You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" A'hh kice ke kande ce?

" bata ranta tayi tace banson sunan nan...

" murmushi yayi yace ai kuwa dole kiso domin acikin maza aka haifeki...

" hawaye ne yafara bin fuskarta...

" stop it ke dakike da sunan yan gayu babban suna humairat...

" Kallonsa takeyi yanayin nutsuwarsa tana burgeshi amma har yanzu bai kai ya haruna ba...

" shekarar ki Nawa?

" shekarata 20 babu wata 5

" kice ke yarinya ce wanne uni kikeyi?

" ban faraba.. Ne kadamine bacci zanyi...

" Am sorry my humairat kwanta kiyi bacci tohm...

" cikin k'in kina tace Ne kadaina kallona to...

" murmushi yayi yace toh....

Birni

Abu ya faskara gidan kullum rikeci da kananan magana haruna kullum ciwon kai ga firdausi ta saka shi agaba wasu shiga da takeyi kansa kullum a k'ulle...

" firdausi ce azaune tana faman kada kafa ta saka wasu english wears riga da wando...

" mama farida ce ta sakko daga bene shigar da firdausi tayi ya sata tsayawa cikin bacin rai tace firdausi...

" daga kanta tayi tace Naam ya akayi?

" Wannan wacce irin shiga ce?

" me kuma shigata tayi, i think Nan gidan ubana ne i have the right nayi duk abunda naga is right for me....

" Mama farida tace Has i said it kudinga jin tsoron Allah wannan shigar babu abunda zai jawo muku sai fitana gidan nan akwai maza ku kama kanku sai Allah ya baku miji wannan shigar bazata saka so azuciyar haruna ba...

" Toh ne nagaya miki haruna nayiwa toh shima nayiwa sai me? Kije kiyiwa jahilai wanda basuda ilimi....

" kuje kuyi tayi duniya ce...

Bayan haruna yayi wanka Nafila yayi sannan ya tsaya yayi sallar azahar sannan ya shiga kasuwa kaya ya rarraba kayansa a hankali ya huce office babu abunda yakeyi sai juya kujera wayansa ya kunna atake yakira d.p.o wai yanaje shiru ne?

" Haruna muna ta iya kokarin mu soonest muna fata za'a ganta inshaa Allah kudai kudinga yawan addu'a...

" munayi kuma zamu cigaba, yana karasa aikinsa ya huce gida wanka yayi ya zauna ya rike kur'ani a hannun sa bayan yagama karatun ya ajiye...

" Assalamu Alaikum yaya?

" wa'alaikis salam firdausi ya akayi?

" cikin Rangwada ta'isu inda yake zama tayi abakin gado kada idanuwanta tafarayi sannan tace wai har yanzu babu labarin kande ne?

" Kallon ta yafarayi yace eh wallahi kinga har na rame!...

" wallahi Nema abun yafara damuna, Amma ni banga wata ramarka ba, Anya kuwa kande ba guduwa tayi ba?

" Shiru yayi sannan yace bazata taba guduwa ba...

"Hmm haka dai kace good night...

" dauke kansa yayi yace gud nyt sai data fita sannan ya miki yayi sallah tare da Addu'ar Allah ya bayyanata...

" Dady kuwa kullum cikin neman kande yakeyi har yakai yanzu yafara sanar da malaman makarantar Allo domin a tayasu da Addu'a...

Abuja

Ummi ummi fito kije labari mai dadi..

" maryam wannan wane irin kirane?

" kiyi juyi kiyi tsalle kande ta bata an nemita an rasa fa...

" idiot cewar abi ku wanne irin mutane ne kanwarku ce fa...

" Ne ba kanwata bace ba wannan jahilar yar talakawa...

" wanka mata mari yayi nikike gayawa haka ko dayake uwarku ce ta daure muku gindi toh wallahi akan maganar kande sai na sabawa kowa....

" ummi da yake tasan halin abi cikin kissa tace ke maryam banason sha shanci yar uwarku ce fa...

" Kuka ta saka sannan ta huce sama...

" ke kuma saura ke wallahi kiyi hankali dani...

" bayan fitarsa tace Naga ta inda zaka shigo indai ina raye hamza bazai taba auren kande ba ayi mugane....

Kauye

iya habu kiyiwa Allah karkije birni inshaa Allahu za'aganta....

" kai Aliyu shiga tattayin ka banason hauka wannan ai iskanci ne ina haruna daba zaije ya dubota ba ahaba so sukeyi su kasheta hankalinsu ya kwanta!...

" Aliyu ne ya tsugunna karki damu iya kande bazata mutu ba har sai kwanan ta ya kare kuma kiyi fatan b'atan Datayi yazama Alheri.....

" kuka ta saka tace yaya kakeso nayi aliyu goggo batasan darajar yarta ba ' ya mace ce fa yanzu kowanne hali take?

" inshaa Allahu tana cikin koshin lafiya kuma nayi miki Alkawarin zanje birnin gobe zanje halin da ake ciki...

" Tohm na amince kakuma sanar da hassan wallahi haduwar mu bazatayi kyau ba indai bai nemomin kande ba...

" zangaya masa tashi naraka ki gida to...

" goggo ce tace har karakata wallahi iyah tafiye meta...

" Aliyu ne ya zauna kusa da'ita yace gaskiya goggo baki nuna damuwarki akan kande!...

" Aliyu kenan haka kuke gani wallahi kullum addu'a nakeyi kuma inata yin sadaka karfa ku manta kande 'yata ce....

" Toh Allah dai ya Amsa mana ya bayyanata....

Birni

Brox hamza lafiya tun dazu kayi shiru?

" wane kallo ya watsa mata sannan yace tunani na bazai huce halin da masoyi yata take ciki a yanzu ba idan Na rufe idona ita kawai nake gani....

" mtsewww son maso wane kakeyi, Ne bantaba ganin inda ake wannan abu ba kande fa bata sonka kuma kasan mutane dayawa sun riga ka.....

" shoutup malama in bazakiyi Addu'a ba To kiyimin shiru kizuba mana ido....

" yi hakuri dear banyi haka dan nabata maka rai ba....

" Dakko min lemo afrige, mikewa tayi tanata iya yee...

" Tsaki hamza yayi yace kiyi duk wata rangwada ba sonki zanyi ba...

" Farida tace wallahi kayi da 'yar halak sai kazo da kafafuwan ka neman soyayya ta ne kuma A lokacin kuma nariga nafi karfin ka....

" hamza ne yace see this mummu, ke zanso? Aikuwa kana cikin hauka, ita soyayya daya ce kauna ma daya anayi da mutane da ya dace...

" kuka tafashi dashi ta shiga dak'insu....

Kowa sai cigiya kande yakeyi a makaranta yau malam jabir ya tambaya 'yan aji ko lafiya kande...

" Anan kowa yace bai saniba...

" Toh muna fata lafiya..

Bayan fitarsa mlm umar ya shigo kamar yadda ya saba yauma tambaya ce amma ga mutum daya fatima idress inaso ki kawo mana hadisin dake magana Akan falalar kiran sallah....

" Assalamu alaikum acikin hadisi mai numba 614 cikin bukari
An karbo daga Jabir bn Abdullahi Allah ya qara yarda a gareshi cewa Annabi SAW yace: Duk wanda yace yayin da yaji kiran sallah: *ALLÃHUMMA RABBA HÃZIHID DA'AWATIT TÃMMATI WASSALÃTIL QA'IMATI, ÃTI MUHAMMADAN ALWASEELAH WAL-FADHEELAH, WAB-ASHU MAQAMAN MAHMUDAN ALLAZY WA-ADTAHU* to cetona ya zartu/tabbata a gareshi ranar alqiyama .....

Wato wannan addu'a na sanya bawa cikin ceton Manzon Allah SAW ana so mu ringa yin wannan addu'ar bayan mun amsa kiran sallah mun yi salatin Annabi SAW sai mu karanta ita wannan addu'ar sai kuma mu roqi Allah buqatunmu....

Barakallahu fiyki Anan zamu tsaya, fatima kije gidansu Aisha kuje lafiya bata zuwa....

" Tohm inshaa Allah..

Jigawa..

Yau sati Na hudu kenan kullum su mamee suna zirga zirgar asubuti, har sun bawa kande wata sandar koyan tafiya yauma kamar kullum mamee na ruke da ita a bayan asubutin tana dan tattakawa...

" mamee nagaji fah..

" 'yata daure kikai can sai kihuta...

" kande ke kallon ta ciki da kauna dama bazata rabu da mamee ba...

" a hankali ta rungumota suka karasa gurin wata chair suka zauna...

" sannu 'yata bari na dakko miki fruit a dak'in namu...

" Tohm, shiru ne yafara isar kande a hankali ta miki amma ina kokarin wad'uwa takeyi kuka ta saka Nan da nan idunta ya k'ada...

" abdul ne cikin sallama ya iso inda take a hankali yace my humaira...

" tana daga idonta yaga yayi jajir ga wane sabon hawaye yana bin kwancinta....

" my humaira please Don't cry for your loss Allah won't take any thing from a believer without replacing it with something better,
Allah said in the Qur'aan, "Perhaps you may dislike something which is good for you, and like something which is bad for you. Allah knows and you do not." (2:216)....

" kalaman sane sukayi tasiri a zuciyar ta sai kuwa tatafi luuu zata wad'i...

" Hannun ta ya ruko sannan ya zaunar da'ita a kujerar kusa dasu....

" kallonsa kawai takeyi da jajayen idunta da hawaye bai daina zubo mata ba...

" kiyi hakuri my humairat Na rike hannun ki Naga zaki Wad'e ne....

" hannun ta tasaka ta goge hawayen fuskar ta...

" har cikin ransa yana jin tausayin humaira gashi taki tasanar dashi komai akanta ga zuciyar sa tana saka masa wasu abubuwa....

" a hankali cikin sanyin murya tace kaifa kace nadaina tunani mey isa kai kakeyi....

" cikin murmushi yace tunanin ki nakeyi.....

*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment