You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tanada min da ta ganni sai ta ji ta huce. Tausayina ya kamata, da na zo muna cin abinci ta ga yadda  hannuna ya koma sai da ta yi kuka.

"Aaliyah ki rabu da Ahmad dan Allah, zai kashe ki" ta faɗa cikin kuka.

"Ina da ciki" na furta a hankali

Ta ɗago ido ta kalleni ta rasa farinciki za ta yi da labarin da na bata ko baƙin ciki.

"May be its too late for everything dear Sister. I'm  carrying his child" na ƙarasa faɗa lokacin da na haɗiyi lomar abincin da na sa a bakina

Ta riƙe hannuna ta ce "ki duba hannunki Aaliyah. Haka za ki cigaba da rayuwa da shi kenan?"

Na yi murmushi tareda ce mata Ahmad na son cikin jikina kuma ya ce za mu koma London da zama, idan na yi nisa da Inna zan samu sauƙin wasu abubuwan. And who knows Ahmad might change...

Ban bar gidan Sanah ba sai ƙarfe tara na dare. Ita da mijinta su ka dawo da ni gida. Kai tsaye ɗakina na wuce na shiga banɗaki na yi wanka ina fitowa ɗaure da towel na tsaya gaban mirror ina ƙara kallon kaina. Na yi haske sosai, inaga saboda cikin jikina ne amma kuma ba ƙaramin rama na yi ba.  Na sa hannu na fara shafa fiskata zuwa wuya na.

Amma ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin "Aaliyah ga tea na kawo miki, garin akwai sanyi yau" ta tsaida maganarta lokacin da ta ga kafaɗuna zuwa bayan wuyana.

Innalillahi ta fara maimaitawa ta ƙariso wajena da sauri bayan tea ɗin da ta ɗauko ya ɓare a hannunta.

"Aaliyah miye wannan? Mi ya sameki anan? kaman tabon duka na ke gani" ta faɗa tana kai hannunta wuyana.

Towel ɗin na kunce na jashi ya faɗi ƙasa. Amma ta kama baki haɗeda zaro ido ganin raunukan da ke bayana, ɗuwawuna zuwa ƙafafuwana.
"Wa su sun warke, wa su suna kan warkewa wa su kuma sabbin raunuka ne ko?"

Na faɗa gameda juyowa ina kallonta.

"Subnallahi, Aaliyah ba dai Ahmad ne ya miki wannan ba?" Ta faɗa cikin rawar murya

Murmushin takaici na yi na ce " Amma akwai raunin da ya fi kowanne daɗewa ajikina, tun ranan farko da aka kaini Sokoto na sameshi. Ya jima da warkewa sai dai tabo da ya bari a wajen bai bar wajen ba har yau. An dakeni lokacin saduwa, an dakeni saboda maganar baki, an dakeni saboda uwar miji, an dakeni saboda na goyi bayan  gaskiya. Ban san daɗin aure ba Amma, duka da wahala kawai na sani. Ban san farinciki da kwanciyar hankalin aure ba Amma, fargaba, tsoro da baƙin ciki kawai na sani. Ban..."
Na tsaya da maganar lokacin da na ga Amma ta yi zaman dirshan a gabana tana rusa kuka.
Na ɗau towel ɗin da ke ƙasa na ɗaura shi jikina na ce "ina fata dai alfanun da kuke nema da ku ka haɗani aure da Ahmad kun sameshi?" na shige banɗaki da sauri saboda kuka da ke cin ƙarfi na. Na rufe baki ina kuka, kukan abubuwa dayawa na ke yi amma alokacin kukan da ya fi damuna shine kukan ɗan da ke cikina. Ɗan da aka sameshi lokacin da na ke tsaka da Allah ya isa wa Ubansa, ɗan da zai fito ya ganni cikin baƙin ciki da tsanar uban sa. Ɗan da kullum na kalleshi zan so inama bai fito ta satson uban sa ba...

Amma ta jima tana kuka a ɗakina kafin daga baya ta ja ƙafafuwanta ta bar ɗakin. Sai da na ji fitanta sannan na fito daga banɗaki na sa kayan bacci na bi lafiyar gado. Ban jima ba baccin gajiya ya tafi da ni...

Washe gari Amma ko kallona ba ta iya yiba. Da na gaidata da ƙyar ta amsa min, muryanta ya dashe hakanan idonta duk sun kumbura. Tun bakwai ta fita gidan Hajia Badariyya sai dai ko da ta je aka ce ma ta Hajiyar ba ta ƙasar ta tafi Dubai siyayya. Haka Amma ta dawo jiki a sanyaye.

Da ta dawo ina zaune a falo ina kallo, a zahiri kallon na ke yi amma chan zuciyata wani ƙunci na ke ji. Gidan su Jiji na je dan mu gaisa na samu sabbin fiska a cikin gidan da na tambaya sai aka ce wai su Jiji sun jima da tashi.
Wani zafi na ke ji yana mamaye duk ilahirin jikina duk da kuwa sanyi da ake yi a garin. A kowani rana sai na tuna da wani abu na rayuwar da mu ka yi da Sa'eed, duk iya ƙoƙarina na ganin na yaƙice hakan a raina na kasa musamman idan na kalli yatsata na ga zoben da Sa'eed ya sa min a wajen. Sanin akwai auren Ahmad a kaina ya sa na ke yaƙi a kullum dan na dena tunanin sa amma still duk a banza. Halayyan Ahmad su suka sa na kasa mantawa da mutumin da na ke tsananin so a duniya...

Amma ta zauna gefena tana  faɗin "ki yafeni 'yata. Ni ne nan na cuceki, ba abinda zai sa ki zauna da Ahmad yana zaluntar ki face abinda na sa aka miki da ke riƙe ki"
Hannuna ta kamo tana kallon yadda su ka koma.
"Ranan da ki ka yi ƙoƙarin guduwa abin ya bani tsoro. Na san taurin kan ki, na sani ko bayan an ɗaura auren ki da Ahmad za ki iya guduwa. Ina gudun ki jawo mana abin kunya, ina gudun ki yi abinda har ki koma ga Allah za a dinga zagin ki da shi, shiyasa da Hajia Badariyya ta bani shawara na amince. Wajen Malami ta je aka rufe min bakinki ba za ki taɓa neman saki da bakin ki ba a wajen Ahmad. Ba anan abin ya tsaya ba,  ba za ki taɓa guduwa daga gareshi ba kai ko shi ya sakeki bisa ra'ayin kan sa ba za ki bar gidan sa ba har sai an warware abinda aka miki. Niyyata idan kunyi aure kin zauna da shi kin kwantar da kan ki sai na sa a warware abin da aka miki. Na yi wauta Aaliyah ki yafeni" ta ƙarasa maganar tana kuka mai tsuma zuciya.

Inna was right all along shiyasa ta ke min abinda ta ga dama saboda ta san ba zan iya rabuwa da ɗanta ba. Na miƙe tsaye na kalli Amma da ke kuka na ce "ko da abinda ki ka min ya fi wannan ni mai yafe miki ne saboda ke kika haifeni. Zamana a gidan Ahmad na koyi darasin rayuwa, na gani muraratan yadda mace ke iya zama hatsabibiya sheɗaniya saboda dukiya. Na ga yadda kwaɗayin duniya ke sa mutum ya zama marar imani marar tausayi. Na gane cewa kuɗi ko kaɗan ba su ke jawo farin ciki ba kuma ba za su iya siyan farin ciki ba.
Kuɗi kuke tunanin zai sani farinciki shiyasa ku ka ƙi Sa'eed kuka zaɓi Ahmad"
Na share hawayen da su ka cika min ido na ce "Na yafe miki Amma kuma nima ina so ki yafe min. Ko da na mutu a gidan Ahmad na amince addarata ce ta zo da hakan ku dai kawai kun zo a sababin kaini gidan sa ne"
Na wuce ɗaki na bar Amma tana cigaba da kuka...

Cikin kwana biyu Amma kamar za ta zauce, neman numbar Hajiya Badariyya kawai ta ke yi saboda ta samu a warware duk wani ƙullin da aka min. Baba da baya ƙasar ma sai da ta kira shi ta ce ya dawo ya ga yadda na koma, tun a waya ta ce ma sa idan ya zo dolene a raba aurena da Ahmad. Da ke bai san mi ya ke faruwa ba ya dai kwantar ma ta hankali akan dole zai dawo Monday ya gani da idonsa koma minene ta ke magana a kai.

Monday ɗin ya kamata na koma Sokoto sai dai yadda Amma ta takura ya sa na ce zan bari Baban ya dawo kafin na tafi.  Ranan Jumu'ah da misalin ƙarfe uku ina zaune a ɗaki ina karanta wani littafi mai suna Gone with the wind wanda Sa'eed ne ya siya min lokacin muna Cambridge sai  ga Kalim ya shigo ɗakin da gudu. Ce min yai wai Ahmad ya zo yana falo, na zaro ido cikin mamaki ko dai dan dawo yau ɗin ba ne ya biyo bayana. Na yi saurin ɗaukan gyale na yafa na fito falon. Ɗan nesa da shi na tsaya ina kallon sa na rasa ma mi zan ce ma sa.

"Tunda ban samu gaisuwaba ni ba rin gaisa da baby na. Fatan kina kular min da shi?"

"Sannu da zuwa, ya hanya?"  Na faɗa ina ƙoƙarin haɗiye miyau.

"Na baki minti ishirin ki shirya ki fito tafiya za mu yi"

Dama na san sai dai hakan. Na daure na ce Amma ba ta gida ka ɗan ƙara min lokaci ta dawo sai mu yi sallama.

Ya miƙe tsaye ya ce " minti talatin" ƙarasowa yai gabana yai zai shafa ciki na, da na ga ya kawo hannu sai da hanjin cikina su ka kaɗa dan na ɗauka duka zai kai min. Yana ajiye hannun sa a ƙasan cikina ina sauke ajiyar zuciya nima. Ya kalleni ya ce " na gaya miki har ki haifi baby na ba abinda zan miki"

Har ya fita ban bar kallon ƙofa ba, shikenan zan koma gidan tashin hankali. Na koma ɗaki dan na tattara kayana tunda na san halin sa ba haƙura zai yi ba. Na gama shirya jaka ta na ɗauko na fito bayan na rubutawa Amma ƙaramar takarda kan na tafi Ahmad ne ya zo. Ina fitowa falon Amma na shigowa, ganina da jaka ya sa ta ƙariso da sauri tana tambayar ko lafiya. Na ce tafiya zan yi Ahmad ne ya zo ɗauka na.

"Ba inda za ki je, ba za ki koma gidan sa ba. Duk abinda zai je ya dawo ba zan bari ki koma ba" ta faɗa da ƙarfi.

Na girgiza kai a hankali na furta "its too late"

"Its not late Aaliyah. Babanki zai dawo ranan litinin, Badariya ma ta ce za ta dawo ranan laraba kinga komai zai zo ƙarshe kenan. Alhamdulillah ma da rabo bai ratsa tsakanin ku ba, a rashin sani ina chan ina addu'ar Allah ya baki ciki ashe da mugu ki ke tare. Allah na gode da ba ka amsa addu'a ta ba" ta faɗa tana ɗaga hannunta biyu sama kamar mai addu'a.

Murmushin da na yi ne ya yi sanadiyar suɓutowar hawayen da su ka taru a idona.
"Allah ya amshi addu'ar ki, akwai rabo tsakanina da Ahmad"

Amma ta yi taga-taga kamar za ta faɗi na yi saurin riƙota.

"Duk da haka Aaliyah ba za ki koma ba, ba za ki koma ba" ta ƙarisa maganar cikin kuka...



Dreban na mu gudu kawai ya ke fanfalawa a titi. Na dai ga ba hanyar Sokoto mu ka nufa ba amma na yi shiru, lokaci zuwa lokaci Ahmad na sa hannu a cikina yai ta sunbatun sa, a dole yana yiwa ɗan sa hira. Sau uku ina bacci ina farkawa amma tafiya ta ƙi ƙarewa mun tsaya sau biyu dan cin abinci da kuma sallah bayan na lura tun da mu ka taso bamu yi sallar la'asar ba balle magariba da Isha.

"Ba za ki tambayi inda za mu je ba?" Ya faɗa lokacin da ya ga ina ƙoƙarin sake komawa bacci.

"Koma ina zamuje Allah ya sauke mu lafiya"

Dariya yai ya ce "Aaliyah kenan, har yanzu kina da girman kai. Da ki tambaye ni gara kin jira har mu isa inda za mu je ki gani da idon ki kenan. Shikenan Maman baby" ya ƙarisa maganar yana dariya ƙasa-ƙasa...

Lagos mu ka je, ni kaina ban san dalilin zuwan mu ba sai daga baya.
Ahmad ya saki Bilkisu kuma sun yi kaca-kaca da Inna shiyasa ma ya zo ya ɗaukeni akan mu zauna a Lagos kafin visan mu ya zama ready. A gidan Alhaji da ke Lagos mu ke zaune, ni dai ban taɓa tambayanshi abinda ya faru ba, a hankali ya dinga gaya min da bakin sa musamman ranan da ya bugu. Anan na ke jin asalin gaskiyar sa.

Ranan da na bar Sokoto ranan shima ya tafi Kano yai kwana biyu a chan. Kasancewa shi dama tafiyar sa da dawowar sa duk ba a sani shiyasa a rana ta uku ya dira a gidan bagtatan inda ya je ya kama Bilkisu da kwartonta, abin haushin ma ɗaya daga cikin abokan sa ne. Abu da ɗan giya haka ya hau jibgarta ita da kwarton, kwarton ya tsira da ƙyar itama kuma ihun da ta ke yi ya ja hankalin ma su aikinta su ka je su ka sanar da Inna. Inna ta taho da gudunta ta ceci Bilkisu da ƙyar a hannunsa gaba ɗaya ta galabaita ga jini a baki da hanci.

Inna ta fara ma sa faɗa shi ko ya nuna ga abinda ya kamata tana yi, Inna ta ce ai ba komai bane jiba da irin tarbiyan da aka yiwa Bilkisun. Uwa da ɗa su ka shiga yaɓawa junansu magana suna zage-zage ƙarshe ya fita ya bar mata gidan bayan ya rubutawa Bilkisu saki uku. Ba akai Bilkisu asibiti ba likita Inna ta kira ya zo har gida ya dubata. Inna ta dinga bawa Bilkisu haƙuri kan abinda Ahmad yai, ita ba ma ta abinda Bilkisun ta aikata ta ke ba, tsoron abinda Alhaji Ɗan Iya zai yi idan har ya ji labarin dukan da Ahmad yai wa 'yar sa ta ke ji.
Inna ta shiga lallamin Bilkisu tareda yi mata alƙawarin Ahmad zai tsugunna har ƙasa ya bata haƙuri. Ahmad ya dawo chan dare ya samu Inna na jinyar Bilkisu abin ya bashi mamaki. Duk dukan da zai min Inna ba ta taɓa hanashi ba sai ma tace madallah amma kuma sai gashi ya kama Bilkisu da kwarto amma har tana iya zaman jinyarta. Tana fara ma sa maganar Dawo da Bilkisu da kuma ba ta haƙuri ya haukace ma ta a daren ya shiga fizgar da kayan Bilkisu waje yana faɗin idan ba ta bar ma sa gida ba zai kasheta. Inna kanta sai da ta tsorata da yanayinsa ta ja Bilkisu su ka fita su ka koma na ta gidan. A chan kuwa Bilkisu ta juyewa Inna da masifa tana zagi tana tsine ma ta. Inna sai haƙuri ta ke bata amma da Bilkisun ta gaya ma ta kalmar da ta fi tsana a duniya hakan ya sa Inna ta riƙiɗe ta fara maidawa Bilkisu martanin maganganunta. Haka Bilkisu ta bar gidan a daren tana tafiya tana zagin Inna da 'yar matsiyata 'yar talakawa, zuciyar Inna kaman zai fito dan baƙin ciki. Washegari tun asuba Ahmad ya tattaro kayan sa ya taho Maiduguri...

Kwanan mu tara a Lagos mu ka wuce London. Haɗaɗɗen Mansion Alhaji ya siya, ni kaina gidan ya burgeni saboda tsarin ginin. Sati na ɗaya kafin na samu na kira Amma na gaya ma ta ina London. Da muryan kuka ta ke min magana, tun ranan da na je gida Amma ta ke dana sanin abinda ta aikata da wanda ta bari aka aikata a kaina. Cemin ta yi Malamin da yai wa Hajia Badariyya aiki ya rasu, yanzu haka sun nemi wani malami ya ce zai iya karya alkadarin. Ni kam tabbatar ma ta da cewa na yi da abinda su ka min ya karye da bai karye ba idan ba Ahmad ne ya sake ni da ra'ayin kan sa ba zan cigaba da zama da shi duk rintsi. Amma kam cewa tayi ba zai yiwu ba dole ne na rabu da Ahmad. Ni 'yar gata ce gaba da baya, ban cancanci miji kamar Ahmad ba, ni kam na ce daga baya kenan.
Baba ya kirani sau ɗaya inda ya ke neman na gaya ma sa gaskiyar abinda ke faruwa tsakanina da Ahmad, shima dai yana maganar ne cike da tarin nadama duk da girman kai bai bari ya yarda da hakan ba. Ba abinda ya sa ya aminta da zancen Amma face lokacin da ya kira Ahmad tun muna Lagos akan ya zo ya sameshi za su tattauna sai Ahmad ya ce ba shi da lokacin sa. Wannan kalmar ta shocking ɗin Baba matuƙa.
Ni ban ma san anyi haka ba Amma ke gayamin komai. Ga Inna a gefe da dama tun batun rabon gadon Alhaji Wamako su ka ɓata da Baba, da Baba ya san a gaba Ahmad zai ma sa fiye da baƙar magana ina ga da tuntuni ya zo ya tafi dani ko da ta ƙarfi ne, amma aka ce rashin sani ya fi dare duhu...

