You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi karatu ba..

" karki damu zaki haye inshaa Allah...

" Abdullahi uba ga tambayar ka akwai hadisi mai lamba 6846,6406 bukari da muslim ne suka rawaito Amma lafazin hadisin na muslim ne me hadisin yake magana akai...

" hadisin yayi magana akan kalmomin da Allah yakeso ne.. An karbo
daga gareshi -Abi Huraira Allah ya qara yarda a gareshi- daga Manzon Allah SAW yace: (( Kalmomi guda biyu masu sauki akan harshe, masu nauyi akan mizani -ranar alqiyama-, Allah mai Rahama yana sonsu :
*SUB-HÃNALLAHI WA BI HAMDIHI, SUB-HÃNALLAHIL AZÊM ))*

" jazakallah...

" Aisha ga tambayar ki, wacce addu'a ce sayyadl istigfari? A wane hadisi aka kawota? Wanene ya rawaito? Da kuma falalarta...

" sai da cikin kande ya kada sannan ta mike cikin rashin kuzari tace
Bukari ne ya rawaito cikin hadisin sa mai lamba 6306, itace shugaba cikin zikran neman gafara kamar yadda yazo acikin hadisi cewa : An karbo daga Shaddad bin Aus daga Annabi SAW yace: "Shugaba cikin zikran neman gafara mutum yace: *(( ALLÃHUMMA ANTA RABBY LÃ'ILAHA ILLA ANTA, KHALAQ-TANY WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MAS-TA'DA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA'ATU, ABUU'U LAKA BINI'IMATIKA ALAYYA,WA ABUU'U BI ZANBY, FAG-FIRLY, INNAHU LÃ YAGFIRUZ ZUNUUBA ILLÃ ANTA))*

Kuma yace: (( Duk wanda ya fad'eta a yini yana mai sakan-kancewa da ita, kuma ya mutu a wannan yinin kafin ya kai yammaci, to yana cikin 'yan aljanna, kuma duk wanda ya fad'eta da daddare, alhali yana mai sakan-kancewa da ita, sai ya mutu kafin sãfiya, to yana cikin 'yan aljanna...

" barakallahu fiyki...

Mumy ce ke faman masifa da zagi a palour wannan yar iskar yarinyar ina ta shiga haka zata barmana palour kacha kacha....

" mama farida ce ta sakko daga sama to mekike nufi idan batanan Ne zangyara...

" karkiyi min rashin kunya wallahi...

" rashin kunya ta nawa kuma ai sai dai in bakiyi abunda za'ayi miki fitsarar bani kin sangarta 'ya'ya basayin komai basu iya komai ba sai kwanciya ko kina tunanin ba gata kukeyiwa kande ba?

" gidan uban su ne babu abunda zatayi...

" itama gidan uban nata ne tunda kawunta ne....


" k'ande ke faman tafiya ita kadai burinta taje tayi sallah ta kwanta wata sallama taje sai da kirjinta ya buga...

" a hankali ta amsa tare da fadin ina yini?

" lpy ba lafiya ba kinbarni cikin k'ewa da damuwa, gaskiya ya kamata ki samu waya Aisha...

" Allah uncle isyaku?

" Allah kuwa wannan kwanakin dakikayi duk sun hargetsani wallahi kullum tattausar muryarki kemin yawo acikin kaina, soyayyar ki ta faskara kuma nan da next mouth za'akawo kudi fa...

" kamarya?

" cikin murmushi da mazan taka hace ai an aiko gidan ku...

" dakewa tayi tace Allah ya zabama abunda yafi alheri...

" Ameen matas, k'insan Allah ina masifaffan k'aunar k'i ne bikin ma banaso yakai 5mouth wallahi nagaji....

" Dariya tasaka tace ne wallahi kunya kake bani uncle...

" zan ma daina baki ayayin dana fara kashe ki da kalamai na...

" bye bye ni dai nazo gida...

" shigar kande kenan mumy tace toh tam badaddiya, mai bin maza, daga dawowa har kin ja hijjabi kin fita wa zai gyara miki gidan?

" mumy makaranta fa naje...

" Aa ilimin kika jawo dallah shige ki gyara gidan ki kuma dora girke...

" tohm ta Ambata sannan ta shiga dak'in ta...

" gurin karfe tara tana kasan dak'in ta a zaune sai ga haruna ya murda kofar ya shigo...

" zama yayi kusa da'ita ga takeaway na siyo miki nasan bakyacin couscous...

" kallonsa kawai takeyi...

" kanwata please kidaina saka damuwa kikuma daina zama da yunwa kinje?

" Tohm, yaya waya nakeso kacika kasiyamun please....

" ban yarda ke riki waya ba!...

" shiru tayi tace to...

" wayannan mayafan ke daina saka su zankaro miki hijjabai...

" ita dai kawai da to take binsa takasa fahimtar inda ya dosa...

" cikin rashin fara'a tace yaya ina Amira?

" yanzu kice Amirata...

" har yafita tana kallonsa...

"Da safe cikin ta ke danyi mata ciwo bata gyara dak'in da huri ba.....

" Tana fita mumy ta wanka mata mari...

Cikin kuka zata koma dak'in ta haruna ya rikota...

" rungumesa tayi tana kuka....

*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[1/28, 12:38 PM] ('kubrieh cier vervier: _58-62_

*K'ANDE*


Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*


Da safe cik'in ta k'e danyi mata ciwo bata gyara dak'in da huri ba.....

" Tana fita mumy ta wanka mata mari...

" Cikin kuka zata koma dak'in ta haruna ya rikota...

" rungumesa tayi tana kuka Cikin kuka tace yaya bansan me nayi musu ba basa sona basa kuma kaunata ballantana suje tausayina wallahi koda da rana daya ban taba gajiyawa dayi musu aiki ba, cikina ciwo yakeyi shiyasa ban fito ba takara fashiwa da kuka...

" har cikin zuciyarsa yaje ciwo haruna cikin tattausar lafazin sa yace hakuri da jama'a mutunci ne, Duk abunda kayi masoyinka kawai kake burgewa , Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su, Akwai kuma ma su kin ka duk yadda ka kyautata ma su, Dan haka kiyi hakuri komai yakusan zuwa karshe inshaa Allahu, Ahankali ya dago fuskar ta yadda yaga idunta yayi ja yasa shi cewa kidaina kukan jeki huta kinje...

" batare da ta yi magana na ba ta zame daga jikinsa ta shige dak'inta...

" mumy da tayi sukuti abun duniya ya 'isheta kar dai haruna son kande yakeyi tafi minti goma tana tunani Amma takasa bawa kanta Amsa sallamar farida ce ta katseta dama ku nake jira yau naga kudurar Allah...

" mum mai yafaru?

" wannan yar iskar yarinyar naga haruna na lallashi...

" farida tace ai sonta yakeyi!

" so fa kikace farida...

" wallahi mumy sonta yakeyi rannan agabana yafada...

" bantan uban nan ai wallahi bazai yihuba firdausi ce daidai dashi...

" hmm ai matar mutum kabarinsa ....

" Mumy tace dallah yimun shiru uban wa yace miki ba hakaba?

" farida tace ai haruna ba danki bani ballantana kuyi masa dole dan haka kubarsa ya zabe wacce yakeso...

" yimun shiru wawiya wacce bata kishin yar uwarta to bari kije auren firdausi da haruna babu fashi kande kuwa bazan taba barinta taje dadin rayuwa ba....

" hmmm Nidai babu ruwana..

" Dole kuwa yayi ruwanki mumy tashiga daki cike da takaici da bak'in ciki...

" kande dake zaune akan gadonta tarasa me yakeyi mata dadi ahankali tatashi ta'isa palour dantasan mumy ta raga mata ne dan taga haruna in banda ma yananan duka zatayi mata ahaka ta daddafa tashire ko'ina, ta dura girke amma ina cikin ta dai bai daina ciwo ba zama tayi tana sallati daidai lokacin haruna yashigo....

" meke damunki?

" cikina ne yake ciwo tun dazu da nazata zai lafa kaga kara azaba yakeyi...

" tashi muje nakaiki asubiti...

" yaya bangama abincin ba mumy zatayimin fada kuma naga kamar yunwa sukeji....

" ina zuwa sama yahau dakin mama farida tana zaune kan kujera alamar karatun alkur'ani takeyi sallama yayi mata...

" haruna kenan sai yau akaga damar shigowa dak'ina?

" mama kenan am always busy shiyasa please ina bukatar taimakon ki...

" name fa?

" Dan abinci zaki karasa kande bata jindadi ne zan kaita asubuti....

" Bakomai amma me isa bazaka saka su firdausi ba?

