You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tea din....

" wallahi Da matsala dan wallahi bazan kyali yarinyar nan ba sai na salwanta ta....

" mama farida tace wannan magana mara dadi mtsewww....

" kande ce tafito ta gaida su! mumy ce ta dallah mata harara, guri ta samu ta zauna...

" dady yace uwata wacce university din kikeso?

" ko kinason fita abroad ne?

" shiru tayi mumy tace abroad din lafiya 'ya'yanka ma baka kaiba sai wata banza to wallahi bazai yihuba..

" kudin ki ne kokuma akace miki ita ba yata bace ba? To nafi sonta fiye dasu firdausi...

" haruna ne ya fito cikin shiri ya gaida dady yace dady is better asamar mata admission anan...

" ku bari ta zaba da kanta kokuma kinason Abuja?

" Cikin ladabi tace duk inda kukace dady.....

" Mama farida tace ohni ko tayaya k'are ya daina haushi?

" kande tasan da'ita take sai tayi murmushi tace ai abunda bazaiyihu ba ne sai dai ya lafa badai yadaina duka ba....

" haruna ne yace dady inada calling up a america by 3 zamu tashi 3 days kawai zanyi....

" haruna babu abunda zance maka sai dai Allah yakara budi nagani jiya a jarida....

" Amen dady..

" wane dady mumy tace domin haka zasuje dadin yiwa k'ande Abunda suka tsara mata....

" mama farida tace oh ni haruna k'aki yin aure har yanzu ko mai hankali ake dubo mana ne?

" Dady yace ai an kusa....

" mumy tace nefa dady banje kana zancen na kande da isyaku ba....

" Allah sarki yaron kirki dazuma sai da muka gaisa a masallaci da Asuba...

" haruna da haushi ya turniki sa sai cewa yayi ai k'ande yarinya ce abari ta dan kara girma...

" ka jika haruna girman me? Ai nanda wata daya tana gidan sa....

" cikin murya mara sauti yace sai dai dak'ina...

" dady yace uwata ne zan fita mai zan tawo miki dashi?

" cikin murmushi tace dady agwaluma da kashu.....

" Tohm angama, wayancen iyayen sangartar suna chan suna bacci ko?

" mumy tace to baccin ma hanasu za adinga yi ne?

" mama farida tace yadai kamata....

" mumy tace ki bare ki haifa saiki yi magana...

" Dady yace aikuwa tana nan zata haifo...

" mama farida tace yauwa Alhaji na adawo lafiya katawo min da kankana....

" fruits za'asiyo miki anjima za'a kawo ma...

" yauwa mijina adawo lafiya...

" bayan fitar dady mumy tace ga kunan haka zaku kare kuna siyar soyayyar wasu da asiri....

" mama farida cikin dariya tace ai shi kansa asirin iyawa ne in baka iyaba sai dai ayita cimaka kudi...

" mumy ta nuna k'ande zakice ubanki ke k'ande zan nuna miki bambancin birni da kauye...

" Ta ba bakinta tayi ta huce dak'inta...

" haruna ne ya shigo kande?

" Naam yaya...

" ga waya nan nasiyo miki zamu dinga waya...

" cikin murna tace Da gaske?

" ya mika mata wayar to amma menene tukuici na?

" cikin murna tace Allah yabaka mace tagare...

" a'a aini nasamu...

" zaro ido tayi to wacece?

" kece mana..

" fuskarta ta rufe, Ai ne anyi min miji tuntuni...

" bata rai yayi yace banason irin zancen nan kece tawa ta har Abada...

" bakinta ta turo nifa nace maka akwai wanda nakeso....

" ke daina yimun shagwaba kar naji nayi Abunda bai dace ba...

" Cikin dariya tace menene abunda bai dace ba?

" wanne irin kallo yabita dashi kana kallonta kasan na soyayya ne...

" lokacin makaranta ya tawo bari naje na Shirya...

" To ne Natafi kiyimun addua ki kuma kara sona please....

" murmushi tayi sannan ta sake dariya sai kun dawo...

Bayan k'ande ta Dora abincin Rana wayarta ta saka a charge sannan tayi sallah tana tunanin mai yahana uncle zuwa? Haka takarasa girken ta sannan tayi shirin makaranta.....

"Lokacin data isa anyi mata duk'an makara malama hafsa ce a ajin bayan tafita malam umar ya shigo ajin....

" fatima ta kalli k'ande Nefa nagaji da tambayoyin nan da yakeyi mana....

" k'ande tace ai daga yau angama sai nan da 2weeks....

