You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'ande tun kina kara? " tsohuwa kamarki ma tayi ballantana ne yarinya, " ai yayyen ki ma basu isa ba, " su kikace Amma ne ta dabance...

" tunda lokacin abubuwa suka fara sauya wa har Allah yadau ranta!!!

" nan goggo tace ai kin ibo halin tsiya irin nata....

" kayi hakuri kaje baba nadaina fitina...

" bazaki daina fita ba har sai kinyi karatu mai zurfi shiyasa nayi miki kwadayin haruna yaro ne mai mutunce!

" mahaukacin baba!

" ai ba da hauka aka haife shi ba samun haukan yayi anan duniya kuma zai warke!

" kazamine, kuma baya sallah gashi mugu idan kuka auramin shi ya zani ne fa shikenan sai kukaine asubuti ne da jin zafi ku da sannu!

" ayer ayer haruna yafi karfin k'ande wazai aure ta!

" baba ransa a bace yace karki kara saka mana baki in muna magana!

" haruna dakike gani yaje garuruwa da dama kuma yanada degree dinsa! Ke zancen sallah kuwa tun yana karami akayi masa shaida, kuma kowa yasan babu ruwansa, kuma bazai dauwama ahaka ba...

" kuka k'ande tasaka baba ta yaya za'ace yafe karfina bayan nafishi hankali...

" Akwai abubuwan da nakeso kesani cewa ita rayuwa ta muminai ce in kina kyautatawa bayin Allah, to kema Allah zai taimaki ki, kiso mai sonki ko da bai kwanta a zuciyar ki ba, domin kiyayya babu dadi...

" tohm ya mahaifina ina sonka babana komai daran dadewa zan zama mai taimakon al umma!

" inane yake yimiki ciwo yanzu?

" kafata ce..

" zanje gurin ta mai magani yanzu na dawo...

BIRNI

Haruna ya samu cikakke yar lafiya, yauma kamar kullum yayi wankan sa yasaka wane yadi sai da yayi sallar walha sannan ya samu guri ya zauna!

" hajiya da dady suna palour suna hira Firdausi ta fito fuskar ta ciki da murmushi!

" har kun tashi?

" yes dad yau bamuda lecture, dady mota ta wallahi tafara lallacewa ka siyamun wane mana!

" in kinyi kokari a skull zan siya miki shiga kikira mun yayanku!

" ops gaskiya dad kadaina calling dinsa da brother namu...

" hmm firdausi kenan watch him full zakiga abunda bakuda shi...

" tsake tayi shiga dak'in nasa kai mutumin kauye mahauka ce sai kazo inji dady!

" itace sallamar take?

" mamaki ne ya cika ta tace eh ko akace maka zakazo gidan ubana ne kayimin iko?

" Gidan ubanki ko gidan uban mu wai ahaka kuna jami'a sai girman kai da tak'ama...

" mtsew dad kaji yadda ya zage ni!

" alhaji yace ai haruna baya zage banson sharri!

" gyaran murya haruna yayi sannan ya durkusa yace barka da asuba!

" barka kadai...

" ta shigo daki nane babu Sallama naga kuma kowacce yarinya kamarta tanada hankali in batayi sallamar dan niba ai tayi dan samun lada!

" Alhaji yakamata asamo masu yimusu lesson domin babu mai auren su da dabi'ar nan!

" tabbas hakane haruna dama maganar office ne gobe kafara zuwa!

" aa Alhaji nan da 3mounth zatafi masters zan kuma naime aiki da kaina nagode...

" sis abeg mik'i kinga yadda haruna ta canja ke ingaya miki har sharri yayi mana ne da ke...

" what???

Ai kuwa wallahi sai munyi maganin sa...


KAUYE..

A Ranar k'ande gida ta koma sai da aka aiko tazo inji baba sannan ta fita tun ahanya kirjen ta yake bugawa tana shiga soro taje ihun su inna sadiya ta samu tace lafiya kigayamin?

" baba baba sai ta fashe da kuka...

" Kar kice min mutuwa yayi tana kuka tana jijjiga 'yar uwar k'ande data hango mutum akwance baba ya zaka tafi kabarni wayoo nan i tama ta suma....


*Urs Nana diso*



http//:nanadisoo.mywapblog.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[12/16/2016, 7:22 PM] ('kubrieh cier vervier: _20-23_

*K'ANDE*

Ink'iya:-Nita Dabance!!!

*NA NANA DISO*


Baba baba sai ta fashe da k'uka...

