You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abincin saina kai".

"Au yanzun zaman jiranki zanyi ta yi sai kin gama dafa shinkafa tsabar ba'kin hali sannan ki kai markad'e idan kuma aka zo siya da yawun bakin ki zan siyar musu kin d'auka kin gyara kin kai min an markad'o ko saina tashi a kanki" tun kafin Zarah tai wani motsi Umma ta ce.

"Wai Hamah wacce irin rayuwa ce wannan ki ri'ka jin tsoron Allah sanin kanki ne aikin da Zarah ta ke gidan nan ba 'yarki Aliyah ba ko ke ba za ki iya rabinsa ba amma koda yaushe a batai ba take a gurin ki"? Jin abun da tace ya sa Hamah tai mata wani kallo ta na cewa.

"Iyeee sabon salo kiran sallah da usur hawa risho da wandon leda ke yanzu Binta har kina da bakin magana a gidan nan? To bari ki ji ni nafi 'karfinki ba yadda zaki da ni nan gani nan bari kuma Zarah da ki ke magana a kanta ko ke mahaifiyarta ba ki isa ki nuna min iko a kanta domin komai na gidan nan nawa ne ni nake lokaci".

Girgiza kai Umma tai cikin takaici ta ce "ina tsorace miki ranar da duniya za ta juya miki baya ba za ki san kin yi kuskure sai lokaci ya 'kure miki ya kamata ki gyara" a masife Hamah ta ce "ba zan gyara ba in dai wannan abun ne yanzu na tsoma hannu kuma zama a gidan Malam Ubaliyo yanzu na fara ba ranar rabuwa ni da shi tip da taya mutu ka raba takalmin kaza idan ma kina tunanin zai sakeni ne to ki daina domin wallahi yanzu na saka d'ambar zama da shi bari na 'kare miki 'karshen magana sai nayi masa takaba gara tun wuri ki san da wannan idan kishi ne ma ya saka kika tsiri ciwon 'kafar 'karya gara ki ware domin ba ki da ikon da ki ka isa ki fidda ni a gidan nan".

"Shi ke nan Allah ya kyauta ni dai zuciya d'aya nake zaune da ke idan kina da wata manufa dabam a zuciyarki ma Allah yai min tsari" ture farantin gabanta Hamah tai ta na cewa "au a hakan dama da zuciya d'aya ki ke zaune da ni, to fad'a min ni da zuciya dubu nake zaune da ke? Bayan ke kike cuta ta ba dan Allah ya tona miki asiri ba kin gurgunce ai da yanzu kin fitar da ni a gidan nan, to aniyarki ta bi ki" ta fad'a daidai Zarah ta gama wanke kayan miyar ta saka hijab ranta a 6ace ta d'auka za ta fita.

"Ke zararriya akwai injin sadaka ne a garin nan wanda su ke ni'ka ba kud'i ko watan tsoronki ne ya kama za ki ka d'ebi 'kafa ki tafi haka"? Juyowa tai har lokacin ko tari ba tai ba ta kar6a ta fita ta d'an yi tafiya kad'an ta had'u da 'kawarta ita ma da bokiti 'karami a hannunta za ta gidan markad'en su ka tafi tare.

"Ke Zarah kin fita bayan gari kwanan nan kin ga wani sabon kyakkyawan gani da akai har da matakala (beni)" da alamar tambaya Zarah ta kalli Naja'atu ta na cewa "da yaushe ni dai naji ana shelar ana neman matasa na garin nan wai wani babban mai kud'i ya siya fili anan garin wajen gonar baban mu zai yi gini har anyi kenan".

"K'warai an kusa gamawa ma gaskiya ya yi kyau sosai ba ki gani ba kullum 'yan matan garin nan da samari sai sun je kallon gurin kin ga dai da dandali ake tafiya yanzu can ne ya zama dandali acan ake komai".

"Ai kuma fa ya siya fili da yawa domin harda na babanmu a gurin sannan ga filayen mai gari ina tunanin wannan gurin da ya gina ya kai kusan girman 'kauyen nan".

"Gaskiya dai kam, to amma abun tambayar waye daga ina zai zo ya akai ya san 'kauyen nan har ya zo ya d'ago mana da shi domin gaskiya ba 'karya wannan ginin ya d'ago da martabar garin nan sosai tun da har a rediyo na ji ana labarai ana kiran sunan garin sakamakon wannan ginin da akai" d'an murmushi Zarah tai daidai sun shiga gidan masu ni'kan ta ce.
"Allah ya sa alkhairi ne ya kawosu garin domin ni ina tsoron ba'ki kar mu je sai mun fara murna mun sakankance kawai su yi mana wani abun tashin hankalin ni dama da na kasance babba kuma mai fad'a aji a garin nan ba zan bari ko mutum d'aya ya siyar musu da filinsa ba amma wai harda wad'anda su ka siyar da gonaki".

"Uhm su kam wad'annan ko nawa aka basu sai dai mu tayasu da jaje domin wannan ba ci gaba bane" ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta na cewa "mu kan mu za'aiwa jaje ma domin babanmu babbar gonarsa ya saida haka kawai ya bud'e shago gashi nan tun ba'a je ko'ina ba sai mutane su d'auki bashi su hanashi kud'in jiyama da dare ina jinsa ya shigo ya na fad'a wai Umma Hamah ya na binta kud'i ita da Hajiya Laraba ya kai dubu hamsin sun hanashi".

"Allah dai ya kyauta kawai amma Allah na tuba Hamah da Hajiya Laraba aminan juna ne fa duk wanda ya basu bashi sai dai a lahira ai, ke Zarah ba ki tambayeni mutumin ki ba fa"? D'an had'e rai Zarah tai.
"Akan me zan tambaye ki salon kije ki jona ni da shi yaga kamar da gaske nima ina jin abun da ya ke ji d'in" zaro ido Naja'atu tai ta na kallonta da mamaki ta ce.

"Kai wai da gaske ki ke? Kenan me ne matsalarsa da har yanzu ki ke kokwanto a kansa kina kallo fa saboda ba ya so ki ri'ka wahala kina fitowa da bokitin awararki zai amshe gabadaya ya rabawa almajirai ya ba ki kud'in".

"To kuma na sakashi ne, idan ya barni ma da kasuwata wuya na fito yanzu zai 'kare ke nifa ba wata rud'ewa da Adamu zai sa ni nayi kawai ke dai mu bar maganar bari na tafi na baro aiki da yawa a gida kuma yau mu ke so mu mayar da Umma asibiti wajen ganin likita" ta fad'a ta na d'aukar markad'en ita ma Naja'atu ta dauka su ka fita daga gidan sakamakon anguwarsu d'aya ba nisa tsakaninsu ya sa suka tafi tare kamar yadda su ka zo suna tafe su na hira cikin nishad'i da jin dad'i har su ka rabu a in da suka had'u kowa ta shige gidansu.

Zarah ta na shiga ta tarar da Hannatu a zaune a kusa da Umma ta na sake d'an jajja mata 'kafar tata ajewa Hamah markad'en tai ta 'karaso ta na zama ta ce "ina kwana Aunty Hanne dama tun d'azu nake jiranki mu tafi kin ga yau kumburin har ya fi koda yaushe gabadaya hankalinta a tashe ya ke badan dama aiki na ke ba da yanzu naje na fad'a miki gara mu tafi da wuri".

"Yanzu ma bamu makara ba sauri ki yi wanka idan kuma ba sai kin yi ba sako hijab mu tafi" mi'kewa Zarah tai ta na cewa "a'a jirani yanzu zan yi wankan ba dad'ewa zan yi ba tun da ban san ranar dawowarmu ba" ta fad'a ta na shiga da'ki ta d'auko zanin wanka shaf-shaf tai sauri ta d'ebi ruwa ta yi ta shirya su ka taimakawa Umma su ka mi'kar da ita su ka fita Hamah da ke zaune ta na kallon duk abun da su ke ta raka bayansu da harara ta ce "shegu munafikai za ku dawo ku sameni ne duk ina daidai da zamaninku Allah ya sa 'kafar kar ta warke ta lalace ta yadda ba za ta moru ba sai dai a yanke daga lokacin da ta zama gurgunwa zan gani Hannen za ta bar auren ne ta dawo gida saboda ita ko kuma Zaran ce za ta ci gaba da zama a gidan shi ke nan ba za tai aure ba Allah ya sa karta samu mijin aure akan lokaci har sai nayi auren Aliyah ta haihu da shekara biyar sannan ita kuma ta gama lalacewa ta jibge a gida ba aure ko wannan Adamun sai nasan yadda nai na shiga na fita na rabasu tun kafin magana tai nisa, oh ni jikar mutum hud'u ina surutu wutar harta mutu ga icen d'anye ga kuma ko miyar ban d'ora ba ga yankan salad gaskiya yarinyar nan Hanne ta na cuta ta duk ranar da ta zo gidan nan ban isa da Zarah ba sai kace ita ta haifeta amma ba komai in dai na amsa sunana Hamah sai na yi maganinta idan kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a had'u" ta 'karasa maganar ta na mi'kewa da 'kyar sakamakon nauyin jikinta ta tafi gaban murhu za ta gyara ice ganin har lokacin ba alamar Aliyah ya sa tace "yarinyar nan sai ina taka mata burki zan ci ubanta ne tun daga aike tun sassafe ace har yanzu ba ta dawo ba, zan kama ta ne idan na zauneta ta ji nauyi na watakil ta daina wannan shegen yawon da ta ke.
Ta le'ka waje ba kowa cikin takaici ta dawo ta na cizon yatsa har haskowa ta ke ta ri'ke Aliyah ta na jibgarta saboda yadda ranta ya ke a 6ace so ta ke kawai ta samu abun da zata huce haushinta......✍️ YUSRAH MUSA.

⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️
We will meet again⚛️.
Thanks for your supports⚛️.

Ina mi'ko dubun gaisuwar ban girma gareku 'yan uwana Allah ya bar mana zumunci. Amin🤲.
YASNAF FAMILY.

🍎JUYIN MULKI🍎
By
Yusrah Musa Abubakar.
Yma writer.

Dedicated to YASNAF FAMILY.
❤️My sister's and brother's❤️.
Salim Musa Abubakar
Najat Musa Abubakar
Fatima Musa Abubakar
Aishat Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar.

4_Allahumma salli wa sallim ala sayyidina Muhammadun Sayyidil Khaifinah.

🌹OVERLOOK🌹
....................... PAGE 04
Da dare misalin 'karfe takwas da rabi zuwa tara lokacin Daddy ya dawo daga masallaci Momy ta had'a masa dinner d'insa ya yi suna zaune a falo ta kalleshi ta na cewa.

"Wai dan Allah Alhaji me ya sa ka rabu da Irfan cikin sau'ki ne"?.

Jin tambayar da tai masa ya sa shima ya kalleta na d'an lokaci kamar mai tunanin wani abu daga baya kuma ya ce "na 'kyaleshi ne saboda ya kasance har yanzu shi yaro ne ina masa uzuri ne sakamakon idan nace zan takura masa na matsa masa lamba dame zai ji? Gabadaya sai mun rasa kansa dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka ina me tabbatar miki idan na gigita Irfan to fa 'karshe saina fishi gigicewa domin ni zai saka a gaba ya takurawa ina d'an lalla6a 'kwa'kwalwata kar ya burkita min lissafi shi ya sa yana zuwa office d'ina na saka aka sakar masa kaya tun kafin abun ya kai ga saina kirawa kaina likita" tun da ya fara magana Momy ta ke jinjina kai ya na rufe baki ta saki dariyar da ta ke ri'kewa.

"Gaskiya ne Alhaji domin fad'in hakan ya tuna min last year da ya ri'ka gwara kansa a bango ya na hautsina kujerun falon nan akan d'an abun da bai kai ya kawo ba balle wannan da ya tabbatar asara zai yi 'kiri-'kiri".

"To kin gani in dai ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba ai dole na rabu da shi wuya ransa ya 6aci saina kowa ya 6aci tun da shi hargitsattsan mutum ne kamar a kansa aka fara kasuwanci" numfashi mai nauyi Momy ta sauke ta na cewa.

"Nikam dukiyarsa ai har tsoro ta ke ban ko yanzu ya ha'kura ya zauna guri d'aya ya daina komai zuwa nan da tsufansa kud'in da yake da shi ba zai 'kare ba kuma kullum sake shigo masa su ke bai da aiki da ya zauna sai lissafi sai kace maths teacher".

"Ai shi ya sa idan nai masa maganar aure ya ce a'a nake rabuwa da shi domin na tabbata lokaci ne idan mu ka saka ha'kuri wata rana muna zaune zai zo mana da maganar zai yi da kansa ba tare da an saka shi ko an tilasta masa ba har yanzu fa bai kai shekara talatin ba, kawai dai ganin bai rasa komai ba babu sauran wani abu da ya ke jira yasa na damu yai auren domin shi ya rage masa kawai zan zuba masa ido idan muna da rai nan da shekara bakwai lokacin ya cika shekara talatin da biyar komai kasuwancinsa a cikin wad'annan shekarun dole ya samu wacce ya ke jin zai aura dan ra'ayin kansa" da mamaki sosai Momy ta d'an zaro ido ta na cewa.

"Kenan Alhaji haka za mu zuba masa ido a duk wad'annan yaran ba'a sami wacce tai masa ba, ba wacce zai aura"? Ta 'kare maganar mamaki kamar zai she'keta ta na jinjina tsaurin ra'ayi irin na Irfan. Ji tai Daddy ya ce.

"Wad'anne yaran"?.

"Humairah Zuhra Ashfat Faridah Batula kowacce mun san mahaifanta mun san asalinta ba wani abu da yai saura, amma duk cikinsu ya rasa wacce zai ji yana so gaskiya in dai haka ne Allah ya shiryi Irfan lamarinsa da gyara ace dai 'yan mata biyar ya rasa ko guda d'aya wacce zai ji ta burgeshi Allah ya kyauta Irfan!! Irfan!!!"? Ta fad'a ta na sake tsinkewa da lamarin yaron na ta, murmushi Daddy yai jin yadda ta ke maimaitawa da alama dai ta matsu fa taga surukarta ne cikin tsokana ya ce.

"Fad'a min gaskiya".

"Gaskiyar me"?.

"Da alama kin matsu ki fara ganin jikanunki ne ko"? Had'e rai tai ta na cewa "a'a ni dai kawai so nake naga ya shigo layin mutane ne".

"Au yanzun kice a layin aljanu ya ke"? Dariya tai "a'a ba haka nake nufi ba kasan duk ilimin mutun da kamalarsa da kimarsa ba ya cika cikakken mutum sai ya na da matar aure ko"?.

"Eh haka ne".

"To ka gani wannan dalilin ya sa na damu ba komai ba, yanzun tsakani da Allah ba zai duba ya tantance yarinya d'aya a cikinsu yama tsaya ya gansu ne balle yaji yana son nasu"? Ta 'karasa maganar ta na kallon jikin bangon falon inda babban photon Irfan ya ke manne kaita girgiza kamar wanda shi ne da gaske a zahiri ya ke kallonta ta ce.

"Irfan Allah ya shirya min kai".

Sai kuma ta juya ta kalli Daddy wanda fuskarsa take fal da murmushi ta ce.
"Yanzu me ne abun yi"?.

"Eh to bazan ce komai akai ba domin nayi iya yina sauran na Irfan ne kinga kuwa akwai dogon lokaci sai dai idan muka saka ha'kuri kamar yau komai zai zo ya wuce wata rana zaki ga kamar ba'ai komai ba amma ni kam haka ya ce min ba wacce yaji tai masa a cikinsu" Momy tai 'kwafa a 'kufale ta ce.

"Gaskiya bai isa ba dole ya d'auki d'aya a cikinsu idan ya 'ki da kaina zan yi masa komai ya na zaune ba sanarwa sai dai ya ji ana gud'a kuma wallahi bai isa yai min musu ba dole ya zauna da ko ma wace ce" jin abun da tace ya sa Daddy kallonta da murmushi sosai akan fuskarsa ya ce.

"Ni dai ba ruwana idan ki ka 6allowa kan ki abun da zaki kasa barci nawa ido ne yayin da zai zo ya hargitsa gidan nan sai dai na koma gefe nasha kallo idan ta kama ma na d'auki waya na yi muku video" ya na rufe baki Momy ta fara dariya.

"Ba wani kasa barci hakan da zan yi shi ne daidai ba wai dan ya zama tuzuru bane a'a har yanzu yana sahun samari tun da yaushe ma yabar sahun 'kwailaye🤣 amma ka duba ka gani me yake nema a duniya wanda bai samu ba yanzu?.

"Babu".
Daddy ya bata amsa ya na fad'ad'a murmushinsa jin ta kira Irfan da 'kwailaye ya san maybe da yana gurin ta fad'a ta yanzu guguwa ta fara tashi wanda ya girma bai son a kirashi da yaro kuma ya ji ance masa bai dad'e da fita daga layin 'kwailaye ba,.

Ci gaba Momy tai da fad'in.

"To ka gani babun ma da ana ganinta na tabbata Irfan zai mallaka tun da bai rasa komai ba shi kansa a yanzu idan ka ritsa shi bani da tabbacin ya san adadin dukiyarsa iya wacce take hannun mutane ma balle kuma uwa uba wacce ta ke hannunsa ya ke juyata da kansa sannan ya na da girman jiki masha Allah Wanda bai san shi ba zai yi tunanin ya kai irin shekara talatin d'in nan.

"Kar ki damu ki kwantar da hankalinki ni zan sameshi a hankali zan lalla6a shi da magana me dad'i da nasiha in sha Allahu ko da ba wacce tai masa a cikin wad'ancan yaran zai nemo da kansa".

"To Allah ya sa, amma ka yi waya da shi a yau ne"?.

"A'a nayi magana dai da shi jiya misalin sha biyu da rabi lokacin kina barci ina tambayarsa yaushe zai dawo gida ya fad'a min daga can ma gaba zai yi so ya ke daya dawo ya le'ka 'kauyen da aka kai wad'ancan kayan su ma ya dubasu yaga ya abun ya ke tafiya duk da ya zuba wakilai amma gani ya kori ji" ajiyar zuciya Momy ta sauke ta na cewa "to ai nifa ba anan gizo ya ke sa'kar ba fad'in haka da kayi sai kuma naji wani tunani ya zo min dabam".

"Game da me kenan"?.

"Akan lamarin auren nasa man idan ma yayi fa shi ba zama yake guri d'aya ba yau yana nan gobe ya na can wani lokacin sai ya fi wata bai dawo gida ba shiyasa shi ma hankalinsa bai kan auren sannan ba kowa ce zata amince a ri'ka tafiya ana barinta tsawon lokaci ba".

"Wacce take sonsa za tai masa uzuri kuma za ta fahimce shi tasan dalilin da yasa ba ya zama guri d'ayan ai bayan haka ba wani abun damuwa bane zai iya tafiya da ita idan yaga zai ja lokaci kafin ya dawo kawai ke dai kiyi shiru matsayinki na mahaifiyarshi ko yi masa fatan alkhairi wannan shi ne".

"To ba komai Allah ya sa jinkirin shi ne mafi alkhairi fiye da yanzun tun da bamu san mene a gaban ba, watakila kaga in da bamu ta'ba tunani ba acan zai samu matar da za ta kwanta a ransa".

"Sosai anything can happened" Daddy ya fad'a ya na kallon secreen d'in wayarsa da ya kawo haske alamar message ga kuma miscalls har uku wanda kwata-kwata ma bai lura da su ba d'aukar wayar yai ya na dubawa sai kawai yai murmushi ya d'ago ya kalli Momy ya na cewa.

"Wannan yaron naki akwai wayo yana so yai mun ajiya cikin account d'ina idan ya tashi cirewa kuma ya had'a da nawa kamar wanda nasa su ke haihuwa ko ina zai kai kud'i oho" Daddy yai maganar ya na d'an girgiza kai tare da bin kiran da yaga Irfan d'in ya yi masa, duk da ya san bazai wuce maganar kud'in da ya turo masa ba ne amma ya na da kyau su yi wayar yaji ya lafiyarsa.

Dariya Momy da ke gefe tai ta na cewa "to albashinka ni kwanan baya da yai ajiyar millions hud'u da rabi cikin account d'ina daya tashi cirewa millions biyar ya cire ina zaune na ji alert kawai na duba naga shi ya cire kuma bayan ya shigo da nayi masa magana cewa yai wai ladan ajiya ya cira kaji fa, maimakon ace ya d'auki iya millions hud'un ya bar min rabin sai kawai ya had'a da nawan ya 'kwamushe wai ladan ajiya ya d'auka" jinjina kai Daddy yai.

"Eh ba matsala hakan ma daidai ne dakai da kaya duk mallakar wuya ne dashi da dukiyar nasa duk na ki ne" ya fad'a ya na d'aga kiran da Irfan yai masa su ka fara magana Momy ta na zaune ta na sauraron duk hirar da suke sai dai ta d'an ji mamaki sosai da ta ji yana cewa Daddy a halin yanzu ya na California tabdijan jiya fa yake fad'a mata bai samu ya huta ba maybe ya taho gida yau maimakon ta jishi a international airport amma sai taji shi a wata 'kasar kuma,.
"Ikon Allah sai kallo" kawai shi ne abin da ta fad'a ta na sake sauraron maganar da su ke da Daddyn na sa.
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Till we meet
Ana tare.

💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya ANNURI haske💡 le'ka gidan kowa ko da ma'kiya na kallonka ramin kura sai 'ya'yanta.
Gaskiya na yi kewarku sosai mutanen arziki please dan Allah ku raya mana group d'in nan mai albarka😔.
❤️🌹Ina son ku 'yan Annuri🌹❤️

Dedicated to.
My daughter's.
❤️ Fatima Zarah (Elham)
❤️Ramlat Leleh (Ikram)
❤️Habibah Kolii (Ikram)
❤️Bilkisu Koli (Tasleem).

Story and written.
✍️Yusrah Musa Abubakar.
YMA WRITER.
Jigawa state Dutse venture's.

📞Tel. +234 816 098 3083
WhatsApp number.

YUSUF 👑KING____SKEEBOY
Wannan page d'in naka ne d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka kai na dabam ne ina fatan Allah ya kareka a duk in da kake Allah ya dawo da kai Nigeria cikin aminci.
🎸🎶🎧🥁🎺🎻
SHATAN RAPPER REAGAN RB RAP DA KUMA HAUSA HIP HOP.
👍Gabadaya hip hop kaine gatanta
👊Skeeboy tababu ka ke shata
🌹 Malaminta
👍Oganta
❤️Mai gidanta
🍎Limaminta
⭐🌟 Super star.
YUSRAH ina mi'ko gaisuwa.

05_Allahumma salli wa sallim ala sayyidina Muhammadun Sayyidil Da'inah.


..................... PAGE 05
Lokaci ya d'an sake ja kwanaki sun shud'e abu kamar wasa sai da Irfan ya shafe tsawon wata guda da sati d'aya sannan ya samu damar zuwa gida shi ya sa daya dawo ya fi kwana goma bai fita ya je ko'ina ba Momy ce da kanta ta tsare shi a gida tace sai ya huta kar ya je 'kwa'kwalwarsa ta daina aiki hatta wayoyinsa saida ta kar6e Sim card d'in saboda ma kar a kirashi ya d'aga, sosai hakan ya takura shi domin bai saba zama guri d'aya ba sai dai ya tabbata gata tai masa domin koba komai a 'yan kwanakin da ta dakatar da duk wani harkokinsa ya samu cikakken barci sannan ya na zama ya huta ba tare da lissafin wani abu ba har wata sabuwar 'kiba yai ya dad'a zama fari sol yai ja ko'ina a dire masha Allah.

Faridah ta na bedroom a zauna tun safe tai kiran wayar Akil amma a kashe tai masa magana ta WhatsApp bai hau online bama balle ya duba so ta ke ta tambaye shi idan Irfan ya dawo gida domin rabon da ta kirashi a waya ya d'auka har ta manta yanzu kuma idan ta kira ma sai dai ta ji a rufe koda yaushe sosai hakan ke 6ata mata rai amma sakamakon tasan ita taga za ta iya d'auka ba ta fad'awa kowa halin da ta ke ciki.

Ganin zaman jira ba zai kaita ba ga shi yanzu ba samun wuni take a gida ba sai lokaci zuwa lokaci sakamakon aiki da Daddyn ta ya sama mata kuma ya gargad'eta ta mayar da hankalinta akai bai son shashanci sannan duk tsiyarta ta na tsoron mahaifin nata domin bai kasance mutum mai son wargi ba. Tuna hakan ya sa ta mi'ke tare da aje wayar ta shiga bathroom tai wanka ta fita ta gama shiri kenan ta na 'ko'karin d'auko takalmin da zata saka ta ji an kira wayarta da sauri ta juya gurin da ta ajeta haka nan ta tsinci kanta da fatan ina ma ace idan ta duba Irfan ne.

"JAFAR".

Shi ne sunan da ta gani akan secreen d'in wayar da manyan ba'ki wanda hakan ya canza mata yanayi tuni fuskarta ta canza daga yanayin damuwa zuwa tsantsan 6acin rai da takaici ko 'kara kallon wayar ba tai ba ta ja tsaki mai 'karfi ta mayarta ta ajiye ta d'auki takalmin da mayafi sannan ta saka wayar a jaka ta fita" ta je falo sabon kira ya sake shigowa ga shi ta hango Alhaji Sa'id da Mami a dinning gudun kar bata d'aga ba ta 'karasa gurin ya tambayeta da wa take waya sai ta juya da sauri ta koma bedroom ta d'auko wayar a wannan karon ba Jafar d'in data tsana bane Akil ne ya kirata humm ganin mai kiran ya sa a gaggauce ta bi bayansa ya na d'agawa ko jira ta bari taji me zai mata ba tai ba a 'kagare ta ce.

"Hello ina jinka Akil ya akai idan na kira Irfan bai tafiya ko har yanzu bai dawo Nigeria bane"? Daga can 6angaren

Please Login or Register in order to submit comment