You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "wannan ɗin. Allah ya kaimu lokacin"

Alhaji Wamako ya ce " 'ya ta ai sai ɗa na, wagga kyau da kwanya ai sai gida na"

A wannan lokacin ya min tambayan da na yi da na sanin ba da amsarta.

"Za ki auri ɗa na ko Aaliyah?"

Ta ya zai min wannan tambaya a wannan lokaci, ta ya zai sa na yankewa kaina hukunci bisa abin da ban da ilimi a kai.

Na gyaɗa kai na alamar e ba tare da na san me tambayar ke nufi ba.

Abinda ban sani ba shine wannan amsa tun daga wannan lokaci ta ɗaureni gaba ɗaya ta hanani sakat ta hana na samu abinda zuciya na ke so...

Al'amari na gidajen ma su kuɗi sai addu'a. Na fara al'ada da ƙarancin shekaru amma ba ni da wani ilimi mai inganci akan sa. Amma ta was busy da harkokin kasuwancinta, ta sadaukar da ragamar tarbiyata wajen Jiji, Jiji tana iya ƙoƙarinta a kaina amma ita kuma ba ta da wani ilimi mai zurfi, yawanci bayanan ta sunfi kama da gargajiyanci. Hajia na ta shirye-shiryen bikin 'yarta Falmata. Aje nan aje chan duk dan ana so ayi bikin da duniya za ta shaida.
Baba harkokinsa ba sa bari ma ya zauna a gida na cikakken sati biyu ba tareda ya yi tafiya ba. Mukan je makarantar Allo daga baya ni da Sanah mu ka watsar. Aka ɗauka mana malami yana zuwa yana koya ma na karatu. Kuɗin gidan mu ya sa malamin ba ya iya aiwatar da abinda ya kamata. Ba zai iya ma na tsawa ko ya bulale mu ba, mun iya ba mu iyaba a haka dai ake ta tafiyar, wata rana ma ya zo mu ƙi fita.
Hamma ya na koyamin ƙur'ani wasu lokutan saboda tun kafin ya zo yai sauka ta tartil hakanan tun farkon zuwan sa Baffa Manu ya kaishi wata makaranta yana hadda yana karatu.

Na tafka ƙwaɓa dayawa farkon balaga ta. Musamman saboda ƙarancin shekaruna da kuma rashin fahimtar abin. Babban ƙwaɓar da na fara tafkawa shi ne sallah cikin jini. Jiji ta ce min ba'a sallah idan ana al'ada amma ni kam ina yi wani lokaci ma sai na tada sallar sai in tuna maganar Jiji amma sai na dake na ce ai Hamma ya ce ba kyau a bar sallah.

A wata na uku da fara jini na, wata rana ina ɗakin Hamma muna karatu, saboda ko da baya koyamin karatun makaranta haka za ka ga mun samu littafin labarai na turanci muna karantawa. Sai aka kira Sallah, akwai masallaci a ƙofar gidan mu dan haka sai Hamma ya fita, idan akwai babban abinda zan shaidi Hamma da shi a iya tarihin rayuwar mu tare to sallah ne. Yayyena su Bukar da Aliyu ba su damu da sallah ba a wannan shekaru na ƙuruciyar su, banda kiɗa da kallo da zuwa party ba abin da su ka fi bawa amanna.


Bayan Hamma ya tafi na cigaba da karanta labarin saboda na ji daɗin sa, chan na tuna idan Hamma ya dawo ya tadda ban yi sallah ba zai min faɗa. Sai na tashi na je banɗakin su na yi alwala duk da kuwa na san ina cikin jini. Na zo na tada sallah, ina raka'an ƙarshe Hamma ya shigo.

"Aaliyah sallan mi ki ke yi?"

Na yi gyaran murya.

"Ki katse sallan nan"

Ban katse ba sai dai na yi dungure-dungure na ƙarasa a gurguje. Dama sallar ta wa ya aka ƙare dan ma Hamma na ƙoƙarin gyara mini.

"Waya ce mi ki ana Sallah idan ana al'ada?"

"Ba ka ce wanda baya sallah ɗan wuta ba ne"

Sai da ya sa na zauna kusa da shi sannan ya fara min bayani bayanin da ya shigeni farat ɗaya saboda Hamma na ne ke min su. Tambayoyi kam ya sha su wassu ya amsa wassu ya ce bai sani ba amma zai tambaya.
Tambaya ta ƙarshe da na ma sa shi ne " Hamma wai inji Jiji idan ka taɓani zan yi ciki, da gaske ne?"...

Sai da na shekara ɗaya da fara al'ada kafin Sanah ta fara. Da ke tun lokacin dana fara ana cewa na girma sai abin ya shige ni, sai na dinga tsokalarta ai na rigata girma. Wata rana da na isheta sai ta ce "ai nono na sun fi na ki"

Ranan na wuni gaban madubi ina duba kai na ina ganin 'yan ƙananun nono na wanda na san tabbas ba su kai na Sanah girma ba.




*TSOHUWAR💖SOYAYYA*


*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Free page

0️⃣7️⃣


*...........Sa'eed.........*
Feelings

Shekaru bakwai kenan da zuwa na Maiduguri. Wannan gari mai Albarka ya zame mun tamkar asalina. Ina jin daɗin garin, ina kuma son garin sosai. A shekaru bakwai ɗin nan sau uku na je ƙauyen mu, na farko lokacin da Inna ta ta rasu shekara ɗaya bayan na zo Maiduguri mu ka je ta'aziya tareda Jijiɗo. Na biyu mu ka je da Baffa Manu lokacin da mahaifiyar sa ta rasu, sai na uku wanda ya zamo min wani tarihi mai muhimmanci a rayuwa ta.

Ina shekara shatakwas, lokacin ina aji biyar a sakandare mijin babbar 'yar Jijiɗo ya rasu, lokacin ana hutu sai ya zama na tare mu ka tafi.
Ban sanar da Aaliyah ba saboda sun tafi Lagos bikin wata cousin ɗin su.

Su na dawowa daga tafiyar su, ko cikin gida ba ta shiga ba ta yiwo wajen mu da gudu. Kwana biyar kenan ba sa gida.
Da ta zo ta samu ɓangaren mu a garƙame da kwaɗo. Ta shiga wajen su Mama John ta tambayi ina mu ka je. Mama John ta ce mun tafi ƙauye an ma na rasuwa.

Daga wajen ta fara kuka ta shige gida da kuka. Kai tsaye ta je ta fara haɗa kayanta, da ta gama ta fito da jaka ta samu Amma a ɗaki tana baccin huce gajiya.

Yadda ta ke ƙwala sunan ta ya sa tun kafin ta shigo ɗakin Amma ta farka.

" Aaliyah ki na so na zane ki ko? Yaushe mu ka dawo za ki fara damuna da shirmen ki"

Cikin kuka ta ce "Amma wai Hamma da Jiji sun tafi ƙauye, zan bi su"

Takaici ya sa Amma ta ce " Allah ya kiyaye"

Aaliyah ta fito da jaka ta nufi gate. Ma su gadi sun tafi Sallah, Ɗaya Maigadin da baya sallah kuwa ya kwanta a kan benchi yana hutawa bacci ya tafi da shi.  Ta je ta buɗe ƙaramar ƙofa ta fita.
Taxi ɗin da ta tsare tace da shi ƙauyen Durum zai kai ta. Ganin kayan jikin ta ya san 'yar gidan manya ce. Ƙarancin shekarunta da rashin wayo da ya bayyana a fuskar ta ya sa ya gane ƙila guduwa za ta yi. Ya ce ta shigo.
Su na tafiya ya fara ma ta tambayoyi akan mi za ta je yi a Durum, shi da ko sunan ƙauyen ma bai taɓa ji ba sai lokacin.