" Kar kice min mutuwa yayi tana kuka tana jijjiga 'yar uwar k'ande data hango mutum akwance baba ya zaka tafi kabarni wayoo nan i tama ta suma....


" goggo ce ta dauk'e k'ande ta k'aita dak'i da gudu sadiya ta bita nan aka shirya baba sai gidan sa na gaske kowa a kauyen sai da yaji mutuwar alhaji yakubu, su ya abbas sai zirga zirga sukeyi har aka dawo daga kai mahaifin su, kowa agidan sai kuka yakeyi..

" goggo tana shigowa ta k'wara wa k'ande ruwa...

" wayyo Allah na shiga uku k'atana yak'are tasaka ihu wayyo Allah babana Allah yajikanka yayi maka rahama!

" zaki rufemana baki ko sai ranki ya baci..

" k'ande cikin kuka tace ai bacin rai ta fara haduwa dashi har...

" iya habu ta taso tace haba k'ande menene haka kuka banaki bani ba addu'a zakiyi masa...

" wane sabon kukan ne yazubo mata nayi shiru kikace? Kinfine sanin dacen mutuwa kuma ace masoyin kane yatafi...

" toh kiyi hakuri dai...

" babu wanda takara kulawa tunda ta kwantar da k'anta acinyar ta!

" mutane sai gaisuwa ake shigowa..

" goggo da idon ta ya kumbura ta kalle farida tace kidaina kuka domin babu abunda zaiyi miki sama da kisa kanki amatsala..

" farida tace bana tunanin zan samu miji kamar baba, mai tausayina mai sona ga sanin damuwa ta...

" haba farida Allah shi yakarbe abunsa kuma yafemu sonsa...

" Tohm goggo...

Yau sadakar bakwai angama addu'a su goggo sunata karbar gaisuwa!

" babu yadda ba'ayi da k'ande tayi wanka ba Amma tak'i in banda wari babu abunda takeyi...

" k'ande bazakiyi wankan baniba? So kikeyi kijawo mana magana!

" sadiya tace ai goggo bakije warin datakeyi na! Duk ta cika mana dak'i...

" farida tace ai nema tazo nakusa amai saboda warin hammatar ta...

" kuka tasaka tayi gefe tare da tausayin kanta taje sannan tace wari innayi kaina ne kuma jikina ne!

" iya habu da sauran yan gaisuwa sukace tsafta dai tana daga cikin imani..

" haba dame zanji? ba zanyi ba ai jikina ne!

" hajiya asabe tace Ai k'ande ta dabance...

" yaya Abbas ne ya shigo ke k'ande kizo inji adam?

" me zanyi masa?

" gaisuwa zai yimiki tun daga birni yazo yimiki gaisuwa!

" lokacin da yatafi birni ai bai gayamin ba kuma gaisuwa bazan fito ba nayafe! Yayi masa Addu'a daga nan...

" anya kinada hankali?

" ai kasan haukan gadonsa akeyi...

" iya habu tace tashi k'ande kije mana!

" wallhi bani zuwa yayiwa su baba datti gaisuwar...

" to kai Abbas jik'ace bata fitowa...


K'ande ce ta zauna kusa da goggo tana fadin tabata gurasa...

" anya k'ande kinji warin dakikeyi subhanallahi wannan wari haka!

" mikuma nayi..

" goggo ce ta k'auda k'anta wai bakinki kamar mushe, tashi kibani guri bazan shaki wari ba...

" haba goggo kudaina takurawa yarinyar nan cewar iya habu!

Zo kizauna kusa dani zama tayi sannan tace Allah yajikanka baba!

Sallama ce duk'ansu ta katsesu!

Goggo ce tace maraba maraba sannunku aka shimfida musu dadduma...

Alhaji mahmuda ne yazauna sannan matarsa surayya sai 'yayan sa maza haneef da muneef sai hamza...

" ya hakurin alhaji yakubu Allah yayi masa rahama ya gafar tamasa..

" Ameen dan uwa ina sauran 'yayan naka?

" suna jarabaww kuma final ce!

" Allah ya taimaka!

" Aka kawo musu Abinci!

" ina Aishatu ne?

" au K'ande kaganta nan!

" A hankali ta dago idonta dayayi jajir ta fara kallon sa taso tagane fuskar Amma takasa!

" Aishatu babu gaisuwa?

" ina yini? Alhaji mahmud kawai ta gaisar sauran ko k'allon su batayi ba!

" ya hakuri?

" Da godiya!

" Aisha tu zaki bini birni?

" kirjenta ne ya buga sannan taja numfashi tayi shiru..

" kow agurin yasan e zatace goggo da duk kunya ta'isheta...

" muazzam yace badake ake magana ba?

" k'allon su tayi tace bazani ba!

"Tohm in an kwana biyu kafin nan mutuwar ta dan sakeki zan aiko a dauke ki...

" Ahankali farida tace lallai k'ande ta dabance!!!

Birni

Haruna ne ya fito daga dak'insa sanyi da wani blue din yard yayi masa kyau hushiryar nan abude, ga wane irin kamshi ne ke tashi! Firdausi ce ta tawo tana kokarin shiga part din wane kamshi taje tarasa wanene yasaka wannan turare ahankali ta dago idon ta tayi tunanin uncle mu'azzam ne amma kuma mumy batace zaizo ba!

Cikin mamaki tanuna haruna tace you..., it seems like amfara satar mana duk'iya har yaushe ka warke? Dakai nake magana mad man!!!

" murmushi yayi yace excuse please....

" Nan firdausi tashiga wane tunanin..direct dak'in farida ta shiga sister common get up!

" what wrong?

" wannan mahaukacin nagani ban ganesa ba fa wallhi he's so handsome..

" see u mummu which handsome fari ne ya k'e driving dink'i...

" firdausi ce taja wane numfashi that's cool ai, ya maganar Egypt din?

" farida tace we need to ask mumy again fa..

" am praying dad yabiya mana!

" Ameen dai..

" sis see you later inada lecture by 5 zandawo...

" okay bye bye..

" haruna yana isa company din yasamu mai gadi yace manager yana ciki?

" kunyi da shine zakuzo?

" baba ka taimaka kusan sati 3 ina zirga zirga ban ganshi ba kuma ina bukatar aikin!

" tohm muje ciki...sir kanada bak'o!

" how many times baba zangaya maka banida time...

" gudummawa zai bayar ga kamfanin nan fa!

" as you said it! Ya shigo..

" assalam
" wslm

" Barka da asuba!

" lah Nura dama kaine?

" Dan duniya ashe baka samu aiki ba?

" wallahi kam nura nadan same matsala ne but Alhmdlhi yanzu!

" Allah yakara sauki, inasu iya habu?

" duk lpya ga takarduna ko zan samu aiki anan!

"To kaga nan kamfanin Atampha ne kuma manya ba kanana ba kuma kaima bangarin business ne so know zan nunawa manager duk yadda mukayi zakajeni!

" tohm nagode sosai 'ya'yan k'a nawa?

" hahaha kai kazana tuzurzur har yanzu kaki aure, yayana 3!

" its all about time ai soonest zanyi nema!

" okay see you later..

Lok'acin da ya koma gida farida da firdausi ya tarar kujera yasamu ya zauna...

" duk'ansu sun kuro ido suna kallon sa, wayarsa ya dak'ko hello my shukra!

" Dafatan kana cikin s
Koshin lafiya?

" kema ina fatan kina cikin koshin lpya?

" lapia lou yaya yajikin naka?

" Alhamdulihi ina fata kin karasa haddarki?

" eh nagama bari na barka ka huta Allah yakara lpya

" Ameen nagode da kulawarki Allah yayi miki Albarka...

" firdausi ce tayi gyaran murya tace sis yaushe mu'azzam zaizo?

" farida tace kicemin gwarzon namiji mai hankali!

" eh hahaha "yana tafe..

Yanzu abunda kayi ka kyauta haruna?

" Wallhi Alhaji kai nake jira kazo mutafi tare!

" To kashirya yanzu mu tafi yanzu har sati 2,....

" ku shirya kuma...

" dady bamason kauyen wahala muke Allah yajikan tsoho!

" Dan uwa nane uwa daya uba daya kuma yadda kukace tsoho kuma haka za agayawa uban ku sha sha shai...

" tun 4 suka dauke hanyar kauyen 5 da rabi suka i'sa su goggo suna tsakar gida suna tsintar shinkafa!

" Assalamu alaikum!

" wa'alaikussalam

" sannunku da zuwa..

" A'a haruna alhamdlhi kamar bakai ba ga jar fatar takara fitowa!...

" ya hakurin baba Allah yayi masa rahama!..

" Ameen sun dadi azaune suna hira bayan magariba haruna yace nari naje nagaida iyah..

" Tohm sai kadawo...

" ina k'ande ne cewar baba?

" goggo tayi murmushi tana gurin uwar dak'inta!

" toh Alhmdlhi yanzu dai inason nasanar dake nan da sati 1 zanzo dakaina na dauke k'ande itakuma sadiya jibril ya dauke ta!..

" Alhaji tohm mungode Amma Abar mana sadiya....

" tohm shikenan...


Haruna ne ya rangada sallama Assalamu alaikun iya habu!

" Muryar wa nakeji kamar ta haruna!...

" k'ande ce tasaka dariya kardai kima haukan yafara zuwa daga ne fa saike!

" iya habu iya habu...

" kande shine shine haruna kaine ko fatalwa ce?

" Nine goggo nasamu sauke!

" Nan iya habu tayi sujjada ta gode Allah!

" k'ande da ta kura masa ido tana ganin sarautar Allah!..

" to ya zancen Aure haruna!

" Nasamu yarinya shukrah haduwar mu tafarko taimako ne kuma tana sona tun kafin nasamu sauke mahaifin ta bakowa bani kuma tana dai karatu, atakaice dai ta cika duk Abunda nakeso ga 'ya mace!

" to Alhamdulhi,k'ande dauko masa abinci zaci mana!

" ina ai k'ande tana wata duniyar yaya haruna ne yadawo haka dan gayu!

" zungurar ta tayi..

" afirgice ya tashi to..

" kinga yi zamanki ma inada kafafuwa!

" toh ne nace maka gurgune!

" sunata hira da iya ita dai uffan batace ba chan yace k'ande kinadai zuwa makaranta? Kinga shukrata mahaddaciya ce!

" to ne mainene hadina da wata yar birni?

" to kidai dinga zuwa..

"Ai baka fine son karatun ba!

" to ne bari nagudu iya har ya fita k'ande ta rada wa iya habu akunnenta anya haruna ne kuwa?

" to haruna dawo k'ande tace bakai baniba...

" hahha to bari natuna miki wane abu kumatun ta yataba yace (k'ande tayi tsoka iya kifito ki raba) kintuna wannan tsokanar taki!

" tsayawa tayi tana kallon sa!

" oya simile mana!

" ne wallahi bana wari....


*Urs Nana diso*



http//:nanadisoo.mywapblog.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[12/19/2016, 9:52 PM] ('kubrieh cier vervier: _23-25_

*K'ANDE*

Ink'iya:-Nita Dabance!!!

*NA NANA DISO*


To haruna dawo k'ande tace bak'ai bani ba...

" hahha to bari na tuna mik'i wane abu kumatun ta ya taba yace (k'ande tayi tsoka iya kifito ki raba) k'intuna wannan tsok'anar tak'i!

" tsayawa tayi tana k'allon sa!

" oya simile mana!

" ne wallahi bana wari....

" Dariya haruna yasaka ne ba haka nacemiki kina wari ba smile shine wari, har yanzu turancin ku baiyi kwari ba!

" wane guntun tsaki taja tunda naka yayi ai sai kayi murna, tunda mu zama mukeyi agida bamu zuwa makaranta! Aikin kawai kaje kawane ibo al'adun ya hudawa, kamafi kyau da!....

" haruna ya murde mata kunne yaushe zaki nutsu ne? Ke kwata kwata bakida hankali kowacce mace nutsuwa takeyi bandak'e!!!...

" mik'ewa tayi ta dau bota, sai data saiti kofar bayi sannan tace ohhh kajeni da mutum har yaushe aka dawoma da hankalin naka? To insu 'yan birni basu sanka lokacin da kake hawa bola ba to suzo nabasu labarin k'a...

" takalmi iya habu ta cillo mata, uhm haruna kama hanya kutafi Allah ya tsareka!..

" iya habu mi'isa kande takeyi min haka, tun tana yarinya muke tare kuma babu abunda banayi mata amatsayin wa!...

" haba haruna ai k'ande ta dabance yarinya ce kadaina biye mata!..

" To iya abu ga dubu biyar kwayi cifane...

" Toh haruna nagode Allah yayi jagora!...

" Ameen iya habu agaida habu...

" k'ande tanajin tafiyar sa tafito kusa da iya habu ta zauna iya me yabaki?

" Dubu biyar yabamu..

" gaskiya iya bakya kawo wuta komai na tambaya yi kikeyi!

" Ai k'ande kamar 'ya na dauke ki...

" shiyasa nake sonki ke da baba Allah ya jikansa!

" Ameen in tambayi ki mana k'ande?

" ince dai lafiya?

" Me isa baki bi k'awonki na abuja gidansa ba? Ke da kikeson zuwa birni...

" wai kawu mahmuda kike nufi?

" eh shi...

" Tanbijan ai wannan mutumin bana zuwa gidansa indai gidansa zanje to na hakura da birnin!

" saboda me keda kikace zaki jure kowanne irin aiki indai zakiyi ilimi!...

" kuma fa hakane, Amma gaskiya iya habu kawu mahmuda bashida kirki lokacin da goggo taje gidansa mai wake wanke aka mai da'ita kuma itace take musu girke sai da yaya abbas yaje yatawo da ita...

" To ai shikenan gwara muyi zaman mu ai aure ya rabamu...

" hmmm gadai ninan sai yadda Allah yayi dani bari naje gida na dorah Abinci nadawo...

" tohm ki anson goro gurin goggo...

" iya habu idan habu yazo kice ya kaimun gyaran cocilan....

" Tohm...

Salama

" mtseww wai ke menene haka?

" me kuma nayi miki mama farida?

" haka ake shigowa gida sai kace yaro!

" Na shigo din tashi ki rufeni da duka inkin isa!

" Hannu mama farida ta saka ta wanka mata mari...

" wayoo ni kika mara?

" lafiya daga shigowar ki k'ande?

" wallahi goggo babu abunda nayi mata ta mari ne!

" wai haka farida!

" Au goyar bayanta zakiyi toh zagina tayi nagaje da rashin kunyar da takeyi min idan da na haihu ai datune inada kamarta...

" Allah ya kiyaye kizama uwata!Wallahi sai na rama!...

" Goggo ce ta hankada k'ande dak'i ke bakida hankali sa'arki ce!...

" farida tayi dariya sannan tace gwara ki koya mata hankali mutanen birni su sunada hankali...

" k'ande tace bakamar yan gidan ku ba mahauka ta ba!

" au ba zakiyi min shiru ba!...

" kuka ta saka me isa bakya sona goggo nifa yarki ce?

" goggo ce tafara kuka bawai bana sonki bani ba, ina sonki Aishatu...

" yaune rana tafarko da goggo ta taba fadar sunan k'ande....

" yanzu zakiyi nesa dani kuma bansan rayuwar da zaki shiga ba Dan haka nake tausaya miki!

" kamar yaya goggo?

" ke ta dabance, zamanki ga wayanda basu fahimce ki ba da matsala!...

" To goggo aikatau zaki kaine ne?

"A'a k'ande komai Allah yana gani na baki tarbiya daidai gwargwado kuma tarbiyya umarni ne na Allah SWA ,rashin yin ta saba wa umarnin sa ne,kamar yadda ya zo a hadisin Ibn Umar( RA) Manzon Allah S.A.W yace:"Kowannen ku makiyayi ne kuma kowanne ku za a tambaye shi game da abin kiwonsa", Dan haka kiyi hakuri kiyi juriya, banda bin kawaye banda fitina banda fitsara...

" zan kiyaye Amma idan abubuwan sukayi min yawa wallhi sai na rama!

" ni dai fatana Allah ya tsareki ya kuma kare ki...

" Ameen goggo!

" gobe ki wanke kayanki ki shiryasu jibi zaki tafi..

" Tohm bari naje nasiyo karkashi...

" k'ande tana fita ta saka dariya hanyar lambu ta huce tana zuwa ta cinko karkashe danya ta tawo gida ruwa tasaka sannan ta dama sai taga tanata yauk'i kwarawa tayi a kasa daidai dakin mama farida!

Ta samu guri ta zauna ta kwallara kara aguje farida ta fito zuuuu dimmm ta wadi!

" kande tasaka dariya sannan ta gudu...

" lafiya mama farida lafiya?

" Ta karya ne takarya ne!!!

" lah karkashin ke aka zubawa kenan?

" kunsan halin k'ande batada hakuri kudaina biye mata! Yanzu gashinan ko baki karye ba kinsha jiki...

" tunda ta tawo hanya take ta dariya auwalulu ne yaganta...

" k'ande hankalinki daya!!!

" kallon sa tayi cike da fitsara sannan tace hankali na uku dana babanku, dana babarka, da naka...

" zance ubanki...

" kadade bakaga baban naka ba shiyasa zakace sa!!!

" kinsan tsaf zan iya sumar dake...

" ka dadi baka sumar ba shiyasa...

" biyota yayi ta ruga aguje...

" iya habu nadawo!

" ba sallama?

" Assalamu Alaikum

"Wslm

"Ina cocilan din? Au habu baka kai gyara ba?

" bazan iya ba!

" zakaga bazaka iya ba yau sai dai ka kwana a kasa ko bargo bazan baka ba!

" yi hakuri kawo na kai gyaran!

" Dan kan uwa kana kallona kamar wane goruba

Please Login or Register in order to submit comment