You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabon al'amarin cikin nishad'i ta ke kallon ginaginen 'kauyuka da kuma yanayin yadda su ke rayuwa har su ka shiga garin.

Ya na kaita ma'aikatar ko zama bai yi ba ya tafi gurin Zarah domin ya dad'e bai ganta ba maybe ya fi wata d'aya idan lissafawa zai yi.

Da yamma bayan Mimih ta yi wanka yana zaune ta fito ta na cewa.
"Yaya Irfan dan Allah ina so zan shiga cikin 'kauyen nan na ga yadda yanayinsa ya ke".

"No".
Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba d'an marairaicewa tai saboda ta na son fitar ta ce.

"Dan Allah ba dad'ewa zan yi ba yanzun nan zan dawo ba nisa zan yi ba"

"Ok ki kula kuma ki dawo da wuri" ya fad'a ya na mi'kewa su ka fita tare ya saka securities mutun biyu su rakata ta je ta gano cikin 'kauyen ta dawo,.
Su na tafe ta na kallon kowa da komai 'yan garin kuwa sai tururuwa su ke suna bin ta da kallo ganinta da ma'aikatan gurin wancan masana'antar ne sai mafi yawa su ke cewa ai watakil matar Irfan ce ta zo gurinsa tun da gata nan da masu tsaro wasu suce a'a 'kanwarsa ce kowa dai da abun da zai ce.

Mimih kam sosai ta ke nishad'i sannan ba ta da wani girman kai kuma ba ta da 'kyalewa duk inda za ta wuce sai tace musu sannu. Ta na tafiya har ta shigo ta layin su Zarah amma da ya ke ba ta santa ba ta na tsaye a waje Hamah ta le'ko ta na aiko mata da zagi ta nai mata masifa Mimih ta 'karasa gurin ganin da Hamah tai Mimin ta na kallonta kuma ga shi ta ganta da masu tsaronta sai tsoro ya kamata da sauri ta fad'a cikin gida ta na cewa.

"Za ki shigo gidan ki sameni ai matsiyaciya sai na fasa miki kai da wannan icen" ta fad'a ta na nunata da shi ta juya ta koma ciki kallonta Mimih tai ganin yadda hawaye ke zuba a idonta ya sa ta dafa kafad'arta a firgice Zarah ta d'ago ta na kallonta.

Mimih ta ce
"Me ya faru, me ki kai mata Mamanki ce mu je ki bata ha'kuri" ta fad'a harda ri'ke hannunta kai Zarah ta girgiza ba tare da tai magana ba ganin haka ya sa Mimih sake ri'ke mata hannu ta jata su ka shiga gidan tai sallama Hamah ta na zaune ta kalli Mimih ta kalli Zarah sannan ta d'auke kanta.

"Ki yi ha'kuri dan Allah ina nema mata afuwarki idan laifi tai miki" ta fad'a ta na ri'ko hannun Zarah ta ce "ki bata ha'kuri Maman ki ce"?.

Shiru Zarah tai daidai Umma ta d'an dogaro da sanda ta fito ta kalli Zarah sannan ta kalli Mimih ta na cewa "ba'kuwa mu kai sannu da zuwa bismillah ki 'karaso mana" d'an murmushi tai ta na kallon Umma ta juya ta kalli Hamah sannan ta kalli Zarah sai yanzu ta fahimta Umma ita ce mahaifiyar Zarah saboda ta fi kama da ita amma Hamah basa kama maybe ita kuma kishiyar Mamanta ce.

K'arasawa Mimih tai ta cire takalminta ta shiga d'akin su Umma ta gaida ita har su ka d'an yi hira sama-sama ta mi'ke tace za ta tafi amma kafin ta koma garinsu za ta sake dawowa anan Umma ta fahimci ita 'kanwar Irfan ce saurayin da ya ke son Zaranta duk da bata ta'ba ganinsa ido da ido ba amma ya ta'ba zuwa gaida ita da dare sau d'aya.

A 6angaren Mimih ita kam ba ta san Zarah ce budurwar da Irfan ya ke so ba, bayan sun fito Zarah tai mata rakiya har kusa da ma'aikatar sannan tai mata sallama ba ta 'karasa cikin gurin ba duk da ita ma ta fahimci Mimih 'kanwar Irfan ce kuma ta ga suna yanayi sosai ko ba ta fad'a ba indai ka ganta kuma ka san Irfan za ka ce ita 'kanwarsa ce.

Da ta koma Irfan ba ya nan sai dare su ka had'u ya na zaune ta ce.
"Yaya Irfan".

"Yes".

"D'azu ina zaga garin nan har wani gida na shiga kuma na yi 'kawance da budurwar gidan sunanta Zarah har nan ta rakoni amma ba ta shigo ba ta koma" jin abun da tace ya sa Irfan d'agowa ya kalleta kamar me nazarin maganar da ta fad'a masa wato da Zarah ta had'u kenan har su ka 'kulla abota.......

"Yaya Irfan ko ba ka son 'kawancen da na yi da ita naji ba ka ce komai ba"? Mimih ta sake fad'a ta na kallonsa kai ya girgiza ya na mayar da hankalinsa kan aikin da ya ke ya ce.

"Da Zarah ki ka had'u"?.
D'an zaro ido tai ta ce "dama ka santa ne"?.

"Ita ce wacce zan aura ba wata ba" sake sakawa yai ta 'kara fito da idonta waje ta na kallonsa da mamaki ta ce "wayyo dama ita ce ashe na had'u da ita ai ban sani ba har d'akin Ummanta na shiga amma gaskiya ta na da kishiyar Mama wacce ta ke takura mata Yaya ka yi sauri ka aureta d'azu ma da ice ta biyota waje za ta daketa shi ne dalilin da ya sa na shiga gidan na bata ha'kuri" jin abun da Mimih ta ce ya sa ya kalleta da sauri oh wato har yanzu Hamah ba ta daina takurawa Zarah ba kenan humn yana tunanin wannan matar kafin ya auri Zarah sai ya makata a kotu an yi musu shari'a.

Washe gari ma duk yadda ya so ya samu ya je gurinta da wuri bai je ba sakamakon ya yi ba'ki saida su ka tafi sannan yaje da yake ta ga ya d'an dad'e ba ya nan sai batai tunanin shi bane sai da ta fito.

"Wai dama kaine"?.

"Eh baki ji dad'in ganina bane ko akwai wanda ku kai alkawari zai zo"? Da sauri ta girgiza kai.

"A'a kawai dai ban yi tsammanin kai d'in bane naga ka dad'e ba ka zo ba shi ya sa na nuna jin mamaki".

"Ok amma ya akai ki ka daina zuwa kar6ar 'kwai kamar yadda ki ka saba Amar ya fad'a min bakya zuwa sai dai shi ya kai miki me ya sa"?.

"Ba komai".
Ta fad'a ta na d'an sunkuyar da kai "ban yarda ba Zarah saboda yanayin ki ya nuna min cewa da akwai wani abu 6oye min ki ke"?.

"Da gaske nake ba komai".

"Na yarda jiya 'kanwata ta zo nan ko"?

"Eh mun d'an dad'e da ita ma sannan ta tafi amma ban nuna mata na sanka ba".

"Ni na fad'a mata bayan ta koma tace min tayi 'kawa har gidanku ta shiga" ya fad'a sai kuma ya had'e fuska ya ce "wato Zarah wannan matar ta gidanku har yanzu ba ta daina takura miki ba ko"? Da mamaki Zarah ta kalleshi.

"Wa ya fad'a maka"?.

"Wa ki ke tunanin zai fad'a min bayan nima na san da haka maybe saina had'ata da hukuma kafin ta daina yi miki abun da ta ke".

"A'a dan Allah ka rabu da ita meye ma duniyar balle abun da ya ke cikinta komai yai farko zai yi 'karshe wata rana sai labari mai labarin ma wata rana zai shud'e ni ban d'auki abun da take min a matsayin komai ba na 'kyaleta da Allah shi ne me sakamako" shiru yai ya na kallonta daga baya yai murmushi kawai ya na girgiza kai ya ce.

"Shi ke nan tun da kin ce haka nima na ha'kura wacce rana ake samun samu Abba a gida ina so mu had'u da shi".

"Ai da ya ke koda yaushe ya na kasuwa ba zama yake ba sai 'karshen sati ranar asabar da lahadi shi ne ya ke wuni a gida baya zuwa ko'ina".

"Ok yau Friday gobe kenan zan sameshi idan na zo"?.

"Eh".

"Ba damuwa ki fad'a masa zan shigo da safe gurinsa tun da anan zan kwana".

"To zan fad'a masa in sha Allahu ba zan manta ba".

"Na san ba za ki manta ba amma lokacin da Daddy na yazo nan gurinsa kin sani"?.

"Eh na sani amma ban ganshi ba lokacin ina gidan Aunty Hannatu har ya tafi ban sani ba sai da na dawo Umma take fad'a min".

"Nima ban san zai zo ba Amar ne ya rakoshi tare da wani babban amininsa su ka zo ina tunanin sun yi magana mai muhimmanci kuma abun ba zai ja lokaci ba shiyasa na ke son had'uwa da Abban na ku".
Kai ta d'aga amma ba tai magana ba sakamakon jin wata fargaba ta kamata duk yadda ta so 6oye jin tsoronta sai da Irfan ya gane cewa ta na cikin firgici kuma hankalinta ya tashi har ma yai tunanin ko ta canza ra'ayi ne ko kuma auren ne ba ta so yanzu, ita kuwa Zarah a 6angarenta haka nan ta ji fargabar ta sameta karon farko tun had'uwarsu abun da ba ta ta'ba ji ba, shi ya sa take neman dalilin da ya sa ta ji zuciyarta ta buga dan kawai ya na son had'uwa da mahaifinta.
🍇 YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
Jigawa state.

Da anyi kiran Jigawa har wani tunkaho na ke yi
Ana maganar Jigawa har wani canza salo nake yi
Jigawa jiharmu ce
Abar faharin mu ce
An san mu akan zaman lafiya ba a san mu da rigima ba🍒.

JUYIN MULKI
By
Yusrah Musa Abubakar

29_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun wa barki ala Sayyidina Muhammadun 'kuraishiyul Hashimiyyi.

✍️2026/7Aug/ Fri night 09:03PM
Juyin mulki by yma writer Yusrah.

_________________ PAGE 29
____________________
Sakamakon ya san cewa wannan auren nasa ba irin kowanne aure ba ne zai zowa mutane a baibai sannan al'umma da yawa za su 'kalubalanci abun saboda shi ya kasance d'an birni mai kud'i mai ilimi d'an gayu kuma sananne gashi zai auri yarinyar da ta kasance 'yar 'kauye ce wannan abun dubawa ne shi ya sa ya zauna da kansa ya yi rubutu sannan ya je aka buga masa haka helicopter ya wuni ya na watsa takardun a garare dabam-dabam saboda ya na so kowa ya sani kuma ya sheda.

Da dare Momy ta na zaune a falo ta saka TV a gaba ta na kallon yadda jama'a ke ta faman cecekuce akan wannan auren da kuma abun da Irfan ya rubuta a jikin takardun da helicopter d'in ya watsa a ranar kowacce tasha idan ta kunna hirar da su ke kenan ana ta muhawara ta na wannan halin Irfan ya shigo tare da zama ya kalli yanayinta gabadaya ranta a 6ace ya ke ya san dama za'ai haka kuma bai yi hakan dan ya 'kona mata rai bane ya yi haka ne saboda samun salama koda nan gaba kafin auren babu me tararsa da wata magana.

Kallonta yai ya ga idonta har lokacin TV ya ke kallo numfashi ya sauke ya na cewa
"Barka da dare Mom".

Ajiyar zuciya ta sauke tana d'auke kanta daga kallon TV ta mayar da hankalinta kansa ta ce "barka daga ina haka tun da ka fita sai yanzu"?

"Na je anguwa ne gurin Bilal".

Kai ta d'aga sai kuma ta sake kallo TV d'in ta na cewa.
"Irfan dama wannan abun ka ke so ko? Shi ya sa akai ta kawo maka 'yan mata ka 'ki ashe dan ka je ka d'auko mana abun magana ne, ka duba yadda gabadaya gari ya d'auka radio television da kafafen watsa labarai ko'ina maganar da su ke kenan akan aurenka da yarinyar nan ana ta 'kalubalantar abun yanzun nan wani mutum a TV ya gama fad'in cewa ka kafa tarihi domin ba wanda ya ta'ba tunanin yadda ka ke da aji da kud'i da matsayi za ka iya auren yarinyar da ta kasance 'yar 'kauye ce". Daga haka tai shiru ta na kallon Irfan ta ga ko kad'an yanayinsa bai canza ba ci gaba tai "d'ayan kuma cewa yai abin damuwar shi ne ba auren yarinyar ba ya yanayin iliminta da tarbiyyarta su ke ta ya zata fara sarrafa kanta daga lokacin da ta kasance matar aurenka"? Kai Irfan ya jinjina cikin sweet voice d'insa ya ce.

"Amma da 'ya'yansu na ce ina so ba za su fad'i haka ba" numfashi Momy ta sauke ta na cewa "bayan haka wani shi kuma cewa yai "shi abun da ya fi d'aure masa kai shine kai da had'uwa da kai ya ke da wahala ita ta ya ma kuka had'u har ka ganta ka fara sonta"?.

"Zan ba su wannan amsar amma saina aureta gani gata gasu".

Momy ba ta gaji ba ta sake cewa sannan d'ayan ya ce "yadda ka zuba kayan da ko budurwar birni ba za ta iya sarrafa shi ba a gidanka ta ya wacce ta kasance tashin karkara za tai amfani da su"?.

"Ta yadda kowa ya ke yi haka itama za tai amfani da komai, ba wanda aka haifa da sani ko iyawa zan d'auko mutane na musamman su koyar da ita".

Jin abun da yace ya sa Momy ta yi masa kallon da ba ta shirya ta na cewa.
"Ikon Allah da alama maganganunsu ba su 6ata maka rai ba"?.

"Akan me raina zai 6aci bayan duk tambayoyinsu ina da amsar su" 'yar dariya ya saka Momy tai ta na kallonsa ta ce "wato Irfan na fahimce ka duk abun da za'a fad'a akan Zarah zagi kushe aibu duka ba za ka kalla ba"?.

"Saboda ni ita na ke so kuma ita ce za6ina sannan na amince zan zauna da ita a kowanne hali domin ta kasance ita d'in rayuwata ce" sosai Momy ta ke jinjina kai ta ce "lallai na yarda da zuciyarka da ranka da dukkan 'karfinka da jarumtakarka ka ke son Zarah wannan shi ake kira da so dan Allah yanzu yau anan gurin na sake fahimtar cewa ita ce za6inka kuma farin cikin ka ina alfahari da hakan Allah ya albarkaci zaman da za ku yi".

"Amin Mom nagode".
Ya fad'a ya na d'auko wayarsa yai kira Momy ta na zaune ta na sauraron hirar da har lokacin ake yi akan dai auren Irfan d'in ta ji yace "a dakatar da wad'annan tashoshin na tsawon shekara guda kuma ba na bu'katar 'korafi zan nemesu Amma ba kwana kusa ba sai sanda na samu lokaci kuma ka tabbatar musu idan na tashi nemansu za mu had'u da su ne a kotu" ya na fad'in haka ya sauke waya ya na jan tsaki wanda ya saka ba shiri Momy ta kalleshi da mamaki ta na cewa.

"Irfan ya haka kuma, me ya sa zaka dakatar da su har tsawon shekara guda"?.

"Momy ki rabu da su, ba dai magana su kai a kaina ba, duk abun da su ke ji dashi na fisu dan Allah kar ki ce komai kuma kar ki fad'awa Daddy idan ya dawo zai saka na ha'kura ne ni kuma na saka a raina saina d'auki mataki a kansu".

"Ok Irfan ba zan fad'a masa ba amma dan Allah ka kasance mai ha'kuri da yafiya idan wani ya 6ata maka kar kace dan wannan abin da su kai sai kayi shari'a da su".

"Ok Mom zan yafe musu saboda da ke amma ba yanzu ba sai bayan bikin dole ne su amsa query" murmushi Momy tai jin abun da yace ita har ta matsu ma ayi bikin komai ya wuce a daina maganganun auren a tashoshi duk ta san hakan zai d'auki dogon lokaci kafin a daina maganar maybe sai an kusa shekara ana yi sannan abun zai sake zama sabo idan ta haihu.

Jin motsi a kusa da ita ya sa ta kalleshi gani tai zai mi'ke ta dakatar da shi.
"Irfan maganar lefe kuma na ce akwati nawa za'a kai musu naji shiru baka ce komai ba ko su basa yi"? D'an shiru yai sannan ya ce.

"Guda talatin za'a kai".
Ya na rufe baki Momy ta zaro ido waje mamaki kamar zai she'keta ba san lokacin da ta fara maimaita awatuna talatin ba ta kalleshi ta sake kallonsa ta ce.

"Irfan akwati talatin fa naji kace anya ka na da hankali kuwa 'yar 'kauyen za kaiwa akwatuna talatin kamar wanda ka zare"?.

"Haka na d'auka a raina Momy".

"Haka ka d'auka a ranka lallai kuwa Irfan hakan ya yi kyau da ka d'auka ma zaka sauke in banda sokonci dan ka na ganin dukiyar a banza shine za kai lefe har akwati talatin to ai ko 'yar birni za ka aura sun yi yawa balle 'yar 'kauyen 'kayau wacce ba ta san kwalliya ba".

"Momy har yanzu baki fahimci wannan yarinyar ba sakamakon ba ki zauna da ita ba ni da na santa ban san yadda zan yi miki bayani ba amma dai na tabbata wannan yarinyar ta fi 'yan matan nan hankali ta fisu nutsuwa ta fi su tarbiyya da kamun kai wayewa kad'ai za su nuna mata maganar da nake miki har yau ba ta iya d'agowa ta kalli tsabar idona tai min magana saboda kunya amma su fa 'yan matan nan d'in ya suke? Misali ki kalli Faridah wacce duk abun da ya faru har yau ba ta daina bibiyata ba gara sauran dama ba had'uwa nayi da su ba iya photunansu na gani in ban da Batula dama ita na santa sister na ce wannan abun fa a bayyane ya ke Momy duk abun da zan yiwa yarinyar nan ba zan ta'ba biyanta ba, ba za ki gasgasta maganar da nake fad'a miki a kanta ba saita dawo rayuwa a kusa da ke ba ina fad'a miki son raina bane dan na kare ta, dan Allah Mom ki yarda dani" shiru Momy tai ta na jujjuya maganar da ya fad'a mata daga baya ta ce.

"Shi ke nan naji kuma na yarda amma duk da haka akwati talatin ya yi yawa Irfan gaskiya bai fi akai musu guda goma ba ya za tai da kayan ciki ko danginta ka ke so ta rabarwa"?.

Ba tare da ya musa ba ya ce
"Yadda ki ka ce Momy kome ki kace ya yi ni kawai sanyawar albarkarki na ke nema sannan sai da yardarki zan yi komai bana so na gagara wajen yi miki biyayya koda yaushe ina so naga farin ciki da murmushi akan fuskarki ne" kallonsa tai jin abun da ya ce sai taji ya d'an saka jikinta ya yi sanyi shi ya sa tai murmushi dan ta wanke masa zuciya ta ce "Allah yaiwa rayuwarka albarka Irfan shi ya sa nake sonka saboda idan na baka umarni ko bai yi maka dad'i ba za kai min biyayya sakamakon haka na amince kuma na yarda duk abun da kai niyya a zuciyarka ko akwatuna hamsin ka yi mata".

"Na gode da ki ka fahimce ni Momy kuma na ji dad'in haka wa zan turawa kud'in ya had'a min masu kyau"? Ya fad'a ya na kallon Momy wacce ta nuna kanta ta na cewa "ni mana Irfan wa kake da shi wanda ya wuce ni da kaina zan had'a kayan 'yata na za6a mata kyawawa kamar ita ko mummuna ce"? Kai ta saka ya girgiza da sauri sannan ya d'auko wayarsa ya nuna mata photonta.

"Ga ta Mom" kar6a tai ta na kallonta ganin ba 'karya akwai kyan ta ce.

"Uhmm masha Allah gaskiya dai ba laifi Irfan tayi ba 'karya ni ai sai nake ganin bambancin ta da 'yan matan nan d'in ma kad'an ne wannan ta na zuwa da wuri za ta iya komai nifa yadda nayi tunanin ganinta ba haka na ganta ba na d'auka irin muguwar 'yar 'kauyen nan zan gani busukurkura wacce ba ta san komai ba sai kuma na ganta a nutse, masha Allah, Allah ya sa yadda take a photon haka ta ke a fili" ta fad'a ta na mi'ka masa wayar kar6a yai ya na mi'kewa ya ce.

"Zan tura miki kud'in gobe kafin na tafi" kaita d'aga "ok ina jira maybe idan naga da dama kawai waje zan fita na had'o acan zai fi, amma dai yanzu ka je ka kwanta zuwa safiya duk abun da na yanke sai mu 'karasa maganar".

"Ok Mom goodnight".

"Sleep well Irfan Allah ya tashe mu lafiya" ta fad'a ta na d'aukar remote ta kashe TV ita ma ta mi'ke ta je ta rufe 'kofar falo sakamakon Daddy ba ya nan daga ita sai su a gidan.
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
🍅JU🍅YIN🍅MUL🍅KI🍅

Sayyidah Fad'imah (RA)
Uwar gidan Sayyidi Ali
A mata ke ce Afdali
Akila kin cika da hankali a kaunu babu irinki ko d'aya.
Gun zubar gashi wa tai ya ke, kyan dressing malamarsu ke, gun biyayya ko uwa ki ke sarauniyar matan duniya.

Till we meet.
Godiya ta musamman gare ku masoyan asali.
Bintu matar Koli
Salisu Koli (soldier👮 me tambarin no-going-back🔫🔫Allah ya tsare mana kai a duk inda ka ke).

TYPING 📲 ✍️ JUYIN MULKI BY.yusrah Musa Abubakar Jigawa.

Juyin mulki by
Yma writer Yusrah.

30_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Madaniyyil Arabiyyil Mukarrami Yaumul Kiyamati.

__________----________ PAGE 30
Kamar Mami za tai hauka lokacin da Faridah ta dawo gida ta na kuka da takardar da Irfan ya rubuta haka itama Mamin ta d'ora hannu aka ta ri'ka taya Faridan kuka domin ganin abu da ke rubuce a jiki wanda zargin da su ke ya tabbata daga 'karshe soyayya ta shiga tsakaninsu a lokacin da ba su yi tsammani ba.

Da dare lokacin da Alhaji Sa'id ya dawo haka Mami ta sameshi ko kunya.
"Alhaji wai kana kallo yaron nan yai mana wula'kanci ko ka taimake mu"? Kamar Alhaji Sa'id bai san akan me take magana ba ya ce.

"Me nake kallo"?.

"Magana fa nake maka akan Irfan haka kawai ya zo har gida ya daki Faridah ka fad'a min cewa mahaifinsa ya ce zai d'au mataki ashe matakin kenan sai dai mu ji sanarwa zai yi aure"? Ba tare da Alhaji Sa'id ya kalleta ba ya ce.

"Kuma laifin wa ye"?.

"Laifinka ne duk abun da ya faru"? Mami ta fad'a cikin takaici ta na kallon yadda ya ke harkokinsa cikin walwala da alama ko ta'ba zuciyarsa al'amarin bai yi ba.

"Alhaji wai dan Allah me ye haka ne, yanzu tsakani da Allah ba za ka saka baki yaron nan ko da zai auri wancan shegiyar yarinyar ita ma Faridan ya aureta ba, ai ya na da kud'in da zai auri ko mata hud'u ne rana d'aya idan yaga dama amma ka 'ki kula da lamarin"?.
Fuskantarta Alhaji Sa'id yai ya na cewa.

"Da kyau Zulaihat dama na dad'e ina so ki furta wannan maganar na baki amsa daidai da ke, wato kin manta lokacin da na ce Faridah ta ha'kura ta rabu da shi ga Jafar nan yana sonta me ki ka ce"? Had'e rai Mami tai ta na cewa "ai ban san haka zai faru ba".

"Ato yanzu da kika sani sai ki san yadda za ki yi".
Ya na rufe baki Mami ta ce "ai yanzu ma bata 6aci ba tun da har haka ta faru dole Jafar ya ha'kura da auren Mujidat ya auri Faridah tun da dama ita ya fara so tun farko".

Wani irin kallo ta saka yai mata jin maganar da tayi wacce ko mahaukaci ba zai d'auka ba ya ce "anya kina da hankali kuwa wacce irin maganar banza ki ke yi wannan kin san abun da kike fad'a kuwa Zulaihat, Jafar fa kika ce ya bar Mujidat ya dawo kan Faridah bayan duk wula'kancin da ku kai masa? To bari ki ji bada yawuna ba kar na sake jin kin furta wannan maganar har abada Jafar Mujidat zai aura Faridah ta samu wani ita ma aura kin gane"? Kai ta girgiza za tai magana ya d'aga mata hannu amma duk da haka tsabar taurin kai sai dai ta ce.

"Gaskiya Alhaji ba zai yuwu ba, wallahi ba zan yarda da wannan maganar taka ba ka san................

Tsawar da ya daka mata yasa tai shiru ba tare da ta shirya ba, da hannu ya nuna mata 'kofa da sauri ta tashi ta fita tsaki ya ja ransa a 6ace ya ce.
"Shashasha da kina wasa dani ne, zan yi maganinki".

K'AUYE🏕️
Yau Hannatu ta zo gidan sakamakon maganar da Zarah ta fad'a mata jiya da ta je gurinta, su na zaune a da'ki ta ce.

"Umma dama jiya Zarah ta fad'a min wai mutanen nan za su kawo lefe da tun jiyan ma zan zo mu tattauna sai kuma ban samu lokaci ba na ce ya za'ai ne"? Murmushi Umma tai ta na cewa.

"Ai ya kawo komai

Please Login or Register in order to submit comment