You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son Aaliyah, ba na tunanin zan taɓa son wata bayan ta...

Cikin kwanakin da na yi kafin na tafi bautar ƙasa zuciyata ta yi laushi. Ba zan iya furtawa Aaliyah halin da na ke ciki ba, ina so ko da na ƙarshe ne to na kasance da ita, ina kallon murmushin da ke shimfiɗe a kyakykyawar fiskarta, murmushin da domin Sa'eed kawai ta ke yin sa.

Ban yi mamaki ba da na samu tafiya amma Aaliyah ba ta samu tafiya tareda ni ba, na san shirin Alhaji ne dan kar ma mu tafi tare. Lokacin da ta samu tafiya ma maimakon Minna da ta sa a farko sai a ka sa ta Maiduguri bayan kuma ba ta cika da Maiduguri ba.

Ranan da zan tafi kallon ƙarshe na yiwa Aaliyah domin ni kam na san daga lokacin Aaliyah ta yi min nisa.

"Sa'eed ka ga muna gama bautan ƙasa sai aure. Za mu fara zama a Durum kafin mu tafi duk inda aiki ya kai ka. Na missing ƙauyen ku"

Yadda ta ke maganan hakanan na ke jin zafi a zuciyata. Ina ma nima wani ne ko kuma ɗan wani ne a ƙasar. Ina ma Aaliyah ba 'yar kowa ba ce. Ina ma muna duniyar da babu haramci tsakanin auren talaka da maikuɗi.

"Beloved ba ka ce komai ba?" Ta katse tunanin da na ke yi.

Na yi murmushin yaƙe na ce "duk abinda ki ke so haka za ayi"

Da na ɗau jaka na zan tafi ta riƙe hannuna. " ba goodbye kiss ne?"

Na yi seƙeƙe ina kallon ta, ba wai dan ba na son yi ba ne a'a sai dan ina gudun haƙurin da na ke ta yi na tsawon lokaci zai iya ƙarewa.
Ta matso kusa da ni sosai ta    yi ɗegel da ƙafafuwanta saboda ta yi daidai da ni.
Ta sa hannu ta shafa fiskata ta ce " na kusa zama mallakin ka duniya da lahira masoyina" ta yi murmushi sannan ta fara kissing ɗina....

Tunda na tafi na ke cikin ƙunci amma a hankali ina addu'a abin ya fara min sauƙi. Sai da na yi wata ɗaya kafin na rubutawa Aaliyah wasiƙa amma har wani watan babu amsa, na sake kai wani wasiƙan shima shiru. Da bincike na gano abinda ke faruwa, jin mahaifiyar Aaliyah ce ta hana kai wasiƙuna ya sa na haƙura na fawwalawa Allah lamarina ina neman ya taimaka min kafin rashin Aaliyah ya ja min matsala a ƙwaƙwalwata...

Bayan mun samu mafitar aikawa juna wasiƙa Aaliyah ta aiko da wasiƙar da ta rikita ni.

*Sa'eed ka zo gida, idan ba ka zo ba zan kashe kai na, Ba zan iya auren wani bayan kai ba*

Iya abin da ta rubuta kenan. Na san halin Aaliyah na san za ta iya aikata abinda ta ce shiyasa tun farko na ɓoye ma ta abinda Alhaji ya faɗa. Ba ni da niyyar komawa Maiduguri har sai na ƙare bautar ƙasa ta amma wasiƙar Aaliyah ya chanja min ra'ayi. Ba ɓata lokaci na nemi a bani hutun kwana biyu amma hakan bai yiwu ba dole sai dai na haƙura zuwa ƙarshen sati...

Ranan Jumu'ah da yamma na hau mota sai Maiduguri, ba mu isa ba sai ƙarfe huɗun Asuba. A park na kwana sai da safiya na nemi taxi na wuce gida.

Baffa da Jiji sun yi mamakin ganina da sassafiya haka, na nuna mu  akwai abinda na zo yi ne kuma kwana biyu zan yi na koma. Baffa bai yi magana ba amma Jiji ta ritse ni a ɗaki tana neman tabbatar da zargin ta.

