You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinka da ma su arziƙi ba mota za mu bi ba jirgi za mu bi.
Motar mu na fita daga gate ɗin gidan mu na juya na kalli gate ɗin sai ga hawaye yana zubo min. Daga yau na rabu da gidan mu kenan, sai dai ziyara, daga yau na zama mallakin Ahmad ba Sa'eed ba, daga yau na rasa 'yancina na matsayin budurwa tunda na zama matar aure. Na kifa kaina na fara rera kuka...







*14-Black night*



S


A garden na samu Alhaji yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da aka ajiye dan shaƙatawa, Kayan marmari iri-iri da aka yanka ƙanana aka tula a gaban sa yana ci.
Na tsugunna ɗan nesa da shi na gaishe shi. Bai amsa ba sai da ya cakwkwalo apple da fork ya kai bakin sa ya tauna sannan ya haɗiye kafin ya ce da ni "Lafiya Sa'eed"
Yanayin fiskar sa bai nuna alamun da zan gane ko akwai wata matsala ba. Na sunkuyar da kaina gameda sauke nannauyan ajiyar zuciya. Ban ɗago na kalleshi ba amma na san kayan marmarin da ke gaban sa ya cigaba da ci.
Bishiyoyin da ke wajen su ka cigaba da kaɗa iska mai daɗin ni'ima, ga ƙanshin furanni da ya sake sanya iskar ta zama da daɗin shaƙa.
Idan ka cire bishishoyi da furanni da su ke kaɗawa a wajen to sai kuma ƙaran fork da ke gugar faffaɗan tray ɗin da aka zuba kayan marmarin da Alhaji ke ci. Babu wani motsi da ke nuna akwai halittar mutum a wajen.
Shirun yai yawa har na ke tunanin ko dai Alhaji ya manta da ni ne. Ba zan iya tuna tsawon tsugunnon jira da na yi a wajen ba amma na san gaskiya na jima sosai, hatta ƙafafuwana sai da su ka yi tsami. Ban ce ƙala ba na cigaba da jiran tsammani. Ina tsugunne a wajen zuciyata cike da tunani kala-kala sai na ji sallama a bayana. Na ɗago fiskata na juya gefena inda mutumin da yai sallama ke tsaye ƙiƙam yana jira Alhaji ya bashi umurni.
Maimakon Alhaji ya ma sa magana sai ya dube ni ya ce "Sa'eed ka bi Ubaidu, zai kai ka wajen da za ka min wani aiki"

"Shikenan Ranka shi daɗe" na faɗa tareda miƙewa na bi bayan wanda aka kira da Ubaidu. A shekaru na san zan girme shi sosai amma da ke shi ɗin yana da girma da faɗin jiki sai ya zamana ka iya ɗauka ya girmeni sosai. Idan da faɗa zai shiga tsakaninmu na tabbata ba ƙaramin lallasani Ubaidu zai yi ba saboda yanayin sa kaɗai ya nuna ba ƙaramin motsa jiki da aikin ƙarfi ya ke ba. Zubin Ubaidu zubin sojoji ne ko bodyguard.

Na yiwa Ubaidu sallama amma bai amsa mini ba kai ko kallona bai yi ba.
"Malam Ubaidu ai ko ba komai ka amsa sallama"

Jin bai kulani ba na ja baki na nayi shiru muka cigaba da tafiya.
Chan wajen gate mu ka nufa inda wata mota ke jiran mu. Ni da Ubaidu mu ka shiga bayan motan yayinda gidan gaban ke ɗauke da wasu Maza biyu, na musu sallama lokacin da na shiga motar wannan karan na ci sa'a wanda ke zaune a mazaunin dreba ya amsa sallamata. Ban ce komai ba haka su ka tada mota mu ka fita daga gidan.
Tafiya mu ke sosai har mun fara ficewa daga cikin gari, ban iya tambayar su inda za mu ba dan yanayin su bai bani damar tambaya ba. Tunda Alhaji ya ce aiki zan je na ma sa, to na san duk rintsi dai a cikin garin Maiduguri ne aikin.
Tafiyar awa ɗaya da rabi ta kaimu gidan gonan Alhaji. Na taɓa zuwa gidan gonan, lokacin da Aaliyah ta yi birthday ɗin cika shekara shabiyu a duniya.
Muna fita daga cikin motan Ubaidu ya ce na bi shi. Ba mu su na bi shi zuciyata cike da wasi-wasi.

