You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

spy"

Mom murmushi ta yi ta ce " kai da za ka tayani murna na samu daughter sai ka hau fishi, haka ake yi"

Ya harari Aaliyah ya ce "yarinya ƙarama da ke sai shegen shige-shige"

"Eliza,Eliza" ya fara kira da ƙarfi.

Mom ta kalleshi ta ce " Son lafiyar ka kuwa, wace Elizan kuma ka ke nema?"

"Mai aikin ki ma na, ko ta fita ne?"

Hmmm kawai Mom ta ce ta ci gaba da ƙurɓan shayin ta.

Aaliyah ta kalli Zaid da ke rarraba ido ya na kallon Mom ta ce " ni da Mom ne kawai a wajen nan tun ɗazu ba wadda ta shigo"

"This people are trying my patience abi" ya faɗi tareda yin hanyar waje.
Aaliyah na jin shi ya na kiran sunan ma'aikatan gidan.

A tsakiyar main parlour ya tsaya ya na masifa.
"Dan Ubanki Eliza jiya ban ce ke za ki dinga kula da ɓangaren Mom ba. What the hell are you still doing here?"

"Oga...." sai kuma ta yi shiru

"Talk" ya daka ma ta tsawa.

"Ni ne nan na ce kar wanda ya shiga wajen Aaliyah" muryan Inna ya doki kunnen sa.

Ya juyo a fusace ya ce "Inna mi hakan ke nufi?"

" hakan na nufin idan ta na son mai aiki, ta kawo na ta, amma wanda su ke nan ba wanda zai yi ma ta bauta"

" interesting" ya kalli Eliza ya ce " je ki ɗakin Inna ki haɗa ma ta kayan ta she's leaving this house"

"Zaid kana da hankali kuwa" Hajiya Fatima da fitowar ta kenan ta faɗi.

" listen old woman, gidan mijin ki ya na Sokoto Idan bai mi ki ba akwai wani gidan sa a Wamako ki je chan ki zauna ki yi iko yadda ki ke so. But this house is my fathers and he built it for my Mom so ba ki da hurumin aiwatar da doka a gidan nan. Idan ba tsofin zamani ba ma da shegen son duniya ke da ɗanki ya mutu mi ya kamata ki yi banda ki koma ƙuryar ɗaki ki na nema ma sa gafara tareda ke kan ki amma banda tada fitina ba abin da ki ke yi a nan. Look ni Zaid ba zan lamunci cin mutunci daga wajen kowa ba, duk wanda ba zai kyautatawa mahaifiyata ba to zai iya tattara kayan sa ya bar gidan nan. And that includes you Anty" yai maganar ya na kallon Hajiya Fatima.

"Innalillahi, yanzu ni Zaidu za ka ciwa mutunci. Abinda Aaliyah ta ce ka ma na kenan?" ta ƙarasa maganar tana goge hawaye.

Zaid ya ƙaraso wajen ta ya ce " ki yi kuka yadda ki ke so ɗanki ya mutu. Ni tawa uwar ta na nan da ran ta and i will always protect her. Idan wani ya yi ƙoƙarin ƙuntata ma ta i promise, ko waye sai na yi maganin sa"

" ka san dai ba kai kaɗai ke da dukiyar ba, na ga da shi ka ke taƙama" Anty ta faɗi

Dariyar rainin hankali yai sannan ya ce " to waye matsiyaci anan. Aaliyah Badamasi Bulama dai ko da ba ta auri Ahmad Wamako ba ta gaji arziƙi idan ba ki san tarihi ba Inna ta sanar da ke"

"Zaid ni ka ke cewa matsiyaciya, kai Allah ya jiƙan rai" ta fashe da kuka.

Kallon ma su aikin da su ka tsaya cirko-cirko a wajen yai ya ce "Eliza ke da wannan ku wuce wajen Mom and, idan ku ka ƙara barin wajen ta. I will deal with you mercilessly. Now get the hell out of here!" Gaba ɗaya su ka fita da gudu.

Ya kalli Anty ya ce " na yadda ba ni kaɗai ke da dukiya ba, amma ki sani this particular house is my mothers, infact zaman alfarma ku ke yi domin a ko wani lokaci tana da ikon koran ku. You can ask Dad's lawyer if you want" ya na faɗin haka ya haye sama.

Kwalin taba ya ɗauka ya ciro ɗaya ya sa ta a baki ya ɗau lighter ya kunna. Sai da ya zuƙeta sau uku sannan ya ɗau wayar sa da ke ringing. Yawan kira da kuma text da ta ke mi shi ya sa ya gane numbar. Kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka ya na furzar da iskan taban.
Shiru yai ya na sauraron mi za ta ce sai dai kuma kafin ma ta ce wani abu ya jiyo muryan Inna ta na faɗa.
"Wamako plz come, Mom is crying...." da sauri ya cillar da wayar sannan ya jefa tabar a ƙasa ya take ta ya fita daga ɗakin da gudu...

Aaliyah kam yau ta tabbatar da maganar da ake cewa *'the rich also cry'* sai yaushe Mom za ta samu farin ciki, Ahmad Wamako ya rasu amma kuma iyalen sa ba su bar tozarta Mom ba sai yaushe za ta bar wannan ahali wanda ba su san darajar ta ba.

" har Zaid zai ce nan ba gida na bane na koma Wamako ko Sokoto. Gidan Ahmad ɗin, gidan ɗa na!. To ki sani, wallahi wani batun Ahmad ya mi ki kyautan gida duk shirme ne. Ke ce za ki bar gidan nan ba mu ba"

Kamar wani Mahaukacin zaki haka ya shigo falon. Kallon Mom yai da hawaye ke zirya a idonta. Bai yi wani tunani ba ya kaiwa Inna mari wanda Aaliyah ta yi saurin riƙe hannunsa.

Mamaki ƙarara a fiskar Inna da Anty.

"Zaid plz dont" Mom ta faɗi a hankali.

"Mare ni Zaidu, mare ni, sai na san ka cika tantagaryan ɗan iska"

Huci ya ke yi kamar wani mayunwacin Zaki da kakkausar murya ya ce " i swear Inna if you ever insult my Mom again, i will forget the fact ke Kaka ta ce.  Zan mi ki abinda har ki mutu ba za ki manta ba"

Ya kalli Anty ya ce " duk ranan da ki ka shigo wannan waje ba tareda izinin Mom ba wallahi a ranan za ki bar gidan nan. Now get out!"

"Zaid please, iyayen ka ne"

" Ahmad ma kin shanye shi kin juya shi yadda ki ke so balle kuma ɗan da ki ka haifa. Mu na nan da ke Aaliyah" Inna ta faɗi sannan ta juya su ka fita.

Mom ta dafe ƙirjin ta da ke ma ta zafi.

Mom ya faɗi tareda ƙarasawa wajen ta da sauri. "Mom are you Ok?" 
Murmushin ƙarfin hali ta yi sannan ta ce " Zaid dan Allah ka dena ɗaga mu su hankali, they deserve your respect. Bai kamata ka treating na su kamar wasu yaran ka ba"

" kafin su samu respect ɗi na sai sun fara respecting na ki Mom"

"Ba rin shiga ɗaki i'm having headache"  shi da kan shi ya taimaka ma ta ta shiga ɗaki sai da ta kwanta ya ja ma ta bargo sannan ya fito bayan ya kissing goshin ta.

Ya na fitowa ya ga su Eliza su na shiga da kayan abinci kitchen ɗin. Wato tsabar mugunta kayan abincin wajen ma kwashe su a kayi.

Kujera ya samu ya zauna ya miƙar da ƙafar sa ya na kallon ceiling. Maganganun Daddy na yawo a ƙwaƙwalwarsa.

" Zaid take care of your mother. Iya rayuwar auren mu ban kula da ita ba. I hurted her so much not only me even my family too, ni na raba ta da kai for my own selfish gain. Plz dont let her ever cry again......"

