You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Gargaɗi
ban yarda wani ko wata su juyamin wannan labari ta kowani siga ba, ko kuma a karantashi a youtube channel. Labarin Tsohuwar Soyayya hakkin mallakar Azizat Hamza ne.

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

*TSOHUWAR💖 SOYAYYA*

*©Azizat*
Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Free page

*Shimfiɗa*

A duk lokacin da soyayya ta zamo tsakani da Allah to haƙiƙa ta na nan har ƙarshen rayuwa. Yanayi zai iya chanjawa, mutane za su iya chanjawa amma soyayya ta na nan a zuciya.
Soyayyan da ake yanzu yawanci soyayya ce da ke zuwa da buri da ado da ƙyale-ƙyale. Kuɗi,kyau, su suka fi zama jagora a soyayyar yanzu.

Ɗan maikuɗi sai 'yar maikuɗi. Ɗan mai mulki sai 'yar mulki shi ne abinda mu ka samu tun zamanin kaka da kakanni. Bature shi ne wanda ya fara watsar da wannan al'ada ta yanda indai soyayyace ta asali to ba ruwansa da kuɗi ko sarauta. Misalai na nan da dama kamar auren Prince William da Kathrine, prince Harry da Meghan. Ku duba auren Mark Zuckerberge da Priscilla chan, Bill Gates da Melinda.  Aure ne da su ke yi saboda soyayyar asali. Amma idan ka garzayo ƙasar mu Nigeria maimakon abin ya ragu to abin ƙaruwa ya ke. Duk min kyan ki/ka idan zuri'ar ku ba naira to fa sai dai ki auri mutum mai dama-dama amma asalin ƙusosin ƙasa masu kuɗin kuɗi, sai dai ki gansu ko ka gansu a talabijin ko jarida da kuma yanar gizo. Haka nan masu dama-dama ɗin ma ba son raɓan talaka su ke ba kowa ya na son upgrade.
Wannan labari ƙagagge ne idan yai kama da rayuwar wani/wata/wasu to anyi shi dan a faɗakar. Ba wanda ya fi ƙarfin ƙaddara da kuma hukuncin Allah. So whatever happens it's destined already.

I promised you, this story will make you smile,laugh, cry but most importantly it will make you ponder. And you wont regret investing your time, strenght and money in to this journey.

*Follow me as i take you on a journey, a journey of true love.....*

0️⃣1️⃣ It's 2018


Wajen liyafar ya cika da mutane musamman ma'aikatan BBC Hausa harda ma na sashen BBC English. Familyn Bulama su na nan a wajen 'ya'ya da jikoki. Musamman wanda dama su na London a wannan lokaci ko kusa da London ɗin. Wanda su ke nesa ma sun zo, saboda Mom Aaliyah ta kowa ce.

Ta na zaune aka kira sunan ta *Aaliyah Badamasi Bulama* ta taso ta na murmushi wanda ya ke ƙara sanyawa fiskarta alhini. Ta je wajen podium ɗin ta ƙarɓi award da aka bata sannan ta amsa mic ta yi jawabin godiya da Hausa sannan cikin turancin ta na ƙwarewa ta ɗaga award ɗin ta ce "this is for my husband Ahmad may his soul rest in Jannah Amin"

Hawaye ne su ka ciko a idon ta ta yi saurin sa hannu ta goge tareda barin wajen, tana saukowa aka sa tafi.

Da sauri Zaid ya nufo ta ya rungumeta yayinda sauran 'yan uwa su ka fara zuwa ɗaya bayan ɗaya su na ma ta congratulations...

Wata budurwace da ba za ta fi shekara ashirin ba ta ƙaraso wajen da Aaliyah ke magana da wasu turawa.
"Excuse me, can i take a picture with you ma'am?"
Aaliyah ta yi murmushi  ta ce "sure"  selfie ta mu su kusan guda uku sannan ta ce "thank you"
Kai tsaye wajen da Zaid ke zaune ya na magana da wasu 'yan uwan sa ta je. Neman izinin magana ta yi da Zaid wanda ko kallo ba ta ishe shi ba.

