You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakura ya koma shi kadai.



Ko da yaje wa Mamah da maganar sunki yarda ya taho da ita, tq ji haushin abun sosai, dan harta nemi fadawa baban Mairojin amman sai Abba ya dakatar da ita, yace abarsu dai aga iya gudun ruwansu, duk abu dai ba zasu aurar da itaba sai da yardar mahaifinta, da kuma danginsa.

Da wannan ya samu ya shawo kanta dan tadau abin da zafi.





+++



Shigowarta falon kenan tayi sallama taji ba'a amsa ba, hakan ya bata cewa Mamah tana sama, zama tayi tana dan rike bayanta da yake mata ciwo kadan kadan, sakkowar Ummie daga sama yasa ta maida kanta tana kallonta, murmushi tayi mata tana karasowa wajenta tace,

"Auntynmu sannu da hutawa".



Ita ma Khausar murmushin tayi tace " yawwan mu Ummie, yanzu nima ai na shigo, ina Mamah ne, da Laura, kodan ita Laura ana makaranta ai".



"Wllh tana can, baran ma yanzu da suke shirin jarabawar second semister, me zan kawo miki ki dan taba?".



Yamutsa fuska tayi tace" sa Haule tamin dan waken rogo, sai ayankan kabbage da cocumber, da tumatur, yau hakanan dashi na tashi ina kwadayin ci, taimakamin pls".



Dariya Ummie tasa tana mikewa tace"Allah Auntynmu idan babyn nan ya zo, sai na mintsine sa, ya mayar mana dake acici, abinda ba dabi'arki ba".



"Ba ruwanan tsakaninku d'an ki ne ai, idan yazo ki zanesa ma ban da damuwa, ni dai ayi saukri asallameni tun ban fara malelekuwa akasan kafet dinna ba".



Mamah da tun fara maganarsu take jinsu, murmushi ta saki tana karasa saukowa, kaunar Ummie da Khausar din na kara ninkuwa aranta, zamewa Khausar tayi ta gaida Mamahn tana sunkui da kai da gyara hijabin jikinta, ita nan kar Mamah taga cikinta daya fara fitowa dan watannin biyar da kwanaki.



Murmushi kawai Mamahn keyi ta zauna tana jan Khausar din da shira.



+++





" Malik, watanni kusan takwas da auren ka amman har yau baka taba nunamin matarka ba, wannan amintaka ce kuwa, ko dai baka yarda dani bane da kake boyemin iyalinka?".



Bai kalle sa ba, bai kuma amsa masa ba yaci gaba da abun da yake, sai da K2 ya kuma damunsa da mita sannan ya dan numfasa yana kallonsa kamar ba zai ce komai ba kuma sai ya ce"idan anjima sai muje ka ganta, maybe ka samu sukuni".



Yana fada ya tashi ya barshi nan, da ido K2 ya bishi yana jin tsanarsa da kishinsa na wanzuwa aransa, kwafa yai yana kunna sigarin dake hannunsa yaka gyada kai.





Da dare kuwa bayan magaruba , K2 ya iso gidan, sqi daya kira Malik ya sanar dashi gashi abakin kofa sannan shi kima ya zo ya shigar dashi, lokacin Sakeena tana zaune ne, tana gyaran farce, sallama yayi kamar yadda addini ya ce kasancewarsa musulmi dan kasar fakistan, ba laifi ya samu tarba sosai daga wajen Sakeena kodan wannan shi ne karon farko da wani bako ya taba shigowa gidan tun da tazo, sai abun ya dan bawa Malik mamaki, amman ya kauda shi saboda tunanin dayai na yau ta fara ganin wani ya shigo inda suke, kiran da Ahmad ya mai ne ya sanar dashi ya duba email dinsa ya turo mai wani sako, kuma yana bukatar ya duba sa yanzu dan amsa yake so, da gaggawa.

Tashi yai bayan ya dauki excuse, yana barin wajen K2 ya kalli Sakeena data sake abinta kamar tana tare dana gida, lasar bakinsa yayi yace"gaskiya ke kyakkyawa ce".



Murmushi tayi tana jin kanta yana dan fasuwa, tace "thanks, you too".



Kai ya girgiza ya ce" ban kai ki ba, ai mace duk inda take tafi na miji kyau, ko baki san da wannan batun ba, k8na da kira mai kyau gaki yarinya mai dauke da kuruciya, me ya kaiki zaman takura da rashin yanci?".



Kall9n rashin fahinta tamai, sai ya matso kadan cikin murya kasa-kasa yace"tunda kika zo ya kaiki yawo, kinga wani na zuwa inda kuke, ko ya taba fita dake wajen wasan kwallo, ko shan icecream?duk ciki babu abu daya daya aiwatar miki, amman kina zaune kina murna kin auri Done, ba zugaki zanyi ba , amman yanda kike da kyau dinnan ki tashi ki kwaci yancinki da hannunki, idan ba haka ba zai maida ke mai gadinsa".



Gyara zamansa yayi yana kallonta kasakasa, shiru tayi tana tunanin maganarsa, kuma idan ta dorata ama'au ni tabbas yana da gaskiya, mahganarsa babu karya, amman duk da haka tana bukatar nazari da shawara akan hakan.



Kallonsa tayi zatayi magana ya daga mata hannu yace "ungo wannan, lamba ta ce duk sanda kika yanke hukuncin dake ranki zaki iya tuntuba ta dan neman shawara ko karin bayani".



Karba tayi tana cusata cikin rigarta, dai dai Malik shi kuma ya dawo, daganan aka dan taba shira sannan K2 ya musu sallama ya fati bayan ya ajiye mata uban damin kudi, wai ta sayi kayan kwalliya.



    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



   _18_

  Bayan tafiyar K2 shiru tayi tana kuma yin tunani akan abinda yace mata, tabbas da gaskiyarsa kuma babu alamar wasa amaganarsa, ajiyar numfashi ta sauke tana kiyasta yanda zata faso gari itama nan da dan wani lokaci, murmushi ta saki tana jin kanta na wani juyawa.



   Bayan kamar kwanan uku ta gama yanke hukuncin daya mata, number din da K2 ya bata ita ta kira, bugu biyu kuwan ya dauka, bayan sun gaisa take fada mishi ita ce matar Malik daya bawa number rannan,

"Yah...ai na dau murya, yanda muryarki take da dadin nan ai ba za5ayi wuyar dauka aka ba, to ya kin yanke hukuncin ko kuma kinfi son kiyi ta zaman kunci kamar ajail?".



  " na gama yanke abinda zai fisshe ni, sai dai ni bansan dawan garin ba, kuma ba nida wasu kudi ahannuna da zan dan wataya dasu".

Murmushi yayi aransa yace  "anzo wajen".



A fili kuwa sai yace" haba dai, kina nufin duk kudin da ake bawa iyalan 'yan ball duk sati, ke baya baki naki, gaskiya Malik bai kyauta ba, amman kiyi hakuri zan masa magana, shigasa nace miki wannan zaman takura kawai kukeyi".



  Ranta ya baci sosai, har hakan yaso bayyana ta muryarta,

"Ba sai ka masa magana ba, kyqle sa zan yi magana zuwa gida za'a turo min ko nawa nake bukata".



Da saukri ya dakatar da ita yace" inaa....hakan bazai yiyu ba, duk amintar dake tsakanina da Malik ace iyalinsa na bukatar kudi sai ta nema agida, haba mutuncin ai baice haka ba, indai kudi ne zan kawo miki shi da kaina, duk yanda kike bukata".



   Godiya ta shiga yi masa, yace "haba babu komai, ai duk yiwa kaine, abinda nake so dake kawai shi ne karki fada masa idan na baki, kinsan zuciya ba tada kashi, sqi kiga yana tunanin wani abun, kuma ni ba zanso hakan ba".

   " kar ka damu ba zai sani ba, kawai dai ni ina son ka taimakamin na zama celebrity, so nake na zama abar kwatance aduk cikin family dinmu".



Murmushi kawai yake dokawa yace"baki da matsala, gobe zaki ganni, ko zuwa yamma ne".



   Da haka sukayi sallama, ya kashe wayar, tsalle ta daka tana ihun murna, daya daga cikin burikanta yana gab da cika, wai yan Maid zasu ga tsiya da wasali, tuni ta fara kiyasta yanda zataci uban kowa.



++++

Cikin abinda baifi sati biyu ba Sakeena ta fara zama irin yanda take so, kudi kuwan ba matsalarta bane dan K2 yana bata fiye ma da abindata nema, sannan kuma ya hadata da yaran turawa marasa kai, yarane da babu kwaba, dukkan su ta girme musu domin basu fi shekara sha tara ba, ita kuma tana da ashirin da hudu, haduwar su ya kuma sawa idonta ya bude sosai.



Rananr da suka shirya zuwa wani show da za'ayi , sun biyo mata ne don duk cikinsu ita ce ba mota ahannunta, sau ran kowa nada ita, to idan suka shirya fita sai su biyo mata, lokacin Malik na zaune afalon yana waya da coach dinsu kan maganar siyansa da kungiyar Real Madrid zatayi, fitowa tayi ya kalle ta alama yai mata data koma, amman sai ta tsaya taki tafiya har ya gama wayarsa.

Kallonta yayi daga sama har kasa, wani wando ne da bai karasa idon sahun ta ba, sai wata farar riga mai spagetti hand, da itama bata karasa rufe cibiyarta ba, sai gashin da aka kara mata wanda ya saje da gashin ta kamar dama can nata ne, sosai kirarta da take fizgar yaya maza ta fito sosai, kai ya girgiza kawai ya dauke kai sannan yace mata,

"Ki koma ki canza wannan shigar, kar ki manta mu yaran musulmai ne bana kafirai ba".



Baki ta tabe tayi gaba tana mita,

" ni na zata ma akan wani abu mai mahimmanci ka tsaidani, ashema akan wani shirme ne na daban, sai na dawo".

Da kallo ya bita, dan yanzu abindata tsira kenan, kuma babu damar ya mata magana zata fara masa fitsara, shi kuma abin daya tsana kenan, rashin kunya.





Wajen ya kayatar da ita fiye da yanda take hasashen ganinsa, wani dan wajene suka shiga kamar falo haka, anan taga K2 da sauran abokansu kowa da babe din daya kama yana matsewa, da sauri K2 ya kamo hannunta ya zaunar da ita kusa dashi bayan ya sallami yarinyar dake tare dashi yace zai neme ta.

Kallon wajen take gabanta nadan faduwa, dan tunda take tantairancinta bata taba ganin anyi tarayya agabanta ba, amman yanzu kuma, mata ne ma suke neman junansu agabanta, banda mazan da suma wasu na aikata irin haka, da kuma masu tarayya tsakanin mazan da matan _(innalillahi waennailairrajioun, subhanallahi, yanzu fa abinda yake dawainiya da jama'a kenan, mace ta nemi mace, namiji ya nemi dan uwansa namiji, sai ka rasa wacce uwar sukeji idan suna wannan kazantar, ya Allah, ya Rahmanu, ya Gaffaru, ya Zuljalalu wal ikram, ya Rabbhissamawati wal ard, ya Allah ka tsaremu da tsarewarka, ya Allah ya karemu dan girman iyawarka, ya Allah karka barmu da halinmu, ya Allah ka tallafa amana, wannan zamanin Alllah ka bamu ikon danne zuciyoyin mu, kasa mufi karfin duk wani shaidanci da zai shiga idaniuarmu, da kunnuwanmu, ya Allah ka tsare mana bakunan mu da fadar shaidanci da sharri, Allah gamu gareka, wallahi iyaye ku tashi tsaye akan yaranku mata da.maza, kar kawa tazo wajen yarki kice mata wai shiga ciki ina jin barci take, ke kina tsakar gida kina aiki ita tanacan tana miki babban aikin da baki san dashi ba, ana can ana raruke miki yarinya, kusan awanni suna daka su biyu, sai ta tafi kina washe baki kina cewa wance dai Allah ya hada jin8nsu da wance, ai wance tana son yarnan, kai soyayyar da wance kewa yarinyar nan yawa gareta, uhmmm Umma! Mamah! Innah! Momy! Mamy! Ammy! Anni!!!, wllh kina zaine mace zata lalata miki yarinya, ba zaki tashi sani ba sai ta isa aure , ta fara korar samari, saboda duk cikinsu ba wanda takewa kallon wanda zai iya da ita sai yar iwarta mace, dan Allah iyayen mu ku tashi tsaye akanmu, ku dage mana da addua, ku na sa mana albarka aduk inda muke, Allah ya kara karemu)_.



Kai ta kawai dan ko kadan tsantsani abin yake bata, wai mace tana shan pp din yar uwarta, kai ina...ita kam ba zata iya wannan kazantar ba, jin ana shafa ta yasa ta juya ganin k2 ne sai shinshinarta yake dan kanshin nata yai masa, kafin ta ankare ya kwantar da ita ya bi kai yana aika mata da wasu mahaukatan romansi, da fari taso tirjewa sai daga baya taga abin bana wasa bane sai ta bada kai.



Ba ita ta dawo gida ba sai dayan dare, shi ma kuma ba wai dan ta ishi k2 dinba, sai dan yasan halin Malik, idan yasan suna tare tsaf zai iya aikashi lahira, kuma ba yanda za'ai dan yana da daurin kugu da manyan kasar dama wasu kasashen.



Irin wannan rayuwar Sakeena ta daukarwa kanta, tsakaninta da Malik kuwa sai suyi sati basu hadu ba, daman shi baya ta tata, ita ce ma wani zubin take kokarin taga ta sanya shi a idonta kafin ta kwanta, ko kuma kafin ta fita.





+++++





A Dutse kuwa Mamah ta samu baban Mairoji da maganar zamanta a Maid, tunda su basu nema mata makaranta taci gaba ba, ai basa hanata auren wanda take so ba, da ya duba yaga maganarta akan hanya take da kansa ya taka zuwa Maidugurin ya taho da ita duk da rashin mutuncin da Saddiqu yaso masa kuwa, hakan bai hana ya taho da ita ba, kwanan su uku da zuwa juma'a ta zagayo, bayan sakkowa daga masallaci aka daura auren ta da Malik, wanda babu wanda yasan da hakan sai Malam Saje da Abbah, sai Kawu dake kano da Ammy, dan ko Mamah bata sani ba, bare ita Maryam Malik din.



   *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _19_

   Babu wanda yasan da batun daurin auren sainiya isu isu, Malam yafi kowa farin ciki domin kuwan wannan shi ne kusan burinsa na karshe da yake son cikawa, haka ma Mamah tayi murna sosai duk da ita Ahmad tasowa auren Maryam din, amman ganin ya samu Khausar kuma yarinya ce wadda take da wadatacciyar tarbiyya.



   Anan gidan zata zauna kafin Malik yazo hutu sai ya tafi da ita, sosai Mamah take mata yan kananun gyararraki, duk da zaman da tayi aMaid, yasa ko yaushe cikin kamshi take, indai ta zauna awaje to tana tashi ne tabar tsarabar kamshinta awajen.

  Sati daya da daura auren Ammy tazo ta dauke ta, kwananta tara ta dawo amman sai ta wuce can gidan babanta, matar sa mai mutunci sosai, wayayyar mace Anti Lubabatu, haka ita ma tayi mata irin gyaran da taga zata iya sannan ta dawo gida wajen Mamah, da fari bata sakewa Khausar domin haushinta takeji sosai, amman daga baya da Mamah ta zaunar da ita ta mata tuni akan yanzu ita matar wani ce, babu amfanin tana kishi da wadda ba mijinsu daya ba, da haka dai ta samu ta sassauto har idan sun hadu Khausar din tana tsokanarta da amarya, tun bata sakin jiki sai gashi ita ce har bangarensu take zuwa, anan ta kuma kwarewa abangaren girkegirke, domin Khausar dai badai iya girki ba ko Mamah ta na jinjina mata _(ina kuma jan hankalin iyayaen mu dai, wllh duk haduwar mace duk yanda zata juya namiji akan gado indai bata iya girki bako....uhmm kin gama yawo yar uwa, karki yarda mijinki ya fara korafi dake ta bangaren kichen, na rantse yafi miki ace baki iya salon kwanciya ba akan ace baki iya kalolin girke girke ba, Allah mazan yanzu yanda cikinsu yake a hangame idan baki san yanda zaki bi da cimar sa ba ko wllh yu a no more , yar uwa ba iya kula da miji kadai akasan mace da shi ba, zakiga wata idan aka ritseta wane abinci mijin ta yafi so, zatace komai ma yana so, ah ah ba haka ake ba, ke da kike da alhakin kula da hakkin c8kinsa dole ne kisan wane abinci ne idan kikayi yafi ware cikinsa yaci, wanne kuma idan kikayi yake cin kadan yace ya koshi, bawai dan iya koshi din ba, sai don kinyi abinda ba ra'ayinsa bane, wllh akwai wadda take tambaya wai daman ana saka citta da kanunfari idan za'a dafa shayi,wai ita idan ta wulla ganyen shayi ta zuba siga ai shikenan shayi ya hadu,  ina fada muku nafi kwananki ina mamakin wannan abun, har yau nama kasa bata amsar daya dace sai littafin girkegirke nasa aka siyo mata nace ta fara da wannan, irin haka na faruwa, kuma wai sai miji yaje wajen mai shayi yacika tumbinsa, ke kuma ki kona gefe kina fadin wane ya na daukar hakk8nki, ke dan Allah kin kula da nashi hakkin na bangaren cikinsa, dan Allah mata  mu gyara, kamata yai idan an tambayeki kin iya girki, kice eh na iya, ban yarda da wata kalma wai ita na iya dai dai gwargwado, ah ah ba haka ake so ba, kawai kin iya, so samu ne acinkin kaso dari kin iya cassa'in da biyar, amman idan fa kinga zaki dauka, dan rayuwarnan babu tabbas>Ø7Ý shima namijin kamar wutar nefa yake, sai kina tsaka da jin dadinsa zai miki tsiyar, amman idan kika iya takunki, ko tsiyar ce ta tashi zai ji nauyin yin wani abun agaban idonki, iya takunki kuwa nada nasaba da iya girkinki, duk tsiyarsa dai dole sai yaci abincinki uwar hanjinsa ta dauka kafin ya fara tsiro da halin, dan ba'a bori da sanyin jiki=Ø Þ)_.



    Sauran sati uku Malik yazo gida, dan Mamah ta hada mata kayanta tsaf ta koma Jahun, gidan babanta, acan ake son ayi biki sannan adauko ta akawo nan.



+++

  Tinda ya sanar da ita zasu taho 9ja, ta fara masa tambotsai tare da taimakon zugar k2, ta sanar dashi babu inda zata, bai kulata ba ya fara shirye shiryen tahowa, tunda wannan karon ya dade baizo ba.

    Sauran kwanan goma tahowar tasu, ranar bata fita ba zuna saune shi yana cin pizza, ita kuma wani yogut ne ahannunta wanda ya zame mata jiki, ko yaishe tafi gane ta sha shi, domin k2 ne yake kawo matashi, kawai dai tasan tana son shansa ne, wayarta dake gefen tayi kara, sunan Laura ta gani sai ta kashe ta sake kiranta dan tasan ba wani kudin arziki bane awayar ta Laura din ba.



   Sai da suka gama tsokanar juna kamar ko yaushe, sannan Laura tace "ke labari da dumi dumin sa,  Maryam dai an daumra mata aure".

   Cike da son jin gulma ta danna hansfree tace " ke dan Annabi, wa ya jajibarwa kansa kuma?".

"Uhm...kedai  bari kawai Sakeena, ai ina fada miki zance acikin zance, wai inji magajiya, wato dai ashe yarinyar nan watsewarsu suke da Ya Saddiqu, sai rannan kwatsam aka kama su, shi ne fa aka ce ya aure ta shi kuma yace bazai daukarwa kansa ragowa ba, bayan ya gama saninta awaje, kememe dan bana Allahn nan yaki karbar auren yarinyar nan, to dai yanzu an daura auren amman sun rufe sunki fadan da wa aka hada, nan da sati biyu za suyi yinin biki su mikata ga wanda suka bawa".



   Numfashi Sakeena ta sauke tanajin wani sukuni na ratsata, ko banza yanzu ba tada fargabar kar Malik ya aurota, cikin halik ko in kula tace" can ta matse musu, na san wanda ya kwashe ma maybe irinta ne dan tasha, can dazu gada, su karata, ke yaushe ne naki bikin?".

   "Uhmmm....bari kawai ke dai, waccen shegiyar ta kankane komai, amman ina nan ina babban shiri akanta, wllh na rasa.ma yanda zanyi da ita, ko kadan Ya Ahmad baya tani sai ita, banda ma yanzu cikinta ya kusan shiga watan haihuwa,Mamah ta riketa,  da  fa dda ita yake tafiya wajen aikinsa, sai ya shafe kwanaki baizo ba, ni kam ai ina nan ina kallon abun daya isheni".



    Tsaki tayi tace" kema dai da sa kai a uku, ga maza nan rutut ki nemi wani mana sai lallai shi..."

  Tsaki Lauran taja tace "dalla can ana nuna miki Annabi kina runtse ido, wa nake dashi da yakai shi, ko ga kibar wannan maganar kawai, ya ake xiki ne banji kin fara wani motsi na samun karuwa ba".



  

Daga nan suka sauya zuwa wata hirar data shafe su, Malik da tun bayan fara wayar tata yaji komai da kunnensa, ransa ne yai masifar baci, watau ma Maryam din nasa aka aurawa wani, shiyasa ake so yaje kenan ayi bikin dashi, tsabar an maidashi sauna, tashi yayi ya koma dakinsa yana saka wasikar jaki, sosai yake jin bacin rai da wani tukuki yana tasomai.



Abin karin takaicin ma ashe ta maida kanta ballagaza, watau sheke ayarsu suke da wannan danta'addan, ahakan kuma da ya agama cin moruyar ganga sai yada kauronta, zama yayi abakin gado yana dafe kansa, ya gama yankewa ba zaije 9ja dinba, tunda sunyi gaban kansu miye nashi na sai yaje din, daga nan ma zai iya mata addua Allah ya bata zaman lfy ita da mijin nata, zuwan nasa kam ai baida amfani.



Tun daga lokacin ya tsiri yn tafiye tafiye, musmusamman idan basu da wasa sai yai kaura yabar garin ko yabar kasar, ahaka har ya rage sauran kwana daya tal afara bikin, dukda ba wanda ya kuma kiransa daga can don ko sun kirashi din iya karsu kawai gaisawa da tambayar halin da suke ciki, hakan ya kuma tunzurashi, ya kuma saddakarwa Maryam ta kufce masa har gaban abada.







+++

Ranar da zasu fara hidimar bikin haka aka yishi babu wani armashi tunda babu ango, ga ita Mairoji da take fama da zazzabi, washe gari sukayi bridelshower, ran asabar akayi yini kamar yanda al'adun bahaushe ya tanadtanadar, sai ranar ssannan Ahmad yaje can Hajun din, shi ya wakilci ango akayi duk abubuwanda ya dace ayi, sannan ya dauko amarya da yan rakiyarta suka juya zuwa Dutse.



Bangaren Mamah aka kaita, tana zaune tsakiyar su Ta-alhaji kawarta tun suna Rugar Saje, da kuma su Ummie, sai Fannah tacan Maid, kuka take kasa kasa, bawai kukan dako wacce mace takeyi ba idan an kaita gidan miji ba, ah ah ita nata kukan na bakin cikin an kawo ta dakin miji ne amman ba wanda take so ba, sai dai ankawo tane amatsayin matar kanin wanda zuciyarta take so, wanda dole ta kirasa da wan mijinta, kuma yayanta, da kyar aka lallabata tayi shiru sannan Mamah tasata agaba har bandaki tayi wanka, dujda har.lokacin jikin da ssaura, bakin gado ta zaunar da ita bayan ta mika mata kofin shayi sai magani, tace maza ta shanye ta samu ta kwanta.





Washe gari Mamah tayi nata yinin anan gida, a irin kaya da Abbay yai mata ta hade cikin wani yadi ja mai layi layi, sosai tayi wani sihirtaccen kyau, sai dare aka gama watsewa sai iya yan gida kawai, Mamah da kanta ta dangana da ita har bangaren Malik dake gidan, wanda akasakasake kawata shi aka gyara sai kamshin sabon fenti yake dana furniture, ban da kamshin turaren wuta hadin Maiduguri, kuka tasawa Mamahn ganin tana shirin ficewa ta riketa gam, zame hannunta tayi tana dariya tace "ke haba meye na kukan, ai ba ke kadai zaki na kwana ba, ga Ummie nan ga Fannah, suna nan dake har sanda yayan naku zai dawo, ki kwantar da hankalinki naga dai gida daya muke".



Da haka tta samu ta fice ta barta da su Ummie din.



++++



Sosai rayuwa take tafiyar musu don Abbah ya nema mata makaranta nan university of Dutse take zuwa, sannan ya dauka mata driver ya bata dukkan makullayen motocin Malik din yace duk wadda take son fita da ita basai ta na jiran abata makulli ba.



Watanta biyu da tarewa taji batun zuwan Malik abakin Ummie, itama taji ne suna waya da Mamah inda ta nuna masa bacin ranta nakin zuwan dayai lokacin da aka ce yazo din, inda taji yana sanar mata zaizo nan da sati biyu masu zuwa, baki Mairojin ta tabe ta ce" dama yai zamansa wllh, bana maraba dashi".



Duka Ummie ta dala mata akan cinya tana danne dariyarta tace "munafuka, kina nuna baki damu ba amman kusan kullun sai kin gama karewa hotonsa kallo kafin kiyi bacci, za kiyi bayani ne yana dawo wa zan gudu wajen Mamah,

Please Login or Register in order to submit comment