You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannun yayi bayan ya sunbata, ya kashe mata ido adaya yace "ina jiranki pls...hatta kayan da zaki saka, zan aiko miki dasu, bye" 'yan yatsu biyu ya dage mata ya wucewarsa, numfashi itama ta sauke, tana jin wani bakon yanayi akan Fahad din, hanyar da yabi itama tabi da kallo murmushi na musamman yana kubce mata.



Ko da ta koma gida bata boye wa Aunty Huda ba ta fada mata komai, shiru Hida tayi kafin can tace"ki bari kafin goben zan yanke shawarar zuwannan ki ko kuma ah ah".





Da dare yayi kamar ko yaushe bayan an kallama yin dinnar Kawu ya tambayesu ko da mai bukatar wani abun kafin ya wuce sama, duk amsawa sukayi da babu, sannan ya musu sai da safe, Ammy ma bayansa tabi, bayan ta mikawa Bad'ejo furar da ta dama mata, dan ko kadan bata fiya zaman falon ba, ta fi gane zaman daki, hakan ne ma yasa Kawu ya hada mata kayan kallo adakin daduk wani abun da zai debe mata kewa.





*RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman

Wattpad#nusysa.

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



_6_

Tun safe take baza kunnen ta inda Anti Huda zata kirata tace ta amince da zuwan ta wajen partyn, amman shiru har kusan la'asar, gashi taji tana cewa tana da bikin kawarta da zata da yamma.



Ganin magariba ya kawo kai sai kawai ta hakura ta sallame da zuwannata, bayan sun idar da sallah ne suna zaune kamar yadda aka sabar musu, duk bayan idar da sallah Huda tana biya musu karatun kur'ani da sauran litattafan addini, bayan sun gama ne suka nufi dinning dan cin abinci, gani yanda Mairoji take tsakura ne yasa Hudan yi mata magana tace "wai kin fasa zuwa ne, naga sai wani nuku nuku kike?".



'Dagowa tayi ta kalleta tana sakin murmushin jin dadi tace" ah ah Anti zani".



"To kiyi ki gama, ga kaya cen an aiko dasu dazu kuna sallah lokacin, amman tare da Salme zaku".

Salmen da take kara miya akan farar taliya tace" Anti ina da Homework wllh, kuma ne zanyi submiting, taje kawai".



Badan Huda taao ba ta amince da Mairojin taje ita kadai, dan bata son suna nisa da gida babu wani akusa dasu, da haka dai tasa Mairoji ta shirya cikin kayan da Fahad din ya aiko mata, riga ce gown pink sai takalmi da yar porse, passion na sarkan wuya da d'an kunnaye da abin hannu duk kalar blue ne mai haske, ba laifi tayi kyau, dan Huda harda daukarta ahoto, tace ta samu nayin status, dariya suka sa dukansu sannan Hudan ta rako ta har bakin mota dan direban gidanne zai kaita.



Sai da tayi mata kashedi sosai akan karta sake takai dare, duk inda tara da rabi tayi ta tabbatar sun dauko hanyar dawowa, tana tsaye har suka fice daga get din gidan sannan ta koma tana sauke ajiyar zuciya, inda Allah ya taimakesu Kawu bayanan, sai Ammy da suka shirgawa katuwar karya.





++++



Wajen ya hadu sosai, duk da babu wadatar haske, abakin wajen shiga ta tsaya tana kallon tsirarun mutane masu wucewa, kowa sai harkar gabansa yake, ji tayi an kamo gefen kugunta ta baya, azabure ta juya dan ganin waye, ido hudu suakyi da Fahad da ya gama hadewa cikin blue suit sai baza kamshi yake, matsawa tayi tana dan zame hannunsa daga jikinta cike da kunyar kallon kurillan daya ke binta dashi.



Murmushi kawai yayi yana shafa kansa, iska ya furzar yana kuma kafeta da ido, cikin kasalalliyar murya yace"Baby....kinyi kyau fa, badan agida ance nayi kankanta da aure ba, da ba abinda zai hana ni mallakarki acikin satinnan, da ganin ki zaki bada cittahhhh".

Yaja kalmar karshe din yana murza hannun ta daya kamo, yana mata kallon kasa kasa, ita dai ta kasa magana dan wannan bakon abu ne awajenta, duk da tana da yan uwa maza, da suka taso gida daya ma dasu, amman irin haka baya shiga tsakaninsu, ko Ahmad da tafi sakewa dashi fiye da kowa ma, basa irin wannan wasan tsakaninsu.



Maganar sa ce ta dawo da ita , kallonsa tayi yai mata nuni da hanya akan su shiga, ba musu ta bisa hannunta cikin nasa, sai dai ganin sun ahiga duhu yasa ta dan tsorata har ta kamo dantsen hannunsa ba ta sani ba, dai dai lokacin haske ya gauraye wajen tare da zubowar wasu abu masu kyalli kansu, sai muryar mutane tare da tafinsu na taya Fahad din murnar cikar shekara sha takwas.



Abin daya bata mamaki, tayi zaton ganin yan makarantarsu da aiya abokansa kadai, sai dai taga harda manyan mutane, wasu ma data gani kamar iyayensa ne, matar sunyi matukar kama da Fahad din da ita, ceke din daya yanko ya kai bakin ta, rasa makamar dafawa yasa ta bude yasa mata, cike da kunya ta sunkiyar dakai.



Nan aka fara miko mai kyaututtuka yana karba sai ya bata ta rike, sai wajen tara wani abun sannan aka fara watsewa, anan ya gabatar da ita wa iyayensa, cikin sakalci yace"Dad....ita nake so, idan na gama makarantana na fara aiki ita zaku auramin, dan Allah Dad kar sai lokacin yayi kuce min ba haka ba".



Matar dake gefe da alama itace mamansa tace "idan kuma ita taki fa Son? idan lokaci yayi dakan mu zamu nema maka aurenta ka dena damuwa"

Kallon ta yayi ya dauke kai, ya mayar ga Dad din sa yace"ka fadawa matarnan ta dena shigar min magana, dan bada ita nake ba"

Murmushi Dad din yayi yace"Madam....adena shigarwa d'ana magana tunda bada ke ake ba".



Kai kawai ta gyad tabar wajen, cike da jin ciwon abinda Fahad din da babansa suke mata.







Sai tara da kusan arba'in sannan ya dauko ta dan kawo ta gida, ahanyane ta kasa yin shiru ta dan kallesa tace"Fahad, matar nan ta dazu, ba mamanka bace?".



Juyo wa yai ya kalle ta sannan yadan tabe baki yace, "mamata ce mahaifiya ta kuwa, me kika gani"?.



Tsare sa tayi da ido kafin ahankali tace" amman kake mata abu kamar ba ita ta haifeka ba, me yasa, wannan ba dabi'a bace mai kyau, dan Allah ka dena na taso babu uwa, da naga kayi mata haka wllh raina ya baci, idan kuwa haka zaka ci gaba dayi mata, to ka dena kulani".



"Wayyyoooo....ranta ya baci, kawai akan dan wannan abun, Mommmm....duk ke kika ja komai, duk abin dana miki ke kika jawa kanki".

Dukan sitiyarin motar yayi yana cije baki acan kasan makoshi yace" sory"



"You too"



"But Baby..."

"ya isa haka, saukeni basai ka shigar dani ba" ta fada tana dauke kai, duk yanda yaso ta sauraresa ki tayi, kayan da ya taho daau zai bata na gipt din da aka basa ma kin karba tayi ta shigewarta, sai mai gadi ya bawa yace ya mika mata, shi kuma ya koma gida.





Fahad Muhammad Jarfa, yaro matashi mai ji da gayu da tashen kuruciya, shi ne d'a na hudu acikin yan matan yayyensa, kuma dan autansu, ya taso cikin gata da kulawar uba, dukda yana tare da mahaifiyarsa amman bai saba da itaba, dan iamta tafi bawa aikinta muhimmanci akan kula da yaranta, hakan yasa Fahad ya tashi iya babansa kadai yake sakewa dashi, ko gaisuwa wani sa'ilin sai uban ya tsawatar mai sannan yake mikawa Mom dinsa, shi yana mata kallon wadda bata damu dashi ba, ita tana masa kallon yaro mara kunya, ahaka suke zaman su, dan wanda bai sani ba zaice, matar uba ce da dan mijinta.



Kuyi hakuri wllh na rubuta, ya goge ne, shiyasa na sake muku wani amman ba yawa, ma jone gobe ko jibi=ØÞ.



