You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mairoji tayi tace"tab, rai kanga rai?, malam Fahad kana gari ashe?, amman shi ne aka manta da babin mu ."



   Dariya ya danyi kawai yana shafa kansa, gani yayi Mairojin tayi wani mahaukacin sauyawa, ta kara kyau da cika, kawar da batun yayi ta hanyar kamo hannun Ikram yana tambayarta sunanta, dagowa yai ya kalli Maryam din yace "amman yaranki ne wadannan ko?".



  Ya nuna Iklas da Ikram, kai ta gyada mai tare da nuna masa Sultana da Simra, tace " ga babbarsu nan, Simrah sai Mai binta Sultana, sai wadannan yan biyu."



  Baki ya rike yace"ke Maryam, yanzu kece da wadannan yaran, gaskiya an dade ba'a hadu ba, tun fa asecondary, ina Salma tayi aure itama ko?".



   Daga nan kuma sai shira ta balle tsakaninsu, matarsa da take gefensu sai hararar Maryam take, ita fa bata ga abunso ajikin wannan ba, banda uwar hanci da manyan idanu ba tada abun kallo sai dai ko farar fatar, yatsina fuska tayi ta maoda kallonta ga wasan da ake bugawa, ihun da aka saka ne yasasu maida hankalinsu kan wasan.



  Nigeria taci kwallo na biyu kenan, sai yanzu da M.B.Saje ya ciwa Portugal kwallo daya, duk da kowa yasan yaki yaci abokan hanayya ne dan yan kasarsu ne, amman ya samu damarmakin da zai cinyesu cikin ruwan sanyi, sai yanzu dayaga an kusan tashi shi ne ya ci musu daya dan kar atashi da abun kunya.



   Murmushi matar Fahad tayi tace"kai mutumin nan yayi, wllh karshe ne shi wajen buga kwallo, ina yinka M.B".



   Ikram da take kan cinyar Fahad ce ta daka wani tsalle ta fita daga wajen ta fada cikin filin , dai dai shima Malik ya juyo ai kuwan ta dane sa, ganin haka suma sauran yaran suka fita da gudu suka dane sa suna murna, baki sake Matar Fahad take kallon yaran, haka shima Fahad din da yake binsu da kallon mamakin daman su  sanshi ne, kallon Maryam da take ta faman sakin murmushin farin ciki yayi yace,



  "Wai kun sanshi ne daman?, shi ne fa dan kwallon da duk wani dan Africa yakeson koda daha ido ne suyi dashi, naga yaranki sunje wajensa kuma shima da alamun sanayya mai karfi aatsakinsu."



   Kuma kallon Malik tayi sannan ta kalli Fahad tace"ai babu sanayya tsakanin uba da yayansa, sai dai shakuwa da kauna, babansu ne shi ni kuma mijina."



   Baki sake suke kallonta, dan basui zata sun sanshi ba, kafin wani ya kuma cewa wani abun, har an busa alamar ci gaba da wasa, dan baifi sauran mintuna sha biyar ba atashi, yaran ne suka dawo suna ta tsalle suna fadawa Maam dinsu Dady yace ana tashi zasu tafi yawo, murmusa musu kawai tayi, suka ci gaba da kallon wasan da saura mintuna kadan atashi.



  



Ko mintuna uku ba 'ayi ba , dayan dan wasan Christiano ya ci musu wani kwallon, sai ya zama anyi 2-2 kenan, gashi sauran mintuna biyu atashi, kokartawa sukayi yan Nigeria suka kuma cin wani kwallon acikin sakan talatin kafin busa alamar gamawa.



Tafi da sowa wajen ya dauka, bayan wani dan lokaci anyi duka bubuwan da ya dace, Nigeria ta dau kofi, sannan suma Portugal aka basu nasu kambun karramawa, daga nan aka tashi daga wasan, tun kafin su bar wajen Hafsa matar Fahad take kokarin cusa kanta awajen Maryam, kawai ita kam sai tayi murmushi, domin tasan dalilin da yasa take son kulata, haka suka rabu bayan Hafsan tasan yanda tayi ta karbi lambar Maryam din.



Bayan sun dawo gida wanka tayi ta sauya da wata yar riga, dakinsa ta shiga dai dai ahima ya fito daga wankan, ido ya kanns mata yana mika mata hannu, baki ta tura sannan ta kama hannun nasa, janta yai bayan ya zauna kan gado yace,

"Kin danyi kyau kadan."



Fari tayi tana kwanciya ajikinsa tace"idan ma muni nayi, kamarmu dai daya da kai, idan nayi kyau ma, ai kai ne ka kwaiwayo kamata, dan haka kabar fada kasan dai na fika kyau."



Dariya yasa yana shinshinarta, ture sa take tace"dan Allah ka bari, wllh kwanan biyun nan bana cikin wannan yanayin."



Bai kulata basai daya tabbatar ya kaita karshrn makura, sannan ya juya zai sakko daga gadon, kama hannunsa tayi murya can kasa tace,

"Ba kyau fa mugunta, Allah zai kamaka idan ka tafi, kaga kuma banason hakan ta faru da kai, kawai kazo ka ci gaba da neman ladarka."



Dariyarsa ya danne yace,"to ni kam mai zan miki?, kar na takuraki ai, naga bakya cikin yanayin yanzu."



Kai tadan juya, tana cije lebenta na kasa, gashi ta kasa magana sai binsa da take da ido, murmushi yai kawai yana girgiza kai, sannan ya dawo ya fara mata abunda take so, sai da suka samu nutsuwa sannan ta koma gefe tana shirin matsar kwalla, wai bayanta ya fara mata ciwo.



Hararta yai yace"kinsan meye matsalarki?, gulma, idan kika samu hakimaini kika fara lasarsu, sannan kika dangana da sandan ba'are, kika fara cinyeta kamar ba zaki daina ba, banda inayin da gaske da wataran saina neme su na rasa, kin hadiyan yan bangar siyasata, bayin Allah yan biyu kyautar Allah, haka idan na fara kara miki iska, ihu da sambatu har toshe kunne na nake, amman sai kin samu nutsuwa sai ki wani kwayen baki wai ni, nan ciwo, can ciwo, wash Allah na."



Kallonsa take mai cike da harara, takaici duk ya gama kamata, kuma fa ita da gaske take bayanta ne yake mata ciwo, amman ya wani zauna sai tsokanarta yake, tashi tayi ta wuce ban daki, da kallo ya bita kawai, ganin yanda da gaske ta nuna tana jin haushin sa, baki ya tabe, wani sashi na zuciyarsa yana fada masa yaje ya lallashe ta, wani sahen yace, barta inta gaji da fushin zata sauko, haka ya gama shirinsa ya fita ya dau yaransa suka shiga gari.









***

"Na fada miki aikinnan yayi, domin yanzu batun da ake Ummie din ta dawo gida , tace ba zata iya zama da shi ba, shima kuma bai biyo ta ba har yanzu."



Numfashi Jidda ta sauke tace"to batun su wancan sangamin fa?, ni fa so nake na daukarwa yayata da mamata fansa, dan ba zasu haukace abanza ba , wadanda suka yi sanadin hakan, su suna can suna cin duniyarsu da tsinke."



Tsaki Salme taja tace"dalla can, na fada miki duka nasa akayi aikin, farraqu aka musu ai, dukansu yanzu sai dai mu jira batun takardar sakinsu, ita Ummie ai ban huce ba ne, kina fa gani adalinlinta mijina yake fadamin maganganu, har mari na fa ya taba yi saboda ita, ya kirani kazama, ya kirani dakikiya, duk saboda ita, ai nan gaba ko aure goma tayi sai nasan yanda ta fito, ai ba zatayi zaman gidan miji ba, idan kuma tayin to zatayisa cikin wahala ne."



Zama sukayi suna kulla yanda zasu dau fansar abunda akayi musu akan Ummie da Maryam, don sosai sukadau abun da zafi.





   *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _35_



Bayan sun gama tattaunawa ne na yanda zasu tarwatsa zaman Mairoji da Ummie, sannan Jidda ta koma gidanta, tana shiga ta tarar da mijin ta ya dawo, tanbayarta yayi inda taje, tsaki tayi kawai ta shigewarta daki, tana mita,

"Kaima ka kusa dawowa tafin hannu na, bazan yarda da wannan shirmen ba, duk inda mutum yasa kafa ya fita sai an tuhume shi da inda yaje, ko inda zaije, bazan dau wannan takurar taka ba wllh."



Shigowa dakin yayi kuma yaji mai tqke fada, daman yana cike da ita na rashin kunyar da ta yiwa yayarsa, mari ya kai mata, kafin ta dawo daga mamakinsa ya rufeta da duka, sai daya mata likis sannan ya barta awajen ayashe yana buga mata gargadi,



"Wllh ki shiga hankalinki, duk halin da uqarki dabyayarki suke ciki bai isheki darasi ba, sai kin dorawa kanki wani jafa'in?, mai Maryam tayi muku da zaku hada kai keda Salma ku musu asiri, ai duk naji abunda kuke kullawa, na shiga gidan domin kiranki naji duk kullin da kuke yi, to wllh ki kama kanki, kuma daga ya na rufe fita, kin dena zuwa ko ina, kuma ba wanda zaizo inda kike.



Kuma ki sani, zamana dake takalmin kaza ne, mutu ka raba, amman ki rubuta ki haddace, ba zan zauna dake ke dayaba wllh, domin ina bukatar mace mai tsoron Allah, ki godewa Allah ina kaunar banda haka da yau kinyi kwanan gidan wannan matsafiya, mazinaciya, kuma mahaukaciyar uwar taki, shashasha kawai."



Fita yai ya barta tana rizgar kuka, kuma duk da haka bata saduda ba, burinta ta samu damar da zata fita taje wajen bokan , ya mata aikin da zai dawo mata tamkar rakumi da alkala.







****

"Ummie, yau kwananki biyar da zuwa, amman mijin naki bai biyo sahu ba, kuma bai kira kowa ba, gashi Abbanku ya kirasa yaki dagawa, ki fadamin gaskiya mai ya hadaku?".



Kuka take sosai, ta kasa magana sai da kyar ta tsagaita tace " Mamah ni fa bansan komai ba, kawai ya dawo daga office yace min wai na shirya za'a kawo ni nan, karna sake na nemesa sai ya nemen dan kansa, Mamah dan Allah kuyi wani abu, wllh ina matukar son Ya Saddiqu, bazan iya rabuwa dashi ba, bazan iya rayuwa babu shi ba, na dai nasan ban masa laifi ba, muna zaman mu lfy cike da fahimtar juna, amman bansan wacce kaddara ce take son fado mana ba kai tsaye haka, dan Allah Mamah kuyi wani abu akai."



Bayanta Mamah take shafawa ahankali cike da tausayin yarinyar, lallabata tayi da dadin baki kan cewa zata aika Ahmad yaje har can, Kadunan ya gano mata maike faruwa.





Karshen wata kuwan Ahmad yazo, lokacin satin Ummie biyu da zuwa, nan suka tattauna maganar, sannan suka tsayar da batun kan cewa zasu je can Kadunan su samesa, bayan kwanan niyu kuwan suka tafi su uku, Mahmuda, Abbah sai Ahmad, da sukaje basu same sa agida ba, sai da suka jira ya dawo sannan suka shiga tattauna abun dake tafe dasu.



Sai wajen yamma sannan suka baro garin jikinsu amace, sai dai kuma sun fahimci juna sosai, kuma sunyi na'am da hukuncin da Saddiqun ya yanke, koda suka dawo gida, iya Mamah kawai sukayiwa bayani, sannan sukace Ummie din zata zauna anan ne har ta haihu, tunda yanzu cikinta kusan wata takwas ne, itama mamah jikinta yayi sanyi, amman tayi amanna da shawara da suka yanke akan batun.





Kulawa saosai suke bawa Ummie, dukda suna kokarin kwantar mata da hanakali, Laura kam ta kuma kintsuwa fiye da da, gashi ita shiru har yanzu ko batan wata bata taba yi ba, tun Ahmad baya kula ta, yanzu har ya kai wani girmanta yaje gani, domin ita kanta tasan ba santa yake ba, amman haka da daure take zaune dashi da zuciya daya, kuma duk wani banbanci da yake nuna mata da Khausar bata taba kallon abunba, balle ta daga kai tayi magana, sannan tana matukar girmama Khausar ga yaranta da suka zama yan dakinta, musamman Akram da tun da aka haifesa ita ke dawainiya dashi, anan yaye sa kuwan Khausar din tace ta bar mata shi halak malak, wannan abun ya kara mata girma da daraja a idan dangin mijinta, ko Hajiya Tako sai gata tana yar matsal kwalla tana basu hakurin iri cin mutunci da tayi musu lokacin auren Laura dain da Ahmad.







***

A gidan Malik kuwan abubuwa sun tabarbare, domin sosai rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, sai dai matsalar da aka samu, su Jidda sun sa amusu farraqu ne domin su tsani juna, sai shi kuma bokan ya musu wani banzan aiki, sha'awa aka sawa Malik ta hauka, wadda indai zaiyi aka goma yana abu daya ba zai ishesa ba, ita kuma Maryam din sai aka saka mata lalaci, yana fara tabata zata nuna bata so, shi kuma ko ta karfi da yaji ne sai yayi, to ganin hakan sai Maryam din take gudunsa, shi kuma si ya tsiri shareta yana mata wasu yan kananun walakanci, sai ya debi yaransa su bar kasar duk weekend, sai monday da safe zasu dawo, domin makaranta, ita kuma ganin haka sai ta hada ya nata ya nata, ta ce goda zata dawo, in yaso sanda yake bukatarta ya neme ta.





Bai san ta taho ba sai daya dawo shida yaransa daga yawonsu, sannan sukaga bata nan, to sun xata tadan fitane ko wajen aiki, tunda tana aiki da wani asibiti agarin, sai daga baya suka tambayi kukunsu yake sanar dasu ai da kaya akwatu ta fita kuma tun safe, nan hankalinsu ya tsahi suka hau neman layinta.



Gashi wayar tata taki shiga, ana fada musu ai layin baya kan aiki, Malik kam kamar yayi hauka, gashi babu damar ya kira gida yace musu ko ta zo, tunda duk sanda sukayi waya da yan gidan idan sun tambayesa ba wata matsala, yakance musu eh babu, yanzu kuma ai baya kira ya tambaye su waiko tazo ba.





Ita kuma Maryam kamar wadda aka hankada, tana sauka a Nigeria, sai ta rasa ina ya kamata ta nufa, kawai sai ta dau shatar mota zuwa Kaduna, ta gwammaci ta je wajen aminiyarta su kashe su binne ba tare da kowa ya sani ba.





_afuwan ba yawa, jiki da jini, ko jiya sai dana dangana da matsafar bature, aka min juyen bakin mai, mu hadu gobe inshaAllah_=ØOÞ.





   *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _36_



Sanda ta sauka amota, abakin get bugawa tayi mai gadi ya bude, kallon rashin sani yq mara, sannan yace mata wa take nema, jim tadanyi ko dai ta fadi sunan mai gidan ko matar gidan, ganin yana shirin komawa yasa ta yi saurin cewa mai gidan take nema.



   Kallon tsaf ya.mata sannan ya ce ta jira, kamar mintuna biyar sai ga Saddiqu ya fito, kallonta yake cike da mamaki, dan kamar bata cikin nutsuwarta ne, rusunawa tayi zata gaidasa, ya dakatar da ita yace su shiga ciki tukun.



   Sai daya bari tadan sami nutsuwa sannan suka gaisa, kallonta yake cike da neman karin bayani, ita kuma saita rasa ma ta inda zata fara, kame kame ta fara mai, ya tsaidata yace,



  "Ina maigidan naki?, ina yaran na ganki ke daya?."



   Kamar wadda aka daka, ta fashe mai da kuka, hankalinsa ne ya tashi yace "subhanallah Maryam mai yayi zafi haka, mai aka miki?."



  Cikin shesshekar kuka tace "Ya Saddiqu ni dai na gaji da auren Ya Malik, kawai arabamu kowa ya kama gabansa, ni yanzu ma na fara tsanarsa, dan Allah ka saka baki su Abbah su raba auren."



   Kai ya dafe yana ambatar 'innalillahi waenna ilairajioun, hasbunallahu waniemal wakeel'.



  Kallonta yayi yace "Malik din yana can tare da yaran ne, ko tar koka zo kasar?".



   Idonta ta goge tace" ah ah, ni kadai nazo, ba wanda yasan na taho ma acikinsu, kuma ni bana son susan ina nan."



   "Kenan har yarannaki ma bakya so?."



Ya tambayeta cike da fargaba, kada kai tayi tace"ah'ah, ni ina son yarana dukansu, kawai shi ne bana son zama dashi, kawai ni dai ku raba auren, idan ba haka ba wllh daga nan ma gaba zan kara."



Shiru yayi yana kallonta, yama rasa mai ya kamata yayi, kayan nata ya dauka ya kai dakin Ummie, sannan tace ta shiga ciki ta huta, zai san abunyi.



    Waje ya fita, nan ya kira Abbah ya sanar dashi duk abun dake faruwa, salati Abbah keyi wanda yaja hankalin Mamah take tambayarsa lfy,  bai bata amsaba bayan su  gama magana da Saddiqu, Ahmad ya kira ya sanar dashi komai, sannan ya kira Daddyn Yusra ya fada masa shima, nan suka tsaida magana akan zasu hadu anan Dutse washe gari dukansu, Ahmad ne dai saboda yanayin aikinsa sai dai yana tabasu awaya yana jin meke faruwa.



juyowa Abbah yayi yanawa Mamah bayani, zaman dabas tayi tana sakin kuka, mai hade da salati, da kyar ya samu ya lallabata akan karta bari yaran gidan su sani, baran Ummie sai abun yai mata yawa, fita yai daga gidan yama rasa ina zai dosa, bangare Malam Saje ya shiga, ya tarar dasu Khausar suna tare da Goggoji shi kuma Malam din yana dakinsa, kai tsaye dakin nasa ya wuce ya same rike da wani littafin addini yana dubawa, gaidasa yayi sannan anutse ya masa bayanin duk abubuwan dake faruwa, murmushi yayi kawai sannan ya janyo wani allonsa na karfe dake can gefe ya janyo tawwada da alkalami, gyara zama yayi ya fara rubutu, sai daya gama tsaf, sannan ya kalli Abbah yace,



"Yaran yanzu suna sakaci da addu'a, sun riki ilimin zamani kamar na zuwa lahira, su suna ganin basu da matsala da wani, amman mai fakonsu yana can yana zuba musu aikin da ba zasu iya maganceshi ba, ku tashe tsaye akansu, ku nuna musu muhimmancin addu'a, amman sakacin gaskiya yai yawa, duk da wani zubin akwai laifin ku iyaye, maganin baki, maganin mayu, duk bakwa nemawa yaranku, sannan idan aka hado yaro da asiri bakusan ku masa ayatusshafa ba, sai fmdai ku fara dana asibiti saboda kunfi yarda dashi, ba dole sammu ya samu waje  zama ba, ya kamata dai ku kiyaye."



   Kada kai kawai Abbah jeyi, domin duk cikin kalaman Malam din babu na yarwa, maganarsa gaskiyace, yana nan zaune har ya gama rubutun ya wankesa da ruwan zamzam, sannan ya dauko mu'uwardi da zuma farar saka, da ruwal khal, duk ya zuba.



   Mayuka ya kuma hadawa, dan shi baya rabo dasu irinsu man zaitun, man habba, man ridi da man darbejiya, hadasu yayi waje daya, sannan ya dauko wani dan kulli abu a tsumma, ya basi yamai bayanin duk yanda za'ayi amfani dasu.



   Su mayukan su zama na shafawarsu, ko kitso za'a musu shi za'a na sawa, sqi wannan rubutun suna shansa, na kwana uku sai turaren dake akulle sunayinsa safe da yamma, sannan ya hada masa da sauran addu'o'i, yace,



   "Ku godewa Allah Saddiqu duk tantirancinsa, ya rike ibada da addu'a, wannan yasa isirin bai tabasa ba, amman ya ninke wadanda sukayi abaibai, suna gani kamar sunyi galaba ne akansa, shi kuma shiri yake akansu, amman batun wancen dan wasan kwallon kafar, ku tunasar dashi addua, matar tasa da ake ganin mai hankali ashe duk zamu ce ta tarar da muje mu, jeka kai musu, Allah ya shige mana gaba."



  Bayan ya fito ya kira Saddiqu ya fada masa yanda sukayi da Mamalm saje, sauran bayanin kuma indan yazo gobe zasu tattauna.





***

   Washe gari kuwan sai ga kowa ya hallara, harda Tako da take can Ruga sai da aka kirata, sai Mahmud yayansu Ummie da yanzu ya kintsu kamar bashi ba, Daddyn Yusra ma sunzo da Matarsa Lubabatu, nan Abbah ya musu bayanin komai, sannan saddiqu shima ya dora da nasa, na zuwan Maryam da tayi.



  Kowa yayi mamakin wannan al'amari, kenan so ake matan duk rayuwarsu ta tabarbare abanza, Tako kam, kuka tasa tace,



   "Duk abunda aka miki Ummie ni ce naja miki, da ban nuna son kai na da son xuciya ba, da hakan bata faru ba, dan Allah ku yafen ku gafarceni nasan alhakin Ahmad da matarsa ma ba zasu barni ba."



   Kuka take sosai saida Abbah ya mata magana sannan tayi shiru, gyaran murya Daddyn Yusra yayi yace"Alhmdllh, yanzu dai komai yazo karshe, kuma bai kamata mutum yana dorawa kansa laifi ba, duk abun daya samu bawa, daman can kaddararren ne, sai dai kai ka zama sila, dan haka sai mu godewa Allah daya barmu da ranmu da lfy mu, idan kana da lafiya wani baida shi, sai ka duba ni'imar da yai maka, maybe ya baka lfy ne dan ka taimakawa mara ita, dan haka godiya zamu masa ba atsaya ana tashin zance ba".



  Kowa kai ya gyada dan sun gansu da bayaninsa, nan Saddiqu yace musu ai yasan wadanda sukayi aikin, domin mijin Jidda ya kirasa ya asanr dashi komai, da fari yayi nufin daukar fansa akan abun, zayi musu kaikayi koma kan mashekiya, amman yanzu ya janye, zai barsu ne da buwayar mahalicci, tunda Allah ya bashi baiwar sanin asirai da makarinsu, suje su karata da halayensu.



  Nanma kowa yayi na'am da zancen, sai batun Maryam zata zauna har sai komai ya lafa, domin idan asirin ya sake su, da kansu zasuyi marmrin ganin juna, sannan Ummie kuma daman saita haihu zata koma Kd.



***

  Bayan sati guda abubuwa sun sauya, domin yanzu Maryam da kanta take zama ta tsara sakonni na soyayya, sai tayi yunkurin turawa Malik kuma sai ta fasa, tunda shi har yanzu bai kirata ba, bai kuma neme taba.



  Abangaren Ummie itama tana cime da kewar mijinta, tun ranar da akayi zaman nan, ya koma, shi ma bai kirata ba, kuma babu wani sako, idan kuma ita ta kirasa bata shiga, sai da suka shiga kwanan na goma ne, sai gasu sun sauka kamar marasa gaskiya, wai ashe nan hadawa sukayi da Malik da Saddiqu kar wanda ya kira matarsa, dan aga wanda zai iya jurewa, ranar kam gidan cike suke da murna.



   Ta fito wanka kenan suakyi ido hudu dashi ya na kallonta, kai ta dauke tana murguda baki ta nufi wajen madubi tayi shafe shafenta, sannan ta bude ma'ajiyar kaya ta daukanta saka, fita take shirinyi , taku biyu kuwa ya danko ta yana wullata gadon, kara ta saka tana shirin tashi yabi ya danne ya hade bakinsu waje daya.



   Sai daya gama luguigui tata sannan ya kyale ta yana sauke ajiyar zuciya, ganin yanda ta runtse ido me yasashi murmushi yace"magulmaciyata, kin gama cinyen baki kuma wai kunya kike ji, ke ko yar kewata bakiyi ba ko", shi kenan daman, dawowar da nayi Malam sajene ya ke nemanin auren wata jikar abokinsa, kinga ke kiyi zamanki anan, mu saimu tafi can da ita, idan na sami lokaci sai nake zuwa."



   Murmushi tayi ta mike take "na iya jure zzama da Sakeena ma, balle wata can daban, Allah ya kawo ta lfy, ai abokiyar zama ce ita din, sannan idan bikin ya tashi zan dau nauyin hada lefe, da kuma kayan na gani inaso, Allah ya nuna mana lokacin, amman dai ba za'a saka da yawa ba ko?."



  Haushi ne da mamaki suka ishe sa, yace "lallai Maryam ashe rashin son da kike min yakai haka, idan na fahinta bakya kishi na ko?, to wllh baki isa ba, ke kadai ce zamu zauna tare, babu wani aure da zan kara duk abunki muna tare iya ni dake, yar rainin wayau kawai, wllh zaki maimaita baunda kika ce ne, zamu koma ainihin gidan mu jibin nan, zaki sani."



   Yana fita ta saka dariya tace"haka kawai ka dorawa kaina hawan jini abanza, ai maganinku kenan, idan kunga ana damuwa daku irin na haukan nan, ai kuma mannawa mutun hauka kuke, yanzu idan ma da gaske auren zaka kara ba gashi ba na ssamawa kaina mafuta ba cikin sauki."



   Shigowar Ummie ne yasa tadan tsagaita da dariyar da take, ita ma dariyar take rikewa sai data zauna sannan tace"wai me ya hadaki da mutumon naki, muna tare da Hayateey yaje ssai muzurai yake, karshe fa kinga koroni yayi, sai masifa yake shi kadai."



   Nan Maryam ta labarta mata yanda sukayi, darita sukasa suka tafa tace"amman baki da kirki wllh, Allah sarki dan uwana, shi yana tunanin ba'a damu dashi ba, nqn kuwan anfi kowa damuwa da lamarinsa."



   Shirarsu suka dan taba, kafin Ummie tadan zame, ta kwanta, Maryam din tana mammatsa mata kafafunta.





*RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*



Please Login or Register in order to submit comment