You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayawa"? Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Zarah wacce ta tashi zaune tana goge jikinta ta ce.

"Ke fad'a min waye uban cikin ko a cikin wad'ancan ma'aikatan ya ke ya sunansa in an jima na tura Aliya ta kirashi ya zo muyi magana a sirri ba tare da kowa ya ji ba sannan yanzu ya biya kud'i a kai ki asibiti a duk bayan kwana biyu ya ri'ka kawo miki kifi da kaji ana dafa miki kina ci dan ki haifi yaron 6ul6ul da shi" Zarah ba ta iya magana ba numfashinta ya na fita da'kyar ta mi'ke ta fita waje ta zauna Hamah da ta biyota ta tsaya a kanta ta ce.

"Yau fa ba zan barki ba sai kin fad'a min wanda yai miki cikin nan ko dai shugaban gurin ne shi ya sa ki ka 'ki fad'a wannan me ba ki bashin 'kwan nan ne ko shine ya lallame ki fad'a min a hankali kar ma'koftan mu su jiyo kin san munafikai ne sai su je su yad'a a gari" jin da Zarah tai ta cika mata kunne da surutu ya sa ta mi'ke ta na nufar hanyar da'ki Hamah da ta bita da kallo ta ta6e baki.

"Ahaf munafika har da wani wucewa kina tafe sumi-sumi idan ma ba ki fad'a ba ai za ki haihu za mu gani idan yai kama da me baki bashin 'kwan za ki ci 'kwal ubanki a garin nan sai na kad'a muku gangar masifa".
Duk abun da take fad'a Umma ta na jinta tari da bai kamata ba batai ba sakamakon ta san 'yarta ba ciki ne da ita ba dan meye za ta biyeta mata azo ana jinsu a ma'kwabta gara ta rabu da ita kare baya haushi shi kad'ai sai ya samu abokin yi...........
BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR

Till we meet na gode.
Ayi ha'kuri idan an samu typing error matsalar keyboard ne.

☘️ JUYIN MULKI ☘️

Dedicated to
My daughter
Fatima Zarah Elham (little Zaran Aunty💃 Ililin Abba🤙).

25_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil D'ayyibinah.

........................... PAGE 25
Tun zazza6in da ya samu Zarah sai da takai kusan kwana goma ba ta le'ka ma'aikatar ba sannan ba ta je gidan Hannatu ba kullum sai dai Amar ya je ya kar6a tun Irfan ya na sharewa har wata rana ya tambayi Amar me ya sa ta daina zuwa anan ya fad'a masa ai bata da lafiya ne kamar zai ce suje ya rakashi gidan sai kuma ya fasa.

Kwana biyu da tambayar Amar da yai Zarah zo sai dai ta rame sakamakon rashin lafiyar kuma sai yaga ta sake zama shiru-shiru sannan ta na d'an waige-waige lokaci zuwa lokaci, ita kam Zarah gabadaya hankalinta ba'a kwance ya ke ba cikin d'ari-d'ari ta zo sauri take ta kar6i 'kwan ta tafi kar ta had'u da Faridah ta sake ganinta tare da Irfan ta san har gidansu za ta iya zuwa taci mata mutunci.

"Ya jikinki Amar ya fad'a min ba ki ji dad'i ba fatan kin samu lafiya bana gari na je gida shi ya sa ban saka an zo an dubaki ba".

"Da sauki na samu lafiya".

"Me ya ke damun ki"?.

Shiru tai har sai da ya sake tambayarta sannan ta ce.

"Farko na...........

Sai kuma ta sake yin shirun ta kasa fad'a domin a rayuwarta ta tsani 'karya sannan ta ya zata fara fad'a masa ga abun da Faridah tai mata duk da bata san Faridan wace d'insa ba ko me ye matsayinta a gurinsa ba........

"Zarah ina tambayarki kin yi shiru ko akwai matsala ne"?.

"A'a amma dai ya zama dole na fad'a maka saboda ni ban iya hayaniya da kowa ba wannan budurwar da ta ke zuwa wajenka ita ce tai 'ko'karin bugeni a mota ranar da na bar nan sannan ta ri'ka marin fuskata ba abun da nai mata".

"Faridah"?.
Ya fad'a da d'an surprise a fuskarsa.

"Ni ban san sunanta ba amma dai ta na zuwa nan tayi min abubuwa da yawa wanda ban ji dad'insu ba".

"Ina jin ki me ya faru fad'a min"?.

"Da fari ban san me nayi mata ba ta rabani da mahaifiyata da 'yan uwana ta d'auke ni ta tafi dani wani gari................

"Ban gane ba ina ta kai ki"?.

Numfashi Zarah ta sauke kamar za ta ce masa abar maganar sai kuma ta ci gaba "kwanan baya lokacin da ka daina gani na ina zuwa nan ita ce taje har gidan mu ta cewa kishiyar Mamata ta zo ne daga birni ta na d'aukar 'yan mata aiki a gidan abinci duk wata ana biyansu kuma za'a saka su a makaranta ta ce a bata ni bana son zuwa sakamakon mahaifiyata bata da lafiya Amma dole na ha'kura na tafi na barta ta d'auke ni a mota ta tafi dani ta kai ni wani gidan 'yan iska ta biya kud'i nayi kwana d'aya tace washe gari za ta dawo ta d'aukeni ashe kawai ta rabu dani nasan yadda zanyi ne nafi wata guda a gidan sannan tashin hankali ya samu ana fad'a wuta ta kama a gidan 'yan sanda suka zo na had'u da wani Alhaji ya ce saina bishi na ce a'a karshe ina yawo a cikin anguwanni ban san kowa ba na sake had'uwa da shi zaije anguwa shi da matarsa su ka d'auke ni na zauna a gurin su zuwa kwana biyu da kansa ya dawo dani gida sannan ran nan dana bar nan na kusa zuwa gida na sake ganinta a mota ta tareni ta ri'ka zagina ta sha'ke min wuya da hijab ta ri'ka marina karshe ta hankad'e ni ta tada mota zata hau kaina ta danne ni na gudu shine ta ce kar na sake zuwa in da kake idan ba haka ba saita hallaka ni".

Sosai Irfan ya 'kame guri d'aya kamar an dasa shi ransa in yai dubu ya gama 6aci jin abun da bai ta'ba zato ba wato a kansa Faridah ta so jefa rayuwar Zarah cikin had'ari take neman kasheta bayan shi ba cewa yai ya na sonta ba, ai kuwa zai nuna mata ta yi kuskure kuma ta ci bashi.

Ji yai Zarah ta ce.
"Amma ban fad'a maka dan ka same ta da maganar ba kawai ka rabu da ita komai ya wuce".

"Me ya sa"?.

"Saboda ba na son tashin hankali kar abin ya zama babba ya kai 6acin rai".

"Ok kin yafe mata kenan"?.

"Ni dama ban ta'ba d'aukar zafi akan abin da tai min ba".

"Da kyau" ya na fad'in haka ta ga ya juya ya bud'e 'kofa ya shiga kai Amar da ke tsaye ya girgiza ya na cewa "mu je na kai miki egg's d'in da alamar wannan maganar ta tunzura boss sai abun da hali yai" ya fad'a ya na kallon yadda Zaran ta canza lokaci d'aya.

"Amma me ya sa baki fad'i abun da tai miki tun farko ba ki ka bari sai da ta nufi kasheki"?.

"Saboda ni bana son rigima ne shi ya sa dan Allah idan ka dawo ka fad'a masa kar yai mata magana akan haka ya 'kyaleta".

"Ai ni ban isa tunkararsa da wata magana ba yadda ya d'au zafin nan sai dai kawai nayi addu'ar Allah ya sa abun ya zo da sauki amma Faridah kam ba zai ta'ba 'kyaleta ba wannan a zaune take" numfashi Zarah ta sauke ba ta sake cewa komai ba har su ka je ya sauke mata 'kwan ya taho ya na dawowa ya tarar da Irfan tsaye a jikin mota ya na jiransa ya na zuwa su ka tafi kai tsaye gidansu Faridah ya cewa Amar su je sosai tsoro ya lullu6e Amar domin bai san me zai faru ba idan su ka je Kuma ya na tsoron kar yaiwa Irfan d'in magana nan ma a samu matsala.

A waje ya saka yai parking da motar shi kuma ya shiga gidan da 'kafa har cikin falonsu ya shiga tamkar d'an gidan a lokacin kuwa Faridah ta na zaune a falon kawai sai gani tai Irfan ya shigo ransa a 6ace da sauri ta mi'ke ta na cewa.

"Irfan lafiya me ya faru"?.

"Me Zarah tai miki ki ke 'ko'karin hallaka ta fad'an ki dani ne ba ita ba dan me ya sa zaki sakata a ciki bayan kin kawota bariki ta koma gida sannan ki ka bita da mota ki ka mareta har ki ke 'ko'karin kasheta fad'a min me tai miki ko ce miki akai ita ce ta hana ni na aureki"? Sosai jikin Faridah ya d'au rawa domin ba tai tunanin Zaran za ta iya fad'awa Irfan komai ba tun da taga ba ta cika yawan magana ba ashe za ta iya fad'a masa, sosai ta rud'e, rasa abun da za ta ce masa ta yi kawai ganin yadda ya ke a fusace sai ta fara ja da baya za ta gudu wani irin lafiyayyen mari ta ji ya sauke mata a fuskarta wanda ya saka ta fad'a kan kujerar da ke bayanta ta na 'kwalla 'karar azaba wanda ya saka Mami da su Aisha fitowa da gudu da mamaki duk su ka tsaya su na kallon Irfan wanda ya mayar da belt d'insa ya na sake d'aga hannu ya kifeta da sabon mari ko in da suke bai kalla ba ya juya ya fita da gudu Mami ta 'karaso in da Faridan take ganin gefen bakinta ya fashe ya na fitar da jini ta ce.

"Ke d'in me ki kai masa ya zo har gida ko kunyar idona bai ji ba ya zare belt ya dakeki"? Cikin kuka Faridah ta ce.

"Mami akan wannan shegiyar yarinyar da nake fad'a miki ce 'yar 'kauyen nan shine ta fad'a masa abun da nai mata ya zo ya rama mata" jin abun da tace yasa Mami cewa.

"Oh wacce ki ke zargi sonta ya ke"?.

"Eh mana ita ce".

"To ya akai ta koma garinsu ba kin ce kin d'aukota kin kawota nan ba kodai had'uwa su kai ya mayarta".

"A'a Mami ba shi ya mayar da ita ba sai dai idan da kanta ta koma domin da ace shine ya mayar da ita tun tuni da yanzu ta fad'a masa tun a ranar ita kad'ai ta koma ai ban yi tunanin ta na da hausar da za ta gudu ba da na kaita in da za'a tsareta har abada".

A masife Mami ta ce.
"Ke ma ai duk laifinki ne uban waya fad'a miki ki kaita wata uwa bariki sanin kanki ne kin san komai daren dad'ewa saita gudu gida tun da ba niyyar kanta ce ta kawota ba"?.

"Ai kuma Mami tun da ya dakeni akan yarinyar nan ba zan ha'kura ba saina d'au fansa mafi muni wacce zai yi nadamar abin da yai min saina kasheta na ga wanda ya tsaya mata kaf 'kauyen ba wanda ya isa ya bud'e bakinsa ya ce min 'kala na kashe banza".

"K'warai kuwa ina goyon bayanki d'ari bisa d'ari ki kasheta kar ki barta da rai duk ranar da ki kai ido hud'u da ita ki tabbata ta kwana a jerin gawarwaki".

"Wannan alkawari na ne Mami Kuma saina cika shi" ta fad'a ta na shafa gefen fuskarta jin yadda yatsunsa su ka fito rad'a-rad'a a fuskar mi'kewa tai ta na d'ingisa 'kafa Mami da ta ri'keta ta ce "mu je na had'a miki ruwan zafi gobe da sassafe zan yi dirar mikiya a gidansu na kai 'kararsa gurin iyayensa dole su d'au mataki a kansa".

Irfan kam dama ya na fitowa daga gidan kai tsaye gida ya saka Amar ya kai shi yai wanka kawai ya kwanta har lokacin bai ji ya dawo daidai ba ransa a 6ace ya ke kuma bai fito falo ba har sai da Daddy ya dawo ya na gida Alhaji Sa'id yai kiransa ya fad'a masa abun da ya faru sosai mamaki ya rufe su jin wai Irfan ya je har gida ya da'ki Faridah, kiransa Daddy yai a waya ya ce yazo falo yanzu ya same shi.

Su na zaune ya fito shima ya zauna Daddy da ke kallonsa da yanayin 6acin ran fuskarsa ya ce.
"Irfan me ka aikata wannan akan wata yarinya ka iya zuwa har cikin gidan Alhaji Sa'id ka daki Faridah tsabar rashin hankali"? Kan Irfan ya na 'kasa ya ce.

"Ka yi ha'kuri Daddy abun da tai yai mugun 'kona min raine in dai ba hakan nai mata ba bazan ta'ba hucewa ba".

Kai Daddy ya jinjina ya na cewa.
"Kome tai maka Irfan bai kamata ka je har gida ka daketa ba wannan rashin hankali ne da rashin sanin ciwon kai to amma kar nayi gaggawa kuma kar na yanke hukunci akan abun da ban sani ba bari na tambaye ka kenan ita waccan yarinyar da kayi fad'an a kanta sonta ka ke kome"?.

Kai ya girgiza.
"A'a Dad ni ban ta'ba sonta ba kawai ina ganin kimarta ne da hankalinta shi ya sa ta taso jefata cikin bala'i a kaina shine raina ya 6aci".

D'an murmushin manya Daddy yai ya na cewa.
"Ta ya zan yarda Irfan bayan ga kishinta nan na gani amma kana min musu wai ba sonta ka ke ba, ba ka son nata kai fad'a a kanta sannan kai mata ramuwar gayya"?.

Huci Irfan ya fita ya na cewa
"Da gaske na ke Daddy ni ba son wannan yarinyar na ke ba".

D'an shiru Daddy yai ya na d'an bubbuga goshinsa da yatsa can ya kalli Irfan ya ce.
"Hakan ya yi kyau ai gara da wannan abun ya faru kaga ka kama kanka yanzu ko kana so ko baka so dole ne aure kai da Faridah a d'aura shi".

Wata muguwar zabura Irfan yai a firgice ya ce.
"What!!! Daddy please dan Allah..............

"Kar ka fara ro'ko na ba zan yi maka uzuri ba a wannan karon za ka san koni waye na gama yanke hukunci wannan za6i nane ba naka ba sai ka auri Faridah". Daddy na rufe baki Irfan ya dafe kansa dake mai ciwo tare da mi'kewa yai hanyar waje da sauri Momy ta ce.

"Irfan tsaya ina za ka fita kaje"? Ta fad'a ta na 'ko'karin mi'kewa Daddy ya dakatar da ita "ki rabu da shi ko bangon duniya ya tafi zai dawo garemu tun da bai da wad'anda su ka fi mu in kuma akan haka zai sayi wasu iyayen ne duk 'kofa a bud'e ta ke" ya na rufe baki Momy ta saka masa kuka ta na cewa.

"A'a Alhaji dan Allah ka barni na bi bayansa ya fita ransa a 6ace ina tsoron kar wani mugun abu ya sameshi ba mu san in da ya dosa ba yanzu" kai Daddy ya girgiza ya na sake d'ora 'kafa d'aya kan d'aya ya d'auki glass ya saka a idonshi littafin da ke aje a gefen kujerar ya d'auka kawai ya bud'e ya fara karantawa iya tashin hankali Momy ta shiga ganin abin da Daddyn yai ya sa ta d'auki wayarta da sauri ta fara kiran layin Irfan d'in amma ba a d'aga ba, haka tai ta kira ta na share hawaye ba picking...........
🤙✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR

JUYIN MULKI
By
Yusrah Musa Abubakar
Jigawa state.
New world 🌎 Jigawa venture's 🌴.

👑Matashin Yarima👑
Is loading in sha Allah.

26_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Nabi'inah.

...................... PAGE 26
Irfan kam ya na fita daga falon da ya d'au mota gidan su Bilal ya je yana zaune sai ganinsa yai ya shigo da sauri ya mi'ke ya na tararsa.

"Subahanallahi Irfan lafiya me ya sameka na ganka a haka"? Kai Irfan ya girgiza ya na dafe saitin 'kirjin sa da'kyar ya ce.

"Faridah ta cuce ni Bilal ta lalata min rayuwata".

"Faridah kuma me tai maka"?.

"Mummunan aiki ta aikata kuma na hukunta ta Daddy ya ce dole saina aureta umarninsa ne ba za6ina ba".

"Me tai maka"?.

"Ba zan iya yi maka bayani ba Bilal ina bu'katar samun nutsuwa yanzu dan Allah ka tashi mu je gurin Daddy ka bashi ha'kura wallahi har cikin zuciyata da gaske nake ba na son Faridah ko kad'an zan iya mutuwa idan Daddy bai janye umarnin da yai min akan auren ta ba gara na mutu akan auren Faridah na za6i na bar duniya Bilal ba na son ta dan Allah ka taimaka min" kai Bilal ya d'aga ya na cewa.

"Okay okay Irfan na fahimta mu je gurin Daddyn yanzu amma ka daina wannan maganar" ya fad'a ya na jan hannun Irfan d'in kamar yaro su ka fita lokacin da su ka kaje gidan iya Daddy su ka tarar a falo Momy ta tashi zama su kai a gabansa kowa yai shiru an rasa wanda zai fara magana a cikinsu murmushi Daddy yai ya na kallon Bilal ya ce.

"Mr. Bilal and Mr. Affan me ya ke tafe da ku da alama kuna son magana da ni ne"? Jinjina kai Bilal yai ya na sake gyara zamanshi ya ce.

"Eh Daddy mun zo neman alfarma ne".

"Ok auren Mimih ka zo tambayata sonta ka ke"? Jin abin da Daddyn ya ce daga Irfan har Bilal ya sa suka zabura suna kallonsa da mamaki.

"Umhum ina jin ka ci gaba" ya sake magana ya na kallon yadda fuskar Irfan har lokacin ta ke dan'kare da 6acin rai, kan Bilal a 'kasa ya ce.

"Akan maganar auren Irfan da Faridah ne.........

"Na gane ba bu'katar bayani ya je kun gama tattaunawa kenan yaushe ya fad'a maka ya ke bu'katar asa bikin"? Daddy ya sake katse shi a susuce ya sa Irfan matsowa ya na ri'ke 'kafarsa ya ce.

"Please Daddy na san kasan dalilin zuwan mu gurin ka dan girman Allah Daddy ka tsaya ka saurare ni kar zuciyata ta samu matsala a halin yanzu ma tamkar wacce ta kamu da ciwo haka na ke jin ta na min zafi dan Allah Daddy ka yi min afuwa".

"Akan me kenan"?.

"Auren Faridan da kace umarninka ne ba za6ina ba".

"Irfan kar ka mayar da ni 'karamin mutum man tun yaushe nake binka da maganar ka na ja min rai to yau damata ce ta samu yanzu lokacina na ne ka gama naka komai na yanke maka dole ka bi".

"Dan Allah Daddy ban da auren Faridah ka janye wannan maganar".

"Ba zan janye ba Irfan in kaga ba ka auri Faridah ba to bana wannan duniyar tun da haka ka za6a".

Wani mugun jiri ne ya d'ebe Irfan yai baya zai fad'i da sauri Bilal ya tare shi ya fad'a jikinsa tsabar tashin hankali ko gani baya yi sai duhu bai jin komai tamkar wanda ya mutu ganin halin da ya ke ciki ya sa Bilal cewa.

"Dan Allah Daddy ka yi ha'kuri ka yafe masa zai samu wacce zai aura idan ka ba shi lokaci".

"Sau nawa zan bashi lokacin amma sai ya ri'ka min wasa da hankali gashi ka tambaye shi yadda na ke fama da shi".

"ka bashi dama ta 'karshe zan taya shi duk abun da ka ke bu'kata na yi maka alkawarin za mu yi".

Shiru Daddy yai ya na kallon Bilal ya kuma kalli fuskar Irfan da idonsa ya ke a rufe ya ce.
"Shi ke nan naji zan iya bashi d'an gajeren lokaci amma ba zan janye maganar auren Faridah ba sai ya samu wacce ya ke so kuma ya tabbatar aurenta zai yi".

"Eh Daddy mun amince da sharad'inka" Bilal ya fad'a cikin jin dad'i ya na kallon fuskar Irfan wacce ta ke ji'ke shakaf da gumi kuma ya kasa koda ya motsa lips d'insa ne balle shi ya ce ya yarda d'in mi'kewa Bilal yai ya taimaka masa shi ma ya tashi ya raka shi part d'insa a can ma ya sake zama yai ta masa magana mai kyau wacce za ta amfane shi sannan ya tashi ya tafi gida.

Zuwa dare tsabar yadda Irfan ya d'au lamarin a ransa sai da ya silar da zazza6i mai zafin gaske ya rufeshi ba wanda ya sani sai da Momy ta shigo zata ce masa ya fito yai dinner ta ganshi a kwance jikinsa zafi d'au kuma barci ya ke, wayarsa dake gefen gadon ta d'auka ta kira Bilal za ta sanar da shi.

Ya na d'agawa ta ce.
"Hello Bilal dan Allah idan ka na kusa ka zo ka duba abokinka bai da lafiya".
Ajiyar zuciya Bilal ya sauke dama ya san za'ai haka a take ya zo ya duba shi sannan ya d'aura masa ruwa da allurar zazza6i ya rubuta musu magani bayan tafiyarsa Momy ta baiwa Salim ya siyo Irfan kam har lokacin bai farka ba shi ya sa da dare yai sosai Momy tace Salim ya tsaya ya kwana tare da shi ita kuma ta tafi part d'insa.

Washe gari da wuri ya fito falo ya kwantar akan kujera sakamakon ba ya jin 'karfin jikinsa sosai iya tea ya kar6 a gurin Momy ya sha, sannan ya sake kwanciya Mimih da ta fito za ta tafi school ta ce.

"Yaya Irfan ya jikin"? Kai ya d'aga mata alamar da sauki sannan ta mayar da hankalinta kan Momy ta na cewa "na tafi Mom".

"Ok Mimih a dawo lafiya ki kula"

Bayan fitar Mimih Momy da ta zo kusa da shi ta zauna ta na d'an ta'ba jikinsa ta ji babu zafi ajiyar zuciya ta sauke ta na cewa "sannu Irfan ya jikin na ka"?.

"Da sauki ina Dad ya ke"? Kallonsa tai jin tambayar da yai mata ta ce "ya fita zai je asibiti ya duba Faridah dukan da kai mata jiya ya kwantar da ita ba ta da lafiya har ta fika jin jiki nima in anjima zan je na dubata".

Jin abun da tace ya sa yace.
"Dan Allah Momy kar ki je dubata"?.

"Me ya sa"?.

"Saboda idan ki ka je mahaifanta za su yi tunanin da gaske zan aureta ne ni Kuma ba zan ta'ba auren wannan yarinyar ba har abada ko ganinta ba na so".

"Ai kuma Irfan ko da wannan ala'kar ko babu dole na je duba Faridah saboda kar ka manta mahaifin ta abokin mahaifinka ne kuma Daddyn na ka shi yace min na je na dubata".

"To ki sake fad'a mata sa'ko daga ni Affan Sulaiman na ce bana sonta ba zan aureta ba har abada" zaro ido waje Momy tai ta na kallonsa tsabar yadda maganar ta bata mamaki ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ta ce.

"Tofa na shiga da'ka ni Ru'kayyah tabdijan da hankalina zan je na fad'i wannan maganar Irfan"?.

"Ni zan iya zuwa har gaban mahaifan na ta na fad'a musu dan su tabbatar ba zan aureta".

"To sai dai kai d'in amma ni kam Allah ya suturi bu'kui in ji kishiyar mai doro" ta fad'a ta na mi'kewa ta shiga kitchen domin ta samar masa abun da ya kamata ya ci tasan in ba takura masa tai ba zai iya wuni bai ci komai ba shi idan bai da lafiya ba ya yarda ya sha koda ruwa ne sai da'kyar.

Ya na falon Momy ta had'o masa komai sannan ta je ta shirya ya na zaune ta fito ta tafi dubiyar Faridah bai tashi ya je ko'ina ba sai Bilal da ya zo ya sake dubashi suna zaune Momy ta dawo kusan wuni Bilal yai a gidan sai jikin la'asar ya tafi gida.

Da dare bayan Daddy ya dawo ya kira Irfan zai duba shi.
"Ya jikin na ka"?.

"Da sauki Daddy".

"Masha Allah haka ake so Allah ya 'karo sauki nace jiya ka ji duk maganganun da mu kai da Bilal ko"?.

"Eh".

"To ya ake ciki ina bu'katar jin amsa daga bakinka"?.

"Daddy ka yi min afuwa da gaske na ke har cikin zuciyata ba na son auren Faridah".

"Ok na fahimta sai dai wani hanzari ba gudu ba zan baka za6i biyu ko auren Faridah ko auren wannan yarinyar ta wancan 'kauyen da kai fad'a a kanta itama sonta ka ke na gani a yanayin furucinka idan kuma ka sake musa min cewa ba sonta ka ke ba na baka sati d'aya tal zuwa rana itayau ka samu yarinyar da tai maka idan ka 'ki wallahi tallahi Irfan ko ba ka so saika auri Faridah" da sauri Irfan ya d'ago ya na kallon Daddy ya ga fuskarsa ba wasa kuma ga shi ya yi rantsuwa dole ya tashi a tsaye kafin cikar satin ya samu wacce ya ji a ransa zai iya rayuwa da ita,

"Na yi magana ba kace komai ba"? Daddy ya katse masa tunanin da ya ke, numfashi ya sauke cikin wani irin yanayi wanda bai san me zai kirashi ba ya ce.

"Na amince Daddy zan samu kafin satin ya cika".

"Haka na ke fata idan kuma ka gagara wannan matsalarka ce ni dai na yi rantsuwa kuma ba zan yi

Please Login or Register in order to submit comment