Mmn Mu'ayyad



*RUGAR SAJE*



  By Nusaiba Ayuba Suleiman

Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S. Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*

(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



_7_



  Kusan sati kenan Fahad na azabtuwa da shariyar da Mairoji ta tsiri yimasa, ya bi duk wata hanya dan ta sauraresa amman tayi biris da shi.



    Yau ma  suna zaune ita da kawarta Leemah, yazo ya zauna kusa da ita, idonsa na kanta yayin da ita kuma ta dauke kai kamar bata gansa ba, dariya Leemah tasa tace"loverbird, yau kuma me ake boyewa ne naga sai satar lakkon juna kuke, kowa da abun dayake son fada".



Harararta Fahad yayi cikin tsokana yace"ina ruqanki yar sa idunawa kawai, mai barci da rabin ido".

Tanda yai maganar da murguda baki shiya baya Mairoji dariya, amman sai ta saki murmushin daya bayyana jerarrun hakoranta, kallon ta yayi cike da jin dadin ganin fara'arta, cikin sanyin murya yace"Baby....kiyi hakuri dan Allah na rantse miki bazan kuma wa Mom rashin kunya ba, zanyi duk abinda take so, dan Allah karki kuma fishi dani pls Babyyy.....".



Kau dakai tayi, bata kula shi ba , nan yaita zuba mata shirme, jin ya ishe tane da kiran wani Baby, ta ce masa"wai kai Fahad nawa kake ne, da zaka na cemin wata Baby, naga shekarun naka kaima ba yawa, da har zaka nemi rainan...."



Leemah ce tai sauri katseta ta kama hannunta ta danke, hada ido sukayi ta dan girgiza mata kai, Fahad ya dan yi dariya yana shafa kai, yace "Halee kyale ta ta fadi abinda ke ranta, wllh dan ba za'a yardan min agida bane , da asatinnan na aure ta, sai ta banabance tsakanin aya da tsakuwa, amman ba wani abu, ai akwai lokaci, zai nuna kansa ne".



Baki Mairoji ta tab'e ta tashi ma tabar musu wajen, tunda an koma aji, da kallo ya bita yana jin son ta na kara rastsa shi, sallama sukayi da Leemah tabi bayan Mairoji shi ma ya wuce aji.





Bayan malamin daya shigo ya fita ne, Leemah ta maida hankalinta kan Mairoji da take duba darasin da aka musun yanzu, warce littafin tayi tana galla mata harara, dariya Mairoji tasa tace "Allah ban san haka kiban littahi na".



" anki bayar wa din, Allah Maryam Malik ina rabaki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu ko, kinga ki keda fadar irin wannan maganar agaban Fahad, kece baki san shi ba, kowa yayi mamakin yanda yake son ki har yana cewa auren ki zaiyi nan da wani lokaci, gayen da yan mata ke sonsa kamar suyi hauka, yana sharesu, idan kinsan adadin matan da suka bashi kansu zakiyi mamaki kawai dan ya so su ko na dan lokaci ne, kin gansa dai banda Allah ya kawo ki rayuwar sa da tuni abu gaba ya ke ba baya ba".



"Amman yanzu saboda ke ya dena kula yan mata, ya dena mu'amala da matan da suke kara tunzurashi yake lalacewa, watau shi ne kike ce mai yaro ko...? so kike ya fara nuna miki halinsa ko, kina son ganin aikin yara da alama, kici gaba, wallahi duk randa ya rutsaki bazan nuna nasan ki mbama balle na kawo miki dauki".



Baki ta tabe tana tattara litattafan ta ta ce" kanki ake ji ai ni banga wani abu na daban ba da za'a hanani magana, banda reni ya zai na kirana da wata yar tsana, shidin nawa yake, ina yanzu yake sha takwas, ke ma da kadawa pupu miyar kwai".



Tana sababi da haka tabar ajin, ta zauna abaranda kafin lokacin tashi yayi.







++++

Kwanci tashi, sun dauki watanni har bakwai agidan su Huda, ga cikin Bad'ejo da yake kara girma, Kawu shi ya dau nauyin komai, tun daga awon da ake zuwa mata har gida, ganin yanda cikin yai girma, yasa likitar da da kanta ta bada shawarar ayi mata aiki idan lokaci yayi, domin za'a iya samun matsala, dan tayi kankanta da yawa, gaba daya batafi sha uku ba, kowa yayi na'am da shawarar inda Ammy taci gaba da kula da ita, da kuma bata abubuwan karin jini da lafiya.



Ansa lokacin da za'a mata Cs din sati uku masu zuwa, nan suka maida hankali wajen kula da ita dan gudin kar jininta ya hau, ranan da za'a mata kam, ko su Mairoji basu je makaranta ba, hankalinsu duk ya gama tashi da za'a shiga ne Bad'ejon ta kama hannun Mairoji idonta tab da kwalla tace "dan Allah ko bayan raina, ki dau kar min fansar abinda Oga yamin,ki kular min da abinda na bari, ahannunki na danka sa amana, ki kularmin dashi kamar yanda zaki kula da naki, ki tabbatar Oga ya girbi abin daya shuka, ko me na haifa na baki damar ki sa masa sunan dayai miki, ga amanar abinda zan bari nan".



Kuka Mairoji keyi har numfashinta na neman daukewa, da kyar aka banbare hannunsu sannan aka shiga da Bad'ejon tana hafiye kukan daya ke zuwan mata tana karanta duk addu'ar da tazo bakinta.



Bayan wasu awanni aka fito musu da yarinya katuwa da ita, karban 'yar Kawu yayi yana tofeta da addu'a, cike da tausayin yarinyar da tazo a sababbiyar lamba, sai da kowa ya gama daukar yarinyar sannan aka bawa Mairoji ita, karba tayi tana kallon yarinyar , sak Oga sai dai ta dauko hasken Bad'ejo, kura mata ido tayi tanajin kaunar yarinyar yana ratsata, kallon Kawu tayi zatai magana yace " ba komai Maryam, ki sa mata sunan da kike so, yar ki ce".

Murmushin jin dadi tayi ahankali ta sumbaci goshin yar tace "Allah ka raya min Safiyyah, Allah kasa ta zama haske arayuwar Oga, Allah kasa ta zama silar shiriyarsa, Allah kasa mai yiwa addini hidima ce".



Kowa amsawa yake da amin, Salma kam zuwa tayi kusa da ita tace" bakida hankali Mairoji, sunan mahaifiyar taki kika sanyawa 'yar shege,...! 'Yar zina...."



"Salme.....!!! ya isheki haka , wallahi ko kalma daya kika furtawa ranki zai baci idan ba mai kyau bace, karki kuma cewa 'yata yar shege, Ba'dejo ba zina tayi ta same ta ba, fyade aka mata aka same ta, kuma suna dai na uwata ne bana wani ba, gudu bacin rai irin haka yasani saka mata sunan da nake da iko dashi, amman wallahi kika kuma shegen tamin ita sai ranki ya baci, tunda har yanzu duhun jahilci na dawainiya dake".



Kowa shiru yayi yana kallonsu dan tunda suke basu taba ganin tayi fushi haka ba, ko da ranta ne ya baci sai dai ta koma gefe tayi kuka, har ta huce dan kanta, rarrashinta Ammy tayi tana gargadin Salme da ido.

Suna zaune anan har aka fito da Bad'ejon, tana cikin mayan allurar barci, wani dakin aka shiga da ita dan samun hutu.



Wajen kwana biyar ana jinyarta kafin aka sallamesu, ta warware sosai, sai dai idan ta zauna sai tayi ta kallon Mairoji tana kallon 'yar, tana murmushi, ranar da suka kwanan bakwai, Kawu ya yanka musu raguna hiyu manya, banda kaya da akai mata, duk da ba taron suna za'ayi, to wama suke dashi da zasu kira, in kuma sun kira din suce me? anyi mata fyade ne ta haihu suke taron suna, wannan dalilin yasa babu wanda ya sani ko acikin unguwunguwa tunda daman ba shiga gidajen makofta suke ba.



Washe gain suna sukayi suyar namansu iya su kadai, sai yamma sannan suka samu nutsuwa, da dare una zaune dukansu adadin Bad'ejon sai ta kalli Mairoji da take wa Simrah wasa cikin sanyin murya tace"ban taba ganin inda 'ya da uwa sukayi matukar dacewa kamar ku ba, kinyi kyau da ita ahannunki, Allah ya bar miki ita, Allah yasa ta zame miki haske kuma Alkhairi ".



Da ameen aka amsa sai dai Ammy data tashi tabar dakin tana kau da kai, idon ba gizo idon Mairoji ke yi mata ba, kamar kwalla ne ta gani a idon Ammy, da sauri ta kalli Bad'ejon da take mata murmushi idon ta kyam akanta, tashi sukayi suka fita dan sunji muryar Ya Salman afalo, yanzu ya sake dasu sosai jansu yakeyi ajiki kamar kannan sa.



Sun baje sai shira ake, akan wani series da suke kalla a Televista My Legal Wife,shigowar Ammy yasa suka maida kallonsu kanta, cikin sanyin murya tace musu" yanzu shi ne kuka baro Bad'ejon ita kadai adaki, maza ku kumo ciki ku dan d'ebe mata kewa".

Tashi sukayi suka tafi suna dariya, Salme har tana cewa, Ammy yanzu kin dena son mu, muma ba mu jira Kawu ya dawo mu koma wajensa".



Murmushi mai ciwo Ammy tayi, dan ta yanke kauna da Bad'ejo, bata dawo daga tunanin da take ba taji salatinsu da ihu, dai dai shigowar Kawu, suka yi dakin nasu da gudu dukansu, suna zuwa suka tarar da Bad'ejon tana kalmar shahada da salati, idonta kyam akan Mairoji da tayi mutuwar tsaye, ba ta dawo hankalinta ba sai da taji, Kawo na cewa "Allah akhbar, Allah ga baiwarka nan Allah ka karbi bakuncinta , Allah ka sauketa akyakkyawa masauki".



Rufe mata ido akayi, sannan aka ja zani har kanta ya rufe, kukan Simrah da faduwar Mairoji ne ya kankato da hankalinsu wajen ta, nan danan aka basu taimakon gaggawa sai dai hannun Simrah kamarr ya bugu saboda faduwar da suka yi.







_inshaAllah duk bayan kwana biyu zaku samu page, amman fa ban muku alkawari ba,amman inshaAllah zan kokarta_.

    



*RUGAR SAJE*



    By Nusaiba Ayuba Suleiman

Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango



(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



    _8_



Kwanan zaune sukayi agidan, daga masu sallah sai masu karanta Alkur'ani, da asuba Kawu ya sanar da Liman akwai zana'izar a gidansa, acikin yaran kannensa dake zaune dasu, daya Allah yay mata rasuwa, bayan an fito daga sallah ba wanda yai gaggawar tafiya aka tsaya dan afito da gawar asallaceta sannan amika ta makwancinta.



    Anan cikin gida kuma Ammy ta fadawa matam makota duk an shigo, anan ana mata wanka akayi mata sutura sannan aka fito da ita, anan ne kuma Mairoji ta rike ta kam tana wani irin kuka mai tafiya da imanin mai sauraro, da kyar aka samu ta saki sannan aka fita da ita dan a sallaceta.



     Wajen biyu na rana yan uwan Kawu dake Maiduguri suka zo, dan ya sanar dasu mutuwar kuma sai gashi sunnyi karar zuwa, suna cikin gida suna karbar gaisuwa Salman yazo ya karbi Simrah, watau Safiyya da sukawa lakabi, yan uwan Kawu da suka zo gaisuwa ne zasu ga 'yar, bayan ankai musu ne Alhaji Bulama ya kurawa yarinyar ido can yace wa dan uwansa, "Mahmud kodai ido nane, ko kuma kamanni ne kawai na jariri, amman sai naga kamar an tsaga kara da  Yaya Baba Gana, kamar ta baci kalli har yatsun kafa  dana hannu".



   Wanda aka kira da Mahmud shima mamaki ne fal ya cika shi, karbar yarinyar yayi yana jin kaunar ta yace" Baba Bulama, duk yanda akayi uwar yarinyar nan daga tsatson mu ta fito, daman ai Kawu yace daga Maid suka yo gudun hijrah".



    Kai Bulama ya jinjina yana wani tunani aransa, ya aika aka kira masa Kawu daya ke sallamar wasu abokansa da suka zo mai gaisuwa, zama yayi akusa da  Bulama yace " Yaya gani".

    "Muhammad kace uwar yarinyar nan daga Maid sukawo gudun hijrah?".



Kai Kawu ya gyada yana jin bugun zuciyarsa na tsananta, fatansa dai Allah yasa hasashen da yake ya zama gaskiya, muryar Bulama ya tsinkaya inamda yake cemai" Muhammad baka ga kamar Baba Gana afuskar jaririyar nan ba, babu abinda ta bari nasa, sai data bude idon ta naga sak kalar idon Saddiqu, kasan shekara kusan bakwai kenan ya shiga duniya ba'a san inda yake ba".



   Shiru Kawu yayi sai can yace"uwar yarinyar maganar gaskiya fyade aka mata, da Allah ya tashi ikonsa kuma sai ya kawo rabo atsakani".

  " Wa ya mata fyaden"ya tsinkayi muryar Mahmud da bai ce komai ba tunda aka fara maganar.

   "'Yan tada kayar baya, ko kuma nace 'yan bindiga dadi, amman yanda suka ce su a Ruga suke,dan fulani ne, har yanzu ma hausar su bata nuna ba,  su kuma maharan suka far musu bayan sun kwashewa mutane dukiyarsu, sannan sukayi gaba da yan mata har uku, yanzu biyu suna tare damu anan gida, uwar yarinyar nan ce dai yau ta amsa kiran ubangiji".



   Kai suke gyadawa cime da gamsuwa, Salman aka bawa yarinyar ya maidata gida, sannan su kuma suka bar maganar akan sai bayan addu'ar uku za'a sake tattaunawa akai.



++++



     Ahankali yake saukowa daga matakalar jirgin yana jin wata yar nutsuwa tana saukar mai, gefe daya kuma yana jin faduwar gaba, ba wanda yasan da zuwan sa sai Ahmad dan haka yana gama sauko wa dashi ya fara cin karo yana tahowa inda yake, murmushi auka sakarwa juna bayan sun danji dumin junansu, bayansa Ahmad yadau buga jin yanda yake saukwme ajiyar zuciya.



     Baya ya bude mai yana mai alamar ya shiga, amman ya dauke kai ya bude gaba ya shiga, shima Ahmad din baice komai ba ya shiga  yaja suka bar filin sauka da tashi na jirage.



   Sun fara tafiya ba wand yace wa dan uwan sa komai sai can Ahmad ya tsinkayi muryar Malik din.

    "Wai kai yaushe zaka dena zama direbana, ko yaushe sai dai kana tuki ni ina gefe ko baya?"



   Dariya Ahmad yayi yace "yaro ba zan dena tuka kaba sai randa kayi aure, sannan ne zan san ka gima, ka fara hankali".

   " uhmmmm....." daga haka yai shiru, shima kuma bai kuma masa maganar ba dan yasan ba so yake ba, shi ne ma mai yi masa wannan zancen ya kwana lafiya.

     "Ya wasan naku, fatan dai anyi nassara, kasan ni har yanxu na kasa koyo kallon wasan kwallon kafa, shiyasa ban san ya xa wasan nanku yake kasancewa ba".



Baki Malim ya tabe yace" wasa da dadi ba dadi, da nasara da kuma faduwa, wanna karon ma mun karbi kambu, dan nine na karbar mana kofi, ganin nasarar da muka samu shine manajan Man United ya nemi siyana, ni kuma nafi son zama aclub dina nafi jin dadi".



  "Amman dai sun bani lokaci wai nayi tunani akai, kafin hutun mu ya kare sai asan yanda za'ayi".



  Kai Ahmad ya gyada yana godewa Allah da ya ke dailuakaka mai kani sa duk inda ya shiga, ahankali cike da fargabar abin da zai fada yace" Malik...har yanzu shiru batun su Maryam, har yanzu babu wani labari wallahi na fara sarewa,ga Goggoji da kullum jininta hawa yake, dan ma Abba ya dawo da ita nan Dutse".



   Kai Malik ya kawar ya na kallon titi, yana hadiyar wani abu da daya tokare masa makoshi, shima Ahmad din shirun yayi dan ya kula yau yan maganar basa kansa.Da haka har suka karasa gidan, dai dai lokacin Mama tana jera abinci akan dinning, kallonsu tayi kawai tana murmushi ta kau dakai.

   "Watau saboda baku da gaskiya, kaf dinmu ba wanda zaku fadawa zuwan naku ko, kai yau rabonka da gida wata uku kenan, kai kuma dan kwallon kafa, ka dauki kusan watannin bakwai, amman ba zaku sanar idan zaku zo ba sai da aganku tsulum dan rashin gaskiya ba".

  Ta karasa tana harararsu, dariya suka sa mata, sannan ko wannensu ya rungumota ta gefe suka sata atsakiya, suka bata ligh kiss a forehead dinta, kafin suka saketa suka nufi bangarensu dan watsa ruwa.



 

Please Login or Register in order to submit comment