You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje, ina da sanin Ahmad na shaye-shaye kuma na yi iya ƙoƙarina a kan sa. Da farko na so janye batuna lokacin da kika dawo daga makaranta amma mahaifinki ya nuna min ba matsala domin kun riga kun saisaita kan ku da Ahmad ɗin.
Wallahil Azim ba zan bari a zalince ki ba, idan har ba kya son zama da Ahmad zan sa ya sawwaƙe mi ki yanzun nan.
Ban taɓa tsanar abinda Amma ta sa aka min ba sai wannan lokaci. Ba na son Ahmad kuma ba na son auren shi amma ba zan iya rabuwa da shi ba haka na ke ji a raina. Wannan dama da na samu haka ya wuce ni domin cewa na yi zan zauna da Ahmad ina da yaƙinin zai gyaru watarana. Alhaji ya min godiya tareda addu'a ya kuma sanar da ni ya ɗau mataki akan Inna ba za ta sake min mugunta ba. Da ya tambayeni ko ina da abin da na ke buƙata sai na ma sa maganar Sanah. Na roƙeshi akan yai wa Baba magana ko zai amince Sanah ta auri Sadiq Abbori. Ya min alƙawarin zai yi iyaka ƙoƙarin sa ya ga ya sasanta Baba da Alhaji Abbori ko za su amince su zama sirikai....


Baban miji na yai min gata, domin kuwa washe gari aka kawo min 'yan aiki guda biyu Salamatu da Uwale, sannan Alhaji ya ce idan ya wuce gaisuwa bai yadda na yiwa Inna wani bauta ba. Ahmad kam ina ga faɗan da aka ma sa ya sa ya ji haushi ya bar gidan, domin bai dawo ba sai da yai sati biyu cur.

Waɗannan sati biyun ba ƙaramin murmurewa na yi ba, ba inda na ke fita daga ɗaki sai falo. Ma su aikina kuma su na da kirki, mu kan zauna mu yi taɗi sosai da su, tun suna ɗari-ɗari da ni har su ka saki jiki da ni. Mutane rahama ne, ka zauna da wani ku yi hira shima yana ƙarawa mutum annashuwa da farinciki. Hiran da ban taɓa samu a wajen mijina ba kenan. Inna ma ganin Alhaji na gari ya sa ta fita harkata, ba ta zo wajena ba bata kuma aiko an kirani ba...

Tun da na ji muryan sa a falo raina ya jagule saboda na san baccin daɗi da na ke yi kwana biyu sun wuce ni kenan. Na ƙi fitowa ƙasa kamar yadda na saba, ina zaune a kan gado ya shigo ɗakin.

"Sannu da zuwa" na faɗa a hankali dan na san idan ban faɗa ba ma sai ya tambaya. Ya jawoni jikin sa ya ce " kin yi missing ɗina kuwa? Ni kan na yi missing ɗin ki sosai, matan Lagos duk fanko ne. Ba ta inda su ka kamo ƙafarki, idan zan yi tafiya dole na dinga tafiya da ke"
Banji haushin neman matansa ba kamar yadda na ji haushin yadda ya maida ni sex object ɗin sa, wato ni ban da wani amfani sai wajen sex. Na daure na ce " ni ma idan an kwana biyu zan koma fanko kamar su"

"Never, never" ya faɗa ya na ɗakar bayana daga nan kuma ya shiga sarrafani kamar yadda ya saba...