A hankali ta ce "plz Zaid ka taimaka ka bani minti ɗaya naka, abinda zan gaya ma ka is very important"

"Zaid ka saurareta ma na" inji Hafiz.

Ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa ya cigaba da danna waya.

Ta fito da wayarta daga cikin purse ta danna kira. Sai ga wayar Zaid ta na ringing, ganin baƙuwar number ya sa shi yin tsaƙi sannan ya ɗauka
" Hello"
"Hello Aaliyah ce"
Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta. Kallon a ina ki ka samu special number na.

Murmushi ta ma sa sannan ta ce " na san za kuje Nigeria cikin satin nan so i will be waiting for you there" ta wuce ta barshi da mamaki.
"And who the hell is she?" ya faɗa da ƙarfi

Hafiz ya ce "kai zamu tambaya ai"

Tsaki yai dan ya san irin matan nan ne ma su bibiyar sa.

"Kai amma fa tanada kyau" inji Rabi'u da ke gefen su.

Yarinyar na fitowa daga ɗakin taron kai tsaye taxi ta shiga sai airport. Tun acikin taxi ɗin ta kira Abban ta ta sanar ma sa jirgin su ƙarfe goma sha biyu na dare zai tashi, ya ma ta addu'an Allah ya kawosu lafiya.
Tana cikin jirgin ma selfie da su ka ɗauka da Aaliyah Badamasi ta ke kallo. A hankali ta furta ' its now or never' ....



Wanka ta yi sannan ta gabatar da shafa'i da wutri, da ta idar ta na jan carbi aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.
"Come in" ta bashi umurni. Sanye ya ke da silk pyjamas baƙi. Murmushi ta yi ganin ƙwan na ta ɗaya a duniya.
"Ba ka yi bacci ba?"
Zama yai gefen ta ya riƙe ɗaya hannun da babu carbin ya ce "are you Ok Mom?"
Ta ajiye carbin ta sa hannu ta na shafa gashin kan sa mai tsantsi da yalwa.
"I'm Ok son, thank you"

"Kin missing Daddy ko?"

Ta ɗaga kai alamar eh.

"I miss him too"

ya jima a ɗakin kafin daga baya ya ma ta sai da safe.
Ta jima ta na addu'o'i kafin daga bisani ta je ta kwanta.

Kwantawanta ke da wuya maganganun Ahmad ya fara dawo ma ta, daren rasuwar shi.

*"Na zalinceki Aaliyah, na hukunta ki da horo mafi tsanani ta hanyar rabaki da ɗan ki na tsawon lokaci, ki yafemin. Dont be lonely after my death ki..."*

Ta yi saurin toshe kunnuwanta saboda yadda maganar ke tuno ma ta da abin da ta daɗe da binnewa a zuciyarta.

"Na yafe ma ka Ahmad, haka ƙaddara ta ta zo" ta faɗi a hankali...


....................................

Bayan yai waya da Aaliyah ya ci gaba da kallon program ɗin har sai da aka gama. Ta rame ma sa, haka nan kaman ba ta da lafiya ya ke gani. Zulumin rashin ta da zai yi ya ke. Shekara ashirin da biyar bai taɓa fashin jin shirye-shiryen ta ba tun ta na yi a BBC english har ta koma na Hausa haka nan kuwa a duk lokacin da kewarta ya addabeshi toh programs ɗin ta su ke ɗebe ma sa kewa ya na da record na programs ɗin ta tun daga 1993 zuwa last program da ta yi a farkon shekaran 2018.

"I pray you have peace idan ki ka dawo Nigeria Aaliyah"

........................................

"Abba, Abba...."

Muryar 'yar ta sa ya doki kunnen sa. Yanzu ya ke shirin fita ya je ya ɗauko ta. Ya fito daga ɗaki da sauri, a stairs su ka haɗu saboda yadda ta shigo gidan da gudu. Ta rungumeshi ta na faɗin "i miss you Abba nah"
"Yanzu ke da na ke shirin zuwa na ɗauko ki, sai ga ki"
Ta kissing goshin sa ta ce
"what's important is that im home now"
Ya ɗan ja kunnen ta ya ce  "na hanaki gudun nan ba kya ji ko"

"Sorry Abba" ta faɗi ta na murmushi.

