You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa tai daga birni to amma idan zuwa garin su kai ba'ki ne me ya had'ata da zuwa nan har take kar6ar kaya tukuna ma uwar me take siya, shiru Faridah tai gabadaya ta shiga rud'ani can wata zuciyar tace Mata ba ki sani ba watakil 'yar gidan sarkin garin ce tun da gashi ta fita dabam.

Ita kad'ai dai sai tunanuka iri-iri ta ke har Irfan ya dawo ya zauna bai ko kalli in da take ba amma tsabar naci ko fara abin da yake bai yi ba ta ce.

"Irfan ka na son wannan yarinyar ne"? Bai amsa mata ba yai banza kawai idonsa ya na kan secreen d'in wayarsa, cizon lips d'inta tai cikin takaicin wannan shariyar ta sa wacce ba za ta iya jurewa ba a karo na biyu ta sake cewa "da gaske Irfan ka na son wannan yarinyar"? Jin tambayar da ta sake maimaita ma sa ya sa a wannan lokacin ya d'an d'ago a fisge ya kalleta sau d'aya ya mayar da kai cikin attitude ya ce.

"Stop looking me like that".

Da mamaki ta zaro ido waye ta na sake kafe shi da kallo cikin so ta ce "why"? Shiru ne ya biyo baya dan ba dalilin da zai sa tazo ta takurawa rayuwarsa bayan ita ba komai d'insa bace. Ajiyar zuciya ta sauke tare da d'an dafe kanta cike da tsakanin damuwa ji take kamar tai wa kanta fad'a ta share sa sai dai har abada ba za ta iya ba bata da 'karfin gwiwa akan Irfan in dai akan haka ne.

"Irfan dan Allah ka fad'a min ka na sonta"?.

"I did not".

Ya fad'a kai tsaye sannan ya d'ago ya sake kallonta sakamakon jin wata iriyar ajiyar zuciya da ta sauke kamar wacce ta dad'e ba ja numfashi ba. Ta6e baki yai wanda ya saka dimples d'insa duka 6aruka biyun su ka lotsa maimakon yadda ya caza mata kai matsayinta na mace ta d'aure fuska ta ja mai aji amma sai ta saki murmushi ta na cewa.

"Kai dai komai naka idan ka yi kyau ya ke maka shi ya sa bana gajiya da kallonka ko da za mu kwana a haka".

Iska ta saka ya furzar 'kasa-'kasa ya ce.
"Are you a Witch? Ban ce miki ki daina kallona ba Faridah idan dama abun da ya kawoki nan kenan ki tashi ki koma in da ki ka fito share kuma zan siya amma bana bu'katar ganinki anan" wani irin zaro ido ya saka tai ta na kallonsa da mamaki ta ce.
"Me ye yai zafi Irfan har za ka kirani da mayya"?.

"Ai ba mayya nace miki ba shugabar masharranta ta duniya cewa nai ke mayya ce"? Cikin takaici ta ce.

"To me ye bambanci"?.
Ta na rufe baki ta ji ya ce.

"Look Faridah" ya fad'a da 'karfi d'agowa tai taga yadda fuskarsa ta canza ba wani alamar sauki ya sake furta mata "stay within your limits" ya nuna mata alamar tai taka tsantsan da shi sannan ya na so ta fita a hanyarsa dan ba dalilin da zai sa tazo ta ri'ka takura masa ya na aikinsa lafiya 'kalau ba za ta zo ta hargitsa masa lissafi ba idan dan 5share d'in da mahaifinta ya saka ne take tunkaho zai siye ta koma in da ta fito, ta na zaune ya mi'ke ya fita ya barta a gurin sosai hakan yai mugun ba'kanta mata rai, tsabar yadda maganganun sa suka kashe mata jiki da ba'kin ciki kasa ko da kyakkyawan motsi tai ta ci gaba da zama a gurin kamar an dasata ta na kuma maimaita maganar da ya fad'a mata, lallai yau ta sake tabbatarwa kuma ta yarda da gaske Irfan ba ya sonta har yanzu da ace ya fara sonta to da zai nuna alama ko ya ya ne, numfashi me zafi ta fitar tare da mi'kewa ta d'auki handbag d'inta ta fita.............
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨
Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma writer jikar Muhammad ❤️.

Ina mi'ko gaisuwa gareki Mama.
🤲May Allah open the door of success for you and your families and neighbors Amin.

TYPING MON, JUL 27/26 07:19AM
📖✍️Yusrah Musa Abubakar ce.

••• °°°Juyin mulki°°° •••
••• °°°Juyin mulki°°° •••

Bismillahir Rahmanur Rahim.
In the name of Allah.
Allah the must high dose not sleep, Allah the must high is pure he accept only what is pure🌴🌿.
❤️We love our Nabi Saw he have no limit ya Rasulullah❤️.

16_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Nadiminah.

_____________ PAGE 16
A wanin ranar Faridah ba ta wani kuzari ko kad'an sannan kallo d'aya za kai mata ka fahimci ta na cikin matsananciyar damuwa hatta abinci kasa ci tayi zuwa wajen 'karfe biyar na yamma tai shirin tafiya gida sai dai har ta shiga motarta ta tada kawai shed'an ya fad'a mata wani sharri wanda ya saka ta taka burki tare da fitowa ta shiga cikin masana'antar ta nemo wani ma'aikaci guda d'aya wanda dama already sun san juna, d'aukarsa tai a mota su ka d'an yi nisa da gurin sannan tai parking ta fito ta jingina a jikin motar shi ma fitowa yai ya zo gabanta ya tsaya ya kalleta ya na cewa.

"Wai me ya ke faruwa ne, ina fata dai lafiya na ga kamar ranki a 6ace"? Fuskar Faridah har lokacin a tamke ta ke tana sake waigawa ta kalli garin ta ce "kwarai raina a 6ace ya ke Akil ka san dalilin da ya sa na kiraka nan"?.

"A'a ranki ya dad'e ki na bu'katar wani abu ne"? Ta jinjina kai a hankali ta ce "eh mai muhimmanci ma".

"Akan mai gida"? Ya sake tambayarta zuciyarsa na bugawa ta'be baki tai ta na cewa.

"A'a dalilinsa ne dai".

"Na fahimta kuma zan yi miki kowanne irin wannan abu ne amma ban da kisan kai sannan ban da ta'ba dukiyar al'umma".

"Duk ba wannan bane ni ka san abun da na ke so ka san wata yarinya a garin nan wacce Irfan ya ke d'an kula ta da nuna damuwa a kanta sannan ta na zuwa tai siyayya anan d'azu ma ta zo ka santa"? Kai ya d'aga.

"K'warai akwai na sha ganinta har a cikin nan wajen sosai ta ke zuwa duk bayan kwana biyu".

"Ok tom ka san me nake bu'kata so na ke ka shiga cikin 'kauyen nan ka binciko min labarinta da sunanta da sunan mahaifanta da kuma gidansu idan ka yi min wannan na samu na cika burina ni kuma zan biyaka kud'ad'e masu matu'kar yawa wanda za ka bar aiki a 'kar'kashin Irfan kai ma kaje ka kafa naka babbar masana'antar ka d'auki ma'aikata" shiru Akil yai cikin shakku da tsoro ya na kallonta daga baya ya ce.

"Amma bakya tsoron idan nai haka Mai gida ya gane nifa da wannan aikin nake tunkaho kuma da shi na ke ci nake sha har ma na baiwa wasu idan nai wani kuskuren aka koreni ya zan yi da me zan taimakawa mahaifana gaskiya bana son na rasa aikina ba tare da na samu tudun dafawa ba" ya 'karasa maganar ya na nuna mata a zahirin gaskiya ba za ta saka yai saki na dafe ba kar ya yarda akan d'an kud'in da za ta bashi yai asarar alkhairin da ya ke samu.

Ji ya yi tace "Akil ka fa san wacece ni kar ka damu zan ji da komai ka manta auren sa zan yi sai abun da nace masa zai yi ba za ka ta'ba rasa aikin ka ba idan ka rasa ma zan saka shi dole ya dawo da kai, kawai abin da nake so ka mayar da hankali kan abun da na sa ka ni bar min komai a hannu na" ta 'karasa maganar ta na bud'e motarta ta d'auko kud'i a d'aure ta mi'ko masa.

"Ka amshi wannan somin ta'bi ne na baka su ba wai dan aikin da za kai ba a'a wannan ra'ayi na ne" kar6a yai ya na waige-waige ganin ba kowa ya jinjina kai "shi ke nan Madam duk abun da ki ke so shi za'ai zan fara yi miki binciken daga yau d'in nan"

Murmushi ya saka tai cikin jin dad'i dama tasan duk zamewar da zai yi yuwa ta nuna masa money fala-fala yanzu zai amince ga shi kuwa tun ba'a je ko'ina ba har ya kamu kai ta jinjina ta na cewa "da kyau Akil jeka saina kiraka a waya cikin sati d'aya na ke bu'katar ka kammala komai za ka iya ai"?.

"Yadda ki ke so sai kin ji ni" ya na fad'in haka ya juya ya bar gurin tsaye Faridah tun ta na ganinsa har ya 6ace sannan tai ajiyar zuciya ta na bud'e murfin motar ta shiga ta zauna 'kafafunta suna waje wayarta ta d'auko ta kira Mami.

"Hello Mami ya gida"?.

Daga can 6angaren Mami tai murmushi ta na cewa.
"Lafiya 'kalau Faridah fatan kin sauka lafiya ya ku kai da wannan fitsararren yaron"? Da alamar tambaya Faridah ta ce "wa kenan Jafar"?.

"A'a Ina ruwana da Jafar ko har yanzu ki na kulashi"?.

Faridah ta girgiza kai da sauri sannan ta ta'be baki.
"Hum'um Allah ya sauwake ni da nake so ya fita a hanyata taya zan ri'ka kulashi".

"Yauwa 'yar albarka ashe dai ban yi asarar haihuwa ba na d'auka kin zama saki tumaki 6allo jakuna ne, shi Irfan d'in nake tambayarki ya ku kai da ki ka je"? D'an shiru tai ta na nazari ta san matu'kar ta fad'a mata gaskiyar yadda su kai d'azu da shi akwai matsala sannan Mami laifinta za ta gani shi ya sa ta za6i ta shirga mata 'karya.

"Komai yana tafiya daidai kamar yadda mu ka tsara Mami amma fa maganar gaskiya daga zuwana yau d'in nan har ta ci karo da gagarumar matsala saina tashi a tsaye idan har ina so da gaske Irfan ya zama nawa".

"Ban gane ba matsala kuma ta me har kin sa jikina yai sanyi murnata ta koma ciki me ya faru yau d'in ki yi min bayani".

"Humm Mami daga zuwana har na fahimci wani abu guda sannan akwai wata yarinya a 'kauyen nan wacce ta zo gurinsa d'azu naga ya nuna jin dad'i da zuwanta kuma ya sake mata fuska har magana su kai a gabana gashi abun da na lura ya d'auke ta tamkar 'kanwarshi har kaya ta ke d'auka a gurinsa daga baya ta kawo masa kud'in ina jin tsoron kar daga haka so ya shiga tsakaninsu domin an ce d'an hakkin da ka raina shi ke tsole ma ido" shiru Mami tai ta na sauraron Faridah har ta kai 'karshe sannan tai murmushi ta na cewa.

"Wallahi ba ta isa ba Faridah ita d'in banza bari ki ji na fad'a miki a yadda na ke ji a raina akan aurenki da Irfan koda a cikin 'yan matan birni 'ya'yan masu kud'i ya ga budurwa ya na so saina hallaka ta balle wata 'yar 'kauye ki kwantar da hankalinki Faridah ki na dani fa akan me za ki damu dan kawai kin ga wata yarinya".

"Abun ne da tsoro Mami".

"Ba wani tsoro ki kwantar da hankalinki kawai ki manta da batun wata yarinya ki fuskanci abun da ya kai ki ko duk 'yan matan 'kauyen ya ke kulawa ni nasan hanyar da zan bi da su kin gane"? Kai ta d'aga "eh na gane Mami shi ya sa ki ke burgeni duk mugun halin da mutum ya shiga in dai yai miki bayani za ki warware masa matsalarsa".

"Wannan kad'an daga cikin aikina kenan ki saka a ranki tamkar kin auri Irfan ne kwanan nan hakan zai faru".
"Yauwa na gode Mami sai kin sake jina zan kiraki zuwa safiya" ta na fad'in haka ta sauke wayar wata sabuwar daddad'ar iska ce ta ji tana shiga cikin zuciyarta duk yadda ranta ya kai ga 6aci d'azu yanzu komai ya washe, cikin 'kwarin gwiwa ta shiga motarta ta koma ma'aikatar da ma gida zata tafi amma tun da su kai waya da Mami ta ji kome zai ce mata nan gaba ta na daidai da shi.

A can gidansu Faridah kuwa bayan Mami ta gama waya da Faridah ta na zaune Aisha ta fito ita ma ta zauna ta na kallonta ta ce.
"Zulaihat idan ba za ki damu ba dama ina so zan fad'a miki wata magana" kallonta Mami tai ta san shishshigi za tai mata tun da taji tace haka shi ya sa a yangace ta ce "ok ina jin ki Hajiya Aisha ya akai"?.

"Ba wani abu bane dama magana ce akan lamarin Irfan da Faridah".

Sabon d'aurin kwali Mami ta sake ta na soke shi a gaban goshi ta ce.
"Umhum continue".

"Dama cewa zan yi me zai hana tun da Irfan d'in ya'ki mayar da hankalinsa ku rabu da shi tun da ga Jafar ta aureshi shi ma naga ba laifi ya na da hankali yaron kirki ne" wani irin kallo Mami tai mata ta na ta'be baki ta ce.
"Dama na san ba zai wuce kice haka ba wato mu rabu da Irfan saboda ba 'yarki ya ce zai aura ba ba'kin ciki ki ke mana da arzkin da za mu samu kenan"?.

Kai Aisha ta girgiza ta na cewa.
"A'a ba haka bane kar kiwa abun gurguwar fahimta kawai dai gani nai a rayuwa ba a dole sannan shi hankalinsa ba ya kanta ga shi Jafar ya...............

D'aga mata hannu Mami tai "kin ga Aisha da Allah kalleni nan ba ruwanki a lamarin nan na ki ido ne kawai daga yau kar na 'kara jin kin yi min irin wannan maganar in dai kina son zaman lafiya".

"Haka ne amma kamar naga nima abokiyar zamanki ce ina da hakkin da zan baki shawarar da ta dace bayan haka ina da dama ta ko"?.

"Eh kina da dama amma ta rufe baki na fad'a miki naki ido ne kawai idan isa da mallaka ki ke son nunawa sai dai akan 'yarki Mujidat amma ba Faridah ba baki da wani iko a kanta domin 'yata ce ni na haifeta ba ke ba kin gane"?.

"Na gane shi ke nan Allah ya kyauta amma ina jiye muku tsoron kar ku yi sake reshe kama ganye kun 'ki Jafar Irfan ya zame".

"Bakinki ya fad'i a 'kas Mujidat ce za tai sake reshe kama ganye amma ba Faridah ba ita kam harta 'kare rayuwarta cikin arziki da daula ta ke" jin abin da Mamin ta ce da yadda ta ga ta d'au zafi akan shawarar da ta bata ya sa bata sake cewa komai ba ta mi'ke ta bar mata falon Mami da ta raka bayanta da harara ta ce "ji min munafikar mace har da zuwa kina wani 'kar-'kar da ido wai kin zo fad'a min gaskiya taya zan yarda da ke bayan nasan ba 'kaunata ki ke ba, kuma ba 'kaunar 'yata ki ke ba, humm zan yi maganinki Allah ya sa tsautsayi yasa ki 'kara tara ta da irin wannan maganar sai nai miki mugun rashin mutuncin da har ki mutu ba za ki manta da ni ba".

A wunin haka Mami ta wuni ta na kai komo ta na maimaita maganganun da Aisha ta fad'a mata lallai ta yarda da gaske ba ta sonta dan da tana sonta ba za ta zo tana fad'a mata wannan abun da ta fad'a ba.
Da dare ma tana bedroom a kwance sakamakon ba'a d'akinta Daddyn Faridah ya ke ba sai bata fita gurin dinner ba tai zamanta har sai da shi yaga shirun ya yi yawa tun da indai ya dawo ko ba kwananta bane za ta fito tai masa sannu da dawowa amma yau shiru gashi ya na so za su yi magana da ita shi ya sa ya d'au waya ya kirata sai sannan ta fito ko zama ba tai ba ta ce.

"Alhaji lafiya kuwa na ji ka kirani a waya alhali muna gida d'aya"?.

"Eh lafiya ba wani abu bane zauna magana za mu yi" to ta ce jiki na 6ari ta samu a daddafe ta zauna saboda taga yanayinsa ba walwala ta san ba maganar dad'i bace sai dai tana ro'kon Allah ya sa ba akan Irfan ba ne....

Katse mata tunani yai.
"Am Zulaihat dama ina so na sameki tun ba yau ba rashin samun hutu ya hana nai hakan domin wannan matsalar cikin gida ce dole ba zan had'ata da aikina ba".

"To Alhaji Allah ya sa dai lafiya gabadaya jikina ya mutu".

"Eh lafiya dama magana ce akan Irfan da Faridah lokaci kullum 'kara tafiya ya ke rayuwa ta na gangarawa kwanaki su na 'karewa amma ba wani labari na fahimci shi ba aure ne a gabansa ba kasuwancinsa kawai shi yasha masa kai dan haka ki fad'awa Faridah ta tsayar da hankalinta akan Jafar su fahimci juna, da zarar sun daidaita ki sanar da ni zan saka lokacin bikinta".

A zabure Mami ta d'ora hannu aka muryarta kamar me shirin 'kwalla ihu ta ce "me kace Alhaji na shiga uku na lalace yau na fito rana shi ke nan tawa ta sameni yaron nan ya gama da rayuwata ya cuceni" ta da fad'a a susuce sannan ta sauke hannunta dake ka ta na kallonsa ta ce "Alhaji ban gane me ka ke nufi ba shawara kawai ka yanke kai da zuciyarka ko kuma ka sake zama da Alhaji Sulaiman d'in ne kun tattauna"?.

"K'warai wannan shi ne karo na babu adadi Amma sam Irfan ya'ki yarda da maganar auren su dalilin da ya sa nace ta mayar da hankalinta kan Jafar yau a gabana Alhaji Sulaiman ya kira Irfan ya sake tambayarsa batun auren bari ki ji 'karshen alawa 'kasa kansa tsaye ya ce shi ba zai auri Faridah ba kuma ya na fad'in haka ya kashe kiran" ya na rufe baki Mami ta dafe 'kirjin ta na salati

"La'ilaha ilallahu, shi ke nan naga ta kaina innalillahi wa inna ilaihi raji'un yau ta faru ta 'kare anyiwa me dami d'aya sata duk tsawon lokacin da mu ka d'auka muna jiran amsarsa amma shi ne yai mana wannan tozarcin"? Ta fad'a cikin 'kunar rai.

"Ba tozarci bane domin ni hakan da yai dad'i na ji kuma na gode masa" jin abin da yace ya saka Mami kallonsa da mamaki idonta ya fara juyewa kamar wacce take shirin suma ta ce.

"Me ya sa Alhaji, dama ba ka so ta aureshi ne"? Kai ya girgiza ya na cewa.
"A'a ina so man amma dai naji dad'i da ya fito fili ya fad'i gaskiyarsa bai yi shiru ba da wani ne bari zai yi ya aureta sannan ya san ba sonta ya ke ba zai ta azabtar da ita ya na wula'kanta ta ne kinga wannan shine anyi ba'ai ba ko da mu zo muna dana sani maganin kar ayi kar a soma"? Kai Mami ta girgiza ta na cewa.

"A'a wallahi a'a gaskiya Alhaji ni dai ban amince ba Faridah ba za ta rabu da Irfan ba kuma ba za auri Jafar ba".

"Shi ke nan tunda haka ki ka za6a ni nayi iya yina a matsayina na uba sauran ya rage naku tun da kince ba za ta auri Jafar ba saita nemo wani ko kuma dai ku san ya zaku yi wannan duk matsalarku ce Jafar yaro ne mai hankali amma tun da bai yiwa 'yarki ba zan bashi auren Mujidat tun da Allah ya sa nima ina da wata 'yar ba iya Faridan ba ce balle nasha kunya".

"Me ye abun shan kunya dan kawai Faridah ta'ki ta aureshi"?.

"Da kunya man tun da ni ne na turo shi ya nemi aureta ba wai ra'ayin kansa bane shima bai nuna gardama ba sai ita"? Ta'be baki Mami tai ta na cewa.

"Da alama shi d'in hakan ya burgeshi ne ita kuma bai yi mata ba bata sonsa ko ana so dole ne ta ce yai ha'kuri ya rabu da ita amma dan naci kullum sai ya zo".

"Bakin al'kalami ai ya riga ya bushe kuma mun gama magana in dai akan Jafar ne nace zan d'aura masa aure da Mujidat".

"Allah ya sanya alkhairi sai ka fad'awa Aisha ta fitar mana anko da wuri" Mami ta fad'a cikin gatse ta na dariya a ranta shi kam daga haka bai sake ce mata komai ba yai shiru kawai rabu da ita zai tuna mata wannan ranar amma sai ranar da duniya ta kaita ta barota kanta ya gwaro da bango sannan zai tuna mata da wannan maganar da su kai, a halin yanzu ba zaice ya cire hannunsa a lamarin auren Faridah ba amma ya zuba mata ido ta samo mijin aure da kanta duk abun da ya biyo baya ba ruwansa tun da shi yana duba abun da ya dace a rayuwarta ne shi ya sa ya za6a mata Jafar d'in amma tun da ta 'ki shi ke nan an wuce gurin.................

Tun a ranar yai magana da Aisha akan shawarar da ya yanke cewa zai baiwa Jafar auren Mujidat ita ma kuma ta amince sakamakon tunawa da tai Mami ta ta'ba ce mata idan ta ji haushin abun da Faridah tai wa Jafar ta bashi auren Mujidat.

Washe gari Mujidat ta na d'akinta ita kad'ai ta kunna kallo a wayarta Aisha ta shiga ta na cewa "Mujidat kashe kallon nan ki saurare ni ina so za mu yi magana" kashewa ta tattara hankalinta gabadaya ta na cewa.

"Allah ya sa dai lafiya har na ji jikina ya yi sanyi" d'an murmushi Aisha tai ta na cewa "na fad'a miki lafiya ba wani abu bane dama magana ce akan Jafar kin san cewa ya na son Faridah ko? Kai ta d'aga.

"Eh na sani".

"Yauwa to maganar gaskiya Faridah ta'ki tsayar da hankalinta akan sa sannan ta ce Irfan take so shi za ta aura to Abbanki ya na jin kunya da nauyin Jafar shi ne ya ce na fad'a miki idan ki na sonsa zai zo ku fahimci juna daga baya sai a san yadda za'ai amma dan Allah Mujidat kar ki tulawa Alhaji 'kasa a ido kamar yadda Faridah tai masa ko da a ranki kina jin cewa bakya son Jafar ki yi ha'kuri ki aureshi wata rana za ki ji son nasa".

D'an shiru Mujidat tai ta na nazari daga baya ta d'ago ta kalli Aisha sannan d'aga ta na cewa "shi ke nan Ummi zan yi yadda ki ka ce amma ya zan yi da Fauzan"? Da alamar tambaya ta ce.

"Wa ye Fauzan kuma"?.

"Wani classmate d'ina ne amma ya girmeni sosai kuma sona ya ke ya fad'a min ma tun ba yau ba".

"Ina ba cewa yai zai turo mahaifansa ba"?.

"Eh bai fad'a ba kuma bai ta'ba zuwa nan gidan ba sai dai idan mun had'u a school".

"Ok to ai ba wata matsala idan ya furta sai ki fad'a masa yai ha'kuri akwai wanda za ki aura kafin ya furta ma ki fad'a masa akwai wanda za ki aura yai ha'kuri".

"To Ummi zan yi hakan".

"Masha Allah Mujidat Allah yai miki albarka Ubangiji ya sa aurenki da Jafar shi ne mafi alkhairi a gareki fiye da auren kowanne namiji".

"Amin Ummi na gode" ta fad'a ta na d'auko wayar ta ci gaba da abun da take yi Aisha kuma ta mi'ke ta fita cikin 'kwarin gwiwa dama ta na da tabbaci a kan Mujidat ba za tai musu ba ko me aka ce mata za tace to kuma ta na farin ciki da hakan shi ya sa bata ji ko d'ar ba lokacin da ta zo fad'a mata.
📖✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Start your day beautifully with fajr prayer📿 and Quran recitation🌹 ya Allah make us among those who never miss Salah Amin🤲.

JUYIN MULKI
By
YMA WRITER
Yusrah Musa Abubakar Jigawa.
New world🌎 Jigawa venture's🌴.
____Y_________
______________M_________
___________________________A______

✍️2026.
©Yusrah Musa Abubakar.

17_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Shakirnah.

_______________PAGE 17
Kamar yadda Faridah ta umarci Akil cewa ya shiga cikin 'kauyen ya binciko mata labari haka ya aikata ya na yawo ya dajin gari ya zo wucewa ta wata hanya ya had'u da wani mutum monomi ya dawo daga gona ya na kwance a 'kar'kashin bishiyar mangoro ya na barcin gajiya da fartanyarsa a gefensa Akil ya du'ka a kusa da shi ya na d'an ta'ba shi ya ce "assalamu alaikum barka ka farka Malam monomi ka tashi haka" ganin bai motsa ba ya sake girgiza shi a firgice mutumin ya farka tare ta

Please Login or Register in order to submit comment