You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fitowa fili dan
kar ta tashe sa ya farka ya ga tana kuka..

A hankali kamar mai jin tsoro ta shiga yaye mai blanket ɗin idon ta kyar a kan innocent gentile face ɗin
sa da ke nan so calm and good looking.

A hankali ta kai hanun ta dake shaking kan fuskar sa,,hannun ta na kaiwa kan fuskar sa ta lumshe
idanun ta sai ga hawaye na silalo mata dan ba komai take tunani ba illah kanta da take tausayawa dan
Zaid....bata gabar sa ita ta sani taimakon ta ɗaya ne Allah bai bashi izinin tambayar ta Asma'u ba dan ta
san da zarar ya san halin da take ciki shikenan tata ta ƙare sai dai ta haƙura dan ita ta ɗorawa kanta
lalurar da ta san ba zai kawo mata hanya mai ɓillewa ba..

Har bakwai saura tana kallon sa tana hawayen tausayin kanta haka shima tausayi yake bata dan ta san
in har ya gano Asma'u ta taimakawa Mudan har yayi achieving kai su ƙasa toh zai zama so shattered
kuma he will be heart broken ko zai iya ɗaukar wannan abin?Allah ne masani..

Share hawayen tayi a karo marar adadi sannan ta yi calming kanta ta ja iska sannan ta furzar kusan sau
uku tana breathing exercise kafin ta mai wani kallo wanda ke tafe da tsantsar tsananin so mai zafi zafi
dan hucin son na kan huro mata yana huro mata zafin sa wanda ke ratsa jikin ta har ya fara melting mata
jinin jikin ta.
Ita wannan ne kuma ƙaddarar ta a rayuwa ya zata yi da irin zazzafar son sa da ya shige ta ya ɓula ƙowani
gaɓa a jikin ta??jan hanci tayi sannan ta hau kiran sunan sa tana yi tana gyara muryar ta dan ya fara rawa
kuka ke son kwace mata but she didn't allow it..



Sau biyu tayi tapping nasa sannan ya juyo da corny looking face nasa ya sauke kan nata already falon is
spread with light sai hasken ya so tona asirin halin da take ciki but ganin zai gane sai ta sunkuyar da
kanta ƙasa sam ta manta banu kaya a jikin ta sai rigar wanka.

Shiru shiru ta ji bai ce komai ba haka bai yi attempting tashi ko moving ba sai tayi zaton ko baccin ne bai
ishe sa ba ya koma dan haka ta ɗago dan kuma tada shi sai dai abin mamakin shine tangaras ta gan sa a
kwance ya kafe ta da idon sa yana mata kallon ƙurilla sai ta rasa abin faɗa dan haka ta bi inda yake kallon
da ido sai ta ga ƙirjin ta ya kafe da ido ɗan buɗaɗɗen wurin da yayi exposing ƙirjin ta sakamakon rashin
haɗewar rigar wu guda saboda kamar falmarar riga yake haɗawa ake yi a ɗaure toh nan space ɗin yake
kallo kamar his life is laid on it sai dai the most surprising and amazing things is that she didnt react,bata
yi wani silly reaction ko response ba illah maida idon ta kan sa da tayi tana mai cewa

"Lokacin sallah ne yayi ka tashi kar ka makara"a yanayin maganar ta one can see the misery she is in
presently ga alamun karaya daga muryar ta.

Kallon ta ya shiga yi cikun ɗaurewar kai yana mamakin rashin responding ko reacting ma kallon da ya
mata.

Tashi yayi daga kwancen ya ɗan zauna haɗe da haɗa hannayen sa biyu yayi cupping fuskar sa yayi
zugum kafin daga baya kuma ya tashi yana mai ce da ita

"Thanks"ta mai murmushi haɗe da saukar da idon ta ƙasa dan bata son haɗa ido da shi kallon sa kaɗai na
increasing venom da je yawo a jikin ta wanda ya sami kafar shiga ne sakamakon son sa da yayi poising
ɗin ta because his love at this moment have no difference with a poison dan ya shige ta ba a lokacin da
ta shirya ba ba da sanin ta ba ya shige ta so she consider his love as a poisoning element that convert
and react to her chemical electrodes that moves and perform their functions by each passing second
and she have no justification to this love she have for him indeed this is *the love saga....*



Tana kallon sa yayi shigewar sa ita kuma ta zauna a wurin tana tausayawa rayuwar ta ko ya zata
kasance in har ta gama tabbatarwa da ita kaɗai ke shawagi cikin son sa amma ban da shi..

Da yake tana fashin sallah ɗazu da ta shiga wanka ta ga ta fara staining pant ɗin ta sai ta gane monthly
period nata ne ya zo hakan ne ma ya sakata zama ba tare da ta saka kaya ba dan ko ta saka ɓaci zasu yi
kuma wahala take sha ba lallai bane ta iya wanke su ko a gidan Umman ta ke mata wankin in ta fara but
now she is married kuma ba so take Zaid ya san halin da take ciki ba because they are still different basu
zama abu ɗaya ba..
Tashi tayi ta nufi table da landlune ke ajiye,so take tayi making order na dinner ɗin su,har ta kai hannu
ta ɗauka sai ta ga ya leƙo daga shi sai towel da yayi tying around his waist jikin sa jiƙe da ruwa ga kumfa
nan a wasu sassan jikin sa kamar ya sani har ya fara soaping kansa sai ya fito dan bai so su ci abincin
hotel ɗin he wanna give her a special treatment for taking care of him.

"Don't bother calling,a waje zamu ci abincin dare humm"!!ya ida yana mai assuring nata da idanun sa sai
ta ɗan murmusa sannan ta mayar da wayar ta ajiye shi kuma ya koma ciki dan ƙarasa wankan sa..



Zama tayi duk jikin ta ya saki ga matsalar menstrual cramps ga damuwar abin da tayi discovering just a
while ago,shiru tayi ta daɗe a hakan sannan daga bisani ta tashi ta shige nata ɗakin tayi freshening kanta
haɗe da saka kaya ta ɗan yi kwalliya kaɗan ta dawo falon ta zauna tana jiran sa.

Abin na ɗaure mata kai wai dama haka shi _*so*_ yake ko dai tata ne ta zo mata da wannan sigar?
tukunna ma ita kaɗai ke wannan abin da ita kaɗai ke jin wannan abin game da shi but him...,baya jin
wannan abin towards her abin da yake ji ya zama mallakin Asma'u..

Wuf ta tashi ta tsaya hankalin ta tashe dan har zazzaɓi take ji kamar zata yi hauka wannan abin ya
shammace ta haka ya yaudare ta ta ya ma za'a yi zuciyar ta ta kamu da matsanancin son Zaid a lokacin
da bai dace a lokacin da shi bai yi realising ya gane ainihin taste ɗin sa ba,in aka bar shi da yarinyar nan
da tayi silar faɗawar sa halaka yake son cigaba da rayuwar sa har ƙarshe..



Tana tsaka da tunanin mafita sai ta ji sound ɗin takalmin sa ta bayan ta sai ta juya ta kalle sa,,for the
very first time ta mai kallon so kallon da bata taɓa mai ba kallon da ke ɗauke da abubuwa daban daban
kama daga zazzafar son sa,tausayin sa,sadaukarwar da zata iya yi akan sa at any cost,baza ta iya rasa sa
ba haka zalika ba zata iya haƙura da shi ba ko da kuwa me za'a bata..



Twinkling fingers nasa yayi a daidai saitin idon ta wanda hakan ya saka ta lumshe idanun ta sannan ta
buɗe su tarr a kan nasa fuskar straight to his charismatic eyes da ya kafe ta da su,jin wani irin son sa take
a cikin jikin ta chan ciki cikin jikin ta dama ba lafiya ne da ita ba sai abin ya haɗe mata bibbiyu tuni ta ji
sanyi na shigar ta silently sai ta hau karkarwa da rawar ɗari wanda ya fallasa har ya saka Zaid gano hakan
da idon sa sai shima ya shiga ruɗu a ruɗen yayi saurin kawo mata agajin gaggawa dan shima ganin
yanayin ta ya saka sa cikin duhu ko dai bata jin daɗi ne sai dai bai kai ga samin amsar tambayar sa ba ya
ga amsar a gaban sa.

Rungumo ta yayi sosai dan gabaɗaya jikin ta ya saki kamar bata da laka,ya tsorata ba kaɗan ba dama
bai da masaniya akan rashin lafiyar da tayi a lokacin da yake nasa rashin lafiyar dan haka bai san bata
gama jin sauƙi sosai ba ya ɗauka kawai sudden collapse ne.
Saurin kwantar da ita yayi saman 3 seaters leather chair ɗin falon idanun ta lumshe ta fara losing
consciousness nata cikin ruɗewa ya shiga kiran sunan ta yana jijjuga ta in yayi ya hau tapping kumatun ta
duk ya ma ras abin yi yanzu yanzu ana zaune ƙalau me ke damin ta ne

"Bilkisu...Bilkisu..wake up,,,ki tashi me ke damin ki..common wake up you were fit and sound just some
seconds ago what happened....tashi mana Bilkisu stop all these kin san bana son ire iren waɗannan
puzzles ɗin ko...wake up"..



A haka fah ya share mintuna yana girgiza ta ya manta da wani abu wai first aid treatment bare ya ɗauko
ruwa ya yayyafa mata lallai wannan shine rule da ke magana akan ma'aikatan asibiti akan *"you should
"NOT" treat your family member"* saboda a duk lokacin da ma'aikacin asibiti zai kawowa family
member na sa agaji in yana cikin wani hali toh abu biyu ne zai fari ko ya ruɗe ya rasa samin mafita
kokuma yayi overreacting har ya zamo ya kasa treating abin da ke damin sa ya je yana treating wani abin
daban.

Sai da ya ga ba sarki sai Allah sai ya tuno da ana yayyafawa sumamme ruwa dan farfaɗar da shi..

Da sauri ya tafi kitchen dake apartment ɗin ya ɗebo ruwa da zuwan sa ya shiga yayyafa mata yana kiran
sunan ta sau shida yana yayyafa mata ruwan sannan ta ja numfashi a hankali ta yi ajiyar zuciya sannan
ta buɗe idanun ta ta sauke su kan fuskar sa sai ya shiga tambayar ta

"Me ke damin ki Bilkisu?baki jin daɗi ne dama kokuma sudden collapse ne"?tsakanin sa da Allah yake
tambayar ta sai ta shiga duhu ta kasa tantance reality ne ko kuma wild dreams ne Zaid asking her abin da
ke damin ta strange..

Sai tayi faking facial expression nata ta saka fake grimace ta ce

"Bana ɗan jin daɗi ne Zaid but..,,na ji sauƙi yanzu,thanks for the care".

Ɗan boko ne dan haka sai ya ce

"A'a Bilkisu ban yarda ba you collapsed suddenly out of the blue sannan ki ce min kin ji sauƙi...no no
way dole ki zo muje a duba ki a asibiti ban yarda ba"zata yi magana ya miƙe yana faɗin

"And that's final bana son jin komai daga bakin ki ki zo mu tafi asibiti a duba ki bana son taurin kan nan
naki"ya faɗa yana wani tsare gida irin he is the boss ɗin nan sai abin nasa ya bata dariya har ta ɗan fidda
murmushin ta fili wanda ya saka sa kallon ta yana mamakin dalilin ta na mai murmushi sai ya saku yana
kallon ta kafin yace

"Hey baby doctor listen up...,am the boss here ba a gida muke ba daga ni sai ke a nan ƙasar in ban kula
da ke ba Ammi ba zata yafe min ba dan she warned me not to make you feel uncomfortable and
insecure dan haka dole ne in kai ki asibiti"!.

Yayi maganar ne da iya gaskiyar sa amma sai ya ga ta saka dariya dan dariyar ya bata sai ta ce
"Boss huhh??toh me zai hana ka kasa treating nawa a nan ba sai mun tafi asibiti ba i guess hakan ya fi ai
ko the boss"..

Sosai ya ji mamakin moral da ta samu har take daring nasa sai ya karkata wuyar sa ya ce

"Kenan kina daring na"??ta ce cikin kafe sa da ido cikin idanun sa



"Ina ganin haka"ta faɗa tana ɗage gira ɗaya sama yayin da take bin sa da kallon in ka isa tana
murmushi..abin da tayi ne ya saka sa jin dole ya gyarawa yarinyar nan tunanin ta dama ɗaga mata ƙafa
yake yi dan ganin yadda take kula da shi but yanzu tana son ta ƙure sa.

Takawa yayi har gaban ta ya shiga durƙusowa har ƙasa yana kallon ta tana bin sa da ido tana kallon abin
da yake yi,yana kai gwiwar sa ƙasa ya kawo hannun sa ya kai saman kumatunta a hankali ya shiga yawo
da hannun sa a kan fuskar ta,ita dai tana kallon sa har ya kawo kan bakin ta ya sauke hannun,yatsar sa a
kan lips ɗin ta yana jujjuyawa kawai sai ta tsinci kan ta cikin wani hali ta shiga lumshe idanun ta har ta
hau sauke ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba sai ta ji ya dakata daga yi mata abin da yake yi hakan ya saka
ta buɗe idon ta ta sauke kan sa.

Shima ita yake kallo da wani irin siga wanda shi kaɗai ya san ma'anar hakan bai furta komai ba yana kan
kallon ta kamar bai san ta ba haka itama tana kallon sa,idanun ta har sun fara cikowa da hawayen
tausayin kanta dan wani salon son sa ne ke fizgar ta kai tsaye tana ji a jikin ta kamar nan ba da jimawa ba
zasu rabu rabuwar da Allaj kaɗai ya san lokacin haɗuwar su.bata kai ga saukar da hawayen ta ba sai ta
jiyo muryar sa a hankali cikin sanyi yana tambayar ta

"Kina daring ɗi na ne Bilkisu"??yayi mata tambayar yana mai kallon bakin ta zuwa ƙwayar idanun
ta.tsabar sanyin maganar da izzan da ya haɗa cikin muryar sa yayin da yake furta kalamomin bakin sa ya
saka ta jin faɗuwar gaba mai tsanani wanda ya haifar mata da fargabar gaba mai ƙarfi dan tana jin kishin
sa a ran ta tana tsoron rasa sa sai ta saka idanun ta cikin nasa idon ta buɗe baki ta fara magana

"Eh...,,,Zaid...,i..amm...dari...nn..,,.bai bari ta kai ƙarshen maganar ba ya haɗe lips ɗin su wu ɗaya
attraction ne mai gauraye da tsantsar affection ya shige su su duka sai suka lumshe idanun su at the
same time this being their first time to experience such thing sai suka rasa sukuni a zukatan su daga ita
har shi heartbeat ɗin su yayi increasing yayi elevating sosai dan da za'a gwada su da stethoscope toh
lallai ƙarar *_"Lup Dup"_* da ventricles na heart ɗin mutum ke bayarwa za'a tantance banbancin ƙarar
da tasu ke bayarwa dan a haɗe ya gauraye ya rinƙa bada ƙarar at the same time hankulan su a tashe
yake bata taɓa yi ba haka shima bai taɓa yi ba abin ya zamo masu alien a duniyar su.

For some seconds lips ɗin su na haɗe ba tare da sun yi komai ba haka idanun su na lumshe kamar masu
bacci sam basu so su dawo duniyar a haka suka ɗau lokaci sai daga baya tayi ƙoƙarin buɗe idanun ta a
hankali kamar mai tsoron gamuwa da mugun abu.

Tana buɗe idanun ta sauke kan nasa lumsasdun idanun da ke rufe ruf gab da nata idanun tana ganin
yadda yake fidda numfashi in-out and she can say that tun da suke basu taɓa yin kusanci da juna kamar
yau ba and the only time she sees him panting like was once ranar da yayi surgery shi kaɗai ba tare da
assistance ba wato ranar da ya ƙi nemar taimakon ta alhalin gata ga shi a cikin theater suit ɗin.

Lips ɗin su na kan maintaining position da suka masu wato lock up position,sai ta fara jan nata lips ɗin
baya baya har ta raba da nasa lips ɗin sai kuma ya buɗe lumsassun idanun sa da suka komo kamar
wanda ya tashi daga bacci babu abin da ke cikin ƙwayar idanun nan nasa sai buƙatuwa,tsantsar buƙatar
mace ne ke taso mai amma abin mamakin shine bai san hakan ba bai san yana buƙatar mace ba duk
tunanin sa strange illness ne ya same sa ba tare da ya sani ba dan ya san lafiyar sa ƙalau kuma shi so
yake ya nunawa Bilkisu kuskuren ta na daring nasa and he wanted using a positive reenforcement in her
but he end up hurting his self ko ina dalilin hakan??

Cikin lumana ya raba fuskokin su haɗe da tashi daga tsugunnen da yake hankalin sa a ɗan tashe dan ya
ji abin da bai taɓa ji ba a iya rayuwar sa,kansa a ƙasa ya shiga gyara collar na rigar sa da ya ɗan canza
position ita kuma bin sa da ido take yi tana son tantance abin da ta karanta a google sai dai bata ida
analysis ɗin ba ta ji muryar sa na faɗin

"Let's go"daga haka ya fita dan yana so ya bar ta ta ƙara kimtsawa..bayan fitar sa sai ta shiga yiwa kanta
murmushi tana bin lips ɗin ta da yatsar ta tana tuno abin da ya faru tsakanin su was that a reality act ko
dai mafarkin ta ne sakamakon saka abin da tayi a ran ta gashi tayi googling ɗazu ta ga abin da take
buƙata abin da ya faru da su na ɗaya daga cikin alamomin da ta karanta but in their case can she call that
as a strong sign?girgiza kai tayi tana jin kunyar kanta sai ta tashi ta gyara rigar jikin ta haɗe da gyara
gyalen ta sannan ta fita.



A step na huɗu ta same sa tsaye yana latsa wayar sa sai ta tsaya kallon sa again kamar bata san sa
ba,imagining take yi ya rayuwar su zai kasance in har Zaid na jin abin da take ji?ko zai nuna ko zai barwa
kan sa?..

Shi da kansa ya gane presence ɗin ta saboda ƙamshin ta ya iso sa sai ya ɗago idanun sa ya sauke a kan
ta wani irin munafukin kallo yake bin ta da shi wanda yake ganin kamar bai da lafiya ne in ba haka ba ta
yaya zai tasa ɗiyar mutani a gaba yana kallon ta he thinks he need to see a physician..

Ƙarasa saukowa tayi tana ɗan aika mai da murmushin da bata san tana yi ba sai da taga shima yana
mata sannan ta gane cewa ita ce ke yi shi yasa shima ya mayar mata da martani.

A sukune suka ƙarasa saukowa har suka bar hotel province,.

Yau basu tafi wannan eatery ɗin ba wani nan kusa suka tafi inda suka ci light dinner tsaf suka kammala
suka fito pretending not to remember what happened between them earlier on,a hanyar su ta komawa
hotel ɗin ne ya canza ra'ayin sa ta hanyar ce mata trekking zasu yi sai ta juya ta gwalalo mai idanun nan
nata

"Trekking kuma?sai ta ɗan ɓata fuska kafin ta ce ni kam a'a ban iyawa kawai mu tafi a cab am tired
already"surprising look ya bita da shi bakin sa buɗe yana murmushin mamakin ta ita kam ko a jikin ta
tsakani da Allah take dan kam ta san tata ta ƙare in har basu koma gida da wuri ba cramps ɗin ta zai ƙaru
ta ga azaba a gaban sa ita kuma ba haka take so ba..

"Me kike nufi?in fah ban manta ba ke doctor ce mai kaiwa awa huɗu zuwa shida a tsaye kina surgery
toh why the sudden change and weakness?just trekking na how many minutes da zamu yi mu koma kina
faɗin baki iyawa"?ƙyale sa tayi har ya dire ayar maganar sa ita kuma tayi picking up

"Zaid i can't..gaskiya bazan iya ba bana jin daɗi and anything can happened if care is not taking i can't
afford seeing myself being demoralized in front of you i just can't so please ka min rai mu shiga cab mu
koma gida"har ta gama kawo dalilin ta shi linking yake yi da issues na crises nata dan garin akwai alamun
saukowar ruwa any moment but ai suna iya kaiwa gida ruwan ma bai fara ba dan haka sai ya janyo ta
kusa da shi yana mai ce mata.

"Kar dai ki ce min har kin fara tsoron crises naki ne?kar ki damu har mu kai gida babu abin da zai faru
trust me"girgiza kai ta shiga yi tana jin pains ɗin na increasing intensively ta shiga ce mai

"Baka gane ba kuma ba ganewa zaka yi ba Zaid ni na san abin da ke dami na ba tsoron crises nake ji
ba.."kasa ƙarasawa tayi dan wani irin unexpected cramp da ya riƙe ta hakan ya saka sa kasa furta abin da
yake son furtawa sai ya hau tambayar ta ko menene ke damin ta amma ta kasa basa amsa ƙarshe ma
faɗi ta kusa yi but yayi nasarar grabbing nata ya riƙo ta firmly ya hau girgiza ta but idanun ta har sun fara
lumshewa alamar sume mai zata kuma yi for the second time a 360° ya dakatar da mai cab ya shigar da
ita sannan ya shiga a rikice ya ce da mutumin ya wuce da su asibiti.



Tafiyar 15minutes suka yi ya kawo su wani asibiti inda da shigar su ya tsaya a emergency ya kirawo
masu kula da lafiyar dake wurin suka kawo mai agaji aka shigar da ita ciki dan duba ta shi kuma ya hau
yin zirga zirga a tsakankanin ɗakin yana iya hango su a ciki.

Almost 25minutes sannan doctorn ta fito haɗe da kiran sa gefe ya tafi jikin sa na bashi wani abin gaban
sa na faɗi but sai ya ga ta ɗan murmusa ta ce da shi

"She is your wife"?a cikin tsantsar damuwa yake dan haka bai san lokacin da ya shiga girgiza mata kai ba
sai ta ce da shi.

"She is fine and she will be fit as soon as she wakes up just experiencing her cycle cramps i guess you
know that already,so right now we were able to stabilize her and she is calm by 9 you can take her home
if she wakes up because she need yo rest adequately but fir now,she is good"godiya ya mata sannan ta
tafi shi kuma ya koma ya shiga ciki haɗe da zaman jiran ta har ta farka,shu tausayi ma take ba sa ya
ɗauka ba duka mata ke shan irin wannan wahalar ba sai gashi bayan baby sis ɗin sa Bahajjatu a yau ga
matar sa ma na experiencing cycle pains hala ma shi yasa ta yi collapsing ɗazu..

Tausayin ta ne ya kama sa sosai dan haka ya shiga yi mata fatar samin lafiya as soon as possible..
Awar sa ɗaya yana zaune yana jiran farfaɗowar ta amma bata farka ba sai ya bar inda yake zaune ya
dawo kusa da ita ya tsura mata idanu yana mata kallon tausayi a ce da ran ka da lafiyar Ka amma kayi
losing consciousness naka har tsayin awa ɗaya he really felt bad and he curse this pains..

Yana kan kallon ta yana jin tausayin ta sai ya ga ta fara mutsu mutsun farkawa,da sauri ya kuma
matsawa kusa da ita yana mai riƙo hannun ta cikin nasa har dai ta gama buɗe idanun ta ta ga inda suke
ta kalle sa zata yi magana ya riga ta

"Kar ki yi magana,,am sorry i couldn't understand you ɗazu har sai da na bari kika zama helpless am so
sorry,doctor ta ce zamu iya tafiya in kin farka dan kina buƙatar hutu shall we?can you walk or i should
support you"?da iya gaskiyar sa yake nuna kulawar sa gare ta sai ta girgiza mai kai alamun zata iya tafiya.

Taya ta tashi yayi sannan suka fito haɗe da yi ma doctorn godiya haɗe da yi mata sallama sannan suka
fita.



_*35 minutes later*_



Tana kwance ya shigo ya same ta haɗe da tambayar ta ko akwai wani abin da take buƙata ta ce mai a'a
sai ya mata sai da safe sannan ya koma ɗakin sa but sai me??he couldn't sleep he kept on thinking about
her yana ji kamar he is connected to her dan haka ya tashi ya bar ɗakin nasa ya nufi nata ɗakin,ko da ya
isa har ta fara bacci but he can't leave her all alone what if ta farka cikin dare tana buƙatar wani abin
kuma babu mai yi mata kusa.

Da wannan tunanin ya nemi wuri ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta cikin nasa yana ɗan murzawa
duk tausayin ta ya ishe sa he can't wait to see her fit again dan mood nata duk ya canza har maganar da
suke ɗan yi basu yi ba wannan ciwo ai wahalarwa ne.

Shi kaɗai yake ta zancen zuci in yayi ya kalle ta ya ji sabon tausayin ta na kuma shigar sa haɗe da wani
abin da shi bai san ko menene ba..



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*



Please Login or Register in order to submit comment