You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aminai sosai suka daɗe kafin su yi goodnight..



Haka ta rinƙa kiran ƴan gidan su suna gaisawa kamar ba gobe sai goma na dare ta fito ta tarar da zulfa'u
tana ta jiran ta dan tana so ta tafi turakar mai gari tana jiran ta zo ta rufe ƙofar ɗakin



"Kaii likiciya kin daɗe kamar baki da ranar fitowa toh ni dai zo ki rufe ƙofar zan tafi sai da safe"

Dariya maganar ta ta bawa Bilkisu ta ce
"Toh amaryar mai gari Allah ya tashe mu lafiya"ta raka ta ta tafi ita kuma ta dawo ta rufe ƙofar ta
chanza zuwa kayan barcin ta ta haye gadon ta kunna laptop ɗin ta da tun da suka zo bata taɓa bi ta kai
ba shiga fannin movies ta yi ta yi playing wani nollywood movie mai suna If i were the president tsantsar
siyasanci da ha'incin gwamnati ne a ciki ta yi nisa a kallon ta ji ana buga ƙofar ɗakin da mamaki ta diro
tana ƙoƙarin saka falmarar rigar ta ta ce

"Wa nene"?

Aka amsa mata cikin haɗa baki

"Likita mu ne"da mamaki ta ce

"Ku?ku su wa"?

A karo na biyu suka kuma ce mata

"Su hindatu ne likita"a nan ta gano su wato matan mai gari ne hindatu ita ce uwar gidan sai halima sai
karime.

Buɗe masu ƙofar ta yi suka shigo suna leƙe leƙe kamar marasa gaskiya.

"Ku zauna mana"suka zazzauna a kujerar falon ita ma ta zauna sai suka rasa ta ina zasu fara ita ce dai ta
yi initiating maganar ta hamyar cewa



"kun yi shiru da fatan dai komai lafiya babu wata matsala"?

Suka shiga girgiza mata kai kafin hindatu ta ƙoƙarta ta ce



"Likiita dama wata magana ce mai muhimmanci muka zo da ita wadda muka ga zai fi mana sirri in zulfa'u
bata nan dan yarinyar nan akwai karaɗi da iyayi".



Oh ikon Allah mutanin nan ba shiryuwa zasu yi ba kishi har a gaban baƙo.

"Toh ina jin ki maman usee me kuke son in maku"?ta tambaye su tana son maintaining eye contact da
su dan ta nuna masu cewa tana tare da su kuma maganae tasu na da muhimmanci a gare ta.

Cikin sakin jiki hindatu ta ce

"Likita wannan karatun ta arabi,shi muke son a rinƙa koya mana in an gama koyawa yaran mu amma a
ɗaki na zaki rinƙa koya mana ta yadda wannan ƴar ba zata sani ba dan Allah ki taimaka mana"matuƙa ta
ji mamaki dan haka ta ce
"Toh maman usee me ya sa ba za ku so zulfa'u ta sani ba kamar abu marar kyau"?

Numfasawa hindatu ta yi kafin ta ce

"Ƴar nan kin ga dai tun zuwar wannan yarinya ta rinƙa ƙoƙarin tursasa mana akan addinin mu muka ƙi
yanzu da kika zo muka ga tsarin ki sai muka ji ran mu ya biya har ma muka yanke hukuncin tunkarar ki
dan ki fara koyar da mu tunda hasken rayuwa ya biyo mu har gida kuma da kunya a ce kina koya mana
yarinyar nan tana gani ai sai ta raina mu". Ta ida tana ɗan chanza mood ɗin ta abin ya ɗaurewa baby
doctor kai wai dama haka jama'a ke yawo da duhun kai?lallai tafiya mabuɗin ilimi duk dan kishin da bai
kai ya kawo ba.



"Hmm maman usee kin ga ni dai shawara ɗaya zan baku in fah kun ji nawa,tunda dai baku ji kunyar zuwa
neman ilimi ba bana jin ya kamata ku ji kunyar ƴar uwar zaman ku duba da cewa gida ɗaya kuke ko mu
jima ko mu daɗe wataran zata sani kuma kunyar da zaku kwasa sai ya fi ta wadda in kuka bari ta san da
fara koyon addinin ku tun yanzu in kun ji nawa kawai ku basar ai ba'a girma a neman ilimi"daga nan ta yi
shiru dan jiran jin opinion ɗin su.



Ɗan shiru suka yi suka rahe murya suna ƙusƙus kafin daga bisani ita mouthpiece ɗin su ta magantu



"Toh likita mun ji shawarar ki amma ki mana alfarma ɗaya"ta kalle su ta ce

"Ina ji".

"Yauwwa so muke ki banu daga yanzu zuwa gobe iwar haka zamu sanar da ke shawarar da muka
yanke".



Jinjina masu kai ta yi suka miƙe suka mata sai da safe sannan suka tafi,dawowa ciki ta yi tana mamakin
wai ita da ta zo health outreach kuma ta ɓige da karantar da ahalin gidan mai gari karatun addini har ma
da na bokon da zasu fara,

"Ikon Allah komai na da sanadi"ta ce da kanta tana mai kwantawa a kan gadon,ƙarasa kallon ta yi sannan
ta kwanta barci.



************
First week ɗin su went successful da orientation phase ɗin kuma they were able to picture out
matsalolin yankin wanda mafi akasari wife/husband battery,domestic violence kuma akan mace ne da
ƴaƴan ta wato ƙuntatawa abokin zama wanda a nan garin matan aka fi ƙuntatawan da ƴaƴan su kuma ta
lura akwai matsalolin mata da ya shafi jikin su sosai wanda har yayi affecting mata da dayawa ciki kuwa
har da wata marar lura da damuwa da kanta ta ke faɗawa baby doctor cewa in ta zaga bayangida wasu
lolutan ta kan ga kamar mahaifar ta ya tulluƙo amma wasu lokutan bata gani sai kawai ta saka hakan a
matsayin haihuwar da ta yi ne watanni shida da suka wuce a nata tunanin ai zai tafi bayan watanni
takwas ta ƙi zuwa asibiti bare a duba ta toh wannan issue ɗin duk ya fi damin baby doctor dan haka ta
sanar da Dr Zaid ya ce da ita dole asibiti zasu tafi kafin a duba a ga degree ɗin annular detachment of the
uterus ɗin in wanda za'a iya replacing ne sai a yi in kuma wanda sai dai a yi surgery ne sai su sanar da
family ɗin ta su yi.



A fannin su hindatu uwargidan su zulfa'u bayan kwanaki biyu na ɓuya da nunnuƙe sun yi finalising zasu
na zuwa tare da ƴaƴan na su ana koya masu tare wanda da fari dariya zulfa'u ta masu sai da baby doctor
ta nuna mata rashin dacewar hakan sannan ta daina,

Ƴaƴa kam ana samin ƙaruwar su dan har ƴaƴan makota da ke zuwa koyon kararun basu ƙirguwa yayin
da baby doctor ta zama tamkar tauraruwa a ƙauyen _koma_ kamar su bauta mata ga ta dai very smallish
amma akwai ilimi da fasaha,ganin haka ya sa Dr Zaid yanke hukuncin zuwa tare da ita gidan su Asma'u
dan su shawo kan ta ta amince da karatun da za'a na koya mata.



Tun ranar da suka rabu baram baram basu kuma yin hirar arziƙi ba sai dai abin da ya shafi aikin su da shi
ya kawo su garin dama takan yi mamakin sa na rashin son aiki son jiki ya mai yawa dan ko a wun
outreach ɗin ita ke major work ɗin baya son yi kwata kwata bata san cewa aikin shi bane wato punishing
ɗin ta a garin ko zata rage girman kan tsiyar da ke ɗawainiya da ita shi kuma bai san kan sa yake cuta ba
dan ita kam tsakani da Allah ta ke aikin ta babu gajiya ko rangaji a tattare da ita sai ma ta daɗa daraja da
ƙima a idon jama'an ƙauyen dan kaɗan ya rage su fara worshiping ɗin ta saboda ire iren kayayyakin da
suke kai mata wasu kaji wasu namar dabbobin su wasu fresh milk wasu girki suke yi na musamman su
kawo mata duk wannan budirin a idon Dr Zaid ake yin shi ta tafasa sauke bata taɓa ce da shi ba haka
take enjoying goodies ɗin ta ita da ƴan gidan..



*********

_Friday evening_

_4:00pm_
Cikin shigar atamfa hollandaise ɗinkin riga da skirt 8 pieces da ɗaurin Aisha Alhassan wato wanda ake
turo shi gaba inkiyar ture ka ga tsiya,da mayafin ta na mutunci haɗe da takalmin spline mai ɗan tudu riƙe
da wayar ta a hannu ta fito ƙofar gidan inda ta same shi cikin shigar kaftan lilac colour da hular sa ƙafar
sa samye da normal skin takalmi yayi kyau ainun dan abin da ya daɗa fiddo da shi shine baƙar speck ɗin
da ya saka sai ya haɗe da jikin sa yayi ras gwanin sha'awa



She must say that he looks handsome in his cultural attire dan haka tana tafe ta bashi unexpected pic
wanda ya bala'in yin kyau a hoton amma on reaching to him sai ta ɗan haɗe rai irin kar ya rainata ɗin
nan.

"MashaAllah"ya furtawa kan sa da yayi tozali da ita amma shima ganin ta ɗaure sai ya mazge haka suka
kama hanya tinƙis tinƙis sai gidan su Asma'u ma'ullen Mudan.



A ƙofar gidan su suka tsaya ya aika yaro da a masu iso babu jimawa aka basu damar shiga



Tarbo mai kyau aka masu kasancewar shi ɗin ɗan gida ne sai aka karrama su sosai ko da yayi tambayar
Asma'u rasa abin cewa mahaifiyar ta tayi dan tun wuraren ƙarfe uku da rabi rabon ta da ita sai ta buɗe
baki zata kauce amma sai suka ji bambamin masifar ta



"Wallahi wallahi bilahilazimin ba za'a ci bulus da ni ba ni Asma'u ma'ullen Mudan sai sun san sun ɗebo
ruwar tafasa kan su tabɗijam bala'i"......



Kasa kunne suka yi suna sauraron ta sau gashi ta bankaɗo labulen zauren gidan na su ai ko ta ci karo da
su Dr Zaid tana ganin su ta antaya a guje wai ta ji kunyar ɗaga muryar da ta yi a gaban su,miƙewa yayi
yana kwaɗa mata kira tana cewa

"Ɗan birni bani sake haɗa ido da kai sai nan da sati guda tabb da ni za'a yi abin kunya inaa".. Sai rafka
gudu take ai ko daidai wani dandamalin kwata ta antaya ciki bata lura ba............



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

#vote

#comment
*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



_i love u all dan kuma kuna so na wato masoya na a duk inda kuje ku san cewa ni siyama ibrahIm ina son
ku_

*7*
"Asma'u ki dakata mana kin ga abin da kika janyowa kan ki ko a kan wani silly reason"yana maganar ne
yayin da yake ƙoƙarin matso ta ai ko ta tsala wata ihu mai razanarwa wanda yayi sanadiyar firfitowar
jama'a har da su baby doctor da je zaune cikin gidan su Asma'u tana mamakin rashin hankali irin na ta..



Taruwa sosai aka yi a wurin ga shi dai ana son yin dariya amma kowa na tsoro dan kana darawa ta san
fuskar ka anjima Mudan na zuwa zai keta maka rashin ɗa'a dan haka kowa gimtse dariyar sa yake yi bugu
da ƙari ga bokan turai a wurin sai suka rinƙa mamakin abin da ya haɗa shi da ita amma suka yi gum suka
bar wa kan su suka tsaya kallon ikon Allah.



Dr Bilkisu da fitowar ta kenan tayi arba da aika aikan da Asma'u ta ma kanta ga Dr Zaid a tsaye a kan ta
ga jama'a duk ita ake kallo ai bata san lokacin da ta kece da dariyar da bata san dalilin zuwan sa a dai dai
lokacin ba sai yi take yi har da ƙwalla.

Mahaifiyar Asma'u da ke gefe tana tir da halin ɗiyar ta ta dan irin kunyar da ta ji baya misaltuwa shiru
ta yi tana kallon Asma'un yayin da Dr Bilkisu ke ta dariya babu ji babu gani dan haka cikin mugun ɓacin
rai da fusata ya daka mata tsawa cikin turanci dan kar a san me yake nufi ya ce



"For crying out loud Bilkisu will you stop laughing some one is here crying for her life and you are
standing there laughing don't you have human sympathy"? Ya ƙarasa yana mai daka mata tsawa kamar
ɗiyar gaban shi.



Sai a sannan ta ankare da ɓaranɓaramar da ta yi sai ta ji babu daɗi ko ba komai mahaifiyar yarinyar na
wurin kuma ba zata ji daɗi ba dan haka sai ta gimtse dariyar ta ta matsa kusa da su daidai kan Asma'u ta
miƙe mata hannu sai dai atafau Asma'u ta ƙi miƙa mata nata hannun wai ita sai dai ɗan birni ya bar
wurin shi kuma tsoron matsawa yake gudun kar baby doctor ta wuntsila ta cikin kwatan bayan ta ɗago
ta since he knew that ba su cikin good terms.

Ganin bata da niyar miƙo hannun sai baby doctor ta gane cewa kunyar jama'a take ji ciki kuwa har da
shi saurayin ma'ullen Mudan ɗin wato Dr Zaid sai ta juya ta ce da shi

"Please she needs privacy"!! A ɗage ya kaklle ta dan ya san ba tsakani da Allah zata taimake ta ba sai ya
girgiza kai alamun ba zai matsa ba.



"Are you for real?huh?don't you see that your saviour is sinking in this dirty pit"?kallon ta yayi yana son
sanin shin tsakani da Allah ta ke son taimakon Asma'un ko dai ganin ido ne sai dai bai hango komai ba
dan bata bashi wannan space ɗin ba so he have no any other option but to give them space...
Yana ba da baya Asma'u ta miƙa hannun ta da taimakon baby doctor ta fito daga cikin kwatar duk kayan
ta ya ɓaci dan har ƙuƙurjewa ta yi a hannun ta haka ta fito fuskar nan tam cike da bala'i ta hankaɗa masu
kallon banza ta ce



"Munafukai algungumai annamimai toh ƙwalelen ku ban mutu ba kuma ban kasara ba ku jira ni anjima
sai mun zo dukkan ku zaku gane munafurci bai maku rana ba".. Ta ida tana ɓalla masu harara kamar zata
zazzago manyan idanun ta haka dai ta lallaɓa suka koma cikin gidan su yayin da su Dr Zaid da mahaifiyar
ta suka biyo su a baya bayan ƴar tazarar da suka ma juna dan ce mai tayi ya juya zuwa direction ɗin da
aka fiddo ta har su shige ciki kafin ya biyo su hakan ya yi.



Da zuwan su direct cikin ɗakin su ta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikin ta dan haka Bilkisu bata bi bayan ta
ba ta zauna a tabarmar tana mamakin halin Asma'u ga shi dai a zahiri tsayayyiyar yarinya ce mai kyau
amma abaɗini babu halin kirki a ce an fiddo ki daga kwata amma babu kunya kika tsaya fetsa rashin
mutunci Allah ya kyauta.



Bayan kamar mintuna goma suna zaune ana ta hira tsakanin Dr Zaid da mahaifiyar Asma'u ita dai nata
ido sai complains ta ke ta mai a kan Asma'un a nan ta ke sanar da shi abin da ke gudana tsakanin ta da
Mudan toh a nan baby doctor ta daɗa kashe kunne dan jin ta bakin mahaifiyar Asma'un ai ko ta sami
labarai da kyau har ta tabbbatar cewa eh lallai Asma'u akwai hankali da wayo duk rashin jin na ta akwai
mutuncin ta tare da ita dan dama wai shi Mudan ɗin ya daɗe yana maganar a kawo kuɗin aure amma
yayyen ta sun ƙi kuma duk iskancin su shi kan sa baya taɓa ta dan yana riƙe mata gyale sai sun yi sati
biyu basu haɗu ba ta ɗau gaba da shi kenan kuma kaf gidan su sai sun san Mudan ya taɓa mata gyale
kuma ta shaida cewa sai ta ɗau sati biyu kafin su shirya sai dai a ji ta kawai dan ta saba ire iren
maganganun but her momma is very conscious of her act a kuum in zata dawo gidan cikin dare sai ta
mata full inspection ta duba jikin ta sosai sannan take samin kwanciyar hankali.



Shiru Dr Zaid Maher yayi dama shi son maso wani yake yi bai sani ba ashe saurayi gare ta bai sani ba?
toh shi yaya zai yi da son ta da yake ji da shi?inaa dole ma kawai shi Mudan ɗin ya yafe mai Asma'u dan
da shi ta dace ba Mudan ba da me Mudan ɗin zai raine ta?da talauci ko jahilci?no way he have to stop
their relationship..



Ganin ya shiga state of shock sai baby doctor ta ɗan gyara murya ta ce da mahaifiyar Asma'un
"Uhmm mama dama wata shawara muka zo da ita wacce in har zaki bamu haɗin kai toh mun miki
alƙawarin taimakon Asma'u kuma mu raba ta da shi wannan Mudan ɗin da ba kya so har abada muddin
ta hau kan abin da muke son ɗora ta akai toh ba za ta kuma yarda da Mudan ɗin nan ba da fatan za ki
mana kyakyawar fahimta mama"?jin maganganun ta cikin hikima sai ya sa mahaifiyar Asma'u amincewa
da abin da suka zo da shi har da ma dai bata ji ba but ta sami relief at least ɗiyar ta za ta rabu da wannan
gallababben yaro sai ta ce



"Ƴa ta ina jin ki menene kike son ɗora Asma'un a kai"daɗi sosai baby doctor ta ji dan haka sai ta ce

"Kin ga akwai karatun da na ke koyarwa a chan gidan mai gari karatun biyu ne na addini da na zamani
kuma duk yaran gidan har da na makwaftan gidan na halartar karatun kuma har yanzu ana kan taruwa a
gidan sai na ke ga in har Asma'u za ta na zuwa wannan karatun toh lallai ba zata na samin lokacin
sauraran Mudan ba tunda za ta rinƙa bitar karatun ta haka zata so ta sami kyautar da za'a na ba ta
kullum kenan wannan karatun zai ɗauke mata hankali tunda kin ga yau da gobe sai Allah tun ana
kiyayewa wataran Allah ya kare wani mummunar abin na iya faruwa tsakanin su kuma ba dole ne ta faɗa
ba kin ga tun da an gano abin sai a fara kare shi daga faruwa ko ba haka ba mama"?jijina kai ta yi cikin
gamsuwa ko ba komai ƴar ta zata sami ingantacciyar rayuwa ko da kaɗan ne dan haka ta ce



"Na yarda ƴa ta shawarar ki ya ba da ma'ana sosai kuma na yarda da shi ko ta amince ko bata amince ba
dole in nuna mata iko na na uwar da ta haife ta"daɗi na ya kama Bilkisu dan ita ma yanzu ta fara
tausayawa Asma'u duba da yadda take taka tsantsan da rayuwar ta ba dan wauwtar da ta mata yawa ba
toh lallai in an natsar da ita zata yi hankali nan abin ne ya mata yawa ga jahilci ga zaman ƙauye babu
wayewar kai ga taɓara babu kwaɓo but apart from that yarinyar zata shigo da kyau dan tana da wayo



