You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

safe ta fita daga cikin gurin da ta shiga taga ashe ma bencin ajiye-ajiye ne na suyar kifi duk ta 6ata kayanta da hijab d'inta da mai'ko saita tashi kamar wacce ta fara hauka ga dama ba takalmi a 'kafarta haka ta ri'ka tafiya a layin ba ta kallon kowa ba ta kallon komai sai mutane da suke faman bin ta da ido suna kallonta harta fita daga layin ta shiga wani cikin rashin sanin in da zata nufa gajiya tai da yawo ga yunwa kawai ta zauna a wani gurin tai shiru, ta dad'e a zaune wata mota ta zo harta wuceta sannan ta dawo da baya wanda ya ke ciki ya sauke glass wani Alhaji ne d'an matashi zai kai shekara arba'in da wani abu da mamaki ya kalleta ya na cewa.

"Ke yarinya lafiyarki 'kalau kuwa"? Shiru Zarah tai ta na kallonsa ba tai magana ba ya 'kara cewa "ko taimako ki ke nema"? Sai sannan ta girgiza kai ba tai magana ba ganin haka ya sa bai sake ce mata komai ba ya wuce ya bar gurin da kallo Zarah ta bi motar harta 6acewa ganinta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta na gyara zamanta jikanta duk 'karnin kifi ji take zuciyarta ta na tashi amma ba yadda za tai tun da indai ba cire kayan gabadaya za tai ba baza ta daina jin 'karnin ba.

Haka ta wuni a gurin ba karyawa ba sallah duk lamarin duniya ya isheta har jikin sallar magriba sosai mamaki ya kama wannan mutumin ganin a in da ya barta anan ya dawo ya sameta shifa tunaninsa ya fi bashi ko ta6in hankali ta fara samu domin ba tai kama da mahaukata ba amma ta yi yanayi da masu gushewar tunani.

Ya na shiga gida ya sanar da matarsa abun da ya gani saboda shi ya kasance mutum mai tausayi a take ya saka su ka fito duk da matar tana da tsoro amma haka ya saka ta ri'keta su ka tafi zuwa cikin gida duk da tirjewa da Zarah ta ke itama a nata 6angaren tsoron ya gama cikata ba ta san su waye su ba bata san me za su yi mata ba idan su ka kaita gidan haka ta ri'ka rusa musu kuka a falo gabadaya ta cika gidan rasa yadda za su da ita su kai ta gama caza musu kai.

"Alhaji ko dai mu fitar da ita daga gidan kawai tun da ta nuna ba ta yarda da mu ba"? Matar ta fad'a ta na kallon yadda Zarah ta ma'kale a gurin d'aya ta'ki sakin jikinta, kai ya girgiza "a'a ba za mu yi haka ba kar ki manta duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimaka masa shi ya sa na damu a kanta dole na san yadda zan yi na samo 'yan uwanta, bari mu gani ko za'ai sa'a ta daina kukan" ya fad'a ya na d'an matsawa in da take tsaye dan sam ta'ki zama, ganin ya matso in da take ya sa ta ja da baya da sauri kai ya girgiza ya na sauke ajiyar ya ce.

"Kin ga kiyi shiru ki nutsu ba wani abu za mu yi miki ba kawai mun ga kina bu'katar taimako ne shine za mu taimaka miki ba za ki fahimce mu ba sai kin yi shiru ba cutar da ke za mu yi ba kin ji"? Kallonsa Zarah tai jin abun da ya ce, Allah ya sa da gaske har cikin zuciyarsa yai maganar domin yanzu duniya ba abar yarda bace wanda ka ke ganin zai kareka sai ya canza zuwa wanda zai had'a baki a cutar da kai amma ko ba komai ta ji dad'i a ranta da ya ce taimakonta za su yi........

"Ki na cikin hayyacinki ne za ki iya bada amsa idan an tambaye ki"? Kai ta d'aga ta na goge hawaye da'kyar ta ce.

"Eh".

Kallon juna su kai cike da mamaki shi da matar tasa kenan ma lafiyarta 'kalau ba ta'bin hankali ta samu ba, in dai haka ne akwai abun da ya rabota daga gida "nifa na fi tunanin 6atan kai tayi ko kuma masu garkuwa ne su ka sato ta"? Matar ta sake fad'a ta na bin Zarah da kallo kai ya girgiza ya na cewa "ke dai ki yi shiru kawai bari na yi magana da ita duk yadda akai ta baro gida za ta fad'a" mayar da hankalinsa yai kanta ya na cewa.

"Ya sunanki sannan ina ne anguwar ku"?.

"Sunana Zarah ni ba 'yar nan garin bace".

"A wanne gari ki ke"?.

"Garin mu 'kauye ne daga can aka kawoni nan".

"Wa ye ya kawoki"?.

"Wata budurwa ce".

"Wata budurwa kuma, ba ki santa ba"?.

"Eh a ranar na fara ganinta".

"To ya akai ki ka biyota bayan ba ki santa ba"?.

"Har gidanmu ta je ta taho dani wai zata kawoni na ri'ka aiki a gidan abinci ta na turawa kishiyar Mamanta kud'in shine da ta kawoni nan garin ta kaini gidan karuwai ta gudu ta barni ban sake ganinta ba har yau jiya an yi fad'a a barikin shine wata ta watsa fetur ta kunna wuta gidan ya 'kone muna tsaye a waje motar 'yan sanda su ka zo gurin shine muka gudu a daren na zo inda ka ganni a zaune anan na kwana da gari ya waye ban san ta inda barikin yake ba balle na koma shine na ke zaune a gurin".

"la'ilaha ilallahu, subahanallahi Alhaji ka ji wani rashin mutunci haka kawai yarinyar ta na zaune a gaban iyayenta cikin mutunci wata 'yar iska ta je ta d'aukota wai harda 'karyar aiki a gidan abinci ana biyansu albashi".

"Ai ba laifinta bane ba ki ji tace kishiyar Mamanta ce ta yarda aka taho da ita kin ga wannan ba abin mamaki bane" sai kuma ya kalli zarah wacce ta sunkuyar da kai ya ci gaba "mun fahimceki sosai kar ki damu Allah ya tseratar da ke daga sharrin da taso ta jefaki na yi miki alkawari da kaina zan kai ki har cikin gidanku kin ji"

"Ba ki da Mama ne"?.

"Ina da ita"?.

"Amma ta barki ki ka taho"?.

"Ba ta da ikon da za ta hana domin ba ta da lafiya 'kafafunta suna mata ciwo ko da yaushe muna kan hanyar kaita asibiti sannan mahaifina ba mazauni bane shima kullum ya na kasuwa shine tai amfani da wannan damar ta turo nayi aiki a tura mata kud'in".

"Allah ya kyauta duk wacce tai miki haka ta cika jahila akan me za tai 'karya ta kawoki gidan karuwai salon su watsa miki rayuwa haka kawai ta san ba gaskiya bane me ya sa ta d'aukoki wannan ta cancanci d'auri da ace kin santa har gidan ubanta zan tura hukuma su kamata sai ta fad'i dalilin da ya sa take son jefa rayuwarki cikin matsala ba laifin tsaye bana zaune" juyawa yai 6angaren da matarsa take ya ce.

"Yanzu abun da za'ai ki rakata d'akin Ikram ki nuna mata toilet tai wanka tai sallah sai ta fito ki had'a mata abinci in sha Allahu gobe da safe zan mayar da ita gidansu" kaita d'aga ta na mi'kewa ta kalli Zarah "taso mu je" tashi tai ta bita, suka je d'akin ta nuna mata gurin wanka sannan ta fito.

Zarah kam da ta samu wadataccen ruwa da sabulu sai da tai wanka ta 'kara sakamakon 'karnin kifin dake jikinta.
Bayan ta fito ta d'auki hijab d'inta ta saka ta koma falon sakamakon barci za tai sai Hajiyan ba ta bata kaya a daren ba ta barta da zanin ta saka mata abinci taci sannan ta sake rakata d'akin ta bata kayan barci ta saka tai mata sai da safe ta rufe 'kofa shiru Zarah tai ta na kallon pop d'in saman d'akin a ranta ta na tunanin yau kuma nan ta fad'o bayan ta bar bariki ga ta a inda ba ta ta'ba tunanin za ta zo ba har ta 'kare rayuwarta. D'an rufe ido tai ta sauke numfashi kawai fuskar Faridah ta ke hangowa a ranta daga lokacin da ta fara ganinta a falon Irfan lokacin da taje kar6ar 'kwai har zuwa ranar da ta kawota wannan garin tunani ta fara kenan in dai haka ne Irfan da ita sun san juna ko kuma akwai ala'ka a tsakaninsu tun da ta gansu tare sai dai ta tabbata duk rintsi Irfan bai san tai mata haka domin ba zai bari ba, kuma ta d'auka a ranta idan ta koma ko ya tambayeta inda ta je a cikin kwanakin ba za ta fad'a masa ba saboda gudun tashin hankali..

Washe gari kamar yadda mutumin ya fad'a bayan sun karya da kansa ya d'auketa a motarsa harda matarsa su ka mayar da ita a lokacin Ubaliyo ma ya na gida mutumin yai bayanin halin da ya tsinceta sannan ita ma Zarah ta fad'i komai daya faru daga lokacin da Faridah ta d'auketa zuwa ranar da Khalidah tai fad'a da rainbow ta 'kona gidan.
Sosai ran Ubaliyo ya 6aci domin shi daya dawo 'karya Hamah ta shirya masa har ya ke ganin laifin Umma wacce take 'ko'karin fad'a masa gaskiya ashe da yanzu 'yarsa ta lalace ta zama 'yar duniya bai sani ba.
Godiya sosai yai musu harda kukan sa wanda za mu iya cewa na ba'kin ciki ne domin ko waye ba zai so a nemi wula'kanta masa d'a ba sai iya inda 'karfinsa ya 'kare.
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Yusrah Musa
Mai tambarin yma writer
Marubuciyar
1_Yarima Abdul-maleek
2_D'an millionaire
3_Safreeyyah
4_Me kamar sarki
5_Minister Ashraf
6_Royalty
7_Zuciyar Aliyu ce
And now
8_Juyin mulki
Later
9_Yarima Aryan

TYPING 📲Sat, Aug 1/2026 9:30PM
WhatsApp no: +234 816 098 3083

JUYIN MULKI
By
YMA WRITER
YÜSRÄH
✍️To ai yanzu wasan zai fara😀.
______________ Yusrah ______________
_____________________________________

22_Allahimma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Akraminah.

_______________ PAGE 22
Sakamakon shi ma Irfan bai samu zuwa 'kauyen sosai ba a wad'annan kwanakin ya na ta ayyuka sai dai Amar shi ne yai mugun kewarta musamman da ta daina kawo awarar kuma Hannatu ta daina yi musu ita ma sannan ba sanarwa ba sanin ta bar gari su kai ba balle kuma su san Faridah ce ta d'auke ta.

Ya na zaune a falo bayan ya shirya da wata babbar sar'ka a gefensa ya ajeta Mimih da fitowarta kenan ganin sa'kar yasa cikin murna ta 'karaso ta na zama a kusa da shi duk zatonta sa'kar nata ne tun da tasan baida budurwa kuma bai da wacce zai kaiwa ta ce.

"Good morning".
Tun kafin ya amsa ta sake cewa "Yaya Irfan wannan sar'kar fa"? Ta na d'aukarta ta fara kalla "bro nace wannan sakar fa"? Ta sake fad'a sakamakon jin bai amsa mata da farko ba sai yanzu.

"Ya akai"?.

"Tawa ce"?.

"A'a"
Mimih ta zaro ido "wayyo ta waye wa za ka baiwa".

"Wata yarinya".

"Budurwarka".

"Noooo" ya fad'a da 'karfi har sai da Mimih ta tsorata Momy ta kalleshi Salem ya saki 'karamar dariya ya na girgiza kai gaskiya lamarin Irfan sai mai ha'kuri. Cikin naci Mimih ta sake cewa.

"Amma Yaya Irfan na ga sar'kar gwal ce za tai tsada sosai amma za ka baiwa wata"?.

"Ta cancanta ne".

"Dan Allah ka bar min ka siya mata wata".

"No".

"Please Yaya Irfan".

"I said no".

Kamar za tai kuka ta kalleshi har za ta sake magana sai kuma ta fasa kawai tai shiru ta na kallo ya mi'ke ya d'auka ya fita cikin shagwa6a ta ce.

"Momy sar'kan gold ce fa kina kallonsa zai kaiwa wata bayan gani ina so".

"Eh to me zance".

"Da kin hana shi dole zai ha'kura ya bani".

""Akan me zan hana shi wannan ba hurumina bane ya riga ya yi niyyar kyauta saina hana ai bai kamata ba idan ki kai ha'kuri ma maybe kema ta ki ta na nan ya siyo miki kawai dai bai fito da ita bane amma in 'ki kika sake tambayarsa ko ya hanaki ba ruwa" Momy ta fad'a ta na nuna mata alamar maganar da tai da gaske take d'an tura baki Mimih tai kamar za ta sake cewa wani abu har ta bud'e baki sai kuma ta fasa ta mi'ke ta d'auki jakarta tai waje ta bar iya Momy da Salim a falon.

Lokacin da Irfan ya shiga ma'aikatar ya yi sa'a kuwa ya na parking da motarsa bayan Amar ya bud'e masa 'kofa ya fito ya hango Zarah ita ma zuwanta gurin kenan za ta tambayi inda Amar d'in ya shiga sai ta hangosu shi ne ta taho wajen.

A hankali tai sallama sannan ta gaida Irfan cikin ladabi kamar yadda ta saba girmama shi dan bata ta'ba yi masa kallon wai ai shi ya kasance saurayi bane a'a kawai ta na ganin darajarsa sosai sannan ya na da kima a idonta musamman yadda ba shi da girman kai shi ya sa ita ma taga ya zamo wajibi a gareta ta ri'ka girmama shi tamkar d'an uwanta Yayanta haka ta ke ji a ranta.

Su na tsaye ba wanda ya sake cewa kowa komai kawai gurin ya yi shiru ta na jiran Amar ya fito Mata da 'kwan su tafi can 'kasa ta ji muryar Irfan ya ce.

"Zarah".

"Na'am".
Ta amsa ba ta d'ago ta kalleshi ba kanta ya na kansa har lokacin, shi kam idonsa ya na kanta sannan tambayoyi ne da yawa a ransa a kanta amma sai ya ji bakinsa ya yi masa nauyi kawai yai shiru daga haka har Amar ya fito ya na cewa Zarah ta zo su tafi, ganin ta juya za ta bar gurin ya sa a karo na biyu Irfan ya sake cewa.

"Zarah".

Tare da ita da Amar su ka juyo suna kallonsa had'e fuska yai sosai ya na cewa.

"Ina son magana da ita ne".
Ya fad'a ya na sake tamke fuska saboda kar Amar ya kawo wani tunanin dabam a ransa ko yai tunanin sonta ya ke, shi kam Amar ganin abun da Irfan d'in yai da kuma abun da yace ya sa ya kalleshi kamar zai yi dariya amma ya danne da'kyar ya bar gurin ya na toshe baki gudun kar dariya ta fito fili uban gidan nasa ya ji.

Bayan wucewar Amar ma gurin sake d'aukar shiru yai a 6angaren Irfan ya rasa dalilin da ya sa ya tsayar da ita sannan ta tsaya d'in ya kasa ce mata komai, haka ita ma Zarah a nata 6angaren kawai tai shiru ta na sauraro ta ji me ya sa ya tsayar da ita.

D'an dafe goshi yai ya na nazarin me ya kamata ya tambayeta, sai kawai ya samu kansa da cewa.
"Zarah ina ki ka tafi tsawon lokaci ba na ganin ki kuma Amar da yaje gurin Auntyn ki bata fad'a masa komai ba kawai ta ce kin yi tafiya"? Jin tambayar da yai mata ya sa ta d'ago ta kalleshi ta mayar da kanta 'kasa ta ce.

"Eh na je wani gari ban dad'e da dawowa ba" kai ya jinjina ya na d'auko sar'kar da ya taho da ita ya mi'ka mata ya na cewa "nima na yi tafiya zuwa Switzerland ne kin san 'kasar"? Kai ta girgiza.

"A'a ban ta'ba jin sunanta ba ma".

"Ok amma ki na so ki je"?.

Nan ma kan ta sake girgiza masa "a'a ni nafi so na zauna a garina na yi rayuwa cikin kwanciyar hankali akan na je inda ban san yadda tsarin dokarsu ta ke ba, watakil abun da nake ganin daidai ne anan can ya zama kuskure a wajensu, ni ko barin garin nan ba sosai nake yi ba balle kuma na haura wata 'kasar".

D'an murmushi yai kad'an ya na kallonta ya ce "wata rana za ki je wuraren da baki ta'ba tunanin zuwa ba idan ki ka zama babbar 'yar kasuwa ba wanda ya san me zai faru a gobe sai Allah dan haka kar ki mamaki wata rana ki ga kin je ko"?.

Kai ta d'aga amma ba tai magana ba daidai Amar ya le'ko su ka had'a ido da Irfan da sauri ya kau da kai ya na 'karasowa ya tsaya a gefensu, juyawa Zarah tai za ta tafi haka nan Irfan ya ji dad'in tsayawa da ita sannan ya ke jin dad'in hirar da su ke yi.

"Zarah ki kula".

Jin abun da ya ce yasa murmushi ya kubcewa Amar kawai ya kalli dukkan su biyun ya na jinjina kai ita ma Zaran duk da ta d'an ji mamaki amma sai ta 6oye jin mamakin nata ta ce.

"Na gode".

Tsabar gulma tana cin Amar bai bi bayanta ya rakata har gida da 'kwan ba ya barta ta tafi ita kad'ai ta na fita ya kalli Irfan ya na cewa.

"Sir".

"Yes".

"Zan iya tambayarka wani abu"? Jin abin da yace ya saka Irfan ya d'an kalleshi ya na d'age gira ya ce.
"Umhum".

"Dama ranka ya dad'e cewa zan yi ko ka fara son wannan yarinyar ne"? A dari ya saka shi zabura ya na juyawa ya yi masa wani irin kallo wanda ya saka cikin tsoro ya ce.
"Sorry Sir it was a mistake" ya fad'a ya na dukan bakinsa ganin yadda Irfan yai mugun hade rai kamar ba yanzu fuskarsa ta ke fal da murmushi ba.............
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Mai tambarin yma writer Yusrah Musa Abubakar Jigawa state.

❤️I❤️Love❤️My❤️Mom❤️No❤️One❤️But❤️You❤️Mamana💃🤙❤️.


🌲JUYIN MULKI🌲

By👇
Yusrah Musa Abubakar
Jigawa state.

Writer........
Yarima Abdul-maleek_____________01
D'an millionaire___________________02
Safreeyyah_______________________03
Me kamar sarki__________________04
Minister Ashraf___________________05
Royalty___________________________06
Zuciyar Aliyu ce__________________07
And now
Juyin mulki_______________________08
Later
Matashin Yarima_________________09


23_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Munzirinah.


............................. PAGE 23
Mami ta na zaune a falon part d'inta tare da 'kawarta ta zo mata ziyarar bazata.
"Gaskiya ba ki da kirki Hajiya Rabi wato sai yau ki ka zo min tun alkawarin da mu kai da ke cewa kina kan hanya"? Hajiya Rabi tai dariya ta na cewa.

"Ki yi ha'kuri 'kawata kin san yanzu liyafa taci gaba ba samun zama na ke yi ba shiyasa bana le'ko miki amma ai kin san ba zan watsar da ke ba".

"Na sani amma dai da naga idan na kira ba koda yaushe ki ke d'agawa ba ko idan nayi miki magana ta WhatsApp ba reply sai nake tunanin ko laifi na yi miki ko kuma sabin 'kawaye ki kai".

"Humm ai kuwa dai ba wani laifi kuma ba sabin 'kawaye sai tsabar sabgogi da su kai min yawa kullum fa bana wuni a gida sai ranar weekend shi ma ba koda yaushe ba" ta fad'a daidai Faridah ta fito ta gaida da ita sannan ta kalli Mami ta na cewa "na tafi gurin aiki Mami".

"Ok Faridah Allah ya tsare ki kula sai kin dawo".

"Zan kula Mami na tafi".
Ta bud'e 'kofa ta fita Hajiya Rabi ta kalli Mami "wai dama Faridah ce"? Kai Mami ta d'aga ta na cewa.

"Eh ita ce kin ga ta sauya miki ko"?.

"Gaskiya ta canza min sosai sai naga ta zama 'yar 'karama kuma ta rame ko dai tayi rashin lafiya".

"A'a ba wani rashin lafiya sai dai rashin kwanciyar hankali kawai".

"Kamar ya ban gane ba".

"Rabi ki bar ni da kayan ba'kin ciki da takaici kefa wani yaro ta ke so, kuma magana akai tsakanin Alhaji da mahaifinsa za'a d'aura musu aure su daidai amma shi sam hankalinsa baya kanta ya'ki sauraron ta kullum sai wula'kanci idan ta kira wayarsa ba zai d'aga ba".

"Au wai akan haka ku ka zauna kuna 6ata lokacin ku bayan kuna da ni".

"Me ki ke nufi".
Mami ta fad'a cikin muryar rad'a ta na waige-waige kamar wani ke jinsu ta ce "ki yi min bayani 'kawar arziki ko kin san wani abu ne wanda zai taimaka mana"?.

Jinjina kai Hajiya Rabi tai ta na cewa.
"K'warai kuwa ai ban sani ba da ba'a kawo yanzu bata aureshi ba shi d'in banza waye shi ko da me yake tunkaho a gurina shi ba komai bane dan ni da kika ganni nan na zama ciwon ido sannan ni 'kashin cikin turmi ce maganin wadan kare da ace tun farko kin same ni da zancen da yanzu kun manta da ta aureshi" humm Mami fa abun nema ya samu da sauri ta sake yin 'kasa da murya ta na cewa.

"Yauwa dan Allah Hajiya Rabi ki taimaka min wallahi yaron nan ba iya Faridah ba nima ya na cutar dani saboda kullum bana iya cikakken barci sai tunanin yadda zan 6ullowa al'amarinsa ashe ma ni ina da maganin matsala ta".

"Tabbas Zulaihat ki share hawayenki sannan ki saka a ranki kwanan nan zai zama surukin ki bari zan miki magana da wani babban malamin duba muje na raka ki gurinsa ya duba miki komai idan ma hankalin Irfan d'in aka janye a kanta baya kulata duk zai fad'i komai" jinjina kai Mami tai ta na cewa.

"Humm kice na d'aura d'amarar yin dambe kenan ai indai muka je malamin ya fad'i haka na tabbata ba wanda zai d'auke masa hankali sai Aisha" d'an zaro ido Hajiya Rabi tai ta na cewa.

"Au wai dama kin san ita ce amma ki ka 'kyaleta"?.

"A'a ba wai sani nayi ba kawai zarginta na ke daga yanayin maganarta da wasu abubuwan da take shi ya sa nake zargin ko ita d'in ce ba ta da aiki sai cewa mu ha'kura da Irfan mu rabu da shi Faridah ta samu wani ta aura tun da shi ya'ki fitowa" Mami na rufe baki Hajiya Rabi ta ce.

"Dalla rabu da ita 'yar ba'kin ciki ce na tabbata ku na 'kyaleshi sai ta shiga ta fita ta san 'kulalliyar da ta 'kulla Mujidat ta aureshi".

Zubura ta saka Mami tai ta na cewa.
"Kan bala'i ai kuwa ranar da anyi ya'kin da ba'a ta'ba yin irinsa ba a gidan nan dan wallahi basu isa na zuba musu ido ba in dai tsautsayi yasa su kai munafirci Irfan ya auri Mujidat ko ya saketa ko kuma na kasheta sai su za6i d'aya".

"To kuwa in dai kinsan haka ne sai ki tashi a tsaye kar ki huta kar ki runtsa har sai kin ga hankalinsa ya dawo kan 'yarki ya zo anyi magana sannan an saka lokacin biki an gwangwaje ta je gidansa matsayin matarsa a san nan ne zaki iya barcin ki har da munshari ba sauran wata fargaba sai kwasar daula dan na san idan ta aureshi ba 'karamin hutawa za ku yi ba wanda ya ra6u da ku ma sai ya ci arziki ya bar arziki a mazaunin arziki yanzu abun da za'ai kina jina"? Sake matsowa kusa da ita Mami tai ta na cewa.

"Eh ina jinki Hajiya Rabi yanzu yaushe za mu je gurin wancan malamin dan har na matsu na ganni ga ni gashi kawai na karanta masa matsala ta idan da ace so samu ne auren kar ya wuce sati uku ko wata d'aya saboda ma'kiya ko kuma wani sa6ani ya shigo ciki a fasa" ta fad'a ta na kallon Hajiya Rabi wacce ita ma ta kalleta sannan ta ci gaba "yanzu misali ace sai da aka saka rana yace ya fasa, wai da kuwa na shiga uku yadda na 'kwallafa raina akan yaron nan ace ya'ki ya aureta tabdijan guguwar da za ta tashi ni kad'ai nake hangota a raina".

Dariya Hajiya Rabi tai ta na kallonta ta ce "ai ba iya uku ba sai dai kice kin shiga tara irin wannan mahaukaciyar dukiya da ya tara kamar yayi ai ko nice na samu ya ke kula 'yata ko baya sonta sai nayi abun da zai sota gaskiya dole mu tashi tsaye mu ri'ke shi 'kam ya aure mana 'yarmu mu sake zama farin wata sha kallo mu sake yin suna duniya ta sake sanin mu tashi ki shirya Zulaihat mu tafi gurin Malamin da zafi ake dukan 'karfe" jikin Mami har rawa ya ke saboda murna ta mi'ke za ta shiga bedroom ta na cewa.

"Bari na fito yanzu kin san dole saina kira Alhaji na fad'a masa zan fita kuma sai na san 'karyar da zan yi kafin ya barni".

"Idan kin kirashi ki fad'a masa nice bana jin dad'i shine za ki je gidana ki gano ni" Hajiya Rabi ta fad'a ta na kashe mata ido murmushi Mami tai ta na cewa "gaskiya 'kawata kina kawo wuta kanki ful yake da caji hundred percent bari na fito mu tafi" ta fad'a ta na shigewa ciki ta bar Hajiya Rabi zaune ta na duba wayarta.

A ranar Hajiya Rabi ta raka Mami gurin Malamin kamar yadda ta ce

Please Login or Register in order to submit comment