You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai yazo , ya kusan awa ma da sauka, sai tace mai ai itama tana wani waje ne, amman zata kwatanta mai yanzu yazo, baiyi musu ba ya amsa sannan suka kashe wayar.

    Cikin mintuna kalilan ya isa inda ta turo masa da kwatancen, awajen wani gida mai kyau ya ganta, da murmushi akan fuskarta ta kama hannunsa tace "dan Allah muna shiga ka rufe idonka kaji, wani abu zan nuna maka."



   Hararar wasa ya mata sannan suka shiga ciki da sallama, idon nasa ya dan lumshe yana shakar kamshin da gidan yake, sai da suka zo tsakiyar gidan sannan ta tsaya ta ce masa ya bude, ahankali yake ware su tas ya sauke su akan mutumin da yake ganin kamar basu da maraba sai na girma da manyanta, idonsa ya murza yana kara matsawa kusa da mutumin dayake ta sakar masa murmushi, sannan ahankali ya maida kallonsa ga Maryam da itama take sakin masa nata murmushin.



     Kallon hutuma da tambaya yake mata, sai kawai tamai dariya ta koma kusa da Uncle dinta ta ce"Uncle Abdulmalik Muhammad  Saje, kanin Abba yayan mamana kuma."



    Kallonsa Malik ya mayar kan Uncle din murya na rawa yace "da gaske kai ne? ashe zamu kuma ganinka, tsawon lokacin nan kana raye amman babu wanda ya sani, dan Allah kaine?kar ya zama gizo kake mana."



   Murmushi Uncle yayi yana bude masa hannu alamar ya taho, da sassarfa kuwan Malik ya shiga jiki sa yana sauke ajiyar zuciya, farin ciki ne ke dibansa, ji yake kamar ya taka rawa, sai da aka gama nutsuwa tukun na, sannan Malik ya tambayesa bayan rabuwa mai ya faru da shi, ya akayi kuma yazo nan.



     Shafa kansa yayi cike da kulawa da kauna yace"zan so na baku labarin abin daya faru yanzu, sai dai kuma da zakumin hakuri zuwa bayan shan ruwa, kunga yanzu karmu cinye lokacin mu anan gashi yamma ta farayi."



  Kai suka jinjina sannan suka ci gaba da firar yaushe gamo, sai da sukayi sallar la'asar sannan Malik ya kira Sakeena yace ta shirya zaizo ya dauke ta, akwai inda zasuje, to wajen magriba yaje ya dauko ta suka taho nan gidan, ita sai ranar ma taga Maryam tunda suka zo, sai kuma take kallon Uncle cike da mamakin kamanninsa da Malik dinta, sai dai tabar abun batayi mahana ba, har sai bayan da aka sha ruwa.



     Anan ne yake fara fada musu yanda akayi, yace "lokacin da kwale kwale ya nitse damu kasa nayi tunda daman ban iya ruwa ba, to bansan dai yanda aka yi ba na ganni ne awani waje sai bayan na dawo hankalina,  sannan na kula kamar a kurkuku nake, sai bayan kwanaki sannan wasu mutane larabawa da bakar fata su biyu suka zo suka fitar dani,anan naji wai tsintata akayi gaban wani ruwa da ke Nijar, shi ne wadanda suka tsinceni din suka iyo safarata zuwa nan, to kuma sai aka kamasu da hodar iblis, shi ne nima na shiga cikin, shi ne su kuma wadannan suka nemi fita dani akan zan amsa wani laifi ne su kuma zasu dau nauyin zamana anan har karshen rayuwata sai dai kuma ba damar na fita daga kasar don da zarar nayi kokarin fita, to abin da suka boye ne zai bayyana, daga nan kuma hukuncin kisa ne zai tabbata akaina.

Badan na so ba na amsa da hakan, aka fito dani, sannan suka hadani da wani malamin addinin musulunci dan na samu ilimi, to sai Allah ya hada jininmu dashi wannan malamin har ya nemin jin tarihina, nikuwa na fada masa komai , acikin yaransa akwai wadda muke mutunci da ita sosai, daga karshe dai soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu, har mahaifinnata, kuma malami na ya bani aurenta."

Ya juya yana kallon Bahiyya dake sunkui da kai, murmushi yayi yace"Shugabar yan kunya, wasannan ya'yanki ne ai, duka babu surukai anan, ki dena wani jin kunyarsu."



Kai ta dauke tana son danne kunyar sake taso mata, anan kuma ta janye matan suka koma dakinta da yaran.



Bayan kwana biyu aka yi karamar sallah, ana cikin hidiman sallah kuma Malik yana can yana kokarin zama da manyan kasar, akan lamarin Uncle dinsa, so ba'a dau wani lokaci ba aka wanke Uncle Malik insa aka gane baida wani laifi, daman ya amsa ne saboda ya kubutar da rayuwarsa, bayan sati guda kuma suka gara shirin dawowa gida gaba dayansu.





_Alhamdulilla, anan zan dakata kuma sai Allah ya nuna mana bayan sallah, kuyi hakuri dani naso gama littafin ne kafin azumi sai dai halin dana ke ciki na yau lafiya gobe cuta yasa nake jinkirta rubutun, kumin addu'a dan Allah, idan Allah ya bani lfy da tsawon rai zuwa bayan sallah zaku ganni, idan kuma lokaci yayi sai na ce Allah ya sada mu da rahamarsa, wllh ina jin jiki dan Allah kusa ni a addu'oinku, Allah ya bamu lfy mai albarka da amfani, ya bawa sauran yan uwanmu musulmai lfy, wadanda suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya jikansu, idan tamu tazo yasa mu cika da imani._





   *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _28_

 

   _MashaAllah, Alhmdllh barkan mu da karamar sallah,barkan mu da shan ruwa, Allah ya karbi ibadunmu, yasa muna daga cikin yantattun bayi_.



    Babu wanda yasan da dawowarsu sai Ahmad, sai suka bar abun amatsayin zasu musu ba zata ne, sati biyu dayin sallah suka tattaro gaba dayansu har yaran uncle din suka taho 9ja.



   Ba tsammani kawai sai ganinsu akayi, Abbah ne ya fara yin tozali da kaninsa Malik, yayin da suka shigo gidan shi kuma yana niyyar fita, tsayawa yai yana kallon d'ansa malik da kuma kaninsa dako bayan daruruwan shekaru ne suka shude bazai manta dashi ba, bai dawo daga mamakin ganisa ba sai ji yai an rungume sa an fashe da wani irin kuka, cikin muryar da duk wanda yaji yasan mai ita dauriya yake kawai ya ce"Abdulmalik, kai ne yau agaba na, bayan tsawon shekaru yau gani gaka, na godewa Allah daya dawo mana dakai lfy, kuma iyayenmu zasu ganka kafin su koma ga mahaliccinsu."



    Dagosa yai yana goge masa hawayen, yai dan murmushi yace"to kuma kai kana kuka, idan yaranka suka gani suma suyi ko, share hawayen mu shoga ciki ko?."



  Gaba daya suka yi masauki ababban falo, nan danan aka fara bugawa yan uwan nesa dana kusa, ana sanar dasu dawowat Abdulmalik, kan kace kwabo tuni har jama'a sun taru sosai, Hajiya Tako ma tazo da nata tawagar, sosai ake cikin farin ciki baran ga dattijan su agefen su.



   Cikin kwanaki kadan yan uwa duk sun zozzo an hadu an gaisa bayan kwana biyu suka shiryawa zuwa Maiduguri, sai dai  banda Maryam , dan kamar cikinta jira yake suzo gida ya bayyana kansa, laulayi take sosai, to sai Mamah ta hana tafiya da ita, ba haka Malik yaso ba dan yana matukar bukatar matarsa akusa dashi, haka dai akayi tafiyar harda Khausar matar Ahmad.



  Satinsu daya suka dawo, wanda ya rage sauran sati uku bikin Laura da Ahmad, sosai acan Rugar Na-ma'u Hajiya take shiri, gashi sun samu yanda suke so da Ahmad din, tatsarsa kudi suke kamar shi ne masarrafar kanta, abangaren Khausar kuwa Maryam da Mamah ne ke kwantar mata da hankali dan da fari taso daga hankalin nata, sai daga baya da suka mata nasiha da nuna mata muhimmancin karbar kaddara sannan ta samu ta nutsu, Sakeena kam dama bata dawo ba sai gab da bikinsu Laura sannan zata dawo.



   Kwana uku ya rage afara shagalun biki yan Maid suka iso, harda Sakeena da mamanta, da yan dakinsu Saddiqu, sai dai shi bai zo ba sai ran daurin aure, sai dai tunda suka dawo Malik bai sanya Sakeena a idonsa ba, sai dai bai damu ba tunda shima yasan ba ta gabansa ne, matarsa da abin cikinta sune yanzu damuwarsa.



RANAR DAURIN AURE/BAKAR RANA.



     Tun safe na tashi gabana na wata irin faduwa, kasa daurewa nayi na samu Mamah adaki ita da ummie suna shirya wasu kaya acikin kwalaye, zama nayi kusa da ita idona taf da kwalla nace " Mamah kamar bani da lfy, zuciya ta bugu take kamar zata fashe."



Juyowa tayi ta kallen, sannan ta zauna kusa dani tace"kina matsayin yar musulmai, wadda tasan addini, mai yasa ba zaki lazinci addua ba, ki tashi maza kina sakaci kwannan, na kula walhar da kike kinja baya da yinta, maza lkc na kurewa tashi kiyi sallah ki mikawa mai duka kukanki."



Ayanda naga tana magana, sai na kula kamar itama tana cikin yar damuwa ne, dan haka sai na tashi na nufi bandakinta nayo alwala, nazo na gabatar da walhar, sannan na zauna ina mika lamurana ga Allah tare da adduar samun sassaucin abunda ke shirin kusantoni.





**

"Wai ke dalla Jidda banson hauka, kina jin abunda mutumincan ya fada, kar wanda ya ganmu sanda muke aiwatar da aikinmu, ke kuma kowa kika gani sai kin masa magana ke gaki kinsan mutane ko? wuce ni muje lokaci na kuremin."



Baki Jiddan ta tura tace"ke fa wllh Aunty aka hada aiki dake sai kin addabi mutum da masifarki, banda abunki ai dauke mana hankalinsu nake, idan aka ga mun wuce bamuyiwa kowa magana ba, ai dole a zarge mu, amman yanzu da muka gaisa da wasu ba shikenan ba, babu wanda hankalinsa zai hau kan mu".





Tsaki Sakeena tayi , sannan ta karasa jikin wata yar bishiyar fulawa, haka tayi mai dan zurfi sannan ta ciro wani abu kamar ruwa sai dai kore ne sosai, kuma idan ka kura ido kamar hayaki ne yake dan tashi, sai wani irin wari mai masifar hawa kai dayake tashi, abun ta saka acikin ramin sannan, ta maida kasar ta rufe tana fadan wasu irin maganganu idonta rufe, ta fi mintuna goma sannan ta kammala da ambatar sunan Maryam da Malik, tana gamawa suka juya suka tafi sunawa juna murmushi .







** Malik kuwa yana daki ya gama shiryawa dan tafiya daurin auren, dukda bai so zuwa ba amman Abbah ya tilasta masa, kamar wanda aka tsikara ya tashi yana waige waige, sai can kuma ya dafe kansa dake masa wata irin sarawa, futowa yai adaddfa ya nufi dakin Mamah,dukda gidan ya fara tara jama'a yan tafiya daurin aure, adan koridon da zai sadaka da dakin mamah yaci karo da wani , yana dubawa sukayi ido biyu da Saddiqu daya sha kyau cikin dakakkar danyar gazner sky blue, harara Malik maka masa sannan yai wucewarsa yana jin wata mahaukaciyar tsanarsa tana mai kaikawo akwanya.



Kamar wanda aka jefo ya fadon dakin ko sallama babu, damkar gashin Mairoji yayi cike da wutar masifa yace"ubanwa ya kawo wancan dan dabar gidannan?, ke kika kirasa ko?, watau ni zaku ciwa amana ko, ni zaku ha'inta, shi ne kika kirasa dan yazo ku hadu ......"

Bai gama fadar abun dake bakinsa ba yai saurin angizata yana toshe bakinsa da hancinsa, kan wani daurin kaya ta fada don ta tafi ruf da ciki ne, take ta saki wata irin kara tana dafe cikinta, har cikin kahon zuciyarsa yaji karar tata, yai saurin runtse ido yaba daka mata gigitacciyar tsawa yace"dallah kimin shiru, kin cikawa mutane kunne da ihun banza da hauka, karya na miki ne ai na gansa yana fita daga nan dakin tsabar cin amana, kije duniyace ta isheki darasi Maryam tunda har da aurena akanki amman kina iya kiran taohon saurayinki har daki, dakin ma na uwata, na gode."



Dai dai zau fita kenan Mamah ta fito daga bandaki don daman tana ciki, tsawa ta daka masa tace"dawo nan mahaukaci, daka nemi kashe musu 'ya, wa kake tunanin zai dau maka ita, maza dauketa kuyi asibiti kana ganin sai zubar da jini take".