Kai tsaye ɗaki ta shiga ta yi wanka sannan ta fito a dining ta ga ƙannenta na breakfast sai a lokacin su ka ganta saboda Lokacin da ta shigo gidan ba su tashi a barci ba. Ta joining ɗin su su ka karya tare, su na ci ta na basu labarin bikin da ta je a London...

Gaba ɗaya ta gama haɗa kayan ta tun jiya, ita da London yanzu kam sai dai ziyara wanda ba ta tunanin za ta yi shi nan kusa, amma ba dai zama ba. Ta yi murmushi lokacin da ta tuna farkon zuwanta gidan nan. Rayuwa kenan komai yai farko zai yi ƙarshe. Gashi yanzu ƙarshen zaman ta a London ya zo ƙarshen kasancewarta matar Ahmad ya zo.

"Mom an gama fitar da kayan?" Zaid da ya leƙo ɗakin ya ke tambaya.

"Yes son nima ina saukowa yanzu"

Ok ya faɗi sannan ya tafi.

A hankali ta ƙarasa wajen  dressing mirror ɗin ta, ta ɗan tura shi ƙasa sai ga wani safe a jikin bango. Ta danna number kamar haka 0108 sai gashi safe ɗin ya buɗe. Wata ƙaramar jaka ce acikin safe ɗin. Ta fito da jakar tareda rungumeta ta na hawaye. Muryan Zaid da ta jiyo ya na bawa ma su aikin gidan umarni ya sa ta yi saurin ɗaukan jakar ta sa acikin handbag ɗin ta, da shi ke handbag ɗin babba ne sannan ba komai a ciki, ya sa jakar da ta cusa ciki ya zauna daɓas. Ta yi saurin goge hawayen ta sannan ta ɗau jakar ta fito.

Har su ka isa airport zuciyar ta bai bar bugawa da ƙarfi ba. Haka kawai gaban ta ke faɗuwa. Tun rasuwan Ahmad rabonta da Nigeria wannan kaɗai ya isa ya sa ma ta fargaba musamman idan ta tuno rabuwar ta da Hajiya Inna.

Hannunta saƙale da na ɗan ta Lokacin da su ke fitowa daga jirgin. Da mamakin su har lokacin ba su ga wani ya zo tarban su ba. Cikin ɓacin rai Zaid ya fara kiran 'yan gidan na su  saboda rashin mutunci bayan ya riga ya shaida mu su yau zasu taho amma ba wanda ya zo ɗaukan su bayan har Lokacin da za su sauka ya faɗa.

"Zaid Ahmad Wamako" ya ji wata siririyar murya ta kirashi
Murmushi ta ke mu su har ta iso. Kamar dai ya taɓa ganin ta amma ba zai iya tunawa ba dan 'yan matan da ya gani cikin satin nan kaɗai sun fi ashirin.

Ta ƙaraso ta rungume mom, "i'm so happy na same ku da ban san ya zan yi ba."

"And who are you?" Zaid ya tambaya da ƙarfi. Ta maida kallon ta ga mom ta ce " mom ni die hard Fan ɗin ki ce, saboda ke na je bikin retirement na ki a london" ta fito da wayarta ta na nuna ma ta selfie da su ka yi ranan.

"Ayya, 'yata ya sunan ki?" mommy ta tambaya.
"Aaliyah"

"Ashe ke takwarata ce,na gode"

" mom da alama ma su zuwa ɗaukan ku ba su ƙaraso ba, ki min alfarma na kaiku gida"

"Kar ki damu 'yata za su ƙaraso nan ba da jimawa ba"

"Plz mom do this for me, ko dan son da na ke mi ki"

Mom ta ce " Ok dear" ta kalli Zaid ta ce "mu tafi"
"But mom you dont even know h..........." ya katse maganar lokacin da ya ga mom ta fara tafiya da Aaliyah, Aaliyar ce ma ta ke jan akwatin ta. Bayadda ya iya dole dai bin bayansu yai.  Wata haɗaɗɗiyar mota su ka nufa wanda driver ke tsaye a wajen ya na jiran su. Sai da ya ƙaraso wajen ya hango motar gidan su na shirin tsayawa ya cewa Mom da ke shirin shiga motar Aaliyah "Mom ga driver ya zo, barin bi shi"
Ta ɗaga masa kai.
Har su Aaliyah su ka bar airport ɗin bai shiga motan ba yana tsaye yana zubawa driver masifa.

Sun yi nisa da tafiya Aaliyah ta ce "Mom bari ki ji wani surprise" ta bawa driver wayarta ya haɗa da radio ta fara playing wasu recordings.

Muryan ta Mom taji a cikin recording ɗin, ba za ta iya tuna shekarar da ta yi wannan program ɗin ba amma ta san ya jima ƙila tun farkon shekaran da ta fara aiki a sashen BBC Hausa ne. Ta sake tabbatar da hasashen ta lokacin da ta ji muryarta na kiran *"shiri ne wanda ni Aaliyah Badamasi Bulama zan gabatar"*
Aaliyah ta katse record ɗin ta kalli Mom da idon ta ya cicciko da hawaye ta ce "you are surprised ko?"

"A ina kika sami wannan?, inada tabbacin sanda na ke gabatar da shirin nan ba a haifeki ba"

Aaliyah ta yi dariya. "Gaskiya ne Mom, sai dai kamar yadda na faɗa mi ki ni  Fan ɗin ki ce tun ina ƙarama. Na taso da soyayyar ki da son sanin ke ɗin wace ce"

Mom ta zaro ido
"Dont be surprise mom idan na ce mi ki inada records na duka shirye-shiryen ki tun lokacin da ki ka fara aiki har zuwa ƙarshen program ɗin ki a gidan radio"
ta yi wani ƙayataccen murmushi ta ci gaba " ku masu aikin gidan radio ai farin jini gareku. Zazzaƙar muryarki mai sanyaya zuciya. Kar ki sha mamaki idan na ce mi ki takanas saboda ke aka sa min suna Aaliyah"

"Wow! I'm speechless dear"

Aaliyah ta cigaba da kunna ma ta records ɗin  wanda Mom ce ta buƙaci hakan. Ta na ji ta na tuna Lokacin ƙuruciyar ta a wajen aiki da kuma girman ta. Muryar dai idan ba ka lura ba ka iya cewa bai chanja ba iya waɗannan shekaru sai dai fa ita ma'abociyar muryar ta chanja sosai girma ya kamata, shekaru ashirin da biyar ba wasa ba ne, shekaru biyar a sashen Turanci sai shekaru ishirin a sashen Hausa.


*Tsohuwar soyayya labari ne mai ɗaukan hankali cike da darussa na rayuwa. Labari ne da ba za ku so ya wuce ku ba. It's a different journey entirely, different from mutum mugu ne, duk kyan namiji da sauransu. Labari ne da ya zo da salo na daban wanda sai wanda ya karanta zai san the journey is worth investing in.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai guda biyu wato tsohuwar soyayya da sakatariya ta*







*TSOHUWAR💖SOYAYYA*

*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Free page

0️⃣2️⃣ find the diary

Har su ka iso tangamemen gidan, Aaliyah ba ta bar yiwa Mom magana akan aikin ta ba tareda ba ta wasu bayanai a kan ta, wanda ba kowa bane ya sani. Like makarantan da ta yi tun daga primary har masters na ta. Like exact date and day da ta yi aure har kalar kayan da ta sa ranar da aka yi wushe-wushen ta a Maiduguri thirty years ago.

"Who are you Aaliyah?" Mom ta faɗi lokacin da motar ta tsaya a farfajiyan gidan.

"Kamar yadda na gaya mi ki i'm your biggest fan Mom. Ina son ki, ina son komai na ki. Infact idan kin bani dama i want to be a daughter to you"

"Ina ganin dole mu zauna mu yi magana" Mom ta faɗa sannan ta fita daga motar.

Ganin Aaliyah ba ta fito ba ya sa ta ce " 'yata ki shigo ma na"

Aaliyah ta yi murmushi ta ce " na san da gajiya a jikin ki, zan zo gobe idan kin huta"

"Thank you dear" ta faɗi tareda maida duban ta ga gate saboda buɗewa da akayi. Motar da ta ɗauko Zaid ne dan haka ta tsaya saboda su shiga gidan tare. Sai da Zaid ya fito daga motar sannan Aaliyah ta fito da sauri ta ce "Mom idan ba za ki damu ba barin yi magana da Wamako"
"No problem dear"
Ta ƙarasa wajen Zaid da ya haɗe rai ganin ta nufo shi.
"Plz Wamako give me two minutes"
"Na san maganar ba za ta wuce barar soyayyata ba. Kar ki ɓata bakin ki dan ba za ki samu ba"

"You guessed wrong, Zaid ka taimaka ka bani lokaci mu yi magana, there's something you need to know about your mother"

" rubbish"  ya faɗi tareda barin wurin.

Murmushi Aaliyah ta yi sannan ta wuce wajen motar ta saboda Mom ta bar wajen.

"My prince mi daughter ke ce ma ka ne na ga ka haɗa rai?"

" she's just like the rest, she's crushing on me"

"Amma kamar ba haka na ke gani ba"
Ya kama hannun Mom ya haɗa da na shi ya ce " manta da zancen ta, she's a nobody"...

Kamar yadda ta tsammanta hakan ne ta faru kallon kirki ba ta samu a wajen Hajiya Fatimah ba balle ta samu tarba mai kyau.
Sashen Hajiya Inna da su ka shiga ma abu ɗaya ne nan kam maimakon shiru Inna sai da ta zageta tatas kamar yadda ta saba. Zaid da ya ke ƙoƙarin kare Mom ɗin ne ya sa abin yai sauƙi.

Ɓangarenta na nan yadda ya ke ba abinda aka chanja. Gyara shi kawai aka yi saboda ƙura. Ta zauna gefen gado maganganun Hajiya Inna na ma ta yawo a ka.
*" ashe za ki iya takowa gidan nan, ai na ɗauka daga chan gidan ku za ki wuce tunda Ahmad ya rasu, alaƙa ta yanke. Tsabar sheɗanci yaushe Ahmad ya rasu amma za ki gama aiki wai har wani dinner ki ka haɗa ki na wani bubbuɗa haƙora irin ga ki bazawara ko. To wallahi indai zawarci za ki yi ba anan gidan ba kije chan cikin dangin ki ki yi...."*

"Mom are you Ok?" Muryan Zaid ya dawo da ita.
Murmushi ta ma sa. Ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta ya riƙe hannunta biyu. "Mom kar ki damu da maganganun Inna. She's old and crazy"

"Kakar ta kan" ta faɗi tana dariya.

"Yeah she's crazy"

Dukkan su biyu su ka sa dariya...

...................................

Aaliyah na komawa gida ta turawa Zaid text kamar haka:

*dan Allah ka bani dama mu haɗu gobe, we really need to talk. Aaliyah*

Ta na gama tura text ɗin Abba ya leƙo ya ce "princess zan fita, ba zan dawo da wuri ba kar a yi lunch da ni"

"Ok Abba"

Ta na tsammanin reply ɗin Zaid amma har yamma shiru. Ta sake tura ma sa wani text ɗin amma still bai yi reply ba. Ta kirashi ya ƙi ɗauka.

Ta na zaune ta na karatun ƙur'ani Nusrat ta shigo ɗakin da gudu.
Ta na zuwa ta faɗa jikin Mom.
"My Mom ashe kin dawo, mun kalle ki a Tv ni da su Inna da Mummy ranan. I miss you"

"Oh I miss you too dear"

Kallon yarinyar ta ke yi wanda kamannin Ahmad gareta.

"Mom ina Yaya?"

"Ina ga yana part ɗin sa ki duba shi acan"

"Mom kar ki gayawa Mummy na gaya mi ki, ranan Inna ta ce kar kowa ya shigo wajen ki, wai idan ki ka gaji za ki tafi. Mom ina ba za ki tafi ba ko?"

Ta girgiza ma ta kai.

Sai da Nusrat ta fita sannan ta sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Abin ya kai haka ta faɗi a zuciyar ta.
Saboda Zaid za ta zauna anan, saboda shi za ta shanye ko me za a ma ta...

Sai da ta shirya za ta kwanta text ya shigo wayarta ta duba baƙuwar number ce ta karanta text ɗin, saƙon bangajiya ne sai daga ƙarshe aka rubuta yours Aaliyah. Ta yi murmushi sannan ta kira numbar su ka sake gaisawa da Aaliyar. Ta rasa dalilin da ya sa lokaci guda yarinyar ta shiga ran ta...

*"a duk inda ki ke, a ko wani lokaci, a ko wani hali, duk min rintsi, ina son ki Aaliyah, har ƙarshen rayuwa ta, har ƙarshen numfashi na a doron ƙasa. I will forever love you Aaliyah"*

Waɗannan kalmomi su ne abu na ƙarshe da ta tuna kafin ta yi bacci.

Washe gari ba abinda ya chanja ba wanda ya zo wajen ta ita ce dai ta je ta gaida Inna sannan ta duba Zaid a part ɗin sa wanda bai jima da tashi daga bacci ba. Gaisawa su ka yi sannan ta wuce ɓangarenta. Kitchen ta shiga dan ta nemi abinda za ta ci saboda jiya haka ta wuni da yunwa sai dai ba kayan abinci a store ba komai a kitchen ɗin sai kitchen utensils.
Ta fito ta zauna a falo ta na tunani.
Wayar ta ya shiga ringing a ɗaki ta yi sauri ta je ta ɗauko ta ga numbar Aaliyah ce kafin ta ɗauka wayar ta katse. Ta yi saurin kiran ta
"Hello Mom ina cikin gidan ku ki aiko a shigar da ni"

" tsaya zan zo da kai na"  ta faɗi sannan ta shiga ta sa hijab ta fito.
Motar jiya ne ta kawota. Aaliyah na ganin mom ta fito ta yi saurin fitowa daga motar ta na murmushi. Ta ɗauko basket a cikin mota sannan ta nufi wajen Mom. Da murna ta tareta su ka shige cikin gidan. Kai tsaye falo su ka zauna.

"Sai ga ki da safe na ɗauka sai yamma za ki zo ai"

"Mom wallahi Abba ne yai ma na breakfast shi ne na ce dole sai na kawo kin ci kin ji girkin Abban mu"

"Kai kai Aaliyah da rigima, shine tun daga gida ki ka taho da shi"

"Yes Mom i have to. Kin san Abba na shi ne number one fan ɗin ki in this whole world"

"Kayya, to na gode"

"Hope ba dai kin karya ba dan dayawa na kawo saboda mu ci mu ƙoshi"

Mom ta yi murmushi.

"Mom ina ne kitchen na ɗauko ma na plate da cups"

Mom ta tashi ta ce "barin ɗauko"

A falon su ka baza kolin sinasir da miyar taushe da su ke ci wanda miyan ya ji nama. Sai da Mom ta kurɓi shayin da Aaliyah ta kawo ta ji wani abu ya tokareta.

Aaliyah ta ce "you dont like it?"

"No, shayin nan kamar..." sai kuma ta yi shiru

"Abba ya iya haɗa shayi, this is his favourite recipe, he calls it Aaliyah's tea. He'd being making it for more than 30yrs now"

"Aaliyah mi ye sunan Abban ki?" Mom ta tambaya.

Aaliyah ta san anzo wajen but this is not the right time dan haka ta ce " Sani, Aaliyah Sani suna na"

Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce "Oh that's nice, ki ce wa Abba ya iya haɗa shayi"

Su na cikin cin abinci ya shigo falon da sallama.
Mom ce ta amsa ma sa yayinda Aaliyah ta shagala da kallon sa. Sanye ya ke da baƙin jeans three quarter da farar vest, gashin kan sa a kwance lub-lub sai sheƙi ya ke yi.

"And what are you doing here? Ba dai a nan gidan ki ka kwana ba?"

Sai a lokacin Aaliyah ta yi firgigit da kallon sa.

"Mom i dont like this, daga haɗuwa da yarinya kin shigo da ita gida har kuna cin abinci tare. What if she's a

Please Login or Register in order to submit comment