" Assalamu alaikum kamar yadda zamu cigaba acikin karatun mu na tambayoyi Tambaya ta farko zuwa ga Aisha me ake nufi da kyautata alwala?

"K'ande ce ta miki Kyautata alwala abune mai mutukar mahimmanci acikin rayuwar mu domin in alwala bata inganta ba babu ta'inda sallah zatayi, kuma ma'abota kyautata Alwala zasu samu daraja da sakamako kamar yadda mukaje acikin hadisi manzon Allah (saw) yace wanda yayi alwala ya kyautata, laifukansa suna fita daga jikinsa har su fita ta qarqashin faratunsa.... [sahih muslim 245]

" Mashaa Allah... Tambaya ta biyu itace wacce Addu'a ce akeyi yayin farkawa daga bacci?

" k'ande tace malam yayin da mutum ya farka tsakar dare ko kuma yayin da mutum ya tashi daga bacci?

" yayin da mutum ya farka tsakar dare(cikin barci)..

" k'ande tace Yazo acikin hadisi mai number 1154 wanda bukari ya rawaito, An karbo daga Ubadatu bin Assamit: Allah ya qara yarda a gareshi daga Manzon Allah SAW yace: (( Wanda ya farka cikin dare sai yace: *LÃ'ILAHA ILLALLAHI WAHDAHU LÃ SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WAHUWA ALÃ KULLI SHAI'IN QADEER.* *ALHAMDULILLAH SUB-HÃNALLAH WALLAHU AKBAR WALÃ HAULA WALÃ QUWWATA ILLÃ BILLÃH. SANNAN YACE: ALLÃHUMMA-GFIRLY* ko yayi addu'a to za'a amsa masa, in kuma ya tashi yayi sallah to za'a karbi sallarsa........

" barakallahu fiyki..Wa jazakillahu fil jannah...

" Ameen...

Anan zamu tsaya sai kunjimu Gobe...

" Fatima ta kalle k'ande lallai sannunki Aisha kina kokari fa, kuma ta yaya kike ruk'i wa yannan Addu'o'in?

" fatima kenan ai duk yawancin abunda malam umar yake tambayar mu abubuwa ne da kusan kullum yakamata ace munayi arayuwar mu ki duba kiga kamar tambayar yau akan Alwala aikinga kullum mukeyi, Da kuma tambayar addu'a yayin farkawa daga bacci wadda ya kamata aci dukkanin musulmi ya haddace ta domin falalarta...

" hakane kam tashi mu tafi....

" Tana shiga cikin gida kafarta dazata saka acikin falon taje an zuba mata bulala firdausi na faman dukanta hajiya kuwa ball takeyi da'ita...

" wayyoo Allah na menayi muku wayyo kada ku kasheni...

" ka tak'on da farida ta k'wala she yasa jini yafara zuba ajikin kande...

" Mumy tace ai saimun nakasa ki wallahi in muka koreki naga ta inda haruna ko hamza zaice yana sonki....

" firdausi tace munafuka tsinanniya riketa sukayi har gate suna zuba mata bulala cillata sukayi sannan suka rufe gate dinsu...

" baba mai gadi cikin tashin hankali yace me tayi muku....

" To munafiki cewar farida da firdausi saura muje kagayawa wane kaima haka zamuyi maka....

Suna shiga palour suka rungume mumy wooo mumyn mu munje dadi wallahi kinga yanzu su hamza sun zama namu...

" kudai ku kwantar da hankalin ku indai ina rayi zaku auresu....


" kande dake tafiya dakyar idanu wan ta sai zubda hawaye sukeyi ga jini yana wanke mata fuska tsallakawar Da zatayi sai shuuuuuuuu kikeji wane mai mota ya bugeta....

" A guje mai motar yafito yana innalillahi wa inna.......

*Urs Nana diso*


nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[1/31, 9:34 PM] ('kubrieh cier vervier: _66-69_

*K'ANDE*


Ink'iya:-Nita Dabance!!!


*NA NANA DISO*



Firdausi tace munafuka tsinanniya riketa sukayi har gate suna zuba mata bulala cillata sukayi sannan suka rufe gate dinsu...

" baba mai gadi cikin tashin hankali yace me tayi muku....

" To munafiki cewar farida da firdausi saura muje kagayawa wane kaima haka zamuyi maka....

Suna shiga palour suka rungume mumy wooo mumyn mu munje dadi wallahi kinga yanzu su hamza sun zama namu...

" kudai ku kwantar da hankalin ku indai ina rayi zaku auresu....


