You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini duk da wannan mugayen halayen nasa acikin families dinnan namu, yan mata da dama suna jarabar son sa, uhm....idan nace miki zan fayyace miki waye Ya Saddiqu , batun zai kaimu har dare bamu gama ba, kawai abinda zance miki ki iya takunki idan ya dawo, dan bai san bako ba shi".



Tunda ta fara Salme da Mairoji ke kallonta tare da al'ajabin wannan da kowa yake kaico da dawowarsa gida, sabanin wasu da suke murna idan wani nasu da ya dade baizo gida ba, zai zo.



Watsar da zancen sukayi anan, suka shiga harkokinsu, domin gobe ne za'a daura aure.





++++



Wajen hudu na yamma Salman shi da wani abokinsa suka taro Malik , ahanya banda shagiyanci babu abunda suke mai, Salman harda cewa " Katon tuzuru, har yanzu shiru dai, ka bari kawai idan nayi auren zan fada ma yanda yake, idan na haifi yarinyata ta fari sai na ma kiyo".



Harara ya maka mai yana tsaki, cikin sanyin rai yace"ajiyata......ajiyata nake jira ta kirani, zaku sha mamaki idan na tashi aure na".

"Zaka auro yar sha tara ne, malam mai akidar auren karamar yarinya".

Baki ya tabe yace " ko ma dai meye, idan nayi aure, sunana mai gida, kamar yanda za'a cema maidiga".



Dayan abokin da suke tare yace"wai Salman wannan ba dan ball dinnan bane, dana sani kamar Malik B.M?".



Salman yace "shi ne mana, rabona dashi tun da mu kayi makaranta a Ringim, kusan shekaru shida kenan bamu ga juna ba sai yau, wai dan ma muna danyin waya jifa jifa".



Bakin abokinnasa har kunne, yau gashi ga shahararren dan wasan nan, da kowa kesan ya gansa koda sau daya ne, lallai bikin Salman yazo mai da abunda bazai manta ba.



Har suka karasa gida, Salman tsokanar Malik yake, da katon tuzuru.





+++

Akaguce Salman ya runtsa yana tsimayin zuwan gobe, anan ne shima Malik ya rama, suka hadu suna mai tsiya.

Washe gari kuwa kafin tafiya daurin aure Salman ya ce su shiga su gaisa da Ammyn sa, da kuma Kawu, har Malik din na ce masa shi fa kunya yake ji, takanas baije Kano gaida Ammy da Kawu ba sai da bikin sa, dariya Salman din yamai yace" wannan kuma matsalarka malam, zuwa dai ya zaman ma dole".



Yana sinsinke kai ya gaida Ammy, bayan sun danyi raha kamar yanda aka saba, har da Huda data gama mai tsiya, tace "kai Malik, rabon mu dakai tun a Ringim, lkcn kuna gaba dani, amman bazan manta lokacin ba, sai dai ka kyauta daka zo, Allah yabar zumunci".



Amsawa yayi da amin, sannan suka tashi fitowa, karo suka kusan yi, yai saurin ja da baya, cike da jin haushi, bai ko kalli wadda suka so bangazar juna ba ya sa kai zai fice.

Har ya fita yaji Salman yana magana, da sauri ya juyo yace " maimaita abinda kace, wane suna naji ka ambata yanzu".



Cikin mamakin sauyawarsa daya gani lokaci daya yace"cewa nai Mairoji an sha kyau, ko kaine Mairojin da zaka nemi rudewa?".



Cikin fitar hayyaci ya cakumo rigar Salman yace "a ina kasan ta, tana ina, ina take?".

Gaba daya ya rude, yanda kuma yake maganar murya asama sai ya janyo hankalin wanda ke wajen.



" Ya Malik...!".



Da sauri ya juya yana kallonta, aiko cikin mata dubu ne zai gane ta, kuma ko wankan inji za'a mata, sai ya gane kayansa, da sassarfa ya karaso wajenta, baiyi wata wata ba janyota jikinsa ya rungume ta tsam, yana hadiyar zuciya, itama rungumesa tayi tana sakin wani kuka, yayinda shi kuma ahankali yake bubbuga bayanta alamar rarrashi.



Jin an dafa bayanta yasa ta sake shi ta juya, ganin Ammy yasa ta kuma sakin wani kukan, tace"Ammy yaya nane, dan wan Mamata, kuma dan kanwar babana, shi ne ya Malik dinmu, wallahi shi ne Ammy".



Kawu ne yai gyaran murya yace"yanzu dai lokaci na kure mana dan haka mu karasa wajen daurin auren , tunda abu yazo duk na gida ne, daga baya sai a tattauna".



Fita sukayi dukansu, amman Malik sai waigen Mairoji yake, gani yake kamar idan ya dawo za'a ce masa ai mafarki yayi, ko kuma gizo idonsa yamai.



 

*RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_12_



Bayan an dawo daga daurin aurenne, aka kuma taruwa ababban falo, sai da Malik ya kuma ganin Mairoji da idonsa sannan ya yarda ba mafarki ne ko gizo ba, Baba Lawan ne ya bude taro da addu'a, sannan ya tambayi Malik dangantakarsa da Mairoji, babu wani dogon bayani ya fada musu yanda suke da ita, take wajen ya kaure da hayaniyar murna, sai da Baba Bulama ya yi magana sannan akayi shiru, Ahj Bara'u ne yai gyaran murya yace"to Abdulmalik kamar yanda ka fada mana dangantakarku, muma nan zamu fada maka dankantakarmu daku biyun duk da ita Maryam din ta sani, kaine dai baka sani ba".

Nan ya sanar da Malik yanda suke, da kuma yanda su Mairoji suka zo hannunsu, kamar yadda Kawu ya musu bayani. Idon Malik taf da tsantsar tausayinsu yake kallonta kamar ya maidata ciki, haka yake ji.



Bikin sai ya zamana anyi shi cike da jin dadi, domin kowa ka gani da farin cikin faruwar abubuwa da dama atare dashi.



+++



Bayan sati komai ya gama kintsuwa na hidimar da akayi, sannan ne aka fara haramar zuwa can Dutse tunda Malam Ahaji ya koma can da zama, babu yanda Mairoji batayi ba da Malik ya kira mata Goggoji awaya yaki, ta nemi ya bata lambar da zata samu wani na gidan ma amman yaki, yace bazata yake son yi musu ne.

Sauran kwana biyu su tafi haka ya dauketa da sauran yan matan family da zuwansa gidan duk suka tare agidan, domin ba kyarya, ya tafi da imanin da dama daga cikinsu, ko da suka fito za'a tafi ma sai da wata Sakeena ta bata mai rai, abin daya faru kuwan.



Sun fito sai Mairoji ta bude gidan gaba zata shiga, zaraf sai sakeenan ta rike murfin motar tace wa Mairoji ta koma baya, to ta girme mata, sai batayi musu ba juya zata shiga bayan, shi kuma yana ganinsu tunda yana mazaunin direba ne, bai kula su ba sai data shogo ta zauna ne sannan shi kuma yace ta koma baya itama, kallonsa tayi taga kamar bashi yai magana ba, ita ma sai ta dauke kanta, dan ta nuna mai tanada aji , ransa ne ya baci dan bai fiya son yana maimaita magana daya ba kamar karamin mutum, kin tada motar yayi , a karshe ma sai ya fita ya koma kusa da maigadi ya zauna yana laluben waya.

Takaici ne yasa Sakeena fitowa tana watsawa Mairoji kallon tace "saiki koma gaban ai, sai kuci uwar da zaku ci".



Ita dai Mairoji ba tace uffan ba ta koma gaba ta zauna, sauran yan matan suna kallonsu, daga masu hararar Sakeena sai masu hararar Mairoji, kamar mintuna biyar sannan ya shigo ya tayar suka tafi.



Wani babban Supermarket ya kaisu, yana cikin motar bai fita ba dan yaga wajen da mutane, kuma yana fita zai janyowa kansa hayaniya, cemusu yai kowacce taje ta dibi abinda take so, har sun fita ya kira Mairoji ya bata card dinsa bayan ya fada mata code din da zata sa, sannan suka shiga cikin wajen.



Suna shiga kuwa Sakeena ta karbe card din tana harararta, murmushi tayi aranta tace 'zaki dawo dashi ne' . Kaya suka zage suna diba kamar ance musu kyautane, abin harda hauka da fariya, masu hankalin cikinsu sune suke daukar abun da zai amfane su.

Mairoji kam, bangare turare ta nufa wani mai dan karen dadi ta dauka, irin na maza, sai agogo na maza, mai kyau da tsada, sai necktie, ko wanne hurhudu ta dauka, sai bangaren abin hannu dana kafa, ta zabi masu kyau kusan set uku, iya abin data dauka kenan,sai man zafi data dibarwa Goggoji, dan tace shi kadai zata kai mata tsaraba, sai bangaren kwalam data nufa, anan suka ci karo dashi, dan da fari bata gane sa ba, sai daya dago kansa sannan ta gansa, riga mai hula ce ya dora akan kayansa, ya rufe kusan rabin fuskarsa, kallo daya ya mata ya dauke kai yana kallon tarkace cakulatin data kusan cika kwandon hannunta dashi, rabawa yai ya wuce wajen jallabiyun mata da jakkunkuna.



Sai da aka zo wajen biyan kudinne, sannan Sakewna taji wata kunya, don cewa akai ta fadi code din amman bata sani ba, har mutumin na mata kallon tuhuma, Mairoji da tun tuni take bayanta tana mata dariyar mugunta ta matso, ta fada masa, bayan ya saka ne da karanbani Sakeena ta mika hannu zata karba, shi kuma ya hanata ya mikawa Mairoji harda karin nasa card din yana murmushi, yace"idan an huta gajiya, dan Allah atabo ni ta wannan lambar".



Murmushi tamai kawai ta wuce, suna fito wa suka hangosa har lokacin yana zaune amota yana shan vanilla icecream, suna shiga, ta mika masa katin amaimakon ya karba kawai sai ya share ya dora mata ragowar icecream din akan kafarta.



Zata dauka Sakeena tai saurin daukewa tana murmushi yake tavmce"yayanmu ba ka sani ba ai Maryam bata shan kayan sanyi, da dai mune nan mufa fi kauri".

Ta cikin mirror ya mako mata wani bahagon kallo, amman sai ta mayar masa da murmushi tana lasar labbanta data jikashi da icecream din.



Kai ya kaudar yana jin takaicin yarinyar, rawar kanta ya fiye yawa, da alama sai ya saita mata kai tukun zasu daidaita, wai Maryam bata shan kayan sanyi, to shi yanzu kaf duniya akwai wanda ya kaisa sanin wace Maryam, aiko Goggoji data tashi agabanta ba zata ce masa tasan Mairoji sama dashi ba, amman tabban idan taci gaba damai wannan shisahigin zai ya maganinta ne.



Koda suka koma gida, kowacce taje ta nunawa uwarta kayan da Malik din yasai mata,tuni iayaen suka fara yiwa yaran fanfo, ta yanda yarinya zasa same sa cikin sauki, tunda Allah ya yishi mai sakakken hannu ai dole ma ayi tafiyar dashi.





+++



Ranar da zasu tafi, da wuri suka shirya duk da cewa jirgi zasu bi, Mairoji har kuka tayi ita ba zata hau jirgi ba, amma haka Malik yai banza da ita, karshe mai sai yabar gidan dan zuwa tai tasa shi agaba da fitina, shi kuma baya son jin kukan ne.





+++



Kamar yadda suka wayi gari da daukin zuwa gida, haka suma mutan garin Dutse suka tashi da hidimar zuwan Haj Tako da sauran matan kanne da suke zaune tare dasu.



Tun dare Malam Saje yake jin faduwar gaba da tsinkewar zuciya, amman bai bari Goggoji ta kula ba dan yanayin jikinta, sai da safe ne ma Abba yake fadamai ya kwana da wani irin yanayi, nan shima Malam Alhajin yace mai ai shima haka ya ke ji tun dare, to sun dai barwa kawunan su batun, tare da addu'a Allah yasa alkhairi ne ke kusantosu.



Uku da wani abu na rana suka sakarwa mai gadin gidan Alhjai Badamasi horn, da azamarza ya bude yana mamakin daga ina, dan manyan motoci ne guda biyu sai kananu uku, kusan duk wani babba dake cikin motar gabansa ya tasannata bugawa dan basu san da wane ido yau zasu kalli dan uwansu kuma uba agurin wasu, hakanan kaka agun wasu.



Sai dai gani Malik acikin daya daga cikin motocin yasa mai gadi maida mamakinsa, yana musu sannu da zuwa, kowa gidan yake karewa kallo suna yabawa tsarinsa.

Dungumawa sukayi zuwa cikin gidan kamar yadda Malik ya musu jagora, afalo suka yada zango dai dai lokacin Abba na saukowa daga matakalar bene, idonsa ne ya hangomai mai kama da mahaifinsa sak, sai ya danfi mahaifinnasa girma da shekaru, da sassarfa ya karaso yana aro juriya ya daurawa fuskarsa dan jin zuciyarsa kamar zata fado, kafin ya samu damar musu magana ne yaji muryar da bazai manta da ita ba ta daki dodon kunnensa.



"Abbah na...!"



Da saurin sa ya juya yana kallon Mairojinsa kamar amafarki, da gudu ta karaso wajensa sai dai ta ja ta tsaya tana sakin kuka, kafadunta ya kama cikin rawar murya yace"uwata.....kece? kece Mamana, Mairoji ta, ke nake gani ? Alhamdulillah, ya Allah na gode maka daka nunan baiwarka, Allah na gode maka".



Mama ya kwalawa kira da itama kamar taji muryar Abban na kiran Mairoji da sauri ta sakko tana kallon mutanen dake wajen kusan rai ashirin manya da yara, duk da ta ga Mairojin amman sai ta dake ta tarbi bakin da ta gani wanda hakan shiya janyo hanaklin Abbah shima ya tarbe su aka shiga gaisawa, Kawu ne ya fara magana yace "baku waye damu ba, amman idan babu damuwa muna son ganin Muhammad".





Babu bata lokaci Abbah ya cewa Malik yaje ya taho dashi daga can bangarensa, bayan kamar wasu yan mintuna sai gashi tare da Goggoji data matsa sai tazo taga wa yake neman mijinta, suna shigowa Baba Gana daya kafe kofar shigowa da ido ya mike yana nuna Malam Saje da hannu bakinsa na rawa yace " Autan Ya Mallam".

Duk duniya Malam Saje yasan babu mai kiransa da wannan sunan sai yan uwansa, shima jikinsa har rawa yake ya zube agaban Baba Gana cikin rikicewa yace"Baba Gana, Yaya Lawan, Yaya Baraka, Hajja Yaana".

Yana gama fadar sunansu ya fashe da kuka mai mugun cin rai, Lawan ne ya riko kafadunsa ya tashe sa ya dawo dashi tsakiyarsu yana share mai hawaye, shima kukan yake amman kira yake"Autan Ya Malam, kuka ya kare ai, ya isa haka kaji".



Vda kyar dai aka samu tsoffin nan sukayi shiru da kukan murnar ganin junansu, sannan ne kuma su Goggoji suka kula da Mairoji da sai cika take wai Mamah bata kulata ba, baki taru zata fara musu abinda aka dade ba'ayi ba, Malik ya watsa mata kallo, sannan ya mike yace "Part dina yayi kura, kije ki gyaran, minti talatin na baki, kafin na fito daga bangaren Mamah ki tabbata kin gama".



Cikin rashin sanin maganar ta fito fili tace " daga dawowata, ko hutawa banyi ba, ban gana da iyayena ba, afara da bani aiki, ni dai gaskiya...."



Juyowan dayai yana kallonta ne yasa ta gane yaji mai tace, tashi tayi ta nufi hanyar fita dan pard dinau da Ahmad na tacan bangaren ajiye motoci.



Babu wanda ya kula ta, sai Baba Bulama ne ma zai magana Malam Saje ya tare sa"kyale ta, dole ai ta sabawa hidimarsa, tunda wataran karkashinsa zatayi rayuwa idan Allah yaso".





    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_13_



  Bayan fitar ta ne sannan aka shiga bawa juna labarin bayan rabuwa, kiran sallahr la'asar ne ya tada su, matan  bangaren Mama aka kaisu, yan matan kuma dakunan su Ummie, Laure yar rawar kai har ta samu abokiya dan tuni suka dinke da Sakeena, samarin ma bangarensu Malik aka kaisu, kowa dai da inda aka kaisa dan ya huta.



    Bayan isha aka kuma haduwa, dan zuwa lokacin su Haj Tako sun zo, Mairoji da Ummie suna dakin Mamah dan can maman tace ta koma, shira suke  cike da kewar juna, wayarta ne yai kara tana dubawa taga bakuwar lamba, kin dagawa tayi har kusan miss call biyar, sannan aka hakura da kiran, bayan kamar mintuna uku sai ga Mamah ta shigo kallon yanda sukayi baja baja akna gadon tayi ta girgiza kai tace"an hadu kuma, ba sauki sai na Allah, kije yayanku na kiranki, yace ki hada masa shayi da abu mara nauyi yunwa yake ji".



   Kamar zatayi kuka haka ta tashi, ta daura hijab akan kayan baccin data saka, kicin ta shiga ta na tunanin me ya kamata tayi masa to, taliya tadauka, bayan ta dauko kifi a frige ta gyarasa ta dora akan gas, tana gama tafasashi ta dauko kabbage da yakan spieces, nan danan ta hada mai miyan kifi da kabbage, bayan ta dafa mai taliyar fara, tana juyewa taji an shigo, dubawa tayi taga Sakeena ce da Laure, dauke kai tayi dan tasan halinsu ba kai ne da su ba, yanzu zasu nemi yi mata tijara.



   Ashe wai suma sun je nemantane dan Sakeena nason karban wannan card din na Malik, shi ne Mamah tace musu tana kicin.

   Kallonta sukayi awulakance, Laure ta fara bude flaks din data gani arufe, kamshi miyarne ya daki hancinta, ta hadiyi wani mugun yawun kwadayi, dayan ta kuma budewa taga faran taliyace, wani faranti dake gefe ta dauka zata diba, dan bata bi takan Sakeena dake titsiye Mairoji ina katin yake ba, burinta kawai ta dibi abincin dan da gani miyarnan zatayi dadi.



    Dagowa tayi zatawa Sakeena tayin diban abincin, karaf idansu ya hadu yana aika musu da wani kallon idan na kama ku, da sauri ta ajiye farantin tana sunkui da kai.Sakeena ce itama ta kalli sashen da yake, cikin inda inda ta fara neman kare kanta, dan ya ganta ne dumudumu ta murdewa Mairoji hannu.



Bai musu magana ba, illa farantan daya diba da abin dazai bukata, fita yayi bayan yawa Mairoji kallo daya, ya dauke kai.Itama babban faranti ta dauka ta jera komai akai har da flaks din shayi haka ta raba ta gefensu ta fita.



Sai bayan fitar ta ne, sannan Sakeena ta sauke gwauron numfashi tace wa Laure"wllh gayennan karshene, ya gama tafiya dani, amman waccen shegiyar yarinyar da alama kanta na rawa, kuma zan saita mata shi, Malik ai mijin manyan yara ne ba, irinta kwailaye ba, ni fa kinga ko da bazai aureni ba, zan iya basa kaina, dan da gani zai bada wuta, Allah ya basa irin zubin da nake so ajikin namiji, wllh ko zan rasa komai na bazan yarda na rasa wannan hajar ba".



Baki Laure ta tabe tace"ai wllh duk haduwarsa bai kai yayan saba, tab....ke kinga Ya Ahmad kuwa, karshen kyau da haduwa".



"Au daman yana da yaya, amman ba'a nan yake ba ko, dan tunda muka zo ban gansa ba".



" yana da wa, wanda suke uba daya, babarsa kanwar Hajiyarmu ce, auren zumunci aka musu, amman ta rasu tun bayan ta yaye sa, sai dai fa yafi kanin nasa dadin sha'ani, yanada da dadin zama".



Sakeena tace "wowww amman zanso na gansa gaskiya, naji kince yafi wannan haduwa".

Harara laure ta maka mata tace" ki kama kanki, Ya Ahmad nawa ne ni kadai, abinda zai fi miki shi ne ki kama Malik, dan dashi kika fi dacewa".



Shiru Sakeena tayi dan ta tabbata Laure ta fita buyagi, kuma ta fita iya tafka rashin mutunci dan haka taja bakinta tayi shiru, har suka karasa dakinsu, sannan suka shiga wata shirar, anan Sakeena take fadawa Laure ai Mairoji cikin shege fa tayi shi ne ta haifi wannan yar tata, nan tayi ta mata famfo, tare da zugata akan ta tabbatar yan uwansu na nan sun san abinda Mairoji tayi, domin karta bata musu sunan gida.





++

Ahankali ta tura kofar falon ta shiga da sallama, yana kwance rigingine da kananun kaya kamfanin addidas, rigar armless sai wandonta treequarter, remote ne ahannunsa yana serching na wasu tashoshin ball, bai kalle ta ba amman ya amsa sallamar aciki.

Ajiye tiren tayi akan center tabble dake tsakiyar falon, faranti daya ta janyo ta fara hada masa abincin, bayan ta gama ta hada masa shayi awani babban kofi, sannan ta mike tayi hanyar fita, sai data kama handle din kofar sannan yai magana yace"waya baki izinin fita?".



Cak ta tsaya sannan ahanakli ta tako ta dawo gefensa ta tsaya tana cura baki, dan ita barci take ji, yana hankalce da ita amman sai ya share ta, bai ankara ba sai gani yayi tana sharar kwalla, tana jan shessheka, tashi yai zaune yana kara daure fuska, tuni ta hadiye kukan da take shirin saki, gefensa ya nuna mata alamar ta zauna.



Ba musu ta zauna tana takurewa waje daya, farantin data hada mai abincin ya turo mata gabanta, murya can ciki yace"cinye kibani flat din".Shi kuma ya dau kofin shayinsa yana sha, ya maida hankalinsa kan tv.



Adan raunane tace"nifa na koshi".

"Kina batan lokaci".

" Allah ni dai na koshi, kuma ni barci nake ji".

"Raini ya fara shiga tsakaninmu ko?".

Jan hanci tayi tana sauke wasu kwalla, ta janyo abincin ta fara ci, tan matsal kwalla, da yake gulmaammiya ce sai gashi ta kusan tashi da fiye da rabin abincin, ruwa tasha tana sauke gyatsa, tare da yin mika tana hamma.



Harararta yayi yace" dalla sauke hannunki kasa, kin wani cikamin hanci da warin hammata, kazama kawai, tashi ni kibani guri".



Tashi tayi tana cura baki ta fita, tsayawa tayi abakin kofa ta daga hannunta tana shinshina hammatarta taji wai ko da gaske warin yake, karamin tsaki tayi jin banda kamshin sure babu abinda ke tashi, hararar kofar tayi tana sakin kwafa, sannan ta wuce bangarensu, tana shiga ta tarar da Ummie har tayi barci ita da Simrah, rabawa tayi gefensu itama ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.





++++



Mutanen Maid sun dau kusan sati sannan suka fara haramar juyawa, Babagana ya dage lallai sai da Mairoji zasu tafi, magana dai har takai gun baban Mairoji shima ya shiga ciki, da kyar aka barta akan zata na zuwa Maida ita da sauran yan uwan na nan don karfafa dankon zumunci.

Salme ma an mika ta ga ahalinta, sunyi murna sosai kuma sunyiwa Kawu godiya daya tsaya mata har ta kammala sakandire, anan ne kuma suka nuna aure zasu mata, tunda ta isa, Baba Lawan ne ya nemawa Gimba aurenta, tunda shine jikansa na fari, kuma basu taho da iyayensa ba, dukda su iyayen Salme sunji dadi kuma sunyi na'am da abun, sai dai ita Salmen ba haka taso ba.



Burinta ta auri wanda zai tayata nunawa duniya itama wata ce, so take tayi auren da ko yaushe za tayi wa mutane alfarma akan komai nasu, burinta tayi auren da zata nunawa Mairoji ba ita kadai bace mai sa'a arayuwa, yanda kusan ko da yaushe Mairojin sai tazo wajen ta cin arziqi da neman alfarma.

Duk yanda iyayent suka so ku nuna mata dacewarta da Gimba abun yacu tura, karshe sai da wani kanin babanta ya mata dukar kawo wuka sannan aka samu sauki akanta, dukan daya sata daumar alwashin ramuwar gayya akan Mairoji, tunda duk kusan ita ce taja mata, da ace ta bar mata farinjinI da daukakar da take dashi ai da ba haka ba.



Bayan tafiyar yan Borno ne, da sati biyu Malik ya tattara ya koma, bayan dogon kashedin daya samu daga wajen Goggoji kan cewa yana kuma samun hutu ya dawo ayi maganar aurensa da Mairoji, amsa mata yayi da to sannan ta barsa ya tafi, dan Malam Saje yabi yan uwansa zuwa Maid.





+++

"Khaura Abdullahi Mahangi, ya ta uku awajen Ahj Abdullahi Mahangi, dan majalisa ne daya rike mukamai kafin wannan matsayin da yake kai, gaskiya gidansu ba laifi akwai tarbiya, kuma akwai wadatar ilimin addini, idan tayi maka, zan iyama jagora".



Numfashi ya sauke, sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment