You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin ga kaji ma guda goma ya turo wani yaronsa ya kawo mana ga su can a keji wanda za'a yanka idan za su zo".

Kai Hannatu ta d'aga.
"To kuma kayan abinci fa inace gobe za su zo"?.

"Eh gobe ne ga buhun shinkafa can ma da jarkar mai da kayan maggi da abubuwa da yawa wani ma ban ta'ba ganin irinsu ba sai dai ke ki d'an dudduba tun da kuna zuwa birni dangin mijinki watakil kin san wasu abubuwan" jin abun da Umman ta ce yasa Hannatu ta mi'ke ta na cewa.

"Bari na d'auko mu duba" ta fad'a ta na mi'kewa ta fita suna 'kofar d'akin ta d'auko sannan ta dawo ta zauna ta fara duddubawa ta ga kayan itama wasu ba ta sani ba amma sakamakon mijinta ya na da 'yan uwa a birnin su na d'an zuwa in ana biki ta san wad'ansu kayayyakin daga ciki kuma ana amfani da su a gabanta, sauke ajiyar zuciya tai ta na cewa.

"Wannan ai kayan fried rice ne ba abun da za'a bu'kata tun da komai akwai" sai kuma ta d'ago ta kalli Umma ta na cewa "yanzu yadda za'ai idan na koma gida zan turo a kama kajin akaiwa Sadi me suya na bakin tasha sai a biyashi ya yanka ya gyara su saina sulala gobe idan na tashi saina taho mu yi aikin a nan bari na tafi yanzu saina aiko a d'ebi kajin gara mu yi komai da wuri ya kasance ace lokacin da za su zo mun gama komai sai dai mu jira zuwansu".

"To Hannatu Allah yai miki albarka Allah ya kai mu goben cikin masu rai"

"Amin Umma Ina Zaran take tun da nazo ban ganta ba".

"Zarah ta je gidansu Sabuwa ne zata kar6o ko littafinta ne a gurin 'kawarta kuma shi ne ba ta dawo ba har yanzu kin san idan ka damu zance sai a hankali".

Hijab d'inta Hannatu ta d'auka ta na cewa.
"To idan ta dawo ki fad'a mata ta sameni a gida mu d'an yi aikin kajin tare saboda ni zan yi abincin dare kar lokaci ya 'kure".

"To zan fad'a mata saita shigo".

Bayan fitar Hannatu Umma ta samu ta d'an dogara da sanda ta fito waje ta zauna.
Ba ta dad'e da zama ba Hamah da ke zaune ita ma acan 'kofar d'akinta ta ta'be baki ta na cewa.

"Humm muna nan goben muna zuba ido zan ga shegun da za su zo kawo akwati gidan nan ku girka furendire (fried rice😂) d'in za ku cinye kayanku ko kuma ku rabawa almajirai sadaka dan ba zan bari su ci ko cokali d'aya ba zan d'aga musu hankali kuma za ki gani" kallonta Umma tai ta na girgiza kai ta ce.

"Ai ke Hamah tun ba yau ba na fahimci kin samu matsala ba zan biyeki ba sai dai ki yita bada'kalarki ke kad'ai amma ni dai na daina kulaki kome za ki ce min" dariya Hamah tai ta na cewa.

"Wayyo Allah dad'i kashe ni, za ki kula ni ne bari Allah ya kai mu gobe da rai za ki ga abun da zan yi muku ni kad'ai na san me na shirya a raina".

"Ba'kar aniyarki ta bi ki" Umma ta fad'a ta na nunata.

"ku za ta biyo saina saka ku kuka da idanunku gobe in dai ina gidan nan yadda ba'kin za su zo da akwatin haka za su koma da shi Allah ya sa 'kwallo d'aya ne".

"Wannan kuma ke kika sani in a ba'kar leda gari yai zafi suka kawo ma ni bana ba'kin ciki fatana Zarah ta zauna lafiya da mijinta kawai.

"Ba wani nan ji 'karyar banza a zilamar taki ce ki ke so a kawo miki lefe a ba'kar leda ai dama kowa yaji labarin wannan auren sai ya tsine muku ke da 'yarki saboda an san ba son Allah bane asiri ku kai masa idan ba haka ba yana Mai kud'i d'an birni d'an gayu taya zai yarda da hankalinsa ya auri 'yar 'kauye ko a tatsuniyar gizo da 'ko'ki ban ta'ba ji ba".

"Yau ai gashi kin gani bama ji ba sai ki sake babbar d'amara".

"Ba sai kin fad'a ba dama d'amara na yita jiran gobe kawai nake ba'ki su zo nai muku muguwar ta6argaza na fasa 'kwan na tarwatsa lamarin".

"Sai dai ki tarwatse amma ba ki isa ki tarwatsa lamarin ba komai za ki fad'a sai dai ya koma kanki".

"Ba abun da zai dawo kaina a kanki zai zauna kuma za ki gani me ru6a66iyar 'kafa Allah ya sa tai ruwa ta ru6e ta lalace ace ba za ta warke ba sai dai a yanke".

"Wannan kuma ba ki isa ba in sha Allahu bakinki ba zai kamani ba domin ba kece me bada lafiya ba Allah ne idan ya so saina warke na taka 'kasa da 'kafafuna nayi tafiya kamar kowa".

"Ahaf dole ki yi fatan warkewa ki taka da 'kafafunki man tun da 'yarki za tai aure a gidan Naira zaki koma can ki tare ki ci me kyau ki kwanta a me kyau Allah ya sauwake mace mai son zuciya irinki anyi wayon banza" ta fad'a har da tsartar da yawu baki Umma ta bud'a za tai magana Zarah tai sallama shi ya sa tai shiru kawai bayan ta 'karaso ta kalleta ta na cewa.

"Zarah yanzu kuwa Hannatu ta bar gidan nan ta ce idan kin dawo na fad'a miki ki bita za ki d'an tayata ayyukan kayan nan da aka kawo" kai Zarah ta d'aga ta na aje abun da ke hannunta a kusa da Umma ta juya ta fita.
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR

Thanks for your supports🔥
Yma writer Yusrah Ms Abubakar.

✍️2026
©Yusrah Musa Abubakar
Jigawa state Dutse.

🍇JUYIN MULKI🍇

Ina gaisuwa gareku 'yan uwana rabin jiki da kuma 'yan Annuri writer's.
Ku ne masu tambarin home of hospitality and harmony gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya.

31_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun wa barik ala Sayyidina Muhammadun Sayyidi Ahlil jannati.

______P___A___G___E 31
Washe gari tun asuba Hannatu ta zo su hau aiki iya su biyu Hamah da Aliyah su na gefe suna kallonsu suna zaginsu 'kasa-'kasa su na harare-harare.
Zarah da ke zaune ta d'ago ta na cewa.
"Wai Aunty Hannatu ya ake amfani da wannan ne"? Ta fad'a ta na nuna radishes da peas 'yar dariya Hannatu tai ta na cewa "kin ga tun da baki san wad'annan d'in ba ki je ki tafasa shinkafan ni bari na zo na kula da nan d'in amma ki tsaya a kusa ki ri'ka kula da duk abin da na ke yi saboda kin ga ke ba rayuwar 'kauye za ki ba nan gaba babban birni Allah ya d'aukaka ki" d'an numfashi Zarah ta sauke ba ta ce komai ba ta tsaya ta na kallon yadda Hannatu ta ke har su ka gama.

"Umma mun gama komai gashi nan na juyashi a kuloli na sai sauran idan Zarah ta d'iba muku ta sakawa baban mu sai ta zubawa Hamah ni idan na dawo naci ko yaya ne bari na je gida na d'an yi abun da ya kamata kuma nai wanka kafin ba'kin su iso" kai Umma ta d'aga ta na cewa.

"To Hannatu Allah yai miki albarka sai kin dawo nima ki saka Zarah ta kai min ruwan wanka band'aki na fito nai wanka kafin ku tafi".

"To Umma bari na kai miki da kaina Zarah ta yi gaba" ta fad'a ta na fita ta d'auki baho ta cika mata shi da ruwa ta kai mata sannan ta zo ta d'auki hijab d'inta ta bi bayan Zarah.

Su na can basu san ba'ki sun sauka ba sakamakon su na shigowa gidan da sallama Hamah ta d'auko manyan tabarmi ta ri'ka shimfid'a musu cike da gulma kamar gaske daidai Umma ta fito ta nai musu sannu da zuwa kafin ta samu yaron daza ra aika ba zato ta ji Hamah ta ce.

"Sannunku da zuwa bayin Allah ashe kuna tafe nifa da naji Binta ta kira yaron nan har da'ki sun yi magana jiya na d'auka shi ke nan ya ha'kura ashe halin d'an yau watakil ma bai fad'a muku cewa kar ku zo ba ko"?.

Jin abun da tace ya sa Umma kallonta cike da mamaki jin sharrin da tai mata da yaushe Irfan ya zo gidan jiya har su kai magana ko kayan abincin nan Amar ya aiko amma ga shi tace wai har magana su kai........

Katse tunanin da take ta yi jin d'aya daga cikin ba'kin ta ce.
"Wani abu ne ya faru ko auren aka fasa ba shi"?.

Da sauri Hamah ta d'aga kai ta na kallon yadda Umma ta zuba mata ido kamar za tai dariya ta ce.
"Eh d'an uwan hakan ne saboda har gida akai kiransa dan kar a 'kwareshi aka fad'a masa ciki ne da ita yarinyar da ya ke so d'in amma taurin kai yasa ya barku ku za sha wahalar zuwa ba Dan yanzu Allah ya rufa mana asiri anyi mana titi ba da ciwon jiki ma ya isheku" ta na rufe baki duk su hud'u su ka zaro ido a firgice Hajiya Safiyyah 'kanwar Momy ta ce.

"Mun shiga uku ciki kuma"?.

Kai Hamah ta jinjina da 'karfi ta ce.
"K'warai ciki na haihuwa ma kusan watansa d'aya da 'yan kwanaki ran nan dana rakata asibiti haka likita ya ce ashe shi ya d'auka 'karya ne da aka ce yai ha'kuri shine ya je ya turoku to 'yar iska ce wacce ya ke so aura kwana ta ke a d'akin samari kuma ba ta da wata kunya da rana ido na ganin ido sai ta shiga d'akin gardi su dad'e har a manta da su sannan ta fito irin wannan yarinyar wa zai so had'a iri da ita, maganar gaskiya ba zan 6oye muku ba ya zama dole in fad'a sai dai ku yi ha'kuri ban san a yadda za ku d'au maganar ba".

Jikin Umma na rawa ta kalli Hamah ta na cewa.
"Hamah ki ri'ka jin tsoron Allah za ki mutu ki tarar da abin da ki ka shuka ki kiyayi shigarki k'abari da yaushe ki ka raka Zarah asibiti har likita ya ce ta na da ciki uban waye ya fad'a miki ta na shiga d'akin samari"? Kallonta Hamah tai ta na danne dariyarta ta ce.

"Laaaah ji munafircin banza au ba zan fad'i gaskiya ba dan kin ro'keni akan na rufa miki asiri za ki bani dubu goma na 'kara jari idan sun zo kar na fad'a musu Zarah ta na da cikin shege kin ce nai shiru da bakina a yi musu rufin baki ta aureshi da ciki dan ku samu gadon dukiya" sai kuma ta fasa kukan 'karya ta na rufe fuska har da shesshe'ka ta ce "to wallahi ba zan iya ba, ba za'ai wannan muguntar da ni ba ina tsoron Allah ya kamani taya zan bari a yi cuta dani akan wasu shegun kud'i da ba su yanke min talauci ba wayyo Allah kaico Zarah kin cucemu kin ci amanar ubanki kin tozarta mu a gari wannan abin kunya har ina ku yi ha'kuri bayin Allah kunya ta sa na kasa had'a ido da ku ban san me zance muku ba sai dai Allah ya huci zuciyarku kuma Allah ya mayar da ku gida lafiya sannan Allah ya saka muku wahalar da ku kai na san duk laifin Zarah ne........................

Muryar Umma cikin tsawa ta ce
"Hamah ki iya bakinki akan 'yata ki dawo cikin hankalinki ki san me ki ke fad'a kuma ki bar mummunan furuci akan Zarah Allah yai mata tsari daga abun da ki ke siffata ta da shi bata kasance tayi watsi da tarbiyyar da muka bata ba wannan sharrin naki sai dai ya koma kanki azzalumar mace kawai" ta 'karasa maganar ranta a 6ace ta na kallonsu ta ce "dan Allah ku yi ha'kuri ku rabu da ita wallahi duk abun da fad'a 'karya ta ke sharri tai mata Zarah ba fasi'ka ba ce".

Wani irin kallo Hamah tai mata ta na cewa.
"Sharri nai mata au abun da zaki fad'a kenan dan na'ki goyon bayan ayi zalunci dani ke dai Binta bakya tsoron Allah harda wani sharri nai mata humm ai ido ba mudu ba amma ya san kima sun san da hankalina babbar mace kamar ni na zauna inai musu 'karya me ye ribata ke dai kawai ki rabu da su, su tafi ki 'karata da borin kunyarki".

Ganin da Umma tai masifa Hamah ta ke son d'ora mata a fasa auren kamar yadda ta fad'a ya sa ta rabu da ita ta mayar da hankalinta kansu ta na cewa.
"Dan Allah ku rabu da ita halin sharri ne kawai duk abun da za ta fad'a ku shareta".

Hajiya Safiyyah da farin ciki ya cika zuciyarta jin abun da Hamah ta ce ta san matu'kar su ka koma da kayan nan to rabon Batula ne tun da ya ce baya son Faridah shi ya sa ta kalli Umma fuska ba rahma cikin wula'kanci ta ce.
"Ta ya zamu shareta bayan mun ji komai dama haka 'yar taki ta ke watsattsiya ba dan wannan matar ta tona mata asiri ba haka za ki mana shigo-shigo ba zurfi ki saka ta auri d'an mu bayan biki sai ace ba jinya ya mutu kin sa ta kashe shi dan ku samu gado ko, to Allah ya bankad'a asirin da ku ke rufewa gara da haka ta faru za mu koma da kaya mu je mu fad'awa mahaifiyarsa komai" Hajiya Safiyyah tai maganar ta naiwa Binta wani kallo dama da biyu an jefi biri da rani ba dan ranta ya so ba ta taho kawo lefen nan dan ba yadda za tai ne kuma kar ace ba'kin ciki ta ke dan Irfan ya 'ki auren 'yarta to amma yanzu tun da haka ta faru dole ta tashi a tsaye ta hana yai wannan auren tun da dama Momy ba so take ba saita zugata ya auri Batula kawai.

"Dan Allah ku yi ha'kuri ku zauna mu yi magana ta fahimta".

"Ke kin ga ki rufa mana baki dama aure a hannun mu yake kuma tun da haka ta faru Irfan ya fasa auren 'yarki kalleni da kyau ki ganni sunana Hajiya Safiyyah kuma ni 'kanwar mahaifiyarsa ce uwa d'aya uba d'aya kin ga duk dokar da na ka fa masa dole ya bita ko yana so ko baya so to na soke wannan auren kin gane Hajiya Hauwa ku tashi mu tafi" ta fad'a ta na mi'kewa ta fara jan akwatuna ta na kaiwa waje.

Wata iriyar gud'a Hamah ta sake lokacin da ta ji tashin motarsu.
"Ayuriyuriiiiiiiiii duniya ta yi min dad'i dama me nace miki kwanan baya na fad'a miki in dai ina raye ba zan bari Zarah tai aure ba kuma jiya ma na fad'a miki ashe kin d'auka wasa ne to yanzu dana wargaza wannan maganar fad'a min taya za'ai su sake yarda su dawo garin nan kawo wata uwa akwati ko shi sirfanin ko irfani me ye sunan na shi, ko shi aka fad'awa ta na da ciki kuma ta na kwana a d'akin samari na san ba zai aureta ba".

⚜️⚜️⚜️⚜️
Momy ta na zaune a falo taga su Hajiya Safiyyah sai shigowa su ke da kaya sosai mamaki ya kamata.

"A'a Safiyyah ya haka kuma ya na ganku kun dawo da kaya"?.

Zama Hajiya Safiyyah tai ta na cire mayafi ta cire d'an kwali ta na sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Humm Aunty kedai bari kawai in ana sallah ba'a magana abu ne fa ya 6aci kin ganmu mun dawo miki da kaya dai jiki a mace Hajiya Halima ita dama muna zuwa kwanar gidanta ta ce a sauketa anan ba za ta iya dawowa ta fuskance ki da wannan magana ba jin haka ya sa ita ma Hajiya Hauwa'u ta ce mu bi a sauketa kin ganni daga ni sai 'kawarki Hajiya Saudah mu ne ya zama dole mu dawo miki da kaya su da yake dangin miji ne ai kin ga sun zame kowa ta tafi gidanta ba ruwansu da su dawo inda ki ke balle su yi miki bayani saboda ba matsalarsu ba ce".

"Me ya faru ne Safiyyah ni fa ban fahimci komai ba"? Momy ta tambaya da mamaki sosai a fuskarta duk zatonta ma ko iyayen Zarah ne su ka 'ki kar6ar kayan sai kuma ta ji Hajiya Safiyyah ta ce "humm kefa Allah ne ya rufa miki asiri ashe shigo-shigo ba zurfi su kai masa muna kallonsu 'yan 'kauye ashe yarinyar tijararriya ce kuma tantiriya ce a cikin garin ba ta san komai ba sai yawo a gari da kwana a d'akin samari 'karshen magana yau da muka je a gaban kowa asirinta ya tonu harda ciki ta ke da shi" wani irin dafe 'kirji Momy tai jikinta ya na rawa ta ce.

"Ciki kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un 'yar iska Irfan ya ke son aurowa a cikin gidan nan ya kawo mana ita matsayin suruka, ciki dai"? Baki Hajiya Safiyyah ta ta6e ta na cewa.

"Ciki dai, Allah ya sa baza a 'ka'kaba muku jikan da ba naku ba tun da sun ce yaron ciki ne bai fi wata d'aya ba misali idan an sa bikin wata d'aya kinga cikin ya samu wata biyu da tazo wata bakwai ta na cika ta haihu sai ace bakwaini ne tun da dama ana irin haka" sai kuma ta tsaya ta ja numfashi sannan ta ci gaba "hummm tabd'ijan kin ga da magana ba ta fito fili ba shi ke nan ana gama biki sai dai ku ganta da ciki kin ga sai ace tana zuwa ta samu alhali ba jininku ba ne, ki tuna Aunty a halin yanzu fa tana 'kauye ta ke wannan d'abi'ar kuma inaga ya d'aukota ta dawo cikin babbar birni watakil rayuwar club da hotel za ta koma ta ri'ka shan giya ta na kawo masa mazan banza har gida tun da yana yawan tafiye-tafiye wallahi yadda ba zaman nan ya ke ba yana barin gari za ta fara kiran mazan kala-kala su na zuwa in da ta ke".

Shiru Momy tai kanta na juyawa ta kasa magana Hajiya Safiyyah ganin ta samu dama ya sa taci gaba.
"Dan Allah Aunty ki san yadda za ki, ki hanashi auren yarinyar nan, ga 'yan mata nan wayayyu zankad'a-zankad'a a gari ya rasa wacce tai masa sai ya tafi wani tsinannan gari ya d'auko masifa ya kawowa mutane idan kin bincika ma maybe 'yar mayu ce yawan zuwa garin da ya ke ta lashe masa kurwa ya daina ganin kowacce budurwa sai ita".

Kai Momy ta jinjina ta na cewa.
"Da na ha'kura na d'auki 'kaddara ya aureta amma yanzu ko mutuwa zai yi sai dai ya mutu da na bari ya auri wancan yarinyar bai isa ya aureta ba har abada".

"Yauwa Aunty ya kamata ki hanashi dan Allah idan komai ya lafa zan turo Batula ta zo tai miki kwana biyu idan ya ga dama ya bari sun d'an tattauna shi ke nan sai mu san abun yi" tai magana ta na kallon yanayin Momy ta na kuma jiran amsarta ji tai ta ce.

"Idan ma ya'ki amincewa ni na amince dole ya auri Batula ita ce ta dace da shi tun da 'yar uwarsa ce gara ya aureta ko ba ya sonta da ya auro mana abin da yafi 'karfinmu".

"Gaskiya dai abun da ya kamata kenan" ta fad'a ta na mi'kewa ta ce "bari na tafi Aunty Allah ya rufa asiri sai na ji kiranki".

"To Safiyyah ki gaida gida na gode" Momy ta fad'a ta na mi'kewa tai mata rakiya har harabar gida ta saka driver ya kaita sannan ta dawo ciki cike da d'imuwar abun da su ka fad'a mata.
✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

1_YANZU FA AKA FARA🔥 LABARI YA D'AU ZAFI.

2_ME KU KE TUNANIN ZAI FARU?

3_IRFAN ZAI YARDA DA MAGANAR DA HAMAH TA FAD'A?

4_TA YA ZARAH ZATA WANKE A GURIN SU MOMY?

5_DOMIN JIN YADDA LABARIN ZAI KASANCE HAR ZUWA K'ARSHE KU ZAMA CIKIN SHIRI.

Mai son complete d'insa har 'karshe ya tuntu6e ni ta WhatsApp number na domin samunsa har 'karshe akan Naira d'ari hud'u.

#400
2410673902
Yusrah Musa Zenith Bank


Sannan ga masu bu'katar siyan wasu littafan nawa su ma ga nasu farashin👇.
Minister Ashraf 300
Royalty 500
Safreeyyah 400
Me kamar sarki 500
Zuciyar Aliyu ce 700
Kowacce 'kwarya 700.

Sannan akwai sabon novel d'ina da zai fito kwanan nan in sha Allahu shi ma dai akan farashi mai sauki kamar yadda na saba.
❤️MU'AZZAM❤️
Love story.

✍️Yusrah Musa Abubakar
Jigawa state Yma writer.

YMA WRITER YUSRAH MUSA
📙📘📗📖📙📘📗📖📙📘📗📖📙📘
♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️
⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment