You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma'kalewa ki ke wula'kanta ni a kansa Irfan" ya fad'a ya na nuna mata agogon da ke d'aure a hannunshi ya ci gaba.

"Agogo ne wanda aka yi shi da zallar lu'ulu'u da zinare malama ke da me ki ke tunani akaina duk zuwa gurinki da nake dan na jarraba ki ne 'karshe maimakon ki cinye sai ki ka fad'i tirrrr da halin mace me son zuciya irinki" ya fad'a ya na tofar da yawu kamar Faridah ta had'iyi zuciya ta mutu a gurin haka ta kame ta na bin sa da ido tabbas bai yi 'karya ba da baya zuwa da kyawawan kaya kamar haka sannan wannan tsaleliyar motar ita ma bata taba gininsa da ita ba sai yau gashi yanzu ya fi d'aukar wanka.......

Ta na cikin tunani ta ji muryar Mujidat ta 'karaso gurin ta na cewa "Yaya Jafar 'karaso ciki ka yi ha'kuri na barka kana jirana na shiga wanka ne" sai kuma ta kalli Faridah kamar za tai dariya ta danne ta ce.

"Aunty Faridah gurin aiki za ki tafi, a dawo lafiya Allah ya tsare".

Murmushi Jafar yai ya na kallonta yaga yadda tai mugun had'e rai ya ce "Aunty na a dawo lafiya" ya juyar da kallonsa kan Mujidat ya ci gaba "wife to be mu je ko"? Kai ta d'aga suna juyawa tare su ka shiga ta 'kofar 6angaren masaukin ba'ki.
Su ka bar Faridah tsaye idonta ya cika fal da hawayen ba'kin ciki da kishi ta tabbata saboda ita Jafar yai haka dan ya 'kona mata rai ne yayo wasan baya ya dawo ya ke son Mujidat. Fasa fita tai ta juya ta koma ciki gurin Mami wacce ganin yadda Faridan ta dawo ta na kuka ya sa ta tareta hankali tashe ta ce.

"Faridah lafiya kukan me ki ke"?.

"Mami yau an wula'kanta miki ni an tozarta miki ni anyi min cin fuskar da ba'a ta'ba yi min ba tun da nake a duniya" a rud'e Mami ya ce.

"A ina kenan wannan fitar ta ki har kinje 'kauyen kuma a hanya"?.

"Ban je ba a harabar gida na had'u da Jafar ya zo gurin wancan tsohuwar munafikar Mujidat d'in shi ne ya tsareni ya ri'ka zagina ya na fad'a min ba'ka'ken maganganu har da ce min bagidajiya bulkuma" a masife Mami ta ce.

"Gyatumarsa ce bagidajiya bulkuma amma ba ke ba wato dan kar uwarsa dan ya samu lasisi a gurin Alhaji shine har ya ke ganin ya na da 'yancin da zai ri'ka ya6a miki ba'kar magana, tabd'ijan wallahi bai isa ba uwar kuturu ma tai kad'an balle ta makaho ba dai yana gidan nan ba bari naje na kashewa d'an iska warning dan inba tsabar idona ya gani ba shi ke nan ya samu hanyar wula'kanta ki".

"Dan kawai na ce bana sonsa Mami shi ne ya tareni ya ri'ka zagina" Faridah ta fad'a ta na sake sharar hawayen da su ka 'ki daina fitowa ran Mami a 6ace ta ce "eh ba kya sonsa d'in nima na fad'a bakya sonsa sai ya d'au mataki ko kuma ya saita bakin bindiga ya harbe mu dan mun ce bama sonsa idan kuma ana so dole ya fad'a min dan babansa zo mu je" ta fad'a ta na mi'kewa tai gaba Faridah ta bi bayanta Aisha ta na zaune a falo ba ta san me yake faruwa ba sai kawai ganinsu tai sun tsaya mata a ka Mami da ke nunata da yatsa ta ce.

"Aisha Aisha Aisha sau nawa na kira sunanki? Da mamaki Aisha ta kalleta sannan ta kalli Faridah da ke kuka ta ce "lafiya me ya faru"? Ran Mami a 6ace ta ce.
"Ki samu Jafar tun da surukin ki ne kija masa kunne kadaran kadahan kada me gani ya taka makaho hawainiyar Mujidat ta kiyayi ramar Faridah dan ta samu anyi mata alfarma Jafar ya dawo gurinta ya na sonta shine har suka had'e kai take neman wula'kanta Faridah dad'in abun ma ba ganinta yai yace ya na sonta ba tallarta akai masa" murmushi Aisha tai jin abun da tace sai yanzu ta harbo jirgin wato Faridah taga Jafar ya zo gurin Mujidat shi ne ta rud'e harda kuka kaita jinjina ta na kallon Mami ta ce.

"Tallar ma arziki ne tun da ya taya kuma ko yanzu alhamdulillah Jafar ya na son Mujidat amma kefa, son zuciya da son abun duniya ya rufe miki ido kinga yaro da kud'i kin haukace so kike dole sai ya auri 'yarki sai cusata ki ke tana masa shishshigi inace kema Irfan d'in ba cewa yai ya na sonta ba tallarta akai masa kuma har yau bai taya ba balle ya siya kinga kuwa kayi tallar a taya ma wani abu ne ni da kike ganina ko yanzu zan yi alfahari nai tutiya na bugi 'kirji Mujidat ta samu mai sonta da gaskiya wanda ba son zuciya ai bari ki ji zulaihat tun da ki ka hau motar kwad'ayi ku jira kuga ba inda za ta sauke ku bayan ta kai ku tashar wula'kanci sai ta had'a muku da guzurin kuka da nadama in dai ba ku dawo kan hanyar gaskiya ba".

"Ba za a dawo d'in ba nace ba za'a dawo d'in ba in Allah ya yarda ke da 'yarki kune za ku hau motar kwad'ayi ku sauka a tashar wula'kanci sannan a yi muku korar kare ku dawo gida a tsiyace Ina fata kin gane hausar da nai miki? Idan kuma ba ki gane ba bari nayi miki bayani ina nufin sai dai Mujidat tai aure a sakota ta dawo gida ta na kukan nadama da ba'kin ciki amma ba Faridah ba ita ta fi 'karfin ku daga ke har 'yar ta ki da kuma munafikin surukin na ki duk baku isheni kallo ba"

"Au haba, a hakan bamu isheki kallo ba amma har ki ka damu da mu in dai gaskiya ne maganar da ki ka fad'a da Faridan ta zo ta na kuka ta fad'a miki sai ki shiru ki share lamarin da kin yi haka shine zan san kin cika kuma bamu isheki kallon ba" kamar Mami za ta fad'a kan Aisha ta rufeta da duka ta ce.

"Ban share lamarin ba na zo na tareki da maganar idan kin isa ki fad'a min wani abu wanda bai gamshe ni ba kiga aiki da cikawa".

Ta'be baki Aisha tai ta na cewa
"Sai kiyi tayi kuma ke ce a wahala idan kinga dama ki kwana a gurin kina ihu nasan ta haushi ta biyo kuma kune ku kai sake da damarku yanzu hagu ta ri'ke ku sai ku san yadda za kuyi ku zame ko ku sake fad'awa Alhaji ya sake yi muku cikiyar wani Mai kud'in ku gwada sa'arku inai muku fatan alkhairi sannan ina jajanta muku kun tashi ba tsuntsu ba tarko ta'ki auren Jafar ta wula'kanta shi saboda Irfan shi kuma Irfan d'in ya 'ki aurenta saboda ba tai masa ba na tabbata zuwa wannan aikin da ta fara yi ya fahimci kanta ba onga da Maggi Star shi ya sa ya'ki aurenta" ta na rufe baki Mami ta saki ihu cikin takaici ta ce.

"Wayyo Allah na shiga uku tun da nake a duniya ba'a ta'ba cin mutuncina irin yau ba Aisha saina kashe ki".

"Ke ba ki isa ki kasheni ba sai kwana na ya 'kare kuma ko Alhaji ne ya dawo kafin ki 'kulla min sharri zan je nai masa bayani saina tabbatar da ba ki nasara ba sai dai ki tari gaba daga yau zan d'aura d'amarar ya'ki da ke a gidan nan sai kin gane Allah da girma ya ke kuma za ki gani ni dake d'an halak ka fasa dacan ma da kike ganin Ina miki shiru kina min abun da ranki ya ke so ba wai bani da fad'a bane ina binki a huce ne mu zauna lafiya amma tun da ki ka ta6oni za ki ga 'karshen rashin mutunci" jin abun da tace ya sa Mami ta mayar da kallonta kan Faridah ta na cewa.

"Faridah je ki tafi gurin aikinki na fahimci wannan matar annamimiya ce so take ta hanaki ci gaba shi ya sa ta d'auke min hankali da maganganunta na banza da wofi ga shi har lokaci ya fita ki barni da ita zan yi maganinta a gidan nan je ki" ta fad'a ta na turata fita Faridah tai ta na sake waigowa ta kalli 'kofar ba'kin da su Jafar su ka shiga kafin ta wuce ta shiga mota ta bar gidan cike da tunanuka kala-kala...............
📖✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
Me tambarin yma writer jikar Abubakar Muhammad, I love Dumus Town.

🤔Think before you do
Be good be helpful people will look you.

TYPING 📲Thu, Jul 30/26 8:08 AM
✍️ Written Yusrah Musa Abubakar.

❤️❤️❤️❤️❤️JUYIN❤️
❤️MULKI ❤️❤️❤️❤️❤️

By☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
WhatsApp no: 234 816 098 3083


19_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Zakirinah.
_____________________________________
______________PAGE 19______________
A wunin ranar sakamakon Irfan ba ya nan yasa Akil ya samu dama ya sake ya fad'awa Faridah komai duk wani sirrin gidan sai da ya fad'a mata ta yi matu'kar farin ciki kuma ta samu abin da za ta tari Irfan da shi ko baya so saita tambayeshi ta ji me zai ce idan ya na son yarinyar ne ma ta tabbata data fad'a masa halin da su ke ciki a gidansu zai ha'kura.

Kwana biyu da dawowar Faridah daga 'kauyen Irfan shi ma ya dawo a ranar Akil ya kirata ya fad'a mata washe gari tun asuba ta shirya ko tsayawa tai breakfast ba tai ba kawai burinta ta je su had'u tayi sa'a kuwa lokacin da taje ya na free ba ya aikin komai shi ya sa ta samu damar da ta zauna su yi magana.

"Irfan da ka'ki fad'a min wace wannan yarinyar mai sona ya fad'a min sunanta Fatima Zarah sunan mahaifinta Malam Ubaliyo d'an kasuwa ne sannan mahaifiyata sunanta Binta ta kasance nakasashshiya mara lafiya sannan kuma 'yar talakawa ce tun da tai primary da secondary School ba ta sake yunkurin yin wata makarantar ba sai talla kamar hauka, Irfan me ye abin sha'awa a irin wannan yarinyar har ka ke kulata kaifa d'an birni ne mai kud'i mai ilimi d'an gayu ka na da aji a tunanina ko a 'yar aiki ba za ka d'auki wannan yarinyar ba balle har ka ke kulata ka ke iya cin wani abinci da ya fito daga hannunta? Gani tai yai mata banza ta ci gaba.

"Please Irfan dan Allah ka daina kula yarinyar nan kar zuciyata ta buga ka san yadda na damu a kanka amma sai kai ta share ni kana 'kin d'aukar kirana ka fad'a min me ye laifina na gyara"? A wannan karon ma shiru yai kamar ba zai amsa mata ba daga baya ya ce.

"Kin ji nace kina da wata matsala ne"?.

Numfashi ta sauke ta na cewa.
"Haka na ke zato gaskiya Irfan ina bu'katar ganin sauyi a fuskarka" kai ya jinjina ya na d'agowa ya kalleta ya ce "idan ki na bu'katar ki ga sauyi a fuskata ki rabu da ni Faridah shine kawai za ki ga sauyi a fuskata ki fad'a komai ki ke so kud'i mota gida ko wani abu dabam zan baki amma dan Allah ki rabu da ni ki fita daga rayuwata ba na bu'katar ki a tare da ni" jin abun da ya ce yasa a rud'e ta ce.

"Na shiga uku kai ne ka ke fad'ar haka Irfan Irfan Irfan" ta maimaita har sau uku.

"Haka sunana ya ke idan kuma Affan d'in ma zaki ce duk d'aya fad'i abun da ki ke bu'kata daga gareni zan yi miki ko mene ne".

Kamar za tai kuka ta ce.
"Ni aurenka na ke bu'kata kawai".

Kai ya girgiza mata.
"Ban da wannan ki fad'a min abun da ki ke so daga kan million d'aya zuwa iya adadin da ki ke bu'kata zan ba ki amma ki bar maganar aure tsakani na da ke har abada".

"Saboda me"? Ta fad'a ta na zaro ido waje cike da tashin hankali.

"Saboda ba zan iya auren ki ba".

Ya na rufe baki ta d'ora hannu aka ta na cewa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Irfan ka daina fad'ar haka kar kasa zuciyata ta buga na fad'i a gurin nan na mutu za kai azumi sittin fa so ka ke a d'auki gawata ne"?.

Kai ya jinjina ba tare da ya kalleta ba ya ce "abun da ya ke cikin zuciyata na fad'a miki sai dai ki yi ha'kuri".

"Gaskiya ba zan iya ba ni kai nake so kuma kai zan aura" ta fad'a hawaye ya na zubo mata ta na kuma jiran ta ji me zaice mata.

"Ko da ace ni bana sonki zaki iya aurena"?.

"K'warai ni ba sai kana sona ba kawai damuwata ka aureni".

"Ba zan iya auren macen da bana so ba kin gane ina so ki fahimce ni dan Allah Faridah get of my way kafin ki sa na d'auki matakin da ban shirya ba ki fita daga rayuwata ba na son kusanci na da ke ko kad'an da kin san da haka da baki zo in da nake ba please Faridah get of my way dan Allah" ya had'e hannunsa ya na kuma yi mata alama da jajjada maganar yai akan ta yarda har zuciyarsa haka ne tsabar yadda Faridah ta shiga rud'anin da bata ta'ba shiga ba a cikin rayuwarta rasa in da za ta saka kanta tai sai kallonsa da ta ke ido waje bakinta ya yi nauyin da ya kasa bud'uwa balle ya fad'i wata magana har ba ta san lokacin da ya tashi ya ba ta gurin ba sai ta dad'e sosai sannan ta ankara ya tashi ita ma mi'kewa tai jiki a mace ta fita daga cikin ma'aikatar gabadaya.

Sakamakon ta san komai dangane da gidansu Zarah ta na fita kanta tsaye gidan ta tafi a ranar kuwa tai sa'a Umma ba ta nan Hannatu da Zarah sun je kaita asibiti ganin likita sai yamma za su dawo Malam Ubaliyo kuma ya na kasuwa iya Hamah ce da Aliyah a gidan. Faridah ta shiga tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum".

Hamah dake zaune ta amsa
"Wa alaikum salam wa ye"?.

"Ni ce".
Faridah ta fad'a ta na 'karasa shigowa.
Zaro ido waje Hamah tai tare da dafe 'kirji ta na ja baya cikin tsoro ta ce "na shiga uku mutum ko aljan da alama nayi gamo yau kodai anguwar dana fita ne na taka aljanu ban sani ba domin tun da na ke ban ta'ba ganin irinki a zahiri ba sai a waya idan Aliyah ta turo mana video yau kuma sai ga ki a gaske da kyakkyawan kaya"? Hamah ta fad'a ta na sake 'kare mata kallo, kai Faridah ta d'aga ta na cewa.

"Eh aini daga birni nake in dai za ki shiga cikin birane duk irina za ki gani mu haka mu ke nazo ne ina son za mu yi magana".

"Da ni"? Hamah ta nuna kanta cike da tsananin mamaki "eh da ke amma akwai bu'katar mu zauna domin magana ce doguwa" jin abun da tace ya sa jiki na rawa Hamah ta ce "Aliyah d'auko tabarma ki mi'ko min".

Fitowa Aliyah tai da tabarma a hannunta ta shimfid'a ta na sake 'karewa Faridah kallo daga sama har 'kasa, Hamah da ke tsaye sa'ko'ko ta ce.

"To bismillah 'karaso ga gurin zama" 'karasa shiga barandar Faridah tai ta na cire takalminta ta zauna akan tabarma kamar gidansu harda cire mayafi da d'an kwali kitson 'karin da tai har baya Hamah ta jawo kujera ta zauna ta na cewa.
"To ina jinki Allah ya sa dai lafiya"?.

"Eh lafiya dama muna shigowa 'kauyuka ne muna neman 'yan mata idan mun samu muna d'aukar su mu kai birni za su ri'ka aiki a manyan gurare ana biyansu albashi mai tsoka sannan da gurin kwanan su ma a killace ya ke da masu tsaronsu ba wani abu da zai same su kuma idan ba su da lafiya akwai likitoci mata da za su duba su komai akwai a gurin babu ce kawai babu ku na da yaran da ku ke dasu wanda za su yi ana samun kud'i sosai".

Kai Hamah ta jinjina ta na murmushi ta ce "k'warai akwai maraba da wannan tsarin naki na ji dad'i sosai tabbas wannan ba'kuwar zuwanki akwai alheri akwai yarinya guda d'aya da zan baki amma yanzu ba ta nan ta je raka uwarta asibiti sai dai idan ta dawo sunanta Zarah" da sauri Faridah ta kalleta sakamakon jin tarkonta ya kama mata tsuntsuwar da take so ajiyar zuciya ta sauke "ok ba damuwa hakan ya yi idan na gama zaga garin na samu wasu 'yan matan zan dawo gareku domin ribarku idan an tafi da su bayan albashin da za'a ri'ka biyansu har ma makaranta za'a saka su idan ku kai sa'a kafin su dawo sun zama wani abu su iya turanci su iya rubutu sannan su waye su zama 'yan gayu kamar ni" zaro ido Hamah da Aliyah su kai jin abun da ta ce da sauri Hamah ta soma girgiza kai .

"A'a a'a hakan ba zai yuwu ba, ba za'a tafi da Zarah ba sai dai a barta a d'auki Aliyah" ita ma Faridah da sauri ta girgiza mata kai ganin za ta 6ata mata shiri ta ce "a'a da Zarah za'a tafi ba Aliya ba ita na ke bu'kata idan na sake dawowa sai na d'auka har Aliyan" a susuce Hamah ta ce "to ai Zaran da ki ke bu'kata ba ta san komai ba sai talle da'ki'kiya ce".

"Da'ki'kiya"?
Faridah ta fad'a da mamaki kai Hamah ta d'aga ta na cewa.

"K'warai da'ki'kiya ma ta ajin 'karshe ko sunanta yanzu ki ka saita ta da bakin bindiga ba za ta iya rubutawa ba, ba abun da ta sani duk karatun da tai banza ya ke".

"Ok na fahimta ba komai dama irinta mu ke nema da'ki'kai saboda a wayar da su a koya musu abubuwa na zamani" ta na fad'in haka ta mi'ke ganin ran Hamah a 6ace sakamakon kar ta hana tafiya da Zarah saita bud'e jakarta ta d'auko dubu goma ta mi'ka mata.

"Ga shi ki ri'ke wannan kafin na sake dawowa sai kin ganni".

Hamah ta washe fuska cike da son zuciya ta kar6a da sauri ta d'aga 'kasan tabarmar ta 6oye ta na cewa "to ba damuwa sai kin dawo mun gode ki gaida gida".
Kallon Aliyah tai bayan fitar Faridah ta ce.
"Oh ni 'yasu kinga muna zaune arziki ya zo mana har gida" ta'be baki Aliyah tai ta na few "ni kam ban yi farin ciki da zuwan wannan yarinyar ba saboda bada ni za'a tafi ba" jin abun da tace ya sa Hamah sake kallonta ta na cewa.

"Eh ba za'a tafi da ke ba kin manta acan d'in ma tallar abinci za ta yi kuma kema shi ki ke yi anan"?.

"Ai ba irin wannan bane, ke fa irin Wanda mutum ya na zaune akan kujera masu aikin za su kawo su ajiye masa ne fa bakya gani a wayata idan na turo kallo ne"? Kai Hamah ta d'aga "eh ina gani man amma duk da haka ki bari dai mu ga abun da zai faru kar muyi gaggawa nifa ban yarda da ita ba ki ka sani ko 'yar shan jini ce idan ta tafi da mutum ba ta dawowa da shi haka kawai ki bita shi ke nan taje ta siyar dake mu shiga uku ki bari ta tafi da iya Zaran in soyata zata je tayi ma su 'karata" Hamah ta na gama fad'in haka ta mi'ke ta na shiga da'ki..........................
YUSRAH MUSA YMA WRITER.

Dedicated to my daughter
Fatima Zarah Elham.
Little Zaran Aunty.

🍎JUYIN MULKI🍎
☘️By☘️
Yusrah Musa Abubakar
☘️Jigawa state☘️
☘️☘️☘️
☘️

20_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Akilinah.

_________________ PAGE 20
_____________________________________
Bayan wucewar wani lokacin kamar kwanaki sha biyar Faridah zuwanta gidan d'aya su ka sake tattaunawa da Hamah ta fad'a mata gobe shi ne ranar daya kamata ta zo ta d'auki Zarah d'in sakamakon da asuba Ubaliyo ya ke tafi kasuwa kuma ba ta so ya sani, shi ya sa Faridah ta ce yau a nan garin za ta kwana a masaukin ma'aikatar Irfan gobe da safe za ta zo ta d'auki Zarah a motarta su tafi.
Kamar yadda ta fad'a washe gari da wuri ta baro can ko tsayawa ta had'u da Irfan ba ta yarda ta yi ba saboda muhimmancin abin da za tai lokacin da ta zo a tsaye ta samu Hamah a 'kofar d'akin su Zarah ganinta ya sa Hamah ta ce.

"Har kin shigo kenan yanzu ai nima na zo inai mata magana ko uwar me su ke a d'akin oho" d'an ta'be baki Faridah tai ta na juyawa za ta fita ta ce "ku yi sauri domin idan mun je a yau za ta fara aiki watakil nan da sati ku fara ganin albashi" ta na fad'in haka tai waje gud'a Hamah ta saki ta na rawa ita kad'ai.

Zarah kam ta na dur'kushe a gaban Umma idonta ya na fitar da zafafan hawaye saboda ba ta da ikon 'kin zuwa ba ta isa tai musu ba da tasan Hamah za tai mata haka ba za ta kwana a gidan ba gara ta gudu gidan Hannatu ta kwana a hankali ta d'ago ta na kallon Umma wacce ta shiga wani mawuyacin hali muryarta na rawa ta ce "ki yi ha'kuri Umma na sani wannan ma wata jarrabawar ce ta tunkaro ni amma zan yi 'ko'karin cinyewa sannan duk in da naje ki na raina ba zan ta'ba mantawa da ke ba kuma ba zan watsar da tarbiyyar da ku ka ba ni ba zan ri'ke mutuncina zan y..................

Kasa ci gaba da maganar tai tsabar yadda muryarta ta ke ma'kalewa Umma kam har lokacin tamkar gunki haka ta ke a san'kame gurin d'aya ko motsi ba tai tsabar yadda zuciyarta ta buga da jin wannan masifa da Hamah ta ke son jefata a ciki.....................

"Wai uban me ki ke yi a d'akin nan ne da baza ki fito ku tafi ba ta na waje ta na jiranki" su ka ji muryar Hamah daga waje tai maganar har da dukan murfin 'kofar d'akin share hawaye Zarah tai a hankali ta mi'ke jiki ba 'kwari ta fito ta na cewa "ina sallama da Umma ne" harararta Hamah tai ta na cewa.

"Oho ki na sallama da gawa dai haka za ki ce sai nafi fahimtarki sosai dan wannan tsumman gyatumar ta ki bata isa na ba ta ruwa ba balle abinci balle kuma uwa uba matsa mata jiki kamar wata gyada sai dai ta mutu a wancan gurin da ki ka bar ta a zaune har ki je ki dawo ba zata samu gatan wanka ba kuma ba zan bari wancar fitsararriyar yayar ta ki ta sani ba wuce mu je munafika" Zarah ba ta sake cewa komai ba duk da hankalinta ya tashi da jin abun da Haman ta ce akan Umma amma tai ha'kuri ta danne zuciyarta ta san komai yai farko tabbas wata rana zai yi 'karshe.

Su na fita Faridah da ke tsaye ta kallesu ta ta'be baki duk basu isheta kallo ba, ba don burinta ta ke son cikawa me zai had'ata da 'kauyawa irin wad'annan har ta zo in da suke tsaki ta ja mai 'karfi ranta a 6ace haka kawai take jin kamar ta fad'awa Hamah ta fasa ma abun da take son yi sai kuma wata zuciyar ta ba ta shawarar, karta fasa domin idan ba tai nisa da Zarah daga kusa da Irfan ba tabbas wata rana sai soyayya ta shiga tsakaninsu kuma ba zai ta'ba yarda ya tsaya ya fahimceta ba sai ya daina ganin Zarah.

Kai ta jinjina ta na bud'e mata bayan mota (but) ta nai mata wani matsiyacin kallo a 'kyamace ta ce "shiga nan dan ba ki da ajin da za ki shigar min cikin mota balle ki zauna akan kujera" tsaye Zarah tai ta na kallonta ta'ki koda motsi cikin tsawa Hamah ta ce "ba za ki shiga ba saina fito na hankad'aki ciki matsiyaciya ki na mana ba'kin cikin kud'in da

Please Login or Register in order to submit comment