You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cire min kaya ta min wanka ta bani abinci, wani lokaci idan na dawo ban ganta a ɓangaren mu ba to gidan su zan wuce da gudu kamar yadda na ke kiran quarters ɗin su. Ba na taɓa yarda na dawo wani ya min hidima idan ba Jiji ba, duk ranan da Amma ta yi yunƙurin kula da ni sai na fara kuka, wani lokaci har da birgima akan dole Jiji ce za ta cire min kaya ko Jiji ce za ta min wanka ko bani abinci, randa na ishi Amma kuwa har mangareni ta ke yi.

Akwai wani lokaci ina shekara shida Jiji ta tafi ƙauyensu lokacin za a yi bikin 'yarta Nana, sati biyu su ka yi achan ba su dawo ba. Cikin sati biyun nan kuwa sai da nayi rashin lafiya mai tsanani, ta kai sai da na kwana uku ma a asibiti.
Harta Baba da bai cika zama a gida ba saboda yawan tafiye-tafiye sai da yai kwana biyar a gida yana kula da ni, hakan ya rage min kewar Jiji. Ranan da Jiji su ka dawo kuwa ai a  gidan su na kwana na ƙi komawa ɓangaren Amma na.  Jiji Allah bai ba ta yawan haihuwa ba, yaranta  mata biyu.  Lokacin da aka aurar da 'yarta ta fari ba ni da wayo gaskiya, dan Jiji ta ce lokacin ina shekara uku ne. Ina shekara shida kuma aka aurar da autar ta Nana. Abinka da fulani auren wuri duk aka mu su. Asma'u tana shekara shabiyu aka aurar da ita Nana kuma shauku, duk cikin su ba wanda yai makarantar boko.
Bayan bikin 'ya'yanta sai ya zamana ni ne kaɗai 'ya a wajen Jiji, tana sona sosai kamar 'yar da ta haifa a cikinta, hakanan nima ina sonta sosai.

.....................

Bazan taɓa mantawa da wannan rana a tarihin rayuwata ba, wata ranar jumu'ah a shekarar 1975 lokacin ina shekara bakwai a duniya. Na dawo daga makaranta ko cire uniform ban yi ba na yiwo gidan su Jiji saboda ban ga Jiji a sashen mu ba.
Ina shiga falon su na fara ƙwala sunan Jiji. Sai ganin wani yaro na yi ya fito daga ɗakin su Jijin ɗauke da radion Baffa Manu. Na ƙwalla ƙara na fara cewa "ɓayawo, ɓayawo,...Jiji ɓayawo a gidan ku" na fita da gudu na yi hanyar gate, ban tsaya ko ina ba sai gaban Baffa Manu. Ina haki na fara ce ma sa ga wani yaro ya shiga gidan su ya sace mu su radio. Da farko Baffa Manu bai gane ba sai daga baya ya gane ya fara dariya. Ina cikin yi ma sa bayani sai ga yaron yana tahowa inda mu ke. Na nuna shi da yatsa na ce "Baffa ga ɓayawon nan, ga shi chan da radiyon ka Baffa"

Baffa ya kalleshi yai dariya ya ce " ba ɓarawo bane Aaliyah, ɗa na ne"

"Ƙarya ne Baffa, ɓayawon radio ne fa"

Sai da Baffa ya jima yana min bayani kafin na gamsu ba ɓayawo ba ne musamman ma da na ga wannan yaron da ya zo  miƙawa Baffa Radiyon ya yi.

Abinda ban sani ba alokacin shine, wannan yaron ba radiyo ya zo sata ba, ba kuma wani abin daban zai sace ba illa zuciyar Aaliyah. Wannan fari dogo siriri kuma yanƙwanannen yaron ba radiyo ya zo sata ba illa Zuciya ta....




*..............SA'EED...........*
Fulani boy

Ƙauyen Durum shi ne asalina. Inda aka haife ni, iyaye da kuma Kakanni na.
Baffa na ya rasu ina shekara biyu a duniya hakan ya sa lokacin da Inna ta ta sake wani auren aka maidani gaban kaka na Modibbo.
Suna na Sa'eed Aliyu Modibbo amma kasancewar sunan Harɗon ƙauyen mu ne da ni shi ya sa ake kirana da Harɗo ko kuma Lamiɗo, yawanci ma anfi kira na da Lamiɗon.