Zama a London ya zo min da sauyi da dama a rayuwata. Har wa yau ban yi dana sanin zuwa garin ba, akwai ranakun baƙin ciki akwai kuma na farin ciki. A London na ga wani ɓangare na Ahmad wanda ban san da shi ba a zaman da mu ka yi na Shekara ɗaya a Sokoto.




*21- The casino*

*A*


Wata ɗaya da mu ka fara yi ya zo min da kwanciyar hankali, na farko dai banda yawan bacci da cin abinci da cikin jikina ke sani ba ni da wani damuwa. Ina samun isashshen hutu domin ba na wani aiki, aikin wahala da na yi ya ƙare a gidan Inna. Inada mai aiki wata Black American Mrs Payne wanda a ƙalla za ta kai shekaru hamsin a lokacin. Ita ke yin aikin komai ko na ɗan shiga kitchen domin na yi wani abun idan Ahmad ya zo ya gani zai fara faɗa wai zan wahalar da ɗan sa, hakan ya sa na daina komai.
Kamar yadda yai alkawari kuwa ya daina nemana hakan ya ƙara kwantar min da hankali. Na fara sakin raina da gidan kwatsam sai ga Ahmad da wata karuwa wata yammaci ina zaune a terrace na gidan ina shan iska. Daga yanayin yarinyar ya sa na san irin matan da Ahmad ke so kenan, irin macen da yai ƙoƙarin mai da ni kenan. Yarinyar na sanye da wani lether mini skirt babu riga ajikinta sai wa su chains da ta sa dayawa wanda ya ɗan rufe gefen nonuwanta. Akwai rings a hancinta biyu da gefen bakinta har a nonuwanta akwai rings da ta piercing ajiki. Kallo ɗaya na mata na ɗauke kaina dan ƙyama ma ta bani. Ina gani su ka shiga gidan na cigaba da zama a inda na ke domin daɗin zaman wajen da na ke ji. Bai fi minti biyar da shigan su ba na fara jin ihun yarinyar tareda ƙaran duka. Na sauke ajiyar zuciya ina ƙoƙarin ɗauke hankalina daga abin da na ke ji. Amma ina ihun yai yawa na tashi dan na shiga ɗakina na nemi ko littafine nai karatu. Yadda na ke jin ihun yai yawa ne ya sa na sauko dan na tabbatar da zargi na. A tsakiyar stairs na tsaya ina banin yadda Ahmad ya ɗaure yarinyar nan tsaye yana jibgarta yana saduwa da ita. Na juya ciki ina yi ma sa addu'ar Allah ya shirya shi.

Daga Wannan rana baturiyar nan mai suna Cataliya ta zama regular a gidan mu. Tun ina damuwa har na watsar da su na cigaba da renon cikina hankali kwance, idan su ka dameni da ihu kuma idan ba da dare bane fita na ke na je ta baya wajen lambu na zauna.

Ko da a auren so ne akwai lokacin da idan miji ya shareka ya dena saka ka cikin lamuran sa kai ma za ka ajiye shi gefe ka zuba ma sa ido. Balle ni da na ke auren mutumin da ban taɓa so ba ban taɓa ƙauna ba. Idan ba ya zo yiwa ɗan sa hira ba bana gaban sa Cataliya ce komai na sa. Wata biyu da introducing Cataliya a rayuwar mu su ka yi aure. Ahmad Wamako ya auri Cataliya Santiago a kotu. Asalin su Cataliya 'yan mexico ne amma ita a London aka haifeta. Ban san dalilinsa na auren ta ba amma kuma na danganta hakan da business ɗin da ya ke yi wanda ban san komai gameda shi ba. A hankali ranaku su ka shige har ta kai cikina ya shiga wata takwas a lokacin ne kuma ciwukan da ban yi lokacin cikin yana ƙarami ba sai yanzun da ya girma ya fara. Daga ciwon ƙafa, ciwon baya sai rashin kuzari da ciwon kai mai tsanani a mafiya yawan lokuta. Ga rashin son cin abinci duk wani ci da na yi ta yi a baya sai na dena sai na wuni bai fi na ci abinci sau ɗaya ba. Duk halin da na ke ciki ban taɓa cewa Ahmad ya kaini asibiti ba. Shi yanzu ma sai yai kwana ɗaya biyu baya gidan.

Ranan da na shiga wani hali har zazzaɓi ya turnuke ni na kasa fitowa tun safe ya sa dole Mrs Payne ta kira Ahmad amma ya dinga ma ta faɗa ƙarshe dai ta kashe wayan ta kira ambulance aka zo aka ɗaukeni. Kwana na uku a asibitin tukunna aka sallamoni cikin ranakun nan ko mai kaman Ahmad ban gani ba. Cewa su ka yi ina da hawan jini kuma sun na dena sa damuwa a raina idan ba haka ba zan samu matsala wajen haihuwa, su ka bani shawaran na dinga motsa jiki sosai hakan zai kawo min sauƙi wajen haihuwa. Na amshi dukkan shawarwarin su ina ƙoƙarin motsa jiki, wani lokacin Mrs Payne ne za ta raka ni mu fita strolling.

Na yi mamakin da 'yan gidan mu ba su neme ni ba musamman da su ka san ina gab da haihuwa. Na yi ƙoƙarin kiran su amma ba ya tafiya, haka ya sa na haƙura na cigaba da addu'ar Allah ya saukeni lafiya ya kuma shiryar da abin da zan haifa kada ya ɗauko halin Uban sa.
Sati ɗaya da dawowana daga asibiti amma ba Ahmad ba dalilin sa. A lokacin ne na tuno da alƙawurran Sa'eed.
*"zan kasance da ke ako wani hali, idan ba ki da lafiya zan zauna na yi jinyar ki har ki warke. Idan kina da ciki da ni da ke za mu raini cikin, idan za ki haihu zan kasance tareda ke, na riƙe hannun ki na riƙa tofa miki addu'a har ki haihu lafiya"*

Na share ƙwallan da ke zubo min ina ƙoƙarin danne duk wani shauƙin Sa'eed da na ke ji da shi a wannan lokaci.
Ina cikin haka Mrs Payne ta shigo ɗakina da sauri tana faɗamin akwai wa su mutane suna nemana, yadda ta ke maganar ya sa na gane ba lafiya ba. Na tashi da ƙyar na bita mu ka fito.

Wani mutum ne zaune akan kujera da ka ganshi ka san irin Mafia Boss ɗin nan ne. Bodyguards ɗin sa guda huɗu su na tsaye kowanne da bindiga a hannun sa.

Na yi addu'a a raina sannan na tambayi mutumin dalilin zuwan sa bayan na zauna a kujeran da ke saitin sa. Ya kalleni da kyau sannan ya fara min bayani.

Gidan da mu ke zaune na shi ne kuma yana so mu tashi zuwa gobe. Da mamaki na fara tambayar sa yaushe gidan ya zama na shi. Ya ƙyalƙyale da dariya kafin ya tambayeni yaushe rabon na kalli news na ce ma sa ba zan iya tunawa ba dan na jima. Ya ce to zai ban labarin abin da ke faruwa har wanda media ba su san da shi ba.

Don Pedro Santiago wani Mafia Boss ne da yai ƙaurin suna a ƙasar sa Mexico zuwa America, UK da ma Russia. Yanada manya-manyan 'yan gwamnati da ke take ma sa baya shiyasa ya ke tsula tsiyarsa yadda ya ga dama. Yana da wani babban casino a tsakiyar birnin London inda ake gudanar da illegal business da dama. Watannin baya da su ka wuce Ahmad ya zama regular a Casino ɗin inda ya ke buga chacha kuma ba ƙaramin sa'a ya ke sosai ba duk lokacin da yai. Wannan sa'ar da ya ke samu ya sa har aka kai maganar sa wajen Don Pedro wanda yai niyyar hallaka Ahmad a lokacin daga baya zuciyar sa ya raya ma sa yai chacha da Ahmad ɗin. A lokacin ya sa aka ma sa binciken ko waye Ahmad da kuma abinda ya ke da shi. Nan aka gane Ahmad wani wawan ɗan Nigeria ne wanda uban sa ya bar wa kuɗi dayawa. Don Pedro ya fara buga game da rayuwar Ahmad. Cataliya 'yar Don Pedro ce,

Please Login or Register in order to submit comment