" kande dake tafiya dakyar idanu wan ta sai zubda hawaye sukeyi ga jini yana wanke mata fuska tsallakawar Da zatayi sai shuuuuuuuu kikeji wane mai mota ya bugeta....

" A guje mai motar yafito yana innalillahi wa inna Ilaihir raji'um, ku taimaki ne DanAllah ku taimaki ne jini jini....

" wata dattijuwa ce ta nufo gurin k'ande tana fadan subhanallahi bari na taimaka maka ka sakata a mota....

" yau Dan Allah hajiya i sauri kar ta mutu...

" cikin hanzari ta sata a gidan baya baisan lokacin da yaja motarsa ba sai jigawa directly ya nufi babban asibitin garin, Anan da nan likitoci su kayi kanta cikin tashin hankali yake fadin kuyi sauri karta mutu kuyi sauri....

" Dr usman ne yafito yace cool down dear bazata mutu ba sai time dinta yayi zamuyi iya kokarin mu....

" okay.. okay A lok'acin ya dan nawa hajiyarsa waya...hello mamee please k'izo babban Asubuti a k'wai matsala...

" Me kuma ya faru Abdul kaddai Nusaiba ce ba lafiya?

" A'a hajiya please kiyi sauri...

" Tak'e ta sak'a hijjabi, ta dauk'e key din motar ta ta nufi Asubitin, Nan ta tarar da Abdul yayi tagumi hawaye Na wanke fuskarsa....

" subhnallahi lafiya abdul? Me yafaru? Wa aka kawo nan? Dubi yadda fuskarka tayi ja saboda kuka sai kace yaro...

" Na tawo hanyar kano inata sauri sosai tsautsayi dai yasa Na buge wata yarinya...

" ya illahi ince dai da sauki?

" eh da sauki Amma kuma tana ta zubda jini....

" ka kira Nusaiba ka sanar da'ita...

" hajiya k'in manta nusaiban ne? Kinsan halinta Ne dai ki taimaka ki zauna kusa atare da'ita...

" Tohm Abdul Allah dai yabata lafiya Naji doctor ya fito shiga kaje mai zaice...

" Assalamu alaikum, ina fatan jikin dai da sauki?

" abunda muma muke fata kenan gashinan dai dr philips yana Nashi binciken, but actually kafin ka bugeta akwai alamun duka da wasu rauni ka ajikin ta harda inda aka buga mata wane Abun Akanta, ga kuma bugun da kayi mata ta k'arye akafa hannun ta kuma tasamu rauni ka....

" Na shiga uku dr yanzu yaya zanyi? Bansan taba? Ban kuma san dalilin...

" karka damu abdul we are trying our best kuma munyi mata Alurori a kallah 10 yanzu kuma ana yi mata treatment din injuries din, Nan da 2hours za'ayi mata aiki akafar Duk Abunda Nake lissafa maka 1.8million ake bukata....

" inada dr ayi mata koda sukenan kudina sai anyi mata....

" okay...!!!

" To ka tafi gida ka huta abdul 'yark'a ba ta jindadi ma...

" hajiya hutawa fa kikace? Yar mutabe fa na buge? Duk rashin imani na Ai natsaya naga ta farfado....

" hakane Abdul Amma Allah ne ya kaddaro hakan...

" yeah shine but i need to stay...

Mumy ke zaune tana Danna waya zuciyar ta ciki da murna sai murmushi kuma takeyi ringing wayarta takeyi cikin k'ankanin lokaci ta dauka hello ummi?....

" yaya momy ina fatan aiki ya cika...?

" Hahahaha Tun yaushe ai yadadi da cika kande sai dai wata munriga munyi mata illa?

" yauwa kawata har hankali na ya kwanta yarinya zata zamar mana annoba....

" Ai kande ta dabance.....

" To sai anjima yaruwa farida tasa ranta cikin ruwan sanyi hamza ya zama nata ....

" hahaga godiya muke ummi...

" Mama farida ce tashigo gidan ciki da Sallama mumy ince kande ta dura abinci?

" wane Abinci kuma ai tunda tafita bata dawo cikin gidan nan ba ballanta na adora girki....

" To Allah dai yasa lafiya dan bata yaba kaiwa dare ba inacan ina sauri dan Na taimaka mata mugama....

" hmm ni daman banfa yarda da yarinyar Nan ba ina tunanin maza take bi wallahi....

" ai wallahi bai kamata ashedi kande da wannan mugun abun ba domin kande ta dabance wallahi duk fitinarta bata bin maza....

