You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taƙadariyar 'yar ƙwaya ce kuma masochist. Ta jima da barin wajen Ubanta a shekararta sha tara ta zama fitsararriya ta ƙarshe. Uba da 'ya su ka haɗewa Ahmad wanda wauta ya hana shi ganewa domin bai san alaƙar Cataliya da Don Pedro ba. Cataliya ta shiga rayuwar sa har ta kai sun yi aure, ita ta dinga tunzura Ahmad ya dinga buga chacha da duk wani abu mallakin sa. Daga ƙarshe bayan an cinye duk abinda ya tara har bashi sai da aka bishi. Gidan da mu ke ciki ma Casinon Don Pedro ta cinye. Yanzu haka wasu maƙudan kuɗi ake binsa bashi har an rufe shi a prison saboda ba shi da halin biya.
Innalillahi kawai na ke ta maimaitawa a raina dan Ahmad ya wuce tunani na. A yadda Don Pedro ya ke bayani duk wani kuɗi da kadara da na san Ahmad ya mallaka duk sun tafi a chacha. Allah ya tsinewa bature, Allah ya tsinewa wanda ya ƙirƙiro chacha a duniya na faɗa a raina.

Ajiyar zuciya kawai na ke yi na rasa abin faɗa. Don Pedro ya miƙe tsaye yana faɗin saboda halin da ya sameni ya bani kwana uku na bar gidan idan ba haka ba za a zo a watsar da ni waje. Yana son buɗe branch na Casino ɗin sa da gidan na mu dan shi baya wasa da kuɗi.

Mrs Payne ta kawo min ruwa na sha tana kwantar min da hankali. Zama na da ita ta fahimci irin auren mu shiyasa ta ke tausaya mun. Ta kan ce min mijinta Colins lokacin yana raye ba ƙaramin rayuwar daɗi da farin ciki su ka yi ba. Sai dai shekarar su sha biyar da aure ya mutu gashi ba su taɓa haihuwa ba. Bayan mutuwar sa ne ta adopting wani yaro tana kula da shi, to shima sickler ne bai jima ba ya mutu, daga haka ta cigaba da rayuwa ita ɗaya.

Kwana na farko ni da Mrs Payne mu ka fita neman ko a wani prison aka rufe Ahmad amma ba labari, mun dai samu labarin cewa da gaske ne an rufe shi ɗin amma ba a London ba. Rana na biyu Mrs Payne ta sameni akan na bar gidan kafin Don Pedro ya dawo ya sa a mana koran walaƙanci. Na kalleta na ce ina zan je? Ina na ke da shi da zan je?.
Ina da passport amma ban da kuɗin jirgi idan ba a titi zan dinga kwana ba to ba ni da wajen zuwa.
Ta ce idan ba damuwa na bi ta mu je garin Watford akwai ƙaninta a nan. Ba yadda zan yi haka na ɗau jaka na sa kayana da na san nawa ne da passport ɗina na bi Mrs Payne mu ka bar London.

Ƙaninta mai suna Riley yana zaune da matar sa da 'ya'yan sa maza guda biyu, ɗan shekara shabiyar da ɗan shekara shaɗaya. Ɗakin yaran aka bamu saboda gidan ƙaramine ɗakuna biyu ne aciki yayinda yaran su ka koma kwana a falo. Buri na na haihu lafiya idan ya so na nemi yadda zan yi na koma Nigeria tunda ban san inda Ahmad ya ke ba...




S- I Miss her


Shekara ɗaya abubuwa su na ta bunƙasa mini, hankalina ya kwanta sosai saboda cigaban da na kawo a ƙauyen mu, idan ka cire koyarwa da na ke wa 'yan primary ba aikin da na ke yi daya wuce noma da kiwo. Ganin na samu nitsuwa ya sa Baffa da Jiji su ka fara kawomin maganar aure da farko wasa na ɗauka sai da su ka dage sosai ya sa na fahimci abin na su ba na wasa ba ne. Jiji har 'yan mata ta ke nuna min na zaɓa, yaran 'yan uwa da na maƙota, su kan nuna min duk ƙauyen ba wanda mu ka taso tare da bai ajiye mace ɗaya ko biyu ba. I was only 26yrs amma gani su ke na yi shekaru arba'in ban yi aure ba. Ganin maganar ta yi yawa ya sa na shirya tafiya ƙaro karatu a hankali na samu gurbi a Jami'ar Oxford, na ƙi Cambridge ne saboda Aaliyah. Cikin ikon Allah na kammala duk wani shirye-shirye na tafiya kuma Alhamdulillah duk wani hidima da gumi na nayi shi. Ana saura sati uku na tafi na yiwa su Baffa maganar tafiyar wanda ƙarara su ka nuna min fushin su domin sun fi so duk inda zan tafi to na tafi tare da mata.

Ranan da zan bar Durum zuwa Kano haka Jiji ta dinga kuka tana faɗin "Lamiɗo ka haƙura da Aaliyah, dan Allah kar ka guje mu. Dan Allah ka dawo da wuri ko ba za ka yi aure a Ƙauye ba ka nemi mata ka aura"

Na yi ta lallashinta da ƙyar ta dena kuka ta min addu'a sannan na tafi...

With everyday that goes by I Miss her. I miss her so much. Karatu ba wahala dan mafiyanci duk research ne. Wata rana wani abokina da mu ke karatu tare ya rasa iyalen sa a hatsarin mota. Musulmi ne ɗan ƙasar Chad, a Birmingham su ka haɗu da matar sa wanda ta hanunsa ta ƙarɓi musulunci. Joey 'yar gudun hijira ce daga Somalia tana aikin karuwanci a Birmingham kafin dalilin abokina Muzaffar ta bar karuwanci sannan ta ƙarɓi musulunci. Aisha Joey da ɗan sa AbdulShakur duka su ka rasu a hatsarin mota. Ni da shi mu ka wuce Watford inda iyalen sa su ke kafin mutuwar na su. Aisha Joey tana da ƙaramin grocery store da Muzaffar ya buɗe ma ta take zama. Shekarun su bakwai da aure ta rasu.
Dama Joey ba ta da 'yan uwa sai dai abokai kuma gaskiya an mata shaida mai kyau. Yadda Muzaffar ya rikice da ya ga gawar matar sa da ɗan sa ba ƙaramin tausayin sa na ji ba. Ba ƙaramin so Muzaffar ke wa matar sa ba, sai wanda ke yin soyayya tsakani da Allah zai iya auren tsohuwar karuwa. Na zauna da Muzaffar na kwana uku kafin na shirya komawa dan kar abubuwa su min yawa.

BookStore ɗin da na shiga na ke duba littafi na ɗaga Ido na hango ta. Tana tafiya gefenta wata mata tana riƙe da ita. Ina gani su ka tambayi wani littafi inda aka je aka kawo mu su, baƙar matar ta fitar da kuɗi ta biya sannan su ka fita daga shagon. Ina son zuwa na ma ta magana amma ba ni da dalilin hakan. Ga tulelen cikinta da ta ke tafiya da shi da ƙyar ya ƙara tabbatar min da yanzu ba da bane. Na cigaba da duba littafin amma hankalina bai kwanta ba domin ta rame ta lalace, na jingina hakan da cikin da ta ke da shi amma kuma zuciyata ta ƙaryata hakan. Her eyes bears a deep pain, cheerful Aaliyah da na sani ba ita ba ne wannan.
Duk yadda na so na daure na kasa haka na fita daga shagon na bi bayan su da sauri dan sun jima da tafiya. Da ke a hankali su ke tafiyar ba a jima ba na iso su. Ina bin su a baya a hankali cike da tausayinta. Komai nata ya chanja har tafiyar ta.
Wani garden su ka je inda baƙar matar nan ta taimaka ma ta ta zauna a kujera. Littafin da su ka siya ta fito da shi tana karantawa, tana yi tana shafa cikinta. A nan na ƙyalla ido na kalli zoben da na bata yana nan a hannunta. Abubuwa dayawa su ka fara min yawo a ƙwaƙwalwata, hawaye ma su zafi su ka fara zarya a ido na. Komai da ya faru na dinga gani Aaliyah 'yar ƙaramar yarinyar da na dinga goya a bayana, Aaliyah 'yan mata da muryan ta kaɗai na ji ina shiga wani hali. Yanzu kuma ga Aaliyah matar Ahmad ɗauke da tsohon cikin sa. Ina shirin juyawa ta ɗago kai ta kalle saitin inda na ke, muna haɗa ido ta miƙe zumɓur tana nuna ni, na yi saurin barin wajen ina sawa a raina bai dace ba, kallon matar wani bai dace ba musamman irin kallon da na ke wa Aaliyah. Addinin mu ya hana, Al'adar mu ya hana.

Gudu Aaliyah ta fara tana kira suna na amma ban waiwaya ba na cigaba da yin sauri.

Ihunta na ji lokacin da ta tsugunna ƙasa tana nishi da ƙyar. Na juya na hangota durƙushe a ƙasa tana kuka. Ba zan iya ganin Aaliyah acikin halin ƙunci na ƙyaleta ba shiyasa na koma da baya. Kafin na isa wajen Matar nan ta Isa gareta tana ƙoƙarin ɗaga ta. Ina zuwa ta kama hannuna ta ce "Hamma Sa'eed" daga nan kuma ta suma...

Ni da Mrs Doris Payne mu ka kaita asibiti inda ba a jima ba likitocin su ka ce ina mijinta ya sa hannu dan ba za ta iya haihuwa da kan ta ba. Mrs Doris na kalla ina so ta bada bayani tunda tare na gansu da Aaliyah dole ta san wani abu...

Ina hawaye na saka hannu a takardar bayan Mrs Doris ta bayyana min halin da ake ciki. Fatana bai wuce Allah ya sa Aaliyah ta haihu lafiya ba...





*22- Baby Zaid*

*S*

Ina zaune ina addu'a har aka fito mana da jariri, its a boy nurse ɗin ta faɗa. Na ƙarɓi jaririn ina kallon sa, ya ɗauko farin Aaliyah da ƙaramin bakin ta, sai yatsun sa da na ke ganin suma irin na ta ne. Na yiwa yaron huɗuba da Muhammad. Bayan na tabbatar an maida Aaliyah ɗakin hutu sannan na baiwa Mrs Payne yaron na je store na siyo mu su abin buƙata. Har na dawo ba ta farfaɗo ba dan haka na tafi domin nema ma ta mafita, ba zai yiwu ace ta haihu a ƙasar da ba nata ba ace kuma ba kowa na ta a kusa. Numbar Alhaji na nema na kira bai ɗauka ba sai a kira na uku. Ban nuna ma sa ko ni wanene ba na dai sanar da shi halin da Aaliyah ta ke ciki. Ashe Alhajin ma ba lafiya gareshi ba bai jima da dawowa daga ƙasar Egypt ba inda ya kwanta jinya kusan wata ɗaya. Numbar gidan Ahmad sun kira sau iyaka amma ba ta tafiya, jinyar Alhajin ne ma ya sa Amma ba ta taho London ba. Ya min godiya yana tambayar ko ni wanene na kashe kiran ba tareda na bashi amsa ba.
Da tsakar dare na koma asibitin inda aka ce min Aaliyah ta farfaɗo amma an mata allurar bacci saboda rikicewa da ta yi. Mrs Payne ta sanar da ni tunda Aaliyah ta farfaɗo ta ke kiran suna na. Na riga na gaya ma ta indai har Aaliyah ta farfaɗo ta tambayeni to tace ba ni ta gani ba wani bature ne ya taimaketa ba ni ba. Washe gari Iyalen Alhaji Tasi'u Wambai su ka zo daga London. Dama sai abu ya tashi ake tuna zumunci. Alhaji Wambai abokin Alhaji Bulama ne tun su na yara kuma a London ya ke da zama. Ganin Aaliyah na hannu mai kyau ya sa na bar garin Watford bayan na yiwa Aaliyah ganin ƙarshe a Asibiti wannan karan ba tareda ta ganni ba...



*A*


Gaba ɗaya su ka maida ni mahaukaciya lokacin da na ce mu su Sa'eed ne ya kawoni asibiti, Har Mrs Payne ma ƙaryata kwatance na ta yi ta dinga faɗin wani bature ne ba Sa'eed ba. Ta ya zan manta da Sa'eed? Ta ya zan manta da mutumin da na taso da son shi. Ganin sun ƙi kulani hakan ya sa na yi shiru ina ganin su kawai. Kwana na goma na koma Nigeria , Amma ce ta zo min daga Nigeria ita ta zauna da ni a kwana na uku da haihuwa.

A Nigeria kowa Allah wadaran ya ke da Ahmad ganin yadda na ƙara lalacewa fiye da da.
Baba kam bai iya ce min komai ba, ya jiki kawai ya iya min, kunyata ya ke ji yanzu.

Kwana na ishirin da haihuwa aka yi taron suna domin na samu lafiya sosai, yaro na yaci sunan ZAID, Baba ne ya zaɓi sunan saboda sunan ɗan sa na fari kenan da ya rasu a ranan sunan sa, ni ban san da labarin ba ma sai a ranan dan na ɗauka Yaya Bukar ne ɗan fari. Amma da sauran 'yan uwa na kowa ƙoƙarin sa ni farin ciki ya ke. Wata na ɗaya da haihuwa Sanah ta haihu ta samu ɗa namiji, a chan Canada aka yi sunan inda ɗanta ya ci sunan HAFIZ.

Ashe su na da labarin an sake Ahmad amma ba su gayamin ba domin Baba ya riga ya rantse Ahmad na fitowa zai sa ya sakeni. A ƙoƙarin Baba na ganin ya raba aurena da Ahmad ne ma ya sa ya biya maƙudan kuɗin da ake bin Ahmad bashi. Ba ƙaramin asara Ahmad yai ba a chachan nan. Hauka ne kawai Hajiya Inna ba ta yi ba lokacin da aka sanar mata abinda Ahmad yai domin abin bai tsaya a kadarorin Alhaji Wamako na ƙasar waje ba har da na gida Nigeria, gashi dama danne hakkin marayu da Inna ta yi ya sa abubuwa sun lalace ma ta, ga uwa uba kuma chachan da Ahmad yai da dukiyar ta su. Idan za ka kasa dukiyar Alhaji Wamako kashi ɗari to kaso tamanin sun tafi a chacha.


Ahmad na fita daga prison da ya dawo Nigeria gidan mu ya zo ya fara nema na. Dan ya san zuwa yanzu dole na haihu. Da ya zo hanashi shigowa aka yi amma ya tsaya a compound yana mu su hauka a haka Baba ya shigo gidan ya same shi. Yana fitowa daga mota Ahmad ya nufe shi yana faɗin Baba ya fito ma sa da matar sa da ɗan sa. Baba ya tsinke shi da mari yana faɗin ya bar ma sa gida kafin nan kuma ya ajiye takardar saki na. Ahmad ya ce ba abinda zai yi, shi dai kawai a fito ma sa da matar sa da ɗan sa.

Baba ya ma sa tuni da alƙawarin da ya ɗauka kafin a fitar da shi daga prison. Ahmad ya ce bai san zance ba. Takaici ya kama Baba ya sa masu gadi su ka fitar da shi.

Baba ya ɗauka abin ya ƙare daga haka, inda ya bari a kan sai Ahmad ya huce takaici na kwana biyu tukunna kafin ya sake waiwayansa da zancen saki na, kwatsam sai ga sammaci daga kotu wai Ahmad na ƙaran Baba. Rashin kunyar Ahmad ta kai yai ƙaran Baba bayan irin halaccin da Baban ya ma sa.

Ba wannan ba ma harda maganar wa su kuɗaɗe na Alhaji Wamako da su ke iƙirarin Baba ya cinye. Ranan da aka kawo takardan sai da ciwon Baba ya tashi. Aka kaishi asibiti da gaggawa. A asibitin Ahmad ya zo yana yiwa Baba maganar shi ba komai ya ke so ba irin Matar sa da ɗan sa idan har ya maidoni wajen sa to zai janye ƙaran dama ɗaya tuhumar Inna ce ke yin sa ba shi ba. Baba garin mai da wa Ahmad maganan sa ya ƙara rikicewa da ƙyar aka samu aka stabilizing na shi.

Ina zaune a ɗaki ina shayar da Zaid Haruna ya shigo ɗakin yana min masifa akan na san yadda zan yi da Ahmad kafin shi da kan sa ya kashe shi. Duniya kenan shekaru biyu da su ka wuce a ɗakin ya sameni yana zagina kan na ƙi auren Ahmad Wamako sai gashi yau yana maganar zai kashe Ahmad ɗin.

Ina shafa kan yaro na na ce " mi yai zafi Haruna? Ka manta Ahmad kyakykyawa ne ɗan Babban gida kuma mai kuɗi?"

Shiru yai na wasu daɗiƙai kafin ya ce " ki san yadda za ki yi da mijin ki"


Bayan na ji labarin duk abinda ke faruwa ba tareda shawaran kowa ba na shirya kayana da na ɗana na fita. Amma na asibiti shiyasa ban samu matsala ba, dreban gidan mu na samu na ce ya kaini tasha. Kai tsaye Sokoto na nufa duk da kuwa na san yanzu ba asiri ajikina Amma ta ce an warware komai hakanan na daina jin wannan attachment ɗin da na ke ji gameda Ahmad a da. Yanzu zan koma wajen sa ne for peace to reign, ka da dalilina a ci mutuncin Baba. Tausayinsa na ke ji yanzu da ba shi da lafiya, tsoro na ke ji kar baƙin ciki ya kashe shi kamar yadda ya kashe Alhaji Wamako...

Gidan dai yana nan yadda ya ke iya ka ci da na shiga ɓangaren mu na samu wasu mutane a ciki ashe Inna ce ta sa 'yan haya. Na ta gidan na je inda ɓangaren Marigayiwa Alaja Atinuke ma an sa 'yan haya a ciki. Lallai Inna ta ga bone. Na ta sashen ma gashinan ga kamarsa, mai aiki ɗaya gareta wata tsohuwa wanda ban san ta a da ba. Tsohuwar ce ta ce min Inna ba ta nan, na ce Ahmad fa ta ce ba ta sani ba amma za ta duba min. Na zauna a falon ina jira yayinda ta fita zuwa sashen Alhaji na da.

Zaid na kwance a baya na wanda yai kuka ya gaji acikin mota yai bacci. Har lokacin baccin wahala ya ke yi, ina kallon ɗana wanda tun ranan da na buɗe ido aka nuna min shi na ke jin tsananin son sa, ban damu da tsananin kaman sa da Ahmad ba buri na shine halinsa ya banbanta da na uban sa. Na ɗau alkawarin ɗaura shi a akan tarbiyya mai kyau, zan koya ma sa daraja mace, zan koya ma sa ibada da kuma riƙo da gaskiya. Na tabbata kaso saba'in cikin halayen Ahmad sun samo asali daga Inna ce saboda mummunan tarbiyan da ta ɗaura shi akai.

Kaman jira ya ke na kawo shi gidan uban sa kawai ya farka ya fara kuka, na ɗauke shi na sa shi a kafaɗa na ina jijjiga shi dan na bashi nono kafin yai bacci ɗazu a mota.

Kamar mahaukaci ya shigo falon a birkice yana ihu. Ya karɓi ɗan sa a hannuna yana jijjiga shi. Na zuba ma sa ido ina ganin yadda ya koma, a zama na da shi ban taɓa ƙare ma sa kallo kamar yau ba. Ahmad ya fige yai wani fayau da shi, jajayen idon sa sun ƙara zama ja. Lallai wahala ba ta yi ba musamman ga wanda ya saba da jin daɗi.

" Zaid sunan sa ba" ya faɗa yana kallona

Na haɗiye miyau na ce "idan ba ka so sai a chanja"

Ya girgiza kai yana faɗin "duk sunan da ki ka sa ina so. Aaliyah ki ga yadda ya ke ta murmushi ya ganni"

Ya fara kissing goshin sa yana faɗin "Son ka ga Baban ka ko? I'm sorry ba na nan lokacin da ka zo duniya. Na maka alkawarin zan ba ka duk wani gata a duniya, ba za ka taɓa neman abu ka rasa ba"

Ina tunanin ko a ina gatan zai zo ga wanda ya riga ya lalata rayuwar sa.
Bayan Zaid ya koma da bacci ya jani zuwa sashen Alhaji shima sashen fayau ya ke abubuwan ƙyaleƙyale da ke gidan a da yanzu duk babu shi ina da yaƙinin siyar wa aka yi. Yana ɗaura Zaid akan gado ya shiga sarrafani yadda ya ke so, jikin sa har rawa ya ke, ƙoƙari ya ke kar ya ga ya min mugunta kamar yadda ya saba amma still sai da na ji zafi, ban sani ba ko dan na riga na sawa raina akan zan ji zafin ne.

A ƙasa mu ka yada zango inda na tuna da daren farko na da shi yadda ya raping ɗina a ƙasa wannan ɗin ma duk sammakal tunda ba wai ina so ba ne.
Ganin hawaye a ido na ya sa ya rikice yana tambayan dalilin kuka na.
"Saboda Baba ki ke kuka ko? Dan Allah ki bar kuka zan janye ƙaran gobe-goben nan. Dama saboda ke ne ya sa na shigar da ƙaran. Wai ki ji Baban ki ya sa na sa hannu akan idan ya fitar da ni a prison zan sake ki. Ta ya zan sake ki? Ta ya zan rabu da ke? Ke kaɗai ce ki ke zaune da ni babu munafurci, ni da ke mutu ka raba"

Na rufe ido na ina cigaba da kukan zuci "ni da Ahmad mutu ka raba" abin da ya ce kenan kuma abinda ya farun kenan...








*23-Father's death*



*A*

Sai da na yi kwana biyu tukunna Inna ta dawo, ita ma ta chanja amma ba kamar Ahmad ba. Na ɗauka ganin Zaid zai sa na yi daraja a wajen Inna amma abin ba haka bane. Sam yaron ba ya gabanta, yana kwance a gado ta leƙa shi ta ce "ba ri mu ga ko ɗan shege a kawo mana"
Ta ƙura ma sa ido sosai sannan ta ce " saura ka ɗauko farar ƙafar uwarka, dan tunda aka aurota komai ya lalace mana"

Ta kalleni ta ce "ke kuma ki gayawa Ubanki ya fitar da kuɗin da ya cinye idan ba haka ba yadda aka kulle Ahmad haka zan sa a kulle ki"

Ban yi magana ba sai da na bari ta kusa fita daga ɗakin sai na ce " Alhaji Bulama ba ɗan chacha ba ne, kuma bai ta ke hakkin marayu ba balle bala'i da masifa ta afku ma sa kamar yadda ta afko ga wa su Iyalai marasa tsoron Allah"

"Ni Aaliyah ki ke gayawa magana dan Uban ki"
Na juyar da kai na gefe. Ta fara zage-zage kamar za ta ci kan ta ko uffan ban ce ba haka ta gama ta fita...


Sati na ɗaya a gidan, Ahmad ya zo da murnan sa yana gaya min wai ya janye ƙarar Baba da ya ke yi. A ganinsa yayi abin gwaninta kenan...

Amma fushi ta yi dani lokacin da ta dawo ta samu ba na gida, ta kirani ta dinga faɗa tana faɗamin idan na yi haƙuri za a ci galaba akan Ahmad. May be na gaji da komai ne, may be kuma na rufe samun farin ciki a rayuwata shiyasa na dawo ga Uban ɗana.

Zaman mu da chanji sosai compared to da, ni da Inna ba ma ga maciji, bayan gaisuwa wanda idan na yi ba ta amsawa, shikenan. She's so busy bin manyan mutane da neman yadda za su farfaɗo daga karayar arziki da ta samesu. Yadda ta ke marar tausayi haka yaranta duka su ka tashi ba sa tausayinta. 'Ya 'Yanta mata duk manyan mutane su ka aura amma kuma duk sun fita harkanta musamman da aka gama batun rabon gado su ka ga tsananin son kai a ciki. Ni na ke shiga kitchen na yiwa kai na girki, ga ɗawainiyar ɗana. Wani lokaci Baaba Gambo mai aikin Hajia na shigowa wajena ta tayani ba ni na sata ba ita ta saka kanta.

Tsakanina da 'yan gidan mu sai dai waya amma ba mai zuwa mini kuma ba na zuwa gida. Wata na biyu a gidan Ahmad ya samu aiki, shige da ficen Inna ne yai tasiri sai dai ba a Sokoto ba ne a Abuja ne, dan haka Ahmad ya tattara mu muka koma Abuja da zama.

Ahmad ya rage shan giya, dan bai taɓa zuwa gida a buge ba sai dai na kan ji warinta a jikinsa lokaci zuwa lokaci. Duk wata idan aka ma sa albashi haka zai je kasuwa yai ta siyowa Zaid kayan sawa da kayan wasa. Wa su kayan ma ƙila sai ya kai shekara goma kafin ya fara amfani da su amma ba ruwansa haka zai yi ta jibgo su, ban taɓa yi ma sa magana ba na dai zuba ma sa ido.

Shekaran mu ɗaya a Abuja Jikin Baba ya tsananta daga Egypt an wuce da shi India daga nan aka miƙa shi ƙasar Germany, rabona da Baba tun da na dawo gidan Ahmad tun lokacin kuma bai sake lafiya ba daga gida sai asibiti haka ake fama da shi duk wasu business ɗin sa Bukar da Haruna ke kula da shi dan Aliyu kam ya zama zauna gari banza karatun ma ya watsar tuntuni.

Amma ce ta kirani akan maza-maza na zo gida domin Baba na nemana. Yadda

Please Login or Register in order to submit comment