Mahaifiyata ba a Durum ta sake aure ba, a Lame mijin da ta aura ya ke, shi ya sa na tashi ba uba ba uwa sai kakanni.

A shekarar 1975 Kakana Modibbo ya rasu lokacin ina da shekaru shabiyu a duniya. Kaka na bai haihu dayawa ba, yaran sa biyar, biyu maza uku mata.
Baffa Manu shi ne ɗan fari sai Goggo Ma'u, Baffa na sannan Goggo Sadiya da Goggo Aminah.
Da farko an shirya zan koma wajen Inna ta a Lame sai kuma Dadda wato Kakata ta nuna hakan bai dace ba kasancewa Innata ba ishashshen lafiya gareta ba, dan tunda ta yi haihuwarta na uku ta ke jinya. Ƙarshe Baffa Manu ya zo ya ɗauke ni ya tafi da ni Maiduguri inda ya ke aiki a chan.

Baffa Manu bai da niyyar yin nisa da Durum, sai dai auren sa da Hafsatu (Jijiɗo) shi ya sa ya tattara iyalinsa yai nisa da gida.
Baffa Manu ya taso gida ɗaya da 'yar ƙanwar Dadda wacce ake kira da Hebbini. Hebbini ta so Baffa Manu sosai hakanan Dadda ma ta nuna ita ta ke so ya aura. Sai dai shi kam ya jima da fara son Hafsatu kuma baida niyyar auren wata ba ita ba.  Da ƙyar da siɗin goshi Dadda ta amince ya auri Hafsatu, sai dai tunda ta shigo gidan Dadda ta ke takura ma ta. Zagi da habaici ga uwa uba mugunta Dadda ke wa Hafsatu, wanda ko lokacin da ta fara samun ciki sai da ta yi ɓari saboda rashin kwanciyar hankali. Cikin shekara ɗaya da auren Jijiɗo sai da ta yi ɓari sau biyu. Nan Dadda ta fara ƙorafi akan dole Baffa Manu ya auri Hebbini. Shi kam harga Allah ba zai iya ba dan yana son Hafsatun sa sosai. Daga ƙarshe da takura yai yawa ya nemi izini a wajen Modibbo ya ɗauki Hafsatu su ka bar Durum, bai tsaya a Jama'a ba ko Toro ko Bauchi sai ya lula har Maiduguri.

Tunda ya tafi sai da ya shekara uku kafin ya zo gida lokacin Baffa na zai yi aure. Da farko Dadda ta yi fishi da shi ta ƙi ma sa magana amma daga baya ta haƙura dan zuri'a ta shiga tsakaninsa da Jijiɗo dan 'yar su tana shekara biyu a lokacin...

..................

Wata Ranan Jumu'ah a shekarar 1975 kwana na ɗaya a garin Maiduguri ina zaune akan benchi kusa da Baffa Manu aka yi horn da mota, Baffa ya tashi ya je ya buɗe gate, motar ta shigo farfajiyar gidan. Ina zaune ina bin motar da kallo har ta tsaya. Ba ta gama tsayawa ma da kyau ba aka buɗe ƙofa wata ƙaramar yarinya 'yar shekara bakwai ta fito daga cikin motar da gudu tana dariya, kayan makaranta ne a jikinta ta riƙe ɗankwalin kayan a hannu tana gudu iska yana kaɗa ɗankwalin saboda ba ta riƙe shi da kyau ba. Dariyar da ta ke yi ya bayyana fararan haƙoran ta, haka nan gashin kanta baƙi mai yalwa ya ƙara haskaka fiskarta.

"Aaliyah ki tsaya" abinda ɗaya baƙar yarinyar da ta biyo bayan ta ke faɗi kenan sai dai inaaa, yarinyar ko waiwayowa ba ta yi ba gudu kawai ta ke fanfalawa tanayi tana dariya.
Haka na bi yarinyar da kallo har ta shige gida.

"Lamiɗo je ka ɗauko min radiyo na"
Muryan Baffa Manu ta katse ni daga nisan da na yi wajen kallon waɗannan yara...






*TSOHUWAR💖SOYAYYA*



*©Azizat*

Wattpad @000Azee


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Free page

0️⃣5️⃣


*..............Aaliyah.............*
A friend



"Ai sunum?" na ce da shi lokacin da na matsa ku sa da shi.
Kallona kawai ya ke ba tareda ya ce komai ba.

"Mi ye sunan ka?" Na maimaita tambayar da Hausa

"Aaliyah, Aaliyah ki zo in ji Baba"
Muryan Sanah ya doki kunnena. Idan akwai wanda na fi so bayan Jiji to Baba na ne, duk da ba wai muna ganin shi kullum ba ne amma duk lokacin da ya ke nan to ina son kasancewa da shi. Haka na ruga da gudu ba tareda wannan ɗan fulanin ya gayamin sunan sa ba.

Lokacin da na shiga gida sai da kowa ya san da labarin ɓayawon radio. Jiji ma da ke goge-goge a kitchen sai da na bi ta na bata labari, ta yi ta dariya. Kamar yadda Baffa Manu ya ce mini ba ɓarawon radio ba ne haka ma Jiji ta ce min. Na ce "to waye shi? Miyasa ya shiga gidan ku?"

Buɗan bakin Jiji ta ce "Hamman ki ne ya zo Aaliyah"

Zamana da Jiji na koyi yaren fillanci duk da harshe na a lokacin ya fi ƙwarewa a Hausa da Kanuri harta yaren Amma na da ta ke min ba wani ji na ke ba kamar yadda na ke jin fillanci saboda sabo da Jiji. Ita Amma ma munfi yin Hausa da ita.

"Hamma na kuma?" na sake tambaya.

"Ko ba kya son shi?" Jiji ta tambayeni

Ba tareda na san cikakkiyar ma'anar kalmar so ba, ba tareda na san sarƙaƙiya da ke tattare da kalmar so ba na furta " Ina son shi Jiji"...

Da yamma da Jiji ta gama ayyukan ta ta ɗaukeni mu ka wuce gidan su. Anan na sa ke ganin yamutsatstsen yaron nan yana zaune a ƙofar gida yana kallon su John da Shina yaran dreban mu da gardener su na wasa.
Na zauna kusa da shi na ce " wai kai Hamma na ne?"
Bai min magana ba sai ma kallona da ya ke yi. Ganin kallon yai yawa ya sa na kai hannuna na tsokale ma sa ido, na tashi da gudu na shige gida ina dariya. Abinda na tsammanta shine ya biyoni ya dakeni kaman yadda yayuna Bukar da Aliyu su ke idan na tsokale su amma wannan yaron ba abinda yai, bai biyoni ba kuma bai min magana ba. Haka na dinga fitowa ina jan koɗaɗɗiyar rigarsa sai na shige gida da gudu amma ko ajikinsa. Ina cikin haka na ci tuntuɓe na faɗi ƙasa, baki na ya bugi sumunti sai jini. Nan take na fashe da kuka, a wannan lokaci ya taso da sauri ya ɗaga ni yana karkaɗe min jiki na yana faɗin "shannu, shannu ka ji" da gurɓacacciyar Hausar sa. Jin maganan sa a karo na farko ya sa na dena kuka na zuba ma sa ido saboda rashin maganar sa run farkon ganin shi ya sa na ɗauka ko baya magana ne.
Jin kuka na ya sa Jiji ta fito da sauri ta ɗaukeni ta shige da ni ciki tana mini sannu.

Tun daga wannan rana na samu sabon abokin wasa duk lokacin da na je gidan Jiji. Maimakon da da nake maƙalewa Jiji yanzu wajen Hamma na ke maƙalewa. Ba ya damuwa idan na tsokale shi haka nan ko sau goma zan ce ya goyeni ko ya min doki baya min mu su. Cikin ƙanƙanin lokaci sunan Jiji ya fara ɓacewa a bakina, yanzu taɗi na baya wuce Hamma na Hamma na.
Hamma bai cika magana ba amma duk lokacin da na takura shi akan ya bani labari sai yai ta bani labarin shanun su da labarin gona, ko ya bani labarin Rafin da su ke zuwa su yi wanka. Ina son labaran sa, ba na gajiya da su haka nan shi ma ba ya gajiya da maimaitamin labaran a duk lokacin da na buƙata.

Duk da ƙarancin shekaruna a wannan lokacin bai jima ba na fahimci Hamma ba ya zuwa makaranta. Duk da kuwa ya ce min a chan ƙauyen su yana zuwa makaranta idan hantsi yai kuma ya wuce kiwo.
Nan na fara takura Jiji akan a saka Hamma a makarantar mu. Jiji ta kan ce mini za a sashi amma sai maganarta ya zama ƙanzon kurege.
Sai na koma damun Amma na. Hmm ita kan rana na biyu da na kawo maganar da faɗa ta ce min na samu Baba na ba ta son shirme. Haka na fita da gudu ina kuka na wuce sashen Baba amma bayanan, na yi ta zaman jiran shi ƙarshe anan falon sa bacci ya ɗaukeni. Cikin bacci Baba ya shigo falon ya ɗaukeni zai maidani wajen Amma na ya ji na ce "Baba a sa Hamma na a makaranta"
Sai da ya kai ni ya ke tambayar Amma na waye Hamma dan shi ya manta wa na ke kira da Hamma.

"Ɗan ƙanin mijin Jijiɗo ne da ya ke zama a wajen su"

Ta bashi labarin yadda muka yi kafin na je falon sa. Ya ce zai wa Manu maigadi magana akan ya sa Hamma a makaranta.
Sai dai abu da ɗan kasuwa zuwa wayewar gari har ya manta wani maganan Hamma.
Ni kam maganan na rai na da shi na kwana da shi na tashi. Da safe ma sai da na yiwa Amma magana, ta ce min Baba na ya ce za a sa shi, nan ta ke na fara murna. Sai dai kwana biyu shiru ba maganan makaranta...

Da gudu na faɗo falon Baba inda ya ke ƙarɓan baƙin sa ma su mahimmanci.

"Baba ba a sa Hamma a makaranta ba" abinda na faɗi kenan lokacin da na ƙaraso wajen sa ba tareda na yi la'akari da baƙin da ke wajen ba.

"Je ki Aaliyah za a sashi"

"In in" na girgiza kai tareda fara bubbuga ƙafa ina cewa.
"Ai haka Amma ta ce, amma ba ka sa shi ba"

"Aaliyah!" Ya daka min tsawa nan ni kuma na ɓarke da kuka.

"Zo nan 'ya ta" ɗaya daga cikin baƙin ya faɗi.

Na kalleshi sosai, ban taɓa ganin sa ba amma kuma murmushin da ke fiskar sa ya sa na ji zuciyana ta yadda da shi. Na yi saurin ƙarasawa wajensa ina goge hawaye ina shan majina.
Ya ɗaukeni ya ɗaura ni akan cinyar sa ya ce " wa ki ke so a sa a makaranta"

Na ce "Hamma"

"Waye Hamma?"

"Hamma ɗan gidan Jiji mana"

"Alhaji Wamako ka ƙyale wannan mai surutun, rigimarta ya fi ƙarfin ta"
Baba ya faɗi.

Shi kam sai murmushi ya ke yi yana faɗin " 'yata ba ta da rigima, ka bari na ji damuwarta"

Ya kalleni ya ce " yanzu mi za ayi miki"

"A sa shi a makaranta"

Ya shafa kaina ya ce " gobe-gobe za a sashi a makaranta"

"Idan ba a sashi ba fa?" Na tambaya cike da damuwa

"Ni da kai na zan zo na kai shi"...
Daga wannan rana kuka na ya ƙare aka saka Hamma a makaranta sai dai ba makarantar mu ba, sannan ba da mu ya ke zuwa ba, mu ana kai mu a mota shi yana tafiya a ƙafa. Wannan ma na yi ƙorafi akan dole sai ana kai shi tareda mu. Sai dai ban san ya aka yi ba tunda Hamma ya ce shi ba ya son shiga mota sai na dena ƙorafi.




*..............Sa'eed...........*
The rich girl versus the poor boy


Ban san ya aka yi ba shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Aaliyah sai dai al'amari na Allah rubutacce ne kuma tsararre. Tun ba na iya ma ta magana sosai har na fara yi, tun ban fahimtar ta sosai har na fara yi. Duk da shekaru biyar cur da na ba ta rata, hakan bai hana mun zama tamkar abokai ba. Aaliyah to koremin zaman kaɗaici da rashin sabo da na ke yi farkon zuwa na. Mu kan ci abin ci tare mu yi wasa tare sannan mu yi karatu tare. Yayinda sauran yara tsarana su ke ball a ƙofar gida ni ina chan garden ina yiwa Aaliyah do ki ko goyo.

Dalilin Aaliyah aka sani makaranta. Ita ta dinga kuka tana birgima har sai da aka sani a makaranta.
Wata rana ina zaune ina yin Homework (aikin gida) sai ga Aaliyah da kaya a hannunta. Tana zuwa ta watsa min ta ce "gashi Hamma, kai ma ka sa kaya ma su kyau"

Na tsorata matuƙa da wannan kaya saboda irin kayan da su Aliyu ke sawa kenan. Na ce "Aaliyah wa ya baki kayan nan"
Sai ta fashe da dariya tana yi tana rufe baki.
Na ce " ta Aliyu ce ko?" Saboda Aliyu shi ne tsarana ko da na girmeshi ba zai fi da shekara ɗaya ba.

Maimakon ta ɗau kayan sai ta koma da gudu tana faɗin " barin je na ɗauko ma wasu"

Kafin na ma ta magana ta yi nisa. Na ɗau kayan na shiga na nunawa Jijiɗo, ai kuwa ta tisani a gaba muka wuce sashen Hajia.
Jijiɗo ta nunawa Hajia kaya tana ba da haƙuri. Hajia ta ce ba komai mu tafi da kayan wanda riga biyu ne da wando ɗaya.

Ana haka sai ga Aliyu ya shigo ɗauke da Aaliyah, ya direta gaban Hajia.
"Mama idan na daki Aaliyah ki ce na cika mugunta. To ga ta nan na kama ta tana ɗauka min kaya wai za ta kai wa Sa'eed"

"Ni a Hamma zan kaiwa"
Ta katse shi da ƙarfi.

Hajia ta ce " yanzu dai ka yi haƙuri, ka ga Aaliyah yarinya ce"

Ta ɗauki Aaliyah ta ce " 'yar fara ba a ɗaukan abin mutane sai an tambaye su kin ji"

"Mama ai shine ya ce wai a John zai ba wa kaya, wai ba zai ba wa Hamma ba"

Hajia ta ce maza ya je ya ɗauko kayan sa da su ka tsufa ya kawomin.
Aliyu ya fita yana ƙunƙuni.
A ranan saboda Aaliyah sai da na samu kaya kala takwas da takalma biyu. A wajen Aliyu tsofaffin kaya ne amma a wajena kaya ne ma su kyau, domin kaya ne na yayi. Tun daga ranan maimakon su John da ake bawa tsofaffin kayan Aliyu sai ya zama ni ake bawa waɗannan kaya...


Cikin shekaru biyu na gama primary saboda aji huɗu aka sakani lokacin, saboda na iya karatu da rubutu. A makarantar mu ta ƙauye ina aji shida na taho Maiduguri sai dai gwaji da su ka min lokacin da za a sa ni a makarantar ya sa dole su ka maida ni aji huɗu.

A shekaru na goma shahuɗu na fara aji ɗaya a sakandare yayinda su Aliyu da su John sa'annina su ka min fintinkau.
Cikin shekaru biyu na gane banbanci tsakanin ni da Aaliyah. Aaliyah 'ya ce a gidan Bulama sunan da ke sa a kalleka da daraja a kuma mutuntaka. Ni Sa'eed kuma ɗan Baffa Manu maigadi ne. Wannan banbanci da kuma ƙara girma da na yi ya sa na ke ƙoƙarin ja baya da Aaliyah, sai dai a wajen Aaliyah ba ta bani daman yin hakan ba saboda tana ƙara girma da wayo tana ƙara shaƙuwa da kusanci da ni.

Jijiɗo da Baffa na koyaushe suna ƙara nusar da ni akan Aaliyah musamman da ya ke ni na fita wayo sai dai abinda ba su sani ba shine Aaliyah ta jima da zama jinin jiki na. Aaliyah ta jima da mamaye ruhina.





*TSOHUWAR💖SOYAYYA*



*©Azizat*

Wattpad @000Azee


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Free page

0️⃣6️⃣



*..........Aaliyah.........*
A girl, A woman


Abubuwa dayawa sun faru a tsakanin shekaru uku da zuwan Hamma Sa'eed gidan mu. Hamma Sa'eed ya zamo tamkar wani ɓangare na jikina wanda idan babu shi ba zan rayu ba. A gidan mu na koma daga Aaliyan Jiji zuwa Aaliyan Sa'eed. Banida ɗanuwa ko ƙawa dana shaƙu da su sama da Hamma Sa'eed. Sanah da muke kusan kai ɗaya, ita ce kaɗai ƙawata ta kusa dani bayan Hamma.
Mukan je ya koya mana karatu domin Allah ya bashi ƙwaƙwalwa, daga ƙauye ya zo amma ya ɗara mutane dayawa da su ka yi karatu a birni.

Watarana ina shekara goma muna ɗakin Hamma yana koya mana karatu, da ke ni da Sanah ajinmu ɗaya, duk da kuwa ta girmeni.
Abunda Hamma ke koya mana na riga na gane tuntuni shiyasa ya maida hankalinsa kan Sanah domin itama ta gane. Cewa yai na koma gefe na dinga practicing wasu lissafi da ya bani. Ina cikin yi na hangoshi da Sanah su na dariya. Hamma ya kan yi raha da barkwanci lokacin kowa mana karatu musamman darasi na Maths. A ƙarancin shekaruna sai na ji wani kishi ya mamaye ni, na ji ba abun da na ke ji sai haushin Sanah. Ji na ke za ta ƙwacemin Hamma Sa'eed ne.
Na taso da sauri na zo na ture Sanah.
Sanah ta kalleni "Aaliyah ba na son tsokala kinga muna karatu"

"Ki dena zuwa karatu wajen Hamma. Hamma na ne ni kaɗai" ban san maganar da na yi a ranan magana ce da ta ƙunshi abubuwa dayawa ba.
Ba ranan ne muka fara karatu a wajen Hamma tare ba, kusan shekara biyu kenan.

"Aaliyah ba yayar ki ba ce" Sa'eed ya ɗan daka mini tsawa.

"Ta tashi ta tafi, ba ta iya komai ba dama"

Sanah ta fusata fuuuu ta tashi ta fita.

Sai da na zauna ya kalleni ya ce "tunda kin koreta ke ma tafiya za ki yi angama karatun yau ɗin"

Na yi-na yi da shi amma ya ƙi kulani ya ce sai dai na je na bawa Sanah haƙuri, cikin fushi na kwashi littattafaina na tafi. Maimakon na tafi gida sai na wuce garden na je na zauna ina wasa.
Kusan awa ɗaya da rabi ina cikin wasa sai ga jini ya biyo ƙafata na tsorata da ganin jinin nan sai na fashe da kuka dan na ɗauka ciwo na ji a cinyata duk da kuwa ba wai ina jin zafi bane.
Ban je cikin gida ba domin na kai kuka na wa Amma ko wa Jiji wanda na san tabbas tana kitchen tana haɗa mana abincin dare, ban je wajen Sanah ba wanda ba mu jima da yin faɗa ba. Ban je wajen Hajia ba wanda ta ke so na, ta ke son surutu na. Sai na wuce wajen Hamma Sa'eed wanda na san ina fushi da shi amma kuma shi kaɗai zan nunawa ciwo na.

Hamma Sa'eed yana zaune yana karatun wani littafi na faɗo ɗakinsa. Ɗaki ne da kafin zuwan Hamma 'ya'yan Jiji ke kwana amma kuma tun zuwan sa ɗakin ya juye ya koma na shi yayinda Jiji da Baffa ke amfani da ɗaya ɗakin.

Ina kuka na fara ɗaga skirt ɗina ina nuna ma sa pant ɗina da ya jiƙe da jini. "Hamma jini, Hamma ciwo na ji"

A shekarunsa shabiyar ba zan ce ga takamaimai inda ya samu ilimi gameda jinin haila ba. Amma bayan ya duba sai ya gane ba ciwo bane.
Abinda ya fara ce min shine "ki dena kuka, ba ciwo bane"

"To minene?" Na tambaya cike da wasu tambayoyin a cikin ƙwaƙwalwata.

"Bari mu je wajen Jiji"

Akwai wani mayafi da ya ke rufuwa da shi sai ya ɗauko ya ɗaura mini ya ce muje wajen Jiji.

"Idan na yi tafiya jinina zai ƙare Hamma"

Bai ce komai ba sai ya tsugunna, ni kuwa na hau bayanshi.
Ta ƙofar kitchen mu ka shiga inda mu ka tarar da Jiji tana yin farfesun kaza.

Yana direni Jiji ta haushi da faɗa " Lamiɗo ba na hanaka goyon Aaliyah ba, kai ba ka jin magana ko"

Bai ce komai ba saboda shi dama ba mai yawan magana bane balle kuma duk lokacin da babba ke magana to za ka ga Hamma Sa'eed ya yi shiru idon sa a ƙasa.

"Jiji jini a jikina, ki zo ki min wanka"

"Jini kuma?"
A wannan shekaru babu irin gurɓacewar zamani inda ake yawan faɗe musamman har acikin yara saffa. Jiji ba ta kawo wannan a ranta ba sai dai ta tsammanta ciwo na ji.
Ta kama hannuna mu ka bar kitchen ɗin.

A wannan rana Jiji ta zaunar da ni tamin bayani gameda jinin haila cikin ɗan iliminta na gargajiyanci. Ni dai a lokacin ko kashi goma ban ɗauka ba cikin kashi ɗari na abubuwan da ta faɗa min. Sai ma ƙara dulmiyar dani da ta yi musamman yadda ta yi ta jajanta min wai na girma, ta dinga karanto min farillai da mustahabban mu'amala da Hamma Sa'eed wanda jinsu kawai na ke amma yadda su ke shiga haka su ke fita ta ɗaya kunne na.

Abu da mai surutu babu wanda bai san labarin jini na ba, sati uku kenan Baba ba ya gida ranan da ya dawo tare su ka dawo da abokinshi Alhaji Wamako wanda ya zamo tamkar Baba na, duk lokacin da ya zo gidan mu sai ya taho min da tsaraba, sannan ko da su na meeting ne to Baban Lagos kaman yadda na ke kiranshi zai ɗaukeni a cinyar sa ko kuma ya barni na yi ta wasa a wajen.

"Baban Lagos na fara jini" abinda na faɗa kenan lokacin da ya ɗaukeni bayan na ma sa oyoyo.

Baba na da shi Alhaji Wamakon su ka tsaya kallon-kallo
Baba ya ce "Aaliyah shekarun ki nawa?"

Na ɗan ɓata fuska na ce " Baba har ka manta. Ba na yi birthday ba ranan"

Na ɗan ɗaga murya na ce " i am 10yrs 7months now"

Haka na zauna na basu labarin jini na tirtiryan tun daga faɗan mu da Sanah har zuwa yadda na ga jinin.

Alhaji Wamako ya ce " Masha Allah, ashe ɗiyata ta zama 'yan mata, sai a fara haɗa kayan gado"

Baba ya

Please Login or Register in order to submit comment