" kinfi kowa sanin babu abunda suka iya last 2days da suka huce nace ta dafan taliya i can't even take it to my mouth....

" hakane bari nakarasa darajarka tace wallahi amma da itace tasan bazanyi ba...

" Nagode mama, Yana sauka yasanar da kande ta saka hijjabin ta...

" Tohm tace sannan tafita, shikuma haruna ya tsaya yana kallon yadda tagyara kitchen din yayi fes lallai dole aci kande *Ta Dabance*....

" A mota ta sameshi har ta bude gidan baya yace ne driver dinki ne?

" cikin yamutsa fuska tace kamar yaya?

" malama shigo gaba mu tafi, ko amsawa batayi ba ta huce ta shiga tunda suka fita babu wanda yayi juna magana sunkusa karasawa Asubutin haruna yace zafin yakeyi miki ne?

" ta daga masa kai tare da kauda kanta...

" Nan ya karbar musu number sannan ya huce suka zauna ahaka number tazo kansu ta miki zata shiga haruna ya huce gaba...

" Nan dr yayi mata yan tambayoyi yakuma sanar da'ita ta daina yawo babu takalmi ta kuma ta daina shan zaki, yace taje dak'in can ayi mata allura....

" Bayan fitar ta dr yace bawane abu bani tanayin aure zata daina...

" haruna ya karbe takardar maganin ya siyamata su sannan suka huce gida..

" suna isa gida sukayi ido biyu da firdausi sau huce takeyi tana daddaure fuska...

" haruna yana fitowa kande ta fito ta kalleshi tace nagode yaya ta shige cikin gida...

" haruna da ya koma mota ko kallon firdausi baiyi ba ballanta na ya san halin da take ciki...

" gidan ta shiga aguje ta hayi step dinsu dak'in mumy tashiga tana zuwa ta rungeme ta please mumy ayi maganar auren mu da yaya wallahi ina sonsa i can't life without him...

" Karki damu kinje aure kamar anyi angama ko yanaso ko bayaso...

" are you serious mum?

" Yes i am kice fa auta ta farincikin ku shine nawa...

" Nan ta rungema ta i love you mum...

" after kande tayi sallah ta dauki abuncin ta sannan ta sha magaba within 1hours cikin ya lafa Nan ta dauke book dinta ta huce makaranta...

" haruna ne yake cikin office juya kujera kawai yakeyi knock yaje yace come in...

" fatuhu ne yace mutumin 2daya baka shigowa office...

" kai dai bari fatuhu yarinyar nan ce tafara rudane wallahi am always thinking about her....

" wai u mean firdausi?

" Which firdausi ana maka maganar kande she have change her life style, her walking, talking even her body build kai bari ma kaje she's so silent like never....

" wuff bantan uba dole ta rikirkita ka, yanzu what wrong what going on?...

" hmmm knows a days ko bacci banayi sosai kullum tunanin ta, da ban dauki sonta komai ba yanzu kuwa inna rasata i think nema sai an rasane....

" hahaha yaga yar budurwa ta chanja shi, gwara kayi auren haruna fa dubine nema da yaya 2 fa...

" kullum tunanin iya habu nayi aure amma yanzu lokacin yazo....

" hakane wallahi ai kamayi hakuri...

" haha over hakuri ma nayi wallahi jiya datayi hugging dina tana kuka wallahi i feel something har cikin kaina am so shock kai mutuwar tsaye nayi....

" hahaha Mutumin baka dakyau gwara dai karabu da magunguna kakama da'ir...

" Soonest ma inshaaAllahu but bata wane damuwa akaina fa it seems like bata sona....

" ai kai zaka koya mata son naka always show concern a kanta...

" hahaha okay i will makesure nayi trying...

" kai jibe ne fa tafiyar nan America...

" why not kuje ku kadai?

" aa haruna karfa kajawo nana asara fa zuwan mu zai kara habbaka kamfanin mu...

" hakane Allah ya kaimu...

"Ameen..


K'ande suna cikin aji suna bada hadda after tagama malam jabir yace Aisha ki tsaya kiyi karatu saboda kwakwalwar ki ta karatun ci kuma kina taimakon mutane a class dinnan baki da kyashi...

" cikin ladabi tace inshaaAllahu malam zanyi Allah dai yabamu masu Albarka...

"Ameen, bayan fitarsa malamin fiqhu ya shigo malam hassan sanadiyar ya sanar dasi shima yau tambayoyi zaiyi...

" fatima tace Aisha nefa wannan tambayoyin Allah wahala sukeyi min...

" komai sai da nace fatima kidinga kokartawa please ahaka kima zaki dage...

Tohm Aisha nagode...

" malam hassan ne yafara sallama sannan yasanar dasu zamu fara tambayoyi zamu fara da fatima tambayar ki itace ayayin da mace take cikin Al'ada bata samu damar yin azumi ba me ya kamata tayi?

" Sai Ta kasance cikin lazumi da karatun kur'ani da kuma yawan kabbara da sadaka farantawa bayin Allah kame bakin daga mugun zanci da tsare kai daga cin naman mutane da kuma zalunci...

" Mashaa Allah..

Tambaya ta biyu Amina sageer inaso ki sanar damu menene yake wajabta wankan jababa?

" Assalamu alaikum abunda yake wajabta wankan janaba shine fitar maniyyi ta kowacce hanyan biyan bukata ta aure ko ta hanyar mafarki ko ta hanyar babbar sha'awar data jawo maniyyi yafita, iDan mace ta gama jinin Al'adarta da jinin haihuwa in har ya dauke wajibe ne da suyi wanka....

" Mashaa Allah..


Tambayar mu takarshe Aisha zaki yimana bayane siffofin mace saliha guda uku...

" kande ce ta mike tare da sallama tace mace saliha itace mai addini tana karfafa mutane akan addini tana dura yayanta da mijinta saboda mace tanada tasiri akan mijinta in ta karfafashi zaiyi aiki inta jarya masa gwuiwa bazaici nasaraba Domin manzon Allah saw yace mumini bai taba samun fa'ida ba bayan tsoron Allah kamar mata saliha mai taimakawa mijinta akan Addini (shih muslim)..

" Mace saliha itace mace mai gaskiya son zuciya bai rufe mata ido ba kullum burinta ta fadi gaskiyi kamar yadda Allah yace yaku masu imani kuji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya(suratul tauba)manzon Allah yace gaskiya tana shiryarwa zuwa ga bin Allah bin Allah yana shiryarwa zuwa ga Aljannah(bukhari da muslim)...

To jazakumullahu khair sai mun hadu wane satin...

A hanya kande na cikin tafiya kamar yadda tasaba Jin sallamar uncle ce ta katseta...

" ina yini uncle? Ai nayi tunanin bazaka zo ba yau..

" cikin rashin fara'a yace ai gani nazo dai ko?

" ba taji dadin yadda ya furta maganar ba sai tace wallahi nima ban jindadi shiyasa ban dubo result dina ba..

" ya kamata mudinga waya Aisha wallahi inason kasancewa dake sosai Amma ke gani kikeyo kamar bana sonki...

" cikin jindadi tace karka damu nakusa yin waya Nema...

" any way saura 3weeks aturo gidan ku...

" kirjenta taje yayi mugun bugawa can kuma sai ta rufe fuskarta...

" Na duba miki weac dinki tana gurina anjima da daddare zan kawo miki...

" serious? Na wadi ko?...

" hahaha uwar tsoro zakigane da idonki saina kawo...

" tohm inajera bye...

" Shigarta cikin daki tayi wanka tayi sallah addua takeyi sosai Allah yazaba mata mafi Alheri....


Abuja

" hamza ne ya kalle abi cikin ban tausayi yace abi har kadawo?

" eh nadawo yanzu inajinka wacce yarinya ce ? Aina take? Yar wace?

" ummi tace nema dai na dago naje yarinyar nan ko hankali na zai kwanta duk ya damu kansa saboda soyayya...

" cikin raunin murya yace Abi batasona Amma ne inasonta...

" ya sunanta?

" bakowa bace face kande 'yar gidan goggo....

" Aishatu wai kake nufi??

" eh itace..

" will you shoutup impossible wallahi how come's karasa yar dakakeso sai ita yar talakawa....

" Abi yace kaga son daina hawaye fuskance ne dama baka son farida?

" wallahi bantaba son farida ba ko maganar soyayya bamu tabayi ba katambayi ta kaje...

" Wata sabuwar cewar Abi...

" ummi ta miki cikin masifa tana fadin nifa bazan amince da wannan kwamachalar ba sam bazata sabo ya auromin dangin tsiya ba....

" Abi yace dani kike wato tunda mahaifiyarta yaruwata ce ai...

" wallahi baka isa ba bazaka auro min wannan yarinyar ba....

" Abi yace kakwantar da hankalin ka hamza indai ina rayi zanyi iya bakin kokarina dan ka aureta....

" yauwa Abi nagode...

" Ai wallahi baku isa ba...


Birni..

" gurin karfe 12 haruna yakasa bacci juye kawai yakeyi jikinsa babu karfe ya miki ya tura dak'in kande bacci takeyi...

" A hankali yace kande? Kande??

" cikin ya mutsa fuska tace lafiya da daddaren nan zaka shigo min daki?

" Wallahi nakasa bacci kaunarku ita ke yawo acikin raina dan Allah ki yarda bikin nan kar yakai 1mouth...

" atsorace tace biki fa kace yaya wane biki koma?

" wallahi a matse nake nagaji...

" kace gaba da hakuri yaya komai lokacine...

" wane hakuri kuma kande? Bayan wanda nayi am almost to 35 fa? In banyi aure yanzu ba mata kikeso nabi? Ai da'ace ina bin mata gwara nayi auren cuz am in need...

" ita dai kallonsa kawai takeyi...

" Gobe zanje kauye domin maganar auren...

" Gaskiya ya..sai kuma tayi shiru...

" nasan kina sona kamar yadda nake sonki Dan Allah ke amince dani Aisha...

" bayan fitarsa ta mike ta shiga toilet ta gabatar da Alwala tafara yuwa Allah kirari....

" Da sassafe wayar mumy tafara ringing cikin barci ta dauka salamu alaikum...

" ba bacci zakiyi ba tashi zakiyi kinakasa kande domin hamza ya dage sonta yakeyi....

" a firgeci tatashi hamza kuma???.....


*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[1/31, 8:24 PM] ('kubrieh cier vervier: _62-66_

*K'ANDE*


Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*



" Nasan k'ina sona k'amar yadda nak'e sonk'i Dan Allah k'e amince dani Aisha...

" bayan fitarsa ta mik'e ta shiga toilet ta gabatar da Alwala tafara yuwa Allah k'irari....

" Da sassafe wayar mumy tafara ringing cik'in barci ta dauk'a salamu alaikum...

" ba bacci zakiyi ba tashi zakiyi k'i nakasa k'ande domin hamza ya dage sonta yak'eyi....

" a firgeci tatashi hamza kuma???.....

" ummi tace eh shimana tun jiya muke fada da mahaifinsa nace bazai aure ta ba ina dalili ak'awo min talaka kazama jahila gidana ai wannan bazata sabo ba sauro yayi fada da zaki....

" Ne wallahi Nama kasa magana anya yarinyar nan ba Asiri takeyi ba?

" zata aika ai bakiga kallarta ba ma...

" Ai kuwa zatasan ta tabo tsuliyar dodo wallahi sai tabar gidan nan.....

" Ai kafin ma ta bar gidan ki tabbatar kin nakasa ta....

" Angama...

K'ande dak'e zaune tana faman duba littafi wanne tunani ne yazo mata babu shiri ta mik'e tayi tunanin duk bacci suk'eyi sai ta fita da rigar dake jikinta saboda aikin zai fi yimata sauki sauri takeyi har tagama wanke wanke ta dura tea...

" haruna kuwa yana zaune a palour yana ciki wasu files...

" lokacin da kande ta fito bata kula dashi ba sharar ta kawai takeyi har sai da tazo gurin kafarsa sannan ta daga kai takalli shi.....

" k'allon ta yake tayi wane abu dayaji yana yimasa yawo har cikin kwa-kwal-warsa ahankali cikin murya mai taushi tace ina kwana yaya?

" cikin murmushi yace Amma wannan kayan bai kamata kina sawa acikin gidan nan ba!...

" cikin ladabi tace nayi tunanin babu kowa a palour ne shiyasa....

" okay jiki chanja su...

" tohm tace sannan ta saka hijjabin ta tafito ta karasa sannan tatafi kitchen domin fito da kayan tea....

" haruna dake faman juya bairo yama kasa cigaba da rubutun cikin zuciyar sa ke faman fadin lallai kande tayi kaunar ta har cikin jini na nakejinsa....

" lokacin da ta karasa wanka taje tayi ta rangada kwalliya don tasan uncle yau zaizo....

" mumy ke faman juya spoon takasa karyawa...

" Dady ne yace what wrong mumy naga kin kasa shan

Please Login or Register in order to submit comment