You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin 'karo ne"?.

"Eh na dad'o kwano biyu ne da rabi maimakon kwano da kofin da ake yi da yanzu na ninka biyu kenan tun da kinga cewa yai kawai idan na soya na ri'ka fita dashi zai zo ya amsa sai dai ya bani kud'in kawai" murmushi Hannatu tai ta na cewa "iya ribar wannan awarar ta isheki kayan da'ki ni naji Babah Sabuwa ta ce min iyayen Sabitu sun kai ro'kon arziki ko, to Allah ya sanya alkhairi Allah ya nuna mana lokacin cikin aminci da lafiya kin ga kina gama jarrabawa sai mu sha taushe ko"? Y'ar dariya Zarah tai harda rufe fuska ta ce.

"Kai Aunty Hanne".

"To ai gaskiya na fad'a ki tashi ki tafi gida watakil Umma za ta nemeki ga shi kin zo kin yi zamanki mi'kewa Zarah tai ta na mayar da hijab d'inta ta saka sannan tai mata sai da safe ta fita.

Washe gari tun asuba da Zarah ta tashi tai sallah ba ta komai barci ba bayan ta gaida Umma ta fita lokacin Ubaliyo bai dawo daga masallaci ba ta wuce gidan Hannatu ta tarar harta markad'o cire hijab d'inta tai ta taya ta, su ka tace sannan ta hura wuta ta dafa shaf-shaf ta tafasa su ka zuba sinadari ta had'e suka d'ebe jin sallama a waje ya sa Zarah le'kawa har Amar ya zo kar6a ba'a soya ba shi ya sa ya tsaya su na d'an zance da Zarah sama-sama har Hannatu ta gama soyawa tai kiranta ta kai masa.

Kamar yadda ya saba kullum sai ya kaiwa Irfan in dai ya kar6o duk da ko sau d'aya bai ta'ba ci ba amma shi ma Amar d'in ba ya gajiya.
Da sallama ya shiga ya na cewa.

"Good morning Sir"?.

"Morning".
Irfan ya fad'a ba tare da ya d'ago ba Amar ya ce "ba shishshigi nake maka ba amma yau dai ya kamata ka d'and'ana ka ji ko yaya ne Boss" d'an guntun murmushi Irfan yai ya na cewa.

"Me ya sa kake so dole sai na ci kuma kullum sai ka kawo min"?.

"Saboda ya burge ni maybe kaima yai maka dad'i idan kai tasting" jin abun da yace ya sa Irfan ya d'ago ya kalleshi kawai ya girgiza kai yace.

"Ni da kai bamu kasance mutum d'aya ba kowa da ra'ayinsa na fad'a maka ba zan ci ba amma kai ka dage dole sai na ci meyasa"? Jin abun da ya ce sai kawai Amar ya aje plate d'in cikin tsokana ya ce "maybe kallonta kad'ai idan ka yi zai d'ebe maka kewa sannan ta na saka nishad'i" ya na rufe baki ya saka Irfan sake d'agowa ya kalleshi a karo na biyu sannan ya kalli plate d'in tabbas a haka kamar dai za tai dad'i sai dai ba ya jin zai iya cin wani abinci daya fito daga cikin 'kauyen komai yunwar da ya ke ji saboda bai san taya suka sarrafa shi ba..

Ganin kamar nazari ya ke hakan ya baiwa Amar damar cewa.
"Ka ganta Sir".

"Yes".

"Ta burge ka"?.

"No, idan kana bu'katar na ci ina so sai ta fi haka kyau".

Amar ya zaro ido "like how"?.

"I don't know" shi ma ya ba shi amsa a kame sannan ya mi'ke ya na d'aukar glass d'insa ya maida fuskarsa sannan ya d'aura agogo ya kalli Amar.

"Mu je".
Tun Amar bai ce komai ba ya nufi waje da sauri ya bi bayansa domin dama ya fad'a masa yau zai je gida................................
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

Manzon Allah SAW.
Yai mana nasiha mu so juna mu ri'ke gaskiya da amana mu raya zumunci hanya ce ta samun rahma da aljannah ma'kiyin zumunci ba zai samu ceto ba😔.

✍️©®2026.

🌹JUYIN MULKI🌹

Story and written
✍️ YMA DUTSE.

Think before you do.
Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your Life always.

12_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Kaiminah.

..................... PAGE 12
Kamar yadda Amar ya saba koda yaushe shi kad'ai ya ke zuwa ya kar6o tun ranar da ya had'u da ita ta nuna masa gidan shi ke nan sai dai kawai Hannatu ta soya ya zo 'kofar gidan ya bata kud'in ya kar6a. Yau ma da wuri ya zo domin ko gama soyawa ma ba'ai ba shi ya sa Zarah ta fito su ke hira kafin a 'karasa.
Su na tsaye 'yar gidan Hannatun ta fito ta na cewa "Aunty Zarah wai ta gama ki zo ki kar6a" to Zarah ta ce tana kallon Amar wanda yai murmushi ta ce.

"Bari na kar6o yanzu zan kawo maka" kai ya d'aga "ok Fatima I'm waiting" juyawa tai ta na shiga gidan ta d'auko plastic d'in ta fito ta mi'ka masa har ya juya zai tafi sai ya fasa ya dawo yadda ya ke ya fuskanceta sosai ya nuna awaran.
"Nace wannan abar ana iya mata kwalliya ne kamar ayi mata ado da wani abu wanda zai saka tai kyau"? Kai Zarah ta d'aga ta na cewa.

"Eh ana mata kwalliya da kayan lambu kamar albasa me lawashi da tattasai saboda tai kyau".

"Ina so uban gidana ya ci tun da nake siya kullum sai na kai masa amma sam ya 'ki yace sai anyi mata ado gobe dan Allah idan za'a samu ki yi mata ki had'o da kyakkyawan yaji za'a samu"?.

"Eh sosai yanzu ma ba'a makara ba ka jira na shiga ciki na d'auko kud'i akwai wani mai siyar da kayan miya saina siyo a gurinsa na zo na yanka maka".

"Yauwa dan Allah jeki siyo ko nawa ki ka kashe ni zan iya ninka miki burina na ga mai gida cikin nishad'i" ya fad'a ya na saka hannunsa a aljihu ya d'auko dubu d'aya ya mi'ka masa "gashi Ina jiranki please ki yi sauri dan kada ya wuce" kar6a tai ta na wucewa shi kuma ya samu guri ya zauna ba ta dad'e ba ta dawo ta wuce ciki gidan Hannatu ta na zaune ta ganta ta shigo da alamar tambaya ta ce.

"Wai dama ba gida ki ka tafi ba da naji shiru ai na d'auka kin wuce ne"? Girgiza kai Zarah tai ta na d'auko wu'ka ta zauna ta fara yankawa ta ce "ba gida na tafi ba cewa yai ya na so a saka masa kayan kwalliya wai zai kaiwa uban gidansa".

"Tofa ikon Allah shi uban gidan nasa ba zai ci ba kenan in ba kayan lambu ko kuma wani sabon salon ne haka".

"Uhm ni kam ai kud'ina kad'ai na sani duk da yanzu shi ya bani na siyo" ta fad'a ta na mi'kewa ta je ta wanke sannan ta d'auko 'karamar roba fara mai murfi ta zuba a ciki ta kai masa godiya sosai yai mata kamar wanda kyauta tai masa.
Cikin 'kwarin gwiwa yau ya tukari Irfan ya na fatan Allah ya sa yau dai ya ci.
Kamar da wasa yau da yaga an sake mata samfuri ya amsa ya ci Amar ya na gefe a tsaye ya na kallonsa sannan ya na jiran ya ji me zai ce.

"Sir fatan ta burgeka"?.

Kamar ba zai magana ba sai kuma ya girgiza kai ya na cewa.
"How to impress you"? Jin abin da yace ya saka Amar sakin dariya tare da dafe kanshi humm boss Irfan ba sau'ki dama ya san hakan za ta faru kuma ya tabbata ta burgeshi daga yadda ya ke cinta, amma ga shi ya musa bari ya gani zuwa nan da kwana biyu me Irfan d'in zai ce.

Sakamakon Zarah ta na makaranta ba ta san dangin Sabitu sun zo gidansu ba sai da ta dawo bayan taci abinci tai sallah da wanka ta na zaune ta na yanka ku6ewa Umma ta kalleta jiki a sanyaye ta ce.
"Zarah iyayen Sabitu sun zo gidan nan jiya da dare sannan kin yi barci da safe kuma naga kin makara sauri ki ke zaki tafi makaranta bayan da kika dawo daga gidan Hanne shi yasa ban tsayar da ke ba dangin Sabitu sun zo amma maganar da suka fad'a min ba tai min dad'i ba kuma tai min ciwo sosai" daina yankawa Zarah tai zuciyarta ta na bugawa ta ce.

"me ya faru Umma"?.

Kai Umma ta girgiza a damuwance ta ce.
"Ban sani ba Zarah a iya sanina na san ba wata matsala tsakaninki da Sabitu tun da ya fara neman aurenki sai kyakkyawar mu'amala to amma abun da ya kulle min kai shi ne bayan mun gaisa suka ce wai sun zo bani ha'kuri ne Sabitu ya ce ya fasa auren ki" Umma ta na rufe baki Zarah tai wata iriyar zabura kamar wacce aka sokawa wu'ka muryarta na rawa ta ce.

"Ya fasa kuma Umma"?.

"Eh haka ya aiko su fad'a mana daga jin wannan al'amarin an san akwai ma'kar'kashiyasa sai dai ba komai Allah ya kyauta, ki yi ha'kuri Zarah ki d'auki komai ba komai ba ina fatan hakan ya zama miki mafi alkhairi Allah ya sa haka shi ne daidai akan aurensa dan Allah Zarah ki d'au 'kaddara ki saka a ranki dama Sabitu ba mijinki bane ba wanda ya ke za6arwa kansa abokin rayuwa sai wanda Allah ya za6a masa sannan duk abun da ya sameka dama ba zai kuskure maka ba kuma duk abun da ya kuskure maka dama ba zai sameka ba".
Goge hawaye Zarah tai duk irin yadda ta ke ji a ranta musamman da Umma ta fad'a mata wannan maganar maimakon ta ji ta daina sonsa sai wata sabuwar 'kofar sonsa ce ta shiga zuciyarta wanda ba arziki ta fara addu'a ta na share hawaye a hankali ta ce.

"Shi ke nan Umma Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi na yi ha'kuri da Sabitu ko da rabuwa da shi yana nufin mutuwa".

"In sha Allahu hakan ba zai zamo ajalinki ba idan ki kai ha'kuri ki ka dage da addu'a kina zaune Allah zai kawo miki miji nagari har gida" Umma ta fad'a ta na sake kallon yadda ta ke sake goge hawayen da suka 'ki daina zuba ta ce.

"Dan Allah ki yi ha'kuri Zarah ki daina zubar da hawayenki akan wanda bai san kimarsu ba" kai ta d'aga ba tare da tace komai ba ta goge fuskarta ta ci gaba da aikin da ta ke Amma har lokacin zuciyarta ba abun da take hasko mata sai fuskar Sabitu.

Wannan dalilin ya saka Zarah ta na gama aikin gidan da tai sallah ta kwanta sakamakon sanyi da ta fara ji tasan ba zai wuce zazza6i ba dare na yi kuwa zazza6in mai zafi ya rufeta tashi tai tasha magani sannan ta koma ta kwanta amma tsabar 'karfin hali irin nata gari na wayewa ta tafi gidan Hannatu kamar yadda ta saba taya ta aikin.
Ta fito kenan taga Amar a 'kofar gidan tsayawa tai suka gaisa sannan ta koma ta d'auko masa dama gida za ta tafi kar lokacin tafiya makaranta ya wuce har ta barwa Hannatu sa'kon idan Amar d'in ya zo ya kar6a sai kuma su ka had'u.

Fitowa tai ta na mi'ka masa ta ce.
"Ga shi na kusa makara ne shi ya sa na cewa Auntyn nawa idan ka zo ta baka da tafiya zan yi sai kuma mu ka had'u".

"Umhum sannu da 'ko'kari amma na tambaye ki yau me ya sameki na ga bakya cikin walwala"? D'an kau da kai Zarah tai domin ba ta so ya fahimci hakan ba ta ce.

"Ba komai kawai dai ba na jin dad'i ne a jikina".

"Ok ayya Allah ya kawo sauki kin je chemist ne".

"Jinya ta bata chemist bace sannan ba ta bu'katar yawan bincike" jin abun da tace ya sa Amar cewa "ba damuwa na fahimce ki shi ke nan ga kud'in zuwa jimawa zan dawo miki da plastic d'in kamar yadda na saba" kai ta d'aga ba tare da tai magana ba ya juya ya tafi ita ma ta wuce...................
✍️ Yusrah Musa Abubakar ce.
Mrs Al'ameen Ahmad ce.

🌹 JUYIN MULKI 🌹

YMA DUTSE JIGAWA STATE
Mai alfaharin jihata ce ko'ina nake in da zan zarce, a cikin Nigeria mu ke da gada mun taka kan Dutse birnin daraja da ya batse ga haske 💡 a adob Dutse 🏞️.

13_Allahumma salli wa sallim ala Sayyidina Muhammadun Sayyidil Kaidinah.

___P___A____G_____E 13
Irfan ya na zaune ya na waya da Momy ta na masa magana akan tsakaninsa da Faridah Amar ya shigo tare da tsayawa har ya gama sannan ya ce.

"Sir ka na nemana ne"?.

Kai Irfan jinjina.
"Ina son ganin wannan yarinyar" kamar Amar bai san me yake nufi ba ya ce.

"Wacce yarinyar Sir"?.

"Me wannan abar anan garin ta ke ko zuwa take"? Amar yai murmushi a ransa ya ce "an zo daidai wajen dama nasan haka saita faru amma a fili sai ya ce.

"Yalla6ai ba dama ku had'u sai dai ka je inda ta ke".

"What"?.
Ya Irfan fad'a da 'karfi kuma fuskarsa ta canza ganin haka ya sa Amar cewa.

"Abun da yasa nace haka ba a barinta ta je ko'ina koda yaushe ta na gida".

"A ina ku ke had'uwa ta ba ka"?.

"A can na ke zuwa na kar6o".

"Yau kar ka je".

"Ok Sir" Amar ya fad'a cikin girmamawa ya na Kuma kallon yanayin fuskar Irfan ya ga me zata nuna akan tambayar da yai masa. Kuma kamar yadda ya umarce shi bai je d'in ba sai da taga shiru-shiru har lokaci ya fita sannan ta cewa Hannatu bari ta je ta kai masa har gurin aikin hanata Hannatu tai saboda tsoron abun da zai je ya dawo amma daga 'karshe da taga ba zuwan zai yi ba da gaske sai ta had'ata da 'yarta ta ce ta rakata sun d'an yi tafiya kad'an su ka had'u da Amar murmushi yai ya na 'karasowa ya ce.

"Sorry yau kin ga ban je a lokacin da ya kamata ba na yi aiki ne sannan boss d'ina ya dakatar da ni" kaita d'aga ta na mi'ka masa ta ce "ba komai dama ganin shirun da nayi shine nace bari na kawo maka ko da matsala ne".

"No ba wata matsala lafiya 'kalau sai dai uban gidana ya na bu'katar ganinki Zarah" jin abun da yace ya sa ta kalleshi da sauri sannan ta nuna kanta.

"Ni kuma"?.

"Eh maybe akwai bu'katar ku tattauna ya ce na fad'a miki ya na son ganinki idan ba damuwa" kai ta girgiza har da matsawa da baya kamar wanda ya ce mata kamata zai yi ko bata so ya kai ta tace.

"Gaskiya sai dai yayi ha'kuri ba zan iya zuwa in da ya ke ba".

"Saboda me"?.

"Saboda ba maharrami na bane kaga ba ta yadda zan ke6e da shi mu yi wata magana".

"Ai kuma harka ce ta kasuwanci kar ki ji komai shi ya kasance mutumin kirki ne ba shi da wata matsala na yi miki alkawari ba abin da zai same ki kuma ba iya ku kad'ai za ku ke6e ba shi koda yaushe ba ya kasancewa shi d'aya dole za ki sameshi tare da guards d'in sa Zarah na San kin yarda da ni wallahi ba zan yi abun da zai cutar da ke ba, magana ce kad'ai za ku yi kin ji"? Shiru tai jikinta ya na rawa tabbas ba 'karya ta yarda da Amar sosai ta san ba zai cutar da ita ba amma duk da haka ta na tsoron zuwa ma'aikatar nan sai dai za ta gwada, d'agowa tai ta ga yana kallonta ya na kuma jiran amsa a hankali ta d'aga kai a sanyaye ta ce.

"To zan zo amma ba yau ba tun da gobe asabar sai nazo ranar da bani da makaranta" murmushi Amar yai ya na cewa "yauwa masha Allah naji dad'i sosai kuma na gode goben idan na zo kar6a sai mu tafi tare ko"? Kai ta sake d'agawa ya d'auko kud'inta ya bata su ka juya shi ma ya koma.

Ya na komawa ya wuce ya sanar da Irfan yadda su kai.
"Sir na fad'a mata tace za ta zo amma sai gobe ranar weekend" kafad'a Irfan ya d'aga har da ta'be baki ya ce.

"Better".
Daga haka bai sake magana ba sai Amar da yai murmushi kawai ya tsaya ya na kallon abin mamaki wato ya saka ayo masa magana da ita sannan ya ri'ka wani basarwa kamar wanda akai masa dole.

🌹🌹🌹Da dare Zarah ta na zaune tare da Umma su na zance ta na fad'a mata cewa shugaban wancan ma'aikatar ya na son ganinta akai musu sallama.
"Assalamu alaikum wai ance Zarah ta zo a waje"?.

Yaron da ke tsaye a 'kofar d'aki ya na kallon Zarah wacce gabanta ya fad'i duk zatonta ko Amar ne ko kuma uban gidan nasa da ya ke fad'a ta ce.

"Koma kace waye"? Yaron bai motsa ba ya sake cewa.

"Sabitu ne ya ce ki zo".
Sosai gaban Zarah ya sake fad'uwa har saida ta dafe 'kirjinta da'kyar ta ce.

"Sabitu kuma, me zan yi masa kace nace ba zan zo ba ya bar 'kofar gidan nan" to ya ce zai juya Umma ta tsayar da shi.

"Kai Abdul-wahab kace ta na zuwa ka ji" to ya sake cewa sannan ya fice kallon Zarah tai wacce ta gama mugun had'e rai sannan yanayinta ya canza ta ce.

"Tashi ki je ba ki san me zai fad'a miki"?

"Ni Umma ba zan je gurinsa ba me ya ke dashi wanda zai fad'a min bayan wulakancin da yai min".

"A'a Zarah ni fa taurin kai ne bana so baki san me ne dalilin zuwan nasa ba kar ki yanke hukunci lokacin da ki ke cikin fushi Zarah ban sanki da wannan d'abi'ar ba tashi ki je kin ji" d'an rufe ido Zarah tai cikin 6acin rai ta mi'ke ta d'auki hijab d'inta ta fita.

Ya na tsaye ya zubawa 'kofar fitowa daga gidan ido kamar daga sama ya ganta ta fito ajiyar zuciya ya sauke ya na murmushi sai dai ya yi mamakin ganin yadda ta fito a fusace kuma ko sallama ba tai masa ba, sake kallonta yai yaga ba ta da niyyar magana ya ce.

"Yau waye ya ta'ba min sarauniyata ne naga ta fito a haka bayan ban saba ganin fushi a tare da ita ba"? Shiru tai kamar ba ta ji shi ba sai da ya sake magana zuciyarta na tafasa da rainin wayon da ya zo ya na karanta mata bayan ya gama da rayuwarta ta ce.

"Sabitu me kuma ya sake dawo da kai 'kofar gidan mu ko 6atan kai kayi nan ba gidan su sabuwar budurwar da ka yi bane sai ka 'kara gaba nan 'kofar gidan su Fatima Zarah Muhammad ka ke ka gane"? Da sabon mamaki Sabitu ya sake bud'e idonsa a kanta ya na kallonta ya ce.

"To me yai zafi haka Zarah waye ya fad'a miki nayi sabuwar budurwa kuma a ina take ni banda kowa bayan ke" ya na rufe baki ta ce.

"Ada kenan".

"Kamar ya, ban gane ada kenan ba"?.

"Sabitu ka daina sake 6ata min rai akan wanda nake ciki idan abin da ya kawoka gurina kenan ya isa haka za ka iya tafiya" ta fad'a ta na shirin juyawa da sauri Sabitu ya ce.

"Dakata Zarah tsaya dan Allah wai me yake faruwa ne ko kwana biyun da nayi ban zo gurinki ba kuma ban saka Mubarak ya zo ya fad'a miki ba shi ne ki ka d'au zafi da ni"? Juyowa Zarah tai muryarta ta fara canzawa tsabar yadda ya sake dulmiyata cikin sabon 6acin rai ta ce.

"Waya fad'a maka na san baka gari har raina zai 6aci akan haka sa'kon da ka turo danginka suka fad'awa su Umma shi ne ya 'kona min zuciya kawai ba wani abu ba sannan gashi yanzu ka zo sai wani dad'in baki ka ke min kamar ba ka san komai".

Nuna kansa Sabitu yai da alamar tambaya ya ce "ni kuma da yaushe na turo dangina gidan nan me su ka zo dan Allah Zarah ki yi min bayani yadda zan fahimta nifa gabadaya kaina ya kulle ban san komai ba bana gari wallahi bani da labarin wasu dangina da su ka zo" sosai Zarah ta tsaya ta na kallonsa kuma a bayaninsa da yadda ta ga ya nuna a fuskarsa maganar gaskiya da alama d'in fa bai san komai ba dole ya kamata ta tsaya ta sanar da shi, kai ta jinjina tare da juyowa ta koma yadda ta ke ta ce.

"Yau kwana biyu danginka sun zo gidan nan gurin su Umma amma ban san waye da waye ba saboda ina gidan Aunty Hannatu a lokacin sai da na dawo Umma take fad'a min 'yan uwanka sun zo wai kace a fad'a min ka fasa aurena sannan su ka tilasta sai da aka basu kud'in gaisuwa da su ka kawo" zabura Sabitu yai ya na kallonta ido waje ya dafe 'kirji kamar zai yi hauka ya ce.

"Da yaushe nace na fasa aurenki Zarah, wallahi Allah ki yarda dani ban san komai akan wannan al'amarin ba bani da masaniya innalillahi wa inna ilaihi raji'un sun kashe ni sun cuceni Zarah Zarah ko da kowa zai 'karyani nasan ke za ki gasgatani ki yarda da duk abun ya fito daga bakina wallahi Zarah ban san komai ba" ya fad'a ya na dafe kansa shiru Zarah tai ta na kallon yadda ya shiga cikin mugun rud'ani da alama fa bai san komai d'in ba gaskiya da ace da gaske shi ne ya turo su to ba zai zo inda ta ke ba balle ya kirata da sarauniya...............

Katse mata tunani yai da cewa.
"Akwai bu'katar mu zauna mu yi magana ta fahimta Zarah sai dai yanzu ba na cikin kyakkyawan yanayi ba zan iya fad'ar abun da ya dace ba dan Allah ki yi ha'kuri bari na je gida na ji gaskiyar abin da ya ke faruwa gobe zan dawo mu tattauna kin ji ina fata kin fahimce ni" kai ta d'aga jiki a sanyaye amma ba tai magana ba har ya juya da sauri ya bar gurin ajiyar zuciya ta sauke ita ma ta shiga gida.

Tamkar zautacce haka Sabitu ya shiga gidansu a gigice ko sallama bai iya yi ba kawai ya fad'a d'akin Mamansa ta na zaune sai ganin mutum tai a kanta tun kafin tai wani yun'kurin tashi ya jefa mata tambaya.

"Mama da bana nan me ya faru ne, su waye su ka je gidan su Zarah suka ce nine na turasu wai nace na fasa auren ta da yaushe nace haka da wa nai maganar kin san da zancen ne"? Ya na rufe baki ya samu tu'kuicin harara sannan ta ce.

"Da ban san da kwanan zancen ba taya zan tura su fad'i haka" da mamaki ya ce "Mama ke ce kika tura me yasa haba dan Allah Mama nifa da gaske auren Zarah zan yi".

"Ba za ka aureta ba Sabitu na yanke wannan hukuncin kuma har abada ka gane"? Cikin tsananin tashin hankali ya zauna jagwaf a gabanta muryarsa na rawa ya ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me ya sa zaki hana na aureta Mama"?.

"Saboda 'yar iska ce ta fara mu'amala da samarin banza an sha ganinta da su"

"Samarin banza kuma su waye"?.

"Ba zan fad'a ba amma an ganta ba 'karya ba kuma wacce ta fad'a ba za tai mata sharri ba tun da komai a idonta ya ke faruwa ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba bari na 'kare maka 'karshen magana wannan ma'aikatar da aka gina a nan ma ance ta yi saurayi yanzu ta daina siyar da awara shi kad'ai ta ce yiwa ya na biyanta kud'i masu yawa kullum sai ya je 'kofar gidan yayarta Hannatu ya kar6a kuma bayan ya tafi uban wa ya sani ko binsa take yi yana abin da yaga dama da ita ya na bata kud'i ba wanda bai san haka ba a garin nan" sosai ran Sabitu ya 6aci ya San daga jin wannan maganar 'karya ce zalla shi ya sa ya ce.

"Ko akan haka ki ka tura musu sa'kon da bansan da shi ba cewa na fasa auren Zarah"?.

"Eh dalilin kenan ba wani abu ne ya faru ba".

"Mama ina son Zarah kuma ko me ta zama zan aureta na zauna da ita".

"Ko me ta zama kace Sabitu saboda ba ka da hankali ba ka san ciwon kanka ba"?.

"Na san ciwon kaina Mama sanin ciwon kan nawa ne ma ya saka na fad'a miki haka dan Allah ki saka a mayar da kayan nan sannan ku fad'a musu ba nine nace na fasa auren Zarah ba ina sonta sosai kuma zan aureta ko karuwa ta zama".

Zaro ido tai

Please Login or Register in order to submit comment