You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ke magana ya sa na san ba lafiya ba dan haka da Ahmad ya zo na ce ma sa zan je gida Baba ba lafiya.

"Ni ba na son ki je gidan nan Aaliyah, Baban ki so ya ke ya rabani da ke"

Rai na a ɓace na ce "ka san yanada ikon rabani da kai ta ƙarfi idan yana so. I stayed here because i choose to. Ko da ka cigaba da ƙaran Baba a lokacin nan ba galaba za ka ci a kansa ba, ya haƙura ne saboda ni. Idan ba ka barni na tafi ta daɗi ba zan tafi da ƙarfin tsiya and idan na tafi ba zan sake dawowa ba, and there's nothing you can do about it. Ko a da Aaliyah Badamasi Bulama ta fi ƙarfin Ahmad Wamako ƙaddara ne kawai ta riga fata"

Yadda na ke maganar sai da ya tsorata, ya jima bai ganni a asalin Aaliyah ta ba.

"Kin san dai na chanja ko, duk abinda bakyaso na dena. Idan kika gujeni Hauka zan yi Aaliyah dan sai na yi faɗa da duk wanda ya ke ƙoƙarin raba mu even if it's your father. Ki je gida amma kar ki wuce sati ɗaya"

Yana gama faɗin haka ya fita. Na sauke ajiyar zuciya ina kallon Zaid da ke wasa a tsakiyar falon. Buri na Zaid ya banbanta da Uban sa idan ba haka ba na yi asaran haihuwar sa...

Ranan da na je gida sosai na yi kuka yadda na ga Baba na ya koma kamar wani miskini. A keke ake turashi baya iya tashi yai tafiya da kan sa. Abu biyu Allah ya sa wa masu kuɗi fargaban sa. Kowa na tsoron rashin lafiya da mutuwa amma attajirai da ma su muƙami sun fi kowa tsoron mutuwa da rashin lafiya. Abu ne da kuɗi ko matsayin mutum ba sa siyan shi. Gashi dai Baba na da kuɗin amma bai iya siyawa kan sa lafiya ba. An je manya-manyan asibitoti da ake ji da su a duniya amma kuma lafiyar ta ƙi samuwa. Jallah Jalaluhu kenan, ya hallaka Fir'auna da ƙaruna wanda har yau tarihi ba ta manta da mulki da dukiya da su ke da shi ba a zamanin su, ƙarfin ikon su bai sa sun kuɓuta daga halaka ba.
Likewise Baba ma kuɗin sa bai siya ma sa lafiya ba. Wannan kaɗai ya isa ya nuna mana cewa dukkan mu ɗaya muke a wajen Allah amma har wayau maikuɗi gani ya ke ya fi talaka.

Zaid na ɗaura wa Baba a hannunsa bayan ya buƙaci hakan. Yaron sai dariya ya ke lokacin da Baba ke ma sa wasa.

"He smiles just like you Aaliyah. Allah ya ma sa albarka" na amsa da amin.

"Dr Sa'eed da Baffan sa sun zo sun gaisheni" na ɗago ido na kalleshi yana shafa kan Zaid idon sa ɗauke da dana sani bisa ƙaddara da ta riga fata.

Ya cigaba "ya kammala Phd ɗin sa a Oxford kwanakin baya. He's going to be a successful man. Ban taɓa ɗauka soyayyar da na ke miki shi zai sa na tura ki ga rayuwar ƙunci ba. Allah ya jiƙan rai Alhaji Wamako mutumin ƙwarai ne, yana ɗaya daga cikin mutanen da zan iya rantsewa akan iya tsawon rayuwar su ba su yi neme-nemen mata ba kuma ba sa shan barasa. na ɗauka haɗa zuri'a da shi zai ƙarfafa zumuncin mu sannan ya haɗe kan mu har ƙarshen rayuwar mu, na ɗauka dukiyoyin mu za su haɓaka sunan mu zai sake bazuwa a duniya. A yau son zuciya ta sa ni a jirgin da na sani, Aaliyah ki yi haƙuri ki yafe min"... hawaye ya fara zubo ma sa. It was the first and last time dana ga hawaye a idon Baba. Nima ɗin kuka na ke yi domin ambaton Sa'eed da yai ya taɓomin da wani tsohon ciwo a zuciyata...

