You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng  🍎JUYIN MULKI🍎


By📖🖊️
YUSRAH MUSA ABUBAKAR DUTSE JIGAWA STATE.

Bismillahir Rahmanur Rahim.
In the name of Allah the must benefit and the must merciful Allah the must high dose not sleep Allah is pure he accept only what is pure we love our Nabi no one but him no success with out him he's the first and the last he have no limit👍 ya Rasulullah SAW🌹.

WRITER 👇
📗1_ YARIMA ABDUL-MALEEK
📕2_ D'AN MILLIONAIRE
📙3_ SAFREEYYAH
📘4_ ME KAMAR SARKI
📔5_ MINISTER ASHRAF
📗6_ ROYALTY
📕7_ ZUCIYAR ALIYU CE
And now
📝8_ JUYIN MULKI
Later
📃9_ MU'AZZAM
And 10_ MATASHIN YARIMA.

Allahumma salli wa sallim ala sayyidina Muhammadun Sayyidil Mursalina.

✍️Fri Jun 26/2026.

#Astonished
#Ulceration
#Fantastic
#Embellish
#Vixen

📖✍️YMA WRITER.

♦SUDDENLY♦
....................... PAGE 01
Ya na tsaye a jikin window misalin 'karfe shida da rabi na safe ya na kallon harabar gidansu da kuma yadda ya ke cike da masu tsaro tunane-tunane ne fal a cikin ransa kyakkyawa ne sosai fari sol a shekara bai fi twenty eight to twenty nine years ba, ta bayansa ya ji an ce.

"Good morning Sir".

Ba tare da ya juyo ba kuma bai daina kallon waje ba can kasa cikin muryar shi me tsada ya furta.
"What is it"?

Kamar ba abun da ya ke damun shi yai maganar har lokacin bai motsa ba. Cikin shakka wanda ke tsaye da papers a hannunsa ya fara magana "sorry Sir before we find.............
Sai kuma ya kasa 'karasa abin da ya ke son fad'a ganin lokaci guda yadda uban gidan nasa ya juyo ya na kallonsa amma fuskarsa babu alamar d'igon murmushi kamar koda yaushe idan da sabo kuma sun saba ganinsa a haka ba yau farau ba.

"What do you mean"?.

Ya sake jefa masa tambaya ya na jiran amsa sunkuyar da kai jami'in yai dan bai san ya yanayin da zai kasance ba bayan ya san da maganar shiru ne sosai ya ratsa gurin har sai da ya sake tambayarsa sannan ya ce "ka yi ha'kuri ranka ya dad'e mahaifinka ya dakatar da komai tun jiya misalin sha biyu na dare tsoro ne ya hana na fad'a maka kuma ya hana a shigo da duk kayan da ka bu'kata" jin abun da ya ce ya sa ya 'kara d'agowa ya zuba masa ido iya susucewa ya yi jin abun da ya ce amma tsabar miskilanci ya na tsaye ko kad'an bai motsa ba kuma bai yi magana ba.

"Yalla6ai kuma ya 6ata wad'annan takardun ma" ya fad'a ya na 'karasawa ya ajiye masa akan wani table na glass tare da yin shiru ya na jiran amsar da uban gidan na sa zai ce, a hankali ya baro jikin window d'in ya zo ya zauna tare da mi'ka hannu ya d'auki papern ya ga tabbas Daddyn sa ne tun da ga sa hannunsa nan aje papern yai tare da mi'kewa ya nufi bedroom.

"Ka shirya min fita zuwa office d'in Daddy yanzun nan kafin na fito".

"Ok Sir".

Ya fad'a ya juya ya fita. Shaf-shaf cikin mintuna kad'an ya shirya burinsa ya ganshi ga shi ga Daddy ji yake kamar yai fuffuke ya je su had'u ko wayarsa bai tsaya d'auka ba duk da ya na ji ana kiransa gabadaya hankalinsa yai gaba fita yai ganin Momy ba ta parlour ya saka ya 'karasa ficewa a falon suna ganinsa duk su ka nutsu saboda ganin yanayinsa da sauri wanda ke tsaye jikin motar ya bud'e masa 'kofa ya shiga su ka fita daga gidan.

Lokacin da ya je ya samu Daddy ya na da ayyuka sosai har ya saka tsaro cewa yau ba zai ga kowa ba amma sakamakon ganin wannan d'in da ya zo nemansa d'ansa ne ya sa cikin girmamawa wanda ke tsaye a 'kofar ya bud'e masa 'kofa ya na cewa.

"Good morning Sir".

"Morning" ya fad'a ya na shiga office d'in Daddy da cikakkiyar sallama a bakinsa d'agowa Daddy yai ya na kallonsa ganin yadda ya ke a hargitse ya sa ya saki 6oyayyan murmushi ya na mayar da kansa ga kallon takardar da ke gabansa 'karasowa Irfan yai ya zauna.

"Daddy why you..........

D'aga masa hannu Daddy yai "stop my Son" ya fad'a ba tare da ya sake d'agowa ba sai da ya d'au lokaci sannan ya daina abun da ya ke ya d'ago ya na kallonsa.

"Uhum Mr. Affan Sulaiman Affan me ke tafe da kai"?.

Aje masa papers d'in yai ya na girgiza kai ya ce "Daddy why do you do this to me ko na yi wani laifi ne ban sani ba komai fa akan 'ka'ida na ke yi"? Jinjina kai Daddy yai.

"Lallai ma Irfan ko gaisuwa babu daga zuwa sai tambaya"?.

"I'm sorry Dad forgive me".
Ya had'e hannunsa alamar neman afuwa da kai Daddy ya amsa masa sannan ya ci gaba "ina jinka me ya faru"? Ya sake tambaya kamar bai ga akan abin da ya ke magana akai ba.
Sake nuna masa papers d'in Irfan yai ya na cewa "please Dad kar ka min haka da alama na aikata kuskure ne"? Kai Daddy ya girgiza.

"A'a ko d'aya kawai dai na yi maka hakan ne saboda na ga iya adadin yadda ka damu da aikinka".

"Amma Daddy 6ata papers d'in nan zai ja min asarar miliyoyi fa"? Ya fad'a da serious face.

"I know".

Kawai shi ne abin da Daddyn ya ce ya na kallon Irfan wanda ya ci gaba da cewa "sannan duka abubuwan da na saka aka yi order su zuwa Nigeria bai sa6a doka ba kaya ne na 'karuwa wanda zai amfanar da al'umma".

"I know"
Daddy ya sake fad'a.

Dafe kai Irfan yai "please Dad dan Allah ka gyara min takardun nan idan ba ka gyara ba ina da gagarumar asarar da ba za ta lissafu ba hakan zai sanya min damuwa sosai na san ba za ka so abun da zai 6ata min rai ba"? A karo na uku Daddy ya ce "I know that but I wanted to test you" tsuke fuska Irfan yai.

"Ta wannan hanyar kuma Dad"?.

"Yes ba kafi d'aukar business d'in ka da muhimmanci akan aure ba na gwada ka ne ta wannan hanyar domin na maka wata ishara sannan na nuna maka a aikace kuma ka ji abun da nake ji idan na ce maka kai aure ka ba ni amsa da "you are not ready" kuma "still you are not interested" d'an rufe ido Irfan yai cikin son kwantarwa da Daddyn hankali ya ce.

"Zan yi Dad ka 'kara min lokaci har yanzu ban ji a jikina matar da zan aura ta na kusa da ni ba".

Da mamaki Daddy ya d'an zaro ido waje ya na kallonsa ya ce "bayan Humairah Samhat Ashfat Zuhra".

"Ban da wad'annan Dad".

"Duk ba su yi maka ba"?.
Ya jinjina kai alamar comfirm.

"Ok na fahimta amma momyn ka kwanan baya ta kawo maka photon wata yarinya 'yar 'kaninta meye ma sunanta, Batula ko? Shin ita ma ba ku daidaita ba"?.

"Ban ta'ba zuwa in da ta ke ba saboda ba tai min ba ni kuma ba na kula abun da ban damu da shi ba.

"Na ji duk wad'annan an bar su tunda ba su yi maka ba amma kuma Faridah fa"? Da alama tambaya Irfan ya kalli Daddy tare da d'an d'ora yatsansa akan goshi ya na tunani ganin haka ya sa Daddy cewa.

"Ba ka ganeta ba? Faridah na ke nufi wacce ta dawo daga karatu kwanan nan 'yar gidan abokina Alhaji Sa'id".

Tuni Irfan ya had'e rai domin yanzun kam ya tuna ta tabbas last week idan bai manta ba ita ce ya gani a falon gidansu wai ta zo gaishe da Momy ne, tuna hakan da yai kamar wanda aka sokawa mashi ko wu'ka haka yai wata iriyar zabura wanda ya saka Daddy kallonsa ya na d'auke gira wato ya fahimci ya gano ta.

"Ina sauraronka ita fa"? Sosai Irfan ke girgiza kai ko tsoron ya masa ciwo ba ya yi, ya ce "a duk 'yan matan da naci karo da su ba wacce na ji bata kwanta min a rai ba kamar ita wannan yarinyar da ka ke magana akai Daddy".

"Really"?.

Daddy ya fad'a da tsananin mamaki ya na kuma sake 'karewa Irfan d'in kallo dan ya tantance maganar da yai har zuciyarsa ne ko a'a ya fad'a ne just, sai ya riske babban ya'kini akan cewa da gaske har ransa abin da ya furta haka ya ke kuma ba canji sai ya samu daidai da zuciyarsa wacce ya ji ta kwanta masa sannan ya kasance shi ne da kansa ya ganta ya ke sonta ba tallarta aka kawo masa b......................

"Uhm uhm fa Irfan ina jiye maka tsoron kar ka je ko aljana ce ta aureka"? Ya ji Daddy ya fad'a wanda ya saka ya saki 'karamin murmushi ya na cewa.

"Aljana ba ta aureni ba Dad ina ji a jikina wacce zan aura ba yanzu zan had'u da ita ba".

Rasa gane ainihin in da ya dosa da maganarsa Daddy yai kawai sai ya rabu da shi da wancan zancen ya d'auki wani dabam.
"Yauwa kuma Irfan dama ina so na sameka akan wata magana me ya sa ka za6i zuwa wancan 'kauyen ka zuba kud'in ka masu matu'kar yawa ka na da tabbacin ba ha'inci a gurin"?

"K'warai Dad in sha Allah haka na ke fata wad'ancan kayan ma da ka saka aka tare can za'a kai acan za'ai amfani da su injinan sarrafa abubuwa ne daga nan zan saka a d'ebi 'kwararrun ma'aikata wad'anda za su tsaya akan aikin har akai ga yin nasara" Irfan na rufe baki Daddy yai masa alamar jinjina da hannu sannan ya mi'ke ya na zagayowa in da Irfan d'in ya ke wanda shi ma already ya mi'ke rungumeshi Daddy yai ya na shafa gashin kansa cikin so ya ce.

"Allah ya albarkaci rayuwar billionaire d'ana Irfan" ya fad'a ya na sake rungumeshi murmushi Irfan yai domin ya san fushin Daddyn na sa kamar d'igon ruwa ne kafin a farga har ya bushe.

Daga office d'in Daddy bayan ya fito an bud'e masa mota ya shiga gida ya koma a lokacin ya samu Momy ita kad'ai a dining table ta na breakfast da rolled stuffed moi moi zama yai a kujerar kusa da ita cikin whisper ya ce.

"Good morning Mah".
Kamar ba ya so wani ya ji shi d'an murmushi ya saka tai ta na d'aga kai "morning Irfan ina ka je yau tun d'azu bayan fitarka sai kiran wayarka na ke ka'ki d'agawa har na gaji na ha'kura"?.

"Na je office d'in old man ne"

"Gurin Alhaji kuma me ka yo"? Ta tambaya kamar ba ta san da maganar ba bayan ita ce ta baiwa Daddy shawarar ya aikatawa Irfan d'in ko zai nutsu...

"Daddy ya saka an tare min kayan da na yo order su kuma ya kar6e takardun ya 6ata shi ne na je na bashi ha'kuri".

"Kuma ya ha'kura ne"?

"Eh ai ba zan iya barin Daddy ya huta ba idan ba gani nai kayan sun iso gareni ba" ya na rufe baki Momy ta ce "Shi ke nan ka kama kanka tun da na ji haka zan fad'awa Alhaji kaima ba za mu sake barinka ka huta ba saika nuna mana surukar mu a kwana kusa".

Gajeren murmushi ta saka yai kamar zai yi magana sai kuma ya fasa.
"Me ka ke son cewa ka fasa"?.

"Nothing".

"K'arya ne Irfan ban yarda ba nafa sanka farin sani nice mahaifiyarka duk wanda zai fad'i wani abu game da kai a baya na ya ke".

"Ina Mimih"? Ya tambaye ta domin kawar da wancan maganar kai ta girgiza ita ma ta na barin zancen kamar yadda ya bu'kata ta ce "ta je school".

"Ok Salim fa"?.

"Shi ya na part d'insa bai fito ya yi breakfast d'in ba ko lafiya maybe bai tashi daga barci bane".

"Har yanzu ace ya na barci sai kace wanda ya kwana ido biyu wannan yaron ya manta da koni waye amma zan saita shi zai dawo hanya" ya fad'a ya na mi'kewa ya shiga part d'insa iya wayarsa ya d'auko sai agogonsa da ya d'aura ya sake fitowa zai fita ya ce.

"Ki fad'a masa idan ya tashi kar ya kuskura ya fita ko'ina da shi za'ai wannan tafiyar zan fita akan haka ne ma" kai Momy ta jinjina "ok Irfan Allah ya tsare sai ka dawo ka kula".

"Thanks you Mom" ya fad'a ya na bud'e 'kofa ya fita........................

............📖🖊️YMA DUTSE JIGAWA

✍️Yusrah Musa Abubakar
Till we meet na gode.

[4:58pm Thu, Jul 2/26] 📖✍️ YMA

🍎JUYIN MULKI🍎


Story and writing
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨.

WhatsApp no:
+234 816 098 3083.


2_Allahumma salli wa sallim ala sayyidina Muhammadun Sayyidil Mujahidana.

Page two na ki 6ter Naja'at Musa Abubakar ina alfahari da 'yar uwata ta gari👍🌹.

1_TO MASU KARATU GA WATA TAMBAYA A CIKIN WAD'ANNAN 'YAN MATAN DA NA LISSAFO KU NA TUNANIN AKWAI YARINYAR LITTAFIN🤔?.
1___👉 BATUL
2___👉 ASHFAT
3___👉 SAMHAT
4___👉 ZUHRA
5___👉 FARIDAH
6___👉 HUMAIRAH
2_IDAN AKWAI TA WACE CE😁?.


❤️LOVESTICK❤️
...................... PAGE 02
Zaune wata matashiyar budurwa ta ke a cikin wani falo wanda ya sha manyan kujeru da kayan alatu wayarta na hannunta ta zubawa secreen d'in ido ko 'kyaftawa ba tai. Ta d'auki lokaci mai tsawo a haka daga baya ta sauke ajiyar zuciya tare yin murmushi sannan ta sakarwa wayar kiss ta na 'kara d'agota ta kalla. Ikon Allah ba komai bane a fuskar wayarta face photon Irfan ya na zaune akan wata irin kujera ya d'ora 'kafa d'aya kan d'aya da alama ba a gida ya yi ba maybe cikin tafiye-tafiyen da ya ke zuwa 'kasashe da ya je wata 'kasar acan ya yi.

"I love you Irfan, kaine mafarkina please don't leave me down" tai maganar cikin fargaba da tsoron rasa shi kamar yadda ta ke fata ba ta 'kauna ace wani abu ya rabasu ba ta jin ko duniya ne su ka taru akan ta rabu da Irfan za ta barshi ta amince da 6atawa da kowa idan shi zai yi shiri ta ita ta shirya d'aukar kowacce irin kasada ko bala'in da ya tunkarota ba tare da jin ko d'ar ba muddin Irfan ya na tare da ita tofa ba ta da wata sauran matsala kuma........

"Faridah".
Wata mata da suke kama tai kiran sunanta da alama ita ce mahaifiyarta.

Ko kad'an ba ta amsa ba saboda totally hankalinta ba ya jikinta tayi nisa tunanin masoyinta ya gama cika mata 'kwa'kwalwa..............

"Faridahhh!!!".
Ta sake kiranta da 'karfi.

Wanda ya saka ta juyo a firgice ta na kallon matar da ke kiranta aje wayar tai a gefe kamar ba abun da ta ke da ita ta ce "na'am Mami kirana ki ke"? Kallon tuhuma Mamin tai mata domin tun da taga ta nutsu haka shakka babu tunanin Irfan ta ke ita ta san da wannan tun daga ranar da mahaifinta yai mata maganar za'a had'asu aure ta daina samu cikakkiyar nutsu da kyakkyawan barci.

"Mami ki na magana da ni ne"? Ta sake fad'a ganin har lokacin ba ta daina yi mata canjajjan kallon da ta ke mata ba, d'an sake fuska tai ta na 'ko'karin saisaita nutsuwarta ta ce.

"Ki yi ha'kuri Mami laifin zuciyata ne zuwa yanzu ya kamata ku yi min uzuri domin lokuta da dama na kan samu kaina a cikin gur6ataccen yanayi mai wuyar fassarawa ina tsoron jinyar da ba magani ta kamani akan gayen nan" ta na rufe baki Mami ta ce.

"Irfan ko"?.

Ta tambaya ta na 'kureta da kallo "eh k'warai Mami tun da na dawo Daddy yai min tayin aurensa yace sun zauna da mahaifinsa sun yi magana tun ban ganshi ba na je har gidansu na kai mu su ziyarar bazata na had'u da shi, shi ke nan tun daga wannan rana na daina samun kwanciyar hankali rayuwata ta canza idan ina zaune sai na ji a cikin kunnena kamar muryarsa ya na kirana idan barci na ke bani da aiki sai mafarkinsa ina tsoro kar sonsa ya zama ajalina Mami dan Allah ki taimaka min".

Jin bayanin da ta koro ya sa Mami kallonta sosai ta na nazarin maganarta kafin ta samu guri a kusa da ita ta zauna ta na dafe kafad'arta ta ce "Faridah idan ki na so ki kai ga nasara to tabbas ki rage yawan tunani a kansa sannan ki dawo cikin hayyacinki ki rage yawan wad'annan abubuwan akan Irfan ki tuna har yau bai ta'ba tako 'kafarsa gidan nan ya zo saboda ku samu fahimtar juna ba kawai magana ce tsakanin Alhaji da mahaifinsa kin ga kuwa lalube ki ke yi a cikin duhu ki san da wannan" canza yanayin fuskarta Faridah tai ta na cewa.

"Na sani Mami abin ne ya gama isata koda ace aiki ya hana shi zuwa in da nake a cikin ranaku biyar ai akwai ranar weekend me ya ke da ba zai zo mu samu zama ba"?.

"Wannan ne kuma ban sani ba ya na gidansu ina nan ta ya zan ba ki amsa"?.

"To yanzu ya zan yi Mami dole ina bu'katar shawara"?.

"Farko idan ki na so ki samu kusanci da shi ki ri'ka 'kokari ki na kiransa a waya kullum kuna gaisawa ki na d'an jansa da zance daga haka idan ya fara sake miki ki na jan hankalinsa da magana me dad'i kina masa shagwa6a ki ri'ka nuna masa a bayyane kin damu da shi idan ki kaga ya fara shiga tarkonki sai ki share shi ki fara ja masa aji ki daina kiransa a waya ki yi blocking d'insa na d'an wani lokaci Ina tabbatar miki da 'kafafunsa zai zo gidan nan saboda da ke".

"Allah ko Mami"? Ta fad'a cikin shauki da nishad'i kawai daga wannan bayanan gani take kamar har ta yi komai ta gama ya shiga hannunta sai yadda ta ga dama za tai da shi.

"Amma tsaya Mami ranar da naje gidansu gaishe da Momynsa ko arzikin kallo ban samu a gurinsa ba balle na samu fuskar da zan gaida shi fa, kuma har na taho tun da ya tashi ya bar falon ban sake ganinsa ba" Faridah tai maganar fuskarta ya nuna alamar damuwa sosai, ta'be baki Mami tai ta na kallon yadda fad'in hakan ya saka ta, ta canza yanayi ta ce "haba faridah kar ki bani kunya man sai kace ba mace ba shifa namiji duk in da kika ja shi zai bi ki sannan kome ki kace masa zai yarda kwata-kwata yaushe ki ka dawo Nigeria ba ki fi wata d'aya ba sannan maganar auren naku shima bai fi sati biyu ba amma gabadaya kibi ki takurawa kanki ki hana kanki sukuni akansa, haba faridah, to tsaya na ba ki shawara yadda za ki yi a sau'ka'ke da fari ki daina saka damuwa da yawan tunani a kansa kin san dalili"? Faridah ta girgiza kai.

"Shi ya kasance ba soyayya ce a gabansa kamar yadda ke ki ka d'auka,, bai san komai ba sai business duk wata magana da za ki ji daga bakinsa bai da dangankata da soyayya sai dai kasuwanci duk wani motsinsa haka ne, to ni anan shawarar da zan baki ki tsaya cak da takurawa kanki ki fahimci waye za ki aura mutum ne wanda komai sai kin koya masa domin zuciyarsa business ta sani ba so ba.

"Na fahimci abin da ki ke nufi Mami zan yi 'ko'kari naga na daina yawan saka tunanin shi a 'kwa'kwalwata sannan zan daina kiransa sai dai idan shi a ra'ayinsa ya ji yana son magana da ni dole na nuna masa ni mace ce mai daraja da kima koda ni na fara cewa ina sonsa balle wannan magana ce tsakanin mahaifanmu" Mami ta jinjina kai "yauwa gara da ki ka gane tun da wuri sai ki hattara da taka tsantsan domin tun ranar da Aisha ta ji labarin Irfan a bakin Alhaji ta d'aga hankalinta ba ki ga kwanan nan daga ita har 'yar tata basa cikin walwala ba"?.

"K'warai Mami na gani dama akan haka ne"?.

"Tabbas suna ba'kin ciki da hakan sai dai mu saka ido sosai kar mu je bamu sani ba su yi masa magani rana d'aya ya juye kan Mujidat" a zabure Faridah ta ce "tabdijan kan bala'i ai wallahi ba su isa ba ko ya aureta sai ya saketa".

"Balle ma ba zan bari haka ta kasance ba ke dai ki yi shiru da bakinki kar ma su fito su ji muna maganar" Mami ta fad'a ta na kallon 'kofar part d'in Aisha ganin ba motsin kowa ya sa ta sauke numfashi tare da mi'kewa ta na kallon Faridah ta ce.
"Bari na dawo".
Ta nufi wata 'kofa ta bud'e ta shiga yayin da ta bar Faridah kanta cike da tunanin maganar da su kai yanzun da kuma yadda za ta fara shawo kan wannan zankad'ed'an saurayin⚛️😁.
📖🖊️YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Till we meet na gode❤️.

🕌🕋🕌
It's Friday don't forget to recite suratul al-khaf. May Allah accept our du'as🤲 amin.
🤲Yaa Allah make us among those who never miss Salah. Amin.

✍️Fri—Jun—10—26
©Yusrah ≈≈ Musa ≈≈ Abubakar.


🍎JUYIN MULKI🍎

Story and written
⚜️Y⚜️M⚜️A⚜️
⚛️YUSRAH MUSA ABUBAKAR⚛️

3_Allahumma salli wa sallim ala sayyidina Muhammadun Sayyidil Shahidinah.

______________Y⚜️
_____________________M⚜️
_______________________________A⚜️

😔WREAK😔
............... PAGE 03
🏕️K'AUYE🏕️
K'aramin gari ne sosai amma ya shahara da manoma da 'yan kasuwa masu sana'o'i dabam-dabam akwai tattalin arziki da ma'adanai a yankin wanda hakan ya saka 'yan 'kauyen su ke cikin alkhairi a koda yaushe.
Malam Ubaliyo ya na d'aya daga cikin manyan 'yan kasuwar garin kuma masu fad'a aji sannan wakilin Mai gari ya kasance mutum mai ha'kuri da kuma juriya sannan mai zama a cikin ahlinsa ya tattauna da su ya ji matsalarsu, kwatsam wani babban iftila'i ya faru a gidansa sakamakon aurar macen da ta kasance annoba kuma ba'kar ashana 'kona gari wacce ta kawo masa sauyi na damuwa da d'aci a cikin gidansa.

Kamar koda yaushe yadda ta saba yau ma ta na dur'kushe a gaban Umma ta na matsa mata 'kafafunta da su ka kumbura su ka tashi, a hankali cikin nutsuwa kyakkyawar budurwa ce fara wacce magana ba ta dameta ba sannan kuma ta na girmama na gaba da ita. Lokaci zuwa lokaci ta na d'agowa ta kalli fuskar mahaifiyarta cikin tausayawa, daga waje ta ji ana 'kwala mata kira da babbar murya kamar muryar gardi.

"Zarah Zarah ki na isa 'yar isasshiya me dod'dd'iyar 'kwa'kwalwa da ki ka saba kullum sai an jiraki kin fito ko saina shigo da ta6arya na fasa miki kai"? Wata 'katuwar mata mai jiki tai maganar ta na tsaye a 'kofar d'akin. A hankali Zarah ta saki 'kafar Umma ta mi'ke tare da d'aukar hijab d'inta ta fita.

"Uban me ki ke ina ta magana tun d'azu kin yi kunnen uwar shegu da ni"? Hamah ta fad'a ta na zuba mata wata uwar harara, cikin nutsuwa murya a sanyaye ta ce "ki yi ha'kuri ina matsawa Umma 'kafarta ne sakamakon yau ta fi kullum kumbura" tai maganar a damuwance ta6e baki Hamah tai.

"To kuma Ina ruwana da kumburinta wannan matsalar ku ce damuwata ki fito ki yi min aiki na kawai bai shafeni ba idan kin gama sai ki koma ki ci gaba da matsa mata jikin kamar kin samu gyad'a wuce ga tsintsiya can ki d'auka ki min shara ai kin san aikinki ne sai tsabar rainin hankali".
Zarah ba ta sake yun'kurin yin magana ba kawai ta wuce ta d'auki tsintsiya tun daga farkon gidan har 'karshensa sai data share shi tas ta d'ebe sharar sannan ta had'a kwanuka ta wanke gabadaya ta ware nasu sannan ta ware na Hamah ta je ta kai mata sakamakon kar ta sake ce mata wani abu ta d'ebo ice ta had'a mata wutar da take dafa abincin saidawa kamar yadda ta saba kullum.

Komawa da'ki tai ta samu Umma tai shiru ta na kallon guri d'aya.

"Umma bari na kammala mata aikinta saina dafa miki na ki ruwan tun da lokaci bai 'kure ba zuwa jimawa Aunty Hannatu ta fad'a min za ta zo gidan" ta sake dubaki" kai kawai Umma ta d'aga muryarta na rawa kamar mai shirin yin kuka ta ce "zo ki d'agani ina son fita waje" 'karasawa tai ta d'agota cike da tausayawa ta ri'keta a hankali da bin bango ta samu ta kawota waje ta koma ta d'auko tabarma ta shimfid'a mata ta saka mata fulo a jikin bangon ginin sannan ta taimaka mata ta zauna ta jingina bayanta da fulon kawai ta ci gaba da kallon yadda 'yar tata take faman bauta ta na wahala ita kad'ai bayan akwai Aliyah.

"Ke Zarah me ki ka tsaya kallo har yanzu baki wanke wancan kayan miyar kin kaiwa Talatu ta markad'a min ba"? Hamah da ke zaune tai maganar ta na harararta a gajiye Zarah ta ce "so na ke idan na gama dafa

Please Login or Register in order to submit comment