Kai ya gyada idonsa taf da kwallar bakin kishi da zafin rai yace"bazan iya taba wannan najasar ba Mamah, kiyi hakuri amman wllh bazan iya dora hannuna akan Maryam ba, da aure na.....da aurena fa take...."



Kuka ne yake son kwace masa yai saurin barin dakin, da sauri Mamah ta karasa wajen Mairoji ta tallafeta, wayarta ta janyo ta kira Hibbatu kanwarta da daman tana gidan, cikin lokaci kadan ta shigo, ganinsu ahaka ba karamin rudewa tayi ba, da sauri ta dau wayarta ta kira likitansu tamai kwatancen gidan akan lallai yazo yanzo, ita Mamah ma sai yanzu tunanin kiran likita yazo kanta, cikin abin dabaifi muntina ba kuwa yazo, da sauran wasu likitocin mata biyu dan Hibbatu tamai dan takaitaccen bayanin abundayake shirin faruwa.





Kusan awa aka dauka kafin aka samu komai yai normal,nan suka sanar dasu ai cikin ne yai barazanar fita, amman yanzu an samu ya zauna, sai dai za'a kiyaye sosai banda daukar abu mai nauyi da kuma aikin karfi, har sai kicin yai wata hudu zuwa biyar kafinanan yayi kwari, kafin nan kuwa tuni zance ya baza Maryam ba lafiya za tayi bari, Sakeena na kan gaba wajen nuna tashin hankalinta, har da fake tear dinta kuwa, nan dai ta zauna tare dasu Mamah da Ummie dataki matsawa konan da can, suna haka yan daurin aure suka dawo, anan mazan gidan suka san san abundake faruwa, sai dai Mamah bata fadawa kowa musababin abun daya janyo hakan ba, ta dai ce musu Maryam din ta zame ne abandaki.



Malik kam, yana komawa daki, ya zauna bakin gado ya dafe kansa, tunani yake mai ya kaisa aikatawa matarsa abar sonsa haka, ko banza ai tana dauke ne da gudan jinisa, kuma ita din zabin sace, bai kamata ya mata wannan bahagon hukuncin ba, wayarsa ya janyo zai kirata yaji sallama hade da nocking, ajiyewa yayi yaje ya bude, Sakeena ya gani ya matsa mata ta raba ta gefensa ta shige, gefen gadon ya koma ya zauna, itama ta zauna kusa da shi, sai data gama karantarsa ssannan ta dan sassauta murya tace"kaje ka duba Mairoji kuwa?, tana jin jiki fa, kamata yiyi ace kaine yanzu awajenta ba wani ba, kai kana matsayin mijinta amman ace wani can daban yaje yana bata kulawa, hakan aganina bai dace ba, duk dadai dan uwane shi ma, amman ai kafi kowa kusanci da ita."



Kallonta yayi idonsa kam akanta, cikin kaushin murya yace"waye wani din dake wajen nata?, mai yake yi, mai ya kaisa?."



Mirmushi tayi aboye tace "ah'ah, bafa wani bare bane, Ya Saddiqu ne naga yaje sai shige mata yake ita kuma sai kara narke masa take, abun daya kai ya kamata tana yiwa ba wani ba, amman fa ban fada maka dan kaji haushinta ba, kar ka jaza mun ace na hada fada."



Bai bari ta karasa ba ya mike ya fice da sauri, dariya ta sheke da ita sannan tabi bayansa dan bata son kallo ya wuce ta, dai dai ya bude dakin ya sa kai kenan, Mamah ta dagota shi kuma Saddiqu ya na gyara mata zaman filon, ita kuma Mairojin tana kallon Saddiqun ne damai dan murmushi da jinjina kai alamar godiya, kofar ya buga da karfi ya karasa shigowa yana nuna kofar da hannu yana kallon Sddiqun, cikin tsananin bacin rai yace"fita ko kuma wllh afita da gawarka, ke kuma..!"

ya nuna Mairoji da tayi tsuru da ita yace"ki tattara ki koma gidanku, ai nan ba gidanku bane, gidanmu ne ki koma inda kike da gado akula dake akara miki tarbiyya, idan kinyi hankali sai ku neme ni, kai kuma wllh ko ka fita ko na illataka anan wajen inga dan abun uban daya tsaya maka."



Murmushi Saddiqu yayi ya juya ya fita, Mamah kam dan takaici kawai tsawaya tayi tana kallonsa, tana tunanin wannan Malik nata ne ko sauya mata akayi da wani, tsawa ya kuma dakawa Maryam yace"watau ga dan iska ina magana kin tsare ni da ido, nace ki tashi ki bar mana gida tunda bakida gado anan."



Jikinta na rawa ta yunkura zata tashi Mamah ta maidata, cikin muryar da ba yabo ba fallasa tace"koma ki kwanta, matukar na isa dake ban yadda ki taka kafarki ko kofar dakin nan bakinji ni?."



Kai ta gyada tana satar kallon Malik da yake aika mata da muyagun kallo, cikin bacin rai yace "Mamah ke bakiji irin warin da take ba, gaba daya dakin fa wari yake, wllh tun daga bakin kofa nake jin warin da ke tashi ajikinta, pls ki baeta ta tafi kawai, in dan ta nine wllh na yafe ta bana bukatarta arayuwata ko kadan."



Haka ya gama babatunsa Mamah dai bata kulasa ba, sai dan kansa sannan ya juya zai fita tace "idan ka fita ka jamin kofar, kuma idan na kuma ganinka adakin nan, ban yafe maka ba, matukar bani na neme ka ba, kana iya tafiya."



Shi ji yake ma ko ajikinsa , ko tsine masa zatayi bai damu ba indai akan wannan yarinyar ne, haka ya fita yana gunguni, kuka Maryam ta fashe dashi tana kallon Mamah, hararata Mamahn tayi tayi tace "ke ni yimin shiru, sai e dan ya ce baya bukatarki arayuwarsa, ke da kike da manyan yara masu sonki da gaskiya, idan ma sakinki yayi ai ba rarasa manemi zakiyi ba, bana son wannan kukan naki, kullum ina fada miki ki mika lamuranki zuwa ga Allah, inshaAllahu zakiga sakamakon duk wanda aka zalunta."



Da kyar dai ta samu ta rarrashe ta sannan ta fita dan lokacin mata yan zuwa yini sai shigowa suke, haka yinin ranan ya kasan cewa Maryam ba dadi, ta kira wannan ranar da ko wane irins suna, karshe ta lakaba mata ranar yanke farin ciki.



Da yamma tayi aka dauko amarya, anan part din Khausar din zata zauna dan an ware mata falo da bedrum biyu, sai dai kichen ne yake ahade, sai kuma babban falon part din nasu da kowace zata iya zama tayi harkokinta aciki ba tare da takurawa yar uwarta ba.





  *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _29_



Bayan kwana biyu da yin bikin an gama watsewa, kowa ya kama gabansa, zuwa wannan lokacin duk wanda ya kalli Malik sai ya tausaya masa, saboda wata mahaukaciyar rama da yai, gaahi in dai zai zauna shi kadai, to bashida aiki sai na tunani ko kuma shi kadai ajisa yana kananun surutai, a hankali idan aka fahimcesa kamar yana cikin damuwar da babu mai taimaka masa ne, cikin sati biyu duk ya fita hankalinsa, tun Abbah baiyi magana ba sai da ya magantu, haka Mamah sosai hankalinta ya tashi, sai dai bata kulashi amman ta dage sosai da addua.



   Bangaren Mairoji kam, ita tuni ta manta da wani sabani daya shiga tsakaninta da Malik din, neman hanyar da zata ganshi take, dan rabon dasu hadu tun ranar da abun ya faru, sai dai ta gansa daga nesa, yanda  taga yai wawuyar rama, ga kasumba daya tara, shi da ko saje baya ajiyewa yana taruwa yake cireta, ta tausaya masa matuka ita da za'a barta da sun tattara sun koma ina yaso sa sasanta tsakaninsu.





**

Yana zaune kamar ko yaushe, ya buga tagumi Sakeena ta shigo, harta zauna bai sani ba, sai data cire masa tagumin sannan ya kalle ta adan firgice, numfashi ya sauke yana jin wata yar shakkarta, harararsa tayi cikin bada umarni tace,

"Wato kazo ka zauna kowa ya ganka yace ina takura maka ko, salon iskancin daka koya kenan yanzu, salon ana mun wani kallo daman ga waccan matar da ba sona take ba, sai afkin munafurci data hada aka lika min kishiya, dan bakin hali ita bata zauna da kishiya ba ni tasa an hadani da ita dan tsana."

Kallonta yayi adan fusace kamar yana son mata masifa amman bakinsa ya kulle, tsaresa tayi itama da ido tace"me..? karya nayi kome, da tana so na ne?, ai ita bataki yau ka sake ni ba, da zaka wani bini da ido kamar ga wata sa'arsa tana magana."



Kai ya dan sunkuyar yana ji wani tukuki yana taso masa, tashi tayi ta fara hada kaya tace"kana gani ina aiki amman ko ka karba ko?, yayi maka kyau."

Tashi yai jikinsa asanyaye, ya karbi kayan yaci gaba da hada mata, sai daya gama tana kallonsa ranta fes, sannan cikin sanyin murya yace"na gama."

Tsaki tayi tace"to da ka gama hadan nawan, naka wa zai hada maka, kana wani abu kamar karamin yaro, maza ni ka hada kayanka so nake mu bi jirgin yamma zuwa Lagos daga nan mu wuce inda muka fi wayau."



Jikinsa asanyaye ya hada duka kayansa, har wanda ma baya amfani dasu sai datasa ya hada, yana gamawa ya dan kalle ta adan duburburce yace,

"zanje naiwa Abbah da Ya Ahmad sallama, tunda basu san yau zamu koma ba."



Wata uwar ashariya data narko sai daya runtse idonsa, cikin masifa da tsoron karyewar aikinta tace"babu wajen ko wane munafiki da zaka, ina sune masu tirsasaka daman kana yin abunda ransu keso, to wllh baka isa ba babu inda zaka, ka wuce ka shirya kawai mu tafi."



Bai mata musu ba ya nufi bandaki, amman sai ta dakatar dashi, daya fada matama wanka zai , sai cewa tayi ya barshi yayi idan sun sauka Lagos, haka yasa kayansa yana jinsa duk atakure, shi ya dunga jidar kayansu yana kaiwa mota sannan yazo yace mata ya gama, suna fitowa kuwa sukayi kicibus da Khausar, zata shiga wajen Mamah, kallonsu tayi tace.

"ah'ah Malik sai ina kuma, tun dazu naga kana saka kaya amota ko har zaku koma ne?."

Ta maida tambayar kan Sakeena da take jijjiga tana jiran atabata ta sauke, dauke kai yai bata bata amsa ba, shi kuwan Malik satan kallon Sakeenan yayi sannan ya kalli Khausar yadanyi yake yace"matar Yaya, zamu koma ne, kinsan ina da abubuwa da dama acna, ga batun bude kamfani da mukayi hadin gwuiwa da , da Ansar dan tsohon gwamnan jihar Kano, kinga dole ana bukata ta acan ai mun dan kwana biyu."



Tsawa Sakeena ta daka masa da tasa ko Khausar sai data dan razana, kallon mamaki tayi mata, sannan ta kalli Malik da ya sunkui da kai kamar ma jikinsa rawa yake, cikin masifa Sakeena tace,

"In banda barbadanci waya tambayeka, ko abun data tambaya kenan zaka tsaya yi mata wani bayani kamar ance maka ya akayi, nifa wllh wannan salon daka dauko ne bai minba, ehe dole ma kka sake lale, dan bazai sabu ace ko wanne shirgi sai ka fadawa sirrinki ba abunda na ce maka kar wanda yasan da batun amman shi ne dan rashin jin magana kake fada mata kuma bama tambayarka akayi ba, dalla ni wuce muje."



Haka ya wuce ya nufi mota, sai dataga shigarsa sannan ta kalli Khausar data saki baki tana kallon sabon abu, murmushi Sakeenan tayi tace"ina dai wajen uwar mijinki zaki shiga, idan kinje ki fada mata mun wuce, ita da ganin danta kuma maybe sai dai ahoto, eh to zamu iyayin kara, idan wani agidannan ya mutu muzo gaisuwa mu koma, ita kuma wadda.kuka lakaba mai, ki fada mata ta jira takardar sakinta, zata sameta har gida, kuma idan ta hauhu ta nemawa dan nata uba, dan wannan uban yayana ne kadai ba da wata can ba."



Tana gama fada tayi wucewarta wajen mota, ta shiga suka tafi, sosai Khausar ta shiga rudani, da hanzari ta shiga wajen Mamah, a falo ta tarar dasu ita da Ummie da Maryam, zama tayi tana sauke numfashi, kafin wasu irin kwalla masu dumi suka sauko mata, da hanzari

Please Login or Register in order to submit comment