" Dallah yimun shiru ai dangin ku daya kyafadi haka....

" Ai ita gaskiya daya ce Dan haka ko kinaso ko bakyaso kande tafi yayanki tarbiya....

" inji ubanwa?

" ai ba sai uban wani yafada ba a ma'amala ma ake gani mai tarbiya....

" kina jahilarki...

" hmm zakiga jahila ta hau samanta ta bar mumy nata zanbada masifa...

Bayan sallar isha'i dady ya shigo yanata zam badawa kande kira shiru hakan yasa ya lika dak'inta bai ganta ba ya duba dinning babu ko abinci ke mumy ke farida kufito ina kande ta shiga???

" mama farida tace wallahi Nema ina daki hankali na atashi ahaka Nabarta tana shirin islamiyya har ta tambayi ne me za'a dafa nagaya mata Amma dana dawo gida Akace batanan.....

" mumy cikin taba baki tace hankalina duk atashi run 5 yarinya bata dawo ba kardai acemin ta bata....

" wannan ai shashanci ne ko gidan kawaye bata zuwa ballantana ta dade awane gurin kuma kuna zaune amanar mutane Na karba ke farida ke firdausi dallah ku fita ku nemota....

" To dady tafiya sukeyi suna dariya ko'ina zamu ganta oho masa...

" kyaleshi dallah zomuje musha ice cream...

" da dai yafi!!!...

" dady ke faman zagaye a palour ya kasa zama mama farida ce tace Alhaji kazo kace Abincin Nagama maka!

" wane abinci??

" Alhaji ka kwantar da hankalin ka babu inda tashiga ba wayasani ko tatafi kauye?

" ta ina hankalina zai kwanta uwata ta bata ke duba kiga girken ma kasa yi kukayi ita kuwa bata gajiya kunaso Nashiga cikin tension dayawa ne? Kuma bazata taba tafiya bata sanar dani ba ina zuwa....

" ohh ni yarnan ko ina kande tafada?

" baba mai gadine ya tawo aguje Alhaji gani...

" nasan kaga fitar kande kuma kaga shigowarta bayan ta shigo takara fitane?

" a'a (sai kuma ya tuna zancen firdausi akan zata yan k'ashi indai ya sanar da wani) Alhaji bansan komai ba kayarda dani bansan komai ba...

" Ka ganta tafita dai ko? Kuma kaga dawowarta?

" eh nagani Amma daga nan bansan Abunda ya faruba.....

" bakomai koda wane yayimun karya kai bazakayi min ba shekarar mu 40 tare kasanni nasanka tsoron Allahn ka yasa muke zaune da gaskiyar ka, Amma katashi kaje bari natafi gurin yan sanda....

" haka dady ya dinga tambayar mutane Amma kowa ya tambaya sai ya sanar dashi bai ganta ba directly ya sanar da d.p.o Nan aka fara bincike....

" sannu Alhaji dama hakura kukayi yanzu su farida suka dawo da kuka basu ganta ba...

" Nasanar da hukuma kuma gobe zanje kauye....

" Sai kadawo...

" Sai k'i k'oma dak'ink'i ina buk'atar hutu....

" haba dady Akan wannan yar iskar yarinyar?

" zaki fita ko sainaci mutuncin ki?

" in banda babu aure tsakanin ka da kande da sai naci aurenta kakeso kayi...

" Allah ya shirye ki....

Jigawa

Babu yarda mame batayi da abdul ba akan yatafi gidansa Amma yaki daga karshe ma dak'in da aka kwantar da kande ya shiga ya zauna a gaban gadon ta kallon fuskarta kawai yakeyi duk da rauni ya cika fuskarta Amma tayi masa kyau cikin sanyin murya yace mame kalleta da kyau yarinya ce ma.....

" Na ganta abdul kakwantar da hankalin ka zata tashi inshaa Allah...

" yanzu mamee in taga karayar kafarta yazatayi?

" haba Abdul Ai komai kaddara ne kai dai kasa hakuri....

" Nusaiba ke faman kiransa yana rejecting daga karshe ya kashe wayar .....

" yanzu abdul bazaka koma gun matarka ba? Kabarta cikin tunani da fargaba zan kula da yarinyar nan....

" please kikalleta koina ciwo ga karaya dan banida tausayi sai na tafi nabarta haba mamee....

" Toh ai shikenan...


Abuja

Washe gari abi yana zaune kusa da hamza yace ko kaifa son har kafara kyau nace kasa aranka kasamu Aisha...

" ummi ce tayi dariya tace Ah haba su kande manya faridan fa?

" ke bari kije abunda d'ana yakeso shi zanyi masa kuma tunda yace kande yakeso i will makesure ta zama tasa...

" hamza ne yayi hugging din Abi budar bakinsa yace that's my Dad kande ce kadai matar da rayuwata zata cigaba inna rasata kun rasani nasan nazama mahaukaci akan soyayya my new company will be Aishham....


" ummi dataje wane malolo acikin ranta sai cewa tayi wai kai baka kishin ka aure talaka wacce ba class dinka ba?

" haba ummita Ai class shine Addini talauci kuwa sanin yakamata ne ina sonta overrr.....

" Abi ya kalli ummi ke bakije dadi da kikaga son yana walwala ba? Dubi har wane haske yayi...

" Tayi tsake sai ayi Nagani....

" cikin mintuna abi ya kirawo dady Awaya bayan sun gaisa yace Ai magana nake da'ita dakai Akan kande .....

" kirjensa ne ya buga sannan yace zan kirawo ka yanzu ina aiki....

" Abi ne ya juya wayar hannunsa tare da fadin anya lafiya?

" me yafaru Abi?

" Hamza Akwai matsala agidan dady dan kowa har muryarsa ta chanja...

" Gobe zanje ai....


Kauye..

Dady ke driving cikin kauyen dakyar ya karasa cikin unguwar Nan ya fada gidan goggo maraba tayi masa sannan ta bashi guri.....

" Anya lafiya naganka abe jajan?

" tukunna ina kande goggo?

" kamar yaya ina kande ita tace maka zatazo nan?

" innalilahi yake fada sannan ya ajiye modar ruwan Abbas jika duba min gidan iya habu....

" goggo dake faman salallame wannan yarinya ina ta shiga taje tayi muku halin nata ko?

" ke kwantar da hankalinki goggo bakomai...

" iya habu ce tashigo tana fadin wane irin banzan zance ne wannan?

" goggo ce ta zaunar da'ita...

" Nan yabasu labarin duk abunda yasani har yan sanda da'aka sanar....

" iya habu tace jakar uban nan ai wallahi hassan baka isa ba, ko tsoron amana bakwayi? Yarinyar nan batason rabuwa damu amma saboda tayi karatu tatafi, yanzu matanka sun batar da'ita shine zaka lallabo kanayi mana dadin baki?

" haba iya matanah fa kikace?

" ko bakasan nasan labarin gidan naka bani ta dafa muku tagyara muku ta kuma wanke muku ga bak'in wulakanci shine bai ishesu ba sai da takaisu da ta gayyarata....

" goggo ce tace to Allah ya bayyanata...

" iya tace yimun shiru malama tashi kaje kanemo min kande kafin na hadaku da hukuma....

" goggo tace haba iya menene nasa hukuma acikin harkar nan kuma??

" hassan zaka tashi kokuwa sai nayi maka na matan jiya?

" zan nemota inshaa Allah..

" Ai zama gidanka yakare ta dawo hannuna zanyi iya kar kokarina Nadinga biya mata karatun....

" Nan Ali yasa baki da fadin munanan halin kande tsaf zata iya guduwa....

" iya habu tace kai Aliyu kace gyatumarka ba ga uwar ba ba ga yayanba...

" Nan dady ya nufo hanyar kano jiki babu Dadi yadda yaga in kulawar mumy ya tabbatar akwai matsala fa mama farida kuwa duk rashin jitowarsu da kande yabonta takeyi tana fadin Allah ya jifata hannun nagare....

" dady yakance Amin har yaje dadin Addu'ar....

Tunda firdausi taje yau haruna zai dawo tasa akayi masa lafiyayyun abinci taci kwalliya tasha turare...


Jigawa

A hankali cikin wane radadin azaba da kande takeji ta bude idonta da yayi jajir...

" Abdul ne yayi wata hamdala tare da fadin sannu sannu dr ta tashi kuzo ta tashi...

" kallon dak'in tayi tsaf sai kuma hawaye yafara wanke mata fuska...

" Abdul cikin tsoro yace kiyi hakuri DanAllah wallahi tsautsayi yasa na bugeki har kafarki ta karye....

" a lokacin ta kalle kafarta ta sai kuka bakomai take tunawa ba sai su momy sune sanadin faruwar haka gareta indai har tacika 'ya bazata koma gidan ba kuma ta hakura da haruna har Abada....

" Nan dr yazo yakara yimata alurar bacci

Please Login or Register in order to submit comment