"Shikenan mama na ji daɗi kuma zan fi jin daɗi in Asma'u ta amince wanda na san shi kan sa Dr zai yi
farincikin haka ko ba haka ba ne Dr Zaid"? Ta ida tana juyawa gare shi sai ta ga kamar baya tare da su tun
da suka fara maganar jin su kawai yake ba wai dan yana fahimtar su ba dan haka ta daɗa ɗaga murya ta
ce



"Right"? a firgice ya ce



"Ye...ee...sss yeeee.... sss"sai ya kuma cewa

"Yes yes"abin sai ya bata mamaki toh dama ina hankalin shi ya tafi tana nan tana mai yaƙin sanyin
idaniyar sa shi kuma yana wani tunanin dan haka ta ce da shi
"Are you okey"?saurin girgiza mata kai yayi kafin ya miƙe tsaye ya ce da ita



"Let's get going is getting late"da mamaki ta tashi tsaye ta ce da shi

"Me kuma ya faru ba mu fah gama abin da ya kawo mu ɗin ba kuma kake cewa mu tafi"!!!

"I said let's go"ya ida cikin nuna halin ya fara gajiya da conversation ɗin.

Ƙala ba ta ce da shi ba ta ce da mahaifiyar Asma'u



"Toh mama za mu tafi zuwa goben ma ta na iya fara zuwa karatun in ya so shi likitan sai ya rinƙa rako ta
gida ba ki da matsala da wannan"murmushin gamsuwa ta yi kafin ta ce

"Nagode Allah ya maku albarka ya kare mana ku wannan irin ƙoƙari da kuka min kuka mana a wannan
ƙauye na mi Allah ne kaɗai zai baku lada shi kaɗai zai biya ku"ɗan taƙaitaccen murmushi baby doctor ta
yi ta ce

"Mun gode mama bara mu tafi dare na yi"



"Toh Allah ya kuyaye hanya ga shi nan ta ƙi fitowa tabbatacciyan wai kunya take ji"ɗan darawa ta yi ta
ce

"Hmm mama bara mu tafi"daga haka suka yi sallama shi dai bai ce komai ba har suka yi nisa kafin baby
doctor ta dakata ta ce

"Wait"sai shima ya tsaya ya kalle ta bai ce komai ba



gyara tsayuwa ta yi ta fuskance shi ta ce

"Wai tunanin abin da aka sanar da kai kake yi"?shiru yayi bai ce komai ba sai ta ce



"Toh ai ba abin mamaki ba ne dan ka ji cewa ta na da saurayi you shouldn't be surprise"ta cigaba da
tafiyar ta sai ya ce da ita cikin sanyin murya



"Dama kin san da labarin ne"?dakatawa ta yi tana jin wani iri kafin ta ce
"Yes i know"!!sai ya ji mamaki kafin ya ce

"Tun yaushe"?kasa bashi amsa ta yi dan ya fara bata tausayi dan kuwa ya zurma a son yarinyar da yawa
though is something else not pure love but kamar yana wahala..



"tun ranar da na fara ganin ta a wurin outreach ɗin nan"!! daga haka ta yi shiru tana sauraron sa sai dai
bai ce komai ba ya cigaba da tafiya itama bin sa ta yi a bayan...



*******************



Bayan dawowar su gida sun yi abin da ta dace na yau da kullum wato koyar da karatun da take ma yaran
da iyayen su ta basu assignment ɗin su as usual ta kwanta saman ɗaya kujerar falon yayin da zulfa'u ke
zaune a ƙasa tana gyara zogale na dambun da take son yi washegari da rana kasancewar ita ce da girki
jifa jifa suna hira

Lokaci zuwa lokaci takan tuna scenario ɗin ɗazu sai ta yi dariya ita kaɗai countless time zulfa'u na
tambayar ta amma sai ta ce babu komai karshe dai shiga toilet ɗin zulfa'u ta yi ta danna wa Bahajjatu
kira ringing biyu ta ɗaga.



"Assalamu alaikum baƙin ƙauyen koma"dariya suka saka kafin ta amsa da

"Wa'alaikumul salam matar mu". Dariyar suka ƙara sakawa dan duk lokacin da zata yi shu'umancin ta
toh da shirme suka fara gaisuwar.



"Halan me ya faru ne na ga har goman dare ta yi amma kika danna min kira"

"Ke dai bari wata labari na kawo maki"gyara kwanciya Bahajjatu ta yi ta ce



"Haba da gaske?toh faɗa min ina jin ki"sai da baby doctor ta dara kafin ta ce

"Halan Baha wai wacece budurwar yayan ki"? Da mamaki ta ce

"Budurwar yaya na?wanne a ciki"?

Cikin gatse ta ce

"Bilal"! Doguwar tsaƙi Baha ta ja ta ce
"Ban son wulaƙancin Beelove wani yayan na wa kike nufi"?

Itama tsaƙin ta yi ta ce



"Toh shikenan in kin shirya jin ko wanene sai ki kira ni"cikin hanzari ta dakatar da ita ta ce




"Tsaya tsaya tsaya,kaii Beelove wai menene na wani ɗaukar zafi?babban yaya kike nufi"? Scoff ta yi ta ce



"Toh in ba shi ba dama tare da wa nake"?

"Goodness toh yi haƙuri,babban yaya ai bai da budurwa sai ko in a chan ya samo mana new sister in-
law".

Abin dariya sosai ya ba ma Bilkisu sai ta ce



"Ai ko ya samo maku sabuwar sister in-law apple"ta ida tana me kecewa da dariya

Shiru Bahajjatu ta yi kafin ta ce



"Jokes apart Beelove da gaske yaya ya samo budurwa"?



"Hmm Baha kenan na taɓa kawo maki hirar wannan izgilallen yayan na ki in ban da yau"?

Ta ce"a'a".



"Toh wallahi am serious ya samo wata yarinya kyakyawa mai kyawun kallo sai dai ba natsuwa"!



Miƙewa ta yi daga kan gadon ta diro ƙasa ta ce

"Mene?budurwa a ƙauyen nan?impossible"?
"Hmm Baha kenan wallahi da gaske na ke"a nan ta kwashe duk abin da ya ke ta faruwa tun zuwan su
har ma da tarihin yarinyar ta sanar da ita me Baha zata yi in banda Allah ya raba mana jaha,sai nanata
shi take yi kamar ba za ta daina ba



"Allah ya tsare uhuhm shi kuma yaya haka ya ke son tozarta mu ya daɗe bai yi aure ba sannan ya ce
wannan zai ɗauko?toh ba gidan Dr Maher ba sai dai a chan ƙauyen"?



"Ha'an toh what if in Allah yayi matar sa ce fah?what can you do"? Da sauri ta ce da ita

"Tofar da yawu tun kafin abin ya zama gaske"suka dara kafin daga bisani ta sallame ta ta kira umman ta
a waya.

Ba ta ɗauka ba sai ta kashe sannan ta kuma kiran ta



"Assalamu alaikum umma"

"Wa'alaikumul salam baby ya kike ya garin"?

"Lafiya ƙalau umma ya na ku"? Sai ta yi shiru alamun tana jin nauyin ta sai ta ɗan yi murmushi kafin ta
ce



"Common umma am serious ya London ɗin"? A nan ta sani relieve sai ta ce

"Lafiya lau baby ungo ku gaisa da Ammin ku"ta miƙawa Hajiya Madina wayar cikin raha ta ce

"Baƙin Yola ya kuke"?itama da fara'a ta ce



"Lafiya ƙalau Ammi"

"Ina my boy ya ke ban ji kun kira tare ba"

"Ammi yana ɗakin shi maybe yayi barci nima barcin zan yi"



"Noo i need to

Please Login or Register in order to submit comment