"Zan je ganin Hamma da Jiji ne"

"Ayya 'yan mata, Ashe ki na son Hamma da Jijin na kin nan sosai. Amma ban ga kin ɗauka mu su tsaraba ba, na ga kamar jakar kaya ne a hannun ki"

Aaliyah ta dafe kai "oops ai na manta. Mu koma gida sai na ɗauko mu su tsaraban Lagos"

Dama abinda mai taxi ɗin ke so kenan.

Lokacin da ta ce gidan Alhaji Badamasi Bulama zai kai ta sai da yai mamaki.

A ƙofar gate  ɗin gidan ya tsaya ta fita da gudu ta fara buga gate ɗin. Mr Francis ya leƙo ta ɗan ƙaramar ƙofa da akayi ajikin gate ɗin sai ya ga Aaliyah.  Da sauri ya buɗe ma ta ƙaramar ƙofa ta shigo, yana ma ta magana ma ita kan ko ajikin ta tsarabar Hamma da Jiji ne a gaban ta.
Lokacin da ta fita daga taxi yai dai-dai da karyowar kwanar motar Alhaji Badamasi. Tsayawa su ka yi dreban sa ya fita ya je ya kirawo mai taxi ɗin. Mai taxi ya zo jikin window jikin sa na rawa duk da kuwa shi niyyar sa da Aaliyah ta shiga sai ya miƙawa ma su gadi jakarta ya kuma gaya mu su abin da ta ke niyyar yi. Sai dai abinka da ma su kuɗi yanzu sai a fassaraka da wani manufar.

Bayan yai wa Alhaji Badamasi bayani Alhaji ya fito da kuɗi ya bashi sannan ya ce dreban sa ya ɗauko jakar Aaliyah...

Aaliyah tana chan tana haɗa tsaraba ba ta san mi ake ciki ba sai da ta fito falon su ta ga Alhaji zaune ga jakarta a falon.

"Kiramin Amman ki"

"Baba zan je wajen Hamma da.."

"Je ki kiramin ita na ce" ya daka ma ta tsawa.

Ta juya da gudu ta tafi. Lokacin da Amma ta fito faɗa ya fara ma ta akan tana ina Aaliyah ta haɗa kaya har ta fita daga gidan nan wai za ta je ƙauye ba ta sani ba.

"Alhaji na ɗauka shirme ta ke yi ai"

"Shirme? Idan da wani abu ya sameta nan za ki gane shirme. Ba na son irin  wannan sakacin Mariya. Aaliyah ta fara girma ki sa ido akan ta" daga haka ya fita, haƙurin da Amma ke ba shi ma bai saurara ba.

Wannan ranan Aaliyah har mari sai da ta sha a wajen Amma.

Aaliyah ta ƙauracewa cin abinci, ranan farko Amma ba ta damu ba ta ce idan yunwa ya cita za ta nemi abinci da kan ta. Rana na biyu da yamma mai'aiki ta samu Amma da cewa har yanzu Aaliyah ba ta ci abinci ba kuma ta ki buɗe ƙofa.

"Yarinyar nan ba za ta kashe ni ba, ni kam ko Jijiɗo mayya ce wannan abu da mi yai kama"

Extra key ta nemo ta buɗe ƙofar ɗakin Aaliyah, anan ta ga Aaliyah na kwance zazzaɓi ya rufeta. Ranan Aaliyah sai kwanan asibiti.

Amma ta yi faɗan har ta gaji amma Aaliyah ta ƙi cin abinci, sai da aka kira Alhaji Badamasi wanda ba ya gari ma lokacin. Aka bawa Aaliyah wayar tarho su ka yi magana da Baban na ta, ya ma ta alkawari da ta ci abinci ta warke za a kaita wajen Jiji.

Hakan kuwa aka yi. Duk da Alhaji yana da 'ya'ya mata amma Aaliyah yarinya ce mai shiga rai, ta kasance 'yar gaban goshin Baban ta.

Kwana uku da murmurewan ta Alhaji ya sa aka tsara ma ta tafiyar.  Dreba aka sa ya kawo su Bauchi zuwa Toro zuwa ƙauyen mu Durum. Ita da Sanah, saboda itama ta ce za ta je.

Ina zaune kan wani dutse kusa da rafi ina karatu kamar daga sama na fara jiyo muryan Aaliyah "Hamma Sa'eed, Hamma Sa'eed"

Na ɗan girgiza kai na, dan a ganina kunnena ke min ƙarya.  Ta ya zan ji muryan Aaliyah a nan, bayan Aaliyah ta min nisa.
Sai dai wannan kira sai ƙara kusantoni ya ke. Na ɗaga ido  sai na hango Aaliyah tana gudu, hular ta a hannu tana sanye da doguwar riga irin ta turawa  wanda aka fi kira da 'yar kanti a lokacin, rigan ya tsaya iya silangarin ƙafarta. Iska na kaɗa dogon gashin ta tana dariya. Na tsaya kawai ina kallon ta, sai ya zama kaman ranan ne na fara ganin ta lokacin tana shekara bakwai, sai dai yanzu wannan yarinya ta zama budurwa she's  now 13. Ban motsa a wajen ba ban kuma ɗauke ido na akan ta ba har ta iso.

"Hamma ta ya ka hau dutsen nan? ya yi tsayi dayawa" ta faɗa tana haki.

"Tsaya barin hauro da ke"  na faɗa ina mamakin ganin ta.

Ina saukowa daga dutsen domin na hauro da ita kawai sai ta faɗa jiki na. A da duk lokacin da ta rungumeni ba na jin komai ko dan akwai ƙarancin shekaru ne, ko dan kuma da ɗin bana jin abinda na ke ji gameda Aaliyah yanzu.

"Hamma i miss you, shi ne ka tafi ka bar ni ko" ta faɗa tana ƙara shigewa jikina.

A lokacin ji na yi na shiga wani hali na daban, wani yanayi wanda ke da wuyar fassarawa. Ban san ya akayi kalmomin su ka fito a baki na ba " I miss you more Aaliyah"

Mu ka zauna a saman dutse  tana bani labarin yadda akayi har aka bari ta zo. Tana cikin labari na karɓi hular hannunta na sa ma ta aka na ce "Aaliyah ba na hana ki barin gashi a buɗe ba"

Ta turo baki " Hamma ni kam"

Mu ka zauna a saman dutse kusan awa ɗaya da 'yan kai muna hira. Da magriba ta gabato mu ka koma gida.

Sati ɗaya Aaliyah ta yi a ƙauyen mu. Kullum mu na fita na nuna ma ta yadda ƙauyen mu ya ke, mu je gona, mu je kiwo tare, mu je rafi. Aaliyah was so excited and fascinated with my village, ni kuma na fi kowa farin ciki da zuwan ta.

Da su ka yi sati dreba ya dawo ɗaukan su saboda makaranta da za a koma. Mu ma albarkacin Aaliyah mu ka shiga mota aka tafi da mu.

Wannan rikici da Aaliyah ta yi kafin a barta ta zo ƙauyen mu shi ya jawo Jiji ta fara ja baya da Aaliyah hakanan ni ma ta min faɗa akan na rage mu'amala da Aaliyah saboda yanzu ba yarinya ba ce.
Sai dai Aaliyah idan tana son abu ba mai hanata. Duk wani hannunka mai sanda da Jiji ko ni ke ma ta kamar ba ta san ma munayi ba, sai ma ƙara shige ma na da fa ke yi.
Ni kam na shiga wani hali domin kuwa zuciyata ta na jin wassu sabbin shauƙi gameda Aaliyah, zuciya ta tana raya min wani al'amari mai daɗi gameda Aaliyah wannan al'amari da ya ke da kamar wuya. Amma ko da mafarkine to zan so na cigaba da yin wannan mafarki har ƙarshen rayuwa ta...

Kasancewa jarrabawata ta yi kyau sai aka awarding nawa scholarship karatu a Cambridge da ke ƙasar England.
Har falon Baba Aaliyah ta raka ni na nuna ma sa admission ɗin. Ya ji daɗi kuma ya sa min albarka. A wajen Aaliyah ta ce "Baba ni ma Cambridge za ka kai ni ko?"

Baba ya ce "duk inda ki ke so 'ya ta"...

A hankali ina ta shirye-shiryen tafiya har ya zama rana ta zo, gobe da safe zan tafi.
Kullum sai Aaliyah ta min ƙorafin zan tafi na barta ita ba ta so na tafi, wai na bari itama ta ƙare sakandare sai mu tafi tare. Ni kam kawai dariya na ke yi dan nima ba ta san ya na ke ji gameda rabuwa da za mu yi ba.
Da yamma ta zo muka  wuni a ɗakina da maghriba ta wuce cikin gida.  Ban ɗauka za ta dawo ba shiya sa nima ban dawo daga masallaci da wuri ba.  Wajen ƙarfe goma na shigo ɗakina sai na tarar da Aaliyah tana zaune tana jirana.

"Aaliyah dare ya yi, mi ki ka dawo yi?"

"Anan zan kwana" abinda ta faɗa kenan kai tsaye.

Na sani ta kan yi baccin rana a ɗakina, hakanan lokacin ba ta kai haka ba bacci kan ɗauketa a ɗakina da dare in ɗauketa in mai da ta gida ko Jijiɗo ta maidata. Amma yanzu Aaliyah budurwace she's 14.
Duk yadda na yi da ita ta tafi ta ƙi. I have no choice haka mu ka kwanta tare a gado ɗaya tun ina tunane-tunane har bacci mai daɗi ya tafi dani. The best sleep i ever had.

Washe gari Jiji ta ga Aaliyah ta fito daga ɗakina, Nan ta fara faɗa.  Ba dan tafiya zan yi ba da ban san irin masifar da Jijiɗo za ta min ba.

Dreban gidan Aaliyah ta sa ya kaini airport wanda tun cikin motan Aaliyah ke hawaye har muka isa. Nima daurewa kawai na yi amma ina jin yadda ta ke ji a ranta, ina jin ma fiyeda yadda ta ke ji....





*TSOHUWAR💖SOYAYYA*


*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Free page

0️⃣8️⃣

*.............Aaliyah.............*
Confession

Lokacin da Hamma Sa'eed ya tafi Cambridge, sai ya zamo kamar ya tafi da rabin jiki na ne sauran rabin kuma yana Maiduguri. Duk su Jiji sun ɗauka rashin ganin Hamma  zai sa na dena damuwa da shi amma abin bai zamo haka ba. Kullum na dawo daga makaranta ɗakin sa na ke tarewa wani lokaci na yi ta kuka, wani lokaci  na zauna na wuni ina kallon hotunan sa. Abin ta kai har kwana na ke a ɗakin sa duk da kuwa Jiji ta hana ni amma na ƙi ji. Itakam Amma ta yi faɗan har ta gaji ta sallama ni.
Lokacin da Yaya na Bukar ya tafi Oxford karatu mu kan yi waya da shi lokaci zuwa lokaci, amma Hamma tun ina irga kwanaki har na fara irga watanni ƙarshen shekara na baza ido ko zan ga Hamma kamar yadda Ya Bukar kai zuwa duk ƙarshen shekara amma ba Hamma ba dalilin sa.
Safiyar wata Lahdi ina karatu a ɗakin Hamma, Jiji ta shigo da murnan ta. Ta miƙamin wani envelope mai ɗan girma ta ce yanzu Baffa Manu ya kawo, an aiko daga post office wai na karanta mu su daga Sa'eed ne. Ai da sauri na farke envelope ɗin na fiddo da abinda ke ciki. Akwai wani envelope madaidaici wanda  ke ɗauke da sunana a jiki.
Ban san lokacin da na kissing envelope ɗin ba ina shaƙar ƙanshin jiki.  A gurguje na karanta ma ta abinda ya rubuto mu su. Gaisuwa ne da kuma bayanin yadda za su rinƙa amsan kuɗin da zai dinga turowa. Ina gama karanta ma ta na yi waje da gudu. Ban tsaya sauraron wasu tambayoyin ta ba balle na amsa su. Ina zuwa na faɗa kan gado na ina maida numfashi. Finally Hamma Sa'eed ya turomin saƙo. Kenan bai manta da ni ba, kamar yadda ni ma kullum ya ke rai na. Sai da na samu na nitsu sannan na buɗe envelope ɗin na fiddo da takardu goma shabiyu da ke ciki. Na fara karantawa ɗaya bayan ɗaya saboda ya sa number a jiki. Taƙaitattun bayanai ne akan yadda shekara ɗayan nan ta kasance ma sa a Cambridge ba tareda ni ko su Jiji ba. Duk inda ya rubuta *i miss you Aaliyah* sai na bi wajen da kiss. Haka na sa letters ɗin nan a gaba ina karantasu ina sake maimaitawa...

Shekara na biyu ya zo min da sauƙi saboda mun yi musayar letters har sau shida. A wannan shekara na yi jarrabawar Waec ina aji biyar. Babban abinda ya fi sa ni farin ciki da kammala jarrabawar nan bai fi tunanin tafiya Cambridge da zan yi ba. Ina tunanin zan kasance tareda Hamma na.

Sanah Oxford ta zaɓa ni kuma na zaɓi Cambridge duk da ma dai Baba ya so mu tafi waje ɗaya tunda tare mu ka taso amma kowa da ra'ayin sa. Ita Sanah tuntuni Oxford ta ke son zuwa ni kuma tun lokacin da Hamma ya samu scholarship a Cambridge na sa wa raina Cambridge zan je.

Abu ne na 'ya'yan ma su kuɗi. Ko ina za ka je indai ana zuwa to ba matsala ba ce a wajen ma su arziƙi. Baba ya sa aka fara ma na shirye-shiryen tafiya. Ni excitement ɗi na ba na makarantar da zan je bane sai dan ganin Hamma da zan yi after 2yrs da ba ma tare.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka  sama mana admission aka arranging ma na komai hatta wajen da zan zauna an shirya komai. Ranan tafiya ta zo, Baba da kan sa ya raka ni airport abunka da shalele, da ke ba tare za mu tafi da Sanah ba ita sai nan da sati uku.

Ban sha wahalar komai ba saboda an riga an shirya wanda zai ɗauke ni tundaga airport ya kaini gidan da zauna. Gidan flat ne ɗaki ɗaya da falo sai kitchen. Ba abinda ke raina illa na ga Hamma, ko ya ya ƙara girma yanzu oho.
Mun riga mun tsara inda za mu haɗu a cikin makaranta idan na zo. Ba tareda hutawa ba na ce da wanda ya kawoni gida akan ya kaini makaranta. Baturen Mr Wallace ya nuna na huta yau gobe sai muje ya nuna min yadda zan ƙarasa registration. Na mai fau-fau akan dole sai mun je makarantar. Ba mu su ya amince, tunda kuɗi aka biya shi ya kula da ni...

Kaman yadda na haddace sunan Hamma Sa'eed haka na haddace sunan address ɗin garden ɗin da za mu haɗu. Ba tareda ɓata lokaci ba Mr Wallace ya kaini wajen. Dai-dai wajen fountain ɗin da ya ce zai zauna ya jira ni dai-dai nan na tsaya amma banga Hamma ba. Na tsaya a wajen ina irga saukar numfashina, wanda ke sauka da sunan Hamma Sa'eed. Ban fi minti goma da zuwa ba amma gani na ke kamar na fi awa ɗaya.  Tun ina sa ran zan ganshi har na fara jin ko dai ya manta ne, ko dai baya son ganina ne ko dai... hawaye su ka fara sauko wa daga ido na. Ina zaune sanyin ruwan da ke ɓulɓula daga fountain ɗin yana ratsa ni amma ni zafi na ke ji.
Daga ta baya na aka sa hannu aka rufe min ido, na sa hannu na taɓa hannun da ya rufe min ido, nan ta ke farin ciki ya mamaye ni. Shekara biyu amma ban manta yadda ɗumin hannunsa ya ke ba.

"Hamma" na faɗa ina ƙoƙarin cire hannunshi da ga fiska ta.

"Miye na kukan kuma?, kwata-kwata minti shabiyar ki ka yi a nan har kin gaji da jira"

Na juyo da sauri and there he is. Hamma Sa'eed ɗina, sai dai wannan ya ƙara ƙiba ya kuma ajiye gemu. Murmushin sa mai rikitata tunani na shi ne shimfiɗe a fiskar sa.
Kallon sa na ke yi ido cikin ido duk da yanzu ina jin wani abu na tasowa daga chan ƙasan zuciyata lokacin da na ke kallon sa. Ban sani ba ko tunda ɗin akwai wannan abun ko kuma yanzu ne da na girma na ke jin wannan abin ko kuma saboda munyi shekara biyu da wata huɗu ba tareda mun ga juna ba ne.
A hankali na tashi ina cigaba da kallon sa, gani na yi ya ƙara min tsayi, sai na ganni 'yar guntuwa a kusa da shi duk da kuwa a cikin shekaru biyun nan nima na ƙara tsayi.  Hannu na sa na shafa fiskar sa ina ƙara tabbatarwa kai na finally Hamma ne a gaba na. Har lokacin bai dena murmushi ba. A hankali na shiga jikin sa ina dariya. Shima ya sa hannu ya ƙara jawoni jikinsa sosai ya ɗan ranƙwafo kan sa ya ce " finally"

Mun jima a haka har ban san adadin lokacin da mu ka tsaya a wajen a haka ba, har cikin raina so na ke mu cigaba da kasancewa haka. Lokacin da za mu bar wajen bayan Mr Wallace ya zo akan yana so ya maidani gida cewa na yi dole Hamma ya goyeni ya kai ni wajen da aka yi parking motar.

"Aaliyah yanzu kin girma fa"
Na tuɓure na ce ban san wannan ba ni dai dole ya goye ni. Ban san miyasa Hamma ba ya son musu ba, ko dan tun asalin sa ba wai yawar magana ba. Haka a wajen nan ya tsugunna ni kuma na hau bayan sa, abin ya burge Mr Wallace har ya sa ya je ya karɓo wani camera a wajen wa su masoya da su ke ɗaukan hoto a gefen mu. Ya ɗauke mu hoto ina bayan Hamma yana dariya ina dariya.
Wajen da aka ajiye motar ba ƙaramin nisa ne da shi ba amma haka Hamma ya jure ya kaini har wajen. Abinka da ƙasar waje ba wanda ya damu balle a tsaya a muku magana. Kallon mun burge sosai ma ake ma na...

Ba zan iya tuna rana ɗaya da ba mu haɗu da Hamma ba tun daga wannan rana duk da kuwa abin da mu ke karanta ba ɗaya ba ne, kuma wajajen ɗaukan karatun mu ba sa kusa. Idan ba mu haɗu a makaranta ba to dole zai zo gidana, duk yadda na dameshi akan ya tattaro ya dawo gidana sai ya ce min a'a tun ina fushi akan haka har na dena.
Wata rana maƙociyata Cassandra wadda ake kira da Cassy ta gayyaceni birthday party ɗin saurayin ta. Da ke bayan Hamma, Cassy ita ce wadda na shaƙu da ita tun zuwana Cambridge.
Na bar wa Hamma saƙo akan idan ya zo na fita tareda Cassy da ke ya san inda na ke ajiye ma sa key.

Ƙarfe bakwai na yamma mu ka fita daga gida amma kafin mu isa wajen da ake party ɗin ma sai tara saura domin chan bayan gari ne

Please Login or Register in order to submit comment