You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaffara saboda kai ba in dai mu ka je har ranar itayau ba ka samu yarinyar da tai maka ba Faridah za ka aura ka ji sharad'ina".

"Na amince Daddy".

"Shi ke nan zan so ka auri za6inka saboda gudun matsala kuma hakan zai fi yiwa kowa dad'i tashi kaje" mi'kewa yai ya na komawa part d'insa ya kira Bilal a waya ya na fad'a masa.

"Bilal Ina cikin matsala Daddy ya saka rantsuwa cikin maganar mu kuma ya ce sati d'aya ya bani na samu wacce tai min gabadaya na rasa yadda zan yi yace in dai sati ya cika ban samu ba saina auri Faridah".

"To kai yanzu ya ake ciki baka da wacce ka ji ka na sonta"?.

"Gaskiya ba ni da ita".

"Har wancan yarinyar ta 'kauyen"? D'an shiru Irfan yai zuwa wani lokaci daga baya ya ce.

"Eh har ita" dariya Bilal yai ya na cewa "kai kar ka cuci kanka fa naji ka fara yin shiru kafin ka bani amsa wato nazari ka ke kenan kana tunanin ka na sonta ko ba ka sonta, to maganar gaskiya in dai haka ne sai dai ka yi ha'kuri ka auri Faridah d'in kawai"

"What Bilal ka san me ka ke cewa kuwa na auri Faridah fa kace"?.

"Eh man ba kace ita wancan yarinyar ba tai maka ba na tabbata a yanzu in dai ba ita ce d'in za kace ba to baka da wata tsayayyiya ko kuma tun da sati ya baka ka tsaya da aikin komai kawai ka shiga gari ka duba za ka samu ai da 'yan mata".

"Ba zan iya ba, wannan aikin wahalar da kai ne".

"To gaskiya ni kam na gama iya nazari na in dai ba hakan za kai ba sai dai ka ha'kura ka auri Faridan dai da ba ka so".

"A'a Bilal ba zan iya aurenta ba dan Allah ka bani shawara gabadaya kaina ya gama kullewa ba na gane komai".

"Ok tsaya to kaji idan ka yarda da shawara ta kar ka ji komai ka je ka fad'awa wannan yarinyar ka na sonta in dai kaga hakan ya dace ni dai a nawa ra'ayin ta yi tun da tana da hankali da nutsuwa kuma ta yi ilimi daidai gwargado ba abin da zai gagara wayewa ce kad'ai ba ta da shi sosai kuma daga zarar ka aureta ta shigo cikin birni za ta 'karasa koyon komai haba Irfan ka santa fa sannan ka na jin dad'i idan ka ganta na tabbata idan har kai haka wata rana za ku daidaita sannan za ka ji abun da baka ji game da ita".

Sosai Irfan yai shiru ya na nazari ya dad'e sosai ya na tunanin abun da Bilal d'in ya ce masa daga baya ya jinjina ya na sauke numfashi ya ce.
"Shi ke nan Bilal na gode zan gwada abun da ka ce min".

"Yauwa Irfan sai na jika zuwa jimawa idan na fito zan shigo na dubaka sannan mu dad'a samun lokaci mu tattauna"..............
🤙YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Yma writer jikar Abubakar Muhammad Mai tambarin yma Jigawa state.

TYPING 📲 ✍️2026/Aug Juyin mulki
☘️ Yusrah Musa ce☘️

JUYIN MULKI
By
Yma writer

27_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Alaminah.

_________________ PAGE 27
Kwana biyu da yin maganarsu da Bilal bai samu ya je 'kauyen ba har aka tafi kwana hud'u yaga saura kwana uku ya rage masa rantsuwar da Daddy ya shi ya sa yau ya na tashi da asuba bayan ya je masallaci daya dawo yai wanka ya shirya kawai ya d'au hanya daya shigo 'kauyen bai nufi ma'aikatar ba kansa tsaye ya wuce 'kofar gidan su Zarah yai parking tare da fitowa ya rufe motar ya jingina a jikinta ya na kallon gidan ya na kuma tunanin yadda zai fara furta mata maganar da ta kawoshi tabbas ya na jin nauyi sai dai ba shi da za6i bayan hakan in dai ba so ya ke Daddy ya d'aura masa aure da Faridah ba dole yai magana da Zarah d'an rufe ido yai a hankali ya sauke numfashi ya na bud'e idon daidai wani yaro zai wuce ta kusa da shi ya ce.

"Kai d'an Boy zo na aikeka gidan nan" to yaron ya ce yana zuwa Irfan ya ri'ke hannunsa ya na cewa "ka shiga gidan nan kace ana neman Zarah a waje".

"To in ji wa zan ce"?.

"Kawai ka ce ana nemanta a waje idan ta ce waye kace Irfan ne".

Shiga gidan yaron yai yana sallama
"Assalamu alaikum Zarah ta zo ana nemanta a waje"? Ya na rufe baki Hamah ta fito da gudu ta na gyara d'aurin zani ta ce.

"Wa ye"?.

"Wani me mota ne a waje".

"Me mota kuma na shiga uku me mota dai kai anya kunne na ya ji daidai kuwa me mota ya zo neman Zarah" Hamah ta fad'a ta na fitowa da gudu ganin Zarah tsaye ya sa ta wuce da sauri tai hanyar waje a hankali ta lalla6a ta le'koshi ya na nan a tsaye yadda ya ke dafe 'kirji tai idonta kamar zai fito waje ta ce "na shiga uku da gaske ne kuwa ni Hamah yau naci karo da abun da ya fi 'karfina innalillahi wa inna ilaihi raji'un waye wannan saurayin kyakkyawa haka ya zo gurinta daga ina ya ke" ta na tsaye ta na le'ke Zarah ta fito za ta fita ri'ko hijab d'inta tai ta na cewa.

"Ke fad'a min gaskiya waye wannan kyakkyawan saurayin ko dai kiranye ku kai ya fad'a kansa"? Jin abun da tace ya sa Zarah kallonta kawai ba tare da ta bata amsa ba ta d'an janye bakin hijab d'in nata daga hannun Hamah ta fita, tsaki Hamah tai cikin takaici ta ce.

"Za ki dawo gidan ki sameni ne zan ci uwarki shegiya munafika" ta fad'a ta na juyawa ta koma ciki, da sallama Zarah ta 'karasa tare da gaida shi daga haka tai shiru ta na saurarensa sannan kuma ta na mamakin abun da ya kawoshi 'kofar gidansu domin tun da ya ke ko layin bai ta'ba zuwa ba ya akai ya sani ko dai..................

Katse mata tunani yai da cewa "na san za ki mamakin me ya sa nazo gurinki ko"? Kai ta girgiza ta na cewa "a'a ba abun mamaki bane watakil wucewa ka zo yi kaga ya dace ka tsaya mu gaisa".

"No ba wucewa na zo yi ba nan nazo gurinki magana za mu yi".

"To Allah ya sa lafiya ko kud'inka ne ya 'karu"?

"A'a ba harkar kasuwanci bane tambaya ce zan yi miki ki bani amsa misali yanzu idan nace akwai wanda naga ya dace ki aura za ki amince ki aure shi"? D'agowa tai ta na kallonsa da d'an mamakin me ya sa yai mata irin wannan tambayar kuma a irin wannan lokacin ko dai so ya ke ya had'ata aure da Amar...................

"Zarah".
Ta ji muryarsa da sauri ta dawo daidai daga tunanin da ta ke ta kalleshi.

"Ba ki bani amsa ba"?.

Sunkuyar da kai tai muryarta na rawa ta ce "zan iya amincewa domin yarda da shi kayi shi ya sa kaga ya dace na aureshi na san baza ka ta'ba yin abun da zai cutar da ni ba, na yarda da kai d'ari bisa d'ari" kai ya jinjina tare da d'an yin shiru sannan ya ci gaba.

"Zarah wani abu ya faru wanda ya sa mahaifina ya d'auki zafi da ni akan wannan yarinyar da taso jefa rayuwar ki cikin damuwa na aikata abun da yaja Daddy na ya saka min iyaka kuma ya yi rantsuwa saina aureta in dai ban nemo wacce zan aura ba nan da sati d'aya wannan zuwa gurin naki da nayi na zo ne ba'a matsayin d'an kasuwa ba, ba'a matsayin mutum mai isa ba kuma ba'a matsayin d'an kowa ba na zo nan ne saboda na furta kalmar so a gareki matsayina na mutum kamar ki" ya na rufe baki Zarah ta zaro ido cike da tsananin tsoro kanta na juyawa da sauri ta fara ja da baya ta na girgiza masa kai sannan ta juya za ta koma gida cikin azama Irfan ya dakatar da ita.

"Kinga Zarah dan Allah ki tsaya akwai bu'katar mu yi magana ba za ki fahimce ni ba sai kin nutsu za ki iya bani lokacinki"? Dakatawa tai tare da juyowa ta dawo kanta a 'kasa karo na farko da ta ji nauyin had'a ido dashi a rayuwarta bayan had'uwarsu sosai ya ke kallonta ya na Kuma nazarin ta yadda zai 6ullowa al'amarin.

"Dan Allah ka yi ha'kuri ba zan iya aurenka ba".

"Saboda me"?.

"Nima ban san dalili ba amma dai gaskiya ba zan iya aurenka ba ka yi ha'kuri ka fi 'karfin auren 'yar talaka irina sannan ni 'yar 'kauye ce ta ya zan iya auren wanda ya kasance a birni ya ke sannan wayayye Mai kud'i irinka kwata-kwata ban cancanci zama matar mutum irinka ba" shiru yai ya na kallonta ya na kuma jujjuya maganarta ya san in dai ba bayani yai mata ba, ba za ta ta'ba fahimtarsa ba kuma ba za ta yarda da bu'katarsa ba.

"Zarah na fad'a miki wata magana, ranar da ki ka fad'a min abun da Faridah tai miki bayan na bar garin nan gidansu na wuce saboda raina ya gama 6aci har cikin falonsu na shiga na daketa saboda in ba haka nai ba ban san me zan yi mata na huce ba, hakan ya haifar mata da rashin lafiya bayan na koma gida Daddy na ya ji labari shi ne ya ce tun da saboda ke nayi fad'a ya bani za6i ko na aureki ko na aureta ko kuma cikin sati d'aya na nemo wacce tai min na shiga tashin hankali akan haka har sai da na kwanta jinya amma daga 'karshe Daddy yai rantsuwa ya bani sati d'aya na san yadda zan yi ko kuma na aureta kuma yau four days saura kwana uku ya rage min" shiru yai daga haka yana kallon yanayin Zarah wacce gabadaya ta gama rikicewa jin wai a kanta yai fad'a har da d'aukar fansa ga shi ta dalilin haka ya shiga damuwa idonta ne ya cika da hawaye ba ta d'ago ta kalleshi ba ta ce.

"Ka yi ha'kuri dan Allah da nasan haka za ta faru da ba zan fad'a maka komai ba ga shi na sanya ka cikin damuwa dole na rama maka da makamancin abin da kai min wannan nauyi ne daya rataya a wuya na in dai haka ne nice na jawo maka ka shiga cikin matsalar da ka ke ciki yanzu dan Allah ka yi ha'kuri" d'an murmushi ta saka yai ya na girgiza kai.

"A'a bake bace Zarah kar ki d'orawa kanki laifi dama akwai tsakani na da wannan yarinyar sai kuma ta sake aikata wannan abun shi ya sa na d'auki zafi sannan Daddy ma ya na neman d'an 'karamin dalilin da zai yi amfani da shi shima sai ya ka fa hujja da wannan abun da nayi.

"Na sani dalili na Abbanka ya sharad'a maka sati sannan ya sanya maka iyaka kuma dole ka bi ta indai kana bu'katar ganin daidai a rayuwarka".

"Na san da haka yanzu ya ki ke gani za ki aureni ko dai me ye ra'ayinki ba na so na takura miki in dai kin ji a ranki bakya son zama dani please tell me dan Allah Zarah kar ki 6oye min kuma kar ki cuci kanki in dai kin san ba za ki iya ba ki fad'a min zan fahimce ki".

"Idan na amince shi ke nan Abban na ka zai ha'kura da yi maka auren dolen da baka so"? Kai ya jinjina "eh amincewarki shi ne samun nutsuwa ta sannan shi ne samun sauki na a gurin Daddy".

"Shi ke nan na amince zan aureka zan zauna da kai in dai ka na bu'katar hakan"?.

"Ba iya bu'kata ba ce Zarah ina so ne kuma da zuciyata na ke so ba da bakina ba ina fata kin gane"? Sakawa yai tai masa kallon da ba ta shirya ba saboda jin amsar da ya bata wanda kuma ta yi mamaki da jin hakan daga gareshi ko da wasa a ranta bata ta'ba tunanin hakan zai faru ba a gaba kenan fa hakan ya na nufin sonta ya ke ba wai kawai ya na bu'katar ya aureta dan kar Daddy ya saka ya auri Faridah bane.

"Zarah".
Ta ji ya kira sunanta ba ta iya amsawa ba kawai da su ka had'a ido dashi sai ta juya da sauri ta shige gida................

Kwanansa biyu a garin ya kama kwana shida da maganar da su kai da Daddy shi ya sa a ranar ya tafi gida domin ya je ya samu zama da Daddyn kuma ya fad'a masa abun da ke ranshi.

"Daddy maganar za6i da ka bani na za6a".

"Ok masha Allah ashe suruka ta, ta kusa zuwa na ganta a ina ta ke 'yar waye"? Yai tambayar ya na murmushi sannan ya kalli Momy wacce ta zubawa Irfan ido jin abun da ya ce sannan ta kashe kunne ta ji sunan yarinyar da zai ambata.

"Sunanta Fatima Zarah sunan mahaifinta Abubakar amma amfi saninsa da Malam Ubaliyo".

"Alhamdulillah gari fa, ko anan ta ke"?.

"A'a a wannan 'kauyen da na ke zuwa take ita ce wannan yarinyar da ka bani za6i ko ita ko Faridah" ya na rufe baki Momy ta ce.

"Yauwa zargina ya tabbata dama na san 'karshen zancen ba zai wuce ka ce kana sonta ba tun da kayi fad'a a kanta gashi kuwa tun ba'a je ko'ina ba ka furta" ta fad'a ta na kallon Irfan wanda yai shiru sannan ta kalli Daddy da shima Irfan d'in ya zubawa ido ya na murmushi ta ci gaba.
"Kai d'in Irfan dan asara tsabar zubar da kima ka rasa wacce za ka aura sai yarinyar da tai tashin 'kauye gaskiya ba ka isa ba sai dai ka nema a nan dan ka ji Alhaji ya baka za6i yace ko ita ko Faridah ashe tsabar sokonci sai ka kama sonta harda zuwa ka fad'a mata kana son ta"? Kai tsaye Irfan ya ce.

"Ita ce za6ina Mom".

"Ita ce za6inka, 'yar 'kauyen"?.

"Ita ce za6ina Mom".
Ya sake maimaita mata tsaki tai ta na cewa "ai gara daka za6eta hakan ya yi kyau ka ga yadda ba ta san komai na kayan amfani ba idan ka aurota wata rana sai ta kunna gas ta babbake maka gida ka na barci ko ta lalata maka gidan wannan duk kai ka sani" kallonta Daddy yai har lokacin fuskarsa da murmushi ya ce.

"Ya kuma ki ke yi masa baki idan ya kamashi fa"? D'aga kafad'a tai irin ko a jikinta d'in nan ta ce.

"Shi ke nan Alhaji sai mu yi masa addu'a Allah ya ji'kan shi da rahma 'yar 'kauye fa yace zai aura ya saka ta a wannan 'katon gidan da ya gina ka tuna kaga irin kayayyakin da ya zuba a ciki wasu ma daga 'kasashen waje ya siyo to idan ba so yake taiwa gidansa gobara ba taya zai tsiro da aurenta"? Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Irfan.

"Kai fa Alhaji ya gwada kane da ya baka za6i ya san ko kanka ya juye ba za ka d'auki wata 'yar 'kauye ba ka bar Faridah wacce tai tashin birni ashe kai tsabar d'anyen kai daga fad'a maka haka maimakon ka je ku daidaita da Faridan ka bata ha'kuri ka baiwa iyayenta ha'kuri sannan ka zo kace mana ka amince za ka aureta sai kawai ka d'auki mota ba sanarwa ka tafi can ka furta wata 'yar 'kauye cewa ka na sonta za ka aureta ko"?.

"Bai kamata ki ri'ka fad'ar irin haka ba bayan ya fad'a miki ita ce za6insa har sau biyu ai ki ha'kura ko"? Had'e rai Momy tai ta na cewa "ai abun ne ya bani haushi Alhaji kawai da naji ya na maganar aurar wata 'yar 'kauye".

"Oh my God Ru'kayyah kenan, kamar a bakinki aka rad'a 'kauyen nan har fad'a ki ke da 'karfi ki jira nayi magana da shi man ai ba ki tabbatar da ita zai aura ba kawai ya fad'a ne" juyawa yai ya kalli Irfan ya na cewa.

"Irfan wancan yarinyar ita ka ke so"?.

"Eh ita ce za6ina fiye da Faridah Daddy dan Allah kar ka ce a'a ita ce tayi min fi ye da kowacce yarinya shi ya sa na za6eta saboda na san wace ita".

"Ok na fahimce ka Irfan Kuma ba zan ce a'a ba, domin ban san albarkar da ta ke cikin auren ba Allah ya sa haka shi yafi alkhairi fi ye da auren Faridah d'in" ya na rufe baki Momy ta ce.

"Gaskiya ni ban amince ba bai isa ba, ba zan yarda ya d'auko min abin magana ba wannan ai salon ya sa ayita dariya ne a cikin dangi ana cewa Allah ya 'kara ya 'ki auren 'yan mata masu aji ya je ya auro 'yar 'kauye wacce ba ta san komai ba wallahi na tabbata wasu ma gulma ce za ta kawo su dan kawai su ganta su je su d'ora a gaba".

"Ke kuwa kin dage sai fad'a ki ke shi kuma ya fad'a miki ita ce za6insa kin ga kuwa ba abun da za mu ce sai fatan alkhairi addu'a ce ta mu".

"A'a Alhaji ka hana shi auren wannan yarinyar kawai ba zai aureta ba".

"A'a Ru'kayyah ki rabu da shi dan Allah ba ki san me auren zai kawo ba kawai ki bishi da kyakkyawar addu'a tun da ya riga ya furta dama so mu ke yayi kuma sai ya furta kin ga wannan abin farin ciki ne zan samu lokaci na sake zama da shi ya tabbatar min da gaske ya ke idan naga alamar har zuciyarsa ne da kaina zan je 'kauyen na samu mahaifinta mu zauna mu yi magana ta fahimta.

"Alhaji wai kaima da gaske ka ke kenan ka amince ya aureta har ka ke maganar zuwa 'kauyen gurin mahaifinta"?.

"Eh ba da wasa nake ba, in dai shi da gaske ya ke nima haka zan je da kaina na nema masa aurenta a gurin mahaifinta domin ban sani ba ko yaronsa na farko namiji ne kin ga sai a rangad'a min takwara ko"? Ya na rufe baki Momy ta zaro ido har ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ta na cewa.

"Kai Alhaji ka na da abun dariya wallahi wato a yi maka takwara".

"Uhmm ke ba fad'a ki ke bazai aureta ba nikam ina so ya aureta ko dan na samu takwara jika da kuma aboki da gaske ina bu'katar na ri'ka ganin 'kananun yara a gidan nan wad'anda za su ri'ka d'ebe min kewa please Ru'kayyah wannan abun da ya ke son yi ba haramun bane abun alfahari ne a wajen mu dan Allah ki taya shi son abun da ya ke so kar ki 'kara kusheta a gabansa ki rabu da shi tun da shi da kansa ya furta mana cewa yana sonta ba wata matsala" kai Momy ta d'aga ta na cewa.

"Tom shi ke nan Allah ya sa haka shi yafi alkhairi na amince da za6in na sa ya zanyi" murmushi Daddy yai ya na kallonta har ya bud'e baki zai fad'i wata magana sai kuma ya fasa sakamakon tuna wani abu.................
YUSRAH MUSA ABUBAKAR CE.
Jigawa state birnin daraja.

Start ur day beautifully with fajr prayer and Quran recitation.
🤲Yaa Allah make us among those who never miss Salah Amin.

JUYIN MULKI
By Yusrah Musa Abubakar
☘️☘️☘️❤️JIGAWA❤️☘️☘️☘️
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Dedicated to my daughter
ELHAM NAKUDU PRODUCER
≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=≈=

28_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Nabiyyi-Zakiyyat-takiyyi


______---------________ PAGE 28
Kusan sati guda Irfan bai sake komawa 'kauyen ba amma Amar ya na can shi ke kula da komai sannan su na yin waya ya tambayeshi lafiyar Zarah.
Ranar da ya cika kwana goma a ranar ya shirya bayan sallar la'asar ya fito falo ya samu iya Momy ba ta ganshi bama sai da ya ce.

"Mom".

Juyowa tai ta na cewa.
"Na'am Irfan Ina zuwa haka ka d'au irin wannan wankan"? D'an murmushi yai kamar ba zai magana ba saboda kar ya tsokano Momyn sai kuma ya raya a ransa bari ya tsokane ta d'in ya ji me zata ce.
"Zan je hira gurin surukarki Mom me zaki bani na kai mata, ki taya ni da addu'a Allah ya sa wannan yarinyar matata ce" jin abin da ya ce ya sa Mom kallonsa ta na cewa "ka manta aure za ka je ba hira ba" sabon murmushi ya sake ya na jinjina kai tare da 'karasowa kusa da ita ya sunkuya saitin kumatunta ya sakar mata kiss tare da mi'kewa ya ce.

"Abun da nake fata kenan Mom Allah ya amsa addu'arki I love you so much" ya sake du'kawa ya 'kara ba ta sabon kiss wanda ya sa ta sakin murmushin da batai niyya ba tare da kallonsa cikin so ta ce "Allah ya shirye ka" ta sake binsa da kallo a karo na biyu ta ce.

"Irfan haka kuma za ka tafi ba ka ci abinci ba"?.

"Eh ina sauri ne saboda bana so nai shigar dare sosai" ya fad'a ya na shirin fita Momy ta dakatar da shi "tsaya ka tafi da shi idan ka je sai ka ci" ta fad'a ta na wucewa kitchen ta d'auko ta sako ta kawo masa kar6a yai ya na murmushi a ransa ya na ayyana uwa mai dad'i kenan da girmansa da hankalinsa amma har yanzu ta na kula da shi kamar yaron goye ba ta so ya zauna da yunwa.

☘️☘️☘️K'AUYE🏕️
Da dare ya na zaune a falo Amar ya shigo ya na cewa.

"Sir".

"Yes".

"D'azu Zarah ta zo nan".

"Nema na"?.

"A'a bata ce haka ba amma dai da alama kamar ta na son ganinka ne" ya fad'a ya na kallon Irfan wanda ya d'an yi shiru sai kuma ya kalli agogon hannunsa tara da rabi dare ya fara yi bai kamata ya je inda ta ke ba yanzu zai bari da safe ya je.

Sai dai a daren wajen sha biyu da mintuna akai kiransa cewa gobe ya na da tafiya 'karfe shida na asuba zai hau jirgin safe zuwa Acapulco Mexico. Duk yadda ya so ya had'u da Zarah ba dama ga shi ba waya ce da ita ba balle ya kirata shi ya sa ya saka a ransa idan zai dawo zai taho mata da ita saboda irin haka kuma bayan nan ya na so ya had'u da mahaifinta domin bai ta'ba ganinsa ba.

Kwata-kwata kwanansa hud'u ya dawo a gida yai kwana d'aya washe gari da safe ya shirya ya fito zai tafi.

"Mom zan tafi"

Da mamaki Momy ta kalleshi ta na cewa.
"Daga dawowarka jiya haba Irfan ko hutawa babu"?.

"Akwai dalilin Momy".

"Dalilin wannan yarinyar ko"?.

"A'a ba shi ba".

"Ok Allah ya tsare saika dawo amma dai nasan saboda ita ka ke wannan saurin kamar za ka tashi sama" d'an murmushi ta saka yai amma bai yi magana ba sai Mimih dake gefensu ita ce tace.

"Yaya Irfan"

"Uhm"

"Nima ina so zan bika na gano wannan garin da ka ke zuwa"

"Me za ki yi acan bayan ki na zuwa school"? D'an shiru tai ta na tunanin 'karyar da za ta sharara masa dan ya amince su tafi.
"Am ba sauran wata lecture da zan yi a cikin satin nan akwai iya guraren da zamu duba domin fara exam d'in mu ka ga zan fi samun nutsuwa a can na karanta sosai" zuba mata ido yai kamar me tunani ya na kallonta ta d'an karya wuya ta turo baki a shagwa6e duk tunaninta kallon da ya ke mata ko zai hanata ne sai kuma ta ji ya ce.

"Ok za ki iya shiryawa cikin minti goma"? Da sauri ta mi'ke cikin farin ciki ta na cewa "eh jira ni dan Allah gani nan zan fito yanzu kar ka tafi fa" ta fad'a ta na yin upstairs da gudu samun kujera yai ya zauna tare da d'ora 'kafa d'aya kan d'aya ba abun da ya ke hangowa kamar wannan nutsattsiyar yarinyar mai yawan shiru wacce ba ruwanta da kowa. Numfashi ya sauke a hankali ya furta.

"My Life" can 'kasa muryar Momy ya ji ta ce "your Life wace ce"? D'agowa yai ya na kallon Momy da mamaki bai yi tunanin akwai wanda zai ji abun da ya fad'a ba sai da ya ji ta tambaye shi amma bai amsa ba har Mimih ta fito su ka fita sakamakon ba shiga gurare irin haka take ba sai abun ya zame mata wani

Please Login or Register in order to submit comment