"Saura kwana shatara auren Aaliyah. Lamiɗo Dan Allah duk abinda ka zo yi ka yi ka tafi ba tareda tashin hankali ba"

Na kalli Jiji wanda ita ta zame min uwa a yanzu na ce "Insha Allahu ba tashin hankalin da zai faru"...

Ban samu ganin Aaliyah ba sai bayan Azahar. Tana shigowa ɗakin ta faɗa jikina tana kuka.
Tsikar jikina ya tashi saboda yadda wani ƙanshi ke fita a jikinta, duk da Aaliyah ma'abociyar ƙanshi ce amma wannan ƙanshin daban ya ke.

"Sa'eed wai aure za'amin, wai ƙarshen wata aurena da Ahmad Wamako. Ka taimakeni Sa'eed ba zan iya auren sa ba, mutuwa zan yi"

"Shhhhhh" na sa yatsata na rufe bakin ta.

"Ban da zancen mutuwa Aaliyah, kin san hukuncin kisan kai kuwa?" Na faɗa ina ƙoƙarin danne duk wani raɗaɗi da na ke ji a zuciyata.

"Laifin ka ne ai, da ka amince da ni tun a makaranta da yanzu babu yadda za'ayi su raba mu"

Ina ƙoƙarin shawo kan ta amma ta ƙi saurarena. Ta riga ta tsarawa kan ta mafita wanda duk ciki babu mai daɗin ji.

"Ka amince mu gudu mu je mu yi aure Sa'eed. Its the only way we can be together"

"Aaliyah" na faɗa a hankali

"Kar ka ce a'a, domin zan aikata abinda ba ka yi tsammani ba"

"Please Aaliyah, mu yi haƙuri, Allah ya...."

Dariyan da Aaliyah ta fashe da shi ya sa na kasa ƙarasa maganar da na ke yi.

"Mu yi haƙuri fa ka ce. Sa'eed son da ka ke min har ya yi raunin da za ka sadaukar da ni ga wani banza. Har za ka iya rayuwa babu ni? Har za ka iya haƙura da ni a rayuwar ka? Ta ya zan fara zama da mutumin da bayan sunan sa ban san komai game da shi ba?. Ta ya zan manta da soyayyar ka da ta riga ta zama jinin jiki na?. Ta ya za ka ce Aaliyah ta sadaukar da farin cikin ta saboda son zuciya irin na iyaye na, ba su damu da ni ko farin ciki na ba, abinda aurena zai haifar su ke hangowa. Sa'eed ban shirya biyayya wa auren dole ba tunda addini ma ya hana hakan"

Shiru na yi ina nazartar maganganunta. Nima daurewa na ke yi amma na san rashin Aaliyah zai iya jawo min matsala a sauran rayuwata. To ya zan yi? Ban taɓa burin na auri Aaliyah ba tareda yarda da amincewar iyayen ta ba.

"Aaliyah albarkar iyaye ta fi komai" na faɗa murya na rawa saboda yadda hawayen Aaliyah su ka sa na ji jikina yai sanyi.

"Ka zaɓa min halaka kenan Sa'eed?"

Na zaro ido ina girgiza kai.

"Idan ba ka amince mu gudu ba kashe kai na zan yi"

Na cigaba da girgiza kai ina ƙoƙarin magana amma na kasa saboda wani abu daya toshe min maƙoshi.

Ta ɗan ja baya kaɗan kafin ta ce " ka yanke shawara daga yanzu zuwa dare, duk abinda ka yanke shi zai tabbatar da rayuwa ta a duniya ko kuma mutuwa ta"

"Aaliyah"

Ta fice daga ɗakin da gudu tana hawaye. Nima ɗin hawayen baƙin ciki su ka samu damar zubowa daga ido na...

Duk inda na je na dawo zancen ɗaya ne, na amince da buƙatar Aaliyah.
Tsoro na ka da na ƙi amincewa Aaliyah ta kashe kan ta kamar yadda ta faɗa. Idan haka ta faru zan ƙarasa rayuwata cikin nadama da ƙunci ina dana sanin ƙin amincewa da buƙatar ta da na yi...

Da dare ta zo jin abinda na yanke na kuma tabbatar ma ta na amince mu gudu amma da sharaɗi ba za mu yi aure ba har sai iyayen ta sun amince.
"Ka na ganin ko shekara nawa na yi ban dawo gida ba idan na dawo Baba zai yarda ka aure ni?"

"Ina da yaƙinin zai amince Aaliyah" na faɗa duk da kuwa na san da kamar wuya.

Aaliyah ce ta shirya komai ita ta tsara tafiyar mu da inda za mu je. Lafiya zamu je, a nan za mu zauna har iyayenta su haƙura da maganar auren ta da Ahmad Wamako. Duk da kuwa ban taɓa zuwa garin ba amma na amince da hakan. Acikin rai na ina fatan idan mun je a hankali na nutsar da Aaliyah da maganar kisan kai da ta ke ta iƙirarin yi saboda yanzu na san tsoron auren ya ke sa ta ke wannan batu.

Bayan tafiyar ta na yi alwala na yi sallah ina roƙon Allah ya kawo mana mafita ya kuma sa kar tafiyar da za mu yi ya jawo ma na sharri maimakon alkhairi da mu ke fata..

Washe gari da safe kusan ƙarfe goma ina zaune a ɗaki ina saƙe-saƙe a raina sai ga Musa ƙanin Aaliyah wanda su ke kira da Kalim ya shigo ɗakina.

"Hamma Sa'eed wai ka je in ji Baba" ya faɗa lokacin da ya shigo ɗakin ba ko sallama.
Na kalli yaron wanda shi ne autan Alhajin na ce " Baban yana ina?"

"Yana Garden" ya faɗa yana cusa yatsar sa a hannu yana tsotsa.

Na yi mamakin ya aka yi har Alhaji ya san ina gari bayan ko haɗuwa ba mu yi da shi ba, asalima ba kowa ya san ina gidan ba. Na tashi na sa rigata na bi bayan Kalim wanda ya fita daga ɗakin ba jimawa...



*........Aaliyah.......*


Tunda na samu Sa'eed ya amince an wuce wajen maganar ma idan mun je ba aure za mu yi ba jin sa na ke yi kawai. Idan har zan dawo gida to sai dai idan da auren Sa'eed zan zo. Na san halin Baba na, ba zai taɓa amincewa da aurena da Sa'eed ba kuma ko da ban auri Ahmad Wamako ba wani ɗan maikuɗin za a kuma jajuɓomin. Idan da auren Sa'eed akai na kuwa duk fushin sa ƙarshe haƙura zai yi ya bar ni na yi rayuwata da masoyina. Ko Sanah ban faɗawa shiri na ba saboda tsoron kada ta faɗa duk da kuwa na san za ta riƙe min amana amma Sanah tana da tsoro idan Amma ko Baba ta dage akan ta gaya mu su inda na ke za ta faɗa.

Ba kasafai na ke fita ba saboda gyara da aka fara yi min. Idan na fita to na je wajen aiki ne. Kwantar da kai da na yi tun daga ranan da na yiwa Amma magana ya sa ta ɗan sake min ba kamar da ba. Ko da aka fara min gyara ban yi gardama ba, duk abinda aka bani na ci ci na keyi hakanan wa ni turara jiki da sauran shafe-shafe duk ina zama ana min. Ni kam duk tanadin nan Sa'eed na ke hangowa ba Ahmad Wamako ba.
Safiyar ranan da za mu gudu na samu Amma a ɗaki akan zan je gidan ƙawata  Daula da ba ta da lafiya ba ta musa ba ta ce na je amma na dawo da wuri. Dreban ta ne ma ya kai ni gidan su Daula.  Zuwan da na yi kuwa rufa ido ne dan daga gidan na chanja kaya na fita ta ƙofar baya. Dreba na nemo na ma sa bayanin inda zai kai mu da kuma inda za mu haɗu da shi. Kuɗin da ya buƙata na ga sun yi kaɗan na ƙara ma sa ninkin sa tareda alƙawarin indai ya kai mu garin Lafiya zan bashi wani kuɗin adadin wancan. Dreban mai suna Bdliya yai godiya ya kuma nuna min lallai zai cika alƙawari. Na koma gidan su Daula daga nan Dreban Amma ya mai da ni gida...

Kuɗi da hotuna da sarƙoƙi, ɗankunne da awarwaro na gwal kawai na saka a sabuwar Jaka ta, wanda daga Cambridge na taho da ita kuma ban taɓa amfani da ita ba.
Kuɗin da na sa zai isa mu kama gida a chan sannan mu fara wani sana'a kafin abubuwa su dai-dai ta, idan ma kuɗin ba su isa ba za mu iya siyar da jewelries ɗi na. Bayan na haɗa komai na sa jakar a ƙarƙashin gado na cigaba da hidima ta...


Ƙarfe shaɗaya da rabi na dare na fito daga ɗaki ɗauke da jaka ta. Amma ke da girki dan haka tana sashen Baba. Ta ƙofar kitchen na fice daga ɓangaren mu ina sauri har na tafi wajen katanga.

Lokacin da Baba ya sawa yayana Aliyu dokar kulle ta baya wajen katangar gidan ya ke haurawa ya fita. Duk da katangar akwai tsayi amma ya riga ya yi rami ta inda zai taka ya hau. Da yamma sai da na zago ta wajen na tabbatar ramukan na nan ta yadda zan iya hawa...

Jaka ta na fara jefawa kafin na diro ƙasa, sosai na bugu dan har ina tunanin gwiwowina sun kukkurje amma ba matsala ta ba ce, matsalata na bar gidan mu, matsalata na bar garin mu, matsalata na auri masoyina Sa'eed.

Gudu- gudu sauri-sauri haka na dinga tafiya har na kai inda na ce Bdliya Dreba ya jirani. Da mamakina sai ban ga Sa'eed ba, tun a daren jiya na gaya ma sa plan ɗina, sannan yau da yamma da na je ɗakin sa na  ajiye ma sa wasiƙa mai ɗauke da ƙarin bayanin inda za mu haɗu da sunan dreban da kamannin sa. Dole ne idan har ya shiga ɗaki sai ya ga wasiƙar saboda na ajiye ne a ƙarƙashin pillow kuma muddin Sa'eed zai kwanta to dole sai ya gyara gado. Balle ma na gaya ma sa idan na zo ban same shi a ɗaki ba zan bar ma sa saƙo.
Amma da ta sani a gaba tana nuna mi ni hotunan wa su kaya ya sa ban samu sararin sake zuwa na duba shi ba.

Ina rungume da jaka a cikin mota ina jiran zuwan Sa'eed amma babu shi babu dalilin sa. Ba ni da agogo a tareda ni amma na yi hasashen a ƙalla zan kai minti talatin a wajen.
Ina cikin mota sai ga wata mota ta hasko mu, na sa hannu na kare ido na saboda ƙarfin hasken. Motar ta yi parking  aka buɗe ƙofa, tunanina Sa'eed ne dan ban gani sosai saboda hasken fitilar motar da har yanzu ba a kashe ba.
Sai da mutumin ya kusa isowa motar mu na ga ba Sa'eed ba ne. Maimakon Sa'eed yayana Bukar na gani. Na yi wuff na fito daga motar na ranta da gudu, shima ɗin ya bi bayana da gudu yana faɗin na tsaya.  Gudu na ke yi kamar rai na zai fita hakanan kuma shi ma Bukar bai bar bina ba daga ƙarshe ma maimakon gudun mutum ɗaya sai ji na yi kamar mutum biyu ke bina. Ina cikin gudu Bukar ya damƙoni ta baya.

"Ka sake ni, ka sake ni in tafi"  inaaaa, duk ihu da kuka na Bukar bai sarara min ba haka ya saɓani a kafaɗa har lokacin ina damƙe da jaka ta ina kuka ina kiran Sa'eed.

Haruna ne a gefen Bukar ɗin, shi ne wanda ya biyo Sanah wanda tsakanina da shi wata goma ne cur na bashi, amma saboda shi namiji ne yadda yai girma ka ce ya girmeni da shekara biyar ne.

Motar su su ka sani ta ƙarfi,  gefen dama na Haruna gefen hagu kuma Bukar.
Ina jin dreba ya ja mota na ƙara sautin kuka na ina kiran " SA'EED"...


Anan na kawo ƙarshen free pages na Tsohuwar soyayya.
*Shin ya labarin Aaliyah Badamasi Bulama bayan wannan dare?*
*Ya rayuwa ta kasance wa Sa'eed Aliyu Modibbo bayan ya saɓa alƙawari*
*wai ya za ta kasance tsakanin Zaid, Zarah da Aaliyah?*
*ko kun yarda cewa kuɗi zalla ba sa saka farin ciki?*
*shin dole ɗan maikuɗi sai 'yar maikuɗi*

Za ku samu cigaban labarin idan kun biya 200 kacal ga wanda ya biya Sakatariya ta kuma zai biya 100.









*13-The wedding*


Wannan karan kuka Aaliyah ta ke yi sosai har da sheshsheƙa. Zaid ya ajiye diary ɗin a gefe ya zuba ma ta ido, yadda ka san 'yar yaye haka ta ke kuka, ko mutuwa aka mata albarka.

"Idan ba ki dena kukan nan ba zan fasa karatun nan, and that will be all. Ke yarinyace da za ki dinga kuka kaman wanda aka zane ki?" ya faɗa yana hararanta dan ta bashi haushi.

"I'm sorry" ta faɗa tana ƙoƙarin tsaida kukan ta...


*A*


Suna fitowa dani daga mota kai tsaye sashen Baba su ka nufa da ni, a lokacin na dena kuka kuma na dena kiran sunan Sa'eed. Ba abinda na ke hangowa kai na irin baƙar rayuwa da zan yi a gaba, rayuwa mai ƙunci rayuwar da babu farin ciki, tabbas na sani tunda na rasa damata yau, tawa ta ƙare kenan.
Zaune mu ka samu Baba da Amma a falo dukkan su sanye da kayan bacci. Kallo ɗaya na mu su na ɗauke kai na daga gare su.
Baba ya tako wajen da na ke tsaye rungume da jaka ina ƙyarma kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwan sanyi.
Wani wawan mari Baba ya saukemun sai da na faɗi ƙasa, na dafe gefen fiskata tareda ɗagowa da sauri ina kallon sa ido cikin ido.

"Wallahi Wallahi idan ba ki nitsu an yi bikin nan lafiya ba. Sai na tabbatar miki da cewa ni na haifeki kuma ina da iko da ke"

Ban ce ƙala ba sai ma cigaba da kallon sa da na ke yi, ina ganin son zuciya ƙarara a tareda shi. Ta yaya Uba zai yi watsi da farin cikin 'yar sa saboda wani buri na shi na duniya? Ta ya zai take abinda addini ya ce ya bi tsarin da 'yan Adam su ka shimfiɗa saboda cimma kan su wani alfanu na banza wanda aka shimfiɗa saboda zalunci da son zuciya.

"Idan ka aura min Ahmad Wamako ka zalunce ni Baba, ba zan taɓa yafe ma ka ba" na faɗa ba tareda tsoro ko fargaba ba. Har zuciyata kuma abinda na faɗa ɗin haka ya ke.
Baba ya kalleni da mamaki ya ce "ni Aaliyah ki ke faɗawa haka? Ni?" Ya jaddada maganar ta hanyar nuna kan sa. Ban cire ido na acikin na sa ba saboda zuciyata ta riga ta bushe.
Ya juya ya kalli Amma ya ce "kin ga abinda 'yarki ke faɗi ko. To ki gaya ma ta ko mutuwa za ta yi sai an ɗaura auren nan"
Ya kalli su Bukar ya ce " ku je ku kulleta a ɗakin ta" daga haka ya haura sama cikin fushi.

Tsananin tashin hankali da ɓacin rai na gani a idanun Amma, wanda ya haɗu da tsoro da fargaba. Dama ita mace ce mai saurin rikicewa musamman idan akan Baba ne, tana tsoron Baba sosai abinda na fiskanta a yanayin zaman su kenan. To ba dole ta rinƙa tsoron sa ba, aure ne aka yi babu ɗigon soyayya ko ɗis aciki.
Sai yanzu na ke ganin da gayya Amma ta ka sa goyon bayana akan soyayya ta da Sa'eed, itama auro ta aka yi saboda cimma wani buri.

Haruna ne na ya ja ni muka bar falon. Sai da mu ka je tsakiyar ɗakina sannan ya tunkuɗani na faɗi ƙasa.

"Kin cika taurin kai Aaliyah. Miyene aciki idan kin auri Ahmad Wamako? Mutum ga kyau ga kuɗi, mi kuma ki ke buƙata?"

Na ɗaga ido na kalli Haruna wanda ya ke matsayin ƙanina amma ya ke gaya min magana kamar ƙanwar sa ko 'yar sa.

"Kyau da kuɗi su ne buƙatun wanda bai mallake su ba Haruna, ga wanda ya ke da su kyakykyawar zuciya da kyawawan halaye su ne abu mafi soyuwa a gun sa"

Tsaki ya ja ya ce " a littattafai kenan Aaliyah, gara ki rungumi ƙaddara ki sawa kan ki salama"
Sai daya fita a ɗakin na fashe da kuka. Kukan abu ɗaya na ke, abu ɗaya da na ke so, abu ɗaya da ya ke ƙoƙarin gagarata, SA'EED na ke so...

Ban san ya aka yi na kai gado ba balle na san ko bacci na yi ko kuma suma na yi. Na dai buɗe ido na washe gari na ganni a kan gado na, Sanah ce ke zaune gefe na idon ta yai ja alamar ta sha kuka. Na yi yunƙurin tashi sai na ji hannuna saƙale da wani abu na bi hannun nawa da kallo sai a lokacin na ga ashe ruwa aka ɗaura min.
Na haɗiyi yawu mai ɗaci tareda ƙoƙarin tuno yadda aka yi aka sa min ruwa a hannu ban sani ba. Ni bayan fitan Haruna a ɗaki jiya da dare ba zan iya tuna komai ba kuma.

"Ya jikin na ki?" Sanah ta faɗa tana ƙoƙarin gyara min pillow saboda na samu na kishingiɗa.

"Ƙarfe nawa?" Na faɗa da dashashshiyar muryata.

Ta ɗaga ido ta kalli agogon ɗakin ta ce min ƙarfe shabiyu da rabi.
Na rintse ido na takaicin abinda ya faru daren jiya, da Sa'eed ya zo da yanzu mun jima da isa garin Lafiya ƙila ma har mun samu gida achan.

"Sa'eed, Sa'eed ya zo nema na?" Na tambayi Sanah ina mai fatan amsar da za ta ban ya zamo mai daɗin ji a wajena.

"Ban sani ba Aaliyah, ko ya zo ba zai samu damar shigowa ba saboda Amma"

Na rintse ido na ina hawaye. Dama ina so ya zo ne ba dan komai ba dan ya gaya min dalilin da ya sa bai zo ba jiya.
Idan ya gaya min bai gane kwatance na bane ko kuma bai ga wasiƙar da na bar ma sa ba, zan ma sa uzuri. Amma idan ya ce bai zo bane saboda tsoron Baba da Amma na ba zan yafe ma sa ba...

Da yamma Jiji ta shigo gaida ni na tambayeta ina Sa'eed sai ta ce min Sa'eed ya koma Minna jiya da yamma. Ba zan iya bayyana kalar baƙin cikin dana shiga ba da jin wannan batu, wani ɓangare na zuciyata na son ƙaryata maganar amma mafi rinjaye na zuciyata ya aminta da maganar Jiji.

"Sa'eed ya koma Minna" da zancen danake kwana nake tashi kenan. Sa'eed ɗina ya saɓa alkawari, Sa'eed ɗina ya zama rago kuma matsoraci, Sa'eed ɗina ya zama butulu maciyin amana. Sa'eed ya yaudari soyayya ta, ya munafurci yardar da na ma sa.

Kwana biyu na yi jinya a ɗaki na warware, ban san ya akayi na saki raina ba da maganar biki da kuma maganar komawar Sa'eed Minna. Na sani chan ƙasar raina akwai soyayyar Sa'eed wadda ta ke ta gaskiya babu algus aciki amma kuma a fili na ka sa nuna ƙin auren dole da za amin. Cikin 'yan kwanaki 'yan uwan Amma na Niger da 'yan uwan Baba da su ke lungu da saƙo na duniya su ka fara cika gidan.
Duk wani abubuwan al'ada an min, ban nuna damuwa ko rashin son auren kamar yadda na ke yi a da ba na saki raina ina shiga ana hidima da ni kamar kowacce amarya da za a mata auren so. A zahiri ne ake ganin wannan Aaliyar amma a cikin zuciyata na sani Aaliyah ta Sa'eed ce...

Biki da buduri aka yi na sati guda, naira da dala sun yi kuka a wannan hidima. Nigeria da duniya sun shaida an ɗaura auren *Aaliyah Badamasi Bulama* da *Ahmad Ibrahim Wamako*

Kafin ranan da za a kaini an riga an wuce da tirelolin da su ke ɗauke da kayana. Kayayyaki da aka haɗo daga sassa na duniya baki ɗaya. Yadda ake gulman kayana kace akaina Baba ya fara aurar da ɗiyar sa mace. 'Yan ubanni da wasu cikin 'yan uwa sun nuna baƙin cikin su ƙarara gameda dukiya da Baba ya narka mini. Sanah ce kawai ba ta damu da komai ba ta ma fi nuna damuwa da yadda na kwantar da kai aka yi hidiman biki na bayan ta san irin tsananin son da na ke yiwa Sa'eed. Ranan da za akai ni ta ke cewa "Aaliyah ina zargin Amma da Hajia Badariyya, akwai abinda na tsinkayi suna faɗa amma ban tabbatar ba saboda ban gama ji ba"
Da na tambayi me ta ji sai ta ke ce min wai ta ji Hajia Badariyya wacce ta ke babbar ƙawar Amma tana faɗawa Amma akan akwai inda za ta je a rufe bakina na amince da auren da za a min. Ni kam dariya kawai na yi dan koma mi Amma da Hajia Badariyya su ka kitsa aikin gama ya gama domin an riga an ɗaura aurena.
Ba nasihar da Amma ta min lokacin da aka kaini sallama wajen ta illa addu'a da kuka da ta dinga yi. Ni kam na riga na gama nawa koke-koken tun kafin ranan, dan haka ko ɗigon hawaye bai sauko min ba. Daga wajen ta sai wajen Baba wanda ya min wata guntuwar nasihar munafurci, wai na ji tsoron Allah na yiwa mijina biyayya. Har shi zai min maganar tsoron Allah bayan shi bai ji tsoron Allah ya haɗa ni da wanda na ke so ba. Ya gama addu'an da zai yi aka ɗauke ni sai wajen motocin da ke jirana za su raka ni airport...


A cikin Sokoto zamu zauna, a danƙarren gidan da aka ce Alhaji Wamako ya ginawa babban ɗan sa da ya ke matuƙar so, dan haka Sokoto mu ka nufa, sai dai saboda

Please Login or Register in order to submit comment