You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za mu samu to in sha Allahu sai na yi arziki a jikinki" kai Zarah ta girgiza a hankali ta sunkuya ta cire takalminta 'kafarta ta saka a bayan motar da d'aurin kayanta sannan ta shiga Faridah ta rufe tare da jan tsaki.

Hamah dake tsaye ta na hararar Zarah ta ce.
"Ai dama na fad'a miki bulkuma ce ba ta san komai ba sai da'ki'kanci" sabon tsaki Faridah ta ja cikin takaici ta ce "zan yi maganinta ne da ni ta ke wasan" ta bud'e murfin motar ta shiga su ka bar gurin. A kunnen Umma duk abun da ya ke faruwa wani irin 'kuna da turiri ne ya ke ratsa kowanne 6angare na zuciyarta ba ta san lokacin da ta fasa kuka mai mugun 'karfi ba wanda ta saka su Hamah shigowa da gudu su na dariya su ka shiga d'akin cikin mugunta Hamah taje kanta har tana taka mata 'kafa ta ce.

"Au nan d'in kuka ki ke saboda Fatima ta yi nisa da ke? Ai kuwa za ki dad'e ki na yi har sai hawayenki sun 'kare idonki ya tsiyaye Zarah ba ta dawo in da ki ke ba in sha Allahu ba za ku sake ido biyu ba har abada ke da ita ba zan ta'ba bari ta dawo garin nan ba kuma za ki gani sannan idan Ubaliyo ya dawo kar ki kuskura tsautsayi ya sa naji kin ambaci sunana ki ce itace tai sha'awar bin ta tana ji an zo ana cikiyar masu neman aiki ta bi ta kin ji"? Ta fad'a ta na sake sakin dariya sannan ta juya ta fita ta na wa'ka duniya tata lahira ko a gidan haya.

Su na tafe a hanya Faridah ta saka kid'a ta 'kure volume yadda sautin ya ke tashi har dukan zuciyar Zarah ya ke sosai ta runtse ido ta na sauraren yadda Faridah ke bin wa'kar cikin nishad'i can ta ji motar ta tsaya kuma ta kashe sautin bud'e ido tai ta gansu a wani guri da ba ta san ko'ina bane amma dai ba zai wuce gidan abinci ba ko mutum bai yi karatu ba zai gane hakan sakamakon manyan kalandun kalolin abinci da ke manne a jikin bangon ginin tabbas ta yarda ta shigo birni yanzu. An dad'e sosai sannan Faridah ta fito ta bud'e motar ta shiga a lokacin har anyi magriba kai tsaye wani babban bariki ta nufa a kofar gate d'in gidan tai parking tare da fitowa ta je ta bud'e Zarah wacce wahala ta saka a wannan lokacin jikinta ya gama yin laushi lis da'kyar ta fito ta na d'ingishi yadda 'kafafunta su kai taruwar jini gaba ta wuce ita kuma Zarah ta bi ta a baya har 'kofar gate d'in tsayawa su kai Faridah ta fara 'kwan'kwasawa kamar minti biyar sannan aka bud'e 'kofar wata 'yar barikin ta le'ko kanta a taje kamar aljana tare da kallonsu ta ce.

"Lafiya"?.

Kai Faridah ta d'aga.
"Eh lafiya na zo kama da'ki ne fatan akwai"?.

"Gaskiya ba da'ki ko'ina da mutane domin d'azun nan wani mutum ya kama d'akin 'karshe sai dai shi kad'ai ne idan za ku iya zama tare da shi ba damuwa" ta'be baki Faridah tai ta na cewa.

"No ba mu biyu bane ita kad'ai ce za ta kwana anan kuma itan ma zuwa safiya zan dawo na d'auketa ga kud'in kwanan da za tai" ta 'karasa maganar ta na bud'e handbag d'inta ta d'auko kud'i ta lissafa duba goma ta mi'ka mata ba tare da ta sake koda kallon in da Zarah ta ke ba ta juya ta bud'e bayan motar ta d'auko takalmin Zaran da 'kullin kayanta ta cullo mata su a fuska ta nai mata wani irin kallo kafin ta shiga motarta ta bar gurin.

"Shigo ciki".

Ta ji saukar muryar 'yar barikin goge hawayen fuskarta ta sunkuya ta d'auki kayanta ta saka takalminta su ka shiga ciki fal gidan ya ke cike da mutane maza da mata 'kungiya-'kungiya kowa da harkar da ta sha masa kai da'ki su ka shiga wacce ke d'akin ce a zaune ta kallesu ta na cewa.

"Ke leema wannan kuma daga ina"?.

Zama tai ta na cewa.
"Daga ban sani ba fita nai a sa'a wata budurwa ta kawota a mota wai kwana d'aya za tai gobe da safe za ta dawo ta d'auketa ta bada dubu goma kud'in kwananta shi ya sa na shigo da ita nan ta kwana tare da mu, mu ri'ke kud'in kawai" sannan ta juya 6angaren Zarah da ke tsaye ta nuna mata alamar cewa ta zauna zama tai cikin tsananin damuwa da dagulewar lissafi kawai tai shiru tana tunanin halin da Umma ta ke tasan ta na can hankalinta a tashe ta ci abinci ko ba ta ci ba tana zaune ko ta kwanta ta yi barci ko idonta biyu wad'annan tunanukan su sukai ta damun zuciyarta ko kad'an ba ta jin duk hayaniyar da su Leema su ke yi. Sun dad'e a haka daga baya ta sauke numfashi ta na kallonsu cikin sanyin murya ta ce.

"Dan Allah ku taimaka min da ruwa zan yi sallah" da hannu Leema da ke waya ta nuna mata toilet d'in da ke d'akin mi'kewa tai ta shiga amma ba ta ga ruwa ba ta dad'e tsaye ta na ta kalle-kalle ko za ta ga inda ruwan ya ke amma ba ta gani ba dole ta juya ta fita tare da ra6ewa da'kyar ta ce.

"Ban ga ruwan ba".

Ta na rufe baki cikin tsawa Safnah ta harareta ta na cewa "kar Allah ya sa ki gani 'yar ba'kauyiya daga ina ki ka fito da alama ba ki san komai ba sai..............

Rufe mata baki Leema tai ta na cewa "kai dan Allah ki bari mana tun da ki ka ji ta tambaya ba ta sani d'in ba ne" sannan ta mayar da hankalinta kan Zarah wacce gabadaya ta gama tsorata ta ce "kin ga ki koma ciki za ki ga d'an wani abu me kai sai ki d'aga abun sama kad'an ki gota ruwa zai fito" jin abin da tace ya sa Zarah juyawa ta koma ciki ta duba kwatancen da tai mata sannan tai yadda ta ce ruwa ya fito tai alwalar ta fito ta kar6i sallaya tai sallolin da ba tai ba bayan ta idar tai addu'a, yanzu kuma abun da yake damunta yunwa ce sannan ta na tsoron sake tambayarsu wani abu kar wannan Safnan ta sake daka mata wata tsawar sai kawai ta ha'kura ta kwanta haka akan sallayar sai dai duk wata hira da su ke ta na jinsu sakamakon ba dare ne yai sosai ba.

Faridah kam cike da farin ciki ta koma gida bayan ta yi wanka ta je gurin Mami wacce ganinta ya sa ta gyara zama ta na cewa.
"Kin dawo ashe ya ku kai da shi fatan dai akwai canza"? Kai Faridah ta jinjina ta na samun guri ta zauna ta ce.

"In sha Allahu Mami kar ki ji komai duk wani abu da ya kasance na Irfan ne ya fara isowa tafin hannaye na yanzu wasan zai fara".

"Alhamdulillah haka nake son ji please Faridah ki nutsu dan Allah kar ki mana wasa da damar nan kin ga dai gashi yanzu Jafar ya koma son Mujidat saboda ki ji haushi to ina so ki nuna masa kin fi 'karfin auren mutum irinsa ki dage ki auri Irfan daga lokacin da ki kai haka duk za su raina kansu daga shi Jafar d'in da Mujidat d'in ke har ma uwar Mujidat d'in duk sai sun sallama miki" murmushi Faridah tai.

"Humm na sani kar ki damu Mami komai fa yazo 'karshe ki zuba ido kawai kwanan nan za ki zama surukar Irfan domin ni kad'ai na san abun da ke faruwa a halin yanzu" jinjina kai Mami tai ta na cewa.

"Da kyau Faridah hakan ya yi idan kin fita ki dinner kar ki kwanta haka na san baki ci komai ba yau Alhaji ba ya nan ya tafi Dutse maybe sai zuwa jibi zai dawo".