Sati ɗaya da na yi kullum ina tare da Baba, ya kan yawan faɗamin na yafe ma sa bayan na riga na yafe ma sa har zuciyata. Nawa mijin ko kiran Baba ya gaisheshi bai yi ba balle ya zo. Jikin Baba da ɗan sauƙi amma kuma ba ya fita. Ranan da zan koma a jirgi aka maida ni Abuja wanda Baba ne ya biya. Ina cikin jirgi ina riƙe da ɗana yayinda maganganun Baba na ƙarshe su ke min kama da wasiyya. Takardu ya damƙa mini sannan ya bayyana mini kyauta ce ya min tun lokacin da na haihu. Shares ne na wani kamfani a ƙasar waje, yadda Ahmad yai wasa da dukiyar Uban sa ya salwantar da shi a chacha shiyasa Baba yai gudun samun matsala idan baya nan. Duk da akwai zaman lafiya tsakanin Hajia da Amma sai dai abinda ba a rasa ba amma kuma sha'ani na gado sai a hankali.

"Ban kai ki gidan da za ki ji daɗi ba amma kuma ba zan bari ki tsiyace ba saboda Ahmad. Aaliyah ke 'yar gata ce" i wish 'yar gatan da ya ke faɗi ba kuɗi ba ne, i wish 'yar gatan da ya ke nufi shine amincewa da soyayyar Sa'eed a lokacin da na nuna duk duniya babu wanda na ke so kamar sa.

Ban so karɓar wani abu na shi ba amma ya nuna idan ban karɓa ba kamar ban yafe ma sa bane...


Tunda na koma Abuja kullum sai na kira Baba mun gaisa, wani lokaci har ya ce na bawa Zaid su gaisa. Zaid yai ta ma sa shirmensa na yara.

Sati uku da dawowa na Muhammad ƙanina ya kirani yana kuka yana sanar da ni Baba ya rasu. Shock ɗin da ya kama ni haka na sake tarho ɗin ta faɗi ƙasa .... Ahmad baya nan dan haka na ɗau ɗana mu ka wuce Maiduguri a ranan. Mai gadi na barwa saƙo ya ajiyewa Ahmad idan ya dawo.

Wato matsalar gado musamman ga mai arziƙi masifa ce. Duk wani haɗin kai da zaman lafiya maganar gado ta wargaza komai. Ana sadakan bakwai aka fara batun rabon gado. Abin da ya sa na tuna da rasuwan Alhaji Wamako kenan. Mu biyar ne a wajen Amma kuma ni kaɗai ce mace. Hajia na da 'ya 'ya bakwai mata uku maza huɗu ban ga abin tashin hankali ba amma da aka fara ƙananun maganganu akan dukiya abin bai tsaya anan ba sai da aka fara batun maganar hannun jari da Baba ya siya min. Haruna da Anty Falmata su suka fara maganar wai dole a raba gado da shi tunda dai Baba ya rasu. Ni ban san ya aka yi su ka san da zancen ba ma. Magana ta kai aka kira lawyer da malamai wanda su ka tabbatar wannan hannun jari ba ya cikin gado. Fiye da shekara ɗaya da ya wuce ya sayi shares ɗin kuma da sunana ya siya, sannan kuma kyautar sa ya min tun alokacin. A duk tarin dukiyar Baba bai isa ba sai an sa ido a kyautar da ya min. Gani su ke tamkar rabin dukiyar sa ya raba ya bani bayan ba haka bane.
Idan ka cire Sanah da Aliyu wanda shaye-shaye ne gaban sa duk sauran haushi na su ke ji. Ganin abin zai zama matsala na cire kai na a cikin gado na ce na yafe. Ai kuwa nan ma ban tsira ba haka aka fara zargin wai bayan hannun jarin da Baba ya siya akwai wasu kyautan da na ke ɓoyewa ne. Sati na biyu a gida na koma Abuja yadda maganar gado ke kawo kace- nace ne ya sa na bar gidan na dawo gidan Ahmad. Ahmad ya san da mutuwar Baba amma kuma bai zo ba haka bai kira ya gaishe ni ba. He's too busy da sabon party da su ka buɗe. Inna ce ta tunzura shi ya shiga harkan siyasa. Ni dai na zuba mu su ido, tunda dukkan su biyu ba su yiwa kan su karatun ta nitsu ba...





*24- Unrequited love*


Zaid na shekara ɗaya da rabi na yayeshi. Kullum addu'ata shine Allah ya inganta rayuwar sa ya rabashi da munanan hali irin na uban sa. While Ahmad is busy ni kam na samu kwanciyar hankali ba zan ce farin ciki ba sai dai kwanciyar hankali tunda duk abinda ke ɗaga min hankali a da kusan kaso saba'in babu su yanzu. Zaman gidan ya isheni, kullum ba inda na ke zuwa daga gida sai gida, ni da ɗana mu ke rayuwar mu mai daɗi. Ahmad bai cika zaman gida ba ƙoƙarin ɗabbaka partyn su su ke.

Watarana Zaid na shekara biyu da rabi Ahmad ya fara maganar sa shi a makaranta. Alhamdulillah yaron nawa Allah ya bashi kwanya, yadda na dedicating dukkan lokacina gareshi ya sa ƙwaƙwalwarsa ta ƙara buɗewa da sauri. Maganar ƙasar waje Ahmad ya min wanda ya sa na kalleshi da mamaki.

"So ka ke na tura yarona chan wata duniya yai rayuwa shi kaɗai?"

Dariya yai ya kamo hannuna ya ce "haba Mommyn Zaid ai ko hauka na ke ba zan bar Zaid yai rayuwar kaɗaici ba. You see, Na yiwa Zaid alƙawarin inganta rayuwar sa so dole na fara ta ɓangaren Ilimi. Dukkan mu za mu koma amma ni zan dinga sintiri tsakanin Nigeria da London"

Na zaro ido na ce "London?"

"Yes Aaliyah, a inda aka ɓata min suna haka zalika a nan zan gyara sunana. I will exact revenge on Pedro Santiago"

Ni dai kawai na buɗe baki ina binsa da kallo saboda rashin hankali ƙarara da na gani a wajen Ahmad. Wato abinda Don Pedro ya ma sa bai daddara ba.

Abinda ban sani ba shine Ahmad ya yi nisa. Inna ta shigar da shi inda zai kaishi ga halaka, a lokacin revenge ne kawai a ransa shiyasa bai damu da abinda ka iya biyowa ba.

For the second time mu ka tattare mu ka koma London, gidan da ya siya bai kai gidan Alhaji na da ba amma shima ba laifi yana da kyau. A ka saka Zaid a kindergarten yayinda ni kuma na koma abinda na saba wato zaman gida. Wata rana mu ka yi waya da Sanah ta ke gayamin ta fara masters na ta a chan Canada na tayata murna sai alokacin ta ce mi zai hana nima na koma karatu ko kuma na nemi aiki. Na yi shiru dan ban san ya Ahmad zai ɗauki maganar ba.
Bayan mun gama maganar na zauna ina juya maganar a raina tabbas makaranta ko aiki zai rage min kaɗaici. Amma Ahmad zai yadda?...

Bayan kwana uku da Ahmad ya zo na jarraba yi ma sa maganar to my surprise sai ya ce " idan aiki ki ke so za ki samu idan ma kuma makaranta ne za ki samu, Ahmad ɗin yanzu ba na da bane"

Ya kissing goshina ya ce " ba abinda ba zan iya yi miki ba. I love you Aaliyah, daga yanzu komai ki ke so shi zan yi"

Wani lokaci Allah ya kan jarrabci mutum da son wani abu da ada ya ƙi shi. Allah ya jarrabci Ahmad da so na, a da bai fahimta ba amma yanzu ya gane cewa xuciyar sa na tsananin son Aaliyah...

