You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  Sai da Abba ya dawo sannan suma suka hallara ababban falon dan yin dinner, sai kuma alokacin ne suka kula da Laure da Ummilo nan Mama ta sanar dasu ai tun bayan wata uku da faruwar abinnan suka dawo nan da zama, dan ba zasu iya barinsu su zauna acan ba, sai Goggoji da Malam Saje da suka dawo nan suna, suna bangaren da akaware musu.



   Anan suka gama dinnar dinsu, dukda ba sakarwa yaran fuska suke ba amman Ahmad, yayi mamakin yanda Laure yake mai abu kamar taga tsohon saurayinta da suka dade basu ga juna ba, nunawa yayi kamar bai ganta ba awajen yayin daya ringa jan Ummilo da hira, dan ita kawai nutsuwa ba kamar yayarta ba.



   Sai bayan sun koma daki ne Malik ya sashi agaba da tsokana yace" lallai gaye kayi kasuwa, kaga yanda yarinyar nan take narke maka, daman ka fara zama tuzuru kawai ka bada kai bori yahau, musha biki ".



   Fulon doguwar kujera ya dauka yana makamai, shi kuma banda dariya da kuma kular dashi babu abinda yake, yar da filon Ahmad yayi ya zauna yana hararar Malik yace " tsiran mu shekara hudu ne, dan haka kaima ka fara xama tuzurun, tunda ajiyar ka bata nan, sai ka fito da wata kulallaba kanku kawai".



    Da biyu Ahmad ya mai wannan maganar, ilai kuwa sai ga fuskar Malik din ta sauya, karshe ma sai ya bar masa falon ya nufi bed room ya kwanta, zuciyar taf da tunane tunane, ahaka Ahmad ya shigo ya same sa, bai masa magana ba ya zauna ya daura kafafunsa akasa yana dan mammatsa masa su, ahaka yaji yana sauke ajiyar zuciya da numfashi alamar yai barci, gyara mai kwanciya yai ya rage karfin ac, sannan shi kuma ya janyo laptop dinsa ya fara aiki, bai ajiye ba sai  wajen sha biyu sannan yai alwala yai nafilfili sanna ya kwanta.





++++



    Bayan sadakar uku, Bulama ya nemi ganin su Mairoji, suna zaune ta rungume Simrah dan bata iya bawa kowa yarinyar, duk da son da akewa yar adauketa amman haka take nanuke ta, ko da sakon kiran ya isa gareta batayi mamaki ba dan da dama wasu dan su ga yarinyar ma ake cewa za'a mata gaisuwa, da sallamar ta tashiga, sannan ta tsugunna ta gai dasu, ido ta tsurawa babban cikinsu kafin ahankali ta sauke tana jin wani irin yanayi.



    Bulama ne ya fara magana inda ya ce "yarinya fada min suwaye kakannin ki, ta bangaren uwa da uba, karki boyemin komai in dai kina son ki koma ga yan gidanku".



    Kanta akasa ta fara fada musu ko ita wace" kakana na wajen uwa yasha fadamin cewa, su yan Maiduguri amman su kansu basu san dalilin barinsu garin ba, domin dashi da yayansa, da kuma mahaifiyarsu suka baro garin, wanda har yau basu koma ba, sai kakana na wajen uba ayanda naji labari su yan Yobe ne, ci rani ne ya kawo mahainsa Hadejia, har yayi aure ya ahayyayfa, ni ma anan babana ya ga mahaifiyata ya aura, bayan ta haifeni ta rasu".



   Bulama daya gama rudewa yace "yarinya meye sunan kakanki na wajen uwa, da kuma mahaifiyarsa da yayannasa?".



   " sunan mahaifiyarsu Mariya anan ce mata Hajja Gana, sai yayansa Mahmud, shi kuma kakannawa Muhammad".



Gaba daya falon suka dau kabbara, Kawu kam harda hawayen farin ciki, hannunta ya kamo cikin rawar murya yace"ashe soyayyar da nake muku ba ta banza bace, ni nan da kika ganni, da kakanki Da babana ubansu daya, sunan kakanki naci, wannan kuma"ya nuna Mahmud yace "sunan yayan kakanki yaci, mu yayan Saminu ne kanin Baba Gana, yayan kakanki kenan kinga Ammyn ku 'yar Falmata ce itama yayar kakanki, auren zumunci mukayi da ita, Shahuda watau Auntyn ki jikar Safiyya ce, wacce mahaifiyar ki taci sunanta,Alhamdulillah da Allah yasa gida kuka fado, na godewa Allah daya sa na ganku, ke yata ce, mu nan dukanmu iyayenki ne".



   Kuka Mairoji keyi kukan farin ciki da godiya ga Ubangijin daya saukaka mata al'amura haka, jin shessheka yasa suka juya, sai ganin Ammy sukayi ita da Huda sun rungume juna suna kukan farin ciki, da alama sun ji komai, da gudu Huda ta taho ta rungume Mairoji tana jin wata sahihiyar kaunarta tana ratsata.

*RUGAR SAJE*



   By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba .A.S.Sarkin zango



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*

(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_



_9_



    Sai bayan sun kuma samun nutsuwa ne sannan Bulama yacewa Kawu da Mairoji zai koma, nan shima Kawu ya nuna bai yarda ba, da kyar dai suka bar maganar kan cewa zata zauna ne, kafin Simrah tayi kwari sai Uncle Mahmud yazo ya kaita taga yan uwa.



   Da wannan shawarar aka tsaida magana, bayan adduar bakwai suka koma bayan sun bawa Mairoji makudan kudade, sun kuma bude mata acc, Salme kam tuni ta gama shan jinin jikinta, sai yanzu ta gane dawa take zaune, ada tana ganin kamar iya Mairoji kadai akawa alfarmar zama agidan Kawu, amman yanzu ta gane ita akawa alfarmar, kuma ita ke cin arziki azaman gidan, hakan yasa ta rusunar da kai tare da yada duk wani makamin ganin tafi Mairoji, sai dai abun daya ke kara bata haushi yanda kowa na gidan yake nan nan da Mairoji, soyayya ta musanman suke bata, ko kadan basason ganin tayi shiru ko tana tunani, yanzun zasu fara shiga damuwa kowa na nuna kulawarsa akanta.Da fari ta dauke kanta, sai dai  ganin abunda aka aiko mata daga Maid sai ya hautsina tunanin Salmen, sabuwar mota yar yayi ta zamani dai dai hawan mace, ita Kawu Bulama ya aiko mata dan fita, Salme taji takaicin wannan abu, ita aganinta wannan ai wariyar launin fata ce, da nuna Mairojin tafi ta, ko yaushe da wannan bakin cikin take kwana take tashi.



+++

   "Ke Laure...na fada miki ki dena shafan hoda, Allah zan hadaki da Mama, ga naki kayan kyalin can amman saikina taban nawa".



   Harara Laure ta makawa Ummie cikin fada tace " amman wllh ke dai anyi yar bakin ciki, yanzu idan banyi kwalliya yanda zanyi kyau na fito amace ba, taya wancen mai kyan usulin ya tanka, Allah Ummie ina matukar son Ya Ahmad, nifa idan bashi na auraba...to bani babu aire, kuma shima haka, dan bazan bari wata ta aure sa ba ina gani".



   Baki Ummie ta rike, tana mata kallon baki da kai, daman ba tun yanzu ba tasan Laure tana son Ya Ahmad, sai dai bata zata abun yakai har tayi ikirarin idan bata same sa ba , ba bu mai samunsa. Zama ta gyara tace "Laure shawarar dazan baki, wllh ki kama kanki, kinga Ya Malik yafi Ya Ahmad fada da masifa, amman hakan ba yana nufin Ya Ahmad bai da fada ba, kinsan halinsa idan ya ganoki tsab zai iya maidake Ruga kije ki karasa rayuwarki acan, kuma banda abinki ai kwarya tabi kwarya, ina ke ina nagartaccen namiji irin ya Ahmad, Allah ki raba kanki da wannan shirmen naki dan babu inda zai kaiki".



   Juyowa Laure tayi tana kallon Ummie, murmushi ta saki sannan tace " ban taba zaton kina cikin masu mini hassada ba Ummie, amman yau kin fallasa kanki, wllh kamar abakin Hajiya, sai na fada mata, karfa ki manta dalilin zuwan mu gidannan, ke kisan yanda zaki janyo hankalin Malik ya soki, ni kuma Ya Ahmad ya so ni, kinga damu da uwarmu duk mun huta, mun auri matasan dake jin da gayu da naira, matsan da ake ji dasu akaf fadin garin Dutse, kiyi tunani da kyau, idan kuma bakin ciki da kyashi zaki tsaya, sai nace Allah bada sa'a".



   Baki Ummie ta saki tana binta da kallon mamaki, ta san dalilin da Hajiya Tako ta turosu Dutse, dan su aure yaran Baba Badamasi, amman ita kam bata jin zata iya bada kanta ta nuna tana son namiji, karatunta tasa agaba idan Malik ya nuna yana ra'ayinta, tabbas zatayi farin ciki, idan kuma bai nuna ba, amatsayinta na kanwarsa zata mai addu 'ar Allah ya kawo masa mace ta gari, ita ma haka, amman ba zata iya aikata abinda Hajiya ta turo su yi ba.

   Tashi tayi ta nufi bandaki ba ta kuma bi takan Laure da take feshe jikinta da turararruka ba.



    Kasa ta sauko jin muryansu suna ta faman hayaniya, duk da ba masoya hayaniyar bane amman idan suka hadu da juna, kamar sa cinye namansu danye, cikin tafiya mai daukar hankali take takowa, har ta karaso inda suke, sallama ta musu bayan ta zauna akujerar dake fuskantar ta Ya Ahmad, wayarta ta dauka tana danne danne, dudka hankalinta daya tafi ga jarumin nata, sai dai abin takaicin ko kallo bata ishesaba, karshe ma tashi yayi yacewa Malik yazi ya rakashi wani waje.



    Kamar ta fasa ihu haka taji, amman dake tana dauke ne da shawarar Hajiya akanta sai tayi saurin cewa"laa...Yaya nazo na rakaku mana, daman ina son yin siyayy...."wani banzan kallo Malik ya aika mata dashi, kafin ya saki tsaki ya fice daga falon, Ya Ahmad kam tuni daman ya fice ko sauraron shirmenta ma baiyi ba.



  Yana fita ya fara mita"wllh wannan yarinyar ta kusan barin gidannan, wannan inskanc8n nata bazan dauka ba, ayi yarinya babu wani kamun kai, sai rashin tarbiyya da rashin kunya!".



Ahmad bai magana ba sai da suka shiga mota ya tayar, sannan ya dan kallin gefen da Malik yake yace "ba zata bar gidannan ba, amman zatayi danasanin zaman ta agidan, ba nason ka kuma nuna mata komai".



Da haka suka fita taga gidan, Ahmad na taisar Malik dan ya dau zafi da abun.



.++++





Bayan shekara biyu, Mairoji Simrah tayi wayau sosai, wanda alokacin ne Mairoji ta gama sakandari, inda Kawu Bulama ya nemi data koma can Maid da zama, badan sunso ba haka aka fara shirin komawarta can, ga bikin Anti Shahuda da za'ayi da Ya Salman, kuma can Maid din zasu ayi komai acan.



Lokaci na karatowa har tafiyarsu ta zama saura kwana uku, dan idan sunje da sati za'a fata biki.

Kuyi hakuri, wllh banda lfy ne, kuma kunsan sanyi ake, ina da mara lfy, shiyasa kuka jini shiru, kuma typing din kadan, afuwa=ØOÞ



    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



     _10_

  Ana washe gari zasu tafi Maid, suka fita dan yin wata yar siyayya, dan so suke idan sunje, basai sun yi wata fita ba, sun huta.

    Kasuwar kantin kwari suka shiga, bayan sun gama siyayyarsu ne Mairoji tace tana bukatar wani less, da ta nunawa mai shagon sai yace taxo ya kaita inda zata samu, sunan basu da shi, shagon cike yake da kalolin lasalasai da alama irin pieces dinnan ake dillar sa awajen.



   Sai data gama dubawa dakyar ta sameshi shima kuma yadi uku ne, bayan an saka mata shi alaida ne taji wata murya abayanta kamar tasanta, da kamar ba zata jiyo ba, sai ta kuma jin muryar sosai, da sauri ta waiga bayanta, idan ba zata manta ba, wannan fuskar ta santa kusan shekaru uku da suka wuce, matsowa tayi kusa da mutumin tayi mai sallama, dago wa yai yana amsawa.



   Da kallon mamaki yake binta,kafin kuma ya saki murmushi yace"Maryam Malik, kece agarin yau, ko aure ne ya kawo ki nan" ya maida kansa ga Simrah dake hannunta ke cikin na Mairoji, daukar yarinyar yayi yace "mashaAllah Maryam yarki mai kyau da ita, sai dai ta fiki kyau, dukda kamar ku daya, amman ta fiki hasken fata".



   Murmushi tayi kawai ta sunkui dakai tana gaidashi, amsawa yai yace" tare da maigidanna ki kike ne, ko ke kadai?".



   Kai ta girgiza tace "ah ah...ni da yan uwa nane, maigidanan Allah yamai rasuwa tun kan na haifi yarinyar".



    " Allahu akhbar.....Allah ya jikansa, Allah ya raya abinda ya bari, muje na gaisa da yan uwan naki ko, nima nazo ganin wani ne, kuma ban same sa ba".

   Suna shira suka karasa har wajen su Anti Huda dake zaman jiranta, gaisawa sukayi da ita Hudan sai Salme data gaidashi tana mai kallon sani, kasa shiru tayi tace"kamar Mlm Saifuddin wanda ya koyar damu a Rugar Saje".



   Kai ya gyada yana mata murmushi yace "ni ne Salme Yahya Me-Mai, ashe tare kuke anan ".

  Tace " wllh kuwa tare muke, daman kai ai dan garinnan ne ko".



Yace "eh....anan nake iyaye na da iyalaina, ya karin hakuri kuma?".



    Kallon Mairoji tayi aranta tace'uwar kilibibi watau har ta fada masa mutuwar Bad'ejo' kanta ta sunkuyar irin an tabo mata abu mai mahimmancin data rasa, tace " hakuri mun gode Allah".



   Cike da tausayawa ganin yanda lkc daya ta sauya yace"ayya Allah ya jikan rai, Allah ya raya abinda aka bari".

   Gaba daya suka amsa da ameen, sannan suka fito inda sukayi fakin motarsu, sai da suka shiga sannan ya mikowa Mairoji wayarsa cikin kasa da murya yace"Maryam ko zan samu number dinki pls, ma dunga gaisawa, ai yafi mu rabu haka ko?".



   Ganin taki karbar wayar yasa Huda dake mazaunin direba ta miko hannu ta karbi wayar tasa mai lambar tana hararar Mairojin, sannan sukayi sallama ya nufi motarsa, su kuma suka tafi.



   Tun a mota ya kirasu kafin su karas gida yace ga lambarsa nan tayi save dinta, da to kawai ta amsa mai bata kuma bi takan wayar bama, har suka isa gida.



Da dare ne suna yin dinnar ya kuma kiranta, tashi tayi ta koma daki sannan ta daga, bayan sun gaisa ne yake tambayarta yasu Malam Alhaji, da sauran mutan Rugarsu, amsa mai tayi da suna lfy, sannan cikin kwantar da murya tace"Mlm Saif dan Allah Rugarmu awane jiha take?".



Shiru yai sannan yasa dariya yace"lallai Maryam, kice zaman kano yasa kin manta da sunan jihar ku, gaskiya dole abawa Kano babban kyauta, to dai ku akaramar hukumar Jahun kuke, jigawa kenan".

Tun daya fara daman da yar jotter dinta da biro, yana fada mata kuwan tana rubutawa, godiya tamai tana shirin ajiye wayar, yai saurin tsaidata yace "Maryam dan Allah tunda yanzu kinga mu ba yara bane, ki bani dama, na shigo sawun manema, ko Allah zai sa na dace".



Numfashi ta sauke, tace" zanyi tunani akai, amman kuma jibi idan Allah ya kaimu zamu tafi Maiduguri, kuma ba lallai bane na dawo nan, maybe na tafi kenan ni da nan, sai ko ziyara".



"Garin masoyi baya nisa Maryam , duk inda kika shiga zan biki indai zaki bani damar hakan".

" ba komai, Allah ya tabbatar mana da alheri".

Kafin ya kuma magana ma ta yanke wayar tana binta da harara, ita fa, babu wanda zataso, mutum daya take so, kuma shi zata ci gaba daso har karshen rayuwarta, "Ya Ahmad" ahankali ta furta sunan tana jin wani shauki na ratsa ta.





++++



Ranar da zasu tafi fitar asubanci sukayi, amman duk da haka sai azahar suka sauka, tunda tafiyar mota ce, babu yanda Kawu Bulama baiyi dasu ba akan su biyo jirgi amman Mairoji tace ah ah, ita tsoron jirgi take balle kuma hawansa.

Tun daga yanayin unguwar da suka shiga ta gane ashe sudin ba kananun mutane bane, gidaje ne kusan iri guda ajere wanda sunkai hamsin dama da hagu, sai wani wanda yafi ko wanne girma da tsaruwa da ke kallon kan titin unguwar, wanda yafi girma nan suka shiga, anan suka tarar da mutanen dake tsimayin zuwansu, kamar ana dan karamin biki, ga yan mata da samari da iyayensu, idon Mairoji ne ya ciko da kwalla tanajin farin cikin ganin danginta, ahakali suka fito daga motar da yawanci munen wajen sun yanyame ta ana wa su Kawu sannu da zuwa, sai masu tsokanar Huda da Salman wai ga amare da angwaye.



Gaba daya aka dunguma aka shiga ainihin cikin gidan, sai bayan sun yi wanka sun ci abinci ne sannan aka suka nufi babban falo dan ganawa da sauran yan uwa, wani farin dattijo Maoiroji ta gani wanda kamarsa da Malam Alhaji har ta baci, kasa suka zube suka kwashi gaisuwa, sannan ne wata mata itama dattijuwa ce ta kalli Mairoji tace "ikon Allah ga wata mai kama da marigayiya Yaya Falmata, sak babu abin daya rabasu sai kuruciya"

Gaba daya falon aka maida kallo kan Mairoji data kasa dauke kanta daga kallon wannan dattijon, Kawu ne yai gyaran murya sannan ya fara basu labarin yanda suka samu su Mairoji, da zaman da sukayi awajensu, har rasuwar Bad'ejo da zuwan da su Bulama sukayi, wanda sai anan suka san Mairojin yar su ce.



Gaba falon kabbara aka dauka, masu arahar hayawe har sun fara kuka, wannan dattijon shima kuka yasa, cikin muryarsa da kana ji kasan tsufa ya gama dashi, yace"zonan....zo 'yata, zo naji dumin jikinki, kakanki shi ne dan autanmu gaba daya, son zuciya da rudin duniya suka sani aikata babban suksuren da nake nadama ayanzu, taho nan".



Da rarrafe ta karasa wajensa ta kama hannunsa tana kuka sosai, ita kuwan wane aikin alheri tayi da Allah yake hadata da danginta aduk inda tasa kafa, sai bayan sun gama koke koken su ne sannan ta bada labarin abindaya faru dasu wanda yaja barinsu gida.

Kowa mamaki yake, yan matan da samarin kuwa abin daya fi basu mamaki da burgewar jin cewa wannan dan wasan kwallon kafa da kowa yasansa, Malik B.M ashe dan uwansu ne, take yan matan ko wacce ta fara hangowa kanta tare dashi.



Sai bayan an gama nutsuwa ne sannan Ishaq jikan Baba Lawal yake sanar dasu yaui waya da Saddiqu, shima yace karshen watannan zai dawo gida ya gaji da yawon duniyar da yake, tuni matan suka fara gunguni dan Saddiqu shi ne dodonsu, har mazan ma bai raga musu dan mugu ne lamba daya.



Duk wata kulawa da wani gata Mairoji tana samunsa awajen yan uwanta, kowa so yake ya jata ajiki(kunsan duk kudinka idan baka da kyau, ba kowa ne zai ce yanayi dakaiba, amman idan kana da dan kyanka, har fariya ake anunaka amatsayin kawa ko dan uwa=Ø4Þ=Ø6Þ).



Da haka aka fara shirye shiryen biki, dan sun bari idan aka gama hidimar bikin zasu dunguma zuwa can Rugar Saje, dan ganin juna.





++++



"Malik...wai da gaske zuwa Maid dinna zakayi, watau kaima ka koyi giringidishi bikin kawar kawa ko?".



Murmushi yai yace" broh....na fada ma badan bikinnan zani Maid ba, wllh ji nake kamar kirana akeyi acan din, kuma kaima ka sani Salman tsohon aboki na ne, duk da ba shi ya bani katin bikinsa kai tsaye ba, amman ai cewa yai atabbatar ya iso gare ni, ni dai tunda ba zaka ba kawai ka dena min magana, ba ruwana da kai, har na dawo".



Yanda ya karasa maganar yana tura baki, sai ya bawa Ahmad dariya yace"sory....dan autan Mamah, dan autan yayansa, kaima kasan banda asatin sama zan koma wajen aiki iada tare zamu ko, kayi hakuri kaji bansan na kumayi laifi irin wannan karo, kusan shekara biu kenan ziwan da mukayi kaga sai dana kara kusan sati uku ban koma ba, kuma duk saboda kai, kayi hakuri to ai bikin naku ne, kune angwayen, Allah yasa kana zuwa ka hadu da yar furanniya ta min gaba da zuciyarka".



Cime da sakalci ya dafe saitin zuciyarsa yana lumshe ido yace"broh...ina ajiki na wannan furanniyar data dade da tafiya da zuciyata kamar ita zanje gani, kar ka damu, nest hutun da zamu dawo sai maganar aurena".



Ya fada mai yana kanne mai ido daya, duka Ahmad ya kai masa akafada, yana dariya yace"yaro ya girma fa, dole ma na maka aure matarka ta karata da kai da shirmenka".



Cike da kaunar juna Ahmad ya taimaka masa ya hada kayansa awata yar jaka kamar ta goyo mai kyau, dan washe gari zai tafi Maid bikin tsohon abokinsa Salman.



   *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



   _11_



   Ranar da mata sukayi taro kamu , ya kama laraba ne, kamu sukayi irin na asalin kanuri, hatta da kofunan wajen kamshi suke, haka duk wanda ya gifta sai kaji kamshi na tashi.

   Awajen ne wani dan uwansu Gimba ya makalewa Salme, da fari taki kulashi, sai daya fito da wayarsa da aka kirashi ya daga, zaro ido tayi cike da mamaki domin, iphone 12 ce, ita tunda take bata tabajin ance gamai irinta ba, sai dai tana tsintar labarinta amakaranta bakin kawayenta.

   Sai bayan ya gama wayar ne ya dawo kanta yace "Salma, kinyi shiru da gaske nake fa, bada wasa nazo ba, tun zuwanku da ganinki hankalina ya kwanta, nasan na samu matar aure na".

   Kai ta sunkuyar tana sakin murmushi, itafa ko kadan bai mata ba, kawai dai taga kamar yana da masu gidan rana, dan haka zata je dashi ne, kafin ta samu wanda ya fisa.



Ganin ya samu karbuwa ne ya nemi ta bashi number dinta, amman sai tace ai bata da waya, wayarsa ya daga yai kira, bayan kamar mintuna goma sai ga wani yaro ya shigo wajen da ake taron, mika masa leda yai ya fita shi kuma ya mikawa Salman yace ta bude.

   Ido ta dan zaro ganin kwalin sabuwar wayar infinix hot 8, dagowa tayi ta kalle sa zatayi magana, yace" u deserved it baby, indai kin amincewa aure na baki da matsala dani".



    Marairaice fuska tayi tace "amman kyautar tayi yawa, wayace fa mai tsada, kuma daga haduwar farko?".



    Shima langabe kai yayi yace" ai duk tsadarta bata kaiki ba, kodan mu bar wannan maganar, muyi abinda zai fi mana muhimmanci ko".



+++



    Washe gari sukayi wani taron su na maza da mata(na manta sunan sa, amman baribari kun san shi ai), awajen ne ango zai bawa amaryarsa kyauta, ta bajinta, idan dangin amarya sunga kyautar ta musu, sai su rama masa bayan ankai amarya, da duk abinda suka san zai sai mata daraja.



  Aranar ne Baba Gana yaga Simrah, dan tun zuwansu bai ganta ba, tana can yan mata na daukarta, dan yarinyar badai farin jini ba da shiga rai, kura mata ido yayi cike da faduwar gaba, cikin sarkewar harshe yace"kai ku nemo min Bara'u, maza".

da saurin su kuwa aka kira Baba Bara'u awaya, aka sanar dashi kiran da Baba Gana yake mai, koda yazo bai saurari gaisuwar daya kawo masa ba ya nuna Simrah, bakinsa na rawa yace "sak fuskar Saddiq, wallahi wannan jinin Saddiqu ne, duk inda yake wannan jininsa ne".



Kallon Mairoji yayi yana hawaye yace, " yar nan, ina kuka ganemin Saddiqu na, wannan 'yar sace na tabbata, wannan jininsa ce".

Abun daya ke ta maimaitawa kenan, hawaye nabin fuskarsa, kwantar mai da hankali akai, da cewa ai Saddiqun ya kusan zuwa akarshen watannan, da haka suka lallaba suka baro wajensa.

Adakin da yan matan suke taruwa Mairojin take tambayar wata Fannah, waye Saddiqun da ake fada.



Gyara zama tayi tace"Ya Saddiqu alabarinsa babu abin dauka,shi ne jikan Baba Gana na fari, mugu ne na bugawa ajarida, idan yana gidannan bamu isa muja numfashi da kyar ba, ko mazan gidan tsoronsa sukeyi, yanzu shekara kusan bakwai kenan baya nan, ba'anan inda ya tafi ba, amman awasu radi radin ance, ya hadu da yan kungiyar tada kayar baya ne, da shi yaron su ne, kafin shi ma ya zama ogan kansa, kuma ahakan kaf cikin jikokin Baba Gana yafi son sa, bama iya Baba Gana ba, har sauran iyayen mu maza da mata, yana da wani irin farin

Please Login or Register in order to submit comment