Mi'kewa Faridah tai ta na girgiza kai ta ce.
"A'a nayo take away a hanya saboda ba na son cin na gidan domin na san yau ba ranar girkinki bane" ta na fad'in haka tai waje.

Kusan sati guda da tafiyar Zarah Hannatu ba ta sani ba sakamakon ba wanda zai je ya fad'a mata ita kuma ba zuwa gidan tai ba sun je biki wani gari dangin mijinta shi ya sa ba ta sani ba sai da 'yarta Iklima ta je makaranta wata yarinya ma'kwabciyar su Zarah wacce akai komai a gabanta taga sanda Zarah ta shiga motar ita ce take fad'awa Iklima ta ga Zarah an saka ta a mota an tafi da ita wani guri.
Ta na dawowa kuwa ta samu Hannatu ta na share-sharen gidan sakamakon jiya su ka dawo, ko zama ba tai ta ce.

"Ummah kin san me? Wai Aunty Zarah ta bar garin nan"? Daina shara Hannatu tai ta d'ago ta na kallonta da mamaki ta ce.

"Ban gane ba wacce Zaran da yaushe tabar garin ina ta je"?.

"Nima ban sani ba d'azu a makaranta Harira ta ke fad'a min ta ganta ta shiga mota sun tafi" cikin kokwanto Hannatu ta ce "kai anya gaskiya ne ta ya Zarah za ta bar gari ban ji ba ina za ta je"? Shiru tai ta na tunane-tunane can ta aje tsintsiyar hannunta da sauri ta wanke jikinta ta canza kaya ta goyi yaronta ta cewa Iklima ta 'karasa mata gyaran bari ta je taji gaskiyar magana.
Ai kuwa ta na zuwa Umma ta fashe da kuka sannan ta fad'a mata duk abun da ya faru sosai ran Hannatu ya 6aci ga shi lokacin data shiga gidan Hamah ba ta nan ta je anguwa jira tai har ta dawo sannan ta sameta.

"Hamah wanne irin cin zali ne wannan za ki tura Zarah wani gari haka kawai ba ki san wace yarinyar da ta tafi da ita ba sai kin saka anje an lalata mata rayuwa me ya sa da tazo ta na neman masu aikin baki bayar da Aliyah ba ita ce 'yarki ba Zarah ba" wani irin kallo Hamah tai mata a gadarance ta ce.

"To fitsararriya zageni ko ki rufe ni da duka idan na ji wuya sai na fad'a miki inda na tura ta isa na yi shiyasa ban tura tawa 'yar ba na tura 'kanwar ta ki 'yar gwana ko za ki tafi ki dawo da ita ne"? Sosai ran Hannatu ya sake 6ace kamar za ta rufe Hamah da duka haka ta ke ji.

"Ba zan tafi ko'ina na dawo da ita ba tun da ban san in da kika tura ta ba amma ki sani ranar da dubunki ta cika ba wanda zai yafe miki a cikinmu sai kin ga sakamako idan dan ki watsa Zarah ya saka ki ka tura ta neman kud'i birni in sha Allahu burinki ba zai ta'ba cika ba babu abunda zai sameta sai alkhairi muguwar mace kawai me ba'kin hali da ba'kin nufi Allah ya isa tsakanin mu da ke" ta na fad'in haka ta koma cikin d'aki gurin Umma ta na kuka dariya Hamah tai ta na cewa.

"Ta ishe uwarki da ubanki amma Allah ya isanki ba za ta hau kaina ba 'yar marar mutunci da ace 'ya'yan da na haifa a gidan baban Aliyah sun tsaya ba mutuwa suke ba ke kin isa fad'i in fad'a dani balle ki zageni amma hakan ma zan yi maganinki kuma ko yanzu nayi nasara a kanku tun da na saka ku kuka da ba'kin ciki"..

☘️☘️ ☘️
Faridah ta na zaune a irin gurin hutawar nan tare da 'kawarta su na magana ta ke fad'a mata abun da taiwa Zarah wanda ba ta ji dad'in hakan ba shi ya sa a take ta ce.
"Gaskiya hakan bai kamata ba Faridah ki tuna har gidan mahaifanta ki ka je kika d'aukota kuma ba cewa yai ya na sonta ba haka kawai ki kaita bariki ki barta sai sun watsa mata rayuwa ni a ganina koda kin barta a garinsu Irfan ba zai ta'ba cewa ya na sonta ba amma wannan abun da ki kai was improper ni 'kawarki ce koda za ki ji haushi na dole na fad'a miki gaskiya idan na ga zaki kauce hanya amfanin abota ta gari kenan dan Allah Faridah ki je ki mayar da yarinyar nan garinsu na tabbata Irfan ba zai ta'ba sonta ba" Anisah ta fad'a ta na jinjina kai alamar tabbatar da abun da ta fad'a kallonta Faridah tai ta na cewa.

"Me ya sa ki ka ce haka"?.

"Saboda ki tuna waye Irfan da matsayinsa da irin daular da ya taso a cikin ta ina da babban ya'kini akan cewa ko a birnin ba kowacce mace ce ta isa ta iya tunkararsa ba kai tsaya me ya sa za ki damu da wancan 'yar 'kauyen har ki rabata da iyayenta kawai ki kawota bariki idan ta lalace fa duk wani alhaki a kanki ya ke, dan me ya sa zaki haka"? Sosai Faridah ta zubawa Anisah ido ta na kallonta daga baya tai murmushi tare da jinjina kai ta ce.

"Hum Anisah ki na da abun dariya kamar dai kin manta waye Irfan sannan ai ita soyayya ba haka ta ke ba, ba ruwanta da duk wannan abun da ki ka lissafa sanda zai kamu da son na ta ina inaa ban sani ba, ba na so hakan ta faru shi ya sa tun farko na d'auki matakin da ya dace dalili kuwa shine kullum ta na zarya a gurinsa ta na kar6a 'kwai ta na sana'a sun saba idan ta je har zance su ke kuma a sake shi ya sa na yanke wannan hukuncin kawai".

Ajiyar zuciya Anisah ta sauke ta na cewa.
"To ba abun da zan ce nikam sai dai na miki fatan alkhairi Faridah Allah ya sa Irfan mijinki ne" da sauri Faridah ta ce "Amin Anisah na gode sosai gaskiya ke 'kawa tagari ce shi ya sa nake sonki wallahi".

"Ba komai amma dan Allah ki duba halin da waccan yarinyar ta ke ciki ki je ki d'auketa ki mayarta garinsu ina ganin hakan zai fi".

"Inaaa har abada ta yi sallama da garin nan sai dai idan Irfan ne ya daina zuwa cikinsa ko kuma na tabbatar da na aureshi a lokacin zan iya mayar da ita kin gane"? Dariya Anisah tai ta na girgiza kai ta ce "kash an anyi ba'ai ba kenan indai dan kin aureshi ne ki ke jin ba zai aureta ba to ki canza tunani idan yaga damar aurenta komai daren dad'ewa zai aureta ai idan har ta koma".

"No ba zai aureta ba Anisah".

"Me ya sa"?.

"Zuciyata ce ta fad'a min haka ki yarda tun da nace ba zai aureta ba, ba zai aureta d'in ba, haba me Irfan zai yi da village girl" gira Anisah ta d'auke ta na cewa "oh kin san da hakan amma ki ka damu"?.

"Dole na damu saboda yanayin mu'amalar ta su akwai abun tsoro shi ne kawai dalili kin ga mu bar maganar yarinyar nan haka ta isheni tashi mu tafi" ta fad'a ta na mi'kewa murmushi Anisah tai itama ta mi'ke ta na kallon Faridan shawarwari da yawa a ranta ta na so ta bata shawara ta je ta d'auki Zarah ta mayar da ita gidansu amma ta san kome za tace Faridan ba za ta ta'ba fahimtarta ba dole ta 'kyaleta ta yi yadda ta ke so amma wannan tsarin da ta d'auko sam ba kyakkyawan tsari ba ne...........
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
Till we meet ina godiya masoya kuma inai muku addu'ar samun gafarar Allah da rahmarsa a duk in da ku ke a fad'in duniya🌍.

🌾Y🌾M🌾A
🍃Y🍃M🍃A ✍️ 🌵Y🌵M🌵A
🍂Y🍂M🍂A

JUYIN MULKI

Dedicated to
❤️MY KIDS❤️
1️⃣ Fatima Zarah ☘️Elham☘️
2️⃣ Ramlat Lele ☘️Ikram☘️
3️⃣Habibat ☘️Ikram☘️

Wannan Page d'in na ki ne yarinyar kirki😍.
ELHAM NAKUDU PRODUCER.

21_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Muhsininah.

__________________PAGE 21
Kusan watan Zarah guda a bariki ba ta sake ganin Faridah ba tun tana saka ran ganinta har ta cire ta wani 6angare kuma haka ya fi mata alkhairi akan ta kasance a hannun Faridan saboda ba ta san me za tai mata ba amma anan ba me tsangwamarta kuma kullum ta na da'ki ba ta yarda ko waje ta le'ko balle ta ga abun da suke sai dai komai a kunnenta ya ke faruwa Leema da Safnah kam in suka fita yawo tun safe sai dare wajen sha biyun wani lokacin ma sai 'karfe d'aya ta yi basu dawo gida ba amma za su bar mata komai kasancewarsu ba masu son aiki bane idan sun tashi haka zasu tafi su bar d'akin kaca-kaca ita zata share ta gyara musu shi ya sa su ma suke jin dad'in zama da ita wanda a halin yanzu ta kasance kamar me yi musu hidima ta gyara musu da'ki su ba ta abinci da kayan sakawa.

Yau ma ta na kwance misalin sha biyu zuwa sha biyu da rabi na dare barci ya d'auketa amma ta bar 'kofar a bud'e saboda su Leema ba sa barikin sun shiga gari.

Wasu 'yan bariki ne su biyu su ka shigo gidan yanzu su na zance su ka wuce duk sauran 'yan barikin da ke gidan kai tsaye d'akin kusa da inda Zarah take su ka 'kwan'kwasa 'kofa farko Zarah ta d'auka nan ne dan a firgice ta tashi ta bud'e 'kofar ta le'ko waje sai kuma ta gansu tsaye a d'aya 'kofar ajiyar zuciya ta sauke ta na komawa ta kwanta tai shiru.

A waje kam suna tsaye har lokacin shiru an 'ki bud'e musu 'kofar ran d'ayar ne ya 6aci da 'karfi ta saka 'kafa ta daki murfin 'kofar ashe dama ba sakata suka saka ta ciki ba kawai irin rufe shi d'in nan su kai.
Suna shiga d'akin taga saurayinta tare da wata zaro ido tai ta na cewa "Rainbow me zan gani haka wata a d'akina"? Jin maganar budurwarsa ya sa ya kalli gurin ta na tsaye kai ya jinjina ya na cewa.

"Eh amma dai ba kece ki ka kama d'akin ba nine kuma ni nake biyan kud'in hayar dan haka ina da damar kawo duk wacce na yi ra'ayi cikin d'akin nan" a masife ta ce.

"Ba ka isa ba wallahi ka yi 'karya ka kawo min wata sokuwa nan".

"Tun da ni ban isa ba ke idan kin isa ki hana ke lokacin da ki ke fita iskancin ki da wasu samarin na ta'ba hanaki fita ne" sai kuma ya nuna mata hanya ya ci gaba "fita ki bani guri malama ban gama abin da nake ba kya iya dawowa in anjima sannan ne nake da lokacinki".

Ya na rufe baki ta ce.
"Wallahi ba ka isa ba babu in da zan fita na je sai dai wannan karuwar tai waje tun da ba d'akin ubanta bane".

"Ok ba za ki fita ba haka ki ka ce ko?.

"Eh haka nace ba zan fita naje ko'ina ba sai dai ita ta fita".

Kujera ya nuna mata ya na cewa
"Ba damuwa ga guri ki zauna dama na fiki iya komai ki zuba mata ido sai ki koyi abubuwan da ba ki 'kware akai ba Sarah mu je muci gaba rabu da wancan abar da alama ta je tasha abun maye ne bana tunanin ta na cikin hayyacinta" murmushi wacce aka kira da Sarah tai ta na fad'awa kan sa kawai ta fara masa kiss cikin 'kunar rai Khalidah tai kukan kura ta fad'a kanta ta fara kai mata naushi ta sha'ke mata wuya za ta kasheta da sauri Rainbow ya tashi ya janyeta sannan ya sharara mata mari dafe kunci tai ta na huci ta ce.

"Ni ka mara akan wannan shegiyar"?.

"Na mareki d'in ko yanzu ki ka sake 'ko'karin zuwa inda take saina sake marinki" ya fad'a ya na nuna ta da yatsa ihu Khalidah tai da gudu ta d'auki wu'ka tai kanta Merry da ke tsaye ganin abun zai kai ga 6aci tai saurin ri'keta 'ko'karin fisgewa ta ke yi ta na cewa.
"Ki sake ni Merry yau saina kashesu ita da shi d'an iska har ni zai fad'awa bariki wallahi saina soka masa wu'kar nan gara na kashe shi ba sai ya zauna a duniyar ba balle ya had'ani da wata tsinanniyar karuwa mu zauna a da'ki d'aya maci amana" ta 'karasa maganar ta na 'ko'karin 'kwacewa fisge wu'kar Merry tai ta na cewa.

"Kin yi hauka ne"?.

"Idan ma haukan nayi ga wanda ya sani nan kuma tun da na rantse yau ba zai kwana a duniya ba sai na kashe shi" ta na rufe baki ta juya da sauri ta fita daga d'akin ta fice ma daga barikin gabadaya a daren ta je ta siyo fetur a cewarta gabadaya gidan za ta 'kona in ya so sai ya san yadda zai yi ba wanda ya lura da ita sai da ta fara watsawa warin fetur d'in ya fara tashi sannan aka ankara ba zato sai wuta aka gani faaaaa ta kama da gudu Khalidah tai waje nan da nan gida ya rud'e aka hau ihu Zarah ba ta sani ba ta riga ta koma barci sai da hayaniya ta tasheta ta ji ana ihu.

"Wayyo jama'a wuta ta kama a gidan kowa yai ta kansa" mi'kewa tai da sauri ta na cewa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce irin wuta kuma da wannan daren"? Bud'e 'kofa tai itama ta fita waje da gudu ko takalmi ba ta tsaya d'auka ba a lokacin har motar 'yan kwana-kwana ta zo wurin sakamakon ba su da nisa dasu.
Su na ta 'ko'karin kashe wutar su Leema saukarsu kenan ganin abun da ya ke faruwa ya sa ta ce.

"Zarah me ya faru"?.

Kaita girgiza hankalinta a tashe ta ce.
"Ban sani ba Aunty Leema ina da'ki ina barci na ji ana fad'a daga haka akace wuta ta kama shine mu ka fito waje" tsaki Safnah tai ta na cewa.

"Aikin banza kawai wad'anne shegun ne su ke mana fad'a a gida da wannan daren har suka kunna wuta" dariya Leema tai ta na cewa "zai wuce rainbow da Khalidah ne ga muryarta can ta na zage-zage shima ya na biye mata kin san duk gidan ba wanda ya kai su fad'a sai kace kaji su da suke tashi tsakar dare su kama dambe d'an sun yi fad'a 'karfe d'aya ai ba wani abun mamaki bane yau dai wannan gidan ba za mu iya kwana a cikinsa ba sai an gyara bari na kira saurayina ya zo ya kaimu guest house d'insa sai mu kwana acan" ta fad'a ta na d'auko wayarta daga handbag ta koma gefe saboda hayaniyar mutane ita kuma Safnah ta 'karasa gurin da su Khalidah su ke taga abun da ya ke faruwa.

Ba'a jima ba suna tsaye sun cika 'kofar barikin jiniyar motar 'yan sanda🚔 ta cika gurin tuni kowa ya kama takai takai ana gudu rud'ewa Zarah tai sakamakon ba ta saba da irin wannan rikicin ba sai ta kasa gudu tai tsaye a wajen har sai da motar ta 'karaso ganin haka ya sa Leema fisgar hannunta da gudu su ka bar gurin sai dai kafin su yi nisa wata motar ta danno kai ta layin da su ka bi wanda ya saka Leema ta sake mata hannu kowa yai ta kansa ko sanin in da take jefa 'kafarta Zarah ba tai ba har tai mugun nisa da anguwar sai da ta samu mafaka sannan ta tsaya ta na mayar da numfashi 'kafarta ko arzikin takalmi babu tsayawa tai bayan ta dawo daidai ta kalli gaba ta kalli baya babu alamar D'an Adam gurin tsoro ne ya rufeta ga shi ko haske babu balle ta san yadda za tai ta fita a gurin ta na cikin wannan halin ta fara jiwo gurnani da sautin karnuka da alama ba iya d'aya bane da sauri ta shige 'kar'kashin wani abu mai duhu data gani a gurin ba ta san ma meye ba ita dai indai za ta tsira shi ne damuwarta sosai ta runtse ido ta 'kan'kame jikinta tai shiru, sai kukan sauro da ya addabe ta amma duk da haka ba wannan ne matsalarta ba.

A wannan halin ta kwana curr a gurin washe gari da

Please Login or Register in order to submit comment