Chan ɓangaren gidajen ma'aikata mu ka je inda muka tsaya a bakin ƙofar ɗaya daga cikin flats ɗin da aka gina dan ma'aikata.
Ubaidu ya ciro key ya buɗe gidan ya shiga ciki bayan ya ce na biyo shi.
Falo mu ka tarar wanda ya sha ƙura saboda daɗewa da aka yi ba'a amfani da shi, ba komai a falon sai tsofin kujeru wanda datti da ƙura su ka jima da samun gindin zama a jikin su.

"A nan za ka zauna har sai Alhaji ya neme ka. Idan ka kwantar da kai ba abinda za mu maka har ka tafi amma idan ka yi taurin kai wallahi umurni aka bamu mu bugeka son ran mu"

Maganganun da Ubaidu ya faɗa kenan yana huhhura hanci. Mamaki, tsoro, fargaba, dana sani duk su ka haɗu su ka mamaye min zuciyata.

"B B Ban gane ba? Ubaidu miyasa Alhaji zai sa a kawo ni nan"
Na ma sa tambayar ina da yaƙinin ko dai ya amsa min da baƙar magana ko kuma yai banza dani, ya bar ni da amsa tambayar da kai na.

"Za a kawo maka abinci sau uku a rana. Zan maimaita abinda na faɗa da farko, idan ka yi taurin kai girman ka ba zai hana mu buge ka ba"
Daga haka ya fice daga falon ya barni tsaye baki buɗe. Ina ji yana kulle ƙofar gidan da key amma ba abinda na iya yi.
Tausayin kai na da kuma Aaliyah na fara yi, idan har Alhaji ya sa aka kulleni kenan ya san da maganar shirin mu da Aaliyah kenan. Lokaci guda na furta "Aaliyah" a fili, ba abinda na ke tunowa irin halin da Aaliyah za ta shiga idan ta jira ni da dare ba ta ganni ba. Ganin ba mafita sai Allah ya sa na shiga kiran sunan sa dan ya kawo min ɗauki...

Da dare da Ubaidu ya kawo min abinci na roƙi Alfarma akan ko da dai ba zai bar ni na fita ba ina so ya nemomin takarda da biro na rubuta saƙo. Ubaidu ya ja tsaki zai fita na riƙe ƙafarsa ina cigaba da roƙon sa. Buri na koda zan rasa Aaliyah ina so ta sani ba da gangan na karya alƙawarin da na yi ba, ba da gangan na yi watsi da shirinmu ba.
Ubaidu ya tureni tareda faɗin idan na sake taɓa shi ba zan ji da daɗi ba. Sai da ya fita daga falon hawayen ƙunci da baƙin ciki su ka fara zubo min. Tsorona kar Aaliyah ta ce za ta kashe kan ta saboda na ƙi bayyana a wannan dare, tsorona kar Aaliyah ta gudu ita ɗaya ta shiga duniya kamar yadda ta ke yawan iƙirari.

Kuka sosai na ke yi ina ambaton Allah ya taimakeni kar Aaliyah ta aiwatar da ɗaya daga cikin abu biyu da na ke tunani. Ban iya bacci ba a wannan baƙin dare.
Ko ban auri Aaliyah ba bana so ta faɗa halaka saboda ni, wannan shine babban buri na a wannan baƙin dare...

Kwana ɗaya biyu uku huɗu... haka kwanakin su ka yi ta wucewa ba tareda na samu hanyar fita daga gidan ba, ba tareda na san halin da Aaliyah ta ke ciki ba. Idan ka cire ruwa ba abinda na ke amfani da shi cikin abincin da su ke kawo mini. Banda sallah, addu'a da kuka ba abinda na ke a ɗan ƙaramin gidan nan, wanda falo ne da ɗakuna biyu sai banɗaki da kitchen. Ranan farko da na biyu na yi yunkurin neman wajen guduwa amma ba hali, haka na haƙura na fawwalawa Allah komai...

Ina irga kwanaki har ya kai saura kwana ɗaya a ɗaura auren Aaliyah. Ina ji ajikina tana raye kuma tana gida, koda Ubaidu da sauran samarin nan ba su sanar da ni komai ba, zuciyata ta sanar da ni Aaliyah na raye kuma tana gida. Daren ranan da na kwanta na yi mafarkin ina tafiya acikin jeji sai na hango wata bukka a tsakiyar jejin. Na yi sauri na nufi bukkar saboda gajiya da ishirwa da ke damuna, ina tunkaran bukkar na fara jiyo ihun Aaliyah kuka ta ke tana kururuwa haɗe da roƙo da magiya. Na sa gudu sosai dan na gaggauta isa bukkar na ceci masoyiyata sai kawai na yi tuntuɓe da wani ƙaton dutse na faɗi ƙasa. Ina jin muryan Aaliyah tana kiran suna na amma na ka sa tashi, na kasa motsawa. Na miƙa hannuna ɗaya ina furta sunan ta a hankali "Aaliyah" ...
Da sunan Aaliyah na farfaɗo daga bacci jikina na ƙyarma saboda tsoro.Duk yadda aka yi Aaliyah na cikin tashin hankali, na tashi da sauri duk da jikina da yai rauni saboda yunwa. Na fara neman yadda zan yi na bar gidan nan ina tunanin idan ban fita yau ba ƙila ni da Aaliyah sai a lahira. Tun da daren da na tashi na ke neman hanyar fita har rana ta fito. Akwai window na glass a banɗaki amma a rufe ya ke kirif da kwaɗo gashi na duba gidan kaf babu abunda zan samu na fasa shi. Abinda na samu na yi ta bugawa plate ɗin roba ne da aka kawo min abincin dare amma bai fashe ba. Na ji haushi na dunƙule hannu na fara nausan windown ko zai fashe, zafin da na ke ji bai dameni ba face zafin rashin Aaliyah, na cigaba da bugun glass ɗin. Glass ko alamar fashewa bai yi ba sai ma nawa hannun daya fashe yana jini amma still ban dena buga hannuna ba. Na jima ina bugawa kafin naji kaman daga sama an jawo ni ana kai min duka ta ko'ina. Bugun da na ke yi Ubaidu ya jiyo lokacin da zai kawomin abincin safe hakan ya tunzurashi ya sa ya shigo banɗakin a guje ya hau jibgata. Ko da ina da isashshen ƙarfi da ƙyar zan iya ƙwatan kaina a wajen Ubaidu balle yanzu rabon da na ci abinci har na manta. Tun ina iya jiyo zagi da tsinuwa da ya ke yi har na dena jin komai na fara ganin duhu ƙarshe na sume a wajen....






*15-Black night 2*

*A*



Mutane takwas ne kawai za su rakani Sokoto, sauran duk daga airport su ka juya.
Ni da Sanah ne mu ka zauna kusa, idan akwai wanda zan iya bugan ƙirji na ce ta fahimci halin da na ke ciki a wannan lokaci to Sanah ce. Akwai yayar mu Falmata sai ƙannen Baba Hajiya Aisha da Hajiya Hafsatu sai yayar Amma wato Hajiya Rahima. Sauran ba zan iya cewa suwaye ba ne dan ƙuncin da na ke ciki ya fi gaban na tsaya duba su waye za su rakani.
Lokacin da mu ka isa tuni motocin gidan Alhaji Wamako su na tsaye su na jiran mu. Tun da na fito wanda su ka zo taran mu su ka sa guɗa su na shewa da tafi. Duk wani shirmen su baya gaba na lissafina yadda kowani rana za ta kasance tareda mutumin da banda sunan sa ba abinda na sani game da shi. Akwai wata Inna Ɓodejo wanda ban san daga ina ta haɗu da dangina ba a chan Maiduguri kafin mu taho lokacin da na ke gaban Amma da 'yan uwanta a falo tana min addu'a.
Ƙus-ƙus ɗin da ake yi na cewa ban yi kuka ba irin wanda Amare ke yi idan za a kai su gidan miji ya sa wasu ke cewa ai saboda ba na son mijin ne. Tashin wannan bagidajiyar mata ta ce " yo ai wannan ba dalili ba ne. Mu da zamanin mu haka ake kai mu gidajen miji ba tareda ko fiskar mijin mun taɓa gani ba. Ko yana da kyau ko mummuna ne sai dai idan an kai ki ɗaki ki ganshi. Kuma a hakan mu ke zama lafiya-lafiya. Aaliyah ki godewa Allah kawai domin kina da sa'a"

Ban san lokacin da na ɗago fiskata na kalli fuskar matar ba, wanda gani ɗaya na mata na san wannan kalen dangi ce. Cike da ɓacin rai na ce "wani sa'a kenan Baaba?" Yadda na yi maganar ya sa aka yi chaa akan ta ana faɗin Inna Boɗejo ba ki kyauta ba wai yarinya na jumurin barin gida kina sake tunzurata.

Kuɗi kenan wanda ke maida yaro babba, maimakon su min faɗa sai su ka yiwa tsohuwar nan chaa har sai da na ɗan ji tausayinta. Wannan rikici ya sa aka tarkatani aka wuce dani sashen Baba...

Ban sake hannun Sanah ba dan haka dole mota ɗaya mu ka shiga aka wuce da mu gidan da zan zauna, gidan aure na.
Babban gida ne sai dai bai kai namu girma ba. Tsarin ginin dai zan ce ya fi namu saboda gidan anginashi aƙalla ba zai fi shekaru biyar da su ka wuce ba, ba kaman namu da ginin ya fi shekara talatin ba, duk da gidan mu irin gida ne sa ke tafiya da zamani amma akwai wasu chanje-chanje na yayi wanda tsarin ginin gidan Alhaji Wamako ke da shi amma namu ba shi da shi.

A Lagos Alhaji Wamako ke yawan kasuwancin sa shiyasa ya fi zama a chan, idan ya zo Sokoto kuwa to a garin Wamako ya ke sauka a nan yai ginin sa a kusa da gidan gadon su. Sai dai ko wani dalilin ne ya sa yai wani ginin acikin garin Sokoto ya dawo nan da zama Allah shi ne masani.
Ɓangaren Alhaji Wamako aka wuce da ni wanda tsakanin gidan da gidan da ya ginawa ɗan sa Ahmad ba ko katanga a tsakani, sai dai gate ɗin gidan biyu ne, na ɓangaren sa da kuma na ɓangaren gidan Ahmad.

Sashen Hajiya Inna wacce ta ke Uwargida kuma mahaifiyar Ahmad aka wuce da ni dan na gaisheta. Tsugunnon dole na yi a gaban matar da kallon arziƙi ni ko 'yan uwana ba mu samu a wajen ta ba.
A wajen ta ke gayawa 'yan uwana magana wai ko iya kayan da aka turo tun shekaranjiya ne kawai kayana ko kuma akwai wanda za su zo daga baya? Dan wai ita ta yi mamakin ƙarancin kayan.

Hajiya Hafsatu wanda kowa ya shaideta cikin familyn mu da zafi da faɗa ta maidawa Hajiya Inna da martani ta ce "Har wata Agola ce za ta cewa 'yar ma su gida kaya sun yi kaɗan?. Wani matsiyaci, tsatson talaucin ne zai ce tireloli goma sun yi kaɗan?. Wa ya taɓa aika 'yar sa da wannan a duk faɗin garin nan?" Ta ja dogon tsaki ta ce "daɗin abin ma shekaru uku da su ka wuce aka aurar da 'yar gidan nan kuma muna da tarihin da mi aka kaita ɗakin ta"

Ni kaina sai a wajen na san trailer goma aka totsa da kayana su ka taho Sokoto. Na sani ba komai ya sa Baba wannan almabazzaranci ba fa ce kawai ya nuna cewa Bulama da Wamako akwai Banbanci, na sani shi a wajen sa kaman ya siya min girma da daraja ne, amma a wajena bai burge ba sai ma haushin sa da na ji.

Hajiya Inna ta sha jinin jikinta dan ta gamu da gamonta. Dama ta kawo maganar ne dan ta ƙasƙantar da ni a gaban 'yan uwanta da 'yan uwan Mijin ta, sai kuma ta samu Hajiya Hafsatu Bulama ta fi ƙarfin gaban raini. Bayan dama tun asali na ji ana cewa ni Aaliyah zaɓin Alhaji Wamako ne, ita Hajiya Inna akwai zaɓin da ta so ɗan ta Ahmad ya aura. Wannan rana shine zan iya cewa ya fara rura wutar ƙiyayya da Hajiya Inna ta ke min...

Fiskoki ba fara'a haka aka fito daga sashen Hajiya Inna aka wuce da ni sashen matar Alhaji Wamako ta biyu wato Alaja Barakat Atinuke. Wannan mata babbar 'yar kasuwa ce a garin Lagos, Mijinta na fari Alaji Ishola AbdulYaqeen ne ya mutu ya bar mata tarin dukiya, kasancewa 'yar su ɗaya da shi ya sa 'yan uwan sa su ka hau kan dukiyar su ka zauna, abinda su ka bata bai fi kaso goma cikin ɗari na abinda ya kamata ace ita da 'yarta Misturah sun samu ba. Da wannan ta fara kasuwanci tana kula da 'yar ta kuma cikin ƙanƙanin shekaru Allah ya albarkaci kasuwancin ta.

Kasuwanci ne ya haɗa Alhaji Ibrahim Wamako da Alaja Atinuke wanda a hankali su ka fahimci junan su. Riƙon addini da kuma riƙo da gaskiyarta ya ja hankalin Alhaji Wamako akanta har yai sha'awar aurenta musamman dan ya kula da 'yarta marainiya 'yar shekara shauku a lokacin.
Auren kusan a sirrance aka ce yai saboda tsoron Uwargidan sa Asma'u wanda ake kira da Hajiya Inna. Sai daga baya ya faɗa ma ta.
So biyu yana aure tana fitinar matan suna guduwa sai akan wata Jamilah 'yar Zamfara ta kasa taɓuka komai akan ta. Abunka da matan manya ko a lokacin anyita cece-kuce akan maganin Jamilah ne ya fi nata ƙarfi shiyasa ta kasa koran ta. Jamilah ta zauna har ta haihu biyu a gidan duka mata sai a na ukun da ta zo haihuwa da ita da yaron su ka rasu. A gida ta fara naƙuda, kafin a kawota asibiti jikinta ya bircike ƙarshe ɗan bai gama fitowa ba ma Jamilah ta koma ga mahaliccinta, yaro kuma dama bai fito da rai ba.

Sha'ani na ma su kuɗi da yadda ake kai mu su gulman 'yan uwan su ma su kuɗi da ɗumi-lumin sa, haka har falon Amma aka zo ana gulmata ma ta wai Hajiya Inna ce ta kashe Jamilah. Amma na ba mai yadda da irin waɗannan abubuwan ba ne shiyasa ina kwance kan kujera ina karatu a falon na ji Amma na gayawa matar da ta kawo gulman cewa Jamilah lokacin ta ne yai ba abinda Hajiya Inna ta mata. Duk da alokacin ina da ƙarancin shekaru ban fahimci maganganun su sosai ba dan ba zan wuce shekara tara ba a lokacin, amma na fahimci yadda ake ta gulmammakin Hajiya Inna to ba makawa matar ba ta kirki ba ce.

Bayan Jamilah ta rasu Hajiya Inna ta kame gida ita ɗaya sai kwatsam ta ji zancen auren Alhaji Wamako da bazawaran Bayarabiya a sama. Ta ɗaga hankalinta matuƙa sai dai har yau ɗin ba yadda ta iya suna tare.
Ba gida ɗaya su ka zauna ba a chan Lagos ɗin dan duk zuwan mu Lagos gaisheda Alhaji Wamako idan mun je ni da Amma a gidan Alaja Atinuke mu ke sauka. Matar ba ruwan ta tana da son jama'a ga ta da yawan kyauta da sadaka, duk Jumma'a aka ce ta ke sawa ayi sadakan abinci safe rana da dare. Alaja Atinuke ta haifawa Alhaji Wamako 'yan biyu maza amma ɗayan ya rasu tun yana jariri daga nan kuma ba ta sake haihuwa ba.

Yaran Alhaji Wamako duk mata ne su ka fi yawa. Hajiya Innar ma bayan Ahmad ba ta da wani ɗa namijin. Ance immediate brother ɗin Ahmad namiji ne amma shima bai yi tsawon rai ba dan bai fi shekara biyu ba ya rasu. Hajiya Inna ta yi ta haihuwan amma still mata ne shiyasa aka ce tana ji da Ahmad kamar ranta...


Tarɓa mai kyau mu ka samu a wajen Alaja Atinuke wanda ta dinga mana barkwanci da gurɓacecciyar Hausarta wanda har yau bai saitu ba. Ta nuna farin cikin ta da wannan aure tareda damƙawa 'yan uwana kyauta. Ban san mi ta ba su ba amma ko da sun san dai sun fi ƙarfin wani kyauta da za ta ba su. Dalilin karamcin da ya sa ta bada kyautan ne ya sa su ka amshi kyautan su ka yaba.
Lokacin da aka wuce da ni gidan mu ba ƙaramin gajiya na ke ji ba ga kaina da ke wani irin sara mini.

Abin mamaki bayan sun gama surutu da nasihohin su na boge su ka wuce su ka barni ni ɗaya. Har Sanah da na roƙa ta tsaya ba su barta ba, ita kam ma da kuka aka fitar da ita daga ɗakina.

Sai da su ka tafi gidan yai tsit sannan damuwa ta sauka min. Ina ma Sa'eed na ke aure, da wannan dare ya zama dare mai cike da tarihi a rayuwata. A wajen hidindimun biki da mu ke haɗuwa da Ahmad ya kan raɗa min a kunne akan wannan dare sai ya kashe min duk wani rashin kunya da na ke ji. Na fara girgiza kai ina ƙoƙarin daurewa kar na yi kuka. Ga dai daren da Ahmad Wamako ke faɗi ga kuma daren da na yi mafarki na ci buri da alwashin mallakawa Sa'eed gangan jikina domin zuciya da ruhi na sun jima da zama ta shi...

Ana kiraye-kirayen sallar Isha na tashi na shiga banɗakin da ke ɗakin na ɗauro alwala na fito na gabatar da sallolin da ake bina tareda zama a sallayar ina cigaba da kai wa Allah kuka na. Na jima ina zaune ina addu'a kafin aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo. Kallo ɗaya na ma sa na kauda kai na na cigaba da abinda na ke yi.
Ina ji ya zauna a bakin gado tareda cewa "ki gama duk noƙe-noƙen ki yau daren na kuka ne da cizon leɓe". Ban yi kamar na ji shi ba na cigaba da gayawa Allah damuwa ta. Bai fi minti biyar da shigowar sa ba mu ka fara jin ƙaran telephone daga wani ɗaki kusa da nawa ya tashi da sauri ya fita. Yana gama amsa kiran wanda ya shigo ta wayar tarho ya fita daga gidan, shiru-shiru zai dawo bai dawo ba dan haka na tashi na hau kan gado na kwanta, ido na biyu ina sallamawa kaina na rasa 'yan ci na har abada daga yau, hakanan na rasa masoyina na gaskiya har abada.
Ina cikin saƙe-saƙe ya banko ƙofa ya shigo. Da kakkausar murya ya ce "saboda dangin ki mahaukata ne shine za su zo har gida su zagi Inna ta. Inna ta ku ke cewa Agola 'yar matsiyata?"

Ɗazu da 'yan uwana su ka kawo ni ɗakina da ake maida zancen abinda Hajiya Inna ta yi shine Hajiya Hafsatu ke bamu tarihin Hajiya Inna. Mahaifiyarta ce ta auri Alhaji Saminu babban ɗa ga wazirin garin Wamako, da Asma'u ta je agolanci wanda kyautatawa na Alhaji Saminu ya sa ya riƙe Asma'u tamkar 'yar sa ba ya banbanta ta da 'yayan sa na cikin sa. Ko kafin ya rasu sai da ya ba ta kyautar gona da shanaye saboda ba ta da gadon sa.

Asalin mahaifinta ance Maharbi ne wanda ya mutu a jeji aka dawo da gawar sa gida. Kyau da ƙuruciyar Fatima mahaifiyar Asma'u ya sa tana gama Idda manema su ka ma ta chaa ƙarshe ta auri Alhaji Saminu ta je a matar sa ta uku.
Tasowa a gidan arziƙi ya sa Asma'u ko na ce Hajiya Inna ta ɗauki rigan girman kai, faɗin rai, jiji da kai duk ta yaɓa wa kanta. Ance ko lokacin tana budurwa yauƙinta ya fi na asalin 'yan gidan.


Tsaki na ja na juyar da kai dan damuwar da na ke ciki ya fi ƙarfin in tsaya ja in ja akan wata uwar miji marar mutunci.

"A ni ki ke wa tsaki?" Ya faɗa yana nufoni da sauri. Ban ce komai ba sai ma wata tsakin da na ƙara yi. Ai kuwa ya jawoni daga inda na ke kwance kan gado ya cillani ƙasa, ba ƙaramin buguwa na yi ba amma kafin in gama samun nitsuwa na ji saukan mari a fiskata bai tsaya anan ba ya cigaba da naushina ta ko'ina, tun ina daurewa har na fara kuka ina faɗin Allah ya isa. Sai da ya ga na yi laushi na dena magana, kukan ma na dena sai sheshsheƙa sannan ya cire kayan sa ya afka mini kaman wata akuya. Kukan da na dena ne na tsala lokacin da ya fara shigata da ƙarfi, bai dena ba sai da ya shiga ciki sosai da ƙarfin tsiya, yana faɗin "na gaya miki sai na rufe bakin rashin kunyar ki, duk wani shirmen da ki ka zo da shi daga gida sai na raba ki da shi"...

A wannan dare na tsinewa Baba, Amma, Sanah, Jiji sannan Sa'eed. Kai kowa ma da ya shafi rayuwata sai da na tsine ma sa. Ban san ya akayi mutuwa ta manta da ni ba lokacin da Ahmad ya hau kai na har ya gama abinda zai yi ban mutu ba.

Bayan ya samu nitsuwa ko ya gaji ne oho, ya kwanta a gefe na yaraf yana maida numfashi.

*"Sa'eed why?"* Abinda na iya

Please Login or Register in order to submit comment