"Wamako, Wamako" muryar Aaliyah ya dawo da shi a hankali ya saukar da idon sa a kan ta. Tsugunne ta ke kusa da shi.

"Plz ka bani 10 minutes na ka mu yi wata magana mai muhimmanci. Its about Mom"

"Minene?" Ya faɗi a hankali

"Can we go to somewhere private plz"

Ido ya ƙura ma ta wanda ya sanya ta yi saurin janye idon ta daga kallon sa da ta ke saboda tasirin da kallon sa ke yi ajikin ta.

" it better be important" ya faɗi tareda tashi tsaye ya ce " follow me"

Ba mu su ta tashi ta bi bayan sa.

Wajen swimming pool ɗin gidan su ka je. Sai da ya kunna taba ya zuƙa sannan ya ce " i'm listening"

Ta fito da wani envelop mai ɗan girma ta miƙa ma sa.

"Miye wannan?"
"Just look at it"  ta faɗi.
Ya buɗe envelop ɗin ya fito da hotunan da ke ciki.
hotunan Mom da Dad ne lokacin bikin su wani a wajen dinner wani a wajen wushe-wushe. Shi wasu hotunan ma bai taɓa kallon su ba sai yanzu.

"What does this mean?" Ya tambaya ya na kallon ta.

Ta miƙa ma sa wani envelop ɗin. Ya karɓa tareda buɗewa hotuna huɗu ne a ciki. Still hotunan Mom ne ta na budurwa amma ta ɗau hoton da wani saurayi wanda da gani kasan hoton masoya ne.
Zaid ya ɗago ido ya kalli Aaliyah ya ce " explain"

Aaliyah ta nisa ta ce " idan ka lura da hotunan farko za ka ga babu murmushi a fiskar Mom idan ma akwai ba genuine smile ba ne. Amma ɗaya hoton she's completely happy."

"And so?"

"Zaid, i need to know the complete story, i need to know if Mom still loves that man"

"This is bullshit, abinda ya sa ki ke damina da kira ke nan?"

"Zaid, ina son ka min wata alfarma. Your Mom has a diary plz find it"

"You must be crazy. Personal diary na Mom zan ɗauka in baki saboda kin sha ƙwaya. See, duk wani stupid idea da ki ke da shi you better drop it. Infact kar ki sake shigowa gidan nan"

"Zaid, na rantse da Allah akwai babban al'amari da ba ka sani ba a rayuwar Mom, and you really need to know. Ba zan iya gaya ma ka komai ba yanzu saboda ba ni da cikakkan labari amma with the diary we'll know everything"

"Aaliyah ki ke ko waye. Tashi ki bar nan"

"Plz Wamako find the diary" ta faɗi sannan ta ɗau jakar ta ta bar wajen ba tareda ta ƙarɓi hotunan a wajen shi ba...


*Tsohuwar soyayya labari ne mai ɗaukan hankali cike da darussa na rayuwa. Labari ne da ba za ku so ya wuce ku ba. It's a different journey entirely, different from mutum mugu ne, duk kyan namiji da sauransu. Labari ne da ya zo da salo na daban wanda sai wanda ya karanta zai san the journey is worth investing in.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma mutum ya biya #300 ya samu labarai biyu wato Tsohuwar soyayya da kuma sakatariya ta*







*TSOHUWAR💖SOYAYYA*

*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Free page

0️⃣3️⃣ Aaliyah and Saeed's diary

Tun tafiyar Aaliyah ya ke kallon hotunan, yana yi ya na zuƙar tabar sa. Tabbas ya san Mom da Dad arrange marriage a ka mu su. To dama haka ake yi ai, rich girl for a rich boy. But for thirty years Mom would've fall inlove with Dad ai. Zuciyar sa ya raya ma sa. Amma kuma idan ya tuna maganganun Dad sai ya ga kamar har ya rasu babu soyayya tsakanin su. Anya kuwa? Good 30yrs fah.

Ya maida hotunan tareda cigaba da tuno rayuwar su kafin Dad ya ɗauke shi a London. Duk da yana da ƙarancin shekaru amma yana iya tuno wasu events da su ka faru. Ƙarar wayar sa ne ya fargar da shi. Ya amsa kiran ganin wanda ya bugo.
"Zaid mi ya faru ne, Fatima ta kira ni tana kuka wai dole a raba gado. What is happening?"

Sai da ya zuƙi taba wanda itace ta uku da ya ke sha ya ce " Uncle, abinda ta ga ya fi ma ta kenan. And i'm Ok with it"

"A'a Zaid, Ahmad ba zai so haka ba, ka san yaran Fatima mata ne kai ne Ubansu yanzu. Responsibilities na su na hannunka har su yi aure.  Zan zo ranan Friday sai mu zauna a tattauna matsalar"

"Ok Uncle"

Sai daya ajiye wayar sannan ya tuna ko breakfast bai yi ba. Dama breakfast ɗin zai je yi a wajen Mom ya tarar da badaƙalar da su Inna su ka shiryawa Mom...

..................................

Kwana biyu da tafiyan Aaliyah amma kuma ya kasa cire maganganunta a ran shi, musamman idan ya kalli Mom sai ya ga kamar tana cikin damuwa. Idan ya tambayeta kuma ta ce ma sa ba matsala.

Yau ma su na cin abincin dare tare amma ya lura a takure ta ke kamar ba ta jin daɗin abincin duk da kuwa ita da kanta ta bada order abinda su Eliza za su girka.

"Mom is there something you are hiding from me?"

"Ofcourse not son, mi ka gani?"

"Mom kamar akwai abinda ke damunki, you always look disturbed. Like you are hiding something very important...."

"Zaid" ta katse shi
"I'm fine son, yes i look worried saboda yanzu ba da bane, but nothing else"

"Mom that night, twenty years ago...."

"Zaid!"  Ta faɗa da ƙarfi.

"Shikenan tunda bakyason maganan"

Ajiye cokali ta yi ta ce " I've lost my appetite"

Sai da ta shige ɗaki ya sauke ajiyar zuciya. Ba zai manta abinda ya faru shekara ashirin da su ka wuce ba. He was only eight amma ya na iya tuno komai. Lokacin da Dad ya ɗauke shi daga London kullum sai ya tuna kukan Mom a daren ranar. The screaming, the cries, everything.
Maganan Aaliyah ya tuno da ta ce akwai babban al'amari a rayuwar Mom that he needs to know about. "Could it be related to what happened 20yrs ago?" Ya tambayi kan sa.

He was only eight years lokacin da ya rabu da Mom and ba ta taɓa neman sa ba.  She stays in London all the while. Ya tuna lokacin da ta zo Nigeria ya ƙi ya je wajen ta. How she kneel and cried.  Hawaye su ka gangaro ma sa. Lallai ne dole ya nemo diary ɗin Mom atleast he will find some answers there...

Ta ya Zaid zai tuno ma ta da abinda ta ke ƙoƙarin ɓoyewa iya tsawon rayuwar ta. This is too much for her.

Ta sa key ta buɗe drawer, ta fidda jakar da ta jima tana adanawa.
"If only you came Saeed, if only you came that day"  ta faɗi hawaye na zirya a idon ta.

*"Ke ce zuciya ta Aaliyah, idan na rasa ki na rasa zuciya ta gaba ɗaya" *  ta tuna maganganun sa lokacin da ya sanya ma ta zobe a hannun ta. Ta kalli yatsarta da ke ɗauke da tabon ƙuna. Ko ba zoben a wajen akwai shaidar zaman zoben a yatsar.
Gani ta ke kamar yau ne komai ya faru. Da saka zoben da kuma cire shi.

"Makhtub" abinda mai duban ya faɗa kenan lokacin da ta tambayeshi.

"Zan auri Saeed?" Tambayar da ba za ta taɓa mantawa ba kenan.

"Makhtub yarinya, rubutacce ne, ko sama da ƙasa za su haɗu sai kunyi aure. Sai dai....."

Ƙaran wayarta ya fargar da ita ta yi murmushi lokacin da ta ga Aaliyah ce.

Ta ɗauka wayar ta na murmushi, lokaci guda Allah ya haɗata da yarinyar nan amma ba ƙaramin shiga ranta ta yi ba.

...........................

Mom ba ta wajen aka yi zaman saboda Zaid bai ma sanar da ita ba. Idon Hajiya Fatima yai zuru-zuru lokacin da lawyer ya gama bayanin sa. "Wannan gidan da ku ke ciki na Aaliyah ce. Aaliyah, Ahmad ya bawa gidan nan"

Gidan da Aaliyah ba ta zauna a ciki na cikakken shekara ba. Ta ya Ahmad zai ma ta haka? Fatima ta tambayi kanta

"Hajiya Fatima, ina so ku daure ku yi zaman lafiya tsakanin ku. Idan ki ka cire wannan gida da Ahmad yai wa Aaliyah kyautar sa Aaliyah ta yafe gadon Ahmad. Daga ke, 'ya'yan ki sai Zaid ku kuke da wannan dukiya, kuma idan aka ce a raba kowa yai na sa waje ba za ku ji daɗi ba. Zaid shi kaɗai ne ɗa namiji dan haka ki bashi haɗin kai ya kula da ƙannen sa"  lawyer ya faɗi ya na harhaɗa takardun da ya nunawa su Hajiyar.

Da Hajiya Fatima da Inna duk ba wanda ya ce wani abu har Zaid da lawyer su ka fita a falon.

...........................

Sai da aka yi sati biyu da dawowar su sannan Mom ta shirya ta tafi Maiduguri. A wannan lokacin Zaid ya samu damar bincika ɗakin Mom. Ya jima ya na dube-dube a ɗakin amma shiru bai ga diary ba.
Ya zauna akan gadon ta ya na haki.
"Kodai Mom ta tafi da shi Maiduguri ne ko kuma Mom ba ta da diary?"
Zuciyar sa ne ya tuno ma sa ɗaya daga cikin drawers ɗin a kulle ya ke da key. Ya tashi da sauri. Ya nemi key ɗin wajen bai gani ba. It's obvious duk sauran wajen ba a sa key ba sai last drawer ɗin definitely akwai abu mai muhimmanci a ciki.

Ganin neman key ɗin zai ɓata ma sa lokaci ya sa ya fita dan ya nemo guduma ya kwaɗe, ya san duk rintsi kafin Mom ta dawo zai sa a gyara ba za ta ma ganeba...

To his surprise wata jaka ya gani a cikin drawer ɗin. Tsohuwar jaka ce wanda aka yi yayinsu a irin 80's ɗin nan. Ya sa hannu ya ɗau ko jakar tsaftsaf ta ke ba ƙura ko dauɗa a jiki. Sai da ya zauna da kyau a tsakiyar ɗakin sannan ya buɗe jakar. Diary guda biyu ne a ciki sai album. Album ɗin ya fara buɗewa yana ganin hotunan da ke ciki. Hoton farko na Mom ne lokacin tana jaririya sai da ya jima yana kallon hoton kafin ya cigaba da kallon sauran, cikin hotunan da ya ke dubawa ya ga harda wanda Aaliyah ta bashi. Sai daya gama kallon hotunan sannan ya jawo ɗaya daga cikin diary ɗin ya buɗe date ya gani a sama sannan aka rubuta *The beginning*
Rufe diary ɗin yai ya kwashe komai ya maida cikin jakan sannan ya ɗau jakar ya fita daga ɗakin...

Tana kitchen tareda Abba su na girki ƙaninta Abdul ya shigo ɗauke da wayarta da ke ringing.

"Z Wamako na kiran ki Anty"

"Abdul ka maida wayar ka ga aiki mu ke zan kira daga baya" ta faɗi tana ƙoƙarin saita nitsuwarta.

"Tun ɗazu fa ake kira" Abdul ya faɗi yana miƙa ma ta wayar. Tana amsar wayar kiran ya kuma shigowa. Abba ya ce " ki je ki amsa wayar ki"
Haɗiye miyau ta yi ta amsa wayar tareda ficewa daga kitchen ɗin da sauri.

Minti biyar sai ga ta ta dawo fiskarta ɗauke da farin ciki. Abba ya kalleta ya ce " waye *Z Wamako*?"

"Ehm. Abba ƙawata ce da mukayi makaranta ɗaya. Zainab....Zainab Wamako sunan ta"

Kamar faɗin Wamako ya tsikareshi lokaci guda ya furta *Wamako*

"Abba ka san wani mai irin sunan ne?"

Ya jima bai ce komai ba, hankalinsa ma ba ya wajenta. Sunan Wamako ya taɓo ma sa wani tabo da ke zuciyansa tsawon shekaru.

"Abba are you Ok?"'
Yai firgigit ya ce " yes, yes princess"...

..............................

Ba ta sha mamaki ba da Abba ya amince da tafiyarta amma da sharaɗin  za ta dawo kafin ƙarfe shida na yamma. Ko ba komai za ta samu ta yi abinda za ta yi kafin nan.

Driver ne ya kaita har gidan su Nawal. Kamar yadda ta tsara. Da dreban su ya tafi sai ta kira Nawal ta fito da motar ta su ka fita. Har cikin compound ɗin gidan su Zaid Wamako ta shiga da ita, su ka rabu akan za ta kirata.

Kiran Zaid ta yi akan ta iso ya ce ta shigo ɓangaren Mom.

A zaune ta sameshi yana karanta jarida.

"Wamako da gaske ka samu diary ɗin?"

Hararanta yai ya ce "idan ban samu ba zan kira ki ne"

"Oh. Ina diary ɗin? Ka karanta?"

"Aaliyah ki ke ko wace, I dont trust you. Ki faɗamin miyasa ki ke bibiyar Mom ɗina"

Ba ta bashi amsa ba sai ta buɗe jakarta ta fitar da wani diary daga ciki ta ce "wannan diary ɗin shi ya sa na san wacece Mom kuma shine dalilin da ya sa na ke bibiyarta"

Kallonta yai na wasu daƙiƙai sannan ya ce biyoni.

Ɗakin Mom su ka shiga inda ya fito da jakar da ya gani a drawer.
Lokacin da ya fitar da abinda ke ciki Aaliyah harda ɗan ihunta.

Zaid ya ce "lafiyar ki kuwa"

Aaliyah ta ɗan yi gyaran murya ta ce "duk farin ciki ne ya jawo haka"...

A ƙasa su ka zauna bayansu na jingine da gado. Nan su ka fara karanta diary ɗin Mom...







*TSOHUWAR💖SOYAYYA*


*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Free page

0️⃣4️⃣

*...........AALIYAH.............*

The begining



Suna na *Aaliyah Badamasi Bulama*. A faɗin garin Maiduguri suna Bulama suna ne da yai ƙaurin suna,  gida ne da ya gaji dukiya da arziƙi tun Iyaye da Kakanni.
Mahaifina Alhaji Badamasi Aliyu Bulama ya fito daga wannan gida mai daraja, ya fito gidan kuɗi kuma ya nemi kuɗi ya samu. A wannan lokaci Alhaji Badamasi yana ɗaya daga cikin wanda su ka ƙara ɗaukaka sunan gidan su saboda yadda Allah ya buɗa ma sa arziƙinsa ya haɓaka sosai.

Mahaifina matan sa biyu, da farko ya auri 'yar dangi wato Hajiya Yana sai daga baya ya auri Mariyatou. A lokacin da ya auri Mariyatou yaran su huɗu da Hajiya Yana. Akwai  Bukar, Falmata, Aliyu sai Sanah wacce ta ke 'yar shekara ɗaya a lokacin.

Mariyatou wadda kowa ke kira da Amma ƙanwa ce ga Alhaji Aliyu Sise Idrissa wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi a garin Agadez da ke ƙasar Niger, asalin su Buzaye ne.

A yadda labari ya zo mana Mahaifina ya je Niger biki ya haɗu da mahaifiya ta. Kyawunta ne ya ja hankalinsa farat ɗaya. Wadda a take ya sa a nema ma sa ko ita wacece. Kasancewarta ƙanwa ga Alhaji Sise sai abin ya zo ma sa da sauƙi saboda Alhaji Sise abokin sa ne.

Wata goma da auren Mariyatou aka haifeni. Kyau da farin fata ta duk daga mahaifiya ta ce. Tun da aka haifeni kuwa Amma ba ta sake haihuwa ba sai dana shekara biyar kafin ta haifi ƙanina Muhammad sannan Usman, Yahya da Musa su ka biyo baya.

Mu shabiyu ne a wajen Mahaifinmu. Hajiya Yana na da 'ya'ya bakwai Amma na kuma biyar.

Tun tasowata na ke cikin gata, daga wajen Amma har zuwa wajen Baba. Yadda na ke da kyau ya sa kowa ke son ɗauka ta, haka nan koyaushe akayi baƙi Baba zai sa a kawo ni, ina maƙale da shi.

Yawan surutu da tambayoyi su ne ɗabi'un da su ka bayyana min tun a ƙarancin shekaruna. Ba na taɓa gani na yi shiru.

Hajiya da Amma su na zaune lafiya, Hajiya ta riƙe girmanta a matsayinta na babba hakan ya sa Amma ta kwantar da kai su ke zaman su lafiya tamkar ya da ƙanwa.

Babban gida Baban mu ya gina a Maiduguri. A lokacin gidan mu na ɗaya daga cikin gidajen da ake kwatance da su saboda girma da kyau. An wadata cikin gidan da kayan alatu na more rayuwa kuma tsarin ginin gini ne mai tafiya da zamani saboda wasu ƙwararrun turawa ne su ka zana gidan.
Parts huɗu ne a gidan na mu, akwai ɓangaren Baba wanda ya fi ko'ina girma, yana amfani da ƙasa wajen ƙarɓan baƙinsa wanda ke ƙunshe da falo biyu  da ɗakuna uku, akwai babban dining room da ke ɗaukan kujeru ashirin, sai sama inda ya ke kwana falo da ɗakuna biyu da ɗakin karatu. Akwai ɓangaren Hajiya da ke ɗauke da falo da ɗakuna huɗu da kitchen, dining da store sai na Amma na ma haka. Bangaren ƙarshe kuma na yara maza ne falo ne da ɗakuna huɗu shima. Chan ta bayan gidan kuma an gina quaters na ma su aiki, sannan akwai garden a gidan wanda aka wadata da rumfuna guda huɗu domin zaman shaƙatawa.

Lokacin da aka haifeni da 'yan watanni kaɗan Amma na ta koma makaranta dan haka rainona kwacokam ya koma hannun Jijiɗo matar ɗaya daga cikin masu gadin gidan mu.
Jiji kamar yadda na ke kiranta ita ta raine ni kuma ita na fi gani a matsayin uwa, saboda na taso na ga ita ke min duk wata ɗawainiya da uwa ke wa ɗiyar ta. Sabo mai tsanani ne ya shiga tsakanina da wannan salihar mata.  Lokacin da aka yayeni kam daina damuwa ma na yi da Amma na, domin hatta 'yan gidan mu kirana su ke da 'yar gidan Jiji.
Lokacin da aka sa ni a makaranta kuwa, a kullum idan na tashi Jiji ce za ta zo ta shirya ni ta bani abinci sannan ta ɗauke ni ta kaini wajen mota inda direba ke jiran mu. Da na dawo kuwa ita za ta

Please Login or Register in order to submit comment