You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farko ma na ɗauka ko faɗa su ka yi da saurayin ta dan na san tana son Damien sosai. Sai da ta faɗa min asalin abinda ya faru sai jikina yai sanyi.
Saurayin ta Damien yai hatsari ya mutu. Abinda ya ƙara ɗaga ma ta hankali shi ne sati biyu da su ka wuce wata ƙawarta ta ma ta kwatancen wani mai duba. Out of curiosity sai ta je, da ta je mutumin ya gaya ma ta Damien zai mutu. Ta harzuƙa da wannan zance ta zage shi tatas, ta kirashi da maƙaryaci. Sai ga shi da safiya aka kirata akan Damien yai hatsari, bai jima da kawoshi asibitin ba ya mutu. Ba shiga rarrashin Cassy ina nuna ma ta lokacin Damien ne yai...

Bayan kwana huɗu da mutuwar Damien na je na samu Cassy akan ta kai ni wajen mai duban nan, ina so nima ya min duba. Da farko ta ƙi saboda tana tunanin kar na je a gaya min abinda zai ɗaga min hankali amma da na nuna ma ta koma minene zan jure ba zan tada hankali ba sai ta yarda...

Mutumin da mu ka je irin sufi ɗin nan ne, yana yin sa da kuma turancin sa ya daɗa tabbatar min da ba zai wuce ɗan ƙasar India ba ne.
Muna zuwa ya kalleni ya ce *Aashiƙan* yai murmushi wanda na rasa gane murmushin ko na minene. Tun kafin na ma sa bayanin mi ya kawo ni ya ce ya sani na zo ne akan maganar soyayya na gyaɗa ma sa kai ina sawa a raina wannan mutumin da gaske yana duba ɗin.

Na miƙa ma sa hannun dama na bayan ya buƙaci hakan. Ya sa yatsar sa yana bin zanen hannuna kafin ya ce *Makhtub* ya cigaba da cewa "ko sama da ƙasa za su haɗu sai kun yi aure" ya kalli ƙwayar idon na ya ce "sai dai za ku yi shekaru talatin kuna kewar junan ku" ba tareda na gama gane ma'anar maganar sa ba na ce "ka ce ni da Sa'eed za mu yi aure?"

Sai da yai dariya kafin ya ce "za ku yi aure"
Kalmar za mu yi aure kaɗai ya wadatar da ni duk wani bayani da ya ɗaura akai duk shirme ne a waje na.
Na ɗau maƙudan kuɗi na bashi sannan mu ka bar wajen sa zuciya ta cike da farin ciki.
Tundaga wannan rana na sawa kai na salama domin ance ni da Sa'eed za mu yi aure. Ko gayawa Sa'eed ban yi ba dan na san zai mun faɗa. Na riƙe abin a raina ni kaɗai...

Saboda ni Bayan Sa'eed ya kammala degree ɗin sa ya ɗora da masters domin mu samu mu gama makaranta tare. Wannan karan tun kafin ayi hutu na kira Baba na ce ba zan zo Nigeria ba saboda zan tsaya yin project ɗi na. Bai musa min ba ya amince kai tsaye. Da na kira Amma na gaya ma ta sai ta dinga mun faɗa domin ta san saboda Sa'eed ne na ƙi dawowa gida. Ni dai ban damu ba tunda Baba ya amince...

Kwamci tashi har Allah ya kawo mu ƙarshen karatuna inda ni Aaliyah Badamasi Bulama na kammala degree ɗina yayinda shi kuma masoyina Sa'eed Aliyu Modibbo ya kammala masters na shi.
Mun sa dogon buri a zukatan mu. Da mun dawo Nigeria kafin mu tafi bautar ƙasa zan sanar da Baba maganar Sa'eed saboda muna gamawa sai a mana aure. Kasancewa an tabbatar min ni da Sa'eed za mu yi aure sai ban sa a raina za a samu matsala ba musamman idan na tuna cewa Baba yana so na ba zai min auren dole ba sai dai...

........................

Cikin ikon Allah ba mu jima da dawowa ba aka tura Sa'eed bautar ƙasa chan Minna. Ni kuma Borno, ban ji daɗi ba dan ina so mu tafi bautar ƙasa tare. Na je na samu Baba a falon sa da letter ɗin da niyyar ya min hanya a maida ni Minna sai na tarar da wani zance marar daɗin ji.
Baba shi ya sa aka posting nawa Maiduguri saboda yana so na zauna kusa da gida.

"Baba na yi karatu a ƙasar waje ma balle kuma bautar ƙasa a chan wani state, za ku iya ganina duk lokacin da ku ke so fa" na faɗa da sigar sakalci.

"Aaliyah ki zauna a gida, ba na son ƙananun maganganu da na ke ji ana faɗa a kan ki"

"Baba wani magana kenan?" Na faɗa cike da tsoron tambayar da na yi da kuma amsar da zan iya samu.

"Aaliyah ba na son kusancin ki da Sa'eed. Dan kun yi makaranta ɗaya ba yana nufin ɗaya ku ke ba. Ki riƙe matsayin ki shima ya riƙe na sa"

Baki na rawa na ce " Baba ina son Sa'eed"

Bai yi mamakin kalamai na ba dan ya san da hakan tuntuni.

"Ko ma mi ki ke ji game da shi ki yakice shi. Na riga na miki miji"

Na fashe da kuka ina bashi haƙuri amma ko saurarata bai yi ba ƙarshe ma ya tashi ya bar min falon...

Kalmar an min miji yana da girma a wajena, hakan na nuna ba ni da 'yan ci kwata-kwata. Ya kuma nuna cewa banida ikon zaɓar mijin da na ke so sai dai a zaɓa min.

Sa'eed yana Minna bai san miya ke faruwa ba ni kuma ina Maiduguri ina fama da ƙunci. Wasa-wasa fa Baba ya ɗauke min wuta, yai biris da lamarina ya nuna matuƙar na cigaba da maganar Sa'eed a gidan nan zai aurar da ni tun ma kafin na gama bautar ƙasa na. Babu wanda ya damu da halin da na ke ciki, kowa nuna min ya ke bamu da ce da Sa'eed ba. Harta Jiji abinda ta ke nanata min kullum kenan. Sanah ce kaɗai ta yarda da soyayyata ta kuma supporting ɗi na...

Na turawa Sa'eed wasiƙa akan halin da na ke ciki amma har yau bai tura mini amsa ba. Ina kwance a ɗakina ina duba tsoffin wasiƙun Sa'eed Amma ta shigo ɗakina.
Na ɗaga ido na kalleta na kau da kai. Ta ajiye min wassu kaya a gabana ta ce, "ki sa wannan anjima za ki yi baƙo"

"Ba zan sa ba" na faɗa kai tsaye.

Amma ta min kallon banza ta ce " idan kin isa ki ƙi sa kayan nan mu gani. Ni da ke a gidan nan"

Yadda ta ajiye kayan nan haka ta dawo ta same su bayan awa ɗaya da rabi.
Faɗa ta shiga min sosai wanda ni kam ko ajiki na.

"Ki tashi ki sa kayan nan Aaliyah ko na sassaɓa mi ki"

Na kalli cikin idon ta na ce ba zan sa ba, idan za ta kashe ni to ta kashe ni amma ba zan sa ba.

Ina ganin yadda ɓacin rai ya mamaye fiskarta lokaci guda amma ni ko a jikina.
Ba ta ce ƙala ba ta fita daga ɗakin.
Minti takwas bayan fitar ta sai ga Baba ya shigo ɗakin ran sa a ɓace. Na ɗan tsorata da ganin sa amma na dake.

"Ɗan gidan Alhaji Wamako ya zo ganin ki ki shirya ki je ki same shi a falon baƙi"

Sai da ya juya zai tafi ya ce " umurni ba shawara ba Aaliyah" ya faɗa kafin ya sa kai ya fita...

Ina kuka ina saka kayan, ina kuma zagin Alhaji Wamako a zuciyata domin duk ƙauna da so daya nuna min tun ina yarinya ashe akwai abinda ya ƙimtsa min ne na baƙin ciki.
Kayan kawai na sa ko kwalliya ban yi ba na wuce sashen Baba.

Yana zaune a falo lokacin da na shigo, an cika gaban sa da tarkacen ciye-ciye da shaye-shaye. Shiga ta alfarma yai, shigan 'yan ma su ji da naira. Ba wannan ne karo na farko dana fara ganin sa ba, na taɓa ganin sa a Sokoto shekaru biyar da su ka wuce lokacin da mu ka je bikin ƙanwar sa.

Ahmad Ibrahim Wamako kenan, babban ɗa a wajen Alhaji Ibrahim Wamako. Kamar yadda mahaifina ke ji da arziƙi da dukiya haka Alhaji Wamako ke ji da kuɗi da dukiya, sunan sa ya shahara a Nigeria da Africa baki ɗaya.

Ban ko zauna ba na kalleshi na ce " kar ka bawa kan ka wahala Malam. Ina da wanda na ke so kuma shi zan aura. Ka nemi wata matar a gaba"

Sai dana gama maganar sannan ya ɗago ido ya kalleni ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya.




*TSOHUWAR💖SOYAYYA*


*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

1️⃣1️⃣

Free page

*za'a samu cigaban wannan labari a 200, idan kuma ka biya kuɗin Sakatariyata to 100 za ka biya. Domin ƙarin bayani 08137311900*



*........Aaliyah.........*
Engagement


Da gudu na shiga ɗaki na ina kuka. Wai miyasa komai ya lalace min ne cikin ƙanƙanin lokaci haka? Abinda na ke ta tambayar kaina kenan.

Maganganun Ahmad Wamako babu tausayi aciki.

"Dole na aureki Aaliyah, ko dan na raba ki da girman kai da tsiwar ki ta banza. Ki na da wanda ki ke so ko? To kuma ba wanda za ki aura sai ni, gara tun wuri ki kwantar da hankalin ki"...

Gado na fara birkitawa kafin na shiga wurgi da kayan ɗakin. Sai da na yi watsi da komai kafin na zube a ƙasa ina kuka ban damu da kwalban turaren da ya ke fashe a ƙasa ba, ban kuma damu da zafin da na ke ji ba saboda yadda kwalbar ta yaga min gefen gwiwa ba, zafin da na ke ji daga zuciya ta ke, zafin da na ke ji daga ruhi na ne.

Sanah ce ta shigo ɗakin ta sameni ina kuka. Ta zo da gudu ta rungumeni, mun jima a haka kafin ta rarrasheni ta miƙar da ni wanda hakan ya sa ta ga jinin da ke ƙasa da kuma ciwon da na ji. Sai da ta kai ni bakin gado na zauna kafin ta fita da gudu dan ta ɗauko first aid box a ɗakin Amma...

Kafin dare zazzaɓi mai zafi ya kama ni, bayan Sanah da Jiji babu wanda ya shigo ɗakina. Amma shareni ta yi duk da kuwa ina da tabbacin ta san sarai abinda ya sameni. Ba wannan ne ma yafi ɗaga mun hankali ba irin yadda Sa'eed ya shareni, babu ɗaya cikin wasiƙuna da ya amsa. Yana so ya ce duk kuka na duk roƙo da na yi cikin wasiƙun bai damu ba. Chan ƙarfe takwas Sanah ta shigo min da abinci, ta tisa ni a gaba dole sai da na ci kaɗan kuma na sha magani.

"Sanah, Sa'eed ya gujeni" na faɗa ina hawaye.

"Bai guje ki ba Aaliyah, yana tareda ke"

"Aaliyah" ta kira suna na a hankali. Ganin ba ta ce komai ba ya sa na ɗago ido na kalleta.

"Ki yi haƙuri dan Allah, na san ban kyauta miki ba"

Ban yi magana ba ban kuma janye ido na daga kallon ta da na ke ba.

"Duk wasiƙun da ki ke turawa Sa'eed ba sa isa gareshi"

Na zaro ido ina jiran ta min sauran bayani. Domin hankalina bai kama maganar da ta yi ba. A ƙalla na aika wasiƙu sama da ishirin cikin wata uku kacal.

"Tun da Sa'eed ya tafi Amma ta sa aka dena aika ma sa wasiƙar ki, haka shima ta shi wasiƙar an hana ma a turo ta nan"

Hawayen da da su ka kafe da ne su ka cigaba da kwaranya a ido na. Duk zuwa post office a banza kenan, duk abinda na rubuta ya bi iska kenan tunda bai isa inda ake so ya je ba. Ta ya Amma za ta min haka? Ta ya Sanah za ta barni na yi ta wahalar banza.

"Ki yi haƙuri Aaliyah, ni ma ban sani ba sai kwanaki da Amma ke hiran da Hajiya. Na so gaya mi ki amma ina tsoro"
Muryan Sanah ya ƙatse ni daga dogon tunanin da na ke ciki. Na yi wuff na tashi domin na je na ji dalilin wannan rashin mutunci da Amma ta min amma Sanah ta riƙe hannuna.

"Aaliyah ba abin da zai chanza idan ki ka je, ki tsaya mu nemi wata mafitar"

Jikina rawa ya ke saboda yadda zuciya ke ci na. Ba dan girman Uwa ba da ba abinda zai hana a wannan dare na je na yiwa Amma rashin mutuncin da har ta koma ƙasa ba za ta taɓa mantawa ba...

Washe gari Sanah ce ta tafi da doguwar wasiƙar da na rubutawa Sa'eed, inda na ke ma sa bayanin abinda ke faruwa. Na sani indai ni na kai ba za su aika ba shiyasa Sanah ta ce za ta kai wa wata ƙawarta ta aika da wasiƙar.

Mai kuɗi kenan, kuɗi da suna da gidan mu ke da shi ya sa ake son raba tsakanin masoya amma ni Aaliyah ba zan yarda ba. Ko da zan rasa komai indai zan kasance da masoyina to babu komai...


.............................

Kasancewa ban kuma ɗaga hankalina ba ya sa aka cigaba da shirye-shiryen biki. Ahmad Wamako bai kuma dawowa ba hakanan Amma ba ta tambayeni ya mu ka yi da shi ba. Dama mi za ta tambaya, abu ne da tun farko ba a nemi shawarana ba balle ya zama ina da abin faɗa cikin lamarin. Satin da ta zagayo Sanah ta amso min wasiƙar Sa'eed.  Hannu na rawa na warware takardar na fara karantawa. Ashe duka aka zalincemu, shima bai san wasiƙun sa ba sa isowa gare ni ba.
Ina gama karanta takardar na cillar da ita na fashe da kuka. Taya Sa'eed zai ce na yi haƙuri na cigaba da addu'a, ta ya zai ce zai yi ƙoƙari ya zo idan ya samu dama.
Sanah ta ɗau wasiƙar ta karanta kafin ta ƙaraso wajena ta zauna, dafa kafaɗuna ta yi kafin ta ce "Aaliyah maganar Sa'eed gaskiya ce, addu'a kawai za ki cigaba da yi nima kuma zan taya ki"

Da wata durƙusashshiyar murya na ce "Sanah ba zan iya son wani namiji bayan Sa'eed ba, ba zan iya auren wani namiji idan ba Sa'eed ba. Idan aka takura ni mutuwa zan yi, mutuwa zan yi Sanah" na ƙarasa maganar ina sheshsheƙar kuka. Sanah ta rungumeni tana lallashina...

A satin da ya zago aka sa mana rana. Ina zaune a ɗaki Sanah ta shigo, ni dama daga na dawo daga wajen PPA ɗina ina nan ƙunshe a ɗaki bana kuma fita sai washegari. Duk wanda ya zo cikin 'yan uwa na ɗaki zai shigo ya sameni, yawancin su haushi na ke basu, su yi ta zagina wai ina ƙyashin auren ɗan gidan Alhaji Wamako. Ba wanda na ke tankawa har su gama abinda za su yi su jajuɓa jiki su fita min daga ɗaki.

"Aaliyah ƙarshen watan da za mu shiga aka sa bikin ki ya za kiyi?"

Murmushi mai ciwo na yi sannan na ce "ba zan auri Ahmad Wamako ba"

Sanah dai kallon da kamar wuya ta ke min ta rasa abin faɗa. Ni kuma na ƙudura a raina da na auri Ahmad Wamako gara na rasa rayuwata ko kuma na bi uwa duniya...

Bayan Sanah ta fita a ɗakin na tashi na je ɗakin Amma inda na samu tana riƙe da wayar tarho, maganganunta ya tabbatar min da 'yan uwanta na Niger ta ke magana.

Sai da ta gama ta ajiye kafin ta juyo ta kalleni, a ƙasa na tsugunna a gabanta, fiskana duk ta kumbura saboda yawan kuka da rashin barci.

"Amma dan Allah indai ke ki ka haife ni, ki yi haƙuri ki yiwa Baba magana a fasa aurena da Ahmad Wamako. Ba na son shi, ba na son auren shi. Sa'eed kaɗai na ke so ba zan iya rayuwa babu shi ba"

"Aaliyah kenan, dan ba kya son shi yanzu idan aka yi aure za ki so shi. Sa'eed ba tsaran ki ba ne, ba ta inda kuka dace, ki manta da shi ki rungumi ƙaddarar ki"

Hawayen da su ka taru a idona su ka fara saukowa, ba zan iya tuna rana ta ƙarshe da na tashi na wuni har washe gari ban yi kuka ba. Ƙila tun a Cambridge lokacin muna tareda Sa'eed.

"Amma, Sa'eed musulmine, mai ilimi, kyakykyawar zuciyar sa ya sa kyawawan halayen sa su ka bayyana. Sa'eed mutum ne na gari, babu wata mace a doron ƙasa da ba za ta yi alfahari da Sa'eed ba.
Amma saboda shi maraya ne?, saboda shi talaka ne? Saboda shi ɗan fulanin ƙauyen Durum ne?"

"Aaliyah" Amma ta kira sunana da ɗan ƙarfi, ban sani ba ko maganganun da na yi sun shigeta ne ban kuma sani ba ko dai mamakin maganganuna ta ke ba.

"Amma, Sa'eed ya yi karatu, nan ba da jimawa ba zai samu aiki. Ba sai kun min komai ba na yafe komai na ku, rufin asirin sa da kwanciyar hankali da zan samu tattare da shi ya fi min komai. Amma ki ceci rayuwata ki sa Baba ya fasa auren nan"

"Aaliyah ke wani irin taurin kai gareki ne. Maganar ki da ɗan gidan Alhaji Wamako an yi shi kusan shekaru goma da su ka wuce, babu yadda za ayi rana ɗaya a ɓata shirin da ake yi tun shekara da shekaru" da ƙarfi ta yi maganar cikin masifa.

A hankali na furta " akwai Sanah, idan burin ku haɗa aure tsakanin iyalen Bulama da Wamako ne, akwai Sanah. Ku haɗa Sanah da Ahmad, za ta iya zama da shi. Ki tausaya min Amma zan iya mutuwa idan na rasa Sa'eed"

Ban sani ba ko dan Amma ma auren haɗi aka ma ta ya sa ba ta damu da halin da na ke ciki ba, ban sani ba ko dai Amma ba ta san soyayya ba ne, ba ta san zaƙin soyayya da ɗacinta ba, ba ta san mi ake kira so ba. Abinda na sani shine ni Aaliyah na san so na kuma san zaƙin sa, ba zan bari na samu ɗacin ta ba saboda son zuciya irin ta iyayena...





*TSOHUWAR💖SOYAYYA*


*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

1️⃣2️⃣

Last free page

*za'a samu cigaban wannan labari a 200, idan kuma ka biya kuɗin Sakatariyata to 100 za ka biya. Domin ƙarin bayani 08137311900*


*The Plan*


*........Sa'eed........*

Na fara samun karaya ne gameda soyayyar mu lokacin da mu ka dawo daga Cambridge.
Ina zaune a kan benchi kusa da Baffa Manu mu ka ji horn ɗin mota. Baffa yai sauri ya tashi zai je ya buɗe ƙofar na yi wuff na rigashi. Motar Alhaji Badamasi Bulama ne ta shigo cikin gidan. Ina gama rufe gate ɗin na ji muryan Baba Umar wanda ya ke tsohon dreban Alhaji Badamasi ne yana kirana. Na ƙarasa wajen sa da sauri ina gaida shi.
" Alhaji ya ce ka sameshi a falon sa yanzu"  abinda ya faɗa min kenan. Ban kawo komai a raina ba na bi bayan Alhajin.

Ina shiga falon sa na zauna ƙasan kujera ina ƙarewa falon kallo ganin yadda falon yai kyau saboda furnitures da aka sake. Shekaru shida kenan rabona da shiga falon, tun ranan da Aaliyah ta kawo ni na zo na nuna ma sa admission ɗina.

Na yi aƙalla minti Ishirin zuwa ishirin da biyar a wajen kafin Alhaji ya sauƙo ƙasa, lokacin ya yi wanka ya chanja kaya zuwa jallabiya ta shaƙatawa.

Daga inda na ke zaune na duƙa na gaida shi. Cikin fara'a ya amsa mini tareda jinjina mini bisa ƙoƙari da na yi a makaranta.

"Sa'eed sai ina yanzu?" Ya sako tambayar bayan dogon shiru da ya karaɗe falon.

"Bautar ƙasa Alhaji" na faɗa kaina a ƙasa.

"Minna ko?" Ya tambaya bayan ina da tabbacin ya san amsar tambayan.

Na amsa ma sa da eh

"Ka na da ƙwazo da hankali, ga kuma tarbiyya" yai shiru yana nazarta na duk da ƙasa na ke kallo amma ina ji ajikina yadda idon sa ke yawo a kaina.

"Sa'eed na yiwa Aaliyah miji"
Da sauri na ɗago ido na kalleshi wanda hakan ne karo na farko a tarihin rayuwata da kalleshi ido cikin ido.

"Ba sai na maka dogon bayani ba,na san ka fahimci abinda na ke nufi"

A wahale na saukar da ido na ina jin maganar Alhaji na tsatstsafomin da wani zafi daga dukkan jijiyoyin jiki na. Abubuwa dayawa su ka fara yawo a kwanya ta.  Duk wani tsari, shiri, buri  ko mafarkina a kan Aaliyah su ka fara min yawo a ƙwaƙwalwa ta.
Ina sane da banbancin da ke tsakanin mu, ina sane da cewa abu ne mai wuya na samu Aaliyah. Sai dai na watsar da komai saboda na yarda da soyayya ta kuma na yarda da Allah. Ban fito daga gida ma su arziƙi ba amma arziƙi na Allah ne hakanan ban cire rai da samun sa ba. A duk lokutan da na yi tunanin rana irin wannan, na kan yi ƙoƙarin janye tunanin da cewa Allah shi ne ke tsara komai, kuma duk abinda ya tsara wa Bawan sa ba makawa sai ta auku gareshi.  Soyayyar da na ke wa Aaliyah daga Allah ne haka nan kuma ko da mun rabu ma daga Allah ne. Tawakkali da na yi da wannan ya sa ban taɓa ɗaga hankalina ba sai ma na sawa kai na samun Aaliyah fiye da rashin samun ta.

Sauran bayanan da Alhaji yai duk ba wanda ya wuce fatar kunnena balle har su shiga su samu mafaka a cikin ƙwaƙwalwata har ma na fahimci abinda ya faɗa...

Ina son komawa wajen Baffa Manu amma kuma ba zan iya zuwa na sameshi a yanayin da na ke ciki ba. Na dinga takawa a hankali har na kai ɗakina, duhu na ga ɗakin ya mun lokacin da na shiga duk da kuwa hasken rana da ya karaɗe ɗakin.

"Sa'eed na yiwa Aaliyah miji" maganan Alhaji ya dinga dawo min. Na tsugunna a tsakiyar ɗakin ina dafe da ƙirjina, farat ɗaya soyayyar Aaliyah ya shigeni ba tareda na shirya ba, gashi yanzu ma farat ɗaya ake son raba ni da ita.

Na jima a durƙushe a wajen ba tareda na san minene mafita a gareni ba. Tabbas rashin Aaliyah a rayuwata tamkar rasa nawa rayuwar ne gaba ɗaya. Na dinga maimaita Innalillahi saboda na samu sauƙin ƙuncin da na ke ciki, ban iya barin wajen ba sai da Jiji ta shigo ta sameni a haka. Ganin yadda ta shiga ruɗu da yanayin da ta ganni ya sa na daure na tashi na yi murmushin da ko makaho ya san ba ta kai zuci ba. Masallaci na nufa bayan na nunawa Jiji lafiya na ƙalau kawai gajiya ce da kuma ciwon kai.

Ban dawo gida ba sai ƙarfe goma na dare duk da kuwa na san Aaliyah za ta yi ta ziryar nema na. Ban ma tsaya a masallacin ƙofar gida ba saboda kar ma ta aiko a kirani. Masallacin da ke chan cikin anguwa na nufa ina mai neman samun nitsuwa idan na je chan.

A ƙofar gida na samu Aaliyah da Baffa su na hira.

Ganina ya sa ta miƙe tsaye tana faɗin " Sa'eed are you Ok? lafiya ka yi dare yau?"
Na sani ba dan Baffa na wajen ba ba abinda zai hana ta rungumeni. Ina ganin tsantsar kewa da damuwa a ƙwayar idonta duk da kuwa hasken farin wata ne kaɗai ya haska wajen.

"Lafiya Aaliyah, na tsaya karatu da wani malami ne"

Na sani ba ta gamsu da bayani na ba, dan Aaliyah tana da saurin gane ƙarya musamman idan ni na faɗeta.

A hankali ta furta "amma dai ka san zan jira ka ko"

"Ki yi haƙuri Aaliyah, mantawa na yi"

Fiskarta sam babu alamar yarda sai ma fushi, ta yiwa Baffa sai da safe ta wuce ɓangaren su.

"Barka da dare Baffa" na faɗa ina ƙoƙarin shiga gida

"Lamiɗo zo ka zauna"
Ya faɗa yana nuna min gefen tabarma kusa da shi.

Ban musa ba na ƙarisa wajen na zauna ina sauke ajiyar zuciya.

"Ina son barin nan, ina son komawa cikin 'yan uwana, Shekaru sun jaa. Sabo da mutanen gidan nan ya sa na kai har iya tsawon wannan lokaci ban tafi ba. Amma idan mu na da rai ƙarshen shekaran nan zan koma gida"

Har ya ƙarasa maganar sa ban ce ƙala ba domin ba abinda zan ce ɗin.

"Lamiɗo" ya sake kira wannan karan da sigar jan hankali.

"Na'am Baffa" na amsa ma sa tareda yaƙinin magana zai min makamancin na Alhaji.

"Na san ka na son yarinyar nan sosai, amma ka yi haƙuri ka janye jiki daga gareta, ba na fata a samu matsala a iya zaman da ya rage min a ƙarƙashin Alhaji. Ka yi haƙuri Lamiɗo na"

Hannuna da ke rawa Baffa ya kamo ya riƙe yana faɗin "ka cigaba da addu'a Lamiɗo, har Allah ya sawa zuciyar ka nitsuwa. Rashin masoyi akwai ciwo"

Mun jima da Baffa a wannan dare yana lallashina. Kafin mu ka shiga ciki dan bacci, ni kam bacci ƙaurace mini yai gaba ɗaya. Ina

Please Login or Register in order to submit comment