You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riga da kayan ciki, shima sai da kyar ta yarda yasa mata, sannan ta tada sallar la'asar, kafin ta idar sai gashi da tire mai dauke da madaidaicin kofi da shayi aciki yana turiri, sai sandwich akan gefe da spoon sai wani dan kananun kwayan magana awata yar gwalba.



Ajiyewa yayi harta kammala, sannan ya dawo kusan da ita ya soma bata, tana gama ci kuwan ta fara kelawa amai awajen, sai data gama ne sannan ya taimaka mata ta dauraye bakinta ta koma kan bed shi kuma ya gyara wajen.



Haka dai ya ke hidima da ita har magrib, sannan ya fita, kafin ya dawo kuwan ta koma dakinta tanayin sallar isha ta dane gado ta kudundune dan wani rikitaccen zazzabi ne yake hawan mata kai.



Shi kuwan bai shigo gidan ba sai wajen goma na dare, kai tsaye dakinta ya nufa dai dai ya shiga yaga wani ya fito daga bandaki da shortnikker ajikinsa sai towel da yake goge suman kansa, kan yayi magana har ya bangajesa ya fita da gudu, mai da dubansa yayi kan Maryam da take sauke nunfashi da kyar da alama zazzabin ne yake dawainiya da ita, sai dai daga ita sai wani karamin siket iya cinyarta sai rigar da bata gama sauka kan cibiyarta ba.



Numfashi mai zafi ya fesar sannan ya fita da sauri, dai dai bakin get ya hango wannan gayen ya fita da gudu, shima bayansa yabi, nan suka kafa yar tsere, abinka da dan ball ya saba guje guje, sai gudun bai masa wuya ba, ya kusan kamasa kenan wata mota data shawo kwana ta daukesa sama, sai daya gama wahala asaman sannan ya fado baya munfashi, da gudu ya karasa kan sa yana dan jijjigasa, taba kirjinsa yayi yaji zuciyarsa tana harbawa kadan kadan, da sauri ya kira motar asibiti anan suka zo suka daukesa, shoma Malik din binsu yai sai dayaga dakin da aka shigar da gayen sannan ya tafi gida zuciyarsa cike da rudani da tunaninnika.



Dakin Maryam din dai ya sake komawa nan ya kwanta agefenta yana sauke ajiyar zuciya, yanzu kam ya tabbatar da cewa ana hada musu gadar zare ne, kuma tabbas na kusa dashi ne ke hada mai, amman baya son ya zargi kowa tukun har sai ya gama bincikensa.



Washe gari da safe haka ya kuma komawa asibitin nan suka tabbatar mai jikin da sauki sannan zai iya farkawama akowane lokaci daman buguwace tasashi suma, sai yada kafatawa ma'aikatan wajen kashedin kula dashi sannan ya bar asibitin.





     *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _25_

Kwana kusan goma ana jinyar wannan gayen, kuma kullum ne sai Malik yaje ya duba sa, sai dai har lokacin yaki magana, yaki ya fadi wanda ya turo sa, amsa daya yake badarwa itace, shi ya turo kansa, to da abin ya ishi Malik sai ya dauke sa daga asibitin ya kaisa wani kebantaccen waje ya fara azabtar dashi.



Kwanasa uku awajen ya gama galabaita, ranar Malik ya mai wani mahangurba, da wahala ta ishesa yace zai fadi komai, gyada kai Malik yayi yaja kujera ya zauna yace "ina jinka, ka fadan komai kar ka ragen, idan kaki fadamin kuma zakayiwa kanka ne, dan sai dai adau gawarka abakin hanya".



Cikin rawar jiki da tsoron mutuwa yake gyada kai, yace zai fadi duk abindaya sani.







++

Bayan kwana biyu ya hada kansu suka wuce London daman ya dage tafiyar ne saboda abinda daya faru, gidan nasa ba wani babba bane sosai saidai ya kerewa wancan da suka baro, babban falo ne sai corrido guda biyu suna kallon juna, idan an shiga dakunane kowanne guda bibbiyu da falonsu, daga gefen dama idan anshiga babban falon kuma wani dogon hanyane da zai sadaka da bangaren Malik din, tsarin ginin kamar anan gida 9ja, sosaigidan ya burge Maryam, haka ko wace ta shiga da jakarta dan ya hana su daukar komai daga wancen gidan.



Kwanan su biyu da zuwa ya dawo dakin Maryam, ranar kuwa tun la'asar ta shiga kitchen ta fara hadamai dinnar lafiyayya, tana gamawa ta samu tayi wanka, dukda ba dadin jikinta take ji ba, dan tun lokacin da abinnan ya faru take rashin lafiya, gashi har zuwa yanzu taki yarda dashi yana fara tabata take sakin mai kuka.



Sai wajen takwas na dare sannan ta fito babban falon dan haka ya gindaya musu duk ran girkin mace za'a hadu ne ababban falo aci abinci, in yaso daga nan kowa ya koma bangarensa.



Yana shigowa kuwa ya saki wani lafiyayyan numfashi yana lumshe ido, ko ina na gidan ya dau kamshin girkinta dana turaren wuta data hada shi a borner, waje ya samu ya zauna ganin babu kowa afalon, sai dai baiyi ko mintuna biyu ba ya jinyo tafiya yana daga kai ya ganta tasha simple makeup, ba wani tarkace akan fuskarta amman she look cutes, hannu ya ware mata cikin kunya da yauki take karasawa wajensa, ahankali ta shiga jikinsa ta lafe akan bare chest dinsa dan ya bude duka maballan rigarsa, sai ya zama wani sexy style kaman yayi shi da gangan.

Wawan tsakin da aka ja musu akai ya sasu saurin dagowa, Sakeena ce ta nufi kan dinnig tana kananun mita, da kallo suka bita, sannan suka maidawa juna wani kallon ganin yanda fuskarsa ya sauya lokaci guda tayi saurin sakarmai muemushi tana tabe baki kamar kuka take son saki.



Shashancewa yayi wajen kallon fuskarta, shi sai yake ganin kamar bai taba ganin wadda tabara da shagwaba yai wa kyau ba irinta, gashin dake gefe gefen fuskarta wanda sak irin nashi ne yake shafawa ahanaklai kamar mai yin rada yace,

"Yar mummunata, yar baka mai gwaigwayayyen gashi".



Tasan ya fada ne cikin tsokana, amman sai tasa mai fuskar sakalci tana son tashi ajikinsa, shi kuwan gaba daya ta gama tafiya ne dashi kawai yana kallon nonuwarta ne da suka bulluko ta samar rigar, sunyi wani irin cika kamar mai danyen ciki.

Baki ya dan lasa yace" honeyput ina jin yunwa, kuma ina jin yunwar abinci".



Dariya ta sa mai daukar hanakli ta mike tana kamo hannunsa tace "taso na cika ma cikin ka yau abincin gida nayi mana ai".



Fuska ya bata ya biyo ta yana mata mita,

" ni daiba wannan yunwar nake ji ba, kawai malama kisan yanda zakiyi dani, haba ai nayi hakuri, kusan sati biyu amman ba 'a kulani, kamar wani dutse".



Bata kulasa ba dan ta kula yau a maganannen sa yake, sauna zama ta janyo plat ta fara saving dinsa, yawun tsokana ya hadiya yace "kai abincin nan da alama zai tsinken kunne, daukon wayata na kira Mamah naji muryarta, kar naje na gama cin abincin na kula kunnena ya fadi kasa".



Dariya ta saka tana dan kallon gefen da Sakeena take tamai alama dayai shiru mana, kafada ya dage yana tabe baki, bayan ta mika masa ne ta janyo wani ta kuma zubawa da dan dama sannan ta ajiye agaban Sakeena dako ta dago kai ta kalle su, danne danne take kawai awaya sai dai hankalinta nakansu ne, baki ta tabe ta janyo plat din tana yamutsa fuska kaman ansata cin abincin dole.



Shiru wajen ya dauka bakajin komai sai karar haduwar cokula da faranti, Malik ne ya fara janye kujerarsa baya yana fadin " Alhamdulillah, sannan yadan kallin sashin da Sakeena take ya kau dakai yadan kalli Mairoji yace"da so samu ne kullun idan girkinki ya zagayo kina min irin wannan cimar ta gida, nasan sauran kwanakin zanyi su ne da cimar kayan gwangwani, Allah ya albarkaci hannunki kici gaba da bani daddadan girkinki".



Cikin gajiya da takaicin su Sakeena ta mike tace "ai basai kasa mata albarka zansanni ba kowa bace awajenku ba, kuma nasan dai duk tsiyar mutum bai isa idan ya tsinen tabi ba dan ba shi ya haifenba, ai kin wofi kawai , kuma sai Allah ya saka min zalintata da kuke, nasan ai tunda ka hadamu dole sai kuna daukar hakki na, kuma wllh ban yafe ba".



Galala Maryam ta saki baki tana klonta, zatayi maga Malik ya dakatar da ita, sannan ya mike ya kamo hannunta ya nufi bbangarensa da ita, har ya kusan shigewa, ya juyo yace,

" idan kin gama haushin naki ki kashe mana glub din ko ina, mu dai mun shiga bita da neman lada, sai da safe".



Tsaki taja tana sakin mawa Maryam din ashariya har tana fadin ai karuwanc8n da take ne har ya fara tabaka, ai de ne ta dage koma dai danginta mutan ruga sun hadota da surkullen da zata dauke hankalinka daga kaina ne, to wllh ta Allah ba tasu ba yar gidan matsiyata, dangin kwadayayyu.



Su dai basu san tanayi ba, dan tuni sun shike turaka, suna shiga kam ya janyota ya rungumeta yana matsa duwainis dinta, kara shige mai tayi dan yanzu kam tana jin itama tana da bukatarsa, cikin hikima da dabara ya rabata da kayanta ya barta da pant kawai dan daman ba za breziar take ba, arba yai da cikakkun na shanunta na ya kara rudewa tuni jikinsa ya fara rawa har yana sakin mata wani dan gurnani agefen kunne.



Itan kam bata san sanda ya cire nasa kayan ba, kawai dai ta jisa naked ne, sosai yake bata wuta da zazzafan romance, ko wani lungu da sako sai da ya lashe, yan kananaun kuka da na sakalci kuwan ya gama ruda masa kunne, sosai take jin fargaba da tsoro dan wannan ne karon su na biyu, sai dai yanda take jinsa ajikinta kamar ta mayar dashi jikinta ne ta huta, idonsa cike da fitina yake kallon yadda take damkar bedshit kaman hanklainta baya tare da ita, anutse cikin salo da dabara yake rabarta har ya samu ya gama shiga yanda yake so, atare suka sauke wani razanannen nishi, ita sai data dan hada da kuka dan wajen kamar an maidashi yanda yake ne da, shi ma wani dan ihu yasa yana jin dumin jikinta har kwanyarsa.



Ahanakli ya fara moven csai dai ko mintuna biyar baiba ya fara fita hankalinsa, nan ya fara da sauri kamar ance masa ga wanin nan zai kwace ta, sosai suke son ruda kansu da kananun ihu da sumbatu, duk da itan wani zubin tana dan jin zafi sai dai kamar dadin abin yafi zafin yawa,ya dau tsawon lomaci yana yawon bude ido a duniyar maji dadi, sannan ya kankame ta yana sauke wani dan kara, gaba daya jikinsa rawa yake, ga uban zufan daya hada.



Kanta yake shafawa ahanakali , sai bayan mintuna sannan ya hadasu da bedshit din ya nufi ban daki, wanka sukayi anan ma sai tsokanarta yake yana neman ta kulasa ya sake mai maitawa amman taki, da haka suka dawo dakin sannan sukayi shirin bacci suka kwanta.





++Haka rayuwarsu take juyawa, sosai ya daukewa Sakeena wuta dan baya shiga sabgarta, idan ta zo turakarsa fine, idan batazo ba kanta, daman kuma ko tazo babu abinda yake mata, haka zata gama mitarta ta kwanta, ga bangaren K2 ma ya dauke masa wuta shi ma, don ma yanzu sunyi nisa da juna amman ahakan zuwan k2 din uku wai ya kawo musu ziyara ne, kuma yayi kewar su.



Watansu biyu a London sai dai Maryam har lokacin ba ta jin dadin jikinta, don haka zata kusan yini da zazzabi, idan yamma tayi kuma ta jita garau har zuwa safiya, ga wata yar cika data karayi, fatarta ta murje sosai, kullum suna waya dasu Mamah, Ya Khausar, Ummie Fannah da sauran yan uwa,sai dai basu taba waya da Laura ba dan batada ma number dinta.





***Rugar Na-Ma'u.



Acan Rugar Na-Ma'u kuwan sosai Hajiya ta daga hankalinta, daman ga laifin da aka mata aka bawa Mairoji Malik, amadadin abawa Ummie, sannan gashi har Malik din ne kewa Laura korar kare wai tabar musu gidansu, ranta kam ya sosu, sai ta rasa yanda zatayi, wata kawarta Haule ita ta bata shawara idan tana da abun hannunta ta kawo adaure mata bakin Mamah kawai da ya Ahmad ya zama sai yanda ssukayi dasu,akuma janyo hankalinsa kan Laura, da wannan shawarar tayi amfani cikin abinda baifi sati ba kuwan sai ga Ahmad yazo Rugar Na -Ma'u wai yazo gaida goggonsa ne, da zai tafi ne yake ce mata aturo masa Laura masa su gaisgaisa.



   *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _26_



    Yana tsaye jikin motarsa ta fito cike da yauki, kallonta yake daga sama har kasa, aransa yake tunanin mai ya kaisa, mai zai da ita, ko kadan bata burgesa, but ko afuska yanajin bai isa ya nuna hakan ba, yana tsaye har ta karaso.



   Taunar cingam take cike da neman daukar hankali, sai yake jin da zai iya, tsawa zai mata yace ta koma tayi sallama amman yana jin bayada wannan kwarin gwuiwar, murmushi ya mata na yake cikin kwantar da murya yace,

"Ranki shi dade, ashe ana ganinku, kwana biyu ya gida ya jin dadi".



Kamar bata son amsa mai, tamai jimla tace " lau, nomal ya kake".



  "Lafiya, Alhamdulilla, ya karatu ana tayi ko?ko an kusa gamawa ne".



   Baki ta tabe ta ce" Uhm....da saura dai, ya mai jego da baby".

   Sosai yaji dadin yanda ta nuna tasan da zaman matarsa da yarsa yace"suna lfy suna gaidaki, bayan bakya zuwa yanzu kin daukewa gidannamu kafa".



   Shiru tayi bata tankaba dan so take ta koma gefe ne ta taka rawa son ranta, da wani ya fada mata yace akwai ranar da Ahmad zaizo wajenta yana janta da hira irin haka ba zata taba yarda ba, amman yau gata gashi yana sakin mata surutai da murmushinsa dake narkar da zuciyarta, mutumin dako agidan su baya sakin baki yai magana, sai idan tare da Malik yake yau gashi sai zuba yake mata.



   Kallonsa tayi tadan narke fuska tace" babban Yaya zan shiga ciki, akwai wanda mukayi dashi yau zaizo, to bana son yazo ya gani dakai kuma yaji haushi".



   Nan danan mood dinsa ya sauya, cikin rawar baki yace"haba mana Laura karkimin haka dan Allah, saboda ke fa nazo garinnan amman kike korata saboda wani bare, pls mana ki bani dama nima na nuna miki kalar tawa soyayyar".

   Anzo wajen ta raya aranta, amman afuska sai ta dauke kai tace "ah ah, kaifa kasha fadamin ni iya matsayin kanwa kawai ka bani , kuma kaida kake da matarka yar masu arziki da abin duniya, ni kawai ka barni na auri wanda yake sona, tunda kai ba sona ne aranka ba".



   Tuni ya dabarbarce ya rude, ya rasa ma ta inda zai fara, kawai sai ya matso dab ta ita, cikin shaukin daya aro yace" Laura pls ki bani wannan damar, ko ayau kika ce na turo ayi magana zan turo, ashirye nake tsab na mallakeki dan , Allah karki juyan baya kinji".



   Kanta ta kawar tace "naji kaje zanyi tunani akai".

Kan yai magana ta shige gida da dan sassarfa dan murna ce ke dibanta, kai ya shafa yana jin haushinta aksan ransa, sai dai bayada yanda zaiyi ko kadab bakinsa bazai iya fadar laifinta ba koya aibata ta, da haka shima ya shiga motarsa ya tafi gida.



   Cikin kwanaki kadan magana tayi girma, Mamah taso hanawa amman sai iyalan Malam saje suka nuna sunfita iko ai dashi dole taja bakinta tayi shiru, amman tabisa da addu'a, bangaren Khausar kam ko kadan bata wani daga hankalinta ba, baran ma da sukayi waya da Mairoji ta babbata shawarwari da yanda zata kame kanta karta bari ko kadan raini ya shiga tsakaninsu da Laura din, sosai taji dadin kalaman Maryam duk da ta girme mata sosai amman atakaninsu basuda abokan shawara sama da junan su, sun gama yarda da nagartar junan su, sosai sukejin dadin mu'amalantar juna kamar wasu shakikan kawaye ko yan uwa.



   An kai kudi an sa ran bayan karamar salla, dan lokacin azimi sauran kwanaki koma ne, sai dai abindaya ke saka kwanciyar hanaklai da Mamah shi ne ko kadan baya wannan rawar kafar da tasan maza nayi idan zasu kara aure, sannan yana kara kyautata ma'amalarsa da matarsa, to ganin hakan sai ta dauke kai tabi su da addua kawai.





****

   Wasa wasa Maryam rashin lafiya ya mike, amatsayin ta na wadda take karantar science tuni ta gano meke damunta, saidai ta rufe ne dan tanason taiwa Malik bazata, kusan satinsa uku bayanan suna fama da Laliga, kuma sai na da wasu sati ukun zai dawo, ana sauran kwana biyu sallahkarama kenan.



  To da yake ta fara ganewa inda Sakeena ta dosa shiyasa ko babban falon ta dena fitowa, ga K2 daya mayar da gidan wajen zuwansa, baya kwana uku ko hudu bai zo ba, haka zasu zo shida kawayenta nacan su cika gidan da kade kade, da bushe bushe, ko sau daya vata taba marmarin zuwa inda suke ba balle su ganta su nemi tada mata hanklai.



   Ahankali ake gabatar da ibadar Allah, sosai Maryam ta maida hankalinta kan ibada da neman gafara, tare da yiwa mijinta adduar samun nasara aduk inda ya shiga, gashi Allah ya taimaketa laulayin da take baya sata jin komai, harkokinta take kamar da can, sai dai idan sha ruwa ne to duk abinda taci sai ya dawo, sai zuwa can dare take samun tasha kunun tsamiya da take da garinsa, shi ne yake dan tsayawa.



   Anyi azumi sha biyar Malik ya aiko musu da visa da komai na tafiya saudiyya, da wannan sakon ya isa ga maryam kam har kuka tayi na farin ciki, haka suka shirya bayan kwana biyu suka tafi ita da Sakeena, kan cewa zai same su acan ana gobe Arfa, ranarda suka sauka kuwan da yake da yamma ne ko mintuna batayi ba ahotel din ta nufi ka'a ba, cike da shauki da alfahrin samun miji kamar Malik, acan tayi zamanta har akasha ruwa sai bayan goma sannan ta dawo masaukinsu.



    Washe gari ma tun asuba ta uma ficewa  sai dare sannan ta dawo, haka ta ke gabatar da ibadarta mai tsafta cikin aminci da soyayyar Addinin islama, ranar data cika kwana biyar da fara zuwa tana zaune gab da za'a sha ruwa, wata yarinya ce balarabiya ta zo wajenta ta tsugunna, mika mata wata nannadaddiyar leda tayi tana mata murmushi, karba Maryam din tayi tana maida mata murmushin, sannan tace ,

   "Shukran, ayna ummuki"



Dariya yarinyar tasa tana mata nuni da bayanta, juyawa tayi tana kallon matar kyakkyawa sosai kamar ka sace ta ka gudu, sai wani magidanci daga gefenta amman ya juya baya, kamo hannuta yarinyar tayi tana janta, kamar wadda aka daurewa baki haka ta kasa magana sai bin ta take, sai data kaita har wajen iyayen nata sannan cikin muryar yaranta tace,

   "Abbie.."

Ta janyo hannunsa ya juyo gaba daya yana fuskantarsu, gaban Maryam ne yai wata mahaukaciyar faduwa, cikin rawar murya take nunasa da hannu tace "kai ne....ya Malik.....yaushe kazo, wannan yarinyar fa taka ce, ina ka sameta, yaushe kayi wani auren har ka ajiye yara haka?".



   Gaba daya ta gama rudewa ssai hawaye kawai take, shi kuwa wanda ta kira da Malik shima suman zaunr yayi yana binta da kallon, kamara sama taji ya ce,

" Safiyya ce ko yarta, kamarku tayi yawa, Safiyya ce ke ko, yar uwata dana rasa?".



  Kai Maryam ta girgiza tace"ba Safiyya bace, yarta ce dai, Maryam amman waye kai dan Allah, kayi matukar kama da yayana Malik, babu abindaya rabaku sai dai ka fishi manyanta, dan Alah waye kai".



   Hannunta ya kamo yacewa matarsa dake kallonsu baki sake"kamata muje gida, zamuyi magana acan, kinga har ansha ruwa muna tsaye anan."



   Kamata kuwan tayi, suka nufi gidansu dake gefen titin bayan ka'aba, sai da suka sha ruwa sannan aka nutsu kallonta Mutumin yayi yace "zan baki amsar tambayoyinki duka, amman kafinnan ki fadan daga wanne gari kike, kedawa kukazo kuma, sannan waye kie cewa muna kama dashi?".



  Kai ta dan sunkuyar sannan ta kuma dagowa dashi tace " sunana Maryam, kuma ni yar Nigeria ce, karamar hukumar jahun, dake garin Hadejia wasun suce mata kuma Jigawa, muna zaune awata babbar Ruga ne da ake kiranta Rugar Saje, watau kakana, sai zuwana nan kuma nida abokiyar zamana ne muka zo."



   Kai yadan jinjina cike da gamsuwa yace"ina shi mijinku da ita abokiyar zaman naki".

  "Mijinmu yana can wajen sana'arsa,sai nan da kwana sha biyu zai zo nan, ita kuma kishiyar tawa ban san inda take ba, dan tunda muka zo ban kuma ganinta ba".



Zama ya gyara yace " to dai da fari ni sunana Abdulmalik Muhammad Saje, ni kanin Mamanki ne uwa daya uba daya, tsautsayi ne ya rufta damu muka fada ruwruwa daga kwale kwale, tun daga lokacin bansan mai ya faru ba, na dai ganni ne anan kasar, tsawon shekaru goma sha bakwai, tun kuna da kwana biyu da zuwa na ganki kuma na tabbatar wa kaine ke jinina ce, ashe kuwan haka ne, ina Safiyya yanzu yaranta nawa, ina Yaya Badan, da Tako da yaran yaya Badan, harda wanda yaci sunana".



   Hawaye ta share tace "mamata ta rasu awannan fadawa ruwa da kukai, sai gawarta aka samo, Abba Badan kuma yana nan da yaransa, mai sunan ka shi ne mijina, ita kuma abokiyar zaman tawa jikar wan Malam saje ce dake can Maiduguri, sai dan gidan inna Sa'adatu mai rasuwa Ahmad, bayan salla za'ayi bikinsa da yar Hajiya Tako, zai kara mata ta biyu".



   MashaAllah kawai yake fada, yanajin kamar yayi tsuntsuwa ya gansa, a Rugarsu, juyawayai yana kallon matarsa dake share hawaye yayi murmushi yace " Bahi sarkin kuka sai ashare hawayen ai".



  Murmushi tayi tana boye fuskarta, sai lokacin suka ankarankara dadare yayisoasi, tashi sumayi su dauro alwala sanna ya musu jami suka sallaci isha da ashan sannan suka kwanta....





    *RUGAR SAJE*



BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN



   WATTPAD@NUSYSA

I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO



  –&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo



                  *[=ØÝÜI.W.A=ØÝÜ]*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



   _Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



  _27_



  Da gari ya waye ma, tare suka fita gaba dayansu, wani babban waje Uncle din ya kaisu yace suyi siyayyarsu duk abinda suke so su dauka, daganan suka wuce masallaci, dai gab da shan ruwa sannan suka nufi gidan wani abokinsa, balarabe ne, anan suka sha ruwa, tun aranar Maryam taso sanar da Malik halinda ake ciki amman Uncle ya hana yace su masa bazata sai yafi.

    Maryam din kuwa tuni ta kwaso kaayanta daga hotel din da suka sauka ta dawo dasu gidan Uncle dinta, da haka suke gabatar da ibadarsu cikin aminci da buwayar ubangiji.



    Ana sauran kwana biuu salla Malik ya sauka, shi da sauran yan tean dinsu musulmai wadanda zasu gabatar da aikin hajjinsu, bai samu Maryam ba ahotel din, sai yai tunanin ta fita ne, sai dai ya taki sa'a dan ya tarar da Sakeena adakinta, anan ta fara kawo mai karairayi wai ai Maryam din bata zama, tayi wasu abokai maza da mata su ne suke daukarta kullum suna fita, sai can dare take dawowa kamar abuge take, to dayake ma yanzu ya gama sanin wace ita sai kawai ya bita ayanda take so, yai ta fada  har yana cewa"wllh dani Maryam take, watau ba zata bar wannan halin nata ba dai?, zata dawo ai ta same ni mai rabani da ita sai Allah".



   Murmushi Sakeena tayi tace "Uhm, wani abunma ai dan karna fada ne kaga kamar na mata sharri, amman lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro ai."



   Afuzge yadan kalle ta yace "kwantar da hankalinki, ai nasan maganinta ne, ina nan zata dawo ma duk inda ta shiga."



Yana fita ya kira Maryam din awaya, nan yake sanar da ita

Please Login or Register in order to submit comment