You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ya fad'a abun da abubuwa shi ma sannan a take yai musu rubutu ya wanke ya basu ruwan ya ce a dafa masa abinci da shi in dai ya ci, tofa magana ta 'kare ba zai sake musu ba komai suka ce masa to zai ce sannan sai ya haukace akan Faridah ba zai ta'ba samun kwanciyar hankali ba sai ya aureta.

Kamar yadda ya ce idan sun dafa abinci ya ci zai susuce haka Mami ita ma ta susuce a gurin farin ciki ya gama rufe zuciyarta haskowa take har anyi komai an gama, sosai taiwa Malamin godiya sannan ta ba shi kud'i mai yawa tun da a ganinta hakan ba wani abu bane ta tabbata kwanan nan za ta ji'ke da kud'i😀.

A ranar ta kira Faridah ta dawo gida tai mata bayanin komai sannan washe gari da kanta ta shiga kitchen ta zauna ta tsara abinci mai kyau wanda ta san zai so shi, ta saka Faridah tai wankan ala tsine uwar me 'karya har da makeup ta je tayi a shago sannan ta saka sabon kaya.

Ta na zaune Mami ta shigo d'akinta ta na cewa "wow masha Allah Faridah gaskiya kin yi kyau dole ne yau kam ya saurareki idan kuwa haka ta gaza samuwa to banga ranar da zai so ki ba".

Ajiyar zuciya Faridah ta sauke ta na cewa "kar ki damu Mami in sha Allahu yau dai Irfan bai isa tsallake tarko na ba balle ki tuna jiya shima ya taho gida ya na nan ya kwana kinga zan je ayi komai a gaban mahaifansa na san ko baya so dole ya ci idan ta saka shi" kai Mami ta jinjina ta na murmushi ta ce.
"K'warai kar ki sake Faridah ki tsaya tsayin daka a gaban mahaifiyarsa ki nuna mata ladabi da biyayya ki 'kan'kan da kai ki ri'ka tausasa harshe sannan idan kin ga alamar ba zai ci abincin ba ki nuna mata damuwa sosai ta yadda ita za ta tilasta masa kin ga na kashe kud'i da yawa jiya na baiwa Malamin nan wannan maganin ya fad'a min bana wasa bane ba kowa ya ke baiwa bama sai irin mu dan haka ki kula sosai".

"Kar ki damu Mami zan kula bazan yi sake ba nima fa na damu sosai idan na samu rana ai dole zan yi shanya a raina na ke jin cewa daga yau Irfan ya zamo nawa haka zuciyata ta ke fad'a min" kai Mami ta jinjina ta na murmushi ta ce "alhamdulillah Allah ya sa a dace sai ki tashi ki tafi ai kar lokaci ya 'kure ki je a makare ya fita ba ku samu damar had'uwa ba ki d'auki motar Alhaji tun da bai dad'e da siya ba ta fi kwarjini".

"A'a Mami ba a mota zan je ba napep zan tara yau ba na son tu'ki" Faridah ta fad'a ta na d'auko wayarta daga handbag ta danna kiran Anisah daidai Mami ta juya za ta fita ta ce.

"Ok sai kin dawo ki kula ina nan Ina jiran dawowarki" ta na fad'in haka ta fita.

"Hello Anisah please ki na ina yanzu"?.
Daga can 6angaren Anisah da ke tsaye gaban mirror ta ce.
"Na fito daga wanka ne"

"Yauwa dan Allah ina jiranki a gidan mu ki zo ki rakani gidansu Irfan".

Kai ta d'aga.
"Ok gani nan zuwa"

"Ina jiranki na gama shiryawa ki sauri please sannan kar ki zo da mota a napep na ke son zuwa" ta na fad'in haka ta sauke wayar tare da mi'kewa ta fita asalin babban falon gidan ta zauna muryar Mami ta ji a bayanta.

"Faridah"

"Na'am" ta fad'a ta na juyawa ta kalli yadda fuskar Mamin ta canza zuwa yanayin 6acin rai 'karasowa tai ta na zama ta sake kallonta fuska ba rahma ta ce "wacce 'kawar ta ki ce naji ki na cewa ta zo ta rakaki"?.

"Anisah ce".

"Anisah ko? Humm ya miki kyau da kika fad'a mata ta zo ta rakaki amma duk abin da ya biyo baya ba ruwa na ki kuka da kanki kin gane"? Da alamar tambaya Faridah ta ce.
"Ban gane ba Mami me zai biyo baya Anisah ce fa"?.

Cikin fad'a ta ce.
"Anisan 'kanwa ta ce da baza ta kamu da son saurayinki ba idan ta yi ido biyu da shi to bari ki ji 'kawaye ba ababen yarda ba ne ki yi a hankali da ita na dai fad'a miki kar ta yaudareki ki ce baki san zancen ba sai ki kula" shiru Faridah tai dan har ga Allah ba ta ga abun aibu ba amma tun da har Mami d'in tace haka ta kula...........

"Wato na yi magana kin yi shiru ko?.

"Ki yi ha'kuri Mami zan kula in sha Allahu".

"Idan ki na so na yarda da hakan ki tashi tun kafin ta 'karaso ki tafiyarki kuma ko a hanya tai kiranki ki ce mata kin fasa zuwa kin tafi gurin aiki" Mami na rufe baki ta mi'ke ta na d'aukar baskets d'in har guda biyu ta fita ta na fitowa 'kofar gidansu ta ga Anisah ta shigo layin nasu ajiyar zuciya ta sauke ta na juyawa da sauri cike da tsoro jin an bud'e 'kofar gate ta d'auka Mami ce sai kuma taga Mai gadi ne ya fito numfashi ta sauke ta na d'an sakin fuska ta kalli Anisah wacce ta 'karaso inda take ta kar6i basket d'in guda d'aya ita ma ta ri'ke su ka juya.

Lokacin da su ka je gidan iya Momy su ka zamu Mimih ba ta kwana a gidan ba ta na gidan Ni'ima Salim kuma ya fita Irfan ya na nan amma bai fito ba ya na part d'insa, sosai Faridah ta ji dad'in ganin yadda Momyn ta tare ta da murna sannan ta karramata kuma ta sake mata fuska su na ta zance da alama tayi mata kuma ta na son ta zama surukarta matsalar a gurin Irfan ne kawai.

Su na zaune su ka ji motsin fitowar Irfan da sauri Faridah ta nutsu ta zubawa 'kofar ido ya na fitowa kuwa da ita ya fara had'a idon sosai mamaki ya kama shi amma sai ya 6oye jin mamakin na sa ya 'karaso gurin ya gaida Momy kawai ya mi'ke zai fita ganin haka ya sa Momy cewa.

"Irfan ga Faridah fa ta zo" bai kalli in da Faridah ta ke ba fuskarsa a had'e sosai kuma bai yi magana ba cikin iyayi Faridah ta karya harshe ta na cewa.

"Ina yini".

D'an shiru yai da farko sai kuma ya ce.
"Barka"

Ya na fad'in haka bai jira ta sake wata maganar ba ya bud'e 'kofa ya fita kamar ta tashi ta bishi da gudu haka ta ji, a 6angaren Momy ita ma haka ta ji babu dad'i ganin yadda ya yarfa ta a gaban 'kawarta shi ya sa da suka tashi za su tafi Momy ta had'awa Faridan abun arziki na huce zuciya ta bata.

Bayan fitowarsu Anisah ta ta'be baki ta kalli Faridah wacce har lokacin jikinta a sanyaye ya ke ta ce "ke Faridah dama irin wannan d'age miki kan ya ke yana sham 'kamshi amma yadda ki ke zuzuta shi ba haka abin ya ke ba"? Ajiyar zuciya Faridah ta sauke ta na cewa.

"To ya zan yi Anisah tun da ina son shi haka zan yi ta ha'kuri har na samu ya aureni ranar da ya shigo hannu na shima ba zan yi masa ta dad'i ba saina rama duk wulakancin da yai min sai ya d'and'ani irin d'acin daya d'and'ana min saina juyashi na gigita masa lissafi na gasashi ta yadda ko balangu ba zai fad'a masa gasuwa ba" Faridah na rufe baki Anisah tai dariya ta na cewa "tabdijan lallai idan ki kai haka bana hango miki dogon zama da shi sannan kin d'auko damin da ba saukewa maganar gaskiya zan fad'a miki kar ma ki fara idan kin samu ya aureki ki rungumeshi hannu biyu ki tarairaye shi ta yadda zai ji baya son yai nisa da ke duk in da ya je ke yake tunawa ko.me yake ke ce a 'kwa'kwalwarsa amma idan ki ka dora masa hau a tunanin ki zai d'auka ne? To bari ki ji ba irin su Irfan ake juyawa kamar waina ba garama ki san da haka".

"Duk da hakan ba zan 'kyale shi ya ci bulus ba Anisah sai na rama sannan hankalina zai kwanta".

"To in dai haka ne ki rabu da shi kawai" wata iriyar zabura Faridah tai ta na zaro ido kamar wacce ta ga wani abin firgici har da dafe 'kirji ta ce "Anisah kin san abin da ki ke fad'a kuwa na rabu da shi fa kin manta waye Irfan ne? Kin san irin yawan dukiyarsa da irin kalar rayuwar daular da ya ke kin san irin mahaukacin gidan da ya gina kawai dan ya saka matar da zai aura a ciki? Humm gida ne na kwatance hawa hud'u falo shida kowanne falo akwai kujeru na alfarma da abubuwan rayuwa wanda sai wanda ya shiga ya gani sannan akwai part guda da ya ware a cikin wani falo har da d'an 'karamin swimming pool an zagaye kewayen shi da fulawoyi an 'kawashi sannan ga manyan kujeru na hutawa a gefe" sai kuma ta tsaya ta na murmushi ta kalli Anisah kamar ta na kallon Irfan ba zato ta saki ihu ta na cewa "wayyo Allah na Anisah zan mutu in dai ban samu Irfan ya mayar da hankalinsa kaina ba Anisah ki taimaka min dan Allah".

Girgiza kai Anisah tai kamar za tai dariya ta kalli Faridah wacce ta bud'e wayarta tare da mi'ko mata "kalli ki gani yadda yanayin gidan ya ke waye zai samu irin wannan damar yai wasa"? K'arba Anisah tai ta na kallon wayar ta ga zahiri ba 'karya ko kurarawa akan abin da Faridah d'in ta ce mata gani ta ke ma yanzu da take gani har ya fi tsananin kyau da d'aukar hankali fiye da yadda ta ke mata kwatance shiru Faridah tai ta na kallon Anisah wacce ta shiga wani irin yanayi tamkar wacce tai nisa da duniyar mutane tun da ta d'auke numfashi ko saukewa ba ta iya yi sosai.........................

Su na tsaye sai gani tai Anisan ta saki wayar kafin tai magana sai gani tai ta fad'i a sume😲 da sauri Faridah ta dur'kusa ta na jijjiga ta ganin ba ta motsi ya sa da gudu ta 'karasa bakin titi ta taro me napep ya zo ya d'auke su hankalinta gabadaya ya tashi daidai za su wuce wani shago ta ce.

"Dan Allah me napep dakata anan na siya ruwa zan zuba mata".

"To Hajiya".
Ya fad'a ya na komawa gefen titi yai parking da sauri ta fita ta siyo ta zo ta d'an shafa mata da tai sa'a saita sauke ajiyar zuciya daga haka can take bud'e ido kallonta Faridah tai ta na cewa.

"Sannu Anisah kar6i ruwa ki sha" amsa tai ba tare da tai magana ba ta sha sannan ta sauke nannauyan numfashi ta na kallon Faridah wacce itama ta ke kallonta ta ce.
"Wai Anisah me ya same ki ne ko baki da lafiya"? Kai ta girgiza a hankali ta ce "lafiya ta 'kalau nima ban san me ya same ni ba amma na fi tunanin ganin wannan ginin da na yi ne shi ya rud'ani har suman ya same ni gaskiya in dai haka ne Faridah ki na 'ko'kari da nice ko tunanin wannan gidan da mafarkin shiga cikinsa zai d'ora min hawan jini" jin abun da tace ya sa Faridah kallonta da mamaki har ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ta ce.

"Kai Anisah wai dama ganin gidan ne ya sumar da ke ai na d'auka wani abu ne dabam to dan Allah ki kalla fa taya zan rabu da Irfan ai ba zai yuwu ba ni ko baya sona zan yarda na aureshi in dai zai amince kawai dai ni auren nasa shine damuwa ta" kai Anisah ta jinjina daidai sun iso layin su Faridah mai napep yai parking su ka fita tuna abun da Mami ta ce d'azu kuma bata san tare su ka je ba gudun karta gansu ya sa Faridah ta ce Anisah ta tsaya ta shiga gidan ta d'auko motarta ta zo ta mayar da ita gida...................
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨.
Marubuciyar Juyin mulki akai mana.


Wai kun san wa akaiwa juyin mulkin?.
Amsa
Umma ce da Zarah
Ada Umma ita ke juya komai auro Hamah da Ubaliyo ya yi saita 'kwace ragamar mulkin ta koma hannunta.
Zan yi muku bayani dalla_dalla.

Ban ga abun ambata ga dukka wanin d'aha ba shi d'aya ne za'a so guda ba wai gaibu ba.

TYPING 📲Wed, Aug 5/26 08:19AM
Juyin mulki by Yusrah Musa Abbkr.

JUYIN MULKI
By
YMA DUTSE

24_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Mubashshirinah.

_______________ PAGE 24
Tun da Irfan ta fita daga gida Momy ta ke jiran dawowarshi amma bai shigo ba sai bayan sallar Isha ta na zaune ya dawo kallonsa tai ta na cewa.

"Oh Allah ya shiryeka Irfan tun da ka fita daga gida sai yanzu ka dawo me ya sa"?.

"Saboda ba na bu'katar dawowa na samu wannan yarinyar a gidan" jin abun da yace ya sa Momy sake kallonsa da mamaki ta ce.

"Wai me ya sa Irfan me ye aibun ta ne"?.

"Babu"

"Ban yarda ba dole akwai dalili man" kai ya jinjina.
"K'warai Momy na farko idan kin duba yarinyar nan a yanzu ma da me na fita tazarar mu kad'an ne kusan sa'ata ce nan gaba kad'an idan na aureta ina mai tabbatar miki Aunty na zata koma ta tsufa ta barni ba wanda zai ce matata ce bayan haka ni ba sonta na ke ba batai min ba kwata-kwata".

Girgiza kai Momy tai ta na kallonsa da har zata ce wani abu sai kuma ta fasa kawai tace "shi ke nan ga abinci ta kawo maka ba ka tsaya ka saurare ta ba balle ta baka amma ta ajiye".

"I don't like it" ya fad'a ya na mi'kewa ya shige part d'insa kawai ita Momy da ta bishi da kallo ma sai taji dariya na son kamata kuma sai ta fara tunanin ko dai da gaske aljana ta aureshi domin ba ta yadda za'ai ace duk 'yan matan da ake kawo masa bai son kowacce kuma har gobe maganar kenan, mi'kewa tai ta na d'aukar baskets d'in ta shiga part d'insa a falo ta sameshi ya na zaune ya d'ora laptop akan 'kafarshi ya na amfani da ita ajewa tai ta na cewa.

"Irfan ga abincin nan ka d'auka ka ci ko yaya ne bai kamata ace ta zo har gida ta kawo maka kai mata haka ba" idonsa na kallon fuskar laptop d'in ya ce.

"No Mom I won't eat it".

"Saboda me"?.

"Kawai ba na so".

Ya na rufe baki ta ce "Irfan ba na son shashanci ka d'auka ka ci zata cutar da kai ne kome ka ke tunani wallahi kana bani mamaki yarinyar nan da kyanta da ilminta ba abun da ya rageta amma sai watsar da ita ka ke nikam ba ruwana idan kai za6en tumun dare matsalarka ce tun da mun yi iya bakin 'ko'karin mu a kanka" ta na fad'in haka ta bud'e 'kofa ta fita tana fita ya mi'ke ya d'auki baskets d'in ya bud'e wata 'kofa ya fita harabar gidan ya baiwa Amar ya ce ya fita waje ya samu bola ya zubar har baskets d'in kar ya dawo da su kuma kar tsautsayi ya sa ya bud'e ko ya ci idan kuma ya'ki duk abun da ya sameshi shi ya sani, kar6a Amar yai ya je ya zubar da su akan bola kamar yadda ya bu'kata sannan ya dawo ya fad'a masa a lokacin Faridah ta kirashi ya na d'agawa ta ce.

"Hello Irfan wai me ya faru ne d'azu nazo har gidanku gashi tare da 'kawata nake amma ka ba ni kunya ko gaisuwar arziki ban samu ba gaskiya ban ji dad'i ba sosai ya kamata ka gyara kar ka manta aure fa za mu yi taya rayuwarmu za ta tafi a haka bayan ba ka tsaya mun fahimci juna ba ka nuna min abin da kake so da wanda ba ka so nima na nuna maka ra'ayina"? Shiru yai kamar kurma ko wanda bai iya magana ba ta ci gaba.

"Irfan ka na jina amma ka yi shiru wai dan Allah me ya rageni ne ka fad'a min na sani domin na gaji da tijararka wannan d'age min kan da ka ke ya ishe ni haka gaskiya ba zan iya ba na gaji Irfan na gaji gaskiya ba zan 6oye maka ba raina ya 6aci d'azu please dan Allah kar ka sake bani kunya a gaba saboda ina sonka ba shi ya ke nufin ka ri'ka wula'kanta ni ba ya kamata kasan da haka" sai da ya bari ta gama fad'ar duk abun da take son fad'a sannan ya ja mata wani dogon tsuka a kunne.
"Mtwwwwww"
Ransa a 6ace ya aje wayar ba tare da ya katse kiran ba".

Tsabar takaici Faridah ba ta san lokacin da ta fas wani ihu ba ta na kuka da gudu Mami ta shigo inda take ta na cewa.
"Faridah lafiya me ya faru ki ke kuka kuma"?.

"Gaskiya Mami ba zan iya ba na gaji yau raina ya kai ma'kura wajen 6aci gabadaya Irfan hankalinsa ba a kaina ya ke ba tun da ba d'an gwal bane ni na ha'kura da shi.

Zaro ido ta saka Mami tai ta na kallonta ta ce
"Kin ha'kura da shi kamar ya babu d'ad'in ji"?.

"To Mami me ye amfanin irin wannan sai binsa ya ke yana zamewa ba maganar arziki tsakaninmu ban isa ya saurareni ba kullum idan na je ma'aikatar wani lokacin harna taho bana had'uwa da shi sau biyu to idan ban ha'kura da shi ba Mami ya zan yi yaushe zai kulani"? Ta 'karasa maganar ta na sake fashewa da kuka d'an shiru Mami tai ta na kallonta sai kuma ta ce.

"Kin ga kiyi shiru haka kar wad'ancan munafikan su jiwo mu zan kira Hajiya Rabi zan san abun yi ki kwantar da hankalinki ki daina kuka nayi miki alkawari yadda yaron nan ya saka ki ka zubar da hawayen ki shima sai ya yi kuka da idonsa a kanki" Mami ta fad'a ta na share mata hawayen ta ci gaba da lallashinta harta samu tai shiru sannan a take ta kira Hajiya Rabi ta fad'a mata duk abin da ake ciki tace gobe za ta zo su koma gurin Malamin ko akwai wata dabarar bayan wannan yai musu.

❤️❤️
Tun abin da ya faru tsakanin Irfan da Faridah ta d'auke 'kafarta ta daina zuwa ma'aikatar ta yi tunanin idan yaga ta daina zuwa zai kirata ya ji dalili sai taga shiru har kusan sati biyu kuma ta tabbata ko shekara za tai ba ta je ba Irfan ba zai nemeta ba shi ya sa dan kanta ta gama fushinta dashi sannan dole ta baiwa kanta ha'kuri ta shirya yau ta tafi da wuri.

Daidai ta yi parking da mota ta ga Zarah ta fita daga wurin amma ba tare da kowa ba ita kad'ai dakatawa tai ta zuba mata ido wato ta fahimci wani abu watakil fa wannan yarinyar a kanta Irfan ya ke wula'kanta ta yau kuwa za ta d'au mataki ashe dama da ta d'auke ta, ta kaita birni gidan bariki ai ba tai tunanin za ta iya dawowa ba ashe ta dawo shi ya sa bata ganin ci gaba, zuciyarta ce ta bata shawara ta je ta sameta jinjina kai tai tare da tada motar ta bi bayanta sakamakon ita a 'kasa ta ke tafiya nan da nan Faridah ta sameta shan gabanta tai sannan ta sauke glass d'in motar ta na kallonta wanda ita ma Zarah a nata 6angaren ta zuba mata ido sosai tabbas ba za ta manta wannan fuskar ba ita ce wacce ta jefa rayuwarta cikin had'ari ta so ganinta a lalace Allah ya ku6utar da ita to abun tambayar anan shine yanzu kuma me ta sake biyota za tai mata, ko dai 'kara d'aukar tata za tai ta kaita birnin? Humm bata san kan mage ya waye ba kenan ai ko uban kuturu ya yi kad'an ballantana na makaho ba taga ta yadda ta isa ta sake yaudararta ba................

K'arar bud'e murfin mota da rufewa ne ya saka Zarah daina maganar zucin da ta ke ta kalli Faridah wacce ta fito ranta a 6ace tare da buge kiret d'in 'kwan da ke hannun Zarah ya fad'i 'kasa ya faffashe sannan ta jawo hijab d'inta ta sha'keta murya a kausashe ta ce.

"Fatan kin san dalilin da yasa nai miki haka? Kin za'ke da yawa akan hurumin da ba naki ba Irfan shine wanda zan aura Ina so ki fita a hanyarsa ki daina zuwa inda ya ke yana ganinki da alama ke mayya ce kin lashe masa kurwa idan ya zo wannan matsiyacin 'kauyen naku ko sha'awar komawa Abuja ba yayi, to bari ki ji koda ke mayyar ce da gaske Irfan ya fi 'karfin auren 'yar talakawa 'yar 'kauye jahila irinki ki rabu da shi domin ba sa'anki bane ki kama jakin 'kauye🙊 irinki ki aura idan tsautsayi yasa na 'kara zuwa garin nan na ganki tare da shi saina zama ajalinki" ta na rufe baki ta fara kifeta da maruka kamar wacce aka aikota sannan ta wujijjigata ta doka da 'kasa tare da nunata da yatsa ta ce.

"Wannan kad'an na nuna miki daga cikin irin u'kubar da zan gana miki idan ki ka ci gaba da bibiyar wanda ya kasance abokin rayuwata ne" ta na fad'in haka ta shiga motarta ta tada kawai kanta tsaye ta nufo Zarah cikin mugun nufi da niyyar take ta ganin abun da take 'ko'karin yi yasa a gaggauce Zarah ta mi'ke da gudu ta fad'a wata gona wanda ya saka Faridah taka burki ta le'ko ta na sake yi mata kallon gargad'i sannan ta ja motarta tai gaba.

Da kallo Zarah ta bi motar har ta 'kule sannan ta dawo da kallonta kan 'kwan dake fashe a 'kasa kafin ta kalli jikinta ga fuskarta na mata rad'ad'i gabadaya yatsun Faridah sun fito a kumatunta a hankali ta mi'ke ta d'ebi takalminta ta na d'an jan 'kafa ta tafi gida".

Ta na shiga da Hamah ta fara cin karo ganin yadda ta shigo ta na jan 'kafa ya sa ta ce.

"Ke daga gidan uban wa kike"? Shiru Zarah tai sakamakon ba amsa tambayarta ne a gabanta ba ganin haka ya sa Hamah ta cewa "wato iskancin da kika saba yau ma shi ki ka fita ko kullum sai magriba ta kusa dan munafirci sannan za ki fita yawon banza da wofi ki na bin daba dabar samari suna baki kud'i ko"? Ganin har lokacin tai mata shiru ya sa tace.

"Za ki ci uwarki ne saina had'a miki mugun sharri a garin nan bari Ubaliyo d'in ya shigo yau sai an yita ta 'kare" jin abin da tace ya sa Umma da ke d'aki ta 'kwallawa Zarah kira domin kar ma Haman ta 'kular da ita tai magana tsautsayi ya sa Ubaliyo ya shigo ya ji dole Zaran zai d'orawa laifi taga kuma burin Hamah kenan.

Da zazza6i mai zafi ranar Zarah ta kwana har gari ya waye rawar d'ari take ta na kwance kusa da Umma wacce ke tofa mata addu'a Hamah da ke waje ta ce.

"Ke uwar me kike da baza ki fito ki d'auki wad'annan kayan ba ko rashin mutuncin da ki ka saba yi yau ma shi zaki yi min"? Muryar zarah na rawa irin ta mara lafiya ta ce.

"Ba ni da lafiya da zazza6i na kwana" ta na rufe baki Hamah ta saki salati ta na tafa hannu ta ce.
"Shi ke nan maganata ta tabbata ga shi kuwa yau asirin ki ya tonu ciki ne da ke Zarah"? Tun kafin tai magana sai ga amai kuwa ta fara kwara shi daga kwancen da take ihu Hamah tai ta na cewa "la'ilaha ilallahu ciki ne gashi nan ki na amai ciki ne ciki ne ashe mun kusa cin naman rago a gidan nan" ta fad'a ta na 'kyal'kyalewa da dariya ta kalli Umma wacce tai shiru ta ce.

"Ji munafircin banza harda ki yi wani so'ko'ko kina kallonta kamar ba ki san komai ba bayan ke ce kike turata yawon iskancin yau wa gari ya

Please Login or Register in order to submit comment