You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗa kenan da dasashshiyar muryar da ba na tsammanin za a iya jin ta, kafin ido na ya rufe...






17-married to a beast

A

Yau Sanah ta tafi bayan ta yi kwana uku tana jinya na. Ba abinda zan ce mata ita da Alaja face Allah ya saka mu su da alkhairi domin su ne suka taimaka min, ban ɓoye mu su dukan da Ahmad ya mini ba saboda ganin tabon dukan da su ka yi a jikina. Inna uwar mijina ba ta leƙoni ba balle na tsammanci gaisuwa daga gareta bayan na san duk abinda ke faruwa ana kai ma ta gulman sa. Mairo da ke ma ta hidima ma ta hanata zuwa wajena. Ahmad kam tun safiyar da Mairo ta zo ban sake sashi a ido na ba. Alaja ce tace min ta roƙeshi akan ya barta ta yi jinyata shiyasa baya zuwa wajena. Alhamdulillah cikin kwana uku na ɗan ji ƙarfin jikina dan ina shiga  banɗaki na yi komai da kaina hakanan sallar asuba ta yau ma a tsaye na yi ta saɓanin kwana uku da na ke yin sallah a zaune. Daga sashen Alaja ake kawo mana abinci ko yau kafin Sanah ta tafi daga wajenta aka kawo mana lafiyayyiyar breakfast.
Ina zaune akan gado ina tuno hiran mu da Sanah jiya da dare. Itama ɗin da alamu irin nawa za a mata nan ba da jimawaba. Sadiq ɗan gidan Alhaji Abbori ta ke so, a Oxford su ka haɗu. Amma kuma matsalar shine ba wanda bai san gabar da ke tsakanin Alhaji Bulama da Alhaji Abbori ba. Ta ke gayamin a hidiman bikina ta ji ana maganar haɗata da Alhaji Umar Bukarti. Mutumin da aƙalla idan bai yi hamsin ba to saura ƙiris hakanan matanshi biyu kuma dukkan su ba jituwa su ke ba hakan ne ma ya sa ya warewa kowa gidan ta. Idan aka aura mata Alhaji Bukarti ina ga da ni da ita ba zan iya faɗin wanda aka fi cuta ba. Na sani Sanah ba za ta tada hankali ba kamar ni, ba za ma ta iya buɗan baki ta ce Sadiq Abbori ta ke so ba balle ta san ko Baba zai iya chanza ra'ayi ko ba zai chanza ba.

Turo ƙofar da aka yi ya sa na ɗaga ido na kalli ƙofar dan na san idan Alaja ce ko masu aikinta to da sallama za su shigo bayan sun nemi izinin shigowa.

Ƙallo ɗaya na ma sa na kauda kai na, ina ƙara jin tsanarsa a zuciyata.

"Haka aka miki tarbiya a gidan ku mijin ki ya shigo ki kauda kan ki gefe ba sannu da zuwa bare mi ka ke buƙata?"
Ya faɗa yana huci. Ƙala ban ce ma sa ba dan idan na ce zan yi magana to ba lallai na faɗi maganar da za ta ma sa daɗi ba.

"Ki shirya Alhaji na neman mu" ya faɗa yana mai ƙaremin kallo gameda lashe bakin sa.

Har ya fita ko kallon sa ban yi ba balle na ma sa magana. Na dai tashi na nemi babban mayafi na saka na fito wanda tun kawoni gidan wannan ne karon farko dana fito daga ɗaki. Ko Sanah da za ta tafi hanani rakata ta yi wai ban gama warkewa ba. A falon da ke ƙasa na zauna ina jiran sa har kusan minti shabiyar kafin ya sauko.
"Wato ba za ki gaisheni ba ko?"

Na dunƙule hannuna biyu ina jin wani masifa na cina amma na daure na ce "Sannu"

Ya ƙyalƙyale da wata shegiyar dariya ya ce "bayan na roƙi gaisuwan ma Sannu kawai zan samu?. Anyway bari mu gama da Alhaji tukunna"...

Yana gaba ina bayan sa har mu ka je sashen Alhajin wanda mu ka sameshi a falo yana shan lemon kwalba ta cocacola.
Na durƙusa har ƙasa na gaidashi duk da kuwa durƙuson da na yi ya sa na fama jinyar da na ke yi. Alhaji ya amsa gaisuwata yana faɗin na tashi na zauna. A kujerar da Ahmad ya zauna na zauna chan nesa da shi.
Alhaji ya min ya jiki tareda faɗin Alaja ta gaya ma sa na yi zazzaɓi, na ce ma sa da sauƙi. Ahmad ya kwashe da dariya  yana faɗin "Alhaji ba a dai gaya ma ka gaskiya ba, ka ƙara bincike"
Takaici ya kamani, shi wani irin daƙiƙi ne da ko kunya ba shi da shi.

Alhaji ya kauda zancen da cewa "Allah ya ƙara miki lafiya 'yata"

Ƙaramar nasiha ya mana sannan ya mana addu'ar samun zaman lafiya. Tareda shaida mana gobe zai yi tafiya zai je London wani kasuwanci kuma zai iya kaiwa wata ɗaya zuwa sati shida, na ma sa addu'ar sa'a tareda tsari. Yayinda Ahmad ke maganar kuɗin da Alhajin ya ma sa alƙawarin zai bashi. A take ya ciro check ya rubuta ma sa kuɗi ya miƙa ma sa, Ahmad ya karɓa ba ko godiya.
Bayan mun fito ya ce mu je na gaida Inna na ce ma sa na gaji ƙafata ciwo ta ke, duk da gaskiyata na faɗa amma kuma ban son haɗuwa da Innar ne ya sa na faɗi hakan.
Ya watsa min kallon banza ya ce "ko ki wuce mu je ko wallahi na miki rashin mutuncin da ya fi na ranan"

Na yi ƙaramar tsaki a zuciyata na bi bayan sa. A hakimce mu ka sameta a falo tana cin gasashshen kaza. Yadda ta ke ci ka ce naman guduwa zai yi, gaskiya kwaɗayi na ga matsiyaci marar godiyan Allah. Duk da rigan arziƙi da ke jikin Inna har yanzu halayenta na matsiyata ne.

Ban yi gigin tsugunnawa ba, a kujera na zauna tareda cewa Hajiya Barka da rana.

"Ina zaune a kujera kema kina zaune" ta faɗa da tsawa.
Na juya gefe na ina tunanin ko da wani ta ke.

"Ba ki ji mi tace bane?" Ahmad ya faɗa yana kallona.

"Au da ni ta ke?"

"Bana son iskanci Aaliyah, ki shiga hankalinki"

"Barta Ahmad, ta gama iskancin na ta na yau ne kawai" ta kalleni ta ce na tashi na fita. Ni kam bajau ɗina domin za ni ne ta tadda mu je, dan haka da sauri na tashi na bar falon na wuce sashen Alaja inda na samu tana ta kan shiri ita da Safiya ƙanwar Ahmad. Safiya 'yar marigayiya Jamilah ce, uƙubar da su ke sha a wajen Inna ya sa lokacin da Alhaji ya auri Alaja su ka gudu su ka koma wajenta, kuma ta riƙe su hannu bibbiyu. Ita ne ma ta aurar da Fadila yayar Safiyar shekaru huɗu da su ka wuce. Ita da mijinta su na chan ƙasar Malaysia.
Ni na ma manta yau da safe Alaja ta ce min gobe za su koma Lagos dan dama bikin Ahmad ne ya sa ta zo Sokoto. Ba ta zama a Sokoto sai dai sallah ko biki ko wani uzuri. Ita da ɗanta da Safiya duk a chan su ke sai dai Alhaji ya je ya gan su, Inna kam tunda ta dawo Sokoto ko sau ɗaya ba ta koma chan ba.
Na yi zamana a wajen su dan ba na son komawa gidan mu na haɗu da Ahmad.  Har dare ina wajen su, a nan ma na ci abinci, haka nan na yi amfani da tarho ɗin Alaja na kira layin gidan mu dan na ji ko Sanah ta sauka lafiya. Ta ce min ta kira tarho ɗin gidana ba a ɗauka ba na ce mata ina wajen Alaja ne. Haka ta labarta min cewa ta samu gida lafiya, ta haɗamin da cewa Hajiya Hafsatu da ta dawo ta samu Baba ta ma sa maganar abinda ya faru a gidana amma Baba ya banzatar da zancen tareda cewa wai gutsuri tsomin mata ne kawai amma Ahmad ba zai faɗi maganganun da ta yi iƙirarin Ahmad ɗin ya faɗa ba. Sosai Hajiya ta rinƙa faɗa ƙarshe ma ta ce inta sake taka gidan Aaliyah da Ahmad Allah ya tsine ma ta. Na yi dariya na ce lallai anyi drama kam dan faɗan Baba da ƙanwar sa da ke bi ma sa ba ƙaramin kallo ake sha ba. Haka mu ka yi hira sosai tareda ba ta shawaran ta faɗawa Hajiyarta maganar Sadiq ta ce min tsoron Hajiya ta ke yi na ce ma ta Allah ya shiryeta ta dinga dariya...

Ban bar sashen Alaja ba sai ƙarfe tara da rabi na dare nan ma sai da ta min magana akan na koma gidana dare ya yi kafin na tafi.
Ina zuwa na samu Ahmad a falo yana kallo ban ma sa magana ba na wuceshi zan haura sama ya ce "zo nan Aaliyah"
Ba musu na dawo na tsaya ɗan nesa da shi.

"Da izinin wa ki ka shiga sashen Alaja?"

"Gaisheta na je yi kamar yadda na je gaida mahaifiyar ka"

"You dont talk to me like that Aaliyah!" Ya faɗa da ƙarfi.
Na haɗiye miyau ina jiran na ji saukan mari ko duka sai ya ce min "kin ci albarkacin Alhaji na nan, mu je ki bani hakkina tunda yanzu kin warke har kinada lafiyar zuwa gulma"

Mamaki ya bani, saboda rashin imani tsantsa da ya ke son nuna min, shi idan aka ce ya kusanceni sai ya yi bayan ya san irin aika-aikan da ya min kwana huɗu da su ka wuce. A fusace na fara maida ma sa magana
"Kai wani irin mutum ne dan Allah. Dan ina matarka ba shi zai sa ka min abinda ranka ya ke so ba, you raped me Ahmad. Maimakon ka barni na yi jinyar kaina hankali kwance shine ka ke maganar haƙƙi, nima inada hakki akan ka, dan haka banida lafiya" na faɗa ina hayewa sama da sauri. Ban gama rufe ƙofar ba ya banko ƙofar sai da na tsorata ya fara dariya yana faɗin "you like it rough huh?" Na fara ja da baya ina huci domin na tsorata da yadda ya ke "kin san miyasa na amince na aure ki bayan Hajiya ba ta so? saboda taurin kan ki, you're just perfect, ba za ki bani da kan ki ba sai dai na ƙwata ta ƙarfi, to ai shikenan cause I love it Wild"...

Ban san beast aka aura min ba sai wannan dare, ashe na ranan soman taɓi ne ga wanda ya min yau da wanda yai ta yi a gaba.

Ɗaure ni yai a kan gado, hannu da ƙafa. Bayan munyi kokawa da shi ya ci galaba akaina, to ina zan iya da ƙarfin sa. Ban fara kuka ba sai da ya ciro belt ɗin sa ya fara zabga min a cinyoyina, tsirara na ke akan gadon nan haka saukar belt ɗin nan ke sauka ajikina ba kakkautawa. Ina kuka yana dariya, shi ƙuncin da na ke ciki shi ne ke sa shi nishaɗi. Ba zan ce ban san akwai mutane irin haka ba amma ko da ya ke acikin litattafai na karanta gameda mutane da su ke da matsalar BDSM. Ni ban san akwai sadomasochist mutane a ƙasar Hausa ba sai akan Ahmad. Sai na tuna kuma Ahmad rainon turawa ne, primary school kawai aka ce yai a Nigeria gaba ɗaya karatunsa a turai yai. Idan ba sharrin bature ba ta ya ganin mutum cikin ƙunci da wahala zai saka farinciki har ya tada maka sha'awa ya kuma gamsar ma ka da sha'awarka. Yadda ya ke sucking breast ɗina gameda cizon su ka rantse zai ɓimcine min nipple ne.

Ya ce he likes it wild amma shine wild, ɗin domin Ahmad kam na sadaƙar ba mutum bane wild Animal ne sanye da rigan mutane. Scracthes ɗin da ya min a kafaɗuna da cikina sai da su ka yi jini. Na jima da dena kuka ina tunanin ma suma na yi. Lokacin da na buɗe ido dai ya kunce ni, ya rungumeni yana bubbuga bayana a hankali yana faɗin wasu maganganu marasa kan gado.
"You're too much Aaliyah, ciki da wajen ki duk daɗine. Dama haka matan Borno su ke? Ko ke ce daban?"

Yai ta sunbatun sa wanda na rasa gane na dukan da ya min ne ko na rough sex ɗin...

Da safe da ƙyar na tashi na shiga banɗaki na yi alwala bayan na yi wanka da ruwa zalla, tabon da ke jikina idan ya ji sabulu zafi zai sa min. A daddafe na sallaci sallar asuba ina yi ina hawaye saboda ni kam na san tawa ta ƙare domin inhar a kwana biyar da kawoni gidan Ahmad shine zai shiga ƙunci haka to na san lallai kafin sati biyar Ahmad ya kashe ni.

Ban iya fita na yiwa su Alaja sallama ba kaman yadda na ce mu su zan je sai dai sun shigo sun min sallama har ɗaki. Ganina a kwance kan gado ya sa su ka ɗauka ko jikin ne, Alaja ta ce duk lokacin da banida lafiya ko na ke da matsala na kira Doctor Linda za ta zo har gida ta duba ni, na amsa ma ta da to...

Kwana biyu kenan da tafiyar su Alaja da Alhaji ganin ba mai kawo min abinci ya sa na nemi kitchen na shiga na dafawa kaina abinci dan kar yunwa ya kasheni. Ahmad ma ban ji ɗuriyan sa ba tun safiyar ranan ɗin. Yau ina kitchen ina dafa jollof ɗin shinkafa sai na ji ana ƙwala min kira, muryan Inna ce dan haka na fito a hankali saboda har yanzu ba isashshen lafiya gareni ba.

"Uban mi ki ke yi ba ki je kin gaida ni ba jiya da na dawo daga tafiya?"

"Ni ba wanda ya ce min kin yi tafiya" na amsa a taƙaice.

"Allah sarki ashe iyayen ki ba sa son ki haka. Ashe ba ki da wani gata. Na ji ance an dasa ki da Ɗana ne ko kasheki zai yi ba za ki iya rabuwa da shi ba"

Ban gane maganarta ba dan haka na juya zan koma kitchen. Ta jawoni ta kifa min mari tana faɗa wai tana magana ina tafiya. Mi zan yi ban da ido ta gama faɗanta ta fita...

Cikin sati uku salon zaman namu ya sauya. Inna ta maidani tamkar baiwarta, tun safe har dare ni ke ma ta hidima, ta hana ma su aikinta aiki wai tana da surukuwa mi za ta yi da 'yan aiki. A gida idan na yi wani aiki to ra'ayin kaina ne ba sani a ka yi ba. Girki ma dalilin Jiji ya sa na koya amma sai gashi ina yiwa uwar miji bautan da ko a mafarki ba zan yi a gidan mu ba.
Mijina kam sai dai na ce Allah ya saka min da alkhairi domin sai ma abin da ya ƙaru. Tun da na ga Ahmad na shan giya na san duk abin da ya min ba komai ba ne tunda mashayi ne. Sex kuwa ni ban san daɗin sa ba. Idan bai dakeni ba kafin yai ko kuma yanayi yana zuba min belt ko bulala to shi baya samun gamsuwa. Randa 'yan mutuncin sa kenan kuma ba duka amma da zafi-zafi zai dinga yin komai maimakon na ji daɗi sai dai zafi. Kamar yadda Sanah ta faɗa kamar yadda Inna ta faɗa, iyayena sun min magani. Duk baƙincikin da na ke ji ban taɓa tunanin na gudu ko na gayawa iyayena ba banjin ma a raina zan iya rabuwa da Ahmad Wamako ko da kuwa zan ƙarasa rayuwata da shi cikin ƙunci...





18- A good father inlaw

A





Ina duba hannuna da su ka yi kanta saboda aiki telephone ɗin ɗaki ya fara ƙara na tashi da ƙyar na je na ɗauka.
"Hello" na faɗa a sanyaye.
Muryan mahaifiyata na ji, rabo na da ita tun ranan da za a kawo ni gidan Ahmad. Sau tari na kan yi tunanin na kira ta mu gaisa amma kuma idan na tuna yadda ta goyi baya wajen rabani da farinciki na sai na fasa. A duk gidan mu da Sanah kawai mu ke waya sai Baba da ya kirani sau ɗaya yana ja min kunne akan kada na kuskura na bari rigimar Hajia Hafsatu ya shafi tsakanina da mijina, na yiwa mijina biyayya. Addini da al'ada wani lokaci su kan sa akai mace ga halaka. Bayan anmin auren dole ba'a barni haka ba aka haɗa da yimin magani sannan kuma ake tsammani na yiwa mijina biyayya ta ko wani hali. Shin wani biyayya zan yi wa ɗan giya? Wani biyayya zan yiwa mutumin da ina da yaƙinin ba ya sallah sai ya ga dama? Shin wani biyayya zan yi wa mijin da ko ɗaya daga cikin haƙƙoƙin da Allah ya ɗaura ma sa nawa bai sauke ba.
"Aure Ibada ne" wannan kalmar ana ma sa mummunan fassara a mafi yawancin lokuta, domin ana fassara shi bisa son zuciya.

"Ki na lafiya? Ya gidan na ku?" Tambayoyin da Amma ta min kenan bayan mun gaisa na tambayi lafiyar ƙannena. Abin mamaki sai na fashe da dariya, dariya sosai kamar wata zautacciya. Tun Amma na jiran in ƙare dariyar na amsa tambayoyinta, har ta haƙora ta katse kiran bayan ta yi ta tambayan dalilin dariyana amma ban gaya ma ta ba. To mi zan ce mata?
So ta ke na ce ma ta ina lafiya ko so ta ke na ce ma ta ba ni da lafiya. Kowanne na faɗa ciki ba abin da za ta iya yi akai illa ta ce Allah ya kyauta.
Ban jima da zama ba Ahmad ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya na ma sa na tabbatar a buge ya ke.
Wani lokaci ina mamakin wani abu, wai shin kowane gidan ma su arziƙi ne ake samun fitsararren ɗa, ɓata gari kamar Ahmad?
Aliyun gidan mu yana shaye-shaye ga satan kuɗin Baba da ya ke lokaci zuwa lokaci. Sosai ya ke bawa Baba ciwon kai kuma ikon Allah duk yaran gidan mu ya fi kowa kama da Baba, yadda ka san photocopy na shi haka ya ke. Bayan na gidan mu na san ɗaiɗaikun gidaje da na san su na da matsaloli irin haka sai dai wannan Ahmad ɗin kam na shi ya kai ƙalu Innalillahi.

"Aaliyah yunwa na ke ji" ya faɗa yana jawo ni jikinsa.

Na san mi ya ke buƙata amma na dake na ce " akwai abinci a dining room"

Ya juyo da fiskata yana busa min iskar bakinsa mai haɗe da warin giya yana faɗin "kin san abincina Aaliyah. You know how i like it"
Ƙoƙarin tuɓe min riga ya ke na fashe da kuka sosai. Wallahi a lokacin da Ahmad ya kusanceni kamar yadda ya saba inada tabbacin mutuwa zan yi. Ba wani ƙarfi ajikina, daga ɓangaren Inna na ke na gama wahala sosai, abincin safe na jera a dining zanci Inna ta aiko aka kirani tunda na fita kuwa sai bayan la'asar na dawo. Yunwan da na ke ji ta gama galabaitar da ni, wanka na yi na yi sallah shine ma kiran Amma ya shigo.

Ban san ko giyan ce ta sanar da shi ya ƙyaleni ba amma sai na ga ya sake ni ya juya ya fita daga ɗakin. Sai da na tabbatar ba dawowa zai yi ba sannan na dena kuka na goge hawaye na je na kwanta akan gado. Cikina daya cigaba da murɗawa ya sa dole na fito dan na nemi abinda zan ci ko da kuwa tea ne. A stairs na samu Ahmad yana sharan bacci cikin aman da yai, na girgiza kai na wuce shi.
Daren ranan kam Ahmad bai barni ba, har na jima da barci kusan ƙarfe shabiyu na ji gurnanin sa a gefena. Yanzu kam dan dole na fara sabawa da yanayin sa, bai dakeni ba amma na azabtu a wajen sa...

Sati na biyar kenan a gidan, gaba ɗaya na fige na lalace, idan ka cire fiskata ba abin da ke da kyan gani ajikina yanzu. Wannan jiki da na yi lokacin da na je makaranta da wannan kyau da na ƙara kafin bikina da na sha gyara duk babu shi yanzu.

Ina goge wa Hajiya dressing mirror ɗin ta cikin rashin sa'a na ture wani kwalban turarenta ya faɗi ƙasa ya fashe. Ba ta ɗakin dan haka na tsugunna da sauri ina ƙoƙarin tattarewa kafin ta shigo, da na duba da kyau sai na ga ina da irin turaren a ɗakina kuma ni ba amfani na ke da su ba. To awa zan yiwa kwalliyar?.

Ina cikin tattarewa sai ga ta ta shigo, jin ƙaran buɗe ƙofa da na yi sai tsoro ya kamani har na yanke yatsata.

"Wato da na ɗan kauce daga ɗaki ta'adin da ki ke min kenan ko? Kin san nawa turaren nan?"


"Inna ba da gangan na fasa miki ba, amma akwai irin shi acikin kayana zan kawo miki"

Inna ta fara tafa hannu tana salati wai ina ma ta gori. Ban san mi zan ce ma ta ba na kauda kai na daga kanta na cigaba da tattara kwalban. Lokacin da na gama ta riga ta fita a ɗakin, na fito domin na je na zubar na nemi tsintsiya na ƙara sharewa sosai sai na ga Inna da Ahmad tsaye a falo su na magana. Na kauda kai zan wuce Ahmad ya kirani, na ce ina zuwa. Niyyata na je na zubar da fasashshun kwalaben kafin na dawo amma sai ya daka min tsawa akan na zo yanzun. Na ƙarisa wajen su ina tunanin ko mi za su min.

"Mi ki ka cewa Hajiya?" Ya tambaya da ƙarfi.

"Mi zan ce ma ta, na fasa ma ta turare na ce zan kawo ma ta wani, mi na faɗa yai zafi anan?"

"Ka ga matarka ko? Ka ji dai da kunnenka irin rashin kunyar da ta ke min ?" Inna ta faɗa tana nunani da yatsa.

"Ki tsugunna ki bata haƙuri" ya faɗa yana kallon cikin ido na.

Kallon sa na ke ina kuma kallon Innan lokaci guda.

"Ba na son haƙurinta, hukuntata za ka yi ta yadda gaba ko ƙwayar ido na ba za ta so kallo ba"

Kamar almara haka na ji kalmomin Inna da ta ke cewa wai Ahmad ya ɗau kwalba ya min zane a fiska. Shi kan sa Ahmad ɗin sai da ya kalli Inna da mamaki.

"Ba ka ji mi na ce bane?" Ta daka ma sa tsawa

"Hajiya amma..."

"Ka san Allah idan ba ka yi ba sai na danneta a gaban ka na yayyaga mata fiska da kwalban nan. Shegen fiskar da ke sata girman kan idan na ɓata shi sai mu ga abinda za ta yi"

Na fara ja da baya lokacin da na ga Ahmad na ƙoƙarin matsoni.
"Please dont do this to me. Please" sai da na kai bango na tsaya har lokacin hannuna na riƙe da kwalban.
Ganin da gaske idan na tsaya zai aikata abinda uwarsa ta sashi ya sa na watsa ma sa kwalban ajiki na fita da gudu sai dai ban kai ko'ina ba Inna ta riƙoni. Na fara kici-kici ɗin fincike kaina daga riƙonta Ahmad ya ƙariso wajen, sai da ya wanka min mari kafin na nitsu na tsaya domin na san ƙoƙarin gudu ma ɓatawa kai na lokaci ne.

"Miƙo min kwalban Ahmad, ni da kaina zan yayyaga ma ta fiskar"

Inna ta ƙarɓi kwalba tana shirin yanka min fiska shi kuma Ahmad ya riƙe hannayena duka biyu.

"Asma'u!" Muryan Alhaji ya tsayar da ita daga mummunan aniyarta.

"Innalillahi, Asma'u ashe bakida Imani?" Yana zuwa ya wankawa Ahmad mari yana faɗin "wallahi na yi asaran Haihuwar ka Ahmad, har da kai za a ci mutuncin matarka saboda ba ka da hankali" ni dai na ji ƙaran mari uku dan ban buɗe idona ba tun lokacin da Inna ta ƙarɓi kwalban hannun Ahmad na rufe ido na domin na sadaƙar.

"Allah ya shiryaku, Asma'u wallahi ki ji tsoron Allah" haka Alhaji yai ta faɗa, maimakon ta yi shiru ko ta ba da haƙuri sai ta ce.
"Nan ka ce ka yiwa Ahmad Mata na ce ma ka sai dai Baiwa dan na riga na ma sa amma ka bi son ran ka, ban ga abinda zai sa ka ɗaga jijiyar wuya yanzu ba."

Alhaji ya shiga ƙwalawa Mairo kira ba tareda ya amsawa Inna ba. Da ta zo ya ce ta kaini gida ta gyarani. Mairo ta kama hannuna mu ka fita a falon...

Da dare Alhaji ya zo gidan mu, ina ɗaki Mairo ta shigo ta ce na fito Alhaji na ƙasa. Na sa mayafi na sauka.
Ina kallon tsantsan damuwa a ransa.

"Tun kina yarinya ki ke burgeni shiyasa na kwaɗaitawa ɗana ke, a lokacin na bayyanawa Mahaifinki burina kuma ya amince min. Na yi son zuciya Aaliyah domin na san ɗana ya lalace a ƙasar

Please Login or Register in order to submit comment