You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa nayi muyi hira?

" cikin firfito sa ido yace dawa dani wai ina maigadin?

" haba baba me gadi ai mutum bai isa ya manta asalinsa ba, Ne da kaganne yar kauye ce sunana k'ande...

" hakan yasa yaji dadi yace kin hutawa rayuwarki domin bakida wulakanta dan Adam...

" La ai ita rayuwa in kanason kace ribarta to ka'iya zama da kowa!...

" hakane kam domin dazu aka fita da hamza rai ahannun Allah ko yaya suke cika oho...

" Basar da hirar tayi batare da ko gizau aranta ba sannan tashiga wata hirar...

Kauye

Haruna da sassafe ya sanar da iya cewa zai tafi...

" haba haruna Ai ka tsaya na dama koko ko?

" Tohm bari naji na gaida goggo..

" yauwa ko kaifa..

" Cikin Nutsuwa ya bude kofar ahanya suka dinga gaisawa da mutane a hankali yayi sallama...

" A'a muryar wa nakeji kamar ta haruna?

" Eh nine goggo durkusawa yayi har kasa yace ina kwana na sameku lafiya?

" lafiya lou ya mutan birnin?

" Duk suna lafiya ai tun jiya nazo duba jikin iya...

" eh wallahi tasa jiki jikin nata amma da sauki ai, ina kande kuna daita hakuri da'ita...

" a'a goggo ai k'ande ta canja!

" To ya zamansu da farida kuwa...

" uhm abun dai sai addu'a wallhi!

" toh kadinga yimata bada Dai...

" Ai kawu mahmuda yazo ya tafi da'ita..

" goggo dai bataji babu dadi sai ta dake tace toh Allah ya dawo da'ita lafiya..

" Ameen bari na tafi toh kashiga kugaisa da su abbas da Ali manah...

" Nan ya lika suka Dan taba hira bayan sunyi sallama sannan ya koma gidan iya habu yayi mata sallama ya huce birni....

Birni

Shigar sa kenan ya tarar da farida tana kuka zama yayi ya dubita lafiya?

" hamza ne bashida lafiya za'ayi masa aiki zuciyarsa...

" subhnlhi yaushe?

" gobe..

" okay ma tafi goben dakkomin abincina!

" Tana cikin daukar abinci mama farida tashigo to iyayen ci da kashi bakwa tabuk'a komai sai ci da barci to ajiye abincin tunda ba ku kuka dafa ba...

" karki zageni bane zanci ba yaya haruna ne zaici..

" muje nagani suna fita ta hadu da haruna yana zaune...

" gashi yaya cikin bacin rai yace Na koshi...

" mama farida ta mika hannu to bani abincina tayi gaba...

" firdausi ce ta sakko yayana mekakeso naji nadafa maka!

" Cikin kashe ido yace kome kika dafamin 'yar kanwata zance...

" Cikin murna ta shiga kitchen...

" cikin awa biyu tagama komai sannan ta kirashi ta zuba meshi ya naci suna hira...

" haka dady ya sakko ya tarar dasu yaji dadi sosai sannan suka gaisa ya fita...

Abuja

Manyan likitoci sun taru Yau za'a gabatar da Aiki, su abi da ummi tun safe suke asubuti...

" Ummi ce tace wai saddika ina wannan bak'uwar ko tace zata biyoku...

" that's what am saying ummi yarinyar batada kirki wallhi...

" kukyaleni da'ita bari naji gida nadawo...

" okay...

" k'ande tana zaune tana ta dariya sanadiyar film din datake kallo...

" ummi ce tashigo to asararriya mara mutunci, son yana can ba lafiya ke kinan kina dariya wane asararrin ne zai hada zuri'a dake, wallahi Na tsaneki kuma.....

*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[1/19, 11:09 PM] ('kubrieh cier vervier: _52-56_

*K'ANDE*


Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*

k'ande tana zaune tana ta dariya sanadiyar film din datake kallo...

" ummi ce tashigo to asararriya mara mutunci, son yana can ba lafiya ke kinan kina dariya wane asararrin ne zai hada zuri'a dake, wallahi Na tsaneki kuma Yadda kika nunamin kiyayya ido biyu to kisane bashi kika dauka Dan iskanci kana gidan mutum ai ko tausayin d'ansa k'aje..

" zuciyar kande ce tafara tafasa nan zuciyoyin ta suka fara aiko mata da sak'o a hankali ta Daga kai tace kiyi hakuri ummi ne bahaka nake nufi ba kuma babu wanda yasanar dani akan bashida lafiya, saddika da maryam ba kulani sukeyi ba!

" Lafiya ce dai Allah zai bashi ko kinyi addua ko bakiyi ba dan haka kiyi duk abunda kikaga dama idiot kawai...

" cikin bacin rai kande ta dago idonta can kuma tace bamasa fatan rashin samun lafiya ba domin nema yaya yake agurina...

" ummi tace Dallah tafi can...

" kallonta kawai tayi sannan ta hau sama cikin tsaki tace ko mai ruwana da d'anku oh? Wama zai hada zuri'a daku bakusan darajar Dan Adam ba!...

" ummi ce ta dauki abinci sannan ta koma asubutin nan ta tarar abi yana ta hamdala...

" Cikin murmushin da yakusa kaiwa dariya tace anyi aiki lafiya ko!...

" maryam ce ta rungumeta suna murna...

" Alhamdulilah Allah yakara masa lafiya..

" suka ce Amin...

" abi yace kinga yanzu yana murmurewa sai ayi zancen auren sa da farida!.??

" haba abi yakakeso akamayar da jiya yau ai kawai kadaina wannan zancen ma...

" saddika tace what am telling him kenan...

" Anan Dr yafito ya sanar musu cewar tomorrow zasu iya ganinsa...

Birni...

Mumy mumy kefa muke jira kiyi sauri...

" oh firdausi irin wannan kira haka ko haruna ne ya gaji?

" haba mumy to haka za'abarsa atsaye kema aikinsan bazai yihuba!

" sannu mai masoyi sannu nace miki toh ina faridar ta shiga?

" Ai tana mota ita da mama farida...

" fitarsu ke da wuya haruna ya shiga mota Nan dady shima ya shiga...

" cikin girmamawa haruna yace ince lafiya najika shiru?

" kaima kafada haruna anzo tambayar auren k'ande ne!...

" duk'an su suka kace k'ande...

" hankalin haruna yafi nakowa tashi cikin in ina yace wanene yaron?

" isyaku ne dan gidan alhaji datti yaro nutsatse...

" firdausi da murna ta isheta batasan lokacin da tace Alhamdulilah ba...

" haruna da brain dinsa take bugawa cikin zuciyarsa yace ai daman nasan narasata...

" dady ya kalli haruna yanaga kashiga damuwa ne ko yaron bashida tarbiya ne?

" Nan yayi murmushi yace nop ba haka bani ba ina tunanin anya tana sonsa?

" sosai ma kuwa yayin da dadi ya furta haka...

" firdausi tace toh yaushe za'akawo kudin ne...

" dady yace wata nagaba za'akawo...

" haruna ne kadai ya daure yace Allah yasa Alkhaire...

"Ameen..

Basu isa Abuja ba sai karfe 8 nadare lokacin da suka shiga farfajeyar kowa kallon gidan yakeyi da dukiyar da Aka zuba...

" cikin palour suka karasa k'ande tana zaune tana shan tea sallamar su ta mik'ar da'ita tsayi tace sannunku da zuwa...

" farida tace oh yab kauye ansamu guri An zauna sai kace gidan su..

" dady yayi saurin katseta da cewa gidab sune mana oh kinga yadda kikaye kiba k'ande...

" Cikin murmushi tace Allah ko dady? Kasan nan bana aikin komai suna da masu aiki kala kala...

" haruna dake faman kallonta tunda suka shigo yakasa cewa komai...

" a'a harda kai yaya haruna? Ina yini...

" dauke kansa yayi, hakam yayiwa firdausi dadi...

" to yamai jikin cewar farida?

" Alhamdlhi jiki yayi sauki kam dan kuwa anyi aiki lafiya duk suna can asubutin...

" uwata me isa bakije ba?

" zuwana matsala ce dady...

" kowa ya zaro ido matsala kamar yaya?

" kamar yadda bazaku gani ba!...

" mumy tace kidai kije tsoron Allah...

" mikewa tayi ta kawo musu lemo tana mik'awa haruna yace am okay ba sai nasha ba...

" wane kallo tayi masa na tuhuma sannan tace bari naje nayi sallah sai na dawo...

" kowannen su ya mik'e ya nufi bandaki bayan sunyi Alwala kowa ya gabatar da sallah...

Dady ne yace su mik'e sutafi Asubitin cikin murya mai karfi ya kira k'ande...

" Naam dady..

" banason sha shanci ki fito mutafi tare...

" cikin rashin jindadi tace toh mayafin ta ta saka sannan tafita zuwa motar...

" Direct asubutin suka isa nan Abi yafito ya tafi dasu sunata gaisawa...

" sannu da zuwan ku mumy farida sannu...

" cikin muryar girma tace ya mai jiki Abi?

" jiki Alhndlhi...

" tana shiga cikin dak'in su ummi suka fara sakar mata harara..

" ko kallonsu k'ande ba tayi ba ta samu guri daya ta zauna...

" cikin damuwa farida takara sa gaban gadon hamza tana kuka...

" kallon ta yayi da idanu wansa su kayi jajir sannan ya kau da kansa...

" farida ta rike hannun sa sannu dear Get well soon...

" Nan suka dinga hira dr ne ya shigo ya sanar dasu da sudan fita haka suka fita..

" kande da ke bakin kofar dak'in Dr yafito yace i think hamza na kirar wata acikin nan...

" mumy tayi saurin cewa bazai huce farida ba..

" ku barshi ya huta ku mik'a masa wannan towel din ya mikawa k'ande...

" k'ande ce takalli kowa ba ma ummi da ta tsira mata ido, haruna ta kallah ta lurah bama kallon ta yakeyi ba...

" Dr fabrick yace collect it mana!

" amsa tayi sannan ta bude dak'in ajiye masa towel din tayi batare da ta kalke shi ba...

" Ahankali hamza ya rik'e mayafinta yana kokarin yimata magana..

" fizgewa tayi tace karabu dani karabu dani!..

" bayan fitowar kande saddika ta shiga hawayen da taga idom hamza yana yi shine ya kara tsoratar da'ita...

" yaya kadaina saka damuwa cikin ranka please lafiyarka tafi komai fa...

" Nan ta sanar da ummi akwai question mark akan kande fa..

" ummi tace ke ba wannan ne problem din ba i think zafin aikin ne...

" okay saddika ta ambata tabar gurin...

Nan dady da abi suke tattaunawa akan yadda zasu hada auren...

" Abi yace aine yar gurinka nake kwadaye farida ita Nakeso ahada da hamza..

" kai mashaa Allah kaga kuwa sai ahada haruna da firdausi tunda naga suna san junansu...

" Aikuwa hakan yayi...

" Lokacin da suka koma gida anata hira kande dai na dak'e tuna nin ta daya yaya rayuwar zata kasance agaba? Wanne irin matsala ce take tunkarone? Amsar data kasa bawa kanta kenan...

" Dr Ne ya kira ummi..

" gaskiya hamza yana matsala over thinking yakeyi yakamata asan menene matsalar sa?

" several times ina tambayar sa dr but amsar daya ce kullum hawaye..

" okay karki damu nan da 4days zamu sallame shi ....

" okay likita nagode...

Da safe ma abi da kande ne su kadai kuka je asubutin a yayen da ummi ta dawo gida...

" Sannu son yajikin naka?

" cikin wane yanayi na ban tausayi yace Abi babu sauke!..

" haba hamza mai isa kake mai da kanka baya...

" Abi indai zan kasance a haka wallahi bazan taba gaba ba yakamata ku dube halin danake ciki in bahaka ba ina gab da mutuwa...

" hamza kadaina fadin irin kalaman nan domin ita mutuwa sai lokacin ka yayi kuma bana tunanin akwai soyayyar data huce ta iyaye...

" k'ande dake tsayi agurin tana kallon su, Abi yace bari naje guri. Likita nadawo...

" bayan fitar Abi kande tayi hanyar kofa...

" hamza ne yace ki taimaka kitsaya domin na sanar dake sakon zuciyata, taimakon sona da zakeyi kamar ceton raini, ki tsaya kije kalamai daga bakina...

" cikin hawaye tace ne yar talakawa ce kuma ma abociyar wari da doyi gani dakikeya, kai kuwa me zakiyi da irin maccen nan?farida itace daidai dakai classy, gentle..lady...

" aisha ki sone, karki gujeni barina ni kadai ba karamin hadari bani ba, ko da ba kyasona ki daure ki aure ne...

" mai isa kakeson sakani cikin matsala? Kanason rayuwata kullum baya da gaba karka manta akwai bamban ci atsakanin mu dan haka rabuwa da soyayyata shine yafi yi maka Alkhairi ta buga kofar ta fita...

Bayan kwana uku an sallamo hamza bakomai ke damun ummi ba illah rashin walwalarsa yau su mumy suke shirin komawa gida farida ce tace mumy tabbas hamza ya chanja min ba kamar da ba, idan zai fadi sunana sai yace Aisha..

" Too karki damu komai zaiyi sauki inshaa Allah..

" k'ande dake faman shirin kayanta saddika tace ai naga sai yamma zaku tafi ai...

" cikin rashin fara'a tace eh...

" hamza dake faman kwara amai ummi nayi masa sannu cikin damuwa da jin kai irin na uwa tace hamza?..

" Naaaam..

" me ke damunka ne wai?

" cikin hawaye yace soyayyar yar kauye...

" bangani ba...

" zaki gane amma not soon!!..

" K'ande ce ta shiga dak'in haruna domin ansar wayarsa...

" mik'ewa yayi ya matsa daf da'ita cikin murya tana sarkewa yace me isa kikeson yaudarar zuciyar da ta dadi tana rainon soyayyarki? Me isa kikeso ke butulci wa tsohowar soyayya? Ina sonki k'ande, ina sonki Aisha zan fito na sanar da duniya akan soyayyata...

" idonta ne yafara zubda hawaye...

" hannunsa yasa yace ki daina kuka ke *Ta dabance*ina kuma tare dake k'ande... kafin ya karasa maganar farida ta shigo....

*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[1/23, 11:07 AM] ('kubrieh cier vervier: _56-58_

*K'ANDE*


Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*



" K'ande ce ta shiga dak'in haruna domin ansar wayarsa...

" mik'ewa yayi ya matsa daf da'ita cikin murya tana sarkewa yace me isa kikeson yaudarar zuciyar da ta dadi tana rainon soyayyarki? Me isa kikeso ke butulci wa tsohowar soyayya? Ina sonki k'ande, ina sonki Aisha zan fito na sanar da duniya akan soyayyata...

" idonta ne yafara zubda hawaye...

" hannunsa yasa yace ki daina kuka ke *Ta dabance* ina kuma tare dake k'ande... kafin ya karasa maganar farida ta shigo....

Shigowar farida d'akin nasa bai hanashi cigaba da maganganu masu mutukar tsoratar wa ba....

" farida da ta tsaya daga bakin kofa tace yaya haruna kaine kake hawaye...

" hannun kande ya rike dake faman kuka yace wallahi wannan itace mahadin rayuwata inasonta ina kaunarta farida kisanar da ita ta soni danAllah, mafarkin ta yazama kamar ruwa agurina kullum sai nayi kamar yadda tunanin ta ya hanani sukuni, Nazo abuja kawai dan dai naganki, zancen aurenki da isyaku pls ki tureshi ki kasance matata DanAllah....

" k'ande dake faman kuka hakan yasa ta fuzge hannunta sannan ta bar dak'in...

" farida dake cikin duniyar tunani anya ba kande asiri tayiwa haruna ba? Fita tayi tahuce dak'in direct dakin mumy ta shega cikin haki da damuwa...

" mai yafaru farida...

" mumy wallahi akwai babbar matsala fa...

" matsalar me?

" can kuma tayi shiru sanadiyar wasu yan tunanuka da tayi...

" common tell me know...

" wane murmushi mai ciki da tashin hankali tayi sannan tace lah tsokanar ki nakeyi fa...

" aa farida tunda kika furta to akwai matsalar...

" karki damu zaki sane a hankali...

" k'ande dake faman kuka a dak'i can kuma sai cewa tayi Ya Allah, you are truly merciful, please forgive me Choose for me,what is best....

" maryam tace ke kuma ke dawa?

" cikin masifa kande tace nayi miki magana ne?

" Dallah malama daga tambaya?

" malamai dai wane yace kiyi tambayar aikin banza kawai...

" ke yar talakawa gyara bakinki kafin nace miki mutunci wallahi...

" harara kande ta zabga mata sannan ta fita daga dak'in...

Shirya shiryan tafiya sukeyi kande takasa hada idanun ta dana haruna balle uwa uba hamza da bata kaunar ganinsa!

" oh kande kin wane rabi sai kace mage...

" ummi tace ai wannan yarinyar ta dabance...

" mama farida tace abun dariya ma sai ku rantse irin mumina ce...

" sai da ta gama jinsu dukk'an nin su sannan tace ai rabewa itace daidai ga mutumin da ake k'yararsa...

" kamar yaya cewar mumy...

" dady ne ya katsesu da cewa kuyi maza kufito haruna baya jindadi dan haka ni zanyi driving din....

" firdausi ce tace dady me ke damunsa?

" kije ki tambayi shi mana...

" K'ande dake faman daukar ledarta adaki farida ta shigo tace wallahi kande kije tsoron Allah yanzu kirasa wanda zakiyiwa asiri sai yaya to bari in gayamiki kizuba ido kigane auren firdausi da haruna babu fashi...

" dariya kande tayi tace ai kinsan komai nufin Allah ne na firdausi ne ya fito...

" maryam tayi saurin fadin dady na jiran ku fa...

" Nan suka sakko Abi sai fada yakeyiwa kande ai kwanakin sunyi kadan...

" Acikin zuciyarta tace wa'zai iya zama da bakar kaddara...

" au kinajina?

" zandawo abi karka damu...

" suna kokarin shiga mota kenan hamza yafito tare da dafe bango....

" dady yayi saurin fadin me zangani haka?

" please kutafi dani zanfi samun sauke fiye da da...

" Dady ne yace kayi hakuri kasamu sauki hamza, after that ma akwai company uku suna jiran sign dinka katsaya ka gina sana'arka.....

" hawayen da yafara zuba a idonsa yasa ummi cewa haba nafa gaje wannan wacce irin cutace abu kadan hawaye....

" abi yace to ko farida ta zauna...

" hararar da hamza yayi mata yasa tace inada lectures....

"Haka sukayi sallama tare da godiya...

Abi ne yaruke hannun hamza suka shiga ciki suna zaune a palour ummi tace ne dai ankar dani wallahi wannan wacce irin cutace?

" saddika cikin yamutse fuska tace wallahi soyayya ce ummi....

" maryam ma tace ai gashinan zai maida kansa kamar mahaukaci yanzu haka yarinyar dayake so din ba clss dinsa bace ba...

" Abi yace hamza kagaya min gaskiyar abunda ke damunka...

" Abi to zaka magance mun ita?

" indai zan iya zan magance maka son...

" wata yarinya nakeso nake kuma so a aura min ita!..

" ummi tayi saurin cewa wacece?

" hamza ya kalli abi tare da rungume sa yace Abi bata sona bata kyaunata!...

" abi yayi hanzarin cewa what yar gidan uban wacece?

" ba yar kowa bace ba...

" okay karka damu bari naje office ana jirana when am back zamu tattauna son but kadaina saka damuwa aranka....

" ummi tace hamza kenan Allah yabaka Mata tagare....

" kallon ta yayi yace ai Allah yabani ma...

Su k'ande suna komawa gida kowanne ya shiga d'akin sa..

" wanka kande tayi sannan ta dau littafan islamiyyar ta duk da ta makara amma hakan bai hanata zuwa ba bata tarar da kowa a palour ba hakan yasa tayi hucewar ta suka gaisa da baba mai gadi har yayi mata ban gajiya...

" sauri sauri takeyi dan ta karasa tana karasawa taga malam umar ne aciki gashi tambayoyi yakeyi sai da cikin ta ya dan k'ada dan batayi karatu ba...

" malam ina yini?

" lafiya lou sai yanzu zakizo makarantar?

" wallahi munyi tafiya ne malam yanzu muka dawo...

" tohm jiki zauna...

" Fatima tace sannu kunshaa hanya amma kika tawo yau...

" ke ne inba dole ba mai zaisa nabar makaranta , tsorona daya yanzu

Please Login or Register in order to submit comment