You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce" ka fara min iso ga mahaifinta tukun, duk yanda yace sai mu ga me zamuyi akai".



Nan sukayi sallama, bayan tafiyar mutumin shi kuma ya kira Malik awaya, nan ya sanar dashi komai dan basa iya boyewa junan su duk abin daya shafe su irin haka.

Shima yayi na'an da batun cewa ya fara tuntubar mahaifinnata tukun, sannan ya sanar dashi abinda Goggoji ta fada mai, tunda daman tuni yasan da dawowar su Mairojin, dariya Ahmad yasa yace"kasan kuwan Goggoji ta rigani furtawa ne, amman nima abinda ke.raina kenan, atsaida maganarku kawai kowa ya huta".



Iska ya fesar daga bakinsa, yace "broh....wancen dan kwayar fa, ya dage lallai sai dai shi zaya aureta, Allah banda ina ganin darajar Hajiya da saina sa an kullen shi, bayan komai ya daidaita ya fito".

Ahmad yace " wai kana nufin Mamudan Hjy Tako?".



"" shi mana, yaron ya mugun shigarmin hanci da kudundune, kawai dai ana barin halas ne dan kunya, amman da yaga aikin yan kwaya wllh".



Dariya kawia Ahmad ke.masa dan babu abun dayake fahimta amutmryar Malik din sai tsagwaron kishi, samu yai ya lallaba sa sannan sukayi sallama.





_Allah ka bawa babanmu lafiya=ØOÞ_.





    *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



   _14_



Bayan wasu yan lokuta aka tsaida ranar bikin Malik da

Mairoji, da kuma na Khausar da Ahmad, domin sun tattauna atsakaninsu, sun aminta da juna kuma.

    Ranar da aka sanar da sa ranar bikin, Mairoji tayi kuka kamar idanunta sa fita, dan ita tunda take bata taba son Malik da sunan so na aure ba, Ahmad take so, shi ta taso da soyayyarsa, kuma shi take fatan kasancewa da shi amatsayin mijinta.



   Acan Maid ma ba karamin rikici akayi ba, dan Sakeena ta daga hankalinta ita Malik ne zabinta, so an tsaida magana akan cewa sai dai tayi hakuri, dan ba za'a so ta dalilin haka zumunci ya samu tangarda ba, da fari kowa yayi na'am da wannan zancen kuma an barsa, amman bayan wasu yan kwanaki sai ga Babagana ya kuma tada maganar yace dole ne abawa yarinya abinda take so, to sudai iyaye basu da ta cewa tunda Babagana dai shine babba dole sai abinda ya yanke za'a aiwatar.



  ++

Da Malik yaji zancen bai ce komai ba, Mamah tayi zaton zaiyi bori kamar yanda ya saba idan za'a masa abinda ransa bai so ba, sai dai abindaya fada mata ya sata wasi wasi, da kuma dora ayar tambaya akansa.

"Mamah...da Maryam da Sakeena dukansu kannaina ne, babu banbaci sai na halayya, kuma ko wacce dai da halinta zata zauna, illa iyaka dai wadda tamin rashin da'a, za ta gani akwaryar cin tuwanta".



   " amman Malik anya kuwan zaka iya rike mata biyu, zaka iyayin adalci atsakaninsu, karfa agarin gyaran zumunci abata zumunci".



Dariya kawai yayi yace "Mamah ki bar batunzanyi adalci ko ba zanyi ba, kawai idan kukaga yarinya na ware ta , to ku tabbata tana kawo min danyan kaine".



   Shiru tayi tana saurarensa, sai can ta ce"bazan boye ma gaskiya ba d'an Maliki, Maryam banyi maka sha'awar aurenta ba, Ahmad nayi wa sha'awar ya aureta, tunda da bakinka ka fada min ita zabin Malam Alhaji ce, gaskiya bazan baka yata ba kuje kuna gasamin ita kaida waccen yarinyar daba hankaline ya wadacetaba".



   Shiru yayi yana saurarenta, baice mata komai ba ya katse wayar dan bashi da kuma abinda zai fada mata, Ahmad ya kira ya fada masa komai, shima dariya kawai yayi yace " kaji Mamah da wani zance wai ni tayiwa sha'awar aurenta, to ai ni kallon kanwata nake mata, banda wannan ban taba kallonta da wata manufa ba, kaga share kawai maybe ta fadi haka ne, dan ganin ba iya yarta kadai zaka auraba, kasan mata ita nan tana taya yarta kishi ne".



  Baki ya tabe yace"koma dai miye, ni duk su biyun ai ba zabi na bane, idan sunce ma ba zasu bani ba, ban damu ba daman dan sun matsa nayi auren ne , banda haka ai da wannan maganar ma bata taso ba".



Cikin tsokana Ahmad yace"har ajiyar taka ma ba zabinka bace?".

   Shiru yai bai amsa masa ba.

"Ok....zan fadawa Mamah ahada ta da Mamuda, tunda shi tun asali ya nuna ita zabin sa ce".



Jin shiru bai amsamai ba yace " Boy....kana ji na?".



  "Yah......zamu dan fita ne da K2 , mayi waya daga baya". Tun kafin ya amsa mai ya kashe wayar yana jin haushinsu duk su biyun, daga Mamah din har Ahmad din.



++

  Ko abangaren Hjy Tako ma abun bai musu dadi ba, amman idan ta tuna ai namiji mijin mace hudu ne, sai taji ba tada matsala mai yawa, tasan yarta zata iya zuwa anan gaba matsayin matar Ahmad din, kuma burin da take ci dai sai ta cika shi.



Haka tasa Laure agaba har gurin wani badiddige yai mata wankan sa'a, da wani koren ruwa sannan suka dawo gida bayan ya basu tabbacin matukar Laure ta shafi jikinta dana Ahmad din to sai buzunsa dan zai zame mata kamar jela ne.

    Tun daga lokacin take taka tsantsan da hada jiki da wani, dan sharadin kenan, kar ta hada jiki da kowa sai shi, koda da kuskure ne, kuma ko tsaohon shekara zai kai baizo ba, kar ta damu, abun yana jikinta, makarinsa dai shi ne hada jiki da wani.



_______



  Maiduguri

    ______



Yau gidan kowa ya tashi da nutsuwarsa, domin sanarwar zuwan Saddiqu zuwa yamma, kowa ka gani acikin nutsuwa yake, duk da bata Allah da Annabi bace ta tsoron fadawa fushin Saddiqu ne.



    Aunty Yaana ita ce kusan babbarsu akaf matasa da yan matan gidan, ita kadai Saddiqu yake dan jin maganarta, ita tazo gidan dan atarbe shi da ita.



  Kamar biyar na yamma, suka iso shida yaransa kamar ko yaushe kusan su bakwai, ahakan ma ya rarraba su ne domin ayarinsu sunfi su talatin kuma shi ne ogan su, bangaren Babagana suka yada zango, bayan yayi wanka ya huta ne da dare aka hadu ababbab falo, nan iyaye da kakanni suka masa fada na barin gida dayai, kamar na Allah haka ya dinga gyada kai yana amsa addu'oin da suke mai, anan aka ci abincin dare gaba dayansu sannan sa'aninsa mazan suka wuce part dinsa dashi kadai ne aciki, anan ma wani sabon zaman shirar akayi, dukda shi hankalinsa baya kansu yana can aikin daya saba na tunanin wacce bai san inda zai ganta ba.



+++



Sati biyu da zuwan Saddiqu su Mairoji suka sauka agarin, sai dai ba Family hause dinsu suka sauka ba gidan yar Inna Baraka suka sauka, anan suka kwanan uku sannan suka wuce ainihin gidan nasu.



    Da murna aka tare su, sai dai  bakin labarin da suka samu na dawowar Saddiqu, Fanna da tasu tazo daya da Mairoji ita take fada mata tayi taka tsantsan, ta kuma iya takun ta.



Kusan sati basu haduba, dukda son ganinsa da Mairoji take, ita hakanan taji koma waye wannan Saddiqun tasan tasu zataso daya, hakanan taji ya kwanta mata tun kafin ta gansa.

  _Afuwan ba yawa_.



  *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_15_



Tana kwance kamar wadda aka tsikara ta tashi ta nufi bangaren Babagana, da sallama ta shiga ta tarar dashi da wani, sai dai ya juya baya keyarsa kawai take gani, ahankali ta karasa wajensu ta zauna tana gaida Babagana, gaban tane ya fadi , hada idon da sukayi ya tuna mata da abun data manta shekaru kusan uku baya.

Kara kallonsa tayi sannan ta sunkui dakai idonta taf da kwalla, murmushi yayi mutumin yace"Maryam yan mata, ina kawayenki da kuma d'ana ko 'yata ?".



Kusa da Babagana ta matsa tana sakin kuka cikin rawar murya tace"Babagana, shi ne, wallahi shi ne wanda ya sace mu daga Ruga, har yaiwa Bad'ejo fyade, Babagana ka taimaka mana kar ya kuma sace ni dan Allah".



Ture ta Babagana yayi cikin bacin rai yace"dan baki da hankali, jikan nawa zaki ce qai shi ya sace ku, yaron kirki mai kamala, shi ne kike neman bata masa suna, tafi can makaryaciyar banza kawai, duk kaunar dana nuna miki shi ne zaki sakan da yiwa gudan jinina sharri".



Baki ta saki tana mamakin Babagana, kallon Oga tayi wanda babu komai akan fuskarsa sai murmushi, gira daya ya dage mata sannan ya kalli Babagana yace,

"Ba sharri tamin ba tsoho, ni ne nan na sace su su uku, amman batun fyade ni ba wadda nayi wa sai ita, ni ban san wata Bad'ejo ba, Maryam dai ita naiwa fyade, kuma lokacin da suka gudu nasan da ciki ajikinta".

Sai ya kalli Maryam din da take kallon sa da mamak8n tagillen da ya ke, yace " ke ina d'an da kika haifa?".



Kafin ta amsa sai ga Simrah da gudunta ta fada kan Mairoji tana mata nuni da bakin kofa tace "Mahmah, Abie yazo yanzu yana wajen uncle uwaisu".



Kallon yarinyar yayi yace " zo nan Mamana, mai.kama da mamanta da babanta".



Tashi tayi kuwa taje wajensa sai ta zauna kan cinyarsa ta daura kanta akadmfadarsa tana wani lunshe ido, kallon Babagana yayi daya saki baki yana kallon ikon Allah yace, "kana kallonta ai kaga Saddiqu, idon, hancin kamannin duka nawa ne, bakin ne dai ta dauko na mamanta".

Ya karasa yana kallon Mairoji da tayi mutuwar zaune, sallamar Malik ta katse musu zaman jimamin da Babagana da Mairoji sukeyi, dan kuwa Saddiqu ya bawa 'yarsa hanakalinsa ne yana mata wasa.



Da sauri ta tashi tana goge hawayen fuskarta, sannan ta gaida Malik din dayake binta da ido, yana kuma kallon Saddiqu da yai masa kallo daya ya dauke kai, ya ci gaba da yiwa 'yarsa wasa.

Zama tai yana gaida Babagana sannan ya mikawa Saddiqu hannu sukayi musabaha, nan Babagana ya gabatarusu da junansu, sannan ya cewa Saddiqu" wannan shi ne wanda zai auri Maryam, za'a hada ne da Sakeena dan biyu zai hada, ja'irin yaro wai shima gasa zai dani".



Ya karasa da fadin hakan yana dariya, murmushi Malik yayi yana dan kau dai kai, Saddiqu kam, tabe baki yai yace"Allah ya sanya alkhairi, amman ka tambayi Maryam din ta fada maka ira wacece, domin ba zata ce min da'yata wani gidan tayi agolanci ba, kuma bazan yarda 'yata tayi nesa da uwarta ba, ka tsaya iya Sakeenan kadai inaga sai tafi maka, idan kuma biyun kake so, akwai yan mata da waya afamily dinnan ka zaba , sai hadaka da wacce tamaka".



Yana gama fada ya foce ya barsu da baki asake, cikin inda inda Babagana yace "am...kana jiko..ahmm, bar shirmen Saddiqu, ai dayake dan fari ne har yanzu akwai wauta atare dashi....kum.....".



Katsesa Malik yayi cikin basarwa yace " ba sai kamin karin bayani ba ai, ba komai, amma ai ita mace allura ce acikin ruwa, mai rabo ne kan dauka".



"Haka ne kuma, Allah ya dafa mana".

Shira suka dan taba kadan sannan ya shiga cikin gida, tunda daman bai gaisa da sauran kakanninsa ba, da kuma iyayensa.





Sati daya Malik yaso yayi su koma tare da Mairoji, sai dai fitinar da Saddiqu ya hada agidan ta hana shi tafiya, dan shi ya ce lallai bai sannwata Bad'ejo ba, shi fa Mairoji yasan yaiwa fyade, kuma sun gudu ne lokacin da cikinsa, ajikinta wata biyu, dan haka babu wanda ya isa ya aure ta sai shi, yayi d aMalik ma ya kafe kan lallai shi ya cancanta da auren Mairojin, tunda shi ne suka taso tare waje daya, kuma ai Malam Saje tuni yace ita ce matarsa.

Kallon kaskanci Saddiqu yamai yace" ashe....ba zabin ka bace, zabin Malam ce, to kaga ni kuma zabi na ce, dan haka kawai ka ja baya, idan ba haka ba kuma faduwa zakayi kasa wanwar".



Da wannan takaicin da Saddiqu ya gumawa Malik ya baro Maid, ganin abun yaki ci yaki cinyewa yasa aka tsaida bikin Malik din da Sakeena, idan yaso batun Saddiqu da Mairojin ayi sa daga baya, da wannan shawarar aka kwantar da tarzomar, duk da Malik ya musu bore kan babu mai hana sa auren zabin Malam.



Bayan sati uku kamar yadda iyayen suka tsara, aka sha bikin Malik da Sakeena, sai na Khausar da Ahmad, inda bayan an gama taro Ahmad ya wuce wajen aikinsa, tunda abin ne yazo akurarren lomaci, dole sai ya koma ya dan nemi hutu sai ya dawo, yasha amarcinsa.



Malik kam, kamar wani kumurci haka ya koma musu agidan, sati daya da yin bikin ya ishi Mahmah da rashin mutuncin da yake shukawa kowa agidan, tattara su tayi tace ya tafi wajen neman kudinsa, shi da maatarsa, su karata acan.

Abin nema fa wai ya samu, matar direba ta haifi mota, tunda Mahama ta mai maganar tafiyarsa yake cikin walwala, domin Allah kadai yasan irin rashin mutuncin daya tanadarwa Sakeenan acan, ko banza anan ganin idon Abbah da Mahma ya hanasa yin wani abun, cikin kwana biyar kuwa suka gama kintsawa suka wuce abroad.



Bayan tafiyarsu da kwana uku Ahmad ya dawo, nan suka bude nasu salon shafin soyayyar daya kusan haukata Laura, domin saboda irin haka yaki tarewa a gidansa yace nan yake son zama kusa da iyayensa.

_afuwa, wllh har yanzu ban gama warwarewa ba ne, mu hadu gobe inshaAllah_.

  



  *RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



    *FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*



–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         

            *œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.



_16_

  Wannan abu da Ahmad yayai ya batawa Mairoji rai, domin gani take ai shima yana sonta, to dan me zai auri wata bayan gata, hakan yasa taki dawowa garin Dutse, domin karfi da yaji take jin kishin Khausar, gefe guda kuma tanajin tausayin Malik, dan ita kadai tasan waya aura, adan zaman da tayi dasu, ta fuskanci inda ita kanta babar Sakeenan ta dosa, mace ce ba mai tsoron Allah ba, indai bukatarta zata biya , burinta zai cika ba tada damuwa da duk abin da zai faru, kyma tana iya karar da komai nata don samun farin cikin yaranta.



   Abangaren Laura kam, sosai Hajiya take tsumata da abubuwa, domin a irin hudubar data mata tace ko kanta ne ta bawa Ahmad din, indai hakan zai janyo ra'ayinsa kanta, Mamah na kula da duk take takensu, sai dai bata daga hankaliba, dom8n Allah ta rike, kuma tasan zai dubi yaranta ya kare mata su aduk inda suke.



______

    Malik&Sakeena

    ______



Ranar da suka sauka aSpain tayi zaton Malik zai kaita iri wajen shakatawan nan da wuraren ban sha'awa, amman sai taga ba inda suka je, sai shi ne ma ya dan fita bai dade ba kuma ya dawo, shi ma kuma tun daga ranar bata kuma sanyashi a idonta ba sai da akayi kusan kwana biyar, sannan ne ta gansa ya shigo da kayan  kanana, yana tsane jikinsa da wani dan shawel, da alama ya dan motsa jiki ne.



   Da dare yayi taci uban kwalliya da wata rigar barci, ta nufi dakinsa yana fitowa daga wanka kenan ita kuma tana shiga, kallonta ya tsaya yi yana jin wata sabuwar tsanarta na shigar mai, ita ko kadan fa bata burgesa, yayi yayi ya sata aransa ko yaya ne amman ya kasa.



   Takowa tayi har gabansa, cike da kirsa ta dora hannunta akan kirjinsa tana kashe masa ido, murmushi yai mata bawai dan ta burge sa ba, ah ah , sai don yana son yau ya kurewa iskancinta, cikin nasa salon mai tafiya da ita ya rungumo ta jikinsa, sannan sunka dangana da gadon dake tsakiyar dakin.



Tun tana jinta duniyar sama, sai ga ta ta fara neman dauki, hakuri take basa tana kuka da iya karfinta amman ko gizau baiyi ba, haushin ta da tsanarta sune suke kuma samun mazauni azuciyarsa, bai taba zina ba bai san yanda mace take ba, amman ayau ya tabbatar ya hadu da macen da ta watsar da kanta atiti, tunawa dayai da Maryam dinsa tuni wata kuzari ta kuma kwasarsa, yanajin bai kai ya sauka akanta ba haka, ya kamata ya nuna mata a maza ma akwai namiji.



So yake ya kawar mata da duk wata banzar tunani dantake yi akan maza, mazan ma ai suna suka tara, to shi kam yana cikin mazan da ba a isa a raina iyawar su ba, sai daya tabbatar ya sauke mata duk wani motsi dake kanta sannan ya sarara ya barta yana kuma jin tsanarta.

Bayan ya fito daga bandaki ne, ya kalle ta sai sauke ajiyar zuciya take, kallon banza ya mata ya dauke kai yana karasawa jikin wadrop dinsa,

"Ki tashi ki wuce kichin, abun ci nake so mai dan nauyi, yunwa nake ji, nazo nayi aikin da babu abun daya karamin sai yasar min dan abin dan ci akai, maza ki tashi karki batan lokaci".



Kallonsa take da mamaki sannan ta kalli agogo sha daya da arba'in na dare, tana shirin mai magana ya juwo yana watsa mata kallon da yasa ta yunkurawa ba shiri tana ciza baki.

Fita tayi tana dafa bango dan j8n kafafunta take kamar ba'a jikinta suke ba, da harara ya bita yana banka mata tsaki, sarai ta ji sa, sai dai ba tada yanda zatayi burinta kawai ya gama shigowa hannunta, alokacin ko kallon Mairoji ba zata yarda ya sakeyi ba balle yai tunanin dawo da ita cikin rayuwarsa.



Tuwon semo tayi, dan taga akwai garin, sai miyar alayyahu da tamai, a ido kam miyar gwanin ban sha'awa, dan tasha mai ga kuma daukar kamshi da take, cikin mintuna talatin da wani abun ta gama komai, ta kawo mai har dakinsa, yana kallon miyar yawunsa ya tsinke domin kuwa da gaske yunwar yake ji, abinc8n ya janyo yana taba tuwon ya biyo hannunsa, alamun bai dahu ba, sai bai ji komai ba dan ko iya miyar ma ta isa ya c8 ya sha ruwa.

Yana kai miyar bakinsa yai dan jim, sannan ahankali ya maida ta bakinsa cikin dan bowl din data ajiye mai dan wanke hannu, tashi yai ya je har dakinta ya samu ta fito wanka kenan, hannunta ya kama, har zuwa nasa dakin ya zaunar da ita yace " cinye shi tas, ko digo bana son gani".



Kai ta girgiza tace"wllh Yaya dear akoshe nake, kaci kawai".

"Wasa nake dake kenan?maza cinye sa kafin na tattakaki anan".

Jikin ta na rawa ta dibi abincin takai bakinta, ita kanta sai ta kasa hadiye wa, domin kamar tayi barin maggi ne aciki, dan yayi yawa sosai, haka tarugun da tasa kamar sai tsaga mata baki, tashi tayi tana kallonsa, tace " dan ....".

Bai saurare taba ya nuna mata kayan yace"yi waje dasu, wawiya kawai, ashe ba iya kanki ne baki killace ba, hatta abinci ma baki san yanda zaki sarrafashi ba".



Simisimi kuwan ta debi kayan ta fita tana gunguni, da kansa ya shiga kicin din ya samarwa kansa abunda zai sawa cikinsa, sai yanzu yqke jin takaicin sallamar kukunsa, aganinsa ai mace zai kawo gidan ba shida matsala da abinci.



Irin wannan rayuwar ita take wakana agidan Malik, domin yanzu da kansa zai shiga madafa ya dafa abinda yake so iya cikinsa, ita kuma idan taga dama ta hada kwamacalarta taci, bai dame sa ba, kuma tun daga qannan lokacin bai kuma neman ta ba, domin ko kadan baya marmarinta, zabin Mqlam ce aransa, akanta kuma yake son ya fara jin yanda dandanon mace yake, kusan watansu biyu amman babu wata ko yar shakuwa data fara shiga tsakaninsu, ko yaushe daga tsawa sai hantara, idan ya mata hakan ita kuma mai makon yar kirsa da shagwaba sai dai ta wuce tana gunguni, ko kuma idan rashin kunyar na kusa haka zasu haukata gidan da cacar baki yana fada tana maidawa, sai idan ya gaji yai kanta dan makewa, ita kuma ta gudu dan ta san lafiyar jikinta.







+++++



"Oga ka fita harkata dan Allah ka barni na auri wanda nake so, indai dan ta 'yar ka ne ka dauki kayanka, amman dan Allah ka barni na shaki iskar yanci".



Bai kalle taba , bai kuma kula ta ba, sai ma surutunsu da suke yi da Simrah don yarinyar tayi wani mahaukacin sabo da shi, tashi tayi zata fice daga falon yace ,

" kina sa kafarki awaje, za ki ji sanarwar daurin auren mu kuwa dake, ki dawo ki zauna har sanda zan sallame ki".



Zaman tayi kuwa tana sakin kuka, domin da irin wannan damar yake juyata son ransa, gashi kuma babu wanda ya isa yace mai bai yi dai dai ba, wanda ma yake dan jin maganarsa Malam Saje, to shi kuma tuni ya koma Dutse, dan haka yake mulkar kowa agidan yanda yaso, barin ma Mairoji taji labari.



+++



"Laura, kar ki sauka kasa na fada miki Ya Ahmad da matarsa.ne fa afalon, karki je kiyi abinda za'a ji kunya dan Allah, kuma fa wannan shigar taki bai kamata ki fita da ita ba".



Ko sauraren Ummie ba tayi ba ta fito ta nufi downstair.





Kallon bakinta da take cuna mai yayi yana murmushi, akan wai ya hana ta robar yaji data dauko akicin bayan tasa an mata wainar fulawa, ganin yana kallonta yasa ta kuma cuna bakin tana son fara mai shagwabar da ko yaushe take narkar dashi, bata ankara ba sai jin saukar bakinsa tayi cikin nata, ido ta zaro tana son tunasar dashi abangaren Mamah fa suke ba bangaransu ba, shi kuma yaki bata damar hakan, domin da gayya yai, yaga sakkowar Laura kuma yasan zuwa zatayi ta zauna musu kamar yadda ta saba ta sasu agaba, shi yasa yai hakan.



Sai daya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, ita sai lokacin ta kuka da Laura din datayi suman tsaye, kunya taji ta kama ta amman sai ta share kawai ta dauki farantin wainar ta fice tana jifan Ahmad din da wani kallo daya sashi tashi ya bita yana sakin murmuahin zan kama ki ne.



Tabata da Ummie tayi shiya dawo da ita hankalinta, murmushi Ummie tayi tace " na fada miki ai karki sakko, duk kawaicin masoyannan yau kin kai su makura sun nuna miki abinda idonki keson gani, sai kije ki sauya shiga ai, wanda kikayi domin sa bai san kina yi ba, dan iska ne ke wahal da mai kayan kara".



Tsaki Lauran ta saki ta wuce dakinsa kamar ta tashi sama, iata gani take kamar da hadin bakin Ummie a wannan wulakancin da ake mata, daki ta shiga ta fashe da kuka mai cin rai, tare da alwashin sai ta kori Khausar daga gidan ita ta maye gurbinta.



*RUGAR SAJE*



By Nusaiba Ayuba Suleiman



Wattpad@nusysa

IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.



*FITTATU 18=ØÚÜ 2 0 2 1=Ø¥Ü*





–&

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO=ØÚÜ*

```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo



*œ&þ{{H.Q.W.A=ØÚÜ}}
'þ*



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE.



_Deducated to my sweet Mamah=Ø
Þ_.

_mashaAllah Laureta, na tayaki murnar gama Zanen Kaddarata, Allah ya bada ladar fadakarwa_



_17_

_bayan wata shida_

Awannan lokacin zuwan Malik daya, shi ma kuma da rigima aka rabu dan yaje Maid akan lallai abasa Mairoji ya taho da ita, amman dake Saddiqu ya gama murda kambunsa sai kowa yace mai ah ah, haka badan yaso ba ya

Please Login or Register in order to submit comment