You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mamah take tambayarta meya faru, kukan ta fashe dashi, duk sun rude sai tambayarta suke, ita Maryam har tana duba jikin Sultana ko wani abu ne ya samu yarinyar, sai da tayi kuka mai isarta sannan ta kalli Mamah tace,

"Dan Allah Mamah mu tashi tsaye akan mazan gidan nan, ban san wacce annoba ce ta kunno mana kai ba, Mamah muna cikin tsaka mai wuya, tun ranar da aka kawo Laura ban kuma ganin idon Ahmad ba har yau, sai dai naji fitarsa da dawowarsa, idan naje bangarensa kuma ba za'a buden ba balle na shiga na gansa, ga Malik shi kuma yanzu matarsa tasashi agaba wai sun tafi, Mamah wannan wacce irin kaddara ce tayi mana sallama acikin gidan nan, ya zamuyi?."

Kuka ta kuma fashewa dashi, daga ji kasan daga kasan zuciyarta yake, kuma abun na matukar damunta, ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana dan satar kallon Mairoji, sannan ta kalli khausar din tace,

"To kuma meye abun kuka anan Fateema, ki kwantar da hankalinki, duk rintsi duk tsiya da tsiyatsiya rabo ya gifta tasakaninki da Ahmad, ko yaki ko yaso dole dai ku nashi ne idan ma bai kula dake ba, dole ne ya kula da yarinyarsa, kuma komai nisan jifa dole kasa dawo, yanda kika zo kina kukan na, insha Allahu wata rana zaki zo kina dariya, da farin cikin ki dage da addua, kinji karki sa abun aranki, kinga shayarwa kike, dan Allah kar ki dorawa kanki damuwa da tunani kinji yarinyata, ki bar kowa da Allah, shi ne kadai zai.miki magani ya kawo mana mafuta akan lamarin."



Da kalamai masu dadi da nasiha ta samu ta kwantarwa da Khausar dun hankali, sai dai duk yanda suka so ayi zanyi Malik ki tayi, haka suka hakura, sukaci gaba da shirarsu, sai dai Maryam bata tofa ko uffan sai binsu kawai take da ido.





***

Bayan wata uku,cikin Mairoji ya fito sosai, sai dai yayi wani irin girma, watansa shida, amman da ka ganta zaka zzata ta shiga watan haihuwarta ne, kulawa kam tana samu daga ko wanne bangare, duk sati Daddyn Yusra, wato babanta yana zuwa kawo mata rubutu duk ran juma'a, ga malam saje da shima ko yaushe yan mata rubutun baki, domin duk wanda yaga yanda cikin yai girma sai ya tanka, Goggoji taso ta zauna bangarenta, amman Mamah taki dan itama Goggojin tana bukatar mai kula da ita, dan ta manyanta sosai ga matsalar kafa da take fama da ita.

Uncle Malik ya samu aikin koyarwa da wata makaranta akasar Egypt ta hanyar wani malamin makarantar abokinsa ne tare suka dau karatu asaudiyya dashi , cikin abun da baifi wata ba ya gama komai na tafiya, hatta karatun yaransa ma can zai koma, haka ma Mairoji ya karba mata transfer zuwa can, ranar wata talata kuwa suka daga, sai dai banda Mairoji da sai ta haihu tukun zataje ta fara nata.





***

Yana kishingide afalonsa yana murza tabarsa acikin wata yar farar takarda, wayarsa dake gefe tayi kara, dagawa yayi ya saka ta a amsa kuwwa, tare da yin sallama, adaya bangaren aka amsa sannan ya fara magana,

"Ranka ya dade, abubuwa fa sai cabewa suke, bawan Allahn nan abun yamai yawa dan yanzu takai ko wajen buga kwallo bai fiya zuwa ba sai an taki babbar sa'a, gashi yanzu wannan abokin nasa ma ya dawo gidan da zama, wllh abun ya kazanta, yallabai ina tausayawa halin da Malik yake ciki, yana cikin jarrabawa."



Iska ya fesar asannan cikin nitsattsiyar murya yace"Gimba, kuna bashi ruwan rubutun nan kuwa?."



"Eh ranka ya dade, har kamfanin da suke buga masa ruwa naje na samu shugaban wajen na masa bayanin yanda muke son abun ya kasance, to da yake ma na sakar masa kudi sosai, shi ne muke kai rubutun saisu hada da ruwan su buga masa nasa daban akawo masa, kuma na tabbata yana sha, tunda babu wanda zai gane ba normal ruwa bane."

Kai ya gyada kamar yana ganisa yace"yayi kuci gaba da kokarinku anan, nima zan sabunta nawa aikin, nida nayi wayo gari gari, jeji jeji babu irin kalar asirin da ban sani, da kuma magungunan karyawa, tun ran daurin auren dan uwansa na gane an jefesa da bakin sihiri, amatsayina na dan uwansa, kuma wanda ya auremin wadda nafnafiso arayuwa, zan taimaka masa, badan shiba sai dan Allah da kuma darajar Maryam, ku ci gaba da aikinku , kuma ka kuma samin ido akan wannan Khabir Khan din."



Daga can bangare ya amsa da "an gama ranka ya dade, Allah ya bada nasara".

Amsawa yai da ameen sannan ya kashe wayar ya fada wani nazari, badan kar abun ya zamo tashin hankali ba, da zai samu Hajja Yargana da zancen, akan su karya asirin da suka sa akawa Malik din, shi kuma zai rufa musu asiri, amman zai kyale su ne har sanda asirin zai karye da kansa, sannan sai su gane cewa yana sane da duk wani kullinsu, idan ta kama ya toni asirin ma sai ya tona.





**

" Gid'ad'o, mai kake nufi dani ne, me hoton Ummie yake yi awayarka, kar dai kace min amanata kake ci?."



Kallon wayarsa dake hannunta yayi ya dauke kai yana Allah wadai da wannan halin a Salma, sai shegen bincike awaya wai ita lallai bata son ganin hotunan yan mata awayarsa, zuwa yai ya karbe sannan ya koma ya zauna ya ce,

"Kina da matsala ne da ita?, naga yar uwata ce, me dan kinga hotonta awayata, laifi ne?."



Ranta a banmce tace"ai wllh ko ka goge sa, ko na fasa wayar, dan yar uwarka ce, ai naga akwai sha'awa atsakaninku, tunda dai ba muharraman juna bane, kawai nidai ka goge wllh ko kuma ka shiyi tashin hanklia agidannan kenan."



Dariya yasa, yana kallonta yace"to fa, sabon fi'ili tonwai idan ma neman aurenta nake meye naki aciki, nifa mijin mata hudu ne, kuma inada wadatata ina da arziqin da zan auro ko yar sanata ce kuma na bata duk abun da take so, balle kuma wai wata daban, kinga ni fa bani da ra'ayin mata biyu, amman wllh kika takuran zaki tsinci kanki dakishiya, idan kuma bakya so, sai ki dau damarar gyara dan kinsan dai kina tauye ni ta bangare da dama ko, dan haka sai ki gyara ki taimaki kanki".



Kuka ta fashe dashi na takaici, cikin borin kunya tace"dan kaga nibyar talakawa ce, mu fulanin Ruga ne, shi ne har damun gorin zaka iya auren yar sanata, saboda ni babana ba kowa bane shi ne har da cin fuska, to na rantse yau zan bar.maka gidanka sai ka auro yar sanatar ka ajiye, kai ka auro ma yar shugaban kasa ma, amman yau dai saina bar maka gidanka."



Murmushi yai ya kishingide yana latsa waya yace"kina fita zan kira Ummie na ce mata ta sanar agidansa sati mai zuwa zan turo magaba tana ayi magana, kafin ki dawo ita kuma ta shigo".



Dawowa tayi ta zaune akunerar da ke fuskantar tashi tana gunguni da goge kwallar fuskarta, dariya yai aransa yana mamakinta, watu tunda sukayi aure take tatsarsa, ya sai mata motoci har biyu amman ita hakan bai mataba, tafison ace kaf cikin kawayenta ta fisu arziqi, gashi ta dorawa kanta bata kawance da matar mai rufin asiri sai dai matar shahararrun masu kudi, kome ya mata sai tace ai irin na wance ne, ni kuma so nake nawa ya fi nata, da haka suke wannan zama, gashi matsalar ba iya nanba, sai ya share wata da sati biyu bata bashi hakkinsa ba, shi kuma yana cikin maza masu bukata, shiyasa ya dau damarar yin azumin nafita dan tsare kai daga aikata zina, gashi ta tsani kishiya, shi kuma sai Allah ya jarrabe sa kaunar Ummie tun lkcn bikinsu Laura da Ahmad yake nacin ta karbeasa amman taki.





   *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _30_

LONDON

_Bayan shekara hudu_



   Fitowarsa kenan daga wanka, yana tsane jikinsa da dan karamin towel, kallon Sakeena dake sharar bacci yayi, ji yake kamar ya rufeta da duka, dan ma yanzu yana dan iya mata musu akan wasu abubuwan, ko ya dan nuna rashin amincewarsa idan ta bashi wani umarnin.

   Kafarta ya dan daka yana kiran sunanta, ahankali ta bude idonta ta sauke su akanza, daure fuska tayi tace ,

  "Me kuma na tashi na haka kawai, kai idan kana barci ina tashin kane?, ni gaskiya ban son takura."



Gaba yai ya karasa jikin ma'ajiyar kayansa ya fara sakawa, cikin sanyin murya yace,

"Ki tashi lokacin sallah yayi, idan kinyi saiki koma baccin."



Tsaki taja tace"daman akan hakan ka wani tashen?, to wllh karka kuma mun irin haka bana so, ai ba kabarin mu daya ba, ka barni duk sanda na tashi ai zanyi, mutum sai shegen takura da sa ido."



  Maida kanta tayi ta koma kwanciyarta tana jan abun rufa, kai ya gyada kawai aransa yana mata fatan shiriya, fita yai daga dakin ya sauko zuwa harabar gidan, anan suka hadu da Gimba, da yake mai aikin direbanci, tasowa Gimba yayi suka gaisa sannan ya nufi motar dayasa aka wanke, dan yaga alamar futa zasuyi.



Suna hanya amma hankalinsa yana wani wajen yana tunane , tunane, kallonsa Gimba yayi cikin tausayawa, yace"Ranka ya dade, kar kace na maka shisshigi amman kamar kana cikin damuwa ko?."



Shiru ne yadan ratsa, sai can yaji yana waya, kamar da Ahmad yake, yaji yana sanar dashi zai shigo gida acikin satin nan, gaba daya hankalinsa yayi gida, suna gamawa ya kalli Gimba cikin sanyin murya yace,

"A Nigeria kai dan wane gari ne?."



"Ranka ya dade, ni haifaffafen Maiduguri ne, amman ina zaune a Kano, anan nake kasuwanci na da sauran harkoki na."



Kai ya gyada yace"Gimba, duk tsanani karka bawa mace amanna da rayuwarka, karshe zata kaika ne ta baro ka, musamman idan ka hadu da marar tsoron Allah, wata burinta tana samunka shikenan, ko mahaifiyarka bata isa da kai ba, wata kuma abun daka tara take son kwashewa, wata kuma rayuwarka take son gani acikin garari, mace ba abar yarda bace, amman idan ka hadu data gari, ka godewa Allah wadda zatana doraka akan hanya, wadda ko yaya ka sabawa iyayenka zata nuna bacin ranta ta nuna maka kay8 babban kuskure, Gimba ba ko wacce wayayyar mace bace abar so, ba ko wacee zaka yarda da ita ba, mata da yawansu suna kai mazajensu wuta, ka nutsu ka yi kyakkyawan buncike kafin ka auro mace ka ajiyeta cikin gidanka."



Kana jin yanda yake magana kasan abun na cin ransa,damuwar dake cikin ransa ce yake fayyaceta cikin hikima da6 dabara, tausayinsa ne ya rufe Gimba, tabbas Malik yana cikin tasku, kai kawai yake kadawa cikin bugar ciki yace,

"Ranka ya dade ai kai ba kada matsala, gaka sananne, ga iyalainka yar dangi, kaima dan dangi, wannan ai kai ba kada wata damuwa."



Murmushi Malik yayi mai ciwo, yana gyada kai, bai kuma magana ba, har suka isa inda zasu, yana shiga wajen shi kuma Gimba ya kira Saddiqu awaya, nan yake sanar dashi Malik zai shigo gida acikin satin da za'a shiga, murmushi Saddiqu yayi yace,

"Aikinku na kyau, sai ku taho tare, kace kaima zaka ganin gida ne."

Da wannan sukayi sallama.





**

"Ummi na makara Allah, idan na biyewa wadannan kawayen naki ba zasu barni naje makaranta akan lokaci ba."



Harararta Ummi tayi tace"naji dai, duk saurinki dasu zaki fita, ki ajiyesu sai ki wuce, kin daiji ai direban makarantar nasu ne yarsa ta rasu, dole yanzu iyayen yara su ne zasu na kai yaran kafin ya koma bakin aiki, ni kuma kinsan ba iya tuki nayi ba."



Baki Maryam ta tura tana hararar Ikram da Iklas, da sai dariya suke mata, dan su kam suna son fita da ita, ita ce dai batason fita dasu wai kar ace yaranta ne, gashi kamar su da ita har tayi yawa, haske da girman jiki sai kananun gashin gaban goshi da saje suka dauko na Malik, amman hatta da maganarsu irin tata ne har tafiya, to kuma duk inda suka shiga an dunga mamakin wai gata yar karama amman ta haife wadannan yaran, har biyu , daliki kenan da bata son tana fita dashu wai an rainata, harda masu tanka mata.



Hakanan badan taso ba suka tafi tare, tana tuki wayarta na hannun Iklas tana duba hotuna, kallonta yarinyar tayi tace ,

"Maam, yaushe Dadyn mu zai dawo, kinga jiya ma sai da muka ga wasansu, har anji masa ciwo ya kasa tafiya, Maam ki ce ya dawo gida zamuyi jinyarsa ko Iki?."



Kada kai Ikram tayi idonta har yayi raurau ya tara kwalla, karbar wayar tayi tana kallon hoton Dadynsu, shafawa tayi cikin sanyin murya tace"get well and come back soon sweetDad, we miss you more, Maam tace kayi fushi da ita, kullum sai tayi kuka, pls ka yafe mata ka dawo mu ganka."



Kanta ta juyar daga kallon yarinyar tana jin tausayinsu, tsawon shekaru daya diba baya tare da su, koda ta haifesu bata moye musu shi ba, kullum saita nuna musu hotunanshi tana musu shirar da fada musu wannan ne Dadynku, tun basu gane shi ba, har suka saba, dukda basu taba ganinsaba sai a hoto, haka idan suka je hutu 9ja, Mamah da Abbah suna yawan basu labarinsa dukdan kada su tashi basu san ubansu ba, sai dai kuma sunyi sahihiyar shakuwa tsakaninsu da Abie dinsu watau Ahmad, sai Anty Sultana da Anty Simrah da Saddiqu ya dawo da ita gaban Mamah, yace daman yar Maryam ce dan haka ta hada ta rike da nata.



Har suka iso makarantar babu wanda ya kuma magana, bayan sun sauka ne taga har lkcn basu saki fuskarsu ba, fitowa tayi dukda tayi latti, tsugunnawa tayi dai dai tsahonsu tana sakin musu murmushi tace,

"Hey friend, Dady yace ya daina fushi fa, kwanan nan zai dawo, amman ba nan ba, gidan Mamah zaije, idan kun samu hutu sai muje ku gansa ko?."



Dariya suka sa, cikin farin ciki sannan suka mata peck akumatu suka shige cikin makaranta suna daga mata hannu, mikewa tayi tana daga kanta sama, tana son maida kwallar data cika mata ido, akasan makoshi ta furta"ya Allah!."sannan ta shiga mota ta dau hanyar tata makarantar, sauranta shekara ta gama, ta zama cikakkiyar likitar mata da yara.





--cikin kwananki kadan ya gama shirinsa, domin sosai hankalinsa yayi gida, burinsa kawai yaga Mamah da Abbah, dan Ya Ahmad ya kawo masmasa ziyara sau biyu bai kuma zuwa ba, saboda yanayin aikinsu shima.



Ranar daya sanar da Sakeena sauran kwana biyu su tafi 9ja hankalinta ba karamin tashi yai ba, nan ta hausa da fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba, karshe dai haka ta shirya itama, ta biyosa bai sanar da kowa zaizo ba, dan gabansa wata mahaukaciyar faduwa yake, gani kamar iyayensa ba zasu saurare sa ba.

Ranar daya sauka, kasa shiga falon yayi, ita kuwan hakilamr tuni ta yima kanta waje akan daya daga cikin kayatattatun kujerun falon, tana baza idon ganin wani, tunda shigar safe sukayi, tasan babu wanda ya fita dai agidan.







**-

" Yauwa antyn yara taimaka/min da wannan dan naki uban kiwa, ke kadai zaki shiryasa ya tsaya, ni ya maidani kakarsa ai."



Murmushi Laura tayi tana jan hannun Akram, ta ce"zo nan ubana na kaina, zo na shiryaka anitse adena mana gori, mui sauri kar baba Habu yai ta jiranku ko?."



Muttsika ido yaron ya fara, cikin muryar yara yace "Ummanmu yaushe Maam zasu zo?, ni zama zanyi yau bazanje makaranta ba, zan zauna jiransu ne."



Kumatunsa tadan ja tana masa murmushi tace"ka bari inshaAllah maybe karshen watan nan suzo, idan basu zo ba, Mamy za tawa Abie magana ya kaiku ku gansu kaji, ka dena cewa ba zaka makaranta ba, kaji yaron kirki."



Langwabar da kainyayi, yace "to Umman mu, na dena."



Goshinsa ta sumbata ta kama hannunsa dana Sultana, ita kuma Khausar da take musu dariya ta sabi Affan akafadarta suka nufi cikin gida dan gaida surkan nasu, abakin dan harabar da sada ka da ainihin falon gidan suka hadu da Malik daya gama diga awajen atsaye ya kasa gaba ya kasa baya.



Kallon rashin sani yaran suke masa, sai dai Sulatana ce ma take mai kallon na sanka, amman na manta waye kai, su kuwa iyayen kallon mamaki suke masa, sa kyar dai Khausar tayi karfin halin mai magana tace,

"Kamar Malik ko?, saukar yaushe?."



Kai yadan sosa yace "wllh kuwan Matar Yaya ni ne, yanzu nazo shi ne nake son shiga kuma..."



Yar dariya tayi kawai, tasan kunya da nauyi ne ya hana sa shiga, hanya ta nuna masa da hannu tace"to bisimilla mana shiga muje."



Haka yana rabe raben sa dai ya shiga da sallama, dai dai saukowar Abbah da Mamah, tana rike da yar jakarsa ta tafiya aiki, da sallama suka shiga, durkushewa yayi awajen ya kasa motsi, sai Abbah ne ya karasa wajensa ya dago sa, dan dukar kafadarsa yayi yace,

"Mazaje na, yau kai ne agarin?, ko batan kai kayi ne?, to sannu dai da zuwa maraba."



Fadawa yai jikin Abbah ya saki wani irin kuka, shafa bayansa yayi yace "to meye kuma abun kuka, ba gaka agida ba dai, jeka wajen mahaifiyarka, tayi kewarka fiye da tunaninka."



Kamar karamin yaro haka ya karasa wajen Mamah yana sharar kwalla, tsugunnawa yai agabanta yadora kansa akan kafarta, yana sauke ajiyar zuciya, shafa kannashi tayi, sannan cikin rawar murya mai hade da tsantsar farin cikin ganin gudan jinita tace,

"Allah ya kara kare mun kai, ya kuma tsare min kai ya shiga tsakaninka da mugu, Allah ya maka albarka da kai da bayanka."



Amsawa kawai yake da amin, sai da taga ya nutsu sannan ta kalli inda Sakeena take, dako kallonsu batayi ba balle ta gaidasu, murmushi Mamah tayi tace"sannu Sakeena ya gajiyar hanya?."

Yamutsa fuska tayi tace"da gajiya kam, dan mun kwasota."



Wani kallon Khausar ta bita dashi, kamar ta shake ta, Laura kuwan kasa dagowa ma tayi ta kalleta dan takaici, dan har yanzu bawai yan gidan suna sakin jikinsu da ita bane, dukda tayi nadama mara iyaka, amman har yanzu basu dauketa kamar Khausar ba.



Mamah ce tace masa su tashi su tafi bangarensu, sai su huta kafin akawo musu abinci, kamar daman jira Sakeena take, tuni har tayi gaba abinta,burinta ta ganta awajen da tayi wannan ha'kar tayi bunni agun, ta tabbata dakyar idan ba wani abu ne ya samu ajiyarta ba.





*RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



*[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_31_

Cikin sauri ta karasa wajen, sai dai abun tashin hankalin, kamar ba wajen bane dan ta kasa gane inane tayi bunnin, domin kamar inyi wani dan gini ne awajen, hannu ta dora akan tana son sakin ihu, da sauri kuma ta maida hannun kan bakinta ta rife wani irin kuka na kufce mata.

Ba mamaki ashe Malik ya fara dawowa hankalinsa, har yayi tunanin dawowa gida, yanzu fargabarta daya kar ya tuna da Maryam, da abun cikinta daya bari, zaman dirshan tayi agun tana sakin kuka, sai can dabarar kiran Mamanta ta fado mata.



Tashi tayi ta goge hawayenta ta lalubo wayarta daga cikin jaka, kiran Mamannata tayi, tana dagawa bata jira abunma da zata ce ba, ta sakar mata kuka, tana fada mata abun dake faruwa.

Ashar Maman tata ta saki cikin fada tace,

"Saddiqu ne, wllh Saddiqu ne kuma sainaci abun uban yaron nan, shi ya rusa min shiri na, shege dan daba ki barni dashi, yanzu ki lallaba ki zauna, idan na gama da Saddiqu zan dawo kan mijinnaki, karki wani daga hankalinki."



Rarrashinta tayi sosai sannan sukayi sallama, bangarensu ta nufa, tana kiyasta yanda zata kuma juyar da hankalin Malik daga kan kowa na gidan.



Watansu biyu da zuwa su Maryam suka sauka suma, sai dai tunda tazo Khausar ta sata agaba da kayan mata, sai da tayi sati biyu sannan ta sarara mata, nan suka shiryawa zuwa Maiduguri, gaba daya har yaran dan zuwa lokacin sun samu hutu suma.



Sai ranar da zasu tafi sannan suka hadu da Malik, gabanta na wata irin faduwa ta ke kallonsa, shi ma ido ya tsura mata yana tunanin 8nda ya santa, dan tabbas kamar yasan fuskar amman bazai iya tunawa ba, kau da kansa yayi ya nufi mota dan hardashi za'ayi tafiyar da Sakeena.



Hawayene ya saukowa Maryam, gogewa tayi ta kalli yaranta dake ta surutu da Sultana, yafitosu tayi da hannu, da gudu suka zo, nuna musu motar daya shiga tayi tace" kunga wani can yana kiranku, kuje ku gaidasa".



Amsawa sukayi sannan suka nufi motar, sai dai kafin su karasa har anja motar anyi gaba, bin motar tayi da kallo wani tukukin bakin ciki na dukanta, kafadarta aka dan bangaza, ta juya da sauri, ido hudu sukayi da Sakeena da take sakin murmushin mugunta,

"An fada miki wai zaku samu kanshi ne cikin sauki har haka?, kinyi kuskure, dan Malik nawa ne ni kadai, duk macen data rabe sa, zata mutu kuwa agwauruwa."

Murushi Maryam tayi ta na dauke kanta, sannan tace "idan kin isa, ki tsince jinina dake yawo ajikinsa, sannan ki haramtawa wadannan yaran jin dumin mahaifinsu, ni da Allah na dogara kuma shi zai taimaka min ako da yaushe, ki abunki babu abun da zai faru sai abun da Allah ya tsara."



Wuceta tayi ta nufi motar dasu Khausar suka shiga, zama tayi tana sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalli Laura tace"wallahi kin taimaki kanki da kika raba hanya da waccan mahaukaciyar, da ace zata nutsu ta dawo kamar ke ai da kowa ya jata ajiki, amman ayi mutum babu komai aransa sai son zuciya , da neman duniya, Allah ya kyauta."



Sunkuyar da kai Laura tayi cikin sanyin murya tace "kiyi hakuri daduk abun dake faruwa, komai mai wucewa ne."



Kai tadan jinjina sannan suka fara wata hirar, dai dai nan Mamah ta shigo motar sannan Sakeena ta shiga suka dau hanya.



Misalin daya na rana suka isa, sun samu tarba mai kyau, sai da suka nutsu sannan aka fara gaggaisawa, anan suka hadu da Saddiqu daya dauki Ikram ya rike hannun Iklas, yana jin soyayyar yaran har jininsa, suna tsaye suna gaisawa yana tambayarta yaushe tazo, fuskarta dauke da murmushi tace,

"Kwanan mu kusan sha shida ai da zuwa, ya aiki ya iyali?."



Dariya ya danyi yace"iyali..?, tab sai dai acikin kawayenki ki samon wata, wadda zata iya da tuzurantaka na, har yau dai babu wani batu akan iyali."



Dariya itama tayi tace"shikenan to, na baka Ummie in tayi maka sai kawa Abbah magana musha biki."



Kai ya girgiza yace "sake wata wannan Gidado ne yake so, ki zabon wata dai."



Dariya kawai ta kuma yi tace "zamuyi maganar daga baya, amman nidai Ummie nasan ita ce zata dace da kai, kyawawan halayenta kamar na marigayiya ne, tana da nagartattun halayen da ni kaina da ina da wa, wanda muke ciki daya da sai na mai kamu, amman tunda gaka tabbas zata zama mallakinka, rabu da batun Gidado, Ummie ba tada hayaniya ba zata iya daukar fadan Salme ba, kawai kayi shiri dan wllh sai na

Please Login or Register in order to submit comment