Na samu sauƙin wahalar aiki amma ban samu na kwanciyar aure ba domin duk daɗin da Ahmad ke magana akai shi kaɗai ya ke jin kayansa ni kan wahala kawai na sani.
Ranan da safe Alhaji ya kirani dana je ya min maganar aiki na ce ma sa ai ban ma gama bautar ƙasa na ba, ya nuna min ba matsala zai yi wani abu a kai. Ashema tuntuni Baba ya sa an maidani Sokoto amma kuma ba na zuwa ko'ina. Sati ɗaya da maganar mu da Alhaji na fara fita aiki a wani gidan jarida.
Maganar sasanta Baba da Alhaji Abbori kam bai yiwuba dan maganar ne ma ya sa Baba ya speeding maganar auren Alhaji Bukarti da Sanah. Duk inda Alhaji Wamako ya fito waɗannan maƙiya sun ƙi sauke girman kai su rungumi soyayyar 'ya'yan su. Wata uku aka sanya bikin Sanah wanda da ƙyar Baba ya sa shi da nisa domin shi ya so ayi bikin nan kusa a wuce wajen kawai. Sai dai Hajiya Yana ta nuna a bari sai wata uku saboda bikin zai yi kusa da na wasu cousins ɗin mu biyu da za ayi. Yadda bikina yai fice yai suna a family ita ma haka ta ke son bikin 'yarta yai, dan haka aka sa shi wata uku...

Ranan wata Jumma'a Alhaji yai baƙuwa a office ɗin sa. Wata tsohuwar 'yar aikin marigayiya matar sa Jamilah ce. Magaret ta zo gaban Alhaji tana kuka tana neman yafiyarsa bisa mummunan laifin da ta yi ma sa, da ya nemi jin laifin sai ta ce ma sa Inna ce ta ba ta magani ta sawa Jamilah a abinci, da farko ta ƙi amma Innar ta yi barazanar kasheta idan har ba ta aikata abin da ta sa ta ba. Magaret ta ce abincin nan da ta ci ne ya sa ta kama ciwon ciki daga nan sai naƙuda gadan-gadan wanda ƙarshe ta mutu wajen haihuwa. Alhaji ya shiga tashin hankali yana kuka yana neman tsari daga muguwar matar sa Hajiya Inna. Cikin tashin hankali ya baro office ya taho gida, dreban sa ya shigo da shi nima na shigo da motata saboda dawowata kenan daga wajen aiki. Na ce barin gaisa da shi kafin na wuce gidana sai kuma na ga Alhaji ya fito daga mota fuuu hankalin sa a tashe. Na bi bayan sa da sauri ina tunanin ko lafiya.

A falo ya samu Inna tana yiwa ma su aikinta faɗa, tana ganin yanayinsa ta sallamesu tana tambayar sa ko lafiya.
"Asma'u akan me? Me ta miki kika sa a kasheta?"

Inna ta zaro ido ta ce "wa kenan?"

Tari ya fara sannan ya ce "JJJJamilah"

Ta ja tsaki ta ce " na ɗauka ma Aaliyah ka ke magana dan ina gab da kasheta."

"Asma..." Alhaji ya riƙe ƙirji yana tarin jini.

"Jamilah tsohuwar gawa ce ai, kuma saboda kai na kasheta. Ta haifi ɗaya biyu duk bai isheta ba sai ta ƙara, gara ta je ta haifa a lahira idan ana haihuwan a can"

"Inna Alhaji" na faɗa ina yin kan Alhajin da gudu wanda ya faɗi yijib a wajen...

Wasu matan duniya da dukiya sun rufe mu su ido kuma za su iya yin komai saboda su gaje gidan mijin su. A hannuna Alhaji ya ƙarasa cikawa wanda hakan ya gigitani. Yadda na shiga tashin hankali ita da mijinta ya rasu ba ta wani nuna damuwarta akai ba...

Lokacin da mu ka je asibiti aka tabbatar mana ya riga ya cika, dama Alhaji yana da hawan jini kuma shock ne ya kasheshi ni kuma na ce Inna ce ta kashe shi.
Mutuwar Alhaji Ibrahim Wamako ya zo da sauye-sauye dayawa wasu na daɗi wasu ba daɗi.

A rana ta biyu da rasuwan Alaja da sauran 'ya'yansa su ka zo. Na yi mamaki da na ga Ahmad ya yi kuka lokacin da ya zo ya samemu a asibiti na ɗauka shima ɗin kamar Inna zai yi farin ciki ne amma sai na ga saɓanin haka. Baba ma wannan mutuwar ce ta sashi ya risina har ta kai ya gaisa da Alhaji Abbori a wajen ta'aziya...

Sati biyu da rasuwan Alhaji Wamako, Alhaji Abbori ya samu Baba akan maganar auren Sadiq da Sanah. Cikin Ikon Allah ya sa mutuwar Alhaji ya sa Baba ya risina musamman da ya tuna yadda Alhaji Wamako yai ƙoƙarin sasanta tsakaninsu kafin rasuwar sa. Baba ya amince da maganar auren bayan ya nemi Alhaji Bukarti ya janya neman, dama shima yana fama da matansa da su ka tisa shi a gaba saboda auren da ya ce zai yi...

Sanah ta taki sa'a ba kamar ni ba.
Yau ina tareda Alaja a falo lawyer ɗin Alhaji ya shigo. Bayan sun gaisa da Alaja ya faɗi abinda ya kawo shi, wai Inna ce ta ke so a raba gado. Ni da Alaja mu ka kalli juna cikin mamaki domin yau ne kwana goma shatara da mutuwar Alhajin.
Dole ta ce a raba gado mana tunda ita ke da 'ya'ya dayawa, ɗa namiji guda da 'ya'ya mata shida.
Alaja ta kalli lawyer ta ce ciki gareta dan haka maganar gado sai ta haihu. Ni kaina sai da ta yi maganan cikin na tabbatar da zargin da na ke ma ta tun kafin ma ta tafi Lagos. Fitan Lawyer daga falon ko minti biyar bai yi ba Inna ta shigo falon tana masifa wai ba za ta yadda da wannan ƙaryan ba. Idan ma wani salon yaudaran ne gara ta dena dan ba zai yiwu ba. Alaja ta miƙe tsaye ta ce "Asma'u ke gado ya dama ba ni ba, amma ki sani sai na haihu ayi batun gado domin cikina yana wata na biyar ne yanzu, kuma zai zo duniya da yardar Allah" daga haka ta bar wajen.

Inna ta sa ihu tana zage zage har da kiran Alaja da Ashawo.

Ni kam na riƙe baki ina ganin yadda Inna ta maida kanta mahaukaciya saboda dukiya, dukiyar da shi Alhajin ma haka ya mutu ya barshi ba tareda ya ɗau komai ya tafi da shi makwancinsa ba...







19-The new bride

A



Abu ƙarami sai ga shi ya zama babba, Alaja da Inna da ya kamata su zauna su yiwa Alhaji takaba cikin kwanciyar hankali sai ya zama kullum cikin case ake yi a gidan. Abu ta kai har manyan mutane sai da su ka shiga ciki. Dama duk cikin 'yan uwan Alhaji ba wanda Inna ke shakka, da akwai wani yayansa Alhaji Abbas da ta ke mugun tsoronsa amma Allah ya ma sa rasuwa kusan shekaru goma da su ka wuce.
Ƙarshe da na ga abin ya zama haka sai na bawa Alaja shawara akan ta janye ƙudirinta ta bari a raba gado idan ya so sai a bar kaso biyu wanda za a ajiyewa jariri ko jaririyarta. Ni tsorona kar Inna ta sa a kashe Alaja tunda da kunnena na ji tace saboda gado ta kashe Jamilah matar Alhaji.
Alaja ba wai gadon ne ya dameta ba kawai dai ba ta so ta ragewa Inna abin da ya ke hakkinta ne da na 'ya'yanta. Ganin ba ta fahimceni ba ya sa na fito ma ta da gaskiyar abin da na ke tsoro da kuma abin da na ji ranan da Alhaji ya rasu. Duk haƙurin Alaja wannan information da ta ji ya sa ta tunzura sosai, ta ɗau alƙawarin maka Inna a kotu a bi hakkin Jamilah da Alhaji. Ni da na faɗa mata dan ta saduda ta haƙura da komai sai ya zamana na jawo wani masifan ne.
Alaja ta fara bincike sosai har ta gano inda Magaret ta ke, har da ni mu ka je muka haɗu da Magaret wanda ta zayyane mana komai tareda alƙawarin za ta ba da shaida a kotu saboda gaskiya ta tuba tana son samun ceton Yesu dan haka za ta faɗi gaskiya a ko'ina. Ni dai tunda Alaja ta fara bincike na ke jin tsoro amma na daure na cigaba da tayata da addu'a.
Ranan ina zaune a ɗaki ina haɗa report sai ga Ahmad ya shigo, yana zuwa ya jawoni daga kan gado ya fara dukana ta ko'ina bugu ya ke yi zagin da ya ke min da maganganun da ya ke faɗa ya sa na gane ba wai dukan sha'awa ya ke min ba. Sai da ya ga na daina motsi ya fita daga ɗakin. A ƙalla na kai kusan awa uku kafin Salamatu ta shigo ɗakina ta ganni kwance a haka. Ta fara salati tana ƙwalawa Uwale kira, suna shirin kaini asibiti na ce su barni. Su ka taimakamin na kwanta akan gado zazzaɓi mai zafi ya rufeni. Daga baya da Alaja ta zo ta ga halin da na ke ciki ta ce yanzu kam bayan Inna har Ahmad za ta yi ƙara saboda abin da ya ke min. Na dinga roƙonta akan kar ta yi ƙaran Ahmad, mutane za su zargeta. Da ƙyar ta haƙura da maganar. Ban gaya mata saboda ita Ahmad ya dakeni ba, domin an kai wa Inna takardar sammaci daga kotu shine ya zo ya sauke haushinsa a kaina wai har da ni acikin wannan munafurcin.
Da na san maganar nan shi zai yi sanadiyar ajalin Alaja da ban yi ba...

Bayan Ahmad Inna ma ta zo gida ta min tatas tareda min alƙawarin idan ta gama da Alaja za ta dawo kaina...

Da ƙaton ciki haka Alaja ta je kotu ranan da aka yi zaman farko, cikinta ya shiga watansa na tara kenan haihuwa ko yau ko gobe. Ba na wajen saboda Ahmad ya hanani fita, tun wancan dukan da ya min ma ya hanani fita ko'ina, har wajen aiki na dena zuwa.

Bayan an gama zaman kotu na ranan aka ɗaga zama zuwa sati biyu ma su zuwa saboda a ƙara bayyana shaidu. Lafiya-lafiya Alaja da ƙanwarta da ke zama tareda ita Madam AdeKumbi su ka shiga mota, da ke family ɗin su mix ne ita cousin ɗinta Kumbi christian ce.  Dreba ya wuce da su gida. Ba su jima da barin kotun ba motar su ta yi hatsari ta kama da wuta. Dreban da Madam Kumbi a take su ka mutu amma ita Alaja sai da aka kaita asibiti da kusan awa ɗaya kafin ta cika. Ana ƙoƙarin shiga da ita theater room a ciro ɗaya yaronta da ke motsi amma da aka sake scanning aka ga shima ɗin babu rai. Haka Alaja Barakat Atinuke ta mutu da ita da 'yan biyunta.

Nikam da labarin mutuwar Alaja ya riskeni sai da na suma saboda gigicewa da na yi. Kafin yamma an kai dreba da Alaja makwancin su yayinda 'yar uwarta Madam Kumbi kuma aka kai mortuary saboda a Lagos 'yan uwanta ke son bisine ta. Kwana biyu ban gane kaina ba. Wannan mutuwar sai ta fi girgizani fiye da lokacin mutuwar Alhaji. Satin da aka yi rasuwan sati na gaba ne bikin 'yar uwata Sanah sai dai har bikin ya zo ban je ba. Na farko saboda mutuwar Alaja da bai sakeni ba har ya sani jinya. Na biyu kuma saboda Ahmad ya hana, yadda gidan ya rikice tun mutuwar Alaja ya sa ba ya son na je ko'ina. 'Yan jarida su ka yi ta yin zirya a gidan ƙarshe dai magana ya wuce kamar ba a taɓa yi ba. Wata guda da mutuwar Alaja kotu ta wanke sunan Hajiya Inna. Maganan gado kam kamar Inna ce ta yi kason domin ɗan Alaja mai suna AbdulWahab bai samu komai ba. Tun rasuwar mahaifiyarsa ma da 'yan uwanta su ka tafi da shi bai sake zuwa ba hakanan ba su waiwayi 'yan uwan mahaifinsa da maganan gado ba.
Safiya ma ɗin Lagos ta koma idan ta zo Sokoto ba ta taka gidan Ubanta sai dai ta je gidan 'yan uwan Babanta a Wamako.

Babu Alhaji ba Alaja duniya sabuwa a wajen Inna. Ta shiga nan ta fita chan, ita da ɗanta kawai su ke sha'anin su. Inaga ma sun manta da ni a rayuwar su. Ahmad ba ya nemana sai ya bushi iska ita kuwa Inna dama she's too busy ne yanzu. A shekaran ta sake zuwa Hajji ta renewing haƙorin da ta sa. Ma su aikina tuni Inna ta fatattakesu ni kaɗai ke hidima ta a gidan. Kwatsam wata rana Inna ta shigo da masu aiki ta ce su fitar min da kayana su maida ɗakin da ke ƙasa ban ce komai ba na zuba musu ido kawai. Inna ta ce idan an gama kwashe min kaya zan koma ɗakin ƙasa domin an kusa kawo amarya. Na ce Allah ya kawota lafiya.
Idan da adalci ɗakuna huɗu ne a sama ɗaya nawa ɗaya na Ahmad sauran biyun ba wanda ke amfani da shi. Amma ni kan daɗina ma tunda amarya za ta zo wahala na za ta ragu musamman wajen Ahmad.

Sati biyu da wannan chanjin aka kawo amarya. Duk wani hidima da bidiri a ciki duk babu ni aciki ban ma san yaushe ne auren ba sai a bakin ma su aikin Inna. Aka yi biki aka ƙare, aka kawo amarya. Ranan sai ga kiran Amma tana ban haƙuri tareda yi min nasiha, da ta ƙare hiranta na ce na gode amma ta adana maganganunta domin ba na buƙatar su. Amma ta tsorata da amsata ta fara tambayana ko ƙalau na ke na ce ma ta ta gaida gida na ajiye wayar. Watana goma da kwana shaɗaya a gidan Ahmad ya ƙara aure...

Amarya Bilkisu 'ya ce guda a gidan Alhaji Ɗan iya, wani attajiri kuma hamshaƙin mai kuɗi a garin Bauchi. Bayan arziƙi har da sarauta domin shine Tafidan Bauchi.
Yadda ka san ƙwai haka Inna ke lallaɓa Bilkisu, daga gidan su ma da ma su aiki uku aka haɗota ga Inna da ta ƙara mata biyu. Sati ɗaya da biki ita da Ahmad su ka wuce honeymoon ƙasar waje. A yadda ma su aikinta ke gaya min sai sun yi wata biyu kafin su dawo amma idan har lissafina yayi dai-dai to satin su biyu su ka dawo. Bayan sun dawo kuwa rikici ya ɓalle a gidan, ban san miya haɗasu ba amma kuma a ɗan ƙus-ƙus da na ke ji halin Ahmad ne ya isheta ya sa ta dawo. Ranan ina ɗakina na ji faɗan Inna da Ahmad akan Bilkisun. Wai Bilkisu ta kawo ƙara akan yadda ya ke mata ba ta jin daɗi. Ina ji yana faɗin " ita Aaliyah ba Mutum ba ce? Duk yadda na je mata ba ta taɓa complain ba amma wannan duk abinda mu ka yi sai ta kwashe ta gaya miki"

"Ahmad, Dole mu lallaɓa Bilkisu domin ba dan Mahaifinta ba da ban kai matakin da na ke yanzu ba"

"I dont care. Ta ce ba ta son duka na dena, ta ce na dinga mata a hankali ina yi. Mi kuma take so? Ban sameta a budurwa ba did i complain? Sai ita ce za ta buɗi baki ta kai ƙarana. To hell with her, idan ba za ta iya daniba ta tafi dama ke kikace na aureta ba ni na ce ina son aure ba"

Ganin ɗanta ya birkice mata ya sa ta shiga lallashinsa daga ƙarshe ya fita ya bar mata gidan. Nikam na ce tukunna ma.

Bayan kwana biyu abubuwa su ka lafa amma ni kam ba abinda ya chanja min yadda Inna ke sani aiki haka Amarya za ta sani aiki duk da tanada ma su mata aiki a gidan. Ni kam i've accepted my fate shiyasa na ke bin komai a hankali, ɗaga ƙafar da na samu daga Ahmad ya min daɗi. Bilkisu ta san banida daraja agidan walau a wajen Ahmad ko mahaifiyar sa. Amma duk da haka kishi ta ke dani, ƙiri da ƙiri ta ce kishin kyauna ta ke yi, wai da tanada rabin kyauna da ba abinda zai sa ta tsaya da Ahmad, wai Ahmad ya yi kaɗan. Nikam sai dai kawai na girgiza kai kawai dan ba abin da zan ce...

Ranan da Ahmad ya zo wajena bayan ya gama lallasani na yi ƙoƙari na tambayeshi ina son zuwa gida. Sanah da mijinta za su koma Ƙasar Canada kuma rabona da ita tun lokacin mutuwar Alhaji. Rashin zuwa bikinta da na yi ya sa take fushi dani har da ta yi aurema ta ƙauracewa gidana.

"Mu ma za mu koma London Aaliyah, akwai gidan Alhaji achan kuma yanada hannun jari dayawa anan. Ina son barin ƙasar nan, this country sucks"

Wannan ne karo na farko da Ahmad ya faɗa min wani abu mai muhimmanci a tarihin auren mu

Na ce ma sa Allah ya kaimu...

Ina wanke-wanke ina murna saboda zanje gida for the first time bayan shekara ɗaya da aure na. Gobe ne tafiyar kuma Ahmad ya ce na yi sati ɗaya a chan. Hajijiya na fara ji wanda ya sa na dafe sink ɗin kitchen ɗin da sauri ina ƙoƙarin saita kaina amma duk da haka sai da na kai ƙasa. Na jima ina zaune har Mairo ta shigo ta sameni, ita ta taimaka min na tashi tace na koma gida za ta ƙarasa aikin tunda Inna ba ta nan. Na mata godiya na tafi.
Ina zuwa na bi lafiyar gado na kwanta. Haka ranan ta wuce mani a ɗaki domin gaba ɗaya wani kasala na ke ji, na kan ji hakan 'yan kwanakin nan amma kuma na danganta hakan da yawan ayyukan da na ke yi...

Da dare Ahmad ya zo wai zai min sallama. Dama tunda Bilkisu ta yi tafiya ya koma min. Ce ma sa ma banida lafiya ma ɓata baki ne dan haka na barshi.  Ya hau kaina ya fara riding ɗina kamar yadda ya saba, wani azaba na fara ji wanda ya jima ban ji haka ba idan yana sex dani tun ina jurewa har na fara kuka ina roƙon sa ya tashi a kaina. Da ƙyar ya haƙura ya tashi, ganin jini a ƙasa na ya sa shi tambayar ko lafiya. Dama dokar Ahmad ne ba a kashe wuta idan yana abunsa.

"Aaliyah kin fara period ne?" Ban kulashi ba dan tuni na suma. Ganin ban tashi ba ya sa ya ɗan ruɗe ya shiga jijjiga ni daga ƙarshe ya sa jallabiya ya naɗoni a bargo ya fito dani sai mota...

A asibiti na buɗe ido na ganni. Ahmad na gefe na fiskar sa da fara'a.

"Sannu Aaliyah, ina ke miki ciwo?" Na girgiza ma sa kai.
"Sannu kin ji. Barin kira Doctor ya duba ki"

Da Dr Munnir ya zo ne ya shaida min abinda ya faru kuma a nan na gane silar murmushin Ahmad ɗin. Wai ƙaramin ciki gareni kuma jiya ɗin na zubar da jini amma cikin bai fita ba yana nan. Dr Munnir ya ba da shawaran Ahmad ya rage sex da ni har sai cikin ya yi ƙwari.
Da mamakina sai na ji Ahmad ya ce " ai idan ka ce na barta sai ta haihu ma zan barta, for my son xan iya yin komai"

Haka Ahmad yai ta nan nan da ni a dole wai dan inada ciki. Ya sanar da Inna amma ba ta zo ba haka na yi kwana biyu a asibiti su ka sallameni. Da na dawo gida Inna ba ta yi murnan wai ina da ciki ba sai ma kwaɗayinta da ta nuna akaina. Wai dalilin barina da ta yi da Ahmad dan gadon da zan samu ne idan Baba na ya mutu. Ikon Allah ita ba mutuwarta ta ke hangowa ba sai na wasu.



20- London

A

A kwana na uku da dawowata Ahmad da kansa ya kai ni airport na shiga jirgi na wuce Maiduguri.  Da ke na gayawa Amma ina zuwa shiyasa aka aiko da dreba daga gida ya zo ya ɗaukeni. Tun a hanya na ke ganin chanje-chanje, sai ya ke min kaman shekara goma na yi ban zo gida ba.
Gidan mu dai bai chanja ba, na dai ga sabon fenti inaga a lokacin bikin Sanah aka yi. Kai tsaye sashen Amma na shiga ina ƙoƙarin yaɓawa kaina murmushin dole.

Ƙannena Yahya da Musa na samu a falo suna kallo, su na ganina su ka fara murna suka zo suka rungumeni. Sai na ga duk sun chanja mani sun ƙara girma sosai. Musa Kalim Auta ma ya yi tsayi sosai.

Muna cikin hira da su Amma ta fito daga ɗaki. Kallon-kallo mu ka tsaya yi da ni da ita. Ita tana min kallon na rame na lalace ni kuma ina ma ta kallon ƙiba da wani haske da ta yi.
"Amma na same ku lafiya?" Na faɗa bayan na janye Ido na daga cikin na ta.

Maimakon ta amsa sai ta jefo min da tambaya
"Aaliyah ba ki da lafiya ne? Kin ganki kuwa?"

Na yi murmushi ina murza yatsuna da su ka koma daga laushi zuwa tauri...

Ranan kowa ya ganni sai ya yi maganan da Amma ta yi. Dan a tunaninsu rashin lafiya ne kawai zai sa nayi wannan mummunan chanjawar. 
Da yamma lis na je gidan Sanah. Kwanciyar hankali da farinciki na tarar a gidanta, itama na da ƙaramin ciki shiyasa sirikarta ke lailayata kamar ƙwai. A wajen Mama uwar mijinta, Sadiq ne ɗan fari dan haka tana ji dashi, soyayyar da ta ke wa ɗanta shi ya raɓi Sanah. Saura sati ɗaya su bar ƙasar zuwa Canada dan a nan Sadiq ya samu aiki.
Duk wani faɗan da Sanah

Please Login or Register in order to submit comment