You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya



Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku





This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC

those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

__ Compiled By Kausar Salis Aglan Nissa.

               



RUGAR SAJE



    By Nusaiba Ayuba Suleiman



*FITATTU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



     Wattpad@nusysa.

IG@Nusaiba A.S. Sarkin zango.



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_

     _01_



"Mairoji...Mairoji...wallahi ki fita daga ido na na rufe, bana san wannan sakalcin na ki, na banza da wofi, banda iskanci kaf rugar nan wa kika ga yabar 'diyarsa mace tana wani karatun boko?banda Allah ya rufa miki asiri, kinyi karamar sakandari, da tuni ba kina da yara biyu ko uku ba....?"



    Shiru matar tayi tana kallon Mairojin da takewa fada, sai tura baki take, tana matsar kwalla, kwafa tayi cike da takaici tace "ai wallahi bari Baffanki Jauro yazo, mu hadu muje mu samu Hamma Gid'ad'o ayi maganar aurenki da Na-makandi sarkin kasuwa tunda daman ya dade yana bid'a".



     Kuka ta fashe dashi cike da kuruciya tace" ni wallahi Goggoji bana son wannan sarkin kasuwan, ni da nayi karatun boko sai ahadani da wanda baiyi ba, ni mijin da zan aura abirni yake, kuma zaizo ya aure ni ya tafi dani".

   Karan dake gofe Goggoji ta d'auka da maka mata, cike da takaicin ta tace"inshaAllahu ba zaki kuma cin laraba agidanna ba, saba'ar watannan zamu aurar dake mu huta, kafaffiya yar Allah bani".

   Baki ta tura ta nufi soro tana kunkuni.



   Abakin kofar soron ta ci karo da Mamuda, baya taja tana kauda kanta daga garesa, dan wani dan banzan wari yake kamar me, shi kuwa kallonta yake tun daga sama har kasa, wani yawu ya hadiya da kyar yana jin yanda ko ina na jikinsa yake amsawa, kawai ganita da yai ma ya wadatar ba sai ya shiga cikiba, daman ita yazo gani kuma ya gantan.



   Rab'awa tayi ta gefensa zata wuce, yai sauri kamo hannunta yana tsareta da idonsa masu cike da kayan maye, kokarin fuzgewa take amman ya hana ta, cikin wata irin murya ta rikakkun yan iskan gari ya ce"Merota...kina gudu na ni kuma ina binki ko.....uhmmmm alkur'an ki kuka da kanki duk ranar da aka bani ke matsayin matata, kai......wuhuhuuuu....ranar za'a ga yanda ake kodimo, araddun Allah saina fanshe duk wata tijara da kike min Mero"



  Ya karashe maganar yana wani rausayar dakai, cike da takaicinsa ta fuzge hannunta da karfi ta fice tana murguda mai baki, gidan su Ta-alhaji ta nufa daman nanne wajen yawonta sai ko gidan Yaddiko Tako, yar babarta.



    Da yamma tayi Baffa Jauro yazo, nan suka zanta yanda abu zai kasance, amman sun bar maganar atsakaninsu, idan Namakandin ya turo iyayensa to sai ai magana, idan kuma bai turo ba sai ahadata da Mamuda, tunda daman ai irin abunnan za suyi, irin gida bai koshi ba , za'a bawa dawa.



++++++++



      Kofin dake hannunsa Ahmad ya kalla, har kusan mintuna goma da hada coffe din amman har yanzu bai kai bakinsa ba, kafadarsa ya dafa cikin taushin murya da tarin kaunar da yake wa 'kanin nasa yace"Malik...." dagowa yai ya kalli yayan nasa, sannan ya kuma mayar da kansa kasa.

   "Me yake damunka? akwai matsala ne?".

     Kansa ya girgiza yana sauke ajiyar zuciya, ahankali yace" hakanan gabana faduwa yake, sai nake jin kama wani abu zai faru a Rugar Saje, tun safe nake jin wannan sabon yanayin".

   Tapping bayansa Ahmad yayi cikin dauriya yace masa"is ok....ba abunda zai faru sai alkhairi, kayi addu a kaji".

    "But broh...you know that ina da ajiya acan ko....if something....." bai karasa ba Ahmad ya janyo sa jikinsa ya dan rungume, cikin muryar rarrashi yace"i know......but inshaAllahu ba abin da zai faru, tashi mu je ka watsa ruwa, ka samu kai barci".

    Da kyar ya lallabasa suke wuve bangarensu, da kansa ya hada masa ruwan wankan mai zafi dan yanayin na sanyi ne, zuwa yai ya taimaka masa ya rage kayan jikinsa ya rakasa har bakin bandakin ya shiga, shi kuma ya dawo ya fara duba masa kayan da zai sa.



++++++++



       `Dare mahutar bawa`haka masu iya magana suka ce, awannan daren kowa ya kudundune acikn abin rufa, kasancewar lokacin sanyi ne, Mairoji tana bayan Goggoji sai sharar baccinta take cike da jin dadi.



Hayaniyar jama'ar ne ya farkar dasu daga barcin da suke, hayakin da suka gani da kaurin daya ke tashi ne, yasa suka farga da abinda ke faruwa, da sauri suka fito jin maganar mutane akusa da bukkarsu, salati suka dauka gaba daya ganin bukkar kusa dasu ta kama da wuta, kafin kace me....kusan bukkokin dake cikin rugar duk sun kama da wuta, nan danan kowa ya fara gudun ceton rai,(fadan yan bindiga dadi) ba wanda ya kula da wanda yake bi, sai da suka kusa danganawa da bakin titi sannan aka kula da Mairoji ba bu ita.

Kuka Goggoji tasa, ta dora hannu aka, wasu matasa aka samu, tare da Mamuda suka koma, kusan awa biyu sannan suka dawo, babu ita, sai bakin labarin kwashe musu shanaye da kad'a garke da kuma kona ruggar da akayi.



Sosai Goggoji take kuka, dan ta rabu da Safiya ne, shekara goma sha hudu, gashi yar data bari itama ta yi batan dawo.

_zanga kamun ludayinku ne, sai kuma jan hankali, dan Allah idan kinsan nan gaba zaki kalubalanceni akan littafinnan to kiyi hakuri kar ki karanta, dan wllh naji abin da bai min ba, tsab zan ajiye rubutun, tunda ba wani ya sani ba, ra'ayin kaina ne, dan nan gaba zai iya zuwa wajen da bazai muku dadi ba, to dan Allah ki karanta kawai ki karfafamin gwuiwa, ko kimin gyara ko jan hankali, amman idan kika zagen ko, kika fadan ba dadi, tabbas baki yasan mai ya fada amman baisan me za'a mayarmai ba, to dan Allah mu karu da juna kawai.=ØOÞ_

   Maman Mu'ayyad



     *RUGAR SAJE*



    BY Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



  _02_

Kuka goggoji take yi kamar ranta zai futa, fadi take"shikenan mairota, shikenan kema kin yi nesa dani, na rasa Safiyya kema gashi na rasa ki, ya Allah duk inda Mairoji take ka zama gatanta, Ya Allah ga baiwarka nan ka tallafi rayuwarta aduk inda ta shiga, kasa ta fada hannu na gari".



   Kowa dake wajen amsawa yake da ameen, masu kuka nayi da kuma masu matsar kwalla.

    Da haka suka karasa daya Rugar dake gaba dasu sosai, duk da ba tada yalwar mutane, kuma bukkokin ciki ba sufi goma ba, *Rugar Na ma'u* sunan rugar kenan, gidan Haj Tako suka nufa dan ita ce gidanta yake da dakunan kasa har uku da kuma shafaffen siminti atsakar gidan, sai bukkoki hudu da rumbu biyu agefe guda.

   Sallama sukai suka shiga iya matan da suka tsira, mazan kuma suka tsaya daga waje, da magagin barci a idonta ta fito tana tambayar waye da yar rocilan ta ahannu, gani Goggoji yasa ta wattsake cike da fargaba tace"Goggoji lfy kuwan awannan dare, ince dai ba farmaki aka kawo muku ba?".



Ta fada tana kallon matan dake tare da ita, wanda yawanci duk danginsu ne, da matan yan uwansu maza.

    Kuka Goggoji ta fashe da shi daman kadan take jira, cikin tashin hankali Tako ta matso wajenta tana tambayarta me ya faru, wata acikin matan Baffa Jauro, mai suna Laraba ita tayi mata bayani da kuma rasa Mairoji da akayi.

    Zaman dabaro Tako tayi tana salatin daya d'au hankalin yaranta dake bacci da kuma mijinta, fitowa sukayi suna tambayar meya faru, nan aka fada musu, kuka Ummilo ta saka dan kawar Mairoji ce sosai, Laure kam tabe baki tayi aranta tace 'watakil ma ita ta bisu, wannan mai idon atsakar ka din ', da kyar aka rarrashe su, sannan akayiwa mazan magana suka shigo, dakunan nan na kasa guda biyu aka basu suka duru aciki matan kuma, suka shiga bukkokin, da haka atakure aka kai asubahi, dukda cewa ba wanda ya samu barci acikinsu sai yara kanana.



    Washe gari da safe kusan kafafen yada labarai sunyi kasuwa da sammakon sanarwar yan bindiga dad'i sun tashi wata Ruga da ke jigawa, bayan sun kad'a garken shanaye dana sauran kiwo, sannan sunyi gaba da yan mata uku daga ciki.

   

    Hankali tashe Alhaji Badan ya shigo gidansa yana sab'a malun malun, idan ka gansa zakayi zatan cewa akai ga gawar babarsa nan, tsabar yanda fuskarsa tayi kutukut da tashin hankali, da Ahmad suka fara cin karo, yai saurin kama hannunsa ya jashi xuwa falonsa, da kyar ya iya daurewa yaima sa bayani, shi ma hankalinsa kamar yaso yafi na uban tashi, yace "amman Abbah karmu bari Malik ya sani, wllh zai iya tashin garinnan baki daya, daman tun jiya yake cemin gabansa na faduwa kamar akwai abinda zai faru a Rugar Saje , yanzu kam idan yaji wannan bakin labarin ba makawa sai hankalin kowa dake garinnan ya tas....." kasa karasawa yai ganin kallon cikin idon da Malik din ke masa, da alama ya dade awajen kuma yaji duk abinda suka fada, bai musu magana ba sai barin falon dayai ya fita waje, kallon Ahmad Abbah yayi bakinsa na rawa yace"yaji mai muka ce....Ahmad yaji fa, shikenan ni kuma tawa kaddarar kenan".



   Da sauri suka bi bayansa, sai dai basu same sa ba, amman sun samu tsarabar karan motarsa ya fita daga gidan da shegen gudu, hankalin Abbah ya gama tashi, shima mota ya nufa Ahmad ya bi bayansa, suka rufawa Malik baya, sai dai basu ga ma alamarsa ba ko kadan, kai tsaye Jahun suka nufa dan anan yankin da rugga ge suke.



++++++

    Yana sharara gudu yana zancen zuci, wai anyi gaba da Mairoji? shifa ganin abun yake wasa, sai kace wata yar bebin wasan yara, wayarsa ya janyo ya fara laluben number din cp, bugu biyu ya dauka yana tsokanarsa kamar yanda suka saba, bai kulasa ba har ya gama dan kansa , ajiyar zuciya ya sauke yace"ba maganar wasa ce tasa ni kira ba friend, ina cikin matsala, kaji labarin harin da aka kai, Rugar Saje ai?".



    Da sauri Cp ya ce "ofcorse ina da labari yanzu hakama muna cikin Rugar da tsirarrun mutanen da auka tsira, kasan mutanen nan sunyi ta'adi da yawa, dan harda gawar mutane kusan goma muka tarar, banda k'ona musu muhalli da akayi, ai wadannan mutanen...." bai karasa ba Malik ya tsaidashi dan Cp kam badai zuba ba.



    "Shikenan....nima ina hanya, innazo zamu tattauna".

Bai jira cewarsa ba ya gintse wayar, mintuna talatin ya karasa, gefe suka koma da Cp din yamai bayanin komai, abun ya saka Cp acikin rudani, jin cewa harda wai kanwar Malik din acikin yan matan da aka dauke su uku, nan ya kwantar mai da hankali tare da mai alkawarin zasu zage dantse, suyi iya bakin kokarin su dan ganin an kwato su, tunda su ba yan garkuwa bane balle su jirayi lokacin da zasu bukaci kudin fansa.

    Sunan tsaye har su Abbah suka karaso, bayan sun gaisa ne Cp da kansa ya kumai wa su Abbah karin bayani tare da kwantar musu da hankali, daganan yai musu sallama ya tafi, daman kuma abindayasa yazo dan Malik ne dake matsayin abokinsa, yasan nan Rugar itace tushen iyayensa da shi kansa, shiyasa yamai karar zuwa,banda haka da ba zaizo ba sai dai ya bada umarnin ayi duk abin daya dace.





++++++





Kallonsu yake yi, ad'age daya bayan daya akan bad'ejo idonsa ya sauka, kallon wani yaronsa yayi ya mai alama da ido sannan ya shiga, dan d'akin tanti da sukayi inda nan suke kwana.

Kama hannun bad'ejo akayi suka turata d'akin suna daga waje, sunyiwa tantin 'kawanya.



Kuka tasa tana kare jikinta dan babu wani suturar arziqi ajikinta, kukan da take ne yasa su Mairoji dake waje suma suka sa kukan, dan ko ba'a fada musu ba sunsan me za'ai mata aciki, tsawar da aka daka musu ce tasa suka yi gum da bakinsu sai kukan zuci da suke yi.



Jin ihun Bad'ejon da magiyar da take ne yasa suka kuma sakin wani kukan, suka kankame juna ita da d'ayar dako sunan juna basu sani ba, su kuwan masu gadin banda dariyar k'eta da mugunta ba abinda sukeyi, sai bayan wasu lokuta sannan aka wurgota waje, tairararta da gudu Mairoji tayi kanta ta lulluba mata hijabin dake hannunta, basu hanata ba masu gadin, saima dauke kai da sukayi.



Garin kamar babu alamar numfashi atare da ita yasa Mairoji ta fara neman inda zataga ruwa, ko takan shi ovan daya fito daga tantin yana kallon karfin halintama ba ta biba, da kyar ta samo ruwan ta shafa mata, wani gwauron numfashi Bad'ejon ta sauke, tana fashewa da wani kukan tana kankame jikinta.



Kallon garadan Mairoji tayi cikin dakiyar da ita kanta batasan tana dashi ba ta ce"sai ku hadamin ruwan zafi ai, tunda kun zama sitarus"



Kallon ogan su sukayi shi kuma ya gyad'a musu kai,nan da nan kuwan suka hura wuta suka hau dafa ruwa, ta sowa tayi ta tsaya gaban ogan, cike da tsiwa da rashin tsoro tace"wllh kaji katuwar kunya, 'yar cikinka ka haikewa ba tausayi bare imani, to ka rubuta ka ajiye ita wadda ka ketawa haddin inshaAllahu sai ta zamai ma karfen k'afa, kuma zaka ce na fada maka".



Dariya yasa yana shafa kasumbar da tamai dashi tamkar wani dan bunsuru, kafe ta yayi da ido yace "gaskiya kin burgeni yarinya, jarumtarki tayi min dole na na reneki na tsawon wani lokaci, nasan kafin cikar shekara uku mai kyau, Allah kadai yasan kayan dazan mora anan".



Maida hankalinsa yai kan yaransa cikin daga murya yace" daga yau wannan yarinyar ta zama sarauniyar wannan yankin, duk wanya ya kuma daga kai ya i matan kallon daban yarda dashi ba, zan cire mai idanuwa ne, kuma albarkacinta yasa daga yau an daina cin ko wane irin abinci sai wanda ta zaba, so nake nanda shekara uku na mori abata, ina fatan kun gane?".



Had'a baki sukai wajen furta "mun gane oga, Allah ya taimaki sarauniyar yanki, uwar dakinmu mallakin ogan mu".







Tsawon kwana uku ita ke kula da Bad'ejo, sosai take bata kulawa duk da wani abin ba sanin kansa tayi ba, amman hakan baisbaisa ta kalli karancin shekarunta ba, ta maida hankalin ta wajen kula da Bad'ejon.





++++

Acan Rugar Na ma'u kam, Goggoji sosai take jin jikin rashin Mairoji, am baza malamai amasallatai da almajirai dan auyi addua, gefe daya kuma jami'an tsaro sun dukufa qajen ganin an dakile wannan ta'asa da yan bindiga dadi suke yi.



Abangaren Malik ma ba bu yanda Mamah da Abbah basuyi ba ya koma bakin aikinsa amman yaki, gashi an shiga kakar wasanni na yankin Europ, watanni biyar ya rage musu su fara UEFA EUROP, kuma dole suna bukatar kwararren tirenin kafin lkcn.



Ahmad ne kadai mai zaman bata lokacin wajen ya lallabashi ya koma, dakyar ya yarda zai tafi, amman duk karshen wata zaina zuwa dan ganinmeke tafiya.



Mmn Mu'ayyad.



*RUGAR SAJE*



    By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S. Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ* 



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_

      _3_

Kwanan su Mairoji shida mutanen nan suka kuma daukesu sukayi gaba dasu,can yankin maiduguri suka yada zango, amman cikin unguwar umalare, sai dai wannan karon gidane babba mai dakuna kusai bakwai, iya su kadaine aciki sai ko yaransa da suka rarrabu.



     Kullum banda kuka babu abin da suke yi, sun rokesu akan su maida su ga ahalinsu, amman sai ogan yayi dariya kawai, yace "ai mun gamu kenan, ku da danginku sai dai alahira, nan da shekara uku zaki zama matata, bayan wata tara kuma ki haifa mi yaro, dan an miji nake so ahaihuwar farko, wanda zai gaje ni, dan haka ku fitar da ran komawa wannan kazamar Rugar taku".



    Gaba daya dariya yaransa suka sa, suna nuna su Mairoji , wani kallo ogan ya musu nan danan sukayi shiru kowa ya koma bakin aikinsa, ahaka suke rayuwa kamar wasu marasa gata, kusan wata guda kenan Bad'ejo na fama da kanta, tun lokacin da abun ya faru take halin cuta,  sunyi tunanin rashin lafiya ne dako wace mace takeyi yayinda aka karbi budurcinta, sai dai ganin abun bana kare bane Mairoji da take ganin kanta wayayya acikinsu, tunda tayi karamar sakandire tuni tsohon karatun da aka dan taba ya motsa.



    Matsowa tayi kusa da Bad'ejon tace " ha...mu gani".

   Ba musu kuwan ta bude bakinta, nan Mairojin ta gama dube duben ta sannan tace ta rufe, idan ta ta dan bude ta duba gefe da gefe sannan ta tashi tana kallon oga daya fito daga bandaki, tabe baki tayi tace "malam sai ka fara tanadin kayan yaro da kuma ragon suna, da abin da za'a ci, da wallahi inta sauka lfy sai munyi taron suna".



    Kallon rashin fahimta yayi mata ya dauke kai, har zai shiga daki kuma sai ya juyo yace" wai dani kike...?"



Cike da turawa mutum haushi tace "ah...ah, da inuwarka nake".



   Murmushi yayi kawai ya shige daki, dan yanzu shi kam, wata irin soyayyarta ke dawainiya dashi.



    Kallonta bad'ejo tayi ta sa kuka tace " dan Allah Mairoji ke taimakan na zubda cikinnan, wallahi idan na koma da dan shege ruga kema kinsan kashe ni za'ai, ki taimaka karna haifi abinda zai zo ya zaman kalu bale ga rayiwata".



    Tsugunnawa Mairoji tayi tadan rungumo kanta, tana shafa bayanta alamar rarrashi, cikin kwantar da murya tace"kar ki damu bad'ejo muna tare dake, ba za'a zubar da cikinba dole.ne ki haifesa, sai dan da za'a haifa ya zame musu babban kalubale ga rayuwarsu, insha Allah ba bu wanda zai miki koda banxan kallo, bare yai tunanin cutar dake idan muka koma Ruga".



   Da kyar dai ta rarrasheta ita da salme dayar abokiyar tasu.



++++

   



     Da d'an sassarfa ya karaso wajen kujerun da aka ajiye dan hutawa, robar ruwa ya dauka ya kafa wa bakinsa, bai sauke ba sai da ya shanye shi tas, sannan yadau wani dan towel yana tsane dan gumin daya dan tsattsafo mai.

   Kallonsa k2 yayi cikin shakiyanci yace, "ya dai man.....ka fara tunanin wasan ne, naga sai zabgewa kake, ko dai aljanar take ce ta kawo maka ziyara take tsotseka ne bamu sani ba".



   Tsaki Malik yayi ya tashi ma yabar wajen yaci gaba da zagayen da yake, dariya k2 da sauran abokan wasansu suka sa masa, Kamal yace " kai guys ku dena dariya fa, gaskiya ku kula da MBM yana cikin damuwa, duk da bai damu da magana ba amman yanayinsa kadai ya nuna yana da damuwa, kune abokansa na jiki ku zaku fuskancesa ku gane mai yake damunsa".



      Shiru K2 yayi yana nazarin abinda Kamal ya fada, tashi yai ya bi bayan Malik din suna gewaye cikin sassarfa amman K2 yana kule dashi, tabbas yaga yana cikin damuwa amman yasan halinsa bazai taba fada masa ba, har yamma suna atisayen kafin kowa ya kama gabansa, kwanan biyar ya rage musu zasu fara karamin wasa, da kungiyar Bounmuth.





+++



Ayanzu kam su Mairoji har sun fara sabawa da zaman Maiduguri, duk da basu taba futaba tunda suka zo, kusan wata biyu kenan, ga laulayi da ya sako Bad'ejo agaba, kamar ba zata kai ba, da haka suke rayuwarsu cike da takura, duk dama ba bu wani abu da ake musu na rashin kyautatawa.



Yau garin sun tashi da fargabar wai wasu yan bindiga sun shigo, tun daren jiya oga suka fita shi da yaransa, sai suka kulle gidan ta waje, to basu kwanan agida ba har gari ya waye, wajen goma na safe aka fara harbe harbe, ga karar tashin boma bomai daya karade unguwanni, kuka Bad'ejo tasaka ta kamo hannun Mairoji tace mata"dan Allah karki bari wani abu ya same mu, kiyi wani abun kina jin mutane unguwa sai gudu suke, amman mu an kulle mu acikin gida, ina da buri akan wannan cikin na jikina, so nake ya zame min makamin da zan yaki wannan azzalumin dashi, ki taimaka mana mu bar nan dan Allah".



Ita kanta Mairojin duk dauriyar sai gashi tasa kuka, ta tabbata yau kam tasu ta kare, dan babu makawa mutuwa zasuyi awannan gidan.



Tashi tayi tana bin gidan da kallo cike da nazari, ta cen wajen bandaki katangar ba tada tsayi sosai, sai bata san ta cen baya ba kuma ya take, tsanin dake jingine agefe ta fara kokarin dauka sai dai yafi karfinta, hakan yasa ta kira Salme ta taimaka mata suka daga shi, suka jingina shi, sai data fara lekawa ta ga yanda tsahon katangar take ta baya sannan ta sauko, Salme tace ta fara hawa ta dira, sannan Bad'ejo sai ita ta karshe, ganin mata da yara na gudu kawai suma sai suka shiga cikinsu.



Tun hantsi suke gudun ceton rai, basu yada zango ba sai kusan la'asar, lokacin sun bar cikin gari sun shiga jeji, ga k'ayoyi da suka taka, dan Mairoji ma jin babban dan yatsanta take kamar ba'a jikinta yake ba, sai da suka tabbatar da sun tsira sannan suka zazzauna ajikin wani dutse, ban da kishi

Please Login or Register in order to submit comment