Bamu yi sati uku da maganar ba ya sama min aiki a BBC sashen turanci. Aiki ya sa duk wani depression da ke tareda ni ya warware. Ni ina fama da aiki shi kuma Ahmad yana ƙara cusa kan sa cikin baƙar rayuwa. Da ƙarfin tsafi Ahmad ya ga bayan Don Pedro, bayan ya ƙwace ragamar harkokinsa. Ahmad was now a Mafia Boss, sai yai wata ɗaya biyu bai zo ya ganmu ba amma kuma kullum sai ya kira musamman dan ya gaisa da ɗan sa. Within one year sunan Ahmad Wamako yai tashe a duniya. Haka kuma rayuwarmu ta koma cikin hatsari. Bodyguards ke tsarona da kuma ɗa na. Gida da wajen aiki duk sai bodyguards sun rakani. Tun ina tsoro har na haƙura na koma addu'a kawai. Ina jin maganganu dayawa akan Ahmad kuma nima ina karanta labaransa a gidan radio, amma ya zan yi Ahmad ya fi ƙarfi na.

Shekaru huɗu mu ka yi Ahmad na cin karensa ba babbaka until komai ya fara lalacewa. Mu baƙaƙen fata mu kan ɗauka turawa ba sa asiri ko magani to ƙarya ne. Alberto ƙanin Don Pedro da Ahmad yai sanadiyar mutuwar sa da kuma Cataliya 'yar sa, cikin shekarun nan sun shiga sun fita domin su ga bayan Ahmad and they took away everything da ya building a shekarun nan. Not only that sun attempting kashe shi amma ya tsira da ƙyar, bullet biyu aka ma sa but he survives it.
Ni ne na fara jinyar sa da ga baya Inna ta taho daga Nigeria, ganin zaman mu ba zai yiwu ba na bar ma ta jinyar sa na koma bakin aikina.

Ranan daga office da na dawo gida sai ga Cataliya a gidan mu. Yanzu ba mu da bodyguards tunda ta ƙarewa Ahmad.

Kashe ni ta zo yi da ni da Zaid saboda ta huce takaicin Ahmad amma ba ta iya yin komai ba. Ƙwayoyin da ta ke sha sun gaya ma ta dai-dai.

"I wanted to kill you" ta yi dariya tana bubbuga bindiga a kanta.
"But then i pity you. Your more miserable than i am"

"Why didnt you leave him?"

"Please dont hurt my son" na faɗa a hankali.

Ta tako wajena ta sa bindiga a goshina tana shirin harbi sai kuma ta fasa tana dariya ta ce "you're a good person i like you" tundaga wannan rana Cataliya ta fita daga rayuwar mu. Bayan an sallami Ahmad Inna ta ce sai dai ya koma Nigeria. Ba shi da wani abin kirki duk abinda ya samu sanadiyar Don Pedro babu shi dama da dukiyar sa ya ke burga dukiyar chacha dukiyar da aka samu ta hanyoyi marasa kyau.

Na fara jin daɗin aikina dan haka ban shirya tafiya ba na ce wa Ahmad ba zan koma Nigeria ba. Inna ta kalleshi tana jiran ya min magana sai ya ce " duk abinda ki ke so shi na ke so Aaliyah"

Inna ta zaro ido ta ce "na shiga uku yaushe kika shanye ɗana?"...

Na cigaba da aiki da BBC English daga baya sashen BBC Hausa su ka nemi na dawo wajen su na kuma amince. Ban san wata tsiyar Ahmad da mahaifiyar sa ke kimtsawa a Nigeria ba tunda ba sa taredani ban damu ba. Tafiyar su da wata uku aka buƙaci kuɗin makarantan Zaid inda sai a nan na san ba ƙaramin maƙudan kuɗi Ahmad ke biya ma sa. Albashina da An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment