hawayen ta ya tsaya dak'in ta ta shiga Alwala tayi tazo tayi sallah....

" hajiya dak'e fa man masifa da bala'i farida na zuga ta!

" au hajiya kallanta zaki dinga yi ne? Ta ci abinci tayi kashe? Ai kuwa bazai yihuba dan haka daga yau ita zata dinga dafa abinci...

" hakane ina zuwa shigar hajiya dak'in ba wuya ta tarar da K'ande tana kan sallah takalmin kafarta ta chilla mata!.....

" k'ande ce tace innalillahi hajiya lafiya takalmi kika cilla min fa?

" au ba'asi kike nema nayi din sai uban me? Ki tashi ki dafa shinkafa da miya kuma kada ki shigar min kitchen da takalmi kicere shi a kofar kitchen din i hope you understand me?

" k'ande ce tayi murmushi indai kunne ne yakeji to aikuwa na jiki...

" karma kije idan na rufe ki da duk'a za kije ai!....

" shiru tayi mata sannan ta mik'e hijjabin jikin tane yake ta wari gashi bata da wane hijjabin direct kitchen tatafi.....

" ita Kuma hajiya ta huce palour tana yar iskar yarinya ai baki isa ki mulki ne ba!

" farida ce ta saka dariya yauwa mumcy gwara da kikaye mata haka ai...

" k'ande kuwa tana kitchen abun duniya duk ya isheta haushin kanta ma takeji data biyo alhaji gidansa ta tuni tana tare da iya habu!

" haruna ne ya katse mata tunanin ta lpya k'ande?

" uhmmm bakomai...

" okay!

" cup ya dauka zai fita k'ande tace ya haruna katsaya Na karasa Abincin sai kaci!...

" never mind zansha tea ma!

" k'ande ta yamutsa fuska ga Abinci me tea zaiyi maka!...

" kinsan ciki ciki ne tea is okay for me!...

" yi tayi kamar zatayi kuka ita batasan me isa ta damu da ya haruna ba yanzu! Chan kuma tace to ai shikenan tunda danuwa na ma k'yama tata yakeyi...

" any way so kike nace miki gurin matata zanje tanason gani na ne!

" matarka kuma dama kayi aure ne!...

" Banza yayi mata ya fita!....

" wane sabon tagumi ta saka chan taje kamar an dasa mata duk'a!.

" Dallah yar kauye yi sauri ki karasa mana abincin kafin ranki ya bace kuma kowa kisaka masa A plate!..

" Tohm mum!!!

" haka takarasa ta zubawa kowa ta kaimusu dinning tana kaiwa hamza ta ajiye masa!...

" wata tsawa ya daka mata will you move away! Kina tunanin naci abincin ki? God forbid! Kalleki how dirty you are ware ko ta'ina look at your hijjab, yasaka dariya fuskarki kamar bakar daddawa, carry your jagwalgwalo and move away....

" mumy ce da Firdausi suka saka dariya....

" farida kuma tace dont mind her my dear bari na dafa maka indomie, ne bansan irin k'ande ba ita ta dabance bata ganin kazantar ta fa!..h

" K'ande tana shiga kitchen ta saka kuka mai ciki da tausayi, wanke fuskar ta tayi sannan tayi wanke wanke tazo ta huce....

" tsaki hamza yayi!...

" mumy wai ina uncle haruna ne?

" dazu yazo mun gaisa kinsan yana masters dinsa...

" wane murmushi firdausi tayi azuciyar ta kuma tace burina ya kusa cika...

K'ande tana zaune tunanin kauye kawai takeyi tunanin ma haifin ta tafara ahaka taga har 9 tayi gashi hijjabin jikinta ya dameta mik'ewa tayi tatafi bangaren baba!..

Sallama tayi sannan tace baba in shigo?

" A'a 'yar gidan baba shigo mana!...

" tsaya anan dan ubanki...

" menene haka hajiya!...

" bansani ba sai dai kai kaje kasameta amma kar ta sake ta shigomin dak'in mijina!

" baba ne yace hmm sannan yafita 'yar gidan baba ya akayi?

" i'donta har yafara cikowa tace sanyi nakeji kuma babu bargo!

" mantawa nayi wallahi Amma zan bari na dakko miki wane!

" baba har da omo!

" jim kadan yafito to gashi gobe inkin dawo daga makaranta maje ki zabe abunda kikeso...

" Tohm tace sannan ta fita!

Tana shigowa palour ya haruna yana danna waya firdausi kowa kallon sa kawai takeyi tana murmushi!....

" k'ande har ta huce haruna yace bargon wa kika dakko?

" banzs tayi masa tana kokarin hucewa...

" kaje dabba ko zata nuna maka halin yan kauye!...

" k'ande kuwa taje maganar har cikin ranta!

" haruna yace kardai gurin baba mai gadi kika karbo?

" dan dai banda imani yaza'ayi Na karbo gurin mai gadi...

" Ai nasan zaki 'iya...

" D'akin ta ta shiga tafara wanke hijjabin ta sannan tayi dauren kirje tasaka wata doguwar riga sannan ta kwanta!...

" Da Asuba baba ya tashita bayan ya dawo daga masallaci yace K'ande?

" Naam baba!..

" yauwa magana nakeso muyi dake dama so nakeyi na aure mama farida!...

" k'ande tayi tiriss ta kauye?

" eh ita ya dabi'un ta yake?

" huu'ujun to dai gaskiya tanada hassada dakuma mugunta, Amma kuma tunda suke tare da goggo basu taba rigima ba kuma tasan darajar baban mu kafin ya mutu ni kadaice bama shiri da 'itah Amma da kabar hajiya baba batayi maka komai fa?

" A'a inason na taimaki mama farida ne!..

" ai kuwa kamar kasan ba'kin jinin aurene dasu!...

K'ande kenan ai komai na rayuwa Allah yariga ya rubuta tub kafin a haife ka! Kuma Allah shi yakeyin komai, Allah ke bada miji ba dan'adam ba kudaina jefan mutane da sunki samun miji inkunayin haka tamkar bakusan Allah ne kadai mai bayarwa ba A lokacin da kukaye wa wane bori kema bakisan karshen rayuwar ki ba, kuma zaki haihu